Showing 303001 words to 306000 words out of 432432 words

Chapter 102 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

hannu cikin aljihun wandonshi ya ɗauko wayarshi,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin lalubo number Abusufyan,ya danna mashi kira ta soma ringing,
  Hajiya Azeema da Alexandra duk sun bi sun ruɗe,
  "Ni babban tashin hankalina ma kada yaran nan su illata kansu,Wlh abun ya tsoratar dani sosai ya tayar mun da hankalina,"Hajiya azeema ce tayi maganar,fuskarta tamkar zata fashe da kuka,
  Hafsat kuwa tana acikin main palour ɗin,Sae faman kuka takeyi,kwatsamm taji takun takalmi,da sauri takai idanunta wurin MARSHAL OMAR ne ke saukowa daga upstairs da gudun gaske ta tunkare shi tana fadin"Ya Omar,gasu jahad can suna faɗa acikin ɗakinsu,kuma sun kulle ƙopa,anyi anyi su buɗe sun ƙi su buɗe....."
  Jin wannan maganar yasa hankalin Omar mugun tashi,da sauri ya nufi bedroom ɗin nasu,lokaci guda kowa na gidan labarin abunda ke faruwa yaje musu,hatta su Junaid dake ɗakunansu suna bacci sae da suka tashi,su fawan twins,dasu Irfan,hada Dr hariis da gwaggon katsina,da Ammi,dukkansu kowa fa amma banda Sgr dake a bedroom ɗinshi,
  A ƙopar ɗakin nasu sukayi cirko cirko,Abusufyan yafi kowa shiga damuwa bawan Allah,kamar ya zauce haka yake bugun ƙopar ɗakin nasu yana roƙonsu akan su daina kokoyin da sukeyi suzo su buɗe mashi ƙopa amma shiru babu wanda ya tanka mashi,Haka Marshal Omar ma,Tamkar zai 6alle ƙopar haka ya dinga bugun ƙopar ɗakin nasu,amma duk abanza,Junaid kuwa tuni ya fashe da kuka,yadda kasan wani ƙaramin yaro,
  Cikin shessheƙar kuka Gwaggon katsina tace"nashiga uku..Wayyo Allah na,wlh nasan duk sharrin Ya sayyadine bazai barsu hakanan ba,yanzu haka shine ya shiga tsakaninsu,Ya Allah kayi mana maganin wannan baƙin shaiɗanin....'kuka takeyi hada majina,
   Lokaci guda sukaji shiru tsit cikin bedroom ɗin nasu babu wani gunjin kuka,hakan ya tabbatar masu da cewar wani mummunan abunne ya faru dasu,nan fa kowa ya shiga kallon kallo,yayin da zuciyoyinsu keta bugawa da karfi,
   Jiki asanyaye Abusufyan ya zame ƙasa,tare da aza hannayenshi saman kanshi,yayin da bakinsa ke furta kalmar"Innalillahi wa'Inna ilaihirraji'un,'
  "Abba,ina ganin kawai a 6alle ƙopar," acewar kanal yousouf,
Omar yace"Nima abunda nake tunani kenan,amma ƙopar fa ta cije sosai,na buga na buga amman ko motsi batayi,duk irin ƙarfin da nake dashi,"
  Cikin shesshekar kuka junaid yace"Bari naje na ɗauko zarto sai a datse kubar,"
   Ya ambaci hakan tare da watsawa da gudu ya nufi weapons Room ɗinsu (ɗakin ajiye makamansu,"A rufe ya samu ɗakin,sam ya manta cewar key ɗin yana a wurin babban yayansu,sae da yayi arba da ƙopar a rufe sannan yasha kwana ya dawo da gudu ya haye upstairs ɗin,
  Faɗawa part ɗin SGR yayi,a rikice ya shiga bedroom ɗinshi,a lokacin Sgr na kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi yana bacci,
  Junaid baibi takanshi ba saboda a ruɗe yake,side drawer ɗinsa ya tunkara,ya shiga bubbuɗeta yana neman key ɗin,duk inda ya duba babu key ɗin,saman gadon ya hau,yana kiran sunanshi"Babban yaya!Babban yaya!pls wake up!babban yaya ka tashi dan Allah,'
  Cikin bacci rafayet yaji muryar junaid dake ta faman kiran sunanshi,a hankali ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka kan fuskar junaid,ganin hawaye jaga jaga a fuskar junaid yasa Sgr yin hanzarin miƙewa daga zaune,hankalinshi aɗan tashe yake kallon junaid,da wata irin kasalalliyar murya ya ambaci sunanshi"Junaid!what are u crying for?meya faru ne?. 
   "Babban yaya,key nake nema na weapon's room,inaso in ɗauko saw ne,za'a 6alle ƙopar ɗakinsu Sehrish"
  Cike da mamaki Sgr yace"For what reason?wani abu ya samu door ɗin da za'a 6alleta"?
  Ganin bai fahimci inda zancen nashi ya dosa ba,yasa shi yi mashi bayanin abunda ke faruwa,
   Saukowa Sgr yayi daga saman gadon nashi,junaid na biye da bayanshi suka fito daga part ɗin nasa,da sauri da sauri suke saukowa down stairs,
   Lokacin da suka shigo Corridor(doguwar hanyar) da ɗakunnansu sehrish suke a jere,Hankalin Sgr ya ɗan tashi musamman daya ga dandazon matasan gidan,ga kuma su Abbansu kowa atsaye cirko cirko,fuskokinsu sun nuna alamun damuwa atattare dasu,'
  Abbansu na ganinshi yayi saurin ruƙe hannunshi yana fadin"Yawwa rafayet,nasan zaku iya kai da Omar,dan Allah ku haɗu ku 6alle ƙopar nan,ko mun samu muga meke faruwa aciki,'
  A hanzarce kowa ya dare ya basu wuri,da iya ƙarfinsu Na ƙarshe suka daddage suka kaima ƙopar wani irin kwakkwaran bugu ji kake daraamm!nan take Sakatar ciki ta zame da kanta,ƙopar ta buɗe,gaba daya suka afka ciki,
  Ba ƙaramin girgiza sukayi ba,gaba dayansu musamman Abusufyan,abunda suka gani yayi matuƙar tayar masu da hankali,Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!!!wannan shine abunda suke ambato a bakunansu,
  Sun tarwatsa komai na bedroom ɗin nasu,ɗigon jini jinin da suka gani shi yafi komai tayar masu da hankali,
Jahad ce kwance ƙasan gadon saman tiles,damtsen hannunta duk sawun cizo ne,wurin duk ya farfashe,hatta saman kumatunta cizon ne,daga can saman gadon kuwa hosana ce,baje hannunta dafe da kanta ta toshe kunnuwanta sae faman mutsu mutsu takeyi da ƙafafuwanta,alamar idonta biyu,Sehrish kuwa basu san ina ta lula ba,
  Zubewa Abusufyan yayi agaban Jahad dake kwance,hannu yasa yana jijjigata yana ambaton sunanta saboda ya gane itace,hawaye sae faman sintiri sukeyi akan fuskarshi,
   Jikin kowa yayi sanyi,zukunnawa Abbansu yayi agaban Abusufyan din yana kallon jahad dake kwance,Sawun haƙoran dake asaman fatar jahad ya tabbatar mashi da cewar faɗa ne ya 6arke a tsakaninsu har sukayi kokoyin nan,
   "Ina tunanin suma tayi ne,wani ya ɗauko mun ruwa dan Allah,"Abbansu ne yayi maganar,da sauri fawan ya fuce daga dakin,ya nufi babban falo don ya ɗauko masu ruwan da za'a yayyafa mata,
....a hankali Sgr yake bin ɗakin nasu da kallo,sunyi mashi kaca kaca,damben daga saman gadon nasu ya fara,Hatta bargon lullu6arsu duk sun jefo shi ƙasa,zagayawa yayi ta dayan gefen gadon,6angaren hannun hagu,tunkan ya ƙarasa ya hango ƙafafun mutun,hakan ya tabbatar mashi da cewar cikon ta ukunsu ce,ta wuntsila ta baya,lokacin daya ƙarasa wurin a kwance ya samu Sehrish,gefen bakinta ya ɗan fashe,ga kuma sawun haƙora asaman ƙirjinta,da kuma damtsen hannunta,zuƙunnawa yayi agabanta yana ƙare mata kallo,
  "Rafayet!wacece anan?ko cikon ƴar ukun tasu ce"?Ishaq ne yayi maganar ganin rafayet ɗin zuƙunne a wurin,
  "Itace," ya bashi amsa atakaice,da sauri Abusufyan ya miƙe tare da sauran suka nufo wurin don suga a wani hali take ciki,
  Tun kafin su ƙaraso Sgr yayi saurin kai hannunshi gaban rigarta yaja rigar ya lullu6e mata ƙirjinta daya fito sosai,
  Fashewa da kuka gwaggon katsina tayi tana fadin"Wayyo Allah ƴa'ƴan Abusufyan ɗina!ni nasan cewa ba yin kanku bane,Wlh sai Allah ya saka maku,Bayin Allah sunji jiki,kowanene yayi masu wannan ɗanyen aikin,jibi yadda aka ciccije masu fata,Yanzu haka ya sayyadine yazo masu da suffar kura yayi masu wannan aika... aikan,' Harris ne ya katseta da cewa"pls gwaggo kibarmu muji da abunda ke damunmu idan ma kina magana ƙara masu zafin ciwon kikeyi,
  Jin haka yasa tayi saurin rufe bakinta,tana cigaba da matsar kwalla a idonta,
   "Abun ya ɗaure mun kai!garin yaya haka ya faru?gaba daya kowannansu sawun cizo ne a fatar jikinsu",Abbansu junaid ne yayi maganar,a yayin da suke tsaye gaban sehrish,Sgr kuma na a zuƙunne,
   Hafsat ce ta basu amsa da cewa"lokacin da nazo ƙopar dakinsu,naji sautin Kukansu acikin ɗakin da kuma sautin bugu kamar suna dambe a tsakaninsu,ina tunanin cewa faɗa sukeyi a tsakaninsu,'
  Jinjina kai marshal Omar yayi tare da cewa"Tabbas sunyi sa insa a tsakaninsu ne har abun yakai ga fada,Kuma wannan cizon dake asaman fatar jikinsu,ba kowa bace tayi masu shi ba fa ce HOSANA!saboda nima ta ta6a cizo na a kwanakin baya,da ranta ya 6aci a asibiti,ta cije ni kuma ba ƙaramin zafi naji ba a lokacin,"
  Abba yace"No wonder!in kuka lura babu sawun cizo a fatar jikinta,indai itace kwance asaman gadonsu,ku kalli jikinta dakyau,kuma bata jigata ba,kamar yarda ƴan uwan nata suka jigata,"
   Suna cikin maganar nan,Fawan ya shigo hannunshi ɗauke da robar ruwan daya dauko masu a fridge,da sauri kanal yousouf ya kar6i bottle water din,ya 6alle murfin,tare da tarbo ruwan a tafin hannunsa na dama,ya watsa shi a fuskar jahad,Nan take taja dogon numfashi tana ambaton sunan Allah abakinta,ajiyar zuciya suka shiga saukewa,da sauri Abusufyan ya dawo wurinta,tare da zukunnawa agabanta,ya ɗago da ita ajikinshi yana ambaton sunanta"Jahad!Jahad!"koda jahad ta buɗe idanunta tayi tozali da fuskar Daddynsu saita fashe da matsanancin kuka tana cewa"daddy kaga abunda hosana tayi mana?kawai daga magana ta hau bugunmu ni da Sehrish,duk tabi ta gartsa mana ciwo a fatar jikinmu....'tana magana hawaye na zuba a idanunta,
  Runtse ido Abusufyan yayi tare da buɗesu a hankali,abun ba ƙaramin ta6a mashi zuciya yayi ba,
  Hannu Omar yasa tare da kar6ar Robar ruwan dake hannun Kanal yousouf ya taka izuwa inda Sgr ke a zuƙunne ya miƙa mashi ita,Kar6a Sgr yayi tare da kur6ar ruwan abakinshi,ya fesar dashi akan fuskar Sehrish,a firgice ta farka gami da mikewa zaune tana faman zazzare idanunta,one by one tabi su da kallo,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin Sgr,ga kuma su hajiya azeema tsaye duk akanta,tafin hannuwanta tasa tare da rufe fuskarta,tana kuka,
   "Wani ya ɗauko min FA box a medical room"Sgr ne ya ambaci hakan,da sauri irfan ya fuce daga ɗakin don zuwa ɗauko akwatin,ruƙo hannun Sehrish Hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita gefen gadon,"sannu kinji,yi shiru ki daina kuka,"cikin lallashi takeyi mata maganar,
     Hawa saman gadon nasu Hafsat tayi,tare da kai hannunta ta ɗago da hosana ajikinta,sae faman kerma jikinta yakeyi,ciwonta ya motsa,da alama an rabu da shan magani,duk a tunanin su abun yayi sauƙi,ashe da sauranta,tabbas hosana tana buƙatar ganin likitan mahaukata,
  A faɗace Omar ya daka masu tsawa gaba dayansu yace"wai duk menene yajawo hakan!ba zaku buɗe baki kuyi ma mutane bayani ba!"
   Cikin shessheƙar kuka Sehrish tace"Hosana ce,tunda sanyin safiya tafarka,tana raira mana waƙar takusa aure ƙara faɗa breaker,kuma hada kiɗa take raira waƙar duk ta takura kunnuwanmu,har muka farka daga bacci,Don munyi mata faɗa shine ta naɗe hannun rigarta ta hau mu da bugu da cizo kamar ta samu jakuna....'
  Cike da mamaki kowa ke kallon sehrish dake kora masu bayani,Ishaq yace"Wai yanzu duk don saboda wannan ku ka kusa illata junanku?gaskiya akwai gagarumar matsala babba ma kuwa,'
   Abbas yace"dama da wuya kaga ƴan biyu ko ƴan uku suna zaman lafiya a tsakaninsu,zakaga suna tsananin son junansu,amma ta wani 6angaren basu jituwa,don akwai labarin dana ta6a ji shigen irin wannan daga kokowa suka kashe kawunansu,"
  Jin wannan maganar ta Abbas ya ƙara daga masu hankali,Abba yace"in sha Allah,ba zamu bari hakan ta faru ba!tunda abun har yakai ga faɗa da jima juna ciwo,dole a raba masu wurin kwana,shine kawai mafita,"
  "Abunda nake ƙokarin cewa kenan"acewar hajiya azeema,
  Ammi dai abun yafi ƙarfinta daga ita har Alexandra da hajiya Saratu suna atsaye sun zuba ma sarautar Allah ido,Lamarin yaran yayi matukar daure masu kai,
   Dawowa cikin ɗakin nasu Irfan yayi hannunshi ɗauke da First aid box ɗin,ya ƙaraso tare da miƙa ma Sgr akwatin,hannu yasa ya kar6e shi tare da ajiye shi a ƙasa,
   Sannan ya zauna,daga gefen gadon,suna fuskantar juna shi da sehrish,wadda ke ta faman shessheƙar kuka,wani irin kallo daya jefa mata,tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa,
   "Close ur eyes,"da sauri ta rufe idanunta kamar yarda ya umarta,tana ji yasa mata audiga a wurin ciwon yana goge mata jinin,a sannu ya shiga yi mata dressing din ciwon da taji,bayan ya kammala da ita,Abusufyan ya ruƙo hannun jahad,ya dawo da ita gefen Sgr ya zaunar da ita,cikin lokaci ƙankani Sgr ya kammala yi mata dressing ɗin itama,
   "Ita kuma hosana ya zamuyi da ita?kodai asibiti zamu kai ta?Acewar Abusufyan,
  Omar yace"Rafayet zai iya duba mana ita anan gida ma"
   "Omar am not a psychiatric doctor,though i've experience about their work,zan iya duba ta,Amma a ƙa'ida,psychiatric doctor ya kamata yayi checking ɗinta,bazan shiga aikin da banawa ba,"kaji turawa,ƴan bin ƙa'ida,
  Jinjina kai Omar yayi fuskarshi ɗauke da murmushi,ya juya tare da kallon Dr harris dake tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi yace"Bismillah,"yayi maganar yayin da yake yi mashi nuni da hosana wadda ke kwance ajikin hafsat,idanunta sun birkice sae farar kwayar idon kawai,yatsunta kuwa sae faman kerma sukeyi,hada na kafafunta,
  Kallonta kawai Dr harris yayi batare daya ta6a jikinta ba,ya faɗi sunan allurar da take buƙata ayi mata,
  Da sauri Omar ya ciro wayarshi tare daddana wasu numbobi,ya kira Dr Emran na asibitin Sgr,kiran na shiga emran ya ɗauka,don haka Omar ya miƙa ma Dr harris wayar don suyi magana,
  Bayan sun kammala wayar,ya dago tare da kallon Marshal yace"Ya sanar dani cewa within 15 mins zaizo tare da allurar da kuma medicine ɗinta,"
Omar yace"Okey,Allah ya kawo shi lafiya,

"Ku kwanta saman gadon,itama mara lafiyar a kwantar da ita before doctor din yazo,Azmee ki shirya masu breakfast dinsu,yanzu haka ma Yunwa ce ke Cinsu,shiyasa su kayi wannan damban," sae yanzu ammi ta tanka masu,saboda tsabar gatanci maimakon asamu wanda xaiyi masu faɗa da tsumagiya a Zane su, amma kowa ya rufe ido,sae lalla6a su akeyi,diyanso kenan,shalelen abusufyan,

miƙewa sgr yayi daga zaunen da yake,sannan yayi masu nuni da su kwanta,a hankali kowaccensu ta kwanta yadda kasan waɗanda suka yi wata suna Jinya don sunji jiki,a hankali Hafsat ta janye Hosana daga  jikinta ta kwantar da ita,har lokacin bata dawo hayyacinta ba,sae faman fari takeyi da idanuwanta,yatsun hannunta dana ƙafafunta sae kerma suke yi,

Haɗa baki su fawan su kayi wurin yi masu ya jiki,kafin daga bisani matasan  suka fita daga ɗakin nasu tare da Ammi da hajiya saratu,Ya rage daga Sgr sae Marshal Omar,Hajiya azeema da kuma abusufyan da kuma gwaggwon katsina sae hafsat,Azmee ta wuce kitchen don ta shirya masu breakfast ɗinsu,within 15 mins,Dr Emran ya ƙaraso gidan,a cikin motarshi yazo,tun a waje ya haďu da dr Harris tare da kanal Yusuf a tsaye,dama shi suke jira,fitowa yayi daga cikin Motar hannunshi dauke da Ledar maganin Hosana da kuma injection din da xa'ayi mata,gaisawa suka fara yi  fuskar kowannansu dauke da murmushi,canal Yusuf ne ya kar6i Ledar da Emran din yaxo da ita,sun so ya shigo daga ciki suyi breakfast atare dashi,Amma ya sanar dasu uzurinshi,hakan yasa suka ƙyale shi,sallama sukayi da juna sannan suka koma ciki da sauri,

Cikin bedroom din nasu,Dr Harris ya shigo ganinshi yasa Omar da Sgr suka bashi wuri donya ƙarasa gaban gadon,batare da 6ata lokaci ba,ya ɗura ruwan allurar acikin syringe,aikuwa kamar akan idon Hosana yana kai hannu zai ruƙota ta zabura,tashiga yan buge²,ganin haka yasa sgr da Omar matsawa kusa dashi,sae da suka rurruketa dakyar aka samu yayi mata allurar,yana  kammala yi mata allurar,nan take zufa ta Shiga tsastsafowa daga jikinta,Kafin wani lokaci tuni bacci yayi awon gaba da ita,hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yayi ba,
  Juyawa dr Harris yayi tare da kallonsu Omar yace"in sha Allah,Zata ji sauƙin jikin nata,sannan idan ta farka,ga medicines ɗinta nan,bayan taci abinci,akwai direction ajikin kowani magani sae a duba,idan za'a bata,"
Amsa mashi sukayi da toh,Omar yace"aikin ka na kyau dr,"sannan ya mayar da idanunshi kan hajiya azeema tunkafin yayi mata magana tace"Zan kula dasu,idan tafarka zan bata maganin da yardar Allah,"murmushi ya saki tare da juyawa ya kalli sgr,"Muje ko?time karya ƙure mana,naga yanzu har 12 ta kusa,nan da wani lokaci xa'a shafa fati.....'bai ƙarasa maganar ba ganin irin kallon da rafayet ya jefa mashi,Dariya Omar yayi yana faɗin"Sorry bro,kada ranka ya 6aci mana,Yau fa ranar farin ciki ce agaremu,murmushi yakamata a gani akan fuskokinmu,ɗanyi murmushi mana,cike da zolaya Omar keyi mashi magana,shi kuwa Namijin sae faman tamke fuska yake yi,daga bisani suka fita daga ɗakin atare da dr harris,

Komawa hajiya azeema tayi tare da samun wuri gefen gadon ta zauna tana kallonsu,duk sun rufe idanunsu kamar masu yin bacci,
   "Bismillah gwaggo ku zauna mana,"azeema ce tayi maganar tare da yi mata nuni da saman bedside drawer dinsu,jiki asanyaye gwaggon katsina ta karasa ta zauna saman drawer din,ita dae har  yanzu bata yarda Cewar Hosana ce ta ciccijesu ba,
   "Azeeme yanzu kema kin yarda cewa yarinyar nan itace da kanta ta gartsa ma ƴan uwanta cizo har haka?Ni nafi tunanin cewa Ya Sayyadine yazo da suffar kura yayi masu wannan aika aikar,mutumin nan fa ba ƙaramin Taƙadari  bane,banbancinshi da shaiďan kaho ne kawai da babu,"wannan maganar da gwaggon katsina tayi ba karamin dariya tabasu ba,
   Girgiza kai hajiya azeema tayi fuskarta ɗauke da dariya tace"gwaggon shagali,ae in ma shine to ta Allah ba tashi ba,ki kwantar da hankalinki,Sayyadi yake kowa,ba abunda ya isa yayi masu bi'iznillahi,"
  Washe Baki gwaggo tayi da alama taji dadin abunda Azeema tace mata,
  "Allah yayi mana maganin la'ananne,"
Azeema ta amsa mata da ameen,
Sae wuraren karfe sha biyu da rabi Hosana ta farka jikinta da sauki sosai,kuma tana bude ido ta fashe da kuka tana ambaton  sunansu sehrish da jahad,sae da aka nuna mata su sannan hankalinta ya kwanta,

Tuni azmee ta kawo masu breakfast ɗinsu acikin dakin,da taimakon Hafsat da kuma hajiya azeema suka ci abincin,bayan sun kammala cin abincin,Hajiya azeema da gwaggo suka bar dakin,ya rage saura hafsat ita kaɗai,gyara masu bedroom din nasu ta Shiga yi,komai yadawo normal Ba kamar daba da suka hargitsa dakin,bayan ta kammala gyaran ɗakin,wuri tasamu saman side drawer dinsu ta zauna tana kallonsu,
  "Hosana ki ji tsoran Allah,jibi yadda kika raunata mu sae kace ba yan uwanki ba,"jahad ce tayi maganar ranta a6ace,
  A kule hosana tace"ae laifin ku ne,saboda me zakuyi mun rashin kunya?ni ba yayarku bace?oumma tace ni ce babba acikin ku,saboda majnun ya faɗa mata cewa ni ce na fara zuwa duniya,sae da na shaƙi iskar duniya da minti biyar sannan ke kika zo daga ke kuma sae waccen uwar tsiwar" "dakyar take magana,saboda har yanxu jikin nata da sauranshi,
  Guntun tsoki sehrish taja"karki kara ce mun uwar tsiwa,in ba haka ba zan nuna maki kalar nawa haukan,mara mutunci kawai,kuranya mai cin naman ýan uwanta..."
  Tunkan ta ƙarasa maganar,da Sauri jahad ta toshe mata bakinta,"Dan Allah ya isa haka,da alama baki ji jiki ba,shiyasa kike ƙoƙarin tsokanota,salon Kija mana jinyar  ta koma a gadon asibiti,"
   Hafsat dake zaune tana sauraronsu,sae faman kunshe Dariya takeyi,

*Boss Bature*

  ❤🤍❤


Gaba ďaya matasan gidan,kowa ya Shiga yin wankan juma'a,Kafin wani lokaci duk sun shirya halarta Sallar Juma'a tsaf,kowa ya ɗauki wanka na mutunci wankan shadda,abun sai wanda ya gani,bakowa ne yasan da zancen ɗaurin auren babban yayan nasu ba ko acikin matasan  gidan,manyan su ne kawai suka son da ɗaurin auren,sauran kuwa koda zasu san da auren sai dai suji  a masallaci a yayin da ake sanarwa.

Zuba mashi ido Alexandra tayi ganin yadda  yake ta rawar jiki,yaci uban ado cikin farar shadda,ya zura malunmalun,ya sanya sabuwar hula akanshi,ga agogo sabuwa ya Sanya a hannunshi,ga haɗaɗɗun takalma masu tsadar gaske ya zura a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login