Showing 18001 words to 21000 words out of 432432 words
Chapter 7 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
magana ba hannu kawai tasanya ta cicci6i hosana ta ɗaura a kafaɗarta sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinta tana cewa jahad "Ki biyo ni,"
Cikin sauri jahad ta tashi tabi su cikin ɗakin, kwantar da hosana tayi asaman shimfiɗeɗen gadonta, sannan ta juyo ta kalli jahad tace "Ga tea nan da snacks nasan kina jin yunwa ki ɗaure ki sha,'
Girgiza kai jahad tayi tana cewa "Bazan iya cin komai ba,
"Soboda me"? Hafsat ta tambaya tana kallonta,
Jahad tace "Sabodo ƴar uwata, bata ci komai ba,idan naci ita kuma fa"?
Shiru hafsat tayi jikinta yaɗanyi sanyi aranta har tana mamakin dama har yanzu akwai ƴan uwa masu ƙaunar junansu haka aduniya? Jinjina kai tayi kafin tace " kada ki damu, zan ƙara dubata yanzu insha Allah,zata ji sauƙi,"
Shiru kawai jahad tayi,amma fa ba zancen Cin abinci agare ta muddin hosana bata ji sauƙi taci ba itama, sai dae yunwa takashe ta,
"Ave a seat," hafsat ta faɗi tana nuna mata saman gadonta,
Jahad tace "Ina so nayi sallah tukunna," ta6e baki hafsat tayi tana cewa "okey ga toilet nan ki shiga,"
wuce wa Jahad tayi ta shige toilet ɗin tana rufe ƙopa tafashe da kuka mai cin rai tunaninta yanzu shine yarda zasu gudu daga gidan gaba ɗaya, don yanzu ta kwammace Su ƙare rayuwarsu a titi akan su faɗa hannun wani, tunda abun nasu ba sa'a kowa baisan taimakonsu don Allah batare daya cutar dasu ba,mutun huɗu kawai tasan suna da kyakkyawan niyya akansu, tsohuwa wadda Allah yayiwa rasu sai Goggon katsina da aunty saude da Yaya Omar ɗinsu.....
hafsat na jiyo kukan jahad dake acikin toilet, jikinta duk ya ƙara mace wa, karo na farko da ta fara jin tausayin wani aduniyar nan,
gaban mirror ɗinta taje wata roba ta ɗauko ta magani na shafawa a ciwo mai kashe raɗadi,
Dawowa tayi ta zauna saman gadon ta buɗe murfin tasoma lakuto shi tana shafa ma hosana a fuskarta, cikin lokaci ƙankani wurin yayi mata wani irin sanyi tamkar an ɗebe ciwon,
"Sannu ya jikin naki," hafsat ta tambaya tana kallon hosana wadda ke ɗan buɗe ido a hankali, sam ta kasa magana,
pillow hafsat ta janyo ta sanya mata kan gadon,sannan ta taimaka wurin tada hosana zaune ta jingine ta ajikinsa,
jikinta sai faman kerma yake yi, cup hafsat ta ɗauka ta shiga haɗa mata tea,bayan ta kammala ta sheƙa mata dashi da wani kofin donya rage zafi daga bisani taimaka wurin bata abakinta, la66anta har rawa suke yi wurin buɗesu saboda wata irin mahaukaciyar yunwa da take ji, sosai tasha tea ɗin kaf tashanye har dae hafsat ta ƙara haɗa mata wani ta bata,
Jahad ba ƙaramin sanyi taji aranta ba ganin yadda hafsat ke kula da hosana tayi mamakin yarda take bata tea abakinta, tsayawa tayi tana kallon su har sai da hafsat ta juyo ta kalle ta tace "ki buɗe closet ɗina akwai hijab ki ɗauko tare da Sallaya,"
Bude wa jahad tayi ta ɗauko hijab tasanya sannan ta shimfiɗa carpet ɗin tashiga yin sallah Hada isha'e tayi wadda ake cikin kira,
Daker hafsat tasamu hosana taci kaɗan daga cikin snacks ɗin data kawo mata saboda ciwon da bakinta ke yi mata, tea ɗin dae ne tasha sosai,
Gyara mata kwanciya tayi, sannan ta sanya bargo ta lullu6e ta,
tashi tayi ta koma saman doguwar sofa ɗin dake facing gadonta ta haye sama ta kwanta itama,.
Bayan jahad ta kammala sallar ta ninke mata abun sallar da hijab ɗin ta mayar dasu inda ta ɗauko su,
Sannan ta koma saman gadon ta haye, ta soma haɗa tea ɗinta tasha tana ci tare da french toast ɗin da hafsat ta haɗo masu, sosai taci don bata rage komai ba duka ta lamushe,
Bayan ta kammala ta shiga cikin bargon da hosana take ta kwanta itama, janyo ta tayi jikinta ta rungume ta tana kiran sunanta "hosanna ya jikin ki"? Har yanzu akwai raɗaɗi ko"?
daker tace "Eh,"
Jahad tace "kiyi haƙuri kinji, insha Allah bazamu ƙara shan wahala ba,inaji araina komai ya kusa zuwa ƙarshe bansani ba ko mutuwa zamuyi ba shine sauƙin mu Allah kaɗai yasani,
saurarawa tayi don jin mai hosana take cewa, saboda fuskarta na'a kwance achest ɗin jahad,sam sautin bai fita sosai
"Bana jinki hosana, kibar magana kawai kada ciwonki ya ƙara raunana,"
Shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, bakomai take son faɗama jahad ba face sunan YA OMAR da take kira.....................................*💋💋🔥The Father Of Soldiers🔥*
ﻗﺼ�? ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴ�? ﺳﺤﺮﻳ�? ﻭﺍﻟﺠﺮﺍ�? ﺍﻟﻌﺎ�? ﺭﺍﻓﻴﺖ❤🔥💞💘�?
*Story & Written by*
*Hafsat Bature Muhammad*
~💋BOSSLADY💋~
*EPISODE 9-10*
https://youtu.be/rnmDunstSN4
Abun da ya faru MARSHAL OMAR bai samu zuwa kaduna ba sakamakon Emmergency Call din daya samu daga wurin Abbansu cewa yana bukatar shi A headquater dinsu, a lokacin Motarsu har ta fita daga garin Abuja amma suka juyo da hanzari saboda Omar baya wasa da Omarnin mahaifinsa ko musu baya iyayi mashi, duk da yadda ya matsu akan son ganin su hosana da jahad amma haka ya haƙura😔
Tun bayan da suka kammala shan corn flakes junaid ya wuce bedroom dinsa saboda dama agajiye yake, sehrish kuwa sai da ta tsaya a kitchen din har azmee tazo suka fara aiki, cikin kankanin lokaci suka kammala dinner,
sannan ta wuce bedroom ɗinta ta kwanta tasha bacci har wurin magrib sannan ta tashi donyin sallah, bayan ta kammala jiki na rawa ta bude wardrobe dinta, tsayawa tayi saboda ruwan ido ta ma rasa me zata sanya acikin kayan, hannu tasanya ta janyo wata haɗaɗɗiyar Gown black colour mai kyalkyali masu daukar ido, jinjina kai tayi tare da cewa "Wannan zan sanya," tayi maganar tare da hanging dinta asaman murfin wardrobe din, shaf shaf ta tube riga da wandon dake jikinta ta tura su, cikin laundry basket dinta, sannan ta dauki rigar ta shiga kiciniyar zira ta ajikinta, bayan ta kammala ta koma gaban mirror tana kallon kanta ta cikinsa, fuskarta dauke da murmushi tana tuna yaushe rabon da taji ta acikin kayan mata, kayan ma irin wannan sabbi masu kyau, rigar tabi shape din jikinta,hannunta mai dan tsayi ne wanda ya tsaya dai-dai elbow dinta,Jujjuyawa tayi tana ƙarewa kanta kallo, kafin tasa hannu cikin jerin Perfumes dinta ta dauko kwalbar turaren TOUCH ta feffesa ma jikinta har wani lumshe ido take yi saboda yarda fragrance dinsa ke dakar hancinta, bayan ta mayar da turaren ta koma cikin wardrobe din ta ɗauko mayafi white colour tayi rolling dinsa irin lagen da larabawa suke yi masha Allah 😍
Kama hanyar fita tayi tana bude kopan azmee na sanyo kai dama dakin nata ta nufo itama, ganin yarda azmee tasaki baki yasa sehrish sa hannu ta rufe fuska don tasan kallon na menene,
"Nama rasa mai zance irin wannan kyau haka? Yarinya kamar ƴar larabawa ashe dama haka kike da Kyau ga ki dirarra,'?
Cikin jin kunya sehrish tace "Aunty azmee ko fa makeup banyi ba, i know u are just teasing me,
Azmee tace "Reesh ae ko ba kiyi kwalliya ba kyau kike, ae ni ban ma so kiyi kwalliyar yanzu, don banson ki rikita samarin gidan nan, mu rasa wa zamu ba acikin su,'
"BABBAN YAYA' ta faɗi acikin zuciyarta a fili kuma tace "Mai rabo," dariya azmee tayi tana cewa "Toh Allah yaba mai rabo sa'a time kawai zamu jira muga wanene wannan in da rai da lafiya,'
Murmushi kawai sehrish ke saki, suna cikin wannan tsayuwar motocin su suka shigo atare mai ɗauke da jiniya, azmee tace "Alhamdulillah shikenan ma, tun da kin shirya in suka shigo ki tabbatar kin kaima Babban yayansu dinner dinsa tare da Omar, yanzu ma na kammala jera na dining din basu kai ga saukowa sunci ba, dama Twins ne da suka dawo bada jimawa ba sai Junaid da HAROON, just zanji da sauran kawai,'
ta ƙare bayanin tare da kama hanyar fita daga ɗakin tana nanata mata,
Sehrish ta amsa mata da "toh insha Allah,"
cikin sauri ta koma wurin window dinta ta janye labulan ta zuge glass din tana hangensu,
kowannansu agajiye ya fito daga cikin Motar, Abbansu ne tare da marshal Omar sai SGR, Abbansu na sanye cikin kaki, haka SGR army trouser ne ajikinsa sai shirt light green mai gajeran hannu sun ɗame jikinsa, Omar kuma Shigar dazu ce ajikinsa wadda yayi shirin Zuwa Kaduna dazu,
tunda Armstrong ya buɗe masa mota ya fito yake faman lumshe ido hannunsa ɗaya na acikin sumar kanshi yana yamutsa ta, kallon shi Abban su yayi tare da cewa "Ko dae saina taimaka na goyaka ne? Naga alamar baka iya tafiya," ɗago da eye balls dinsa yayi ya kalli Abban nasu sannan anatse yace "Dad kenan, ni da kai wa zai goya wani? kai ma ka sani,"
Yayi maganr tare da soma tafiya abban nasu kam dariya yayi yana cewa "Oh kana jin kanka Tamkar giwa ko? Ae ba abun mamaki bane kaga na sa6eka abayana, in banda ma yanzu daka zama jibgege haka ga tsayi nan nan nake ɗaukarka kana yaro har goya ka nake yi," duk Omar na jinsu yana murmushi kawai saboda atare suka jera suka nufi cikin gidan,
ɗan gyaran murya yayi tare da cewa "Abba yanzu ae sai dai ka goya grandchild dinka masu zuwa," Omar ya faɗi,
Abban su yace "hmmmm taya hakan zata faru bayan ƴan bukulu sun hana ruwa gudu, burina kenan kullum kamar yadda na haifa nima nawa su haifa amma abun takaici duka ya'yan nawa babu wanda ya ajiye ko budurwa bayan ni tun ina 20 years aka sanƙamamun aure muka sha soyayya gaba ɗaya,'
Omar yace "Kada ka damu Abba, Insha Allah burin ka zai cika, in har hakan zaisa ka farin ciki, kawai acigaba da yi mana addu'a,'
Jinjina kai abbansu yayi yana ɗan kallon SGR dake gefensa shiru tamkar baya jin me suke cewa,
Ruko hannunsa yayi cikin nasa sannan yace "kai fa Son, Naji baka ce komai ba ? Ko baka son farin ciki na ne?
yatsina fuska yayi tare da cewa "In dai yaron da zaka goya ne zan kawo maka shi,'
"Uwar fa"? Abban ya tambaya adai dai lokacin da suke shiga babban falon SGR yace "Babu," dariya omar kawai yake yi.abbansu kuwa baki sake yace "Shege zaka kawo min,'?
"Ko baka so ne"? Sgr ya tambaya shima da zolaya,
Abbansu yace "Ae da babu gwara ba daɗi, akawomin inaso,"
Omar yace "So funny wlh, abba son jikokin harya kai haka, to. Insha Allah ba shege acikinsu, Original zaka samu daga gurin kowan nan mun, ' cike da nishaɗi suke fira kamar bazasu iya rabu ba, wuce wa Abbansu yayi part dinsa, shima SGR tare da OMAR suka wuce Uptairs nasu parts din,
💪
Tun da Omar ya shiga bedroom dinsa ya rage kayan jikinsa toilet yashiga ya yi wanka, yafito ya zura kayan baccinsa, har cikin ransa yaso ya kira Aunty babba don abasu Hosana yaji Muryarsu amma ransa yana bashi cewa yanzu sun isa suyi bacci, wannan dalilin ya hana shi calling ɗinsu,
Fitowa parlor dinsa yayi yasamu wuri saman sofa yazauna hannunsa ruƙe da wayarsa, sai lokacin yake dana sanin rashin daukar su hosana da jahad hoto ya ajiye acikin wayar shi koya samu na rage kewarsu, yana cikin wannan tunanin wayarsa ta soma ruri karatun kur'ani Ne ringin tone dinsa duba sunan daya bayyana a screen dinsa yayi nan take sunan*ABUSUFYAN*ya bayyana muraran,
Cikin hanzari ya ɗaga ya kara a kunnansa "Assalamu Alaikum Uncle Sufyan yau an tuna dani ne"?
On ther other hand ABUSUFYAN yace "Ko da yaushe cikin tunawa nake yi dakai Omar, nayi trying number dinka dazu baya shiga, kuma na jaraba ta RAFAYET tana ringing amma bai ɗaga ba,'
Omar yace " Kash ! rashin sani ɗazu ne na kashe wayar muna aiki ne shiyasa,"
Abusufyan yace "Dama inaso na maka magana ne About wannan yaran da goggon katsina ta ƙaƙabamun a matsayin ya'ya na"?
Murmushi Omar yasaki kamar yana agabansa yace "Ae ko ɗazu da safe ta kira ni awaya, kusan kullum ne sai ta mun Complain akan ƴa'ƴan abusufyan ɗinta,'
Abusufyan yace"Allah sarki, Nima tana kira na tana mun complain akan nasa ka mayar mata da ya'yana wuri ta, ynx ina yaran suke ne? Ya tambaya yana jiran amsa
Omar yace "A gidan general ishaq suke da zama, can na kaisu,"
"Ina iyayen su suke ne"? Ko yan uwan matar ishaq din ne? Ya tambaya
Omar yace "A'a Uncle yaran fa basu da kowa kamar yadda suka sanar mun, na haɗu dasu ne a asibiti cikin mawuyacin hali tagwaye ne baza su wuce 17years ba Suna buƙatar taimako,
Ajiyar zuciya abusufyan yasaki kafin yace "Meyasa ba zaka dawo dasu nan ba cikin abuja kusa da kai ba"?
"Uncle kaima ka sani, zaman su anan bazaiyi yu ba, maza ne mu duka duk ba wannan ba AMMI bazata ta6a lamuntar wani bare ya zauna acikin jinin ta ba,especially su da suka kasance basu da asali,' bayani yake masa tamkar yana agabansa
ɗan gyaran murya abusufyan yayi kafin yace "Listenin to me OMAR! kana da kyakkyawar niyya akansu, inaso ka kaddara aranka cewa waɗannan yaran jinin ka ne, kasanya wa ranka cewa Ƴa'Ƴa na ne, ya'yan ƙanin mahaifin kane *ABUSUFYAN* ina so ka basu kulawa Omar ! Dan Allah kada ka bari su wulaƙanta kayi mun wannan alƙawarin.......
Jikin Omar ne yayi mugun sanyi jin abun da Uncle Abusufyan ke faɗamasa, yanayin sautinsa da yadda yake yin kalamansa haƙiƙa ya ta6a Zuciyar Omar sosai, tunani omar yashiga yi aransa har sai da Abusufyan yace"Naji kayi shiru OMAR,"
Cikin sauri yace "Insha Allah Uncle i wll take care of them more than u think, nima inajin su araina sosai Uncle, ina ƙaunar yaran har cikin raina,
yana iya jiyo sauke ajiyar zuciyar Abusufyan alamar hankalinsa ya kwanta kuma yasamu natsuwa da bayanin Omar,
ABUSUFYAN yaci gaba da cewa "OMAR! INA SO KA DAWO DA YARAN NAN GIDA NA DAKE ANAN SU CI GABA DA RAYUWA, KA SANYA MUSU SECURITY TARE DA MAI AIKIN DA ZATA KULA DASU, INA SO SU RAYU ACIKIN GIDA NA, KAYI MUN WANNAN ALƘAWARIN!!!"
runtse ido Omar ya ɗanyi yana jinjina kalaman Uncle din nasa daga bisa ni yace "Insha Allah Uncle zanyi komai kake so, zan dawo dasu nan acikin gidan ka kamar yarda kake so,"
Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama, ya ajiye wayar yana mai tunani iri-iri aransa, yana ji aransa in ya ɗauke su hosana daga gidan aunty babba tamkar baiyi mata adalci ba don ya Lura tana son yaran kuma sun saba dasu anya kuwa zai iya cika alƙawarin Uncle Abusufyan Na dawo dasu hosana cikin Abuja da zama!!? 😟
Yana cikin wannan tunanin Sehrish ta shigo da sallama, batare da ya ɗago ya kalle ta ba ya amsa mata sallamar, sam ransa ajagule yake uncle dinsa ya ɗan ruɗa masa brain ɗinsa
Tray na a hannunta ƙarasawa tayi tare da gaishe shi "ina yini ya Omar," ƙiris ya rage omar ya ɗago ya kalle ta saboda Voice dinta tayi mashi kama da ta JAHAD, amma yabar Abun a matsayin muryar mai aikinsu ne ya koma masa ta Jahad Saboda kewarsu da yayi sosai
Amsa mata yayi da cewa "Lafiya lou"
Ajiye masa tray din tayi mai dauke da food stuffs dinsa asaman table Din dake a front dinsa sannan ta juya takama hanyar fita tana jiyo shi yana furta "ngde,"
Sauƙin kan MARSHAL OMAR yana matuƙar burgeta, babu ruwan shi ba kamar SGR ba, yana da IZZA ta wani bangaren kamar abinci muddin takai masa sai tayi saving ɗinshi, amma Omar sam baya buƙatar wannan kawai daga an kaimasa shi yake zuba abunshi yaci,
Saukowa tayi down a lokacin har su Twins da kanal yusuf Sun hallara suna cin dinner dinsu, tayi mamakin ganin babu Abbansu da junaid may be yana a part dinsa azmee takai masu acan
Gaishe su tayi gaba ɗaya suka ɗan dago suna kallonta, Kanal yusif ya amsa mata da sakin fuska amma Ayaan da jahan kuwa sai dai suka bita da ido,😡
Har bugun zuciya take ji in ta gansu cikin hanzari ta shige kitchen ta shirya ma SGR dinner ɗinsa ta fito ɗauke da tray ahannu ta nufi hanyar upstairs dinsa,
Da sallama ta shiga palor dinsa baya aciki, ƙarasawa tayi ta ajiye masa kayan abincin saman table dinsa, sannan ta ɗan dakata ko zai fito amma shiru babu alama,
. yanke shawarar zuwa bedroom dinsa tayi a bakin ƙopar shiga ta tsaya sannan tayi sallama, daga ciki taji ya amsa mata ƙasa ƙasa kafin ya bata permission ɗin shiga ciki,
A hankali ta zura ƙafa ta shiga ciki jikinta na ɗan kerma Hango shi tayi daga shi sai bathrobe ajikinsa kwance abaje saman gadonsa, alamu sun nuna cewa baiji ma da fitowa daga wanka ba, ya kwanta gajiya ce tayi masa yawa, idonsa na'a lumshe yace "Wanene ne,"
sehrish tace "mai aiki ce dama dinner ne na kawo maka yana a palor naga baka fito ba,
Jim yaɗanyi kafin yace "Tea kawai nake buƙata,akawo mun nan,'
Amsa mashi tayi da toh, sannan ta fuce ta koma palor dinsa ta ɗauko kayan tea din dake acikin tray din da ta ajiye anan sannan ta shigar masa dashi,
har gab da gadonsa ta ajiye masa saman madai-dai cin table din dake a wurin ta matsa masa dashi jikin gadonsa,
bin shi tayi da kallo saboda bai buɗe idonshi ba kuma baiyi yunƙurin tashi ba, yayi wani fresh dashi,
Ganin alamun fa zai iya zarcewa da bacci yasa tace "Na kawo maka Tea ɗin,"
"I knew," ya bata amsa, jinjina kai tayi ashe yasan ta kawo ɗin, wahalar tashin ce kawai yake ji, kusan 15 mins sannan ya ƴunkura ya miƙe tare da sauko da ƙafafunsa ƙasa, rigar iya guiwar ƙafarsa ta tsaya, saukin yasa shorts daga ciki amma chest ɗin shi a buɗe yake fari kal,
Zuba mishi ido tayi tana kallon ikon Allah wani