Showing 390001 words to 393000 words out of 432432 words

Chapter 131 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

wayar,picking call ɗin abu tayi tare da kara wayar a kunnanta,batasan wanene ba kawai ranta ya bata cewar Abusufyan ne,tayi tunanin zai yi mata sallama sai taji shiru,
  Batare da ta kawo komai aranta ba,ta soma magana,
  "Assalamu Alaikum,Oummansu Sehrish ce ke magana,dan Allah kadawo gida akwai matsala,Sehrish tana cikin wani hali,yanzu haka bata jin daɗin jikinta,duk ta tsorata saboda abunda Ya sayyadi yayi mata,
  Sgr dake kwance asaman gadonshi,baisan lokacin da ya mike daga zaune ba,a kiɗime yace"What?meya faru da ita ne?Waye ya shigo"?
   Abu bata wayi muryarshi ba,ita dai kawai koma wanene so take akawo masu ɗauki ko dan saboda halin da Sehrish take ciki,
  "Ya sayyadi ne ya shigo cikin gidan,bamu san taya akai ya shigo ba,Ya so ya cutar da rayuwarta....."gaba daya abu ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar dashi a ƙarshe tace"dan Allah idan ka tashi dawowa,Ka biya koda chemist ne asamo mata maganin Zazza6i,ga tashin zuciya da take ji,Tunkan takai ƙarshen maganar,Yayi rejecting Call ɗin,
  Hankalinshi yayi mugun mugun tashi,har wani jiri ya soma gani acikin idanuwanshi,a zafafe ya tunkari ƙopar fita daga bedroom ɗinshi,sai ga Marshal ya faɗo cikin ɗakin har karo suka kusan yi,
  "Bro whats happening?Where are going?"
  Zuciya ce kawai ke fusgarshi,
  "Omar,Airport zani je,"
Damko damtsen hannunshi Omar yayi ganin yana ƙokarin wuce shi ya tafi,
  "Haba Rafayet!Airport kuma at this time?Me zakayi acan "
  "Pls omar,leave alone,ka bani hanya in wuce,Zuciyana tafarfasa take yi,idan har ban kama wancan fasiƙin mutumin ba,hankalina bazai kwanta ba,"
  A ruɗe Marshal yace"Wai wa kake magana akai?ko ka gano waɗanda suka kashe junaid ne"?
  Girgiza kai yayi'A'a,ina magana akan wancan Bastard ɗin dake a Kano,Yau ya taka har gidan da Abusufyan yake..wai har...'kasa ƙarasa maganar yayi saboda raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi,
  Hankalin Omar ba karamin tashi yayi ba,tun kafin ma ya ƙarasa jin abunda ya faru ɗin,
  "Rafayet,pls Calm down ur mind,Kayi mun bayani yadda zan fahimta,'
  Mika mashi wayarshi yayi batare daya furta komai ba,
Kar6ar wayar Omar yayi, kaitsaye ya shiga call log nashi,
  Kiran da Sgr yayi ma sehrish ya fara gani,"Calling ɗin layin yayi,
A lokacin abu na acikin falo tana safa da marwa,jiran dawowar Abusufyan kawai takeyi,
  Kiran na shiga wayar,da sauri tayi picking tare da zabga sallama,
   "Am..sehrish,pls inason sanin meke faruwa anan ne,"?
  Abu tace"ba Sehrish bace,Oummansu ce,"
  Abun ya ɗan ɗaure mashi kai,jin tace Oummansu ce,a iya saninshi tana da ta6in Hankali,gaisar da ita ya fara yi cike da girmamawa tare da gabatar mata da kanshi a matsayin yayansu sehrish,abu ba ƙaramin daɗi taji ba,
  Bata 6oye mashi komai ba,kaf ta kwashe abunda tasan ya faru ta sanar dashi,"
  Jinjina kai Omar yayi,jikinshi har tsuma yake yi,daƙyar ya iya furta"Zan yi magana da Abusufyan ɗin,Ki kula da Sehrish ɗin kafin ya dawo gidan,"
  amsa mashi tayi da toh,daga bisani su kayi sallama,
  Zuba ma juna ido sukayi shi da Sgr,
"Bansan wani irin dabban mutun bane wannan,wai ma ina security ɗin dake tsaron gidan ne?aikin me sukeyi ne da har suka barshi Ya samu damar shiga gidan?shi kuma Uncle bansan ya akayi har yayi dare haka ba awaje,"Omar ne yayi maganar ranshi a matukar 6ace,
  "Last time ma,Ya ta6a yin irin hakan,Ya tafi ya barta ita kaɗai acikin gidan,"Acewar Sgr,
Omar yace"ba don Oummansu na a kusa ba,da bansan mezai biyo baya ba,Amma naji daɗin jarumtar da tayi wurin ceton sehrish ɗin,"
  Kar6ar wayar Sgr yayi daga hannunshi,Layin Abusufyan ya kira,
  Almost 3 times tana ringing ba'a ɗagawa,
  Sauke wayar yayi daga kan kunnanshi,
 Omar yace "Allah yasa dai lafiya,hankalina fa duk ya tashi,abunda za'ayi yanzu Kawai gobe da asussuba su dawo gida kawai,nasan kafin lokacin may be Abusufyan ɗin ya dawo,Zan cigaba da trying layinsa,"
  Dakyar ya samu ya lalla6a Sgr ya fasa zuwa airport ɗin,Amma fa abun ya tsaya Mashi aranshi,gefen gadonshi ya zauna,Omar ma ya zauna akusa dashi,
  "Omar,kodai mun aikata wani zunubi ne da yasa waɗannan abubuwan ke faruwa damu ne?daga wannan sai wannan!
  "Rafayet,ba laifin mu bane Laifin wasu ne aka ɗaura mana,ni tunda nake arayuwata ban ta6a fuskantar tashin hankali irin na waɗannan ranakun ba,kuma ban ta6a tunanin cewa rana irin Wannan zata zo mana ba,"
  "What's the solution now?time fa yana ƙure mana,Daddy ma harya fara karaya da dawowar junaid,ɗazu da safe da yazo bedroom ɗina,Tsare ni yayi akan in faɗa mashi gaskiya,Junaid zai dawo yaci gaba da sa rai,ko kuwa bazai dawo bane,A lokacin saina kasa buɗe baki inyi mashi magana,"Sgr ne yayi maganar
  Omar yace"Wlh nayi regretting ɗin 6oye mashi ainihin abunda ya faru,Duk da munyi hakan ne don mu ceto rayuwarshi,Amma kuma fa mun tabka kuskure babba,Don kuwa duk ranar daya gano cewa Junaid ya mutu,wlh ya gama yarda damu har abada,zuciyarshi zata karaya ne,Inajin tsoron wannan ranar,Rafayet,kodai mu sanar dashi gaskiyar lamarin ne"?
  Shiru Sgr ya ɗan yi yana nazarin maganar tashi,girgiza kanshi ya ɗan yi tare da cewa"That's not the solution Omar,koda ace zai sani,yakasance time ɗin da muka kama waɗanda su kayi silar mutuwarshi,Mu gurfanar dasu agabanshi,before mu yanke masu hukunci akan idonshi,ina ganin kamar zaifi jin sauki acikin zuciyarshi,"
  Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani,Kowannansu ya ɗauro alwala,Suka daidai ta sahu tare da kabbara Sallah,

Ataƙaice

Abusufyan bai tashi dawowa cikin gidan nan ba sai wuraren sallar asuba,Bawan Allah ashe Bayan ya baro gidan su Maman Sadeeq akan hanyar dawowarshi gida aka turo mashi da saƙo cikin wayarshi cewa za'a kashe Ƴarshi da ya bari acikin gidan,Hankalin shi yayi mugun tashi,Ya kure gudun motarshi,idonshi ya rufe saboda tashin hankalin dayake ciki,Baisan sa'adda ya buge wani Tsoho ba dake ƙoƙarin tsallaka titi,Tsohon yaji mummunan rauni dole ya tsaya don yaji bazai iya daukar alhakin guduwa yabarshi cikin mawuyacin halin da zai iya rasa ransa,mutane suka kama mashi tsohon yasa shi a motarshi suka wuce dashi asibiti,babu yadda ya iya,kamar ya fasa ihu haka yaji saboda tsabar baƙin ciki,duk da wani bangare na zuciyarshi na tunasar dashi akwae security guards a gidan,Bashi ya baro asibitin ba sai wuraren Sallar Asuba Ya dawo cikin gidan,Yayi mamakin ganin komai lafiya,Lokacin daya shiga ɗakin abu kwance ya samesu rungume Saman gadon ita da Sehrish suna ta sharar baccinsu,Hankalinshi ya kwanta sosai ganin babu abunda ya faru dasu,

Falo ya koma ya zauna saman sofa,jikinshi duk amace,Ringing ɗin wayarshi dayaji yasa shi zura hannu cikin aljihu ya ɗauko wayar tare da duba sunan mai kiran nashi,Marshal Omar ne,
  Picking call ɗin yayi tare da kara wayar a kunnanshi,
  "Omar me kake yi har yanzu bakayi bacci ba"?
  On the other hand Omar yace"Uncle,Ina ka shiga ne anata nemanka,"?
  Nan Abusufyan yake sanar dashi abunda ya faru dashi akan hanyar dawowarshi gidan,
   "Yanzu na dawo gidanma,Na same su cikin koshin lafiya suna ta bacci,"
  A nan Omar ya kwashe duk abunda Abu ta sanar dasu ya faɗa ma Abusufyan,A zabure ya miƙe tsaye jikinshi na rawa,
  "Pls Uncle,ka kwantar da hankalin ka,Tunda ba abunda ya faru dasu,Abunda ya kamata kawai ku dawo gida yau yau ɗin nan zamanku anan baida amfani,dama saboda ciwon Mahaifiyarsu ne Kuma ta samu lafiya,Yakamata ku dawo gida,Hankalinmu sai ya fi kwanciya,"
..jinjina kai kawai Abusufyan keyi sam ya kasa buɗe baki yayi magana,Allah kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji acikin Zuciyarshi,dakyar ya iya buɗe baki yace"Shikenan Omar,yanzun nan zamu shirya,'
  "Allah ya dawo daku Lafiya,"
"Ameen"daga haka su kayi Sallama,
Komawa Bedroom ɗinsu yayi wuraren karfe 6 na asuba,da alama ko sallar asuba basu yi ba,sai sharar bacci sukeyi,
  Zagayawa yayi gefen da Sehrish take a kwance ya zauna tare da zuba mata ido yana kallonta,Yayin da hawaye ke sharara akan fuskarshi,tsananin tausayinta ne ya kamashi,baiji daɗin abunda ya faru ba,ta wani 6angaren kuma yaji sanyi aranshi da Allah ya tsare mashi ita,ga kuma Mahaifiyarsu da ta dawo cikin hayyacinta ta silar abunda ya faru,
  Shessheƙar kukan da Abusufyan keyi ne ya farkar da Sehrish,buɗe idanuwanta tayi masu ɗauke da bacci,Suna haɗa ido dashi tayi hanzarin mikewa daga zaune tana ambaton sunanshi"Daddy!yaushe ka dawo?meya faru kake kuka,"
  "Daughter,Am sorry!am really sorry,duk laifina ne dana tafi nabarki ke kaɗai acikin gidan,"
  "Daddy,bangane akan me kake magana ba?nifa babu abunda ya faru dani,"tayi hakan ne don ta 6oye mashi gudun karya sanya damuwa aranshi,batasan cewa ya riga daya ji ba,
  "Omar ya sanar dani duk abunda ya faru dangane da zuwan sayyadi cikin gidan nan,"
   Mamaki ta shiga yi taya akai Ya Omar yasan abunda ya faru dasu?can kuma ta tuna da lokacin da Oummansu ta nemi yin magana da Abusufyan may be a wurinta yaji komai,
  "Dan Allah Daddy,kada kasa damuwa aran ka tunda ba abunda ya faru dani lafiyata kalau,Sai ma wani abun farin ciki da ya faru,Oummanmu ta dawo cikin hayyacinta,Sanadin zuwan ya sayyadi,Kuma ta lalata mashi idanuwanshi,karkaso kaga yarda ya dinga kururuwa yana ihu," Tayi maganar tana kwatanta mashi irin yarda Ya sayyadi yayi ihun,
  Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba,dama tayi hakan ne don ta sanyaya mashi ranshi,
  ɗaure fuskarta ta ɗan yi ashagwa6e tace"Daddy banga kana farin ciki da abunda na sanar dakai ba"?
  Daƙyar ya ƙaƙaro murmushi akan fuskarshi yace"Ina farin ciki mana,Naji daɗi sosai,kawai dai nadamu ne akan Halin da kika tsinci kanki a lokacin da bana nan,"
  ɗaure fuskarta tayi"Why Daddy,bana ce ka kwantar da hankalin ka ba?komai ya wuce,Yanzu lokacin farin ciki ne,Ga ka, Ga Ni,ga Oummanmu kuma,Bari na tashe ta daga bacci kuyi magana,"ta ƙarasa maganar tare da sanya hannu tana ɗan bubbuga kafadar Oummansu,
  Murmushi kawai Abusufyan ke saki yana kallonta,
  "Oumma!oumma!ki tashi ga Daddynmu nan ya dawo,"
  Kasa tashi abu tayi saboda kunyar Abusufyan da take ji,Ashe tun shigowarshi dakin ta farka,tana jinsu suna magana amma tayi likimo,

"Nasan cewa idonki biyu abu,bakison gani na ko"?Abusufyan ne yayi maganar ayayin da yake leƙen fuskarta,pillow ta sanya tare da rufe fuskarta dashi,
  Murmushi suka saki atare shi da Sehrish,
  "Inason magana dake,ki tashi daga zaune,"cike da jin kunyarshi ta cire pillow ɗin tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna,Ta kasa ɗagowa su haɗa ido da Abusufyan,kunyarshi ta rufe ta,kamar tayi rami ta binne kanta,
     
   "ZAINAB"ya ambaci sunanta da wata irin kasalalliyar murya,
   daƙyar ta iya motsa lips ɗinta wurin amsa mashi,
   "Na'am,"
Murmushi ya saki tare da ɗaga hannunshi sama yana furta"Alhamdulillah!Alhamdulillah,Almost 3 times yana ambaton hakan,Cike da tsantsar farin ciki,
   Sai faman sauke ajiyar Zuciya take yi,matsawa yayi kusa da ita tare da sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta yana ƙare mata kallo,
  Siraran hawaye ne suka soma Zarya akan fuskarta masu ɗumin gaske,
   "Hawayen menene wannan"?
Cikin Shessheƙar kuka tace"Kayi haƙuri,ka yafe mun,Na gane kuskuren dana yi,Naji jiki Abusufyan,nayi dana sanin butulce maka da nayi,Haƙƙinka ne yake ta bibiyar rayuwata,Ni ce silar duk wani abu daya faru a rayuwarmu nida ƴa'ƴana...."ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka,Hannu tasa ta zame hannayenshi daga saman fuskarta,kafin ta Sauko daga saman gadon ta zuƙunna saman guiwowinta agabanshi,tana ci gaba da yin kukan....
   "Tun da nake arayuwata,ban ta6a ganin mutun mai kyakkyawar Zuciya irin taka ba,duk irin girman laifin dana aikata maka,hakan baisa ka guje ni ba,Sai ma bibiyar rayuwata daka ci gaba dayi duk don kaga Ka taimake ni,Amma na kasa gane hakan,saboda tsabar baƙin kishin da nake dashi na yanke maka hukunci batare dana tsananta bincike ba......"
     Ruƙo hannunta Abusufyan yayi tare da ɗago da fuskarta yace"pls bana son muna tuna abunda ya wuce,Ni komai ya wuce a wurina Abu,tabbas naji zafin abunda kika yi mun Amma wlh banta6a ruƙe ki araina ba,kullum burina inga na taimaki rayuwarki saboda baki da kowa abu,Allah kaɗai gare ki,Sai kuma Ni dana haɗa zuri'a dake,Ba zanso rayuwarki ta wulaƙanta ba,ko ba don haka ba Ke amana ce agare Ni,"

Zuba masu ido Sehrish tayi tana kallonsu fuskarta ɗauke da Murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,
  "Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin bayyana maka irin farin cikin da nake ciki ba,Abusufyan Allah kadai ne zai iya biyanka,",addu'oi ta shiga yi mashi yana amsa mata da ameen,Kafin daga bisani Ya nuna mata gefenshi ta miƙe ta zauna,
   "nasan kinyi kewar ƴa'ƴanki sosai,In sha Allah Yau ɗinnan zamu wuce Abuja,Zaki ga Hosana da Jahad,da kuma sauran Family ɗinmu,"

Fira sosai suka shiga yi,Anan ta samu labarin irin wuyar dasu sehrish suka sha bayan 6acewarta,da kuma yadda akai suka haɗu da dangin mahaifinsu da shi kanshi Abusufyan din har kawo yanzu da suke bata labarin,Abu tasha kuka sosai tsananin tausayinsu ne yakamata,ta wani 6angaren kuma tayi farin ciki sosai Da Allah ya nuna mata wannan ranar da ranta kuma da Lafiyarta,

Batare da 6ata lokaci ba Suka kammala shirinsu na komawa Abuja,A jere Motocinsu suka fita daga cikin gidan,Motar Abusufyan na atsakiyan motocin security ɗin gidan,Kaitsaye hotoro suka wuce domin yin sallama dasu Maman Sadeeq,
  Sunsha kuka sosai,musamman Maman sadeeq da Abu,rungume juna suka yi kamar karsu rabu,babu wanda bai zubda ƙwalla ba acikinsu,kafin su tafi sai da Abusufyan ya damƙa ma Malam Nura key din gidansu dake a nasarawa G.r.a,Ya mallaka masu shi duk da haka sai da ya ƙara masu da zunzurutun kuɗi har miliyan 10,yace ya dauki miliyan bakwai yaba Baban Umari cikon miliyan ukkun,don bai manta da gudunmawar da akace ya bada ba wurin neman abu,anan take ya rubuta ma Malam Nura cheque,Duk da haka bai ƙyalesu ba,Bayan haka kuma yayi masu albishir ɗin cewa tare dasu Za'ayi aikin hajjin bana,Wayyo Allah saboda tsabar farin ciki,kasa bude baki su kayi don suyi mashi godiya,Kuka kawai sukeyi,abun da basu ta6a tsammanin zasu samu a rayuwarsu ba,Yau gashi silar taimakon da sukayi Allah ya ɗaukaka rayuwarsu,
  Sehrish kuwa Dama tayi alƙawarin zata taimaka ma Sadeeq ya gyara keken shi,maimakon kuɗin gyaran keken sai Gashi ya samu kyautar danƙareriyar Motar Abusufyan gaba daya ya mallaka mashi ita,kusan zaucewa Sadeeq yayi saboda tsabar farin ciki,sun jima a wurinsu suna bankwana,kafin daga bisani Sukayi masu Sallama,Anyi rabuwar mutunci sai kuma in Allah ya haɗasu wurin shagalin bikin Ƴa'ƴan abu,

Ɗaya daga cikin motocin security ɗinsu suka shiga Gidan baya Abu da Sehrish,Abusufyan yana agaban motar,A jere Motocin suka kama hanyar fita daga unguwar,

Su Maman Sadeeq na tsaye a kopar gida ita da Mlm nura,tare da sadeeq sai bye bye suke yi masu da hannu,yayin da hawaye ke zuba a fuskar kowannansu,

Sehrish sai lekensu takeyi ta glass ɗin motar dake a zuge,har sai da suka 6ace ma ganinta tukunna ta hakuri da leken,Rayuwa kenan in akayi hakuri Komai mai wuce ne,

Hannu abu tasa tare da janyo Sehrish ta rungumota ajikinta,a lokacin har motocin sun haura saman titi,Sun miƙi hanyar barin garin da matsakaicin gudu,
Da zarar ta ɗago da idonta ta kalli madubin motar,Fuskar Abusufyan take gani yana sakar mata murmushi,Sunnar da kanta ƙasa tayi tana ƴar dariya,
Sehrish batasan wainar da suke toyawa ba,domin kuwa ta lumshe idanuwanta da alama bacci ya fara ɗaukarta,
Sake ɗagowa abu tayi tare da kallon Mirror ɗin,suka ƙara haɗa ido dashi,
Kashe mata ido ɗaya Abusufyan yayi,batasan lokacin da ta fashe da dariya ba cike da tsantsar farin ciki,
Shima dariyar yayi,kusan minti 30 bata ƙara dagowa sun haɗa ido ba,saboda baccin da yayi awon gaba da ita,
Wasa wasa shima bacci ya ɗauke shi,dama duk basu samu isasshen Bacci ba a adaren Jiya,

Wuraren ƙarfe 2 na rana suka ƙaraso Abuja,Slowly motocinsu suka shararo izuwa cikin gidan,tun da Hosana tajiyo sautin shigowar motoci da gudun gaske ta fito daga cikin falon don taga su wanene,

Bayan sunyi parking ɗin motocin,Abusufyan ya fito daga cikin motar,hosana na ganinshi ta ƙwala mashi kira"Daddy"!wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,da gudun gaske ta nufe shi tare da faɗawa jikinshi ta ƙankameshi sosai,tana dariya,
"Hosana,"ya Ambaci sunanta tare da ɗago da ita daga jikinshi yana kallonta,fuskarshi ɗauke da murmushi,
Ɗaure fuskarta ta ɗan yi ashagwa6e tace"Munyi fushi daddy,Sai yau zaku dawo"?
Yana ƙokarin buɗe baki ya bata amsa,karaf idanuwanshi suka sauka akan Jahad wadda ta fito daga cikin falon tana tunkaro su,
Gabanshi ne ya faɗi rass!Ganin yadda kamanninta suka sauya tamkar ba ita ba,ta rame sosai ,tafiyar kanta ma daƙyar take yinta,
Ƙarasawa tayi gabansu ta tsaya batare da tace komai ba,idanuwanta na kallon ƙasa,
"Jahad!kinyi rashin lafiya ne"?ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
"Zazza6i nayi sosae amma naji sauƙi yanzu,"
Hannu yasa tare da janyota ya rungumeta ajikinshi,Kasa jurewa tayi aikuwa ta fashe mashi da kuka sosai,
Hankalinshi ya ƙara tashi,
"Jahad kukan menene"?
Cikin shessheƙar kuka tace"bakomai Daddy,nayi kewarka sosai,"
hannu yasa yana ɗan bubbuga bayanta yace"Am Sorry Daughter,pls ki daina kuka kada kisa nima na fara zubar da hawayen nawa,"
Dakyar ta tsagaita da yin kuka ta ɗago da kanta daga jikinshi tace"Daddy,ina rishi take?ina kuma Oumman mu?Hosana ta sanar dani cewa an ganta,"
Murmushi ya saki tare da sanya hannunshi ya ɗan kwankwasa glass ɗin motar,
Buɗe murfin motar Abu tayi tare da fitowa daga cikin Motar,Zuba mata ido su kayi suna kallonta kamar yadda itama take kallonsu,
Atare suka haɗa baki wurin ambaton sunanta"Oumma!"
Murmushi ta ɗan sakar masu,tare da buɗe masu hannunwanta don su zo ta rungumesu,Matsawa suka yi tare da faɗawa saman jikinta,ta haɗasu duka ta rungume sosai,fashewa sukayi da matsanancin kuka kamar ransu zai fita,musamman jahad da take cikin wani hali na buƙatar kulawarsu,
Itama abun kukan takeyi sosai,babu mai lallashin wani acikinsu,Fitowa Sehrish tayi daga cikin motar ta other side ɗin,jikinta a sanyaye ta zagayo ta wurin da suke,bayansu jahad ta fada ta rungumesu,abu ta haɗa da ita duka ta ƙanƙame abunta,

Tuni hawaye sun wanke fuskar Abusufyan,Yau burinshi Ya cika na ganin ya haɗa kan family ɗinshi,wannan rana ce da bazai ta6a mantawa ba arayuwarshi,,

Suna cikin wannan yanayin sai ga Abbansu junaid tare da Alexandra sun fito daga cikin gidan,tsayawa su kayi suna kallonsu fuskar kowannansu ɗauke da murmushi,
"Bismilla,Ku ƙaraso daga ciki mana,"Abba ne yayi maganar tare da yi masu nuni da hannunshi,
Kallonsu Abu yayi tare da yi masu gyaran murya yace"Koke koken sun isa haka,mu shiga daga ciki mana,"
Raba jikinsu sukayi dana Oummansu,ta ruƙo hannun jahad da hosana acikin nata,Abusufyan kuma ya ruko hannun Sehrish wurinsu Abba dake atsaye,
tunkan su ƙaraso Abba yace" masha Allah,Yau family ɗin Abusufyan ya haɗu wuri guda,Ga Uwar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login