Showing 192001 words to 195000 words out of 432432 words

Chapter 65 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

ba,kamar ya haɗiyeta haka yake ji,ya jima yana mamakin wannan ikon Allahn,
Miƙewa Ayaan yayi tare da cewa"mu zamu wuce gida,ana can anata shirye-shiryen haɗa walimar murnar dawowar uncle abusufyan,ina fata zaki zo mana tare da Amal,'yayi maganar yana kallon Amani,
Tace"mai zai hana,ae muna nan zuwa anjima insha Allah,tare da mu za'a buɗe taron walimar,"
"Allah ya kawo ku lafiya,'yayi maganar tare da mayar da idanunshi kan JAHAN daya ƙurawa Amal ido kamar mazuru yace"bro,tashi mu tafi mana,kada time ya ƙure mana,"
jiki amace jahan ya miƙe tare da ruƙo hannun ayaan cikin nashi,su kayi mata sallama tare da kama hanyar fita daga falon,
Suna tafiya Jahan na waiwayon Amal kamar zaiyi tuntu6e,hakan ba ƙaramin dariya yaba shi ba,saida suka fito daga cikin falon,bayan sun shiga cikin motarsu,Ayaan ya ɗan kallo shi cikin zolaya yace"Jahan ya kaga ƙarmasasshiyar ne?ko nace kingin rami ko?ya ma kace mun ran nan a asibiti daka ganta"?
A tsiwace jahan yace"bansani ba!dallah ni ka tashi motar mu tafi gida,"
dariya sosae Ayaan yayi yayin da yake tashin motar,ya ja ta suka bar gidan,yana driving yana kumshe dariya abakinshi,jin yarda Jahan ke ta faman buga tsoki,duk yabi ya susuce tunda yayi arba da Amal acikin idanunshi,ya nemi natsuwarshi ya rasa,a haka har suka ƙaraso cikin gidan,

wuraren ƙarfe sha biyu,sgr ya fito daga cikin toilet jikinshi sanye da bathrobe,yayin da hannunshi ke ruƙe da guntun towel wanda yake goge Sumar kanshi dashi,agaban dressing mirror ya tsaya yana ƙarasa goge sumar kan nashi,koda ya ɗago da idanunshi da niyyar ya kalli fuskarshi acikin madubin,sae ya dinga ganin fuskar sehrish acikin mirror ɗin amaimakon tashi,lokaci guda ya shiga tariyo duk abunda ya faru jiya atsakaninsu,tun daga lokacin daya je taimakonta,har izuwa lokacin da yaje yi mata allura,tana faman cizon la66anta,hakanan yaji yana marmarin son ganinta acikin idanunshi,tambayoyi ya shiga yi aranshi yana cewa meyasa batazo ta kawo min breakfast ba?ko har yanzu jikin nata ne?
Jin takun tafiyar mutun abayanshi yasa shi kai idanunshi wurin ta cikin madubin ya hange ta tsaye duk a tunaninsa yarinyar ce tazo,koda yayi arba da fuskar hayaam sai ya kawar da fuskarshi cike da mamakin wacece wannan?meya kawota bedroom ɗinshi,
ƙarasawa ciki hayaam tayi tana tafiya cike da kwarkwasa,wankan atampa ta ɗauka ajikinta,riga da skirt ne,kayan sun matse ta sosai,sun bayyana surar jikinta soaai,musamman saman rigarta boobs ɗinta sun fito waje kamar zasu ciro daga cikin rigar,akwai mayafi a jikinta lokacin da ta fito daga bedroom ɗinta,tana ƙarasowa ɗakin nashi ta cire mayafin tare da ruƙe shi a hannunta don taja hankalin shi,cike da ƙwarin guiwa tazo ɗakin nashi,saboda kwallin data shafa ma idanunta,wanda bokansu ya bata don tayi amfani dashi,ya tabbatar masu da cewa muddin sgr ya sanya idanunshi acikin nata,shikenan sun gama dashi,zai haukace akanta,ya rasa natsuwarshi,

Tsayawa tayi daga bayanshi,tare da kashe murya tace"ya kake ranka shi daɗe,ka tashi lafiya,"
Shiru Sgr yayi bai amsa mata ba,gaba daya lamarin ya gama ɗaure mashi kai,ƙarfin halinta ya bashi mamaki,
daƙyar ya iya buɗe baki yace"Ke!wacece ke!what are u doing in my room?yayi maganar batare daya sanya idanunshi acikin nata ba
zagayowa hayaam tayi ta gabanshi tamkar zata manna ƙirjinta asaman nasa,
Cike da rangwaɗa tace"Zuwa nayi don na gyara maka bedroom ɗinka,tunda ita yarinyar dake kula da part ɗin naka,bata jin ɗaɗi bazata iya yin aikin ba,idan ba damuwa inaso ka bani damar na ci gaba da kula dakai kanka,ina mai tabbatar maka da cewar zaka ji daɗin kasancewa tare dani,saboda ni ina da komai da komai,ba gyara ɗaki kaɗai ba,hatta ɗebe maka kewa zan dinga yi,nasan dole ka buƙaci mace akusa dakae especially da daddare haka.

Tashin hankalin da ba'a sa mashi date,yau hayaam tazo yi ma Sgr kwartanci acikin ɗakinshi,ita ga kwararriyar ƴar bariki,tana magana tana ƙara kusanta jikinta da nashi,
Just speechless gaba daya ta gama rufe mashi bakinsa,ya rasa abun cewa,shiru kawai yayi yana jira yaga me take ƙokarin yi mashi,daga nan zai san wane irin hukunci ya dace da ita,don ya lura cewa giya tasha,tana bukatar adawo da ita cikin hayyacinta,kuma har lokacin bai kalli cikin idanunta ba,
  Wannan shurun da yayi ne yasa hayaam ta fara tunanin cewa kodae ya amince mata ne?shu'umin murmushin nan nata ta shiga saki tana bin surar jikinshi da kallo sae faman haɗiyar yawu takeyi kamar zata lashe shi,aranta tana cewa"dama nasani,muddin yayi arba da sura ta,dole ya kwaɗaitu,yanzun nan zan canza mashi alƙibla,zanja hankalin shi sosai,har nasamu abunda nakeso,
  Kafin Sgr yayi wani yunƙuri gaba daya hayaam ta afka mashi tai hugging nashi sosae,tashin hankali saboda tsabar mamakin daya shiga ne yasa bai janyeta Ba,kanshi ya gama ɗaure wa,domin kuwa tunda ya ke arayuwarshi wata ƴa' mace bata ta6a kuskuren ta6a wani sashe na jikinshi ba koda gigin wasa,sae wannan mai rabon shan dukan,

ita kuwa hayaam jin bai yi yunkurin yi mata wani abu ba yasa ta fara kokarin tura hannunta cikin Bathrobe din dake a jikinshi don tasan takan yadda zata ida kashe mashi jikinshi,aikuwa a zafafe ya finciko ta,ya ware faffaɗan tafin hannunshi da ƙarfin gaske ya kifa mata mari zazzafan gaske gami da hankadata ta daki dressing mirrorn,agigice hayamm ta fasa wata irin razananniyar ƙara,wani irin jiri ne ya ɗebe ta,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa tana birgima,taji ƙamshin mutuwa wlh,ihu ta shiga saki tana fadin Wayyo Allanta,
  Adai dai lokacin Sehrish ta shigo part dinshi hannunta ɗauke da tray,na breakfast dinshi data kawo mashi,ganin bashi a parlourn yasa ta nufi bedroom din bakinta dauke da sallama, tana sanya ƙafarta acikin bedroom ɗin,ta jiyo sautin wannan ƙarar da hayaam ta saki,a firgice ta saki tray ɗin hannunta ya faɗi ƙasa kayan abincin suka tarwatse ƙasa,hankali a matuƙar tashe take kallonsu,sautin faɗuwar tray ɗin hannunta ne yasa sgr juyowa karaf idanunshi suka shiga cikin na sehrish,zuba mashi ido tayi tana kallonshi yayin da shima yake kallonta sae faman huci yake yi yarda kasan mayunwacin zaki,da ace sehrish bata faɗo ɗakin nan ba,da ba ƙaramin illata Hayaam zaiyi ba,so yayi ya nakasata,yarda bazata ƙara yin gigin takowa tazo bedroom ɗinshi balle har tayi yunƙuri ta6a wani sashe na jikinshi ba,
  atsorace sehrish ta mayar da idanunta kan Hayaam dake a baje ƙasa,magashiyyan sae faman Birgima takeyi har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,wato taji tafin hannun maza,dama zafin hannu gare shi,shiyasa bai cika son yakai bugu ba,saboda za'a iya samun matsala,da mari kaɗae zai iya sumar da mutun,
A zafafe Sgr ya juya ya tunkari hayaam dake baje kasa,da alama yau fa hayaam sai dai
buzun ta,ganin hakan yasa hayaam da kyar ta rinka jan jiki tana ja baya gami da yi masa magiyar yayi hkr kar ya kasheta hannunta guda dafe da kuncin,gaba daya sautin jin kunanta ya ɗauke ɗuff ta 6arin da daya mare ta,cikin husky voice yace"who the hell are u? da sauri cikin shesshekar kuka la66anta na kerma tace"ni...ni..ƙanwarku ce....au ƙanwar matar yayyen kuce ishaq da abbas" tsayawa Sgr yayi lokaci guda ya gane itace yarinyar da tazo rannan har aka faɗa masa"to waye ya shigo da ita gidan? Ya jefa ma kansa tambaya,

Ganin abunda ke faruwa yasa Sehrish ja da baya zata watsa aguje saboda tsoran kar itama laifin da hayaam ta aikata ya shafe ta,
  da wata irin murya taji yace"ke!zonan,"
  Jiki na rawa sehrish ta shigo cikin ɗakin nashi,sae faman kerma take yi kamar yace zai buge ta,
  ƙarasawa kusa dashi tayi tana faman zazzare idanu hankali atashe take kallonshi,tana jiran jin me zaice mata,
  daidaita natsuwarshi yayi tare da sassauto da muryarshi calmly yace"ya jikin naki!'?
  Tsananin mamaki ne ya kama sehrish,jin abunda yace mata,kuma da irin muryar da yayi mata maganar,hakan yasa taji hankalinta ya kwanta,
  muryarta na rawa tace"naji sauƙi sosai,yanzu bana jin ciwo atare dani,"

Jinjina kanshi yayi kafin ya kuma cewa"Okey,Allah ya ƙara lfy,'
"Ameen,"ta amsa mashi,
shiru suka ɗanyi na wani lokaci,kafin ya mayar da idonshi kan hayaam dake ta faman yi mashi tsuwa acikin dakinshi duk ta cika masu kunnuwansu,
  A fusace yace"get out from my bedroom!'
  Jiki na rawa hayaam ta miƙe da gudu zata fuce a tsawace sgr ya tsaidata ta hanyar cewa" hey! juyowa tayi har lokacin hannunta na akan kumatunta ya cigaba da cewa "make sure u pack all ur shit and leave this house! A kausashe yayi maganar, idasa fucewa daga cikin ɗakin tayi tana cigaba da shar6ar kukan nata,

Lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu akan fuskar sehrish da tai tsuru² jin ance hayaam ta tattara kayanta ta bar gidan, yace"yanzu ya za'ae da breakfast ɗina da kika zubar mun a ƙasa?
  cikin sauri tace"bari naje na haɗo maka wani" juyawa tayi da niyyar ta tafi,kwatsam taji ya ruƙo hannunta acikin nashi,a ɗan tsorace ta juyo tana kallonshi,gabanta ne taji yana faɗuwa ganin yarda Sgr yake kallonta,nan fa ta shiga taitayinta,
  "Meyasa jiya,baki dawo gida ba?ko saboda na datse maki gashin kanki ne"?
   Girgiza kai sehrish tashiga yi tana cewa"a'a ba haka bane,bani da lafiya ne,bacci ya ɗauke ni a school bansamu wanda ya tashe ni ba lokacin da aka tashi har junaid yazo dauka na bai ganni ba,shiyasa bansamu nadawo gida ba,'
  Kallon bakinta dake bayanin kawae yake har ta gama,a hankali ya furta Okey,sannan ya saki hannunta daga ruƙon da yayi mashi,
  juyawa tayi da sauri ta ƙarasa bakin kopar dakin nashi,zukunnawa tayi ta kwashe kayan abincin data zubar mashi aƙasa,duka ta tattara su acikin tray din,sannan ta fuce daga ɗakin nashi,
Gaba daya ta rasa natsuwarta,wani irin yanayi ta dinga ji atare da ita,kallon nan da yake yi mata ba ƙaramin kashe mata jiki yakeyi ba,kamar wadda aka cire ma lakar jikinta haka ta dinga jin kasala,

A kitchen ta samu azmee tana wanke kayan abincin da sukayi amfani dashi na breakfast,
  Ganin ta ɗauke da tray a hannunta yasa azmee cewa"Har ya kammala yin breakfast ɗinne"?
  girgiza kai tayi alamar a'a tace"matsala aka samu,ni ce na 6arar da kayan abincin,shine yace na sake kawo mashi wani,'
  Azmee tace"wasa wasa sehrish kema kin iya shiririta wlh,kina sake da baki har kika zubar mashi da kayan abincin ko?
  "Ae bada sanina,hakan ya faru ba,"ta yi maganar yayin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin,
  "Shikenan bari na sake haɗa maki wani breakfast din ki kai mashi,Amma kada ki jima a part din nashi fa,da zarar na kammala gyara kitchen din,zanyi maki ƙunshin,ko baki so ne'?
  "Inaso mana,"tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,
  Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata wani kayan abincin acikin tray,ta bata takai mashi,sae da ta ja mata kunne akan karta kuskura ta ƙara zubarwa,'
  fitowa daga cikin kitchen din sehrish tayi,fuskar nan ɗauke da annuri,wani irin daɗi takeji aranta,kamar anyi mata albishir da gidan aljana,
  A hankali take taka stairs din,yayin da Zuciyarta ke tariyo mata abunda ya faru aɗakin sgr,batasan meya faru tsakaninshi da hayaam ba,da har ya kwashe ta da mari,amma koma meye dae tana da tabbacin cewa wani abu tayi mashi ba dae dae ba,
  Ta6e baki tayi tana cewa"to ni ina ruwana?meye damuwata da ita?koma meye ita taja ma kanta,nasan cewa babban yaya bazai ta6a ɗaga hannu ya mari mace ba hakanan batare da wani dalilin ba,na yarda dashi sosai,kuma baiyi mun kama da irin mazan dake dukan mace ba,Yau dae hayaam take kowa ma,tasha mari wlh ko a ha6ar zani na,ba ƙaramin daɗi naji ba wlh,babban yaya ya burgeni sosai daya kwashe ta da mari,gobe ma in halinta ne ta ƙara yi mun shisshigi a aikina,angaya mata cewa sauƙi ne kula da babban yaya?nikaina kullum cikin fargabar kada nayi mashi kuskure nake,shiyasa nake lalla6ashi kamar kwai acikin cokali,Allah sarki yau hajia hayaam taji tafin hannun babban yaya koya raɗaɗin yake?tabb dole ma akwae mugun radadi tunda ta kasa cire hannu daga kan kuncinta, gwara ni Almakashi yasa ya datse mun gashin kaina,nan da wani lokaci gashin zai fito,ita kuwa marinta fa yayi? nasan har abada bazata manta da wannan ranar ba,
ashema hakanan take ma mutane kankanba ko sanin wacece ita bai yi ba"

Dariya sosai sehrish takeyi kamar wata zautacciya,sae faman sambatu takeyi,da alama taji daɗin Marin da Sgr yayi ma Hayaam,abun ko ajikinta,
  Lokacin da ta shiga part ɗin Sgr,a kishingiɗe ta same shi saman doguwar kujera,ya miƙe kafafunshi,bai kaiga shiryawa ba,Vest ce kawai ajikinshi sae shorts farare,
  Karasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan tace"ga wani breakfast ɗin na kawo maka,"
  sauko da ƙafafunshi yayi ƙasa ya miƙe daga zaune,ya jingina bayanshi a jikin sofan yana jira tayi serving ɗinshi,
  Sehrish ta jima awurin sgr tana mashi ɗawainiya har sai da ya kammala yin break fast din nashi,sannan ta koma ta gyara bedroom ɗinshi,bayan ta gama ta dawo ta gyara falon sannan ta ɗauko kayan abincin da yayi amfani dasu,ta wuce dasu kitchen,sae da ta wanke komai ta mayar dashi a ma'ajiyar shi,sannan ta wuce ɗakin azmee don suyi maganar zanen lallen da zatayi mata,

Wuraren ƙarfe biyu na rana,Junaid ya kar6o mata kayanta,akwati guda ne na atampha da lace,da kuma shadda,hada materials,duk an ɗinka mata su,
acikin bedroom ɗinta ya ajiye mata akwatin kayan,
sae da suka kammala sallar azhar,tukunna suka zauna zaman yin ƙunshi,anan corridor din ɗakunan nasu azmee tayi masu shimfiɗa suka zauna sama,tunda suka fara ƙunshin junaid keta zarya awurin sae faman santin kunshin sehrish yake yi,tun kafin a wanke mata ƙunshin ma,cikin nishaɗi suke yin firar su,tana yi mata ƙunshin suna fira tare da junaid,don ya kasa ya tsare sae anyi tare dashi,

A6angaren Hayaam kuwa tunda ta faɗa cikin bedroom ɗinta saman gado,take ta faman shessheƙar kuka,fuskarta tayi jawur saboda kukan da tasha,gefen fuskarta dauke da sahun yatsun sgr ruɗu ruɗu sun fito wurin ya kumbura sosai gashi kunnanta daya dumm take jin shi,tunda take arayuwarta wani ɗa namiji bai ta6a gigin ta6a lafiyar jikinta ba,sae akan Sgr ta fara shan mari,ta jima tana mamakin yarda ya ɗaga hannu ya kwasa mata mari,duk irin yarda ta ɗau wanka,ta bayyana surar jikinta don taja hankalinshi amma hakan baiyi tasiri akanshi ba,kwallin data shafa kuma ya tashi abanza saboda bai kalli cikin idonta ba bare asirin ya kamashi,
  ɗagowa tayi daƙyar take iya buɗe idanunta,wayarta ta ɗauko dake ajiye saman side drawer na gadonta,layin Aunty babba ta kira,wayar ta shiga ringing,
Cikin sa'a ta ɗaga kiran,Aunty babba nayin sallama,hayaam ta 6are baki ta fashe da wani sabon kukan,
  Tunda Aunty laila taji kukan hayaam hankalinta yayi mugun tashi,daga zaune take saman kujera amma tana jin kukan hayaam ta miƙe tsaye tana tambayar lafiya!
  Cikin shessheƙar kuka hayaam tace"Aunty lailai,yau Sgr ya gama dani,ya wulakantani kuma ya tozarta ni,yayi mun abunda wani ɗa namiji bai ta6a yi mun ba!'
  Hankali tashe Aunty babba tace"Me yayi maki ne!kiyi mun bayani yarda zangane,kuma kidaina wannan kukan da kikeyi,"
  dakatawa da yin kukan hayaam tayi sannan taci gaba da magana tana cewa"Mari na fa yayi,banyi mashi komai ba ya ɗaga hannu ya kwasa mun mari agaban waccen ƙaskantacciyar yarinyar ya mare ni....'
  Tunkan ta ƙarasa maganar Aunty babba tace"Ƙarya kike hayaam!Sgr bazai ta6a marinki ba batare da kinyi mashi laifi ba!dole akwai dalilin dabyasa ya mare ki,don nasan halinki baki da hankali,kuma baki da kamun kai,halan ƙoƙarin kai mashi hari kikayi saboda gajen hkr!!"
  Cikin en ena hayaam tace"nifa banyi mashi komai ba,kawai da safe ne nashiga ɗakin shi lokacin ya fito daga wanka,nayi ƙoƙarin jan hankalinshi ne da surar jikina,amma ko kallo ban ishe shi ba,shine nayi hugging nasa nayi ƙoƙarin ta6a short ɗin jikinshi don in tayar mashi da sha'awar shi,amma shine kawai ya kwashe ni da wani mahaukacin mari.....'
  dafe kai Aunty babba tayi tana cewa"ka ji tsiyar!wlh kin ban kunya hayaam!bansan ke wata irin mace bace!sam baki da kamun kai,idan jarabarki ta motsa, me yasa bazaki iya control din kanki bane agabanshi!wannan mutumin fa da kaina nayi maki alƙwarin cewa mijinki ne shi,idan kikayi haƙuri nan da ɗan wani lokaci zaki mallake shi duka,sae kiyi yarda kika ga dama dashi,amma tun yanzu saboda gajan haƙuri irin naki kin gaza jurewa,kina ƙokarin lalata mun shiri na!bazaki ta6a burge Sgr ba,saboda shi irin mazan nan ne da basa ra'ayin mace mara kamun kai ballagaza,wadda bata iya 6oye zalamarta akansu......'

Ɗaure fuska hayaam tayi jin yarda Aunty babba ke ta zaginta a fakaice,
Rai a6ace tace"Aunty laila nifa ban kiraki don kici mun mutunci ba,sae faman gaya mun magana kikeyi ta inda kike shiga bata nan kike fita ba,ni da na kawo maki kukana maimakon ki share mun hawaye na,Amma shine kike ta zazzaga mun masifa!wannan abun fa ba laifina bane,ko kece kika ganshi a yanayin dana same shi dole ki kai mashi attack balle ni da nake budurwa........'
  Waro ido waje Aunty babba tayi rae a6ace tace"Hayaam don ubanki ni kike gayama wannan maganar!ashe ke daƙiƙiyace baki da hankali!an gaya maki ko wace mace irin ki ce mara aji da zata dinga kai kanta wurin namiji har tana ƙokarin ta6a jikinshi!ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar mijin da banawa ba,duk irin mugun halin da nake dashi kuwa,a iya miji na natsaya ban zarce nan ba!amma ke fa?kullum kina yawon biɗiɗi wurin raba jikinki ga kowane ƙazamin namiji yayi amfani dake,don ki samu kuɗi,ki faɗamun wace riba kika ta6a samu a yawon barikancin naki!acikin mazan da kikayi mu'amala dasu akwai shegen daya ta6a cewa zai aure ki ne!!saboda baki da wani amfani awurinsu,tamkar totuwar masara kike da zarar sun cinye masarar jikinshi ya gama amfani sae su jefar dashi ƙasa,ni kuwa kinga ina da daraja tunda ina da aure kuma a ƙarkashin kulawar mijina nake,shiyake amfani dani kuma shi yake bani kuɗin da zanyi abunda nake so,riba biyu ga kuma lada ina samu......'
  Wani irin huci hayaam ta shiga fitarwa saboda tsabar 6acin ran kalaman da Aunty babba ta gaggaya mata,
Muryarta har shaƙewa takeyi wurin cewa"Aunty Laila!!ni kike faɗama waɗannan munanan kalaman!yau da kanki kike yi mun gori?Ya salam!wlh bazan ƙyale ki ba,kamar yarda kikayi mun gorin aure,nima zan raba auran ki Da Ishaq,ki dawo bazawara,"
fashewa da dariya Aunty babba tayi tana girgiza kai kafin tace"ni zan aje waya,kada ki manta kisha maganinki na rana,don da alama kin manta jawabin da likitan mahaukatan nan yayi maki,akan kula da shan magungunan ki akai akai,"ta ƙarasa maganar tare da kashe wayar,
 

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login