Showing 117001 words to 120000 words out of 432432 words
Chapter 40 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
sanyin murya yace"jira kike na fara gaishe ki ne"?
cikin sauri sehrish tace"ina kwana,ka tashi lafiya,"
fashewa da dariya junaid yayi yana kallonsu,harara fawan ya watsa mashi tare da mayar da idonshi kan sehrish yace"lafiya lou,haka yadace daga yanxu basai nace ki gaishe ni ba,daga zarar kin ganni kiyi hanzarin gaidani amatsayina na yayanki,"
Murmushi sehrish tayi tare da amsa mashi da"toh,"
junaid yace"bismillah ki zauna muyi breakfast atare mana," girgiza kai tayi tare da cewa"a'a inaso zan shiga kitchen ne wurin aunty azmee,"
Amsa mata yayi da"okey,"
Sannan cikin sauri ta juya tare da nufar kitchen din,
time din da taƙarasa kitchen ɗin azmee ta kammala gyare kitchen din tsaf, dakyar ta iya cewa"ina kwana aunty azmee,"
sai lokacin ta lura da ita,murmushi tasakar mata tare da cewa"lafiya lou babyn junaid,sai yanzu kika tashi daga baccin naki?dazu nashiga ɗakin naki na sameki kina bacci,
ciki sehrish ta shiga tana cewa"Aunty azmee ae da kinsani kin tashe ni,nikaina banasan yawan baccin nan da nake yawan yi,"
Azmee tace"ai baida amfani atlease yakamata ace duk in kika kammala sallar asuba ki daure kina karanta al'qur'ani, sannan ki dinga yawaita yin azhkar,insha Allah duk wani abu dake damunki Allah zai yaye maki shi,"
"Insha Allah zan yawaita yinsu kamar yarda kikace,yanzu inaso in kaima babban yaya breakfast ɗinshi,bansani ba ko kin kai mashi,
Azmee tace"a'a ban kai mashi ba,bari na haɗa maki sai ki kai mashi,"
Tsayawa sehrish tayi tana jiranta,
Bayan azmee ta kammala shirya mata breakfast din nashi acikin tray ta miƙa mata,hannu biyu tasa ta kar6a tare da kama hanya ta fuce daga kitchen ɗin,
Da sallama abakinta tashiga part din nashi,
har time din bai fito ba,yana acikin bedroom ɗinshi,ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan ta wuce izuwa bedroom ɗinshi daga bakin kopar ta tsaya tare da maimaita sallamar,
daga cikin bedroom ɗin tajiyo muryarshi yana cewa"wanene nan"
tuni tasha jinin jikinta,musamman data tuna abunda ya faru jiya ba ƙaramin tsoro ya bata ba,
murya na rawa tace"Ni ce,breakfast nakawo maka,"
"Okey,come in,"
a hankali tasa ƙafa tare da shiga ciki zuciyarta nata faman ɗar ɗar,
tsayawa tayi daga bakin ƙopan tana kallon shi,har lokacin yana kishingiɗe kamar yarda Omar ya barshi,
ganin ta tsaya abakin ƙopar yasa shi cewa"lafiya?
cikin sauri tace"bakomai,"
"Okey shigo ciki,ki fara gyara min toilet ɗina,"
ƙarasawa ciki tayi a hankali take tafiya tana satar kallon shi,eyes ɗinshi na'a rufe tamkar mai jin bacci,duk wani motsinta acikin kunnanshi yake jinshi,tura ƙopar toilet ɗin tayi tare da shigewa ciki,
Sai bayan da ta shiga ciki sannan ya buɗe idanun shi tare da bin ƙopar toilet ɗin da kallo,tunawa da abunda ya faru jiya tsakaninsu yayi,mayar da idonshi yayi tare da lumshe su,
ba da jimawa ba sehrish tafito daga cikin toilet tare da cewa"na kammala gyarawa,saura bedroom din,"
buɗe idanunshi yayi ba tare da ya kalleta ba yace "okey,ki duba cikin closet ɗina,ki ciro mun kayan da zan sanya,"
Cike da mamaki ido waje sehrish tace"dani kake"?
"Ni da waye" ya tambaya a ataƙaice,d'an murmushi tayi tare da wuce wa can ciki wurin wardrobe ɗinshi,mai girma da faɗin gaske gaba ɗaya glass ne ta gabanta,daga waje kana iya hango kayan sawarshi dake aciki gasunan abun kamar a company jeri jeri komai a tsare,tana ɗauke da sliding doors ajikinta,
Hannu sehrish takai ajikin wardrobe ɗin nan take ƙopar ta zuge da kanta,abun ba ƙaramin burgeta yayi ba,ruwan ido ta tsaya yi tama rasa wanne zata ɗauko mashi,saboda kowanne acikin kayan sawar nashi kyau suke yi mata,wata ƙopar ta zuge anan taga jerin kayan hausawa ta jima tana mamakin ashe yana dasu amma bai ta6a sanyawa ba,hannu tasa tare da ɗauko mashi haɗaɗɗiyar shadda gezna sky blue mai ɗaukar ido,
ruƙowa tayi a hannunta tare da dawowa wurin gadon Shi a lokacin harya gaji da jiranta ya sauko da ƙafafunshi ƙasa yana ƙoƙarin tashi,jin takon tafiyarta yasa shi ɗagowa yana kallon kayan data ruƙo a hannunta,
tsayawa tayi dab dashi sannan ta miƙa mashi,
ƙin kar6a yayi saima nuna mata hanya da yayi tare da cewa"basu nakeso ba,ki canza mun wasu bana sa kalar wannan,"
Jiki asanyaye sehrish ta koma ta maida shaddar sannan ta ɗauko mashi jeans da t shirt baƙa,
Komawa tayi tare da miƙa mashi,hannu yasa ya kar6a tare da furta"thanks" a gefen shi ya ajiye kayan sannan ya miƙe tare da kai hannu ya zame bathrobe ɗin jikin shi,cikin sauri sehrish tayi hanzarin barin bedroom ɗin takoma daga waje tana faman sauke ajiyar zuciya,ƙiris ya rage sgr ya saki murmushi don ba ƙaramin dariya ta bashi ba,ita duk atunaninta babu shorts ajikinshi shiyasa tayi saurin guduwa daga ɗakin nashi,
Tsaf ya kammala zura kayan ajikinshi bayan ya gama ya koma gaban dressing mirror ɗinshi tare da kai hannu ya ɗauki kwalbar turarennan nashi shumukh yabi ko'ina na jikinshi ya feshe shi da shi,sannan ya koma wurin shoe rack ɗin shi tare da zaro takalma ya zura a ƙafarshi,
tana atsaye tana jiran fitowarshi muryarshi ta ratsa kunnanta da cewa"ki shiga ciki ki gyara mun,"
Sannan ya wuce ta izuwa cikin falon nashi,
Shiga ciki sehrish tayi anatse ta soma gyara mashi bedroom ɗin nashi,
**************
A hankali motarsu tashiga cikin gidan abusufyan major ne ke driving ɗinshi yayin da yake zaune a back seat na motar,
Bayan yayi parking ɗin motar omar ya fito tare da wuce wa ciki,
Koda yashiga cikin falon samun su yayi azune saman 3seater sun haɗa kai sun kurawa plasma tv ɗin dake manne abango suna kallon tashar bollywood,
ba ƙaramin burgeshi su kayi ba,gyara muryar yayi tare da yi masu sallama,atare suka dago tare da kallon shi,hossana na ganin shi ta miƙe da gudun gaske ta tunkare shi,dakatar da ita yashiga yi da hannun shi amma ina sai da ta faɗa mashi,sosai ta rumgume shi tare da kwantar da kanta a saman wide chest ɗinshi,lokaci guda yaji wani irin yanayi atattare dashi,
Jahad kuwa a fusace tace"hossana menene haka wai?ba zaki bari ya ƙaraso ciki ba?
tamkar bata jita ba,haka ta ƙara ƙanƙame shi tana cewa"ya Omar nayi missing ɗinka sosai,jiya ko isasshen bacci bansamu ba saboda ban saka a idona ba,
hannu omar yasa tare da janyeta daga jikinshi suna kallon juna ido cikin ido yace"Am sorry pls,amma yanzu ae gashi nan nazo ko?
daga mashi kai tayi alamar eh,sannan tasanya hannunta cikin nashi suka ƙarasa ciki atare suka zauna kusa da Jahad saman 3 seater ɗin da take,
Cikin sanyin murya tace"sannu da zuwa ya omar,yasu abba da sauran mutanen gidan,
Fuskarshi dauke da murmushi yace"yawwa jahad,duk suna lafiya,ina fata kuma nasame ku cikin ƙoshin lafiya,"
Amsa mashi tayi da eh,sannan tace"namanta ban tambayeka ba,yasu Aunty zainab,"?
kafin yace wani abu hossana tace"ya Omar wai dagaske kana da aure"?a shagawa6e tayi maganar tamkar zatayi kuka,
cikin natsuwa ya soma kora masu jawabi"Ni banta6a aure ba,saurayi ne ni,ko budurwa ban ta6a ajiyewa ba,"
Jahad tace"amma ya Omar wacece ta ɗaga kiran wayarka da mukayi a lokacin?
shiru ya danyi kafin yace"ina tunanin younger brother ɗina ne Junaid,ya cika zolaya sosai,"
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
�?
maimaita sunan Jahad tayi "JUNAID!ya omar ƙaninka ne shima?
kallonta yayi tare da cewa"eh ƙanina ne,yana da kyau sosai ga kyan hali sannan ya iya kyakkyawan murmushi kuma shagwa6a66e,"
Murmushi su kayi jin yadda Omar ke zayyana musu ƙanin nashi da alama dae ba ƙaramin sonshi yake ba,
"Ya omar ka nuna mana hotonshi mu gani mana," acewar hossana,
Batare da 6ata lokaci ba Omar ya zura hannu a ajihun wandonshi ya ciro wayarshi tare da shiga gallery ɗinshi,hoton junaid ya buɗo tare da miƙa ma Hossana,hannu tasa ta kar6a tana kallon hoton cike da mamaki tace"wow! yaya Omar wai dagaske ƙaninka ne?wlh yana da kyau sosai dan Allah ka kaimu gidanku wata rana mu ganshi,"
Jin yarda hossana keta santin hoton junaid yasa Jahad sa hannu tare da kar6ar wayar,
Lokaci guda taji gabanta yayi wani irin bugu,tunda ta aza idonta akan kyakkyawar fuskar junaid bata ƙara cewa uffan ba,sam tagaza janye idanunta akan fuskarshi,bakomai take furtawa acikin zuciyarta ba face"Tabarakallahu Ahsanul khaliqin,"
Muryar omar ce ta katse ta da cewa"jahad naji kinyi shiru"?
jiki asanyaye ta ɗago tare da kallon shi tace"ya omar pls zan iya tafiya da wayarka cikin ɗakinmu?yanzu zan dawo,"
murmushi ya saki tare da cewa"ba damuwa zaki iya zuwa,"
cikin sauri ta miƙe tare da nufar bedroom ɗin nasu ta shige ciki,
"Ya omar bari nakawo maka breakfast nasan baka ci komai ba," hossana ce tayi maganar yayin da take miƙewa daga saman kujerar,"
Ruƙo hannunta yayi tare da cewa"dawo ki zauna,idan kika tafi wa zai tayani fira,"
ƙayataccen murmushi tasaki tare da komawa ta zauna daga gefenshi sannan tace"Ya Omar yaushe zakayi aure ne?
"Ranar dana samu maisona," ya bata amsa yayin da idonshi ke akan agogon hannunshi,
cikin shagwa6a tace"ya omar ni nasan cewa kana da ƴan mata dayawa da suke sonka,kawai dae kaine baka shirya yin auren ba,"
"haryanzu bansamu kalar wadda nakeso ba hossana,"
ɗan turo baki tayi tare da cewa"ka faɗamun kalar matar da kakeso ka aura,zan tayaka da addu'a insha Allah,"
murmushi ya ɗanyi tare da kwantar da bayanshi ajikin sofa ɗin yadda zai samu damar kallonta sosai sannan yace"Inason mace natsastsiya kamila,miskila mai ilmin addini dana zamani,mai ladabi da biyayya,idan Allah ya bani mace mai irin wannan suffar tuni zanyi wuff da ita,"
tunkan ya ƙarasa maganar hossana ta ɗaure mashi fuska,sunnar dakai ƙasa tayi tamkar zata zubar da hawaye,
"Meya faru ne"? Ya tambaya yana kallon ta,
Cikin shessheƙar kuka tace"ya omar ba dole sai mace nutsastsiya ba,ko miskila,in dai tana sonka tsakani Allah kawai ka aureta,"
kawar da fuskarshi gefe guda yayi yana murmushi,
Sanya hannunta tayi acikin nashi tare da kwantar da kanta asaman kafaɗarshi,
...sun jima a haka batare da wani yace ƙala ba,kusan 30 mins sai ga jahad tafito hannunta ɗauke da wayarshi,tsayawa tayi tana kallonsu shi ya lumshe ido,hossana kuma har ta fara bacci,
murmushi ta saki tare da samun wuri ta zauna daga gefen shi sannan ta ambaci sunan shi "ya Omar,"
Buɗe donshi yayi a hankali yana kallonta,miƙa mashi wayar tayi tare da cewa"thanks,"hannu yasa ya kar6i Wayar sannan ya mayar da idonshi tare da rufe su,.
Ajiyar zuciya tasaki tare da miƙewa ta koma cikin bedroom ɗinsu,saman gadonsu ta haye a inda ta ajiye drawing book ɗinta,ashe lokacin da ta kar6i wayar omar ta shigo dashi bedroom ɗin nasu,zama tayi tare da ɗauko kayan zanen ta acikin school bag ɗinta,a natse ta zauna tare da zana fuskar,ba ƙaramin kyau zanen yayi ba,fuskar ta fito raɗau dauke da wannan murmushin nashi,zuba ma zanen ido tayi tana kallon shi,lokaci guda taji tana son taganshi face to face~~~~
************************
Yau tunda ta farka da kewarsu jahad ta tashi saboda mafarkinsu da tayi,fitowa tayi daga cikin bedroom ɗinta jikinta na sanye da riga bubu ta material,
tsayawa tayi daga tsaye tana sauraron wayar da Aunty babba keyi,da alama da hayaam suke magana saboda taji ta ambaci sunanta sai faman 6a66aka dariya take yi,
"wlh ba kiji irin farin cikin da nake ji ba,yau burina zai cika na ganin kin koma gidan da zama,hayaam bana so ki raga ma yarinyar nan!so nake acikin one week ki ƙuntata ma rayuwarta har taji ta tsani zama acikin gidan,maƙirci kawai zaki cigaba da haɗa mata ae nasan kin ƙware a wannan 6angaren shiyasa nake yin ki,"
girgiza kai hafsat tayi tare da ƙarasawa ciki ta samu wuri saman 2 seater ta zauna tana sauraronta,sun jima suna wayar kafin daga bisa ni su kayi sallamar,mayar da wayar tayi tare da ajiyewa agefenta,sannan ta ɗago tare da kallon hafsat tace"gulmawuya halan kin fito don kiji abunda muke tattaunawa ne?
Murmushi hafsat tayi tace"mommy kenan ashe haryanzu kina akan bakanki na ganin cewa hayaam ta koma gidansu Abbana da zama hmmmm whatever ni wannan ba damuwa ta bane,kawai akwai shawarar da nakeso na baki in ba damuwa,"
zuba mata ido aunty babba tayi tana sauraronta,.
Ci gaba da magana hafsat tayi"Mommy aunty hayam zata koma gidan da zama wannan ba laifi bane Amma zai iya zama abun kunya,amma maganar a ƙuntata ma rayuwar yarinyar dake acikin gidan sam wannan bai taso ba,in ba haka ba wlh zaku yi danasanin yin hakan,"
wata uwar harara aunty babba ta watsa mata kafin tace"ke tashi ki ban wuri!tun kafin ranki ya 6aci,"
Maƙe kafaɗa hafsat tayi tare da cewa"mommy dama ita gaskiya ɗaci gare ta,kullum ina faɗa maki kiji tsoran Allah,ki daina biye ma ruɗin duniya.....'
Katse ta aunty babba tayi tare da cewa"karfa kice zakiyi mun nasiha,ko iyayen da suka tsugunna suka haife ni ban ta6a sauraran nasiharsu ba balle ke ƴar cikina dana haifa,
tana kai ƙarshen maganarta,takai hannu tare da ɗaukar wayarta sannan ta miƙe tare da wuce wa ciki,
"Mommy ae da alama basu yi maki nasihar ma,don da ace suna yi maki da duk ba haka ba,nibansan ma ya akai abba ya auroki ba anya ba rufa ido kukayi mashi ba,"
"Hafsat! Me kike cewa"?
A ɗan firgice hafsat ta juya tana kallonta duk a tunaninta ta jima da barin falon ashe bata ƙarasa fita ba,
Cikin sauri tace "haka nace ni dae na gode ma Allah daya bani uwa tagari kamar ki,"
ba don ta yarda da maganarta ba ta juya tare da wuce wa upstairs,
Ajiyar zuciya hafsat ta saki tana faman tiƙar dariya,
�?
�?
_💋Boss Bature💋_
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
Lokaci guda Amal ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya,ashe magen hayam ce ta faɗo ɗakin,sai faman kuka takeyi miyauu miyauu,da alama yunwa take ji ne,Batare da 6ata lokaci ba Amal ta zuƙunna ta shiga tattara kuɗin da sauri da sauri jikinta na kerma,don a matuƙar firgice take saboda magen nan data tsorata ta,
Miƙewa tayi hannunta ɗauke da kuɗin cikin sauri ta fice daga ɗakin,komawa tayi cikin ɗakinsu hayamm,jiki na rawa ta buɗe wardrobe ɗin kayansu,doguwar riga ta ɗauko ta Abra tare da mayafinta,
A hanzarce ta shiga zura rigar ajikinta,ba ƙaramin yawa rigar tayi mata ba har ƙasa take ja,ga wuyar rigar da yayi mata yawa,yafa mayafin tayi,
Sannan cikin sauri ta fito daga cikin ɗakin,a nan waje ƙopar ɗakin ta ɗauki slippers tare da zura wa aƙafarta,
Jiki na kerma AMAL ta kama hanyar fucewa daga cikin gidan,sai da takai baƙin ƙopar fita sannan ta ɗan tsaya tare da juyawa tana kallon cikin gidan yayin da hawaye ke shararowa daga idonunta,bazata ta6a mantawa da irin uƙubar da tasha acikin gidan ba, ta dan jima a haka,daga bisani tasa kai cikin sauri tabar gidan,
Kamar walk'iya haka Amal tabar santar gidan gaba ɗaya,duk da bata jin kwarin jikinta,haka ta jure ta kama hanyar sauri sauri gudu gudu,ita kanta batasan ina zata dosa ba,amma tana da tabbacin cewa tasha zata nema domin ta hau motar zuwa Abuja,
...(Finally Amal taci nasarar barin gidan,saura fatan sauka lafiya)
*****************
Sosai jahan ke ta faman sakin dariya cike da nishaɗi,bakomai yasa shi dariya ba face Ayaan dake zayyana mashi irin halin daya shiga na barazanar da haroon ke masu,hankalin su kwance basu da wani sauran damuwa,suna a kwance cikin hotel room ɗinsu,basu jima da fitowa daga wanka ba,kowannansu na sanye da white shorts ajikinshi,suna rungume da juna cikin lallausan bargo,
"Wlh jahan naji jiki sosai,wai ashe haka abun yake?sai gani a sume,gaskiya haroon ba ƙaramin shaiɗani bane,nasha Wahala a ranar nan,"
"dama kai rago ne Ayaaan,nafi ka juriya shiyasa abun yazo maka ahaka,ranar naji kishi da baƙin ciki sosai,har yanxu in na tuna abun ba ƙaramin ƙuna zuciyata ke yi mun ba,"acewar jahan,
"Pls ni banaso muna tuna abunda ya wuce,hakan zai iya sanya mana damuwa acikin zuciyoyin mu,mubar maganar kawai,"
Jahan yace"shikenan mu bar maganar amma inaso na tambayeka pls,yanzu kwatsam a lokacin nan da ace bamu ba haroon kuɗin nan ba,ya saki videon mu a social media har Abba da babban yayanmu suka gani,me kake tunanin zai biyo baya,"
Da wasa jahan yayi maganar amma har sai da zuciyar Ayaan ta ɗan buga,
"Abunda zai faru shine,zuciyar Abban mu zata buga anan take ya yanke jiki ya faɗi,babban yayan mu kuma zai yi mana bugun mutuwa,abunda ba'a fata kenan,"Ayaan ya ƙarasa maganar yana dariya,
Shima jahan dariyar yayi yana cigaba da sauraron shi kafin daga bisani suka ɗaura daga inda suka tsaya,"
**************Sehrish
Tun bayan da tadawo cikin bedroom ɗinta,wanka tayi tare da ɗauro alwala,bayan ta kammala sallar,ta koma wurin wardrobe ɗinta,ta ciro kayan da zata sanya,dogon wando ne na roba,Army trouser tun lokacin da suka je siyayya,ta ɗauke shi saboda ba ƙaramin burgeta kayan sojoji suke yi ba,tare da farar shirt off shoulder ta zura ajikinta,ba ƙaramin kyau tayi ba,komawa tayi gaban dressing mirror ta ɗauki turarenta tabi ko'ina na jikinta ta feshe shi,wuri ta samu saman chair ɗin da ke a front ɗin madubin,ribbom ɗinta ta ɗauko tare da zura shi a hannunta,yau taci alwashin saita ɗaure gashin kanta,
da iya ƙarfinta na ƙarshe ta tattare gashin ta haɗo shi wuri guda,tare da zura ribbom ɗin ta ɗaure shi sosai,ya sauko a gadon bayanta,
Murmushi ta saki tana kallon kanta acikin mirror ɗin kafin daga bisani ta miƙe tare da wuce wa gaban gadonta,within 15 mins ta kammala gyara bedroom ɗinta,komawa tayi tare da hayewa saman gadon,takai hannu ta ɗauko wayarta dake ajiye saman side drawer,
Wi-fi ta kunna nan take messages ɗin whatsapp dinta suka soma shigowa acikin wayarta,shiga whatsapp grp tayi na school ɗinsu,new student ne ke ta introducing ɗin kansu tare da pics ɗinsu,tunani ta soma yi bata da hoto ko ɗaya,gashi tana buƙatar pictures saboda ita ma tayi nata introduction din,
tana cikin wannan tunanin kiran junaid ya shigo wayarta,cikin sauri tayi picking tare da karawa a kunnanta,
Tun kafin tayi sallama yace"yunwa nake ji,"yana faɗin hakan ya katse kira,murmushi Sehrish tayi tare da cewa"shagwa6a66e kawai"
Ajiye wayar tayi saman pillow sannan ta miƙe tare da saukowa daga saman gadon,sam ta manta bata yafa mayafi ba,saboda saurin da take yi nata kai mashi tadawo don tayi pictures din,takalmi kawai ta zura a ƙafarta,sannan ta buɗe ƙopar ta fita,
A natse take tafiya hanyar kitchen ta nufa,wayam babu kowa a main palour ɗin da alama duk