Showing 99001 words to 102000 words out of 432432 words
Chapter 34 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
jujjuya kwalbar dake hannunshi,
Tare da ita ya fito daga ɗakin yaso yaje wurin Yarinyar saboda ya rarrashe ta ya fahimtar da ita amma dare yayi sosai baisan awane hali take ciki ba yanzu,wuce wa bedroom ɗinshi kawai yayi tare da kwalbar ruƙe a hannunshi saboda yin Investigation akanta,dole ya binciki yarda akai akasamu allurar acikin gidan saboda dama sun jima suna neman haramtaccen companyn miyagun kwayoyin dake sarrafa allurorin a 6oye masu cire imanin mutun lokaci guda,
😳😳😳
***
A 6angaren sehrish kuwa abun gwanin ban tausayi haka ta faɗa ɗakinta tana faman shan kuka,gefen gadonta tazauna domin ƙarashe kukan nata,ta jima batare da yin motsi ba,hannunta na ruƙe da rigarta sai ƙara matse wurin take yi tana kuka,duk wurin da sgr ya damƙa ajikinta ba ƙaramin raɗaɗi yake yi mata ba saboda baiyi mata ruƙon wasa ba,idanunta sun kumbura sosai saboda kukan da tasha.......'
Bakomai tafi ji ba face yarda taga Omar na bugunshi,tsoranta karya lahanta shi akan abunda take da tabbacin cewa ba yin kanshi bane,😢
Daƙer ta iya miƙewa ta wuce toilet saboda ta tsarkake jikinta,rufe ƙopar toilet ɗin tayi kusan 15 mins sai gata ta fito ɗaure da towel tana faman sauke ajiyar zuciya,har cikin ranta ba ƙaramin sanyi taji ba da Marshal Omar yazo don da baizo ba adai dai wannan lokkacin da SGR ya jima da yin raping dinta,kuma babu tabbacin cewa zata rayu saboda ba ɗigon Imani atattare dashi lokacin,
Wardrobe ɗinta ta buɗe tare da curo wata rigar baccin ta zura ajikinta, sannan ta koma tare da hayewa saman gadon,janyo bargonta tayi tare da lullu6e jikinta dashi,
rufe idanunta tayi nan take brain ɗinta,ta tariyo mata fuskar sgr lokacin da yake kallon cikin idanunta sweat dinshi na zuba a fuskarta nan take wata irin kasala ta rufe mata jikinta,sam bacci yaƙi ɗaukarta saboda daga tazo runtse idonta sai taji kamar SGR zai faɗo mata cikin ɗakin,firgita ta dinga yi duk tabi ta tsoratar da kanta duk da ta rufe ɗakin ammma ji take kamar zai biyota ne,saboda yarda taga ya buge omar ya afko mata ɗazun,tana cikin wannan halin wayarta ta buga uban ringing aikuwa a gigice ta wuntsila ta faɗo ƙasa daga saman gadon tana ƙoƙarin shigewa ƙarƙashin gadon,yadda kasan wadda sanyi ya kama,haƙoranta sai kerma sukeyi kaf!kaf!!kaf, yatsun hannunta kuwa kamar waɗanda aka sanyawa battery sai rawa sukeyi ba ƙaƙƙautawa,ta jima a haka tana faman zazzare ido, sai daga bisani ta gane cewa wayarta ce ke ringing,lalla6awa tayi tataso tana tafiya cikin sanɗa har ta ƙarasa wurin side drawer ɗinta buɗewa tayi tare da ɗaukar wayarta ta dake ringing,tamkar wayar zata sul6e daga hannunta saboda kermar da fingers din nata keyi,Sunan AMRISH ne ya bayyana akan screen din wayar,lokaci ta duba kusan ƙarfe ɗaya da rabi na dare,katsewa kiran yayi saiga message ya shigo nata,cikin sauri ta buɗe tare da karantawa kamar haka
_Hi reesh,nayi missing ɗinki sosai shiyasa na kira don na tsoratar dake saboda nasan cewa zaki firgita in kirana yashigo a wannan lokacin,May be ma kina nan kina Jan minshari ne_
Murmushi sehrish tayi sosai bayan tagama karanta,reply ta mayar mata da cewa"i missed u too my lovely friend,kinci nasara akaina saboda kin tsoratar dani sosai,gobe ba school amma zamuyi video call ne,"
Bayan ta kammala tura mata saƙon ta mayar da wayar asaman drawer din ta ajiye,safa da marwa tashiga yi acikin bedroom dinta tana tunanin taya akai Sgr yyi attempt na raping ɗinta!!!? tsayawa tayi cak lokacin da zuciyarta ta ambaci sunan HAROON,gabanta ne taji ya faɗi bakomai ta tuna ba face maganar daya yi mata nacewa"Basai kin gode mun ba Aikin ladane,nidai burina ki kaima shi ya hanzarta yi gobe da safe kinzo kiyi mun godiyar,
Dafe ƙirjinta tayi cikin tsananin tashin hankali, hannu ta aza akai muryarta na rawa tace"innalallahi wa'inna ilahirraji'un nashiga ukuna!!haroon yaja mun bala'e...tabbas shine silar komai !! Shiya bani allurar dana kaima babban yaya, wayyo Allah na...yanzu dole su tuhume ni akanta!!Haroon ya gama dani.............
A daren ranar sehrish bata runtsa ba yarda taga rana haka taga dare,tasha kuka kamar kamar me ƙarshe ma tashiga toilet tayo alwala tafito ta shimfida carpet tashiga jera salloli har sai da ƙafafunta suka soma raɗaɗi sannan ta dakata tare da ɗaga hannayenta sama tana roƙon Allah ya tsareta daga sharrin Haroon,sai wuraren asuba bayan tayi salla sannan bacci yayi awon gaba da ita a saman sallayar,💔
Morning ❤❤�?
Wuraren ƙarfe takwas azmee tashiga bugun ƙopar bedroom dinta,har cikin tsakiyar kanta tadinga jin bugun,a gigice tafarka tare da miƙewa ta nufi kopar ta buɗe tana tambayar wanene,
Bin ta da kallo azmee tayi ganin yarda fuskarta ta kumbura suntum ga idanunta ma sun ƙankance saboda rashin isasshen bacci,hankali atashe tace"Lafiyarki kuwa sehrish?Anya ma kinyi bacci jiya? Fuskarki kamar ta wanda yasha kuka?
Maimakon ta bata amsa sai ta fashe da wani kukan saboda tunawa da halin da take ciki,ganin hakan yasa azmee shiga cikin ɗakin tare da rufo masu ƙofa,.
ruƙo hijabin sehrish tayi taja ta suka zauna daga gefen gadonta sannan ta kalle ta anatse tace"faɗamun meya faru ƙanwata?meyasa ki shiga cikin damuwa....."
cikin shessheƙar kuka sehrish ta Zayyana mata dukkan abunda ya faru adaren jiya ta ƙare da cewa"a....Aunty azmee wlh ba laifina bane Haroon ne ya bani allurar, banyi tunanin zai cutar dashi bane,yanzu ni bansan ya zanyi ba! Idan babban yaya ya tuna abunda ya faru jiya dole ya tuhume ni akan ni na kawo mashi allurar.........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan daya zo mata,
Shiru azmee tayi kamar mai nazarin wani abun kafin daga bisani tasanya hannunta a kafaɗar sehrish din tace"Just Calm down ur mind!ki share hawayenki,ynx yakamata muyi tunanin samun solution before ya tuna din, amma nayi mamakin a ina haroon ya samu allurar daya baki ashe dama kuna ƴar tsama dashi baki ta6a sanar mun ba!?
cikin shessheƙar kuka sehrish tace"bansan me nayi mashi ba aunty azmee haroon ya tsaneni nima bana son ganinshi saboda ya jima yana ƙuntatamun bana son na tayar maki da hankaline shiyasa ban ta6a sanar dake ba......'
Jinjina kai azmee tayi kafin tace"Kinyi kuskure sehrish!!baki ɗaukeni kamar yarda na ɗauke ki ba,rashin gayan mun da kikeyi shine zai jefa ki cikin matsala....'rai aɗan 6ace azmee keyi mata magana,
"Aunty azmee kiyi hakuri nasan nayi kuskuren rashin sanar dake yanzu nagane hakan,"
ajiyar zuciya azmee ta saki kafin tace"shikenan ya wuce,naji daɗi sosai da yakasance Omar ne ya ƙwaceki a wannan lokacin da bansan mai zai biyo baya ba,ynz babban matsalar dole ne suyi zargin wani abu akanki,koda Omar ya tambayeki wanene ya baki allurar ki sanar mashi kawai that's the only solution!!!
girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"a'a aunty azmee bazan iya cewa haroon ne ya bani allurar ba,saboda bakowa ne zai yarda dani ba,kuma zai iya ƙullamun sharri ne,ina tsoran hakan,"
gyaɗa kai azmee tayi tare da cewa"hakane kuma kin faɗi gsky,abun zai iya juyewa ya dawo kanki,amma naso ki sanar dasu cewa shi ya baki allurar saboda ki samu ki tsira,amma bakomai nasan cewa Omar zai fahimce ki in kikayi mashi bayani,babban tashin hankalin shine idan shi Sgr din ya tuna abunda yafaru gsky akwai matsala!!!!
Sun jima suna tattaunawa kan yarda zasu shawo kan matsalar kafin daga bisani Azmee tace"ki kwanta ki huta don nasan jiya bakiyi bacci ba,ni bari na wuce kitchen,"
Amsa mata tayi da toh,sannan ta cire hijab ɗin jikinta ta kwanta saman lallusan katifan gadon,lamo tayi a hankali brain din tadinga tariyo mata abunda ya faru adaren jiya,musamman yarda yayi mata rumfa da wide chest dinshi yana faman gurnanin nan yana kallon cikin idonta,wani irin yanayi mara misaltuwa,
ba ƙaramin shock taji ba alokacin duk da tana cikin tashin hankali hakan bai hanata jin emotion dinshi ba,
Hannu tasa tare da janyo fillow ta rungume shi sosai ajikinta saboda yanayin daya zo mata tuni taji wata irin kewarshi ta lullu6eta kamar maijin zazza6i,runtse idonta tayi nan take wannan ƙayataccen murmushin daya sakar mata jiya yadawo mata a idonta,cikin sauri ta buɗe su tana faman sauke ajiyar zuciya,ban ta6a ganin kyakkyawan murmushi ba sai adaren jiya Ya Allah ka mallaka mun shi ❤💋�?
Ta furta fuskarta dauke da murmushi daga bisani wani baccin ya kuma yin awon gaba da ita,
******
fitowa Omar yayi daga bedroom dinshi jikin shi na sanye da jallabiya maroon colour,jiya da tunanin abunda ya faru tsakanin SGR da yarinyar nan ya kwana,burin shi kawai yaje yaga ya rabin ranshi ya kwana, shiga part dinsa yayi tare da wuce wa bedroom dinshi,
abun mamaki samun shi yayi tsaye agaban mirror jikinshi na sanye da bathrobe ya ɗaure suman kanshi ta baya,da alama fitowarshi kenan daga bathroom,
shiga ciki omar yayi tare da yi mashi gyaran murya,juyawo sgr yayi ya kalle shi tare da 6ata fuska yace"Am angry wit u omar,bana son ganinka cos i even texted u about my sick amma shine ko kazo ka ganni ko? Ya fadi tare da tsuke mashi fuska,
Tsayawa Omar yayi yana kallon shi kamar mai nazarin wani abu,yayi wani fresh dashi sam babu alamun damuwa attare dashi,
Cikin mamaki yace"Oh kana nufin ka manta abunda ya faru jiya"?
"Meya faru"!? Ya tambayana yana kallonshi aɗan ruɗe,
matsawa kusa dashi Omar yayi tare da aza hannnayenshi akan shoulders ɗin Sgr yace"Wai dagaske kamanta komai?duk abunda ya faru jiya"?
girgiza mashi kai yayi tare da cewa"Omar ni fa i don't know what are u talking abt explain to me pls,
fashewa da dariya Omar yayi daker ya tsagaita yace"pls ka tuna mana ko kaɗanne,
Shiru sgr yayi yana bin shi da kallon bana son raini, can dae yace"Jiya ni bansan ina kaina yake ba,i Can't remember,
jinjina kai Omar yayi har lokacin fuskarshi ƙumshe da dariya yace"kaine kayiwa kanka allura jiya?
ɗan yatsina fuska yayi kafin yace"yeah its me meya faru ne?
girgiza kai omar yayi tare da cewa"babu komai kawai inaso inji kaine ka ɗauko allurar?kuma kasan wace allurace kayi ma kanka"?
ɗan shiru Sgr yayi yana kallon fuskar Omar na wani lokacin a ƙoƙarinshi na ya tuna meya faru,ajiyar zuciya yasaki tare da cewa"Bani bane,wannan yarinyar ne, itace ta ɗaukomin,"
ruƙo hannunshi Omar yayi yaja shi suka zauna daga gefen gadonshi sannan yace"da ka tashi yau da safe kana nufin kwata kwata baka ga wata alama ba ajikin ka ba"?
ɗaure mashi fuska yayi yace"Omar banason wannan tmbyar nifa ban gane me kake nufi ba,"
Hannu omar yasa yana shafa ƙirjinshi yace"kwantar da hankalin ka mana,just tell me da wani yanayi ka tashi yau ajikin ka,
Shiru sgr yaɗanyi na wani lokacin kafin yace"bro i can't explain it,yanayi mara misaltuwa jiya na kwanta da ciwo, but dana tashi naji ni'ima atattare dani ga wani ƙarfi da nake Ji not only that omar When I went to the toilet, I saw something that really confused me because I had never seen it before..................🙊
Weekend mu haɗu on monday insha Allah, don't forget to follow me on tiktok boss_bature❤️
💋Boss Bature💋
Follow this link to join my tiktok acct 👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
"What's it"? Omar ya tambaya yana kallon shi, ganin yarda Omar ke kumshe dariya yasa shi fasa yin maganar ya ɗan ɗaure face ɗinshi yace"omar banason wasa fa pls tell me the truth, Did something happen last night? Naga bed sheet dina duk yayi wani squeezing kamar anyi dambe asaman shi,
dariya sosai Omar yayi kafin yace"no ba wani abu just forget about it, na same ka ne kawai a wani yayi na ciwo so na ɗan taimaka maka ne har nasamu bacci ya ɗauke ka,"
ta6e baki sgr yayi yana kallon shi don bai yarda da abunda ya faɗa mashi ba, hakanan omar bazai tasa shi gaba yana mashi dariya ba just without any reason,
miƙewa Omar yayi tare da kallon shi yace"bari na sauka down ko kana buƙatar wani abu ne nasa akawo maka"?
juyawa sgr yayi ya kalli tray din da ke ajiye saman table ɗinshi yace"wannan yarinyar tazo ta tattara wannan kayan,ga bedroom dina ma inaso a gyaramun,"
"Okey zan faɗa mata, ka huta my man,"
Juyawa omar yayi zai fuce har yakai bakin door din ya waiwayo don ya kalli sgr karaf suka haɗa ido, cikin mamaki yace"Omar nifa wani kallo naga kana min irin kallon jarababben namijin nan......' ya faɗi yana tsuke mashi fuska,
Fucewa omar yayi yana ƴar dariya, yamutsa fuska sgr yayi tare da cewa"Omar nason haukata ni, bansan wannan dariyar nashi me yake nufi ba," yayi maganar tare da kwantar da bayanshi saman lallausar mattress ɗin, kwakkwaran juyi yayi asaman gadon, kai tsaye idonshi ya sauka akan siraran gashin dake zube saman bedsheet dinsa, cikin sauri ya ɗago da kanshi tare da zuba ma gashin ido, mamaki ne ya kamashi taya akai gashin kanshi ya zuba don kuwa yana da tabbacin cewa sumar kanshi bata kakka6a saboda gyaran da take sha, hannun shi yakai a hankali tare da ɗauko siraran gashin guda uku ya zuba masu ido yana kallonsu, dogon gashi ne mai tsayin gaske, sak irin launin sumar kanshi wato dark brown colour, natsuwa yayi yana nazarin gashin, kafin yasanya hannunshi tare da ɗaukar siraran gashin a hannunshi,yunƙuwa yayi tare da miƙewa daga saman gadon, ya nufi gaban dressing mirror dinshi, zama yayi asaman front chair din madubin, sannan ya ajiye siraran gashin asaman shi, hannu yasa tare da tsinko gashin kanshi siriri guda ɗaya, sannan ya ajiye shi a gefen waɗancan sauran guda ukun, within 5 mins ya gane difference ɗin dake tsakanin su,tabbas wannan ba hairs ɗinshi bane to na wanene, asaman bedsheet ɗinshi kuma? hannu yasa ya ɗauki siraran gashinan guda uku, sannan ya tashi tsaye ya nufi bedside drawer ɗinshi, buɗewa yayi tare da buɗe jotter ɗinshi dake ajiye acikinta, a shafi na farko ya saka siraran gashin sannan ya rufe jotter ɗin, tare da mayar da drwer chest din ya rufe, wuce wa yayi wurin closet ɗinshi domin shirya kanshi,
***********💋
bayan fitar marshal omar daga part din Sgr kaitsaye down stairs ya wuce wurin dining area dinsu ya nufa ganin aunty azmee nata faman jera masu breakfast dinsu, tunkan ya ƙaraso ta soma sakar mashi murmushi tana cewa"Omar barka da fitowa fatan ka tashi lafiya,"?
fuskarshi asake yace"lafiya lou Alhmdllh,"
shiru ya ɗanyi kafin yace"am ina wannan yarinyar take ne sehrish"? Har sai da gaban azmee ya fadi rass jin abunda yace,dama tasan saiya tambayeta akan maganar nan,
murya na rawa tace"bata jin daɗi ne tana a bedroom ɗinta,ni nace mata ta kwanta ta huta shiyasa bata fitowa. Ba.......'
"Ta sanar dake game da abunda ya faru jiya"? Ya katse ta da tambaya,
"Eh ta sanar dani komai," ta fadi adabarbace,
Omar yace"okey ina son magana da ita, ki ce tazo tasame ni a part ɗina ina jiranta,"
Cikin sauri ta amsa mashi da toh, sannan ta bar jera abincin da take yi ta wuce ɗakin sehrish,
A hankali ta tura ƙofar tashiga da sallama, kwance ta same ta sai faman sharar bacci take yi, har lokacin jikinta bai daina yin kerma ba,
matsawa tayi dab da ita tare da sanya hannu ta ɗan bubbugi kafadarta "Sehrish !!sehrish!!
Har cikin dodon kunnanta taji kiran a firgice tafarka tare da miƙewa tsaye tana cewa"La'ila ha'ilallah.........' rufe mata baki azmee tayi tare da cewa"ki natsu ni ce" a hankali tashiga sauke ajiyar zuciya tana kallon azmeen da idanunta da suka canza launi saboda bacci,
Janye hannu azmee tayi daga bakinta sannan tace"Omar ne ke son magana dake yace ki same shi a part ɗinshi yanzu,"
zare ido sehrish tayi murya na rawa tace"Aunty azmee ni kuma.....na shiga uku....me zai tambaye ni......'. Katse ta azmee tayi tare da cewa"kada ki damu nasan game da allurar nan ne zai tambaye ki, kawai ki fada mashi gaskiya a wuce wurin,"
fuskarta tamkar za tayi kuka tace"Aunty azmee ina tsoro fa kada naja ma kaina,"
girgiza kai azmee tayi tare da cewa"ba wani tsoro omar zai fahimce ki, kina 6ata lokaci fa ki tashi ki tafi,
Tana kai ƙarshen maganar ta juya ta fuce daga ɗakin, jiki asanyaye sehrish ta sauko daga saman gadon, hannu tasa ta ɗauki hijab ɗinta wadda ta ajiye asaman gadon milk colour ta zura ajikinta,
Buɗe ƙopar ɗakin tayi ta fito tare da miƙar hanya ta wuce part dinsa, tsayawa tayi daga ƙopar shiga tana ƙoƙarin dai daita natsuwarta,sallama tayi mashi amma shiru ba'a amsa ba, ƙafa tasa tashiga daga ciki,babu kowa a falonsa komai anatse yake sai ƙamshi dake tashi,
Shiga ciki tayi tare da samun wuri ta tsaya a kusa da royal sofa din dake a kewaye, gabanta sai faɗuwa yake yi kamar mara gaskiya,
"Ya Allah ka bani ikon amsa tambayar da zaiyi mun,bana son nashiga matsala da kowa acikin gidan nan, nasan zasu iya zargina wayyo Allah na," ta furta tana faman yarfa hannunta, cike take da zullumin me zai biyo baya,
tana cikin wannan tsayuwar wayar shi ta shiga ringing a firgice taɗan ja da baya saboda bata tsammaci jin sautin wani abu ba, bin wayar tayi da kallo tana ajiye asaman 3 seater din don anan yabarta,
katsewa kiran yayi sai ga wani ya kuma shigowa, matsawa tayi a hankali saitin kujerar tana kallon wayar, ranta ne yabata ta ɗaga kiran taji wanene wata'kil kiran gaggawa ne,
Tamkar ana tunzurata haka taji, hannu takai tare da ɗaukar wayar tayi picking call din tare da karawa a kunannta, tun kafin tayi sallama taji ance"Ya Omar shi ne jiya kace in ka koma zaka kira ni awaya amma naji shiru ko? Muryar hossana ce ke magana,
Shiru sehrish tayi tana sauraron maganarta,.
Acan kuwa jin tsit Omar ɗin yayi mata shiru yasa ta cewa"kana ji na kayi mun shiru ko, Allah idan bakayi magana ba yau ko breakfast bazanyi ba....' ashagwa6e tayi maganar,
murmushi sehrish tayi jin yarda yarinyar ke magana, sai a lokacin tace"bashi bane, baya kusa ne,"
�?
Jin muryar mace yasa hankali hossana tashi ruƙe qugu tayi dama tana atsaye jikinta nasanye da kayan bacci riga da wando red colour, ta ƙara kara telephone din a kunnanta, tace
"ƙanwarshi ko budurwarshi ko matarshi wacece ke aciki ? ta tambaya a ƙule,
"Matar shi ce," sehrish ta faɗi cike da zolaya, aikuwa nan take hankalin hossana ya tashi, muryarta tamkar zatayi kuka tashiga kwalama jahad