Showing 111001 words to 114000 words out of 432432 words
Chapter 38 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
shiga ran mutane,ni nagaza fahimtar rishi,amma kai gashinan ka fahimce ta,"
murmushi shima yayi tare dasa kai ya fuce daga kitchen ɗin,
*************
Agalabaice Amal ta kammala wanke uban kayan da suka tula mata,kaf sai da ta wankesu,ba ita ta kammala wankin ba sai wuraren la'asar,da zazza6i taƙarasa shi,gaba ɗaya ga66an jikinta ciwo suke yi mata,
ɗakinsu tashiga ganin babu kowa aciki saboda duk suna can ɗakin mamynsu hayaam da abra wadda bata jima da dawowa ba,tana jiyosu acikin ɗakin suna ta faman ciye ciyen kayan daɗin da abra tadawo masu dashi,babu wanda ya tuna da ita duk wannan uban aikin da tayi masu,shiga ciki tayi jikinta na kerma ta faɗa saman lumbutsetsiyar katifarsu,bargo taja ta lullu6e jikinta dashi,dakyar take numfashi,da wani irin hucin masassara numfashin ke fita,rayuwarta gwanin ban tausayi tun safe ko wanka batayi ba,saboda babu lokacin yin wanka,koda tayi niyyar yin wankan,sun riga da sun hanata amfani da sosonsu ko sabulun wankansu,wani lokacin in jikinta ya soma yi mata tsami,ruwa kawai take ɗiba tashiga ta watsa,daga bayane tayi dabarar yankar buhu tayi amfani dashi amatsayin soso, ba sabulu haka take gurje jikinta dashi,😭
Cike take da tsoran karsu shigo su same ta acikin ɗakinsu,saboda sun hana ta shiga ko'ina na gidan in ba kitchen ba,shima ɗin in zatayi masu girki ne,
tana acikin wannan yanayin tajiyo murya abra tana cewa"ke!uban mi ya kawo ki cikin ɗakin mu?ba mamynmu ta hanaki shigar mana ɗaki ba!! A fadace tayi maganar,tana a tsaye bakin ƙopar ɗakin,yarda kasan photocopy ɗin aunty babba haka kamanninta suke,
Shiru Amal tayi batace komai ba zuciyarta ce kawai ke ta faman bugawa,
Rai a6ace abra tace"ko ki tashi kona zonan inyi wurgi dake ƙazama kawai,"
har lokacin Amal tagaza motsawa saboda nauyin da jikinta yayi mata,jinjina kai abra tayi tare da shiga ciki azafafe don tayi wurgi da ita,har takai hannu zata fisgi bargon da ta lullu6e dashi,jin muryar hayaam yasa ta dakata daga ƙoƙarin cire mata bargon da take yi,
Shigowa cikin ɗakin tayi tare da cewa"meya haɗaki da ita ne,naji kina ta faɗa,"?
turo baki abra tayi tare da nuna Amal ɗin da hannu tana cewa"baki ga yarda ta haye mana katifarmu ba da wannan baƙin jikin nata duk dauda,"
Sai lokacin Amal tasamu damar buɗe bakinta daƙyar murya na rawa tace"dan Allah kuyi haƙuri bani da lafiya,banjin daɗin jikina,"😭�?
dakatar da abra hayaam tayi tare da cewa"ki rabu da ita,wahalar tayi yawa just for to day ta huta,tunda bata da lafiya," sam ba haka taso ba,bata ji daɗi da Hayaam ta hanata hukunta amal ba,a fusace ta fuce daga ɗakin tana huci
Shiga ciki hayaam tayi tare da samun wuri daga gefen katifar ta zauna,jin muryar Amal tana sambatu na raɗaɗin ciwo yasa ta kasa kunne tana sauraronta,
�?
"Ina jin cewa bazan rayu ba,dan Allah ku kaini wurin auntyna,inaso naganta kafin na bar duniya,"
dariya Hayaam tayi tare da cewa"aikuwa dae ba zaki ta6a ganinta ba adae nan duniyar, ae kin ɗaura aure da wahala tunda kika bari aka haifoki acikin gidan nan," tayi maganar tana ƙarashe dariyarta,
Amal kuwa fashewa tayi da kuka mai cin rai,
tsawa hayaam ta daka mata tare da cewa"yi mun shiru, kuka baya maganin komai sai ma ya ƙara jaza maki wani ciwon," shiru Amal tayi tana shassheƙar kuka ƙasa ƙasa
Shigowa abra ta sake yi hannun ta ɗauke da wayar amani iphone 13 sai faman ruri take yi,miƙa mata wayar tayi tare da cewa"Sofwan ne ke kiranki,"
"ɗan wahala," ta fadi tare da kai hannu ta amshi wayar,juyawa abra tayi ta kalli Amal dake ƙumshe cikin bargo,guntun tsoki taja tare da cewa"salon ki sakarwa mutane miyan bacci asaman katifarsu,sai kin shanye shi don ubanki," ta ƙarasa maganar tare da kama hanya ta fuce daga ɗakin,
Kara wayar tayi a kunnanta bayan tayi picking call ɗin,magana suka shiga yi dashi akan tafiyarta,duk wulaƙancin da tayi mashi hakan baisa ya rabu da ita ba, sai ma kiranta da yayi akan cewa gobe yanaso su tafi tare yakaita abujan,
Sun jima suna waya kafin daga bisa ni su kayi sallama,
tana ƙoƙarin ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa,tsoki ta ɗanja tare da cewa"wani jarababben ne kuma yake kira na"!?
Duba screen ɗin wayar tayi Sunan AMANI ne ya bayyana,ɗan juyawa tayi ta saci kallon Amal dake ƙumshe cikin bargo alamu sun nuna cewa bacci yayi awon gaba da ita,hakan ne yasa ta ɗaga kiran tare da karawa a kunnanta tare da yin sallama,
On the other hand amani tace"wa'alaikum salam,hayam y kk ya gida yasu mammy"?
yatsina fuska tayi tare da cewa"duk suna lafiya,"
Amani tace"labarine ya same ni daga wurin aunty laila nacewa zaki koma gidansu Abbas da zama,sam abun bai dace ba wannan abun kunyar har ina?menene alaƙarmu dasu da har zaki koma gidan surukan mu da zama?amatsayin ƙanwar matar yayansu!
Jin wannan maganar ta Amani yasa ran hayaam 6aci,miƙewa tayi daga zaunen da take saboda tsiwa tamkar zata fasa screen ɗin wayar haka tashiga cewa"Ki tsaya iya matsayinki AMANI!!babu ruwanki dani, iya sa idone kawai naki kada kice zakiyi mun shisshigi acikin lamarina! Ni ba kamar Aunty laila bace data saba jan ki ajiki har tayi maki sanadin auren Abbas,kina magana ne da HAYAAM!!!yakama ki iya bakin ki!!!!
�?
jin yarda hayaam ke zazzaga mata rashin mutunci yasa tayi rejecting kiran,
tsoki hayaam ta saki tare da cewa"matsoraciyar banza!!ae banso kika kashe kiran ba,so nayi na sauke maki kwandon rashin mutunci shashasha kawai," rai a6ace ta ƙarasa yin maganar tare da yin wurgi da wayar saman katifar,kama hanyar fita ɗakin tayi domin taje ta sanarwa mamaynsu yarda su kayi da Amanin,
fitarta ke da wuya, Amal ta buɗe idanunta waɗanda suka kumbura jawur saboda raɗaɗin ciwo, ta samu bacci amma tsiwar hayaam ce tafarkar da ita, gaba ɗaya duk wayar da su kayi da amani tana ji a kunnanta,saboda taji lokacin da hayaam ta ambaci sunan Amani,
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
�?
A hankali ta sanya hannunta tare da yaye bargon,a galabaice ta ɗan tashi zaune, hannu takai tare da ɗaukar wayar hayaam wadda tayi wurgi da ita asaman katifar kuma cikin sa'a wayar bata kai ga shiga security ba,
jiki na kerma ta shiga wurin kiran,sai ga sunan amani ya bayyana a list ɗin farko da tayi waya dasu,cikin sauri Amal ta buɗo numbarta, zuba ma numbar ido tayi tana tunanin yarda zata ɗauki numbar,babu wurin da zatayi copying dinta,tuni hawaye sun soma zarya a fuskanta, wannan shi ake ce ma ga ƙoshi ga kwannan yunwa,
runtse idonta tayi tare da buɗe su akan screen ɗin wayar,nan take taji cewa zata iya haddace numbar akanta,muddin taci gaba da bitarta akanta, a hankali take ƙarewa numbers ɗin kallo tana naɗarsu akanta,motsin mutun taji alamar an tunkaro ɗakin cikin sauri Amal ta fita daga wurin numbar amanin ta danna power ɗin wayar tayi duhu sannan ta ajiyeta,da hanzari tashige cikin bargon ta lullu6e dukkan jikinta, Hayaam ce tashigo kai tsaye ta ƙarasa inda wayar take tasanya hannu ta ɗauka tare da fucewa daga ɗakin,
ajiyar zuciya Amal tashiga saukewa,har lokacin tana cigaba da bitar numbar amani akanta,
*******************
Bacci sosai sehrish tasha, har wuraren ƙarfe biyar da wani abu babu alamun zata farka kamar matatta, kusan sau huɗu azmee na leƙowa don taga kota farka saboda ta lallashe ta akan abunda ya faru amma duk in tashigo sai ta same ta tana ta faman shan bacci,
Ƙarar jiniyar motocinsu ce tasa sehrish farkawa a gigice, fuskar nan tayi jaga-jaga da ita saboda kukan da tasha,ko da ta farka zuciyarta nata faman bugawa, a kasalance ta tashi zaune saman gadon tana faman sauke ajiyar zuciya, idonta takai kan agogon bangon dake manne, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba ganin cewa har lokacin sallar magrib yayi, gashi ba tayi la'asar ba, cikin sauri ta sauko daga saman gadon ta wuce cikin toilet donta ɗaura alwala,
�?
Yau da wuri suka dawo, Abbansu tare da marshal Omar da kuma Sgr sai kanal Yousouf, a nan main palour ɗin suka rarrabu, Abbansu tare da kanal yousouf suka wuce bedroom ɗinsu dake a nan down stairs, Omar da Rafayet atare suka haye upstairs,
Tuni azmee ta kammala jera masu dinner ɗinsu a dining, duk anan suka hallara suka ci abincin, banda sgr da bai fito ba, bayan sun kammala ita tashiga kwashe warmers din da sauran tarkacen da sukayi amfani dashi tana kaiwa kitchen, ganin tana ta faman ɗawainiya ita kaɗae ba sehrish yasa junaid kama mata kayan suna kaiwa kitchen atare ba ƙaramin daɗin hakan taji ba,barin shi tayi a cikin kitchen ɗin ita kuma ta wuce don ta gyara masu dining area ɗin, kafin ta dawo har junaid ya kammala yin wanke wanken kayan da sukayi amfani dashi, tare da gyara kitchen ɗin tsaf tamkar ba'ayi amfani dashi ba,
tsayawa tayi tana kallon shi yana ƙoƙarin haɗama sehrish cornflakes acikin kofi,
Juyowa yayi ya kalle ta tare da cewa"aunty azmee irin wannan kallo haka"?
Murmushi tayi tare da cewa"junaid kai na musamman ne,kana bani mamaki yanzu kai da kanka kayi wanke wanken nan?kuma ka gyara kitchen ɗin nan?
Murmushi yayi tare da cewa "menene aciki aunty azmee?nifa ba aikin da bazan iya yi ba,kuma aiyukan mata suna burge ni sosai, naji ma ina shawa'ar inga ina wanke wanke girki da shara,"
dariya sosai azmee tayi tana girgiza kai tace"gsky baka da dama junaid, koda yake abune mai kyau ka koya,yana da amfani hakan saboda wata rana zaka taimaki matarka ne da wasu aiyukan cikin gidan,Ko ba haka ba?" ta tambaya tana kallon shi,.
ɗaga mata kai yayi alamar eh, sannan yace"aunty azmee ki tayani da addu'a Allah ya cikamin burina,inaso nayi aure very soon insha Allah end of this year.....' kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azmee ta saki baki galala tana kallon shi,
fashewa da dariya yayi a lokacin har ya kammala haɗa ma sehrish cornflakes ɗin,
"Joking aside pls faɗamun gaskiya amma dae wasa kake mun ko"?
girgiza mata kai yayi alamar a'a sannan yace"just keep praying for me, insha Allah soon i wll get marriage," yana faɗin hakan ya kama hanyar fucewa daga kitchen ɗin hannun shi ɗauke da Cup sai faman tiriri yake,
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
�?
shiru azmee tayi tana kallon bayanshi har ya 6ace mata, lamarin ya ɗaure mata kai tabbas tasan halin junaid tunda harya iya furta mata aure yakeso to kuwa fa auren zaiyi dagaske, kuma duk abunda ya nuna yanaso sai abbansu ya mara mashi baya,
"Ashe zamu sha biki," ta faɗi da dariya a fuskarta,
Knocking kopar ɗakin sehrish ya shiga yi, a lokacin har wani baccin ya soma ƙoƙarin ɗaukarta asaman sallayar,tana jin bugun ƙopar a firgice ta tashi tana faɗin "Waye"!
daga waje junaid yace"Mijinki ne insha Allah," ita kanta batasan lokacin da tasaki murmushi ba,
�?
"Ka shigo ciki," ta bashi amsa, tura kopar yayi tare da sa kai yashiga ciki yana faman zabga mata murmushin nan nashi, wuri yasamu kusa da ita anan ƙasa ya lankwashe ƙafarsa ya zauna tare da miƙa mata cup ɗin yace"nasan zaki buƙaci wannan,haɗine na musamman daga mijinki insha Allah,"
fashewa da dariya tayi tana kallon shi, kafin ta zuro hannayenta daga cikin hijabin jikinta ta kar6a, jikinta har rawa yake yi wurin ɗaukar spoon ɗin dake aciki tashiga ɗebowa tana kaiwa bakinta, ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
Tun tana sha da cokali har ta tsame cokalin daga cikin kofin ta miƙa mashi tare da cewa"ruƙe mun," hannu yasa ya kar6a, kafa cup ɗin tayi abakinta tashiga kwankwaɗarshi harta shanye duka,
tausayi ta bashi saboda ya lura ba ƙaramar yunwa take ji ba, cikin sanyin murya yace"nasan kina jin yunwa sosai,bari naje na kawo maki dinner ɗinki," yayi maganar tare da yunkurawa zai miƙe cikin sauri tace"a'a nagode da wannan ma,ba yunwa bace damuwata ba, abunda ke damu na shine Har yanzu aunty azmee fushi take dani"? fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar,
"Kada kisa damuwa aranki, nayi ma aunty azmee magana kuma ta fahimce ki,tun ɗazu ma take ta son tayi magana dake,"
Cike da farin ciki tace"dagaske Aunty azmee bata fushi dani kuma nema na take"?
jinjina mata kai yayi alamar eh, cikin sauri ta miƙe tana naɗe dardumar don taje ta ganta,
ɗaukar cup din da ta ajiye yayi sannan yayi mata sallama ya fuce daga ɗakin,
cire hajib ɗin tayi, sannan ta ɗauko mayafi mai girma ta rufe jikinta dashi, buɗe ƙopan tayi sannan ta fito tare da wuce wa ɗakin azmeen, kwankwasa mata ƙopa tayi, a lokacin azmee bata jima da kammala salla ba,
tasowa tayi tare da sanya hannu ta buɗe mata ƙopan, jikinta na sanye da dogon hijabi hannunta na ruƙe da cazbaha,
Zuba ma sehrish ido tayi tana kallonta, cikin en ina tace"Aunty azmee dama junaid ne yace kina son gani na," ta ƙarasa maganar tana sunnar dakai cike da fargabar amsar da Azmeen zata bata,
murmushi azmee tayi tare da cewa"hakane tun ɗazun nake ta son in yi maki magana amma duk in nazo saina same ki kina bacci," jinjina kai sehrish tayi sannan tace"nasan na 6ata maki rai aunty azmee, ki yafe mun,"
hannu azmee tasa tare da shafa gefen fuskarta tace"just forget about the past komai ya wuce ki manta kawai, yanzu ma nake shirin zuwa in shirya maki abinci don nasan kina jin yunwa sosai,
Murmushi sehrish tayi ba ƙaramin kwanciyar hankali tasamu ba,
Sannan tace"bari na barki ki huta nasan kinyi aiki sosai kin gaji,banji daɗi ba ɗazun da kika hanani tayaki aiki," cikin sanyin murya ta ƙarasa maganar,
Azmee tace"ki manta da wannan, yanzu kije ki haɗa abincin ki ci," amsa mata tayi da toh,sannan ta juya zata fita,
Muryar azmee ce ta sake katse ta da cewa"Au na manta ban sanar dake ba, babban yayan ku fa ya dawo, yau da wuri suka shigo, shi kaɗae ne ma ya rage bai ci abincin shi ba, ki fara kai mashi pls,"
Amsa mata tayi da toh sannan tasa kai ta fuce daga ɗakin nata,
*SGR*
gaba ɗaya hankalin shi na akan Laptop dinsa da yake dannawa, yana a hakimce saman royal sofa mai mazaunin mutun biyu, jikin shi na sanye da kimono robe ta cotton,green colour jikinta akwai zane zane masu kyan gaske, rigar bata rufe faffaɗan ƙijinshi ba,hakan ba ƙaramin kyau ya ƙara mashi ba,ya ɗaure igiyar rigar adai dae saitin shafafen cikin sa, a natse yake danna laptop din da zira ziran yatsun hannun shi, ƙamshi ta ko'ina
da sallama sehrish ta shiga falon nashi, batare da ya ɗago ba ya amsa mata sallamar,
�?
Shiga ciki tayi hannunta na ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da fruits tare da coffee,
koda ta ƙarasa dab dashi murya na rawa tace"sannu da aiki,fatan kana lafiya,"
"Alhmdllh," ya amsa mata har time ɗin bai ɗago ba, ajiye mashi tray ɗin tayi daga gefen laptop ɗinsa, sannan tace"kana buƙatar wani abu"? hannu yasa ya ɗauki cup of coffee ɗin yakai bakinsa ya ɗan kur6a, janye shi yayi daga bakin shi sannan anatse yace"na manta phone ɗina asaman pillow a ɗaukomin ita," juyawa sehrish tayi da sauri zata kama hanyar zuwa bedroom ɗin nashi kamar daga sama taji gaba ɗaya mayafin jikinta ya sulale ƙasa daga jikinta, cikin sauri ta juya tare da kai hannu zata ɗauki mayafin daya faɗi ƙasa, ganin ƙafar sgr tayi asaman mayafin ya take shi da farar ƙafarshi, kasa ɗaukar mayafin tayi saboda fargabar da tashi ga, ranta ne ya bata cewa ba dagangan yayi hakan ba, da alama baisan ya take mata mayafin ba,
A ɗan tsorace tace"mayafi na" batare da ya ɗago ya kalle ta ba yace "ina Sane," jiki asanyaye ta juya tare da nufar ɗakin nashi, tsoranta kar ace alluran nan ta jiya bata sake shi ba,
faɗawa cikin ɗakin nashi tayi tare da nufar saman pillow ɗinsa wayar na ajiye asama,hannu takai zata ɗauki wayar kwatsam taji motsin mutun abayanta hakan ya sanyata juyowa a firgice gaba ɗaya sumar kanta ta watso harta gaban fuskarta, tsananin tsoro ne yakamata ganin mutumin da tabaro yana shan coffee tsaye agabanta, a wani irin yanayi yake bin jikinta da kallo tundaga kan ƙafarta har izuwa saman ƙirjinta, ganin haka yasa sehrish ta soma ja da baya a tsananin tsorace saboda tunawa da abunda ya faru jiya atsakaninsu hakan na nufin cewa Allurar bata sake shi bane, har yanzu akwai saura ajikin shi,
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
�?
tuni zufa tasoma tsatstsafo mata a fuskarta, takawa sgr yayi yana matsawa kusa da ita, ja da bayan da zata ƙara yi ke da wuya , gaba ɗaya ta faɗa asaman gadon shi, bin ta saman gadon yayi gadan gadan ya tunkareta, hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka atsorace ta dinga girgiza mashi kai tana cewa"wlh bani bace na ɗauko allurar ba ! Bani ita akayi....ba zan iya cutar dakai ba.......!!" sai faman sambatu takeyi ita kanta batasan me take cewa ba saboda ya ƙureta sosai ta runtse idanunta zuciyarta nata faman harbawa, sam batasan cewa sgr yana cikin hayyacin shi ba,da gangan yayi mata haka saboda akwai abunda yakeson ganowa game da daren jiya da kuma abubuwan da ya gani na canji a bedroom ɗinshi da kuma body ɗinshi, yasan cewa itace last person daya kasance tare da ita,
jin shiru baice komai ba yasa ta ɗan buɗe idonta, ba komai yake kallo ba face doguwar sumar kanta, sai yanzu ya gane inda ya samu siraran gashi guda uku masu tsayi, hakan na nufin gashin kan Yarinyar ne ya tsinta asaman gadon shi ɗazu da safe, acikin sambatun da tayi mashi ta ambaci cewa ba ita bace ta ɗauko allurar ba, ba ta ita akayi, nan ma ya gane cewa kwa6a tayi mashi jiya har ya ɗirka ma kanshi allura, that's why omar ya tambaye shi akan cewa shi ya dauko allurar, natsuwa yayi a hankali yana ƙare ma fuskar sehrish kallo, ita kuwa sai faman haɗiyar yawu take yi saboda tsoro ga zufa dake gangarowa ta cikin gashin kanta kamar mara gaskiya, duk da sanyin A.c dake gudana aciki,
rufe idanuwanta tayi tana faman karanta addu'oi' acikin bakinta,
for the first time daya ƙarewa wata ƴa mace kallo irin wannan aduniyar nan, yana kallon kyakkyawar fuskarta ne aƙoƙarin shi na ya tuna