Showing 225001 words to 228000 words out of 432432 words
Chapter 76 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
na haifesu.... '
Yunƙurawa yayi tare da miƙewa yabar mata ɗakin yana faman buga tsoki,ta jima zaune jugum aɗakin nashi,kafin ta miƙe ta koma bedroom ɗinta,zirga zirga tashiga yi tana neman mafitar yadda zata samu kuɗi don ta tallafama rayuwarsu,bakowa bane ya faɗo mata aranta ba face Ya haris,tana da tabbacin cewa in yaji halin da take ciki zasu iya taimaka mata duk da tana jin kunyar tunkararsu amman bata da wata mafitar data wuce wnn,addu'a ta shiga yi Allah yasa har yanzu da number shi data sani yake amfani,
Da wayar makwabciyarta tayi amfani wurin kiran Haris,cikin sa'a ta shiga,lokacin daya ɗaga kiran taji muryarshi sai ta fashe mashi da kuka,nan fa hankalinshi ya tashi ya shiga tambayarta ko lpy,bata 6oye mashi komai ba,game da halin rayuwar da suke ciki ita da ya'yanta,haris yayi mata al'ƙawarin zai taimaka masu,su bashi lokaci,
Bayan wasu ƴan kwanaki haris yayi mata aiken kuɗi masu yawa,dasu tayi amfani wurin nema masu makarantar boko da kuma islamiyya,wani lokacin har zama takeyi da kanta ta koya masu karatu,sun ɗan samu sauƙi a wannan lokacin kafin sayyadi ya sake ƙunsa masu wani baƙin cikin,ya kwashe mata Sehrish da jahad 6at aka neme su aka rasa,kamar abu zata yi hauka wurin nemansu,ashe zuwa yayi ya saida ma ƙungiyarsu yaran don suyi amfani dasu,shi kuma suka bashi makudan kuɗi,Mijin maman sadeeq ne ya tona mashi asiri a wurinta,saboda yaga lokacin daya gudu da yaran a 6oye ya tafi dasu,ranar kaca kaca sukayi dashi har bugunta sai da yayi saboda shaƙo kwalar rigarshi da tayi tana jifanshi da munanan kalamai,a ƙarshe tace zata haɗa shi da Allah in bai dawo mata da ƴa'ƴanta ba,tun daga ranar ta fara sallar dare tana kai kukanta wurin Allah,duk yadda sayyadi yaso ya juye mata tunani akan ta daina ibadar nan amma abun yaci tura,ko yayi nufin yi mata asiri babu abunda ke yin tasiri ajikinta,
A ƙarshe dae sae gashi a tsakar dare aka dawo mata dasu sun fita hayyacinsu sunyi jaga-jaga dasu,kamar an jefosu haka ta gansu sun faɗo ɗakinta,sae kuka sukeyi ko sutura babu ajikinsu,ga miyau na zalala abakunansu,hankalin abu ba ƙaramin tashi yayi ba,sai lokacin taƙara sanin wanene sayyadi,kuma ta fara kokwanton cewa Anya ƴa'ƴanshi ne,gaba ɗaya kuɗinta sae da suka ƙare wurin nema masu magani don tunda suka dawo ciwon kai,ciwon ido,ciwon ciki,ciwuka iri-iri haka suka dinga fama dasu,har gadon asibiti aka kwantar dasu sukayi jinya duk ita ke faman ɗawainiya dasu tare da Maman sadeeq,har mijin ta yana zuwa dubasu a asibitin sannan ya taimaka masu da wani abun hadi da addu'oi,amma Sayyadi kuwa ko leƙo asibitin baiyi ba,koda aka sallame su suka dawo gidama basu same shi ba,haka abu taci gaba da shan wahalar rayuwa,ko makarantarma acikin sati bai wuci sau biyu suke zuwa ba,saboda rashin lafiyar da suke ta fama da ita,kuma duk in sukaje makarantar da kuka suke dawowa,saboda yara dake tsokanarsu akan cewa mahaifinsu ɗan mafiya ne mai yankar kawunan mutane,wannan abun ba ƙaramin cutar da rayuwarsu yake yi ba,shiyasa duk suka tsani zuwa makarantar,
Akwai wani lokaci da Sehrish ta fito waje cikin unguwarsu ta miƙi hanya tana tafiya tana kuka abun duniya yayi mata,kwata kwata basu jin daɗin rayuwarsu ta ko'ina a ƙuntace suke,a daidai wannan lokacin Wata danƙareriyar mota tayi parking a gefenta,cikin sauri matashin dake cikin motar ya buɗe ya fito ya tunkareta,sam bata lura da shi ba har sae da ya ruƙo hannunta,a firgice ta juyo tana kallonshi da idanunta waɗanda sukayi jawur saboda kukan da tasha,ga majina duk fuskarta ta 6aci,zuƙunnawa yayi agabanta yana kallonta,gwanin ban tausayi ƴar ƙaramar yarinya ko kallabi babu akanta balle takalma,ga kayan jikinta duk sun 6aci,
Kamar yadda yake kallonta haka itama take kallonshi,ɗan gayu dashi yasha wankan suit ajikinshi,
Cikin sanyin murya yace"Ya sunanki"?
..cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ni ka rabu dani,ka ƙyale ni in tafiyana,'
Abun yaso ya bashi dariya,shafo fuskarta yayi tare da cewa"Faɗamun me yasa kike kuka?idan kika faɗa mun zan taimake ki,'
A ƙule tace"Nidai ka ƙyale ni dan Allah,kawai ka rabu dani,kona faɗa maka babu abunda zaka iyayi mana saboda babu mai sonmu Allah ne kawai ke son mu,'
Tuni yaji hawaye sun cicciko mashi acikin idanunshi,Haris dake zaune cikin mota yana hangensu ta glass ɗin motar ba ƙaramin tausayi yarinyar ta bashi ba,
lallashinta ya shiga yi yana cewa"kiyi haƙuri kinji?bakowa ne baisonku ba,Nima gani kuma ina sonku sosai,ashirye nake dana taimake ku indae kunaso,zan ɗauke ku mu gudu mu bar ƙasar nan,in tafi tare daku can wani wuri mai daɗi kuyi rayuwarku ko baki so?
"dagaske kake"?muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
ɗaga mata kai yayi alamar eh,tare da cewa"yanzu ki biyoni mu tafi batare da kowa ya ganmu ba,"
Girgiza mashi kai tayi tare da cewa"Su hosana fa?su bazaka tafi tare dasu ba?Oummanmu fa?itama anan zaka barta,
"Kada ki damu suma duk zanzo in ɗaukesu daga baya,"
Maƙe mashi kafaɗa tayi tace"a'a ni bazan bika ba,sae dae inje in kirasu Johad da hosana,mu tafi atare,"
"Shikenan zan jiraki ki kirasu,kada ki faɗa ma kowa babu wanda zai san mun tafi,"
Amsa mashi tayi da toh sannan jiki na rawa ta juya da gudu ta koma gidan,
Sai lokacin haris ya fito daga cikin motar jikinshi a sanyaye ya ƙarasa inda abusufyan yake zuƙunne,hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarshi yace"Yanzu ka tabbatar da abunda nake faɗa maka ko?
Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"Haris yaran nan fa ƴa'ƴana ne!ina ji ajikina,hatta kamannin fuskarsu ma irin nawa ne,bansan ya akai hakan ya faru ba,mutumin nan baida Imani dama na jima ina zarginshi,kuma zanyi bincike akanshi,bazan ƙyaleshi ba haris,ni babban abunda yafi damuna yadda yake tafiyar da rayuwar yaran,kamar sunfi kowa rashin gata aduniya,ƴar ƙaramar yarinya kamar wannan har tasan cewa kowa baison su,tama rasa ina zata tsoma ranta saboda ƙuncin da take ji,so yake su kamu da ciwon zuciya tunda ƙuruciyarsu," ƙarasa maganar yayi tare da miƙewa tsaye yana share kwallar data zubo mashi,
"Akwai matsala fa,muddin rayuwar yaran nan taci gaba da tafiya ahaka,yakamata muyi gaggawar sanar da Abbanku domin ashawo kan matsalar tun kafin ka rasa yaran nan!amma inaso yanzu idan suka zo mu fara biyawa asibiti domin ayi masu gwajin jini don mu tabbatar da cewar ƴa'ƴanka ne,"
Yana kai ƙarshen maganar tashi,sae ga Sehrish ruƙe da hannun Hosana da jahad,ta ruƙo hannun kowannansu sun fito daga gidan,ko abu batasan da fitar su ba,saboda ta shiga makwabtansu wurin maman sadeeq don ta samo masu abincin da zasu ci,
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar abusufyan lokacin da yayi arba dasu,ruƙe da hannun juna,kamar jira yake yi su ƙaraso wurinshi,ya zuƙunna tare da haɗasu duka ya rungumesu a ƙirjinshi,ya jima dasu a haka kafin ya raba jikinshi da nasu,anan ne yayi masu hoto da wayarshi,ya ɗaukesu a yadda suke kaca kaca dasu da niyyar ya nuna ma gwaggon katsina don taga halin da yaran suke,ko zasu nemi mafita,
Akan idon mijin maman sadeeq mlm nura,abusufyan ya sanya su sehrish acikin motarshi,a back seat suka zauna,haris kuma shike driving ɗinsu,
Shi kanshi yayi mamakin yadda yaran suka amince suka biyo shi,ko mahaifiyarsu basu nema ba,duk irin shaƙuwar dake tsakaninsu da ita wannan zai tabbatar maka da cewar ta kansu sukeyi,sun gaji da komai,
A katafaren gidan nan nasu inda sukayi rayuwa shi da abu,tare dasu hajiya Ameena anan yakai yaran,cikin gidan ya shiga tare dasu,ya rage kayan jikinshi,sannan ya bisu ɗaya bayan ɗaya da kanshi yayi masu wanka acikin toilet,ya wankesu tass ya kuma wanke masu gashin kansu da shampoo,bayan ya kammala yi masu wankan,anan bedroom ɗinshi,ya shafe masu jikinsu da mai,ya gyara masu sumar kansu,sai da yabi kowaccensu yayi mata kalaba guda biyu akanta,ba ƙaramin kyau sukayi ba,bayan ya gama yi masu kitson ya hau saman gadon tare dasu ya kunna masu cartoon awayarshi na tom and jerry suna kallo,
Shigowa haris yayi cikin ɗakin hannunshi ɗauke da manyan ledoji guda biyu,lokacin daya samu abusufyan kwance saman gadon tare da ƴan ukunnan duk sun manne mashi suna kallo,abun ba ƙaramin burgeshi yayi ba,sae yaji aranshi dama a wurin abusufyan yaran suka taso,da sun ji daɗin rayuwarsu,
Ƙarasawa yayi tare da miƙa mashi ledar kayan,ya taso ya kar6a,kayan sawa ne daya siyo masu,sai kuma ledar abincin da yayi masu take away a restaurant,
Bayan haris ya fito daga ɗakin ya fito falo yana jiran Abusufyan ya kammala shirya yaran su tafi asibitin,
Sanya masu kayan abusufyan yayi,sannan ya fiddo masu da take away ɗin abincin suka zauna suna ta turawa a bakunansu,zuba masu ido yayi yana kallonsu,ganin ya kura masu ido yasa Hosana ta ɗebo abincin a hannunta takai mashi abakinshi don yaci shima,
Murmushi abusufyan yayi ya buɗe bakinshi ta sanya mashi abincin,a haka har suka kammala cin abincin,
Yayin da suke nan,Abu nacan tana haukan neman ƴa'ƴanta,gida gida haka ta dinga bi tana neman su hosana,har sai da Allah ya haɗa ta da Mijin maman sadeeq shi ne yake sanar da ita cewa wani matashin saurayi ne mai kama da yaran yazo ya ɗaukesu,tunda taji hakan ranta ya bata cewar Abusufyan ne,jiki asanyaye ta koma cikin gidan,gefen gadonta ta zauna addu'a tashiga yi Allah yasa shine,in ma dagaske shinen Allah yasa karya dawo mata dasu hosana ya tafi dasu kawai duk inda zaije,tabar mashi su,
Lokacin da sukaje asibitin akayi masu gwajin jini,result ɗin ya nuna cewa yaransa ne,nan fa suka shiga murna shi da haris,duk da sunyi mamakin taya akai yaran suka kasance nashi!hakan na nufin da cikinshi abu tayi aure,
Haris ne ya bashi shawarar su ɗauke yaran kawai karsu maidasu gidan nan,Abusufyan shima ya amince da hakan,bai maida su sehrish ba ya koma dasu gidansu,kusan kwana uku su sehrish sukayi awurin Shi,acikin waɗannan kwanakin sun samu kyakkywar kulawa a wurinshi,kullum sai sunce mashi yaje ya ɗauko oummansu itama ta dawo gidan,sai yace masu su ƙara haƙuri zai kawo masu ita,
Ana haka sayyadi yadawo tun bayan da aka sallami su sehrish da jahad daga asibiti bai ƙara leƙo gidan ba sae a wannan lokacin yayi ma abu zuwan bazata,tun aranar ya soma tambayarta ina ƴa'ƴanshi suke,banza takeyi mashi bata bashi amsa,jinjina kanshi yayi tare da cewa duk ma inda takai su zasu dawo ne da ƙafafunsu,
Aranar da yayi maganar,tsakar dare suna kwance abusufyan ne tsakiyarsu,hosana da jahad suna gefe da gefenshi,Sehrish kuma na kwance saman jikinshi duka ya sanya hannunshi ya dafe su,
Kwatsam yaji kukansu acikin kunnuwanshi,a firgice ya farka nan fa yaga tashin hankalin da bai ta6a gani ba,sai birgima sukeyi idanunsu sun canza launi,kowacce ta dafe kunnanta sae ihu takeyi,saboda sunansu da ake ambata da wani irin sauti mara daɗin ji,hankalin abusufyan ba ƙaramin tashi yayi ba,tsoranshi kar yaran su mutu,wata irin zufa ce ke tsastsafowa daga jikinsu,sharkaf suka jiƙe,
Faɗowa cikin ɗakin haris yayi jikinshi na kerma,abusufyan na ganinshi muryarshi na rawa yace"Haris kalli yaran nan ka gani wlh bansan me ya same su ba,ko zamu kai su asibiti ne"?
Girgiza kai haris yayi tare da cewa"Ko mun kaisu asibiti babu abunda zasu iya yi masu!yanzun nan sayyadi ya kirani awaya ya sanar dani cewa mu dawo mashi da ƴa'ƴanshi in ba haka ba zasu mutu a hannun mu ne,kuma zaiyi shari'a damu akan laifin mun kashe mashi ƴa'ƴanshi,ina da tabbacin cewar duk shirinshi ne wannan,"
Jiki na rawa abusufyan ya sauko daga saman gadon ya ɗauko hosana da jahad a hannnunshi,haris kuma ya ɗauko sehrish,
Cikin mota suka sanyasu,sannan haris yaja motar suka nufi gidan Ya sayyadi,wuraren ƙarfe sha biyu kenan na dare,tun kan su ƙarasa ƙopar gidan suka hango sayyadi atsaye jikinshi sanye da jallabiya,ya goya hannayenshi asaman ƙirjinshi,
Parking ɗin Motar sukayi,da sauri suka ɗauko mashi yaran suka kai mashi,abun mamaki suna ƙarasawa inda yake sai gashi sun dawo cikin hayyacinsu,tun daga nan kowa yasha jinin jikinshi,
koda suka saukesu ƙasa,suna ta faman murza idanunsu,suna yin arba da sayyadi,jikinsu na kerma suka ƙanƙame abusufyan suka manne mashi tamkar zasu koma jikinshi,
Hasken fitilar kwan dake a kopar gidajensu da kuma hasken motar su abusufyan dake ajiye,shi ya taimaka masu wurin ganin junansu da kyau,
Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Sayyad da kuma Abusufyan,maƙiya sun haɗu,
Haris ne yace"kaji tsoran Allah,laifin me abu tayi maka ita da yaranta da har kake son cutar da rayuwarta?
Murmushi kawai sayyadi yayi yana kallonsu yace"nagode sosai,da irin kulawar da kuka ba ƴa'ƴana,naga an canza masu kaya,an kuma saya masu takalma,abu yayi kyau,kaga masu Ji da naira,ba kamar mu ba ƴa'ƴan malam shehu.......'
. afusace abusufyan ya katse shi da cewa"Kai malam!ka faɗamun taya akai ka auri abu da ciki na!don bincike ya nuna cewa yaran nan ƴa'ƴana ne!ba naka ba!dama najima ina zarginka wlh!kai ba mutumin kirki bane!"
shu'umin murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"Oh kanaso kasan yadda akai na auri abu da cikin ka"?
Har suna haɗa baki shi da haris wurin cewa Eh,
Dariya sayyad yayi kafin ya matso dab da Abusufyan suna fuskantar juna ido cikin ido yace"tabbas Ƴan ukun nan ba ƴa'ƴana bane!naka ne halak malak,tun lokacin da kuka rabu da abu ta sanar dani cewa tana jin tashin zuciya,anan nagane cewa tana ɗauke da cikinka,shine na kwantar da cikin ta hanyar yin amfani da sihiri na,babu wanda yasan cewa tana da ciki har na aureta,sannan na bayyanar da cikin a jikinta,don su taso amatsayin ƴa'ƴana.......'
Katse shi haris yayi da cewa"meyasa kayi hakan toh"?
Sayyadi yace"bana faɗin dalili sai dae kawai in bada amsa,'
Jiki asanyaye abusufyan yakai idanunshi kansu hosana dake manne ajikinshi sun ƙankameshi,alamar basu so yabarsu anan,tuni yaji hawaye sun cicciko mashi a idanunshi aranshi yace ashe dae dagaske jini na ne su,
"Amma meyasa ka auri abu?yanzu nake kokwanton cewa anya don kana sonta ka aure ta"?
sayyad yace"ina fa?ni sam mace bata gabana!namiji kawai,da maza nake mu'amalata,Na auri abu ne duk don saboda in samu hanyar da zan shiga rayuwarka,kuma na samu,'yayi maganar yana nuna su sehrish dake ƙankame da jikinshi,
Rae a6ace haris ya cakumi wuyan rigar sayyadi yana cewa"wlh bazamu ƙyaleka ba,mugu azzalumi!zamuyi ƙararka kotu akan yaran nan,'
Dariya yayi tare da cewa"nafi ƙarfin kotu haris!babu abunda zasu iyayi mun,'
""Idan ka fi ƙarfin kotu ae baka fi ƙarfin Allah ba,zamu kai ƙararka wurinshi,kuma insha Allahu sayyad ba zakayi kyakkywan ƙarshe ba,sae kayi mummunan mutuwa kamar yadda mahaifinku kakah yayi......'
Buge hannun haris yayi daga cakumar wuyan rigarshi da yayi,cike da mamaki yace"Oh ashe ka gane ni!"
jinjina kai Abusufyan yayi tare da cewa"bangane kaba,amma tunda ka ambaci cewa kana son shiga rayuwata na gane cewa kai daga family ɗinsu kakah kake,Azzaluman mutane,mugaye waɗanda suka mayar da zalunci hanyar cin abincinsu,masu tada ƙayar baya a ƙasarmu,asannu asirinka zai tonu kamar yadda na ubanku ya tonu kuma insha Allah,Abbana da kuma yayana Hussein,kai bama su kaɗae ba nayi maka alƙawarin cewa a hannun ɗaya daga cikin jikokin Amminmu zaka Mutu,mummunar mutuwa kuma a wulaƙance kamar dabba haka zakayi ta,idan Allah ya nuna mun wannan ranar ni kuma zan tuna maka waɗannan kalaman da nayi maka,
Hannu Abusufyan yasa tare da dafa kawunansu sehrish dake manne da jikinshi yace"idan Allah yasa su kayi tsawancin kwana basu mutu a hannunka ba,A gabansu za'ayi komai,"
Fashewa da dariya sayyadi yayi hada dafe cikinshi,lokaci guda kuma ya tamke fuskarshi tamkar bai ta6a yin dariya ba yace"kai fa ƙaramin ɗan iska ne mai kwana da wando,har yanzu bakasan wanene sayyadi ba,labarina kawai kake ji,nafi ƙarfin duk wanda kake tunanin zai iya ɗaukar fansa akaina!danginku gaba ɗaga babu wanda zai iya ɗaga mun yatsa,kuma inaso na sanar maka cewa muna nan muna shirin tarwatsa farin cikin zuri'arku,muna nan muna shirya maku maƙarƙashiya,bani kaɗae bane yawa gare mu kuma muna nan kewaye daku,'
Kallon juna haris da Abusufyan sukayi kafin su mayar da idanunsu kan Sayyadi,
"Daga rana irin ta yau!ina mai gargaɗinka da cewa kada ka kuskura ka ƙara yunƙurin zuwa ɗaukar yaran nan!wlh in har ka ƙara takowa kazo inda suke!ko kuma ka turo wani naka da niyyar ya taimakesu!koma wanene sai ya Mutu!!!!na sanya katanga a tsakaninku dasu,zaku iya tafiya,"
Ya ƙarasa maganar tare da nuna masu hanyar inda motarsu take da hannunshi,hannu abusufyan ya sanya yana ƙoƙarin raba su hosana da jikinshi kuka suka fashe dashi suna roƙonshi akan karya tafi yabarsu a hannun wannan mutumin basu son zama dashi........'wata irin tsawa ya sayyadi ya daka masu a gigice suka raba jikinsu dana abusufyan suka shige gida da gudu suna kuka,ashe Abu tana a la6e a zauren gidan tana sauraronsu,tun lokacin da abusufyan yazo da su hosana,tasha kuka kamar taje ta rungumoshi ajikinta haka ta dinga ji,kamar ta zauce tayi hauka,su hosana na shigowa ta haɗasu duka ta wuce dasu ɗakinta,anan suka zauna suna ta sharar kwalla,
Jiki asanyaye abusufyan da haris suka shige cikin motarsu,tun daga wannan lokacin ne abusufyan yabar Nigeria ya koma Turkey gaba ɗaya,bai ƙara leƙo nigeria ba,ya nesanta kanshi da kowa ne saboda bazai juri zuwa nigeria ba,yayin da ƴa'ƴanshi suke rayuwa awulakance baida ikon taimakonsu ko ya sanya a taimakesu,sai dae Addu'a da yake binsu da ita.
Haka su sehrish suka ci gaba da shan wahalar rayuwa a hannun mutumin nan,wani tashin hankalinma sayyadi ya fara kwaɗaita dasu,ya dinga nemansu a 6oye abu bata sani ba,duk in tayi kuskuren fita ta barsu acikin gidan yazo ya same su haka zai ƙumshe su aɗakin yana tsoratar dasu akan susha mashi gabanshi,duk abu bata ankare ba,sae wata rana da ta ta6a dawowa ta same su suna ta kwarara amai wani irin abu mai yauƙi yauƙi yana fitowa abakinsu,tsare su tayi da tambaya akan me suka sha ne ya 6ata masu ciki,ƙin faɗa mata sukayi saboda tsoran kada Abbansu ya kasheta kamar yadda yayi masu barazana in suka faɗa mata,ganin sunƙi faɗa mata yasa ta ɗauko wuƙa a kitchen ta nuna su da ita tana cewa"Ko ku faɗa mun ko in kashe ku a wurin nan,"gaba daya suka tsorata,sehrish ce ta buɗe baki ta sanar da ita abunda mahaifinsu ke sanyasu suna yi mashi,saboda tashin hankali nan take ta yanke jiki ta faɗi asume,
Kukan da suka fashe dashi ne yasa makwabciyarsu