Showing 216001 words to 219000 words out of 432432 words

Chapter 73 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

a wulakance,yara ne mata guda ukku wani lokacin babu kallabi a kawunansu kuma babu takalma a ƙafafunsu,tun lokacin nake tsananin jin tausayinsu,kuma raina yake bani cewa tabbas ƴa'ƴana ne su.....saboda akwai wani lokaci da nazo nigeria zuwan bazata batare da sanin kowa ba............."

Bai ƙarasa maganar ba suka jiyo muryar goggon katsina tana sambatu tana cewa"ƙarfen nasara ba tabbas,Allah ka tsine ma baturen daya ƙirƙiri motar harisu,shegiyar motar kamar da katako akayita,tun safe muke a hanya take ta bamu matsala mtsswwwwww haba ina dalili,tafiya daga katsina zuwa abuja sai kace mutun zashi saudia a ƙasa?ae dana san haka zata faru da a kafa na tako wlh,shegen maƙo irin nashi,maimakon ya biya mana kuɗin jirgi,ya nace sai mun hau waccen rugwagwar motar tashi..........'kasa ƙarasa maganar tayi ganin yadda matasan gidan suka taru a falon gidan,ga kuma Abusufyan ɗinta dake ta faman sharar kwalla,
Don bala'e,a hannu ta ruƙo zaninta daga ita sae dogon undi fari ajikinta,ta cire zanin gaba ɗaya,ranta ba ƙaramin 6aci yayi ba,da alama,
Tsayawa tayi cak baki asake tace"Na shiga uku ni yau,abun dae ba sa'a,Allah yasa dae ba wani ya mutu ba,wlh yanzu inyi kwana in koma katsina don ni ban shirya ganin gawa ba,dan Allah ku faɗa mun maiya faru"?
Miƙewa sukayi gaba dayansu suna kallonta cike da tuhuma,adaidai lokacin kuma Dr haris ya shigo tare da Saude,suma duk suka tsaya cirko-cirko ana kallon kallon,
Koda Abusufyan yayi arba da goggon katsina,jiki na rawa ya tunkareta,tare da faɗawa jikinta ya rungumota sosai yana cigaba da kukan,
Nan fa hankalin goggon katsina ya tashi,hannu bibbiyu tasa tare da ɗago da fuskarshi daga jikinta tana cewa"Abusufyan ɗina meya faru?meyasa kake kuka?kai da zanga kana farin ciki?ko Omar bai nuna maka ƴa'ƴanka bane.....?
cike da mamaki kowa ya zuba ido yana kallonta,Abusufyan dake kuka nan take ya dakatar da kukan nashi yana cewa"Mommyna...ina abu take ne?ina yaran da ta haifa suke?suna ina?
Bata bashi amsa ba,sae ta kalli Omar dake tsaye yana kallonsu tace"Omaru ina kakai mashi ƴa'ƴanshi ne?yaran nan fa da kazo dasu gidana ƴa'ƴan abusufyan dina ne dama saida na faɗa maka,dan Allah ku nuna mashi ƴa'ƴanshi ya gansu yaga yadda suka girma ko hankalinshi ya kwanta banson ganinshi yana kukan nan"
Tashin hankali!
Nan fa kowa ya ruɗe yana tunanin su wanene yaran da gwaggon katsina take magana akai,
"Gwaggo kina nufin cewa hosana da jahad ƴa'ƴan abusufyan ne!"?Omar ne yayi mata tambayar fuskarshi ɗauke da mamaki,
goggo tace"Eh mana,sune ƴa'ƴan abusufyan ɗina,suna ina ne.....'
Kafin wani ya buɗe baki ya ƙara magana,sai ga Jahad da hosana sun fito da gudun gaske jin muryar gwaggon katsina data karade gidan,tana ganinsu ta washe baki tana cewa"Yawwwa ga ƴa'ƴan abusufyan ɗina nan sun ƙaraso,maza ku ƙaraso in rungume ku ajikina,'
ƙarasawa sukayi tare da faɗawa jikinta,ta hada su duka ta rungume ajikinta,tana ta faman murmushi,
Fawan ne yace"Anya gwaggo tasan me take cewa kuwa?taya waɗannan yaran zasu kasance Ƴa'ƴan uncle ɗinmu?hakan na nufin cewa Sehrish itama ƴar shi ce kuma,su jinin mu ne?
Cikin sanyin murya abusufyan ya juya tare da kallon fawan da yayi maganar yace"Tabbas su ƴa'ƴana ne!nasan zakuyi kokwanton maganarta ne saboda tana da ta6in hankali,to inaso ku sani cewa mommyna tana acikin hayyacinta,tasan me takeyi duk da akwai ta6in hankalin atare da ita,amma ba kowane lokaci bane take kasancewa dashi ba,'
Jin maganarshi yasa Hosana da jahad suka juyo suna kallonshi yayin da zuciyoyinsu ke cigaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi,
Kowa fa ya shiga ruɗani,wasu ma saboda tsabar mamaki sun gaza magana,irin su Sgr da kuma su Jahan,
"Yanzu duk ba wannan ba!dole muji ya akai kasan cewa su ɗin ƴa'ƴanka ne!kuma ya akai kuka bar rayuwarsu ta wulaƙanta batare da kun sanar mana ba!sannan dole muji ta bakin yaran game da irin ruƙon da wannan mutumin yayi masu!'acewar Abbansu junaid,ranshi a6ace yake maganar,
Gwaggo dae bata gane inda zancen nasu ya dosa ba,amma tana da tabbacin cewar abusufyan ya fasa abunda suka jima suna 6oyewa,hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,dama ta gaji da 6oyon al'amarin da sukeyi,saboda ganin irin wahalar da yaran suke sha a hannun mugun mutumin nan,
Omar yace"Abunda ya kamata shine,yanzu naga anata kiran sallar isha'e yakamata muje muyi sallah,kafin mu dawo nasan gwaggo ta ɗan rage gajiya,sai mu zauna ayita taƙare kawai,in yaso sai jahad tayi mana bayanin komai tunda itace mai cikakken hankali acikinsu,Sehrish ita kanta bana tunanin tana acikin hayyacinta yanzu,

Kowa ya amince da maganar omar,batare da 6ata lokaci ba,suka wuje bedrooms ɗinsu domin yin alwala,hajiya azeema ce ta shigar da Gwaggon katsina cikin ɗakinta tare da saude kafin agyara masu inda zasu zauna,

Yau dae gidan Abban sojoji a hargitse yake,Wlh ni kaina a hargitse nake,sai addu'a kawai,

Abbansu na fitowa daga cikin toilet,junaid ya faɗo mashi acikin ranshi,nan fa gaban shi ya faɗi rasss,sae lokacin ya tuna da cewar babu junaid fa acikin gidan tun ɗazu,duk wannan budurin da akeyi babu shi acikinsu,
Hankalinshi amatuƙar tashe ya tunkari wayarshi dake ajiye saman side drawer ya dauketa,tare da lalubo numbar junaid ya danna mashi kira cikin sa'a wayar tashiga tana ringing amma ba'a ɗaga ba,kusan sau huɗu yana kira ba'a ɗagawa,
Ana biyar ɗinne aka ɗaga wayar,kara wayar yayi kunnanshi yana cewa"Junaid ina ka shiga ne!!"shiru yaji ba'a tanka mashi na,nan fa yabi ya rikice,
"Junaid wai baka jina ina magana ne?bazaka amsa mun ba?junaid kodae wani abu ya faru da kaine?
Nan ma shiru ba'a bashi amsa ba,
Muryarshi tamkar zaiyi kuka ya kuma cewa"don Allah babyn Abbanshi kayi mun magana mana!
Muryar mace ce ta amsa mashi da cewar"ka duba whatsapp ɗinka,zaka ga video mun tura maka,"
Jikinshi har kerma yakeyi wurin katse kiran ya shiga whatsapp ɗinshi,new number ya gani tayi mashi message da video,
Saboda tsabar fargaba,tun kafin ya buɗe video ɗin zufa tashiga gangarowa a fuskarshi,dukkan ilahirin jikinshi ya shiga yin kerma,idanunshi sukayi jawur tsoranshi kar a videon yaga junaid cikin wani yanayi,bazai iya jurar wannan ba,
Runtse idanunshi yayi yana karanto addu'o'i abakinshi,kafin daga bisani ya daure ya cije ya buɗe videon,
Zazzare idanunshi yayi waje tamkar kwayar idanunshi zata faɗo ƙasa,
A ƙarshe kuma ya fashe da dariya,tare da zubewa saman guiwowinshi yana tikar dariya,
Bakomai bane acikin video ɗin nan ba,face Mommynsu junaid Alexandra rungume da junaid asaman gado,suna kwance abunsu,da alama ma kamar bacci yake yi ajikinta.......


 
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku


Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.

*💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*




*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,


😔


Abunda ya faru,lokacin da wata mata ta kira junaid da sunan mommynshi don yazo ya ɗauketa a airport,jiki na rawa junaid ya shige cikin motarshi ya kama hanyar zuwa airport bayan ya fita daga gidanne ya tuna da tace in ya fito ya sanar da ita,fiddo wayarsa yayi da niyyar kiranta,tunanin taya zai kirata ma ba number ya shiga yi,adaidai lokacin ta sake kira tambayarshi tayi ya fito ne,ya amsa mata da eh yana a akan hanyar zuwa,cigaba da tafiya yayi zuciyarshi cike fal da son ganin mommynshi,driving yake yi yana ayyana farkon haɗuwarshi da mommynsu baisan wani irin runguma zaiyi mata ba,yayi zurfi acikin tunaninshi kwatsam sae ga wasu jerin motoci sun kusa goma sha biyu,baƙaƙe kuma da black tinted,da gudun gaske suka nufo inda junaid yake,koda junaid ya lura da motocin nan fa hankalinshi yayi mugun tashi,ƙarasowarsu ke da wuya suka zagaye motar shi,yadda bazai iya kubce masu ba,nan fa hankalin junaid yayi mugun tashi,jikinshi ya shiga rawa,tsoranshi kar ace mutanen da mommy azeema ta sanar dashi cewa suna bibiyar rayuwarshi ne,zama yayi acikin motar hankali a matukar tashe,
ɗaya daga cikin motocin aka buɗe,sae ga wani gabjejen mutun faffaɗan gaske sanye cikin suits,kai tsaye ya nufi motar junaid hannu yasa tare da knocking glass ɗin motar,zuge glass ɗin junaid yayi atsorace yana kallonsu sae faman haɗiyar yawu yake yi da kyar,
kafin yayi wani yunƙuri Mutumin nan ya buɗe motar tashi,gaba ɗaya ya cakumi junaid ya toshe mashi baki,ya nufi cikin motarshi dashi,bayan ya sanyashi acikin motor,atare suka tashi motocin da gudun gaske suka bar wurin,
junaid dake a back seat na motar tuni ido ya raina fata,hawaye suka shiga wanke mashi face ɗinshi,muryar shi tamkar zaiyi kuka yace"Su wanene ku?laifin me na aikata maku?dan Allah kada ku rabani da rai na,inason na sake ganin Abbana.....'bai kai ƙarshen maganar tashi ba,ɗaya daga cikinsu ya daka mashi tsawa tare da cewa"Shut up!ko tari ka ƙara yi saina fille maka kai,"
Jin haka yasa junaid yayi tsit zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi,
Wani katafaren gida suka shiga tare da shi,bayan sunyi parking ɗin motocin,ɗaya daga cikinsu ya buɗe motar tare da ɗauko junaid asaman kafaɗar shi,ya wuce dashi cikin gidan,a babban falon gidan ya sauke shi,sannan ya juya ya fuce,
To fa,tsayawa junaid yayi cikin tashin hankali yake kallon haɗaɗɗen falon komai a gyare tsaf,tunani ya shiga yi mai yasa suka kawo shi nan suka ajiye shi?ko dae kidnapping ɗinshi sukayi ne?hannu yasa yana share hawayen shi,bai kammala wiping ɗinsu ba,yajiyo takun takalmi kwas kwas,
A firgice ya ɗago don yaga wanene,zuba mata ido yayi yana kallonta,daga saman stairs take saukowa down,jikinta na sanye da doguwar riga fara mai shegen kyau tabi shape ɗin jikinta,ƙafafunta kuma na sanye da takalma high hills farare duk da tsayin da take dashi don sam ba gajera bace,ba ƙaramin kyau shigan tayi mata ba,kasancewarta farar fata,wuyanta na sanye da ziririyar sarƙa fara ta diamond,hannunta kuma na sanye da Zobe ɗaya kacal a middle finger,shima na diamond ne,ta ɗaure gashin kanta abaya,mai tsayi wanda launinsa yake tamkar golden yellow,

A hankali ta ƙarasa saukowa daga saman benen,sannan ta tsaya tana kallonshi daga inda yake tsaye,duk da akwai tazara atsakaninsu amma suna iya ganin juna sosai,ƙare mashi kallo tashiga yi,burinta junaid ya fara shaida ita wacece kafin ta sanar mashi,
hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa rass rasss,batare da jin tsoro ba ya tunkareta sai da ya kusa kaiwa inda take sannan ya tsaya yana kallonta,ƙwayar idanunta yabi da kallo blue colour wanda hakan ya tabbatar mashi da cewar mommynsu ce, dama kuma yasan ta a hoto,komai na fuskarta irin na Babban yayansu ne,duk da ta kwana biyu aduniya amma hakan bai 6oye kyawun fuskarta ba,tamkar ƴar shekara 30 haka fuskarta take,hatta jikinta yana nan yadda yake da kyau da kuma diri,
A hankali junaid ya furta"Mommy!is you?
jinjina mashi kai tayi alamar eh,da gudun gaske ya ƙarasa tare da faɗawa jikinta,sosai ya ƙankameta saboda tsabar farin ciki ya fashe mata da kuka,nan take itama kukan yazo mata atare suka shiga yin kukan babu mai lallashin wani,tamkar zasu haɗe jikin junansu su koma ɗaya haka suka ƙanƙame kansu,daƙyar Alexandra ta iya dakatar da kukan nata,ta sanya hannayenta tare da ɗago da fuskar junaid tana kallonshi,hawaye sun wanke mashi fuskarshi tass,
muryarta na rawa ta ambaci sunan shi"Ro..meo.ɗina,'
Cikin shessheƙar kuka junaid yace"Mommy,ashe zan sanyaki acikin idanuna,bansan da wasu kalmomin zan bayyana maki irin farin cikin da nake ciki ba,i luv u so much mom....'
Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,duk irin watsin da tayi dashi tabar Nigeria,hakan bai hana shi sonta ba,
Kwantar dashi ta sake yi asaman ƙirjinta,ta sanya hannayenta tana ɗan bubbuga bayanshi,kafin ta mayar da hannunta ɗaya acikin sumar kanshi,ta jima tana mamakin girman shi,ta tafi ta barshi a lokacin da yake ɗan jinjiri dashi,amma yanzu tadawo ta same shi ya girma ya zama babba,ba ƙaramin farin ciki taji ba,mara misaltuwa,
ɗago dashi ta kuma yi daga jikinta cikin sanyin murya tace"romeo ɗina,kayi haƙuri ka daina wannan kukan duk da nasan na farin cikin ganina ne,ni kaina bazan iya misalta farin cikin dana ji ba,wai yau ni ce tare da babyn dana bari yana jinjirinshi,ya girma ya zama babba,nayi danasanin tafiya nabarka romeo,nayi kewarka sosai,hakanan na raba kaina dakai,ba don bana sonka ba romeo,zan iya cewa nafi sonka fiye da kowa aduniyar nan.....na godema Allah daya nunamin wannan ranar....inaso na sake neman yafiya a wurinka saboda na cutar da rayuwarka sosai,ko wani yaro lokacin da yake jinjiri burinshi yaji dumin mahaifiyarshi,ya kasance atare da ita don samun kulawa daga gareta a koda yaushe,koda ace yana da uba,amma kai baka samu wannan gatancin ba,ka tashi hannun maza ba'a hannun mahaifiyarka ba,baka samu soyayyar nan ba,duk da mahaifinka yayi ƙoƙari sosai wurin gina rayuwarka tayi kyau,haka ƴan uwanka ma ba su bari ka zubar da hawayenka ba,amma duk da haka nasan abun ya jima yana maka Ciwo..."
Tana ƙarasa maganar,ta zube saman guiwowinta agabanshi,tana roƙon yafiyarshi,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,cikin sauri shima ya zube saman guiwowinshi suna fuskantar juna ita dashi,
"Mommy dan Allah ki tashi,banason kina duƙamin,komai ya wuce yanzu tun da kin dawo wurinmu da ranki kuma da lafiyarki,har yanzu kina da sauran damar da zaki gyara kuskuren da kikayi abaya mommy," ashagwa6e ya ƙarasa maganar,murmushi ta saki tana kallonshi,ji take yi da tana da ikon da zata mayar dashi cikin cikinta,taƙara haifo shi da tayi,don kawai ta bashi wannan kulawar daya rasa,
Sun jima a wannan yanayin,kafin daga bisani suka miƙe tare,ta ruƙo hannunshi cikin nata,ta wuce dashi upstairs ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake a wurin suka shiga,ɗakin ya haɗu sosai,
"Mommy me yasa ba kije gidaba?wurinsu Abba su ganki? Yayi tambaryar yana kallonta,
"I just came because of u junaid,inaso mu samu lokaci sosai atare,ka ganni dakyau nima na ganka da kyau,tun yanzu in fara aikina na baka kyakkwayar kulawa kamar jariri,in yaso gobe zamu shiga gidan da safe ko?
Murmushin jin dadi junaid yayi tare da cewa"Eh,mommy,dama ni yakamata in fara ganinki tunda dama nine ban sanki ba a zahiri"
"Bansani ba ko kana jin yunwa,amma zansa akawo mana abinci,in baka abaki kaci ka ƙoshi,yau dae atare da babyna zamu kwana,'
Dariya junaid yayi,ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai mommynshi ta shiga bashi kulawa a wannan lokacin,
Kunji yadda akai junaid ya kasance tare da mommynshi,har ta ɗauko ma Abbansu video ɗinsu saman gado ta tura mashi,abunda yasa kuma Abban bai gane Voice ɗinta ba,shine da kanta tayi amfani da wayarta wurin canza muryarta don ta tsoratar da Abbansu.

💋Boss Bature💋

fitowa Abbansu yayi daga cikin ɗakin nashi fuskar nan tashi awashe saboda tsabar farin cikin dawowar Alexandra,bakomai yafi faranta mashi rae ba face Junaid daya gani rungume ajikinta,yaji daɗi sosai,ko ba komai Junaid dae ya haɗu da mommynshi,hankalinshi zai ƙara kwanciya,

Bai sanar masu da zuwan nata ba,saboda sunyi waya da ita ta sanar dashi cewar till tomorrow zasu shigo gidan don tana bukatar kasancewa da junaid don su kara fuskantar juna sosae,hakan yasa ya bari kawai sae goben sannan su ganta unexpected,duk da a kagare idanunshi suke da suyi tozali da ita.

Gaba daya suka haɗu atare suka wuce masallaci,

Jin shiru hayaam bata fito ba tsawon lokaci,yasa Azmee leƙawa ɗakinta,anan ta same ta zaune dirshan gefen gadon ta zabga uban tagumi,jin motsin mutun yasa ta ɗagowa fuskarnan a yamutse ta kalli azmee,
"Hayaam wai dama duk budurin nan da akeyi acikin gidan nan kina ɗaki ƙumshe"?
Jin abunda azmee tace yasa tace"hmmmm,to ina zani Aunty azmee?babban yaya ya kore ni daga gidan nan,nasan muddin na leƙa waje ya ganni sai yasa an kora ni daga gidan nan,'
Cike da mamaki azmee tace"Subhanallahi!taya akai hakan ya faru?laifin me kika aikata mashi da har ya koreki daga gidan nan?shi da ma bai damu da mutane ba"
ta6e baki hayaam tayi kafin tace"Ni banyi mashi laifin komai ba,Sehrish ce ta shiryamun makircin da yasa har ya kore ni,batare da nayi mashi laifin komai ba,"
Tunda tasoma magana azmee ke kallonta,ga rashin gaskiya nan ya bayyana ƙarara a fuskarta,taya akai ma Sgr yasan da zamanta da har zai kore ta?dole sai in itace tayi mashi shisshigin da yasa har ya ganeta kuma ya kore ta,
"Allah ya kyauta toh,!yanzu ya zakiyi kenan?kinfa san halin shi!dole fa ki tattara kibar gidan nan!in ba haka ba wlh zaki fuskanci mummunan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login