Showing 285001 words to 288000 words out of 432432 words
Chapter 96 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
faɗin"Wayyo Allah na!Babban yaya dan Allah kayi haƙuri ka sauke ni ƙasa,wlh bazan ƙara ba,zan gyara maka ɗakin,'
Zuba mata ido yayi yana kallonta tun daga ƙasa har sama,wata ƴar ƙarama da ita,mamakinsa a ina ta samu ƙwarin guiwar gaya masa magana batare da jin shakkarshi ba,
"Babban yaya dan Allah ka sauke ni!Wayyo Allah da.. daddy,nashiga uku,zai kashe ni,gashin kaina zafi,zai cire mun gashina,"saboda tsabar kuka hada majina,fuskarta tayi jaga jaga da hawaye,sai da ta galabaita sosai sannan ya saki gashin kan nata,gaba daya ta zube saman guiwowinta saboda jikinta da ba ƙwari,
Zura hannayenshi yayi acikin aljihun dogon wandon dake ajikinsa,sannan yace"Tashi ki shiga ciki,ki gyaramun bedroom ɗina"
Jikinta na kerma ta miƙe da sauri da sauri ta tunkari ɗakin nashi tana faman shessheƙar kuka,tana ɗaga ƙafarta zata shiga ɗakin taji an dakatar da ita,
"Karki kuskura ki shiga ɗakin nan"!!!! Rass taji gabanta ya faɗi jin Muryar daddynsu,a firgice ta juyo don ta shaidawa idanunta,
Shigowarshi kenan cikin palourn yayi maganar,a wani sukwane Sgr ya wurga eye balls ɗinsa akanshi,takawa yayi har zuwa gabanshi ya tsaya suna Facing ɗin juna,sannan yace"meyasa kake son takura rayuwarta ne?yarinyar nan ba ƴar aiki bace,ƴata ce!kuma ni ne na bata Umarnin cewa ta daina aiki acikin gidan nan!akan me kakeso ta fifita Umarninka akan na mahaifinta?matsayinmu ɗaya ne a wurinta ne"?
Wannan maganar ta Abusufyan ba ƙaramin Fusata shi tayi ba,Yadda kasan zaki haka ya shiga fitar da huci ta hancinsa,ya ma rasa amsar da zai ba Uncle ɗin,saboda zuciyarshi da ta hasala,don har bugu zai iya kai mashi,muryarshi na kerma yace"Un...cle!Are u telling me dat matsayinmu ba ɗaya ba a wurinta!"jinjina kanshi ya shiga yi yana fama ciccije la66ansa,ran manya ya 6aci,yaci gaba da cewa
"Of course our position is not the same,but she's my younger sis,ina da right ɗin da zan sanyata aiki tayi mun,why kake so kajamin raini a wurinta"! daƙyar voice ɗinshi ke fita saboda tsabar 6acin rai zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi,
"Ba raini nakeso naja maka ba a wurinta!tabbas ƙanwarka ce ita halak malak,kuma kana da ikon da zaka sanyata abu tayi maka,wannan gaskiya ne,amma Ni mahaifinta na hana haka!ban amince ba,tayi aiki a ƙarƙashin kowa ba,Azmee itace mai aikin gidan nan!ita yakamata ace tana yin duk wani aikin daya dace,idan ma Aikin azmeen ke baka so,Zan iya sawa a ƙaro wasu masu aikin da zasu rika yi maka,amma ba ƴa taba,saboda ita ba ƴar aiki bace......"tunkan ya ƙarasa maganar Sgr ya daka mashi wata irin gigitacciyar tsawa,a tsiwace yasa hannu tare da toshe ears dinsa yana faɗin"ENOUGH!Enough!banason ji,banaso,she must execute my Command,that's may final say" ya karasa maganar yayin da idanunshi ke aruntse ruff ya rufesu
Abusufyan yayi ma tsawar,amma gigitar da sehrish tayi,tamkar zata zauce,ƙanƙame jikinta tayi,cike da fargaba,
Zuba mashi ido abusufyan yayi yana kallonshi,a hankali ya zame tafin hannayensa daga toshe kunnuwansa da yayi,a hankali ya ɗan ware blue eyes ɗinsa,tare da juyawa ya kalli wurin da Sehrish ke tsaye a ƙopar ɗakinsa yace"Wuce ciki ki gyaramun bedroom ɗina"!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,wannan ƙarfin halin na Sgr ba ƙaramin mamaki yaba Abusufyan ba,a tsananin tsorace ta wurga idanunta kan daddynsu don taji me zaice,
"Karki kuskura ki sanya ƙafarki a ɗakin nan!idan har na isa dake"!!wannan shi ake kira da tashin hankali,zazzare idonta tayi tana kallonsu,ta rasa Umarnin wa zata bi,A zarihi dae tafi tsoran Sgr,a baɗini kuwa tafi son tabi umarnin mahaifinta saboda sanin matsayin da yake dashi a wurinta,sa6a mashi zai iya haifar mata da gagarumar matsala a rayuwarta,haka zalika sa6ama sgr ba ƙaramar matsala zaija ma kanta ba,ta rasa inda zata tsayar da kwayar idonta,idan ta kalli Sgr sai ta kalli abusufyan,kowannansu ita yake kallo,daga ganin fuskar Abusufyan zaka san cewar hankalinsa ba a kwance yake ba,babban abunda yake fargaba shine Sehrish taƙi bin Umarninsa,duba da yadda ta gaza motsa jikinta,tabbas zai kunyata sosai kuma darajar da yake da ita ta mahaifinta zai zube ne a idon sgr,zai cigaba da ganin kanshi ne amatsayin Sarki,wanda ke bada Umarni kuma dole abi,
Wata irin tsawa sgr ya daka mata,wadda har sai da jikinta ya girgiza sosai tabi ta rikice,a fusace yace"won't u go in!"
Yana rufe bakinsa,Abusufyan yace"idan har kika kuskura kika shiga ciki,zan yafe ki ne acikin ƴa'ƴana,babu ni babu ke!"
Jin wannan maganar yasa ta fashe da matsanancin kuka,baiwar Allah tana a cikin tsaka mai wuya,yarfa hannunta tashiga yi tana faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'Un Ya Allah ka kawomun ɗauki!daddy!!babban yaya!!bansan ya kukeso inyi da kaina ba!!dan Allah ku ƙyale ni!kubarni in ba haka ba zuciyata zata iya bugawa in mutu,"
Tuni jikin Abusufyan yayi wani irin sanyi,idanunshi suka cika tab da hawaye,tsananin tausayinta ne ya kamashi,kamar yaje ya rungumota ajikinshi ya lallasheta,Amma yaci alwashin cewa bazai ta6a bari Sgr yaci nasara akanshi ba,
A 6angaren Sgr kuwa,ya gama hasala tunda yake a rayuwarshi bai ta6a bada umarni aka tsaya yi mashi jayayya ba sai yau,sau ɗaya yake bada command kuma dole abi batare da anyi mashi musu ba,runtse idanunshi yayi tare da tura yatsun hannayenshi cikin sumar kanshi yana cakuɗata,yayin da yake ɗan cizon lips ɗinsa,wani irin huci ke fita daga hancinsa,wannan ɗabi'arsa ce aduk lokacin da ranshi ya 6aci sosai,steps uku ne matakin hauhawarshi,idan yakai step na ƙarshen the most dangerous kenan don tamkar aljani yake komawa kuma kowaye gabanshi bai gani tamkar makaho yake komawa,a wannan step ɗin idan ya damƙi mutun a hannunshi yana bugunshi sae yaga gawarshi,kuma babu mai iya control ɗinsa har sai lokacin da Allah yasa zai dawo hayyacinsa,amma zaiyi wuya yakai wannan step ɗin sai in ya damƙi mai laifi zai hukunta shi,iya step na biyu yake tsayawa,mataki na farko shine zaka ga yana huci yana zagaye wuri,na biyu kuma Shine yake cizon la66ansa sosai,ya runtse idonshi ya kuma cusa yatsun hannunshi acikin sumar kanshi yana faman sakin huci tamkar mayunwacin zaki,
Jini ne ya shiga ɗiɗɗigowa daga saman pink lips ɗinsa hakan ba ƙaramin tayar ma sehrish da hankali yayi ba,ita da bata saba ganin yana yi ba,Abusufyan kuwa hankalinshi kwance saboda yasan sgr sarai tun yana yaro yasan shi da wannan baƙar zuciyar,idan ya cije la66ansa har sai ya fasa su,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan cikin shessheƙar kuka tashiga cewa"Dad..ddy dan Allah ka ce mashi ya daina,yana fasa la66ansa da kanshi,!"Shi yake fasa la66ansa amma raɗaɗin ita take jinshi ajikinta saboda tsabar ƙaunar da takeyi mashi,
Da wata irin murya ya kuma cewa"ki wuce ciki nace,karki bari na ƙara maimaita maki hakan!" saboda tsabar ruɗu ta juya zata shiga ɗaƙin,aikuwa abusufyan ya daka mata tsawa,a ruɗe ta juyo tana kallonshi yayin da hawaye ke fita a idanunta,hanya ya nuna mata da hannunshi yace"Zoki wuce"
A tsorace take kallon Sgr wanda idanunshi ke arufe,sosai ya runtse su,ganin haka yasa tayi tunanin watsawa da gudu tabar ɗakin don tabi Umarnin mahaifinta,tasan cewa kafin ya buɗe idanunshi tabar falon,
Daddagewa tayi da gudun gaske ta watsa aguje ta nufi hanyar fita daga falon,sae dai ina kafin ta ankara sgr ya zabura a hargitse yabita,abusufyan na ƙokarin taroshi aikuwa yayi wurgi dashi gaba ɗaya,yayi gefe guda ƙasa,A zafafe ya damƙi waist ɗinta,wani irin ruƙo yayi mata ruƙo bana wasa ba,ya ɗaɗɗagota sosai ya manna ta da jikinshi,bedroom ɗin shi ya nufa da ita,wannan ƙarfin halin har ina,ran abusufyan ba ƙaramin 6aci yayi ba,miƙewa yayi da sauri ya tari Sgr kiciniyar kwace Sehrish ya shiga yi da hannunshi,nan fa suka kacame ma juna,
"Subhanallahi me nake gani haka"!!muryar Abba ce ta karaɗe kunnuwansu,gaba ɗaya suka juyo kowa na huci suna kallonshi,a lokacin Sgr ya saki sehrish daga hannunshi,da gudu ta miƙe tana kuka,ta nufi wurin Abba,gaba daya ta faɗa jikinshi,rungumeta yayi yana ɗan bubbuga bayanta,yayin da idanunshi ke akan Sgr da Abusufyan,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,yadda sgr ya manta wanene abusufyan a wurinshi,har yake ƙoƙarin yin dambe dashi,hauka maganinka Allah,
"Abusufyan da hankalinka kake kokoyi da Rafayet kamar wasu tsararrakin juna?duk akan menene kuke wannan faɗan"?
Yayi tambayar tare da mayar da idanunshi kan Sgr wanda ke tsaye har lokacin sama yake bai sakko ba"Rafayet ka bani mamaki!ka rasa dawa zakayi dambe sae Kawunka,ƙanin mahaifinka!Anya baka fara shaye shaye ba?nafara zarginka," afusace ya juya tare da shigewa cikin bedroom ɗinshi yaja ƙopa ya rufe,
"Bansan me rafayet ya ke ɗaukar kanshi ba,Taya zan ba yarinya umarni A matsayina na mahaifinta sannan yace dole saita take umarni na don tabi nashi?saboda haka fa ya ke ƙoƙarin buguna sai kace wani tsaransa"da alama ran abusufyan ya 6aci sosai,yana maganar yana nufo inda su Abban suke tsaye shi da sehrish,hannunta na ruƙe cikin na abban,wani irin zazza6i ne ya rufar mata mai zafin gaske,ga ciwon kai mai tsanani da take fama dashi,duk don saboda tashin hankalin da suka jefa ta ciki,kuma har lokacin kukan take yi,
Sam Abba baiji daɗin abunda ya faru ba,"kayi haƙuri Abusufyan abunda yayi bai kyauta ba,duk da ba laifinsa bane irin rayuwar da aka saba mashi da ita kenan tun yana yaro,komai yi mashi akeyi,kuma in ya bada Umarni bi akeyi duk don tsoran kada ranshi ya 6aci,"
Gyaɗa kai kawai Abusufyan yayi tare da cewa"babu komai,Ae nasan halinshi sarai shiyasa banji zafin abun sosai ba,inayi mashi uziri ne,"
Ya ƙarasa maganar tare da kallon sehrish wadda ke ta faman matse kwalla,suna haɗa ido dashi ta sunnar dakai ƙasa,
"am really sorry my daugher,banyi hakan don na 6ata maki rai ba,"
Cikin shessheƙar tace"Ammm..ma daddy,cewa fa kayi zaka yafe ni acikin ƴa'ƴanka,idan har nabi umarninsa,"
Murmushi ya ɗan saki akan fuskarshi kafin yace"wasa fa nake maki,banda hankali ne,ae koda ace kin bi umarnin nasa bazan faɗi hakan ba,zan dai ji ɗaci araina,na faɗi hakan saboda ina gudun ki ƙi bin Umarni na,"
"Daddy nidai banason wannan wasan,dan Allah kada ka ƙara faɗamun hakan," yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya yaso ya basu ba,don har sai da ta bubbuga ƙafafunta ƙasa,don ya tabbatar da cewar bataso,
"In sha Allah bazan ƙara ba,kinyi haƙuri ko"?
ɗaga mashi kai tayi alamar Eh,
"Wato kun sasanta tsakaninku,ni kuma kun barmun yaro na,cikin wani hali ko"?Abba ne yayi maganar cikin zolaya,hada ɗaure fuskarshi,
Abusufyan yace"Yaya ai kai kaɗai kasan yadda zaka shawo kanshi,don yanzu duk wanda yayi gigin zuwa wurinshi,ba ƙaramar matsala za'a samu ba,"
Murmushi Abba yayi kafin yace"Shikenan zanje in lallashi abuna,kai kuma kaja ƴarka ku wuce ku bamu wuri,"
Hannun Sehrish Abusufyan ya ruƙe,tare da janta suka bar part ɗin yana dariya,
A bakin ƙopar bedroom ɗinsa ya tsaya cike da zullumin taya zai shawo kan sgr,hannu yasa yayi knocking ƙopar,shiru Sgr bai buɗe masa ƙopan ba,hannu yasa ya ƙara knocking ɗin ƙopar yana kiran sunanshi"Rafayet!ka zo ka buɗe mun ƙopa,inason magana dakai,"shiru bai ji motsinshi ba,babu alamun zai buɗe masa ƙopar,kwantar dakai abba yayi ajikin ƙopar cikin lallashi ya soma magana"haba rafayet ɗina,ni fa ne abbanka,so kake yau in gaza runtsawa?idan har bakazo ka buɗe mun ba anan zan kwana,"ya ƙarasa maganar tare da zuƙunnawa ƙopar ɗakin nashi,abu kamar wasa ya fara gyangyaɗin bacci,duk in ya ɗan farka sai ya ambaci sunan Shi Rafayet ka buɗe mun ƙopa,so kake na kwana anan?
Duk wannan surutan da Abbansu ke yi kaf a kunnan sgr,wanda ke zaune saman front chair na dressing mirror ɗinshi,ya kifa kanshi asaman Dressing mirror,gaba ɗaya sumar kanshi ta rufe mashi side by side na fuskarshi,zuciyarshi ba ƙaramin tafarfasa take mashi ba,ranshi yayi mugun 6aci wai har shi zai bada Command aƙi bin umarninsa?bakowa yafi ji ma haushi ba fa ce Uncle ɗin nasu,don me zaiyi iko da Sehrish?saboda kawai ya haifeta?wani irin huci ne ke fita akanshi tabbas sai ya nemi matsayin dake asama dana mahaifinta ba don komai ba sai don yayi iko da ita,akan idon mahaifinta kuma,
Yana cikin yin wannan zancen zucin yaji Muryar Abbansu kamar ta wanda yasha giya,saurarawa yayi yana sauraron waƙar da Abbansu ke rera masa daga waje,tun yana yaro idan aka 6ata mashi rai,ya fusata da gudu yake shiga bedroom ɗinsa ya rufe ƙopa,idan abbansu naso ya sauko daga fushin da yake yi sai yazo ƙopar ɗakinshi yana kwankwasawa yana raira masa waƙa,cikin ƙankanin lokaci yake saukowa daga wannan fushin,
Jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,ɗan ɗagowa yayi da kanshi ya wurga eyes ɗinshi kan agogon bangon dake a manne ƙarfe kusan ɗaya na dare,Abbansu na waje yaƙi tafiya,kuma in har bai buɗe mashi ƙopar nan ba,to anan wurin zai kwana,saboda ya ta6a yi mashi haka,miƙewa yayi jikin shi babu ƙwari ya ƙarasa tare da jan ƙopar ya buɗe mashi,jin an buɗe ƙopar yasa Abbansu miƙewa jiki na rawa,suna haɗa ido da sgr,yasa hannunshi a idanunshi yana yi mashi kukan ƙarya wai ya barshi a waje,sanyi ya bugeshi,hakan da yayi ba ƙaramin dariya yaso ya ba Sgr ba,
Juyawa Sgr yayi tare da shigewa cikin bedroom ɗin,abban yabi bayanshi,a gefen gadon suka zauna suna fuskantar juna,
"Yanzu faɗamun,me yake damunka"?
Shiru ya ɗanyi tamkar bazai tanka masa ba,daƙyar ya iya buɗe bakinshi yace"Abba,Uncle ya gama dani!har ni zan ba yarinyar can Umarni,ya hanata,don kawai yana taƙamar cewar shi mahaifinta ne"?yana magana muryarshi na shaƙewa saboda tsabar 6acin rai,
"Rafayet!ni bansan me zance maka ba,ka san dai inason farin cikinka,duk wani abu da kake so ni mai iya yi maka shi ne,amma banda wannan!zan iya iko da Abusufyan amma bazan iya iko da ƴarsa ba,shi mahaifinta ne dole tabi Umarninsa tayi mashi biyayya,bijire mashi zai iya sa ta fuskanci matsala arayuwarta....."
Bai ƙarasa maganar ba Sgr yace"That means ba wanda ya isa yayi iko da ita sai shi kawai?kenan Ni bani da wani matsayi a wurinta?bamu isa mu sata abu ba tayi kenan?
Jinjina kai abbansu yayi tare da cewa"Hakane!maganar gaskiya babu wanda ya isa yayi iko da ita a halin yanzu bayan mahaifiyarta sai kuma shi"
"Abba babu wani sama dasu wanda zai iya iko da ita fiye da mahaifanta"?yayi maganar ranshi a ɗan 6ace yana kallon Abban nasu,
Gyara zama abbansu yayi,fuskar nan tashi ɗauke da wani 6oyayyen murmushi yace"duk duniyar nan bayansu mutun ɗaya ne!wanda zai iya yin iko da ita,fiye da iyayenta!'
"Wanene shi"?ya tambaya Yana jiran jin amsar da Abban nasu zai bashi,
"MIJINTA,shine wanda zai iya yin iko da ita fiye da iyayenta!Mahaifinta zai iya kiranta tazo gida mijinta ya hana,kuma dole ta hanu,ko tana so ko bataso,"
Hannu Sgr yasa tare da dafe gefen kanshi,yana faman sauke ajiyar zuciya,muryarshi ƙasa kasa yace"Abba!babu wata hanyar sai wannan"?
Jinjina kai Abbansu yayi tare da cewa"that's the Only solution,"!
Ya ƙarasa maganar yana kallon fuskar SGR,Acikin zuciyarshi kuwa Allah Allah yake akan ya amince zai auretan,Shikenan burinshi zai cika ganin cewa Rafayet yayi aure,
"She's too young for me,Ni bazan iya auren yarinyar da ko Secondry school bata kammala ba,wannan abun kunya ne agare ni,da matsayi na in aureta?da wani ido duniya zata kalleni"?
Zuru Abbansu yayi yana sauraronshi,wato Sgr har yanzu yana nan da wannan ji da kan nashi,
Hannu Abbansu yasa tare da dafa shoulder ɗinshi sannan yace"Rafayet!nima ban goyi bayan hakan ba!idan har ka aureta girmanka zai faɗi ne!Amma ga wata shawara"?
ɗan ɗagowa yayi da idanunshi masu ɗauke da bacci ya kalli abban nasu"Wane shawara ne wannan"?muryarshi a akasalance yayi maganar,
Abba yace"Me zai hana kuyi auren yarjejeniya atsakaninka da ita yarinyar"?
"Kamarya kenan"?
Ƙayataccen murmushi Abbansu ya saki yana kallonshi kafin ya ɗaura da cewar"Wata nawa ya rage maku ku koma U.S"?
"Remain 3 Months,"ya bashi amsa,
Abba yace"Yawwa,before 3 months ɗin nan su cika,me zai hana ka aureta,a matsayin Contract marriage,don tayi maka aiki kawai na tsawon wata uku,kamar yadda kake so da zarar time ɗin ya cika,kawai saika bata divorce letter ɗinta,Amma ya kake gani"?
Shiru Sgr ya ɗan yi yana nazarin maganar Abban nasu,kafin yace"Abba bacci nake ji,i will think about it before tomorrow,"
"Ba damuwa,kafin gobe dae yakamata kayi tunanin abunda ya dace,zan jira jin amsarka da safe," ya ƙarasa maganar tare da juyawa ya fuce daga ɗakin nashi,
Blanket ɗinsa yaja ya lullu6e jikinshi har zuwa neck ɗinsa,maganar Abbansu ce ke tayi mashi yawo acikin kanshi,ga bacci yana ji amma yaƙi ɗaukarsa,sae faman juyi yake yi asaman gadon,tabbas in ya aureta zaici galaba akan Uncle ɗinsu Abusufyan,yana so ya dinga commanding ɗinta akan idon mahaifinta kuma ba yadda zaiyi dashi,na biyu kuma Yana so yarinyar taci gaba da aiki a ƙarkashin ikonshi,har zuwa lokacin da zai koma U.S!!idan har yana so hakan ya faru kenan dole sai ya aureta!?OMG!
"That could not be possible for me as a Surgeon General to marry a young girl who has not even finished her secondary school,"ya furta hakan tare da jan blanket dinsa ya rufe fuskarshi daƙyar bacci 6arawo yayi awon gaba dashi,
*Boss Bature*
Saukowa down abba yayi fuskar nan tashi ɗauke da murmushi,anan ya samu abusufyan tsaye yana jiranshi,yana ganin ya tunkare shi,
"Ina sehrish ɗin take ne"?
Abusufyan yace"Tun ɗazu ta wuce ɗakinsu,Nima kai nake jira muyi sallama kafin inje in kwanta,Amma ya kuka ƙare da rafayet ɗin?ina fata dai ya sauko daga fushin nan nashi"?
Fuskar abba ɗauke da murmushi yace"daƙyar na shawo kanshi,yanzu haka ma ya kwanta,sae kayi haƙuri da surukin naka,"
Dariya abusufyan yayi kafin yace"ae ni bansan ya zamu ƙare da rafayet ba,lamarin ya fara bani tsoro,ƙoƙarin buguna fa yake yi ne?ahaka zan zama surukinsa?yana yi mun kallon tsaransa?Lokacin dana shiga ɗakin nasa samun shi nayi fa ya damƙi gashin kanta ya ɗaga ta sama kamar wata ƴar babyn Roba,yarinya sae kuka take tana bashi haƙuri amma ko ajikinshi,"
Abba yace"Ae rafayet sae addu'a,amma abun nashi ƙara gaba yake yi,yana ji Da ƙarfin nan nasa,bakowa zai iya jure zama dashi ba," suna tafiya suna fira har suka zo ƙofar ɗakin Abba,anan su kayi sallama da abusufyan ya wuce nashi ɗakin,
Fuskarshi a washe ya shiga ɗakin kamar ance ya ɗaga idanunshi karaf suka sauka akan Junaid dake baje saman gadon yana bacci,ga Mommynsa agefe,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,daga fitarsa har ya shigo ɗakinshi,Anya kuwa junaid shi kaɗai ne?yaro kamar mai iska,har leƙa ɗakinshi yayi ya same shi kwance yana sharar bacci shi da Talal,amma yanzu daga dawowarshi ya same shi a ɗakinshi,
Cike da takaici ya shiga cikin