Showing 366001 words to 369000 words out of 432432 words

Chapter 123 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

masu sallama,

Abusufyan ne ya ɗauko su acikin motarshi tare da Baban sadeeq saboda zasu wuce masallaci daga nan,'


Tun bayan da ta kammala sallar magrib,ta koma saman gadon Oummasu ta zauna tana kallonta,a ƙagare take da ta farka duk da tasan cewa,ba a hayyacinta take ba,batasan wacece ita ba ayanzu,
  "Yakamata in sanarwa su Jahad da hosana,"tayi maganar cike da zumuɗi ta dauki wayarta dake ajiye gefenta,
  Contacts ta shiga,tare da lalubo numbar jahad ta danna mata kira,Kusan sau uku tana ringing ba'a ɗaga ba,hakan yasa ta tura mata text message,
   Layin hosana,ta kira itama wayar bata a kusa da ita,tayi ringing harta katse ba'a ɗaga ba,
  Yanke shawarar kiran junaid tayi,cikin rashin sa'a ta samu wayarshi a kashe,
  Tur6une fuska tayi ranta a 6ace,taso ace itace zata fara yi masu albishirin ganin Oummansu,Amma duk sun ƙi ɗaga kiran wayarta,
  Yunƙurawa ta ɗan yi saitin fuskar Oummansu,ta ɗauketa photo da camera ɗin wayarta,kusan hoto uku tayi mata,
ta whatsapp ta tura masu hotunanta,'


Motsin mutane taji acikin palourn,ranta ya bata cewa Su Baban sadeeq ne suka dawo,bata leƙa ba,kwanciya tayi a gefen oummantasu,

Su biyu suka shigo cikin palourn,zama sukayi saman sofas ɗin suna fuskantar juna,Abusufyan yace"Bamu da wasu kalmomi da zamu iya amfani dasu wurin gode maku,kunyi matuƙar yin ƙoƙari,kun kula da rayuwar abu,tamkar ƴar cikinku,kun damu da ita sosai,Allah ne kaɗai zai iya sakamaku,"
  Baban sadeeq yace"duk yiwa kaine,idan ka taimaki rayuwar wani kaima Allah sai ya taimaki ta ka,Naji daɗi sosai,kuma nayi matuƙar farin ciki,daya kasance kaine Mijin Zainab duk da an shiga tsakaninku,kuma mahaifinsu sehrish!hankalina ya kwanta sosai,Abu zata rayu atare da mijinta ga kuma ƴa'ƴanta,uwa uba kuma ga dangin mijinta,Allahu Akhbar,najiye mata daɗi,ƙarshen wahalarta yazo da yardar Allah,"
  Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"Amma malam,Ya maganar sayyadi ne!?ko kuna da labarinshi"?
  Shiru Malam nura ya ɗanyi na wani lokaci yana tunani kafin yace"Ae Sayyadi tun ranar da aka nemi abu aka rasa,tun daga ranar bamu ƙara sanyashi a idanuwanmu ba,gidan ma a garƙame muka same shi da ƙaton ƙwaɗo,".
  dakatawa yayi da yin maganar,
Hakan yasa Abusufyan cewa"dama nasan bazai tsaya ba,guduwa zai yi,"
  Girgiza kai Baban sadeeq ya ɗan yi tare da cewa"A'a,bana tunanin ya gudu,Munafukin duk inda yake yana acikin garin nan!yanzu haka ba mamaki yasan da zuwanku!ae ba ƙaramin shu'umin mutun bane,"
  "Amma taya akai kasan cewa,yana acikin garin nan?ko kun ƙara haɗuwa dashi ne"?acewar Abusufyan,
  Baban sadeeq yace"ƙwarai kuwa!Kama tuna min!ae can shekarun baya lokacin da aka nemi abu aka rasata,fitsararran ya tako da waɗannan ƙafafuwan nashi masu kama dana zabbi har ƙopar gidana,
  Lokacin na dawo daga sallar asuba,na shiga da mashin cikin gida,nadawo zan rufe ƙopa kenan ina ƙokarin rufewa,Naji an banko mun ƙopar,A firgice na kai idanuwana wurin don inga wani taƙadirinne!aikuwa sai nayi tozali dashi,A tsaye ruƙe da qugu,nan fa nashiga faɗin A'uzubillahi minasshaiɗanir rajim,"sai cewa yayi"Ni ne shaiɗanin"?nace mashi "to ae baku da bambanci da shaiɗan,ƙahonne kawai ke babu!shin me ma yakawo ka ƙopar gidana?ko kazo ne kayi mun futsarar taka daka saba ne?sai yace mun saƙo ne yazo dashi,nace saƙo kuma?yace mun eh,yasa hannu cikin aljihun jallabiyarshi ya zaro wata ƴar doguwar takarda,ya miƙo mun tare da cewa"Saƙon Abu ne,idan mun sameta,A bata wasiƙar," jin cewa sakon na abu ne yasa na amsa,to tun daga wannan lokacin da ya haura ƙafa,ban ƙara sanya sayyadi acikin idanuwana ba,hatta makarantar islamiyyar da muke koyawa atare dashi,ya daina zuwa...."
  Lokacin da ya kai ƙarshen labarinshi,Abusufyan yace"Amma kun karanta wasiƙar"?
  Baban sadeeq yace"A'a,babu wanda ya ta6a ta,Ae amana ce,yace wasiƙar ta abu ce shiyasa bamu karantata ba,"
  A ƙagare Abusufyan yake daya ga wannan wasiƙar,
   "Yanzu wasiƙar tana ina ne"?
"Tun lokacin dai,bayan tafiyar sayyadi,dana shigo cikin gida,kaitsaye wurin Maman Sadeeq na wuce,ita nabawa ajiyar wasiƙar,"
  Ajiyar zuciya Abusufyan ya sauke,
  "Gobe,in Allah ya kaimu,sai muje gidan a ɗauko wasikar,yau dai anan zaku kwanan mana,"acewar Abusufyan,
   "Akwai yaronmu fa,mun barshi a gida,"Baban Sadeeq ne yayi maganar,
"idan mun fita yin sallah,sae mu dawo tare dashi," acewar Abusufyan
  Suna cikin tattaunawar nan aka kira sallar isha'e,atare suka fita yin salla daga can zasu wuce gidan,Su ɗaukko Sadeeq,

Fitowa Sehrish tayi daga Bedroom ɗin Oummansu,wuraren ƙarfe 8:30 na dare,a palour ta samu Maman sadeeq zaune,jikinta sanye da hijabi,
  Tana ganin Sehrish ta mike,tare da tunkararta,
  "Rishi,zonan mana,baki bani labarin ya kuka ƙare ba,bayan kun bar nan"tayi maganar tare da ruƙo hannunta,saman 3 seater suka zauna,
  Nan fa Sehrish ta shiga bata labarin rayuwarsu,tun daga lokacin da suka koma katsina har ƙarshe,jikin Maman Sadeeq ba ƙaramin sanyi yayi ba,jin irin wahalar da suka sha,ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin farin ciki tayi ba, 

sun jima suna firar yaushe rabo,kafin suyi sallama kowa ya wuce ɗaki,don ba ƙaramar gajiya suka kwaso ba,

Koda Sehrish ta koma ɗaya daga cikin bedrooms ɗinsu da aka gyara masu,wanda ke a upstairs,toilet ta shiga don ta watsa ruwa ajikinta,kafin ta kwanta,Maman sadeeq kuma a downstairs ta zauna,ɗakunan su Dr haris a lokacin baya,
   fitowa tayi daga cikin toilet,jikinta sanye da undi ta ja shi har saman kirjinta,ƙarasawa tayi gaban gadon,inda ta ajiye kayan baccin da ta dauko don ta sa,tare da phone ɗinta,
  Tana ƙoƙarin kai hannu ta ɗauki wayar,Ta jiyo sautin dirar mota acikin gidan,
  "Su Daddy sun dawo kenan"tayi maganar tare da ɗaukar wayar,Har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi,bakinta fa ya ƙi rufuwa tunda aka samu Oummansu,babban burinta yanzu bai wuci Oummansu ta dawo cikin hayyacinta ba,waƙa ta kunna ta ƙure Volume,Nan fa ta shiga yin rawa,kamar wata zautacciya,juyi ta dinga yi,iska na kaɗa gashin kanta,duk cikin farin cikin ne,yaushe rabon da tayi dancing irin haka harta manta,dama can ita ba ma'abociyar yin rawa bace,duk da tana son yin rawar,yanayin rayuwane yasa bata samu wannan damar ba,a hankali ta soma bin wakar abakinta,
_rawa da girgiza zanyi gabanka,in jujjuya,zanyi maka albishir kayi dace da mai tarbiyya,sannan zan zame maka farin ciki na nan gidan duniya,Nafi kowa saninka acikin abunsha kafi son coffee_
Bata ƙarasa baitin ba,ta tsaya cak sakamakon mutun da ta hango tsaye ta cikin mirror,ya goya hannayensa asaman wide chest ɗinshi,gabanta ne ya faɗi rass,lokaci guda ta shiga taitayinta,duk tabi ta kame kanta kamar wata mara gaskiya,

Bakowa bane fa ce Sgr,still dress ɗin ɗazu ne ajikinshi,tun lokacin da ta fara rawar yazo ɗakin,kuma ta hanyar kiɗan wakar da ta kunna ne yasa ya gane cewa akwai mutun a ɗakin,dama kuma ita yake nema saboda ya tayata Murnar ganin mahaifiyarta,

tsayawa su kayi suna kallon juna ta cikin mirror,kunya duk ta rufe ta,saboda ɗan undi ɗin dake ajikinta sharara yake,gashi ko bra bata sanya ba,

Slowly ya soma takowa izuwa cikin ɗakin,da sauri Sehrish ta nufi wurin gadon tana ƙoƙarin ɗaukar Kayan sawarta,da ta ajiye asaman gadon,
Sai dai kafin tayi wani yunƙuri tuni Sgr ya ƙaraso wurin,at same time suka kai hannu saman kayan nata gabanta ne ya faɗi rass,yayin da take kallon hannunshi da ya ruƙo rigarta,a ɗan razane ta cire hannunta tare da ɗan ja da baya tana kallonshi,
ɗagowa yayi hannunshi ruke da kayan sawar nata yace"Me zaki yi dasu"?
Muryarta na kerma tace"Am..um..sanyawa..zanyi,'
Da buɗar bakinsa sai cewa ya yi"bayan na kammala abunda zanyi kenan"?
Gabanta ne ya kuma faɗuwa,throwing ɗinsu yayi saman gadon,gadan gadan ya tunkareta,jiki na rawa ta shiga ƙoƙarin ja da baya,muryarta na rawa tace"Dan Allah babban yaya kayi haƙuri,wlh bazan ƙara tafiya ba,without ur permission nasan nayi maka laifi,"ita duk a tunaninta,yazo ne ya yanke mata hukunci,saboda zuwan da tayi kano batare da saninshi ba,
"Am sorry Ya Rafayet.."wani irin kallo yake bin ta dashi,wani canji ya fara gani ajikinta,kaitsaye take fisgarshi,sai ƙokarin motsa lips ɗinsa yake yi don ya sanar da ita cewa,ba hukunta ta yazo yi ba,yazo ne don ya tayata murna,Amma ina,sam ya kasa furta hakan,duk zufa ta gama wanke mata fuska,har idanuwanta sun cicciko tab da kwalla,
Hannayensa ya sanya asaman belt ɗin wandon jikinshi,Waro ido waje Sehrish tayi,hankalinta yayi mugun tashi,tsoronta kar ace bugunta zai yi,
Fashewa tayi da matsanancin kuka,tare da aza hannunta asaman kanta,tana faɗin"Innalillahi,wayyo Allah na,"
Da gangan Sgr yake zame belt ɗin wandonsa,duk don saboda ya ƙara ruɗar da ita,lokacin da ya ƙare zare belt ɗin daga jikin wandon ya curoshi yana nannaɗe shi a hannunshi,A matuƙar tsorace sehrish ta juya da nufin ta gudu,Da ƙarfi ya kai hannu zai ruƙo undi ɗin jikinta,aikuwa gaba daya,Ya zame undi ɗin daga jikinta ya sulale,kasa gashi bata sanya komai ba,babu pant bare bra,saboda tsabar kiɗima,fasa ƙara tayi sosai ta fashe da kuka,tare da ƙanƙame ƙirjinta da hannuwanta,bangon ɗakin ta ƙankame jikinta na kerma,
Duk wannan budirin da akeyi babu wanda yasan meke wakana,saboda sun yi nesa da downstairs,
Rumfa yayi mata da faffaɗan ƙirjinshi,ya lullu6eta sosai,nan take taji wata irin natsuwa tazo mata,daddaɗan ƙamshin turarenshi ne ya mamaye hancinta,lokaci guda ta nemi kukan da takeyi tarasa,
"Ain't trying to flog u,"ya furta hakan da wata irin kasalalliyar murya,saboda tsabar rawar da jikinta keyi,har a jikinshi yake ji,
duƙo da kanshi yayi dai dai saitin wuyanta,slowly ya manna mata kiss,har cikin zuciyarta taji wannan kiss ɗin nashi,kafin tayi wani yunƙuri,taji tafin hannunshi asaman ass ɗinta,laushin fatar wurinne ta soma fisgarshi,har ya fara shafata yana matsarta,almost 3 mins kafin ya zame hannun daga wurin,ya zagayo dasu ta front ɗinta,sosai yayi tighting ɗin ta ajikin wall ɗin kamar zai mayar da ita,cikin cikinshi,lokacin da taji hannunshi saman gabanta,gaba daya tabi ta susuce,ta shiga ƙoƙarin kufce mashi,ruƙon da yayi mata ne yasa ta kasa yin hakan,sosai ya shiga shafa wurin before ya janyo tafin hannun nashi izuwa saman ƙirjinta,duka hannunshi biyu ya sanya,duk irin girman tafin hannunshi,sai da boobs ɗinta suka cika su fam,har babu space,damƙarsu yayi sosai tare da runtse idanuwanshi saboda wani irin yanayi da ya fara tsintar kanshi aciki,muryarshi na kerma ya ambaci sunanta"Reesh.."for the first time da Sgr ya fara furta sunanta,tunda take yi mashi aiki bata ta6a jin ya ambaci sunanta ba,tamkar baima san sunanta ba,sosai ya cusa hancinshi acikin lallausar sumar kanta,batare da ya saki ƙirjin nata ba,da alama fa Sehrish suman tsaye tayi,gaba ɗaya sun shiga cikin wani irin yanayi mara misaltuwa,sautin kiɗan da sehrish ta kunna ne ya ƙara jefasu cikin wani yanayin na sha'awar son kasancewa da junansu,Taken waƙar Love Nwantiti ya shiga,baka jin komai sai sautin breathing dinsu dake fita da zafi zafinshi,yayin da heart ɗinsu ke beating very fast at same time,tamkar zata 6allo daga ƙirjinsu,Ya salaam!

*Boss Bature*

A 6angaren su Junaid kuwa,sunsha yawo shi da Jahad,wuraren 8 suka kamo hanyar zuwa gida,bacci cike da idanuwansu,driving yake yi slowly kamar baison yin tuƙin,
Muryarshi tamkar zai yi kuka yace"Jahad,mun ci komae amman bafa musha ice cream ɗin ba"
"Mu haƙura Junaid,hankalina ya koma kan gida,dare yayi yakamata ace tun 6 muna a gida,"
..."Jahad,nidai inaso nasha,na kuma baki,saboda shi na fito ma ni,"
"Asthma fa gare ka,ko ka manta ne?ni bazan so abunda zai cutar mun dakai ba,"
Tana kai ƙarshen maganar taji,ya dakatar da motar a gefen titi,
Juyawa tayi tare da kallonshi,tun kafin ta tambayi dalili yayi saurin cewa"Ga mai ice cream can tsallaken titi,ki jira ni a mota yanzu zanje nadawo,if not wlh bazan yi driving ɗin ba,"zuba mashi ido tayi tana kallonshi,
Ashagwa6e ya kuma cewa"kin yi shiru baki ce komai ba,
Murmushi ta ɗan saki tare da cewa"Kada ka damu my Romeo tunda kana so,Ni zanje na siya mana ice cream ɗin,ka jira ni a mota,naga kaman bacci ma kake ji,yanzun nan zan dawo,"ta ƙarasa maganar tare da ruƙo ƴar purse ɗin ta,
Tana ƙoƙarin fita daga motar,taji ya ruƙo rigarta,tsayawa tayi cak,hakanan ta dinga jin zuciyarta nayi mata wani irin bugu mara daɗin ji,
Juyowa ta ɗan yi tare da kallonshi,lumshe idanuwanshi yayi tare da buɗesu,da wata irin murya tamkar bata shi ba,ya furta mata"I LOVE U SO MUCH,"
har cikin zuciyarta,taji wannan kalamin nashi,dawowa tayi kusa dashi,tare da tallabo fuskarshi ta manna mashi kiss a gefen fuskarshi,tana ƙoƙarin janye la66anta,ya ruƙo waist ɗinta sosai,tare da haɗa bakinsu wuri guda,a susuce suka shiga kissing ɗin junansu sosai,almost 10 mins,kafin jahad ta janye jikinta daga nashi,da sauri ta buɗe murfin motar,ta fita daga cikinta,

Tsallaka titin tayi tana tafiya tana waiwayon motarsu,wurin mai ice cream ɗin taje,mutun huɗu ta samu a tsaye suna jiran ya zuba masu,hakan yasa ta ɗan tsaya tana jiran a sallamesu itama a bata nata,
"Jahad,"Junaid ne ya kwala mata kira,daga cikin motar,da sauri ta juya tana kallonshi dayake akwai hasken Street light daya haskaka titin,
ɗago mata hannu yayi fuskar nan tashi ɗauke da ƙayataccen murmushi,dimples ɗinshi sun lotsa sosai,
Murmushi ta sakar mashi itama,sai faman kallon juna suke yi,
..."madam guda nawa za'a baki ne"?muryar mai siyar da ice cream ɗin ce ya katse ta,juyawa tayi tare da kallonshi tace"Guda biyu nake so,"
Yana cikin zuba mata Corn Ice cream ɗin,ƙarar truck ta karaɗe wurin,Wata jibgegiyar mota ce,gadan dagan ta tunkari motar da junaid ke ciki,
Adai dai lokacin mai ice cream ɗin ya sallameta,har ta biyashi kuɗin,tun kan ta juya mai ice cream ɗin nan ya furta"Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!"a wani firgice jahad ta juya don taga menene ke faruwa,Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,A gigice ta fasa wata irin ƙara mai sautin gaske lokaci guda tayi wurgi da ice cream ɗin dake a hannunta,A zabure ta tunkari wurin da motar junaid take,Sai dai kash ƘADDARA TA RIGA FATA,
Don tuni Motar nan,tabi ta kan motar junaid,Gaba ɗaya ta danne motarshi,tayi mata rugu rugu,
Da gudun gaske mutane suka taru a wurin suna faman ambaton INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN!!!😭😭😭😭

*kullu nafsin za'ikatul maut*

💋Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*



SADDEST MOOD,

THE Greatest Lost,

Gingimarin motar nan,na sauka daga kan Motar junaid,drivern dake tuƙinta ya fusgeta da gudun gaske ko waiwaye babu,kafin mutane suyi wani yunƙuri motar junaid ta kama ci da wuta tamkar Bomb ne ya fashe a cikinta,

Wata irin razananniyar ƙara jahad ta fashe da ita,cikin fitar hayyaci ta nufi motar zata faɗa ciki,Mutane duk suka rurruƙeta,kuka takeyi kamar ranta zai fita,idanuwanta sunyi jawur dasu,jijiyoyin wuyanta duk sun firfito waje,Cizo da yakushi ta dinga kaiwa hannun mutanen dake rurruƙe da ita,muryarta adisashe take fadin"Junaid!yana cikin mota!dan allah kada ku bari na rasa shi!dan Allah ku ciro mun ɗan uwana!ina jin sautin kukanshi acikin kunne na,Dan Allah kutaimakeshi wuta tana ƙona sassan jikinshi........"tana kai ƙarshen maganar,ta yanke jiki ta faɗi asume,Mutane sunyi ƙoƙarin kashe wutar amma sai dai kash babu ruwa a kusa,lokacin da motar ƴan kwana kwana ta ƙaraso,tuni Motar junaid ta ƙone ƙurmus,Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!

Motocin Ƴan sanda ne suka zagaye wurin,tare da ƴan kwana kwanan,sun kashe wutar dake ci a motar tashi but unfortunately,basu samu komai ba dangane da junaid,domin kuwa ya ƙone ƙurmus,sai dai toka,wa'iyazubillah,

 Ƴan sandan Sun samu bayani a wurin mai siyar da ice cream ɗin nan,saboda agabanshi komai ya faru,kuma shi ne ya kira Police men ɗin,da kuma motar kwana kwanar ya basu address ɗin wurin,

A bincikensu sun gano cewa,koma waye da gangan ya aikata hakan,saboda guduwar da yayi batare da ya tsaya ba,
  Ambulance suka kira,aka shigar da jahad cikin motar,kai tsaye suka wuce da ita,asibiti,
   Cigaba da bincike ƴan sandan sukayi,ko'ina na wurin suka shiga dubawa,Anan suka samu ƴar purse ɗin jahad,tare da takalmanta,sae kuma ice cream corn ɗin da tayi wurgi dashi,
..wani Inspector ne ya ɗauki,purse ɗinta,ya zaro wayarta,dake ta ringing acikin jakar,Duba screen ɗin wayar yayi,Sunan Ya Omar ne ya bayyana akan screen ɗin wayar,picking Call ɗin yayi yasa ta Hands free tare da kara wayar a kunnansa,
  "Jahad kuna ina ne!har yanzu baku dawo gida ba?nayi trying number ɗin Junaid,but na same ta a kashe," runtse ido ɗan sandar yayi,jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,
   "Jahad!"Omar ne ya sake kiran sunanta,
  Sai lokacin inspector ɗin yace"kana magana da Inspector Mukhtar ne!yarinyar da ka kira wayarta,yanzu haka an wuce da ita asibiti ne,sakamakon motar da suka hau tare da ɗan uwanta,ta hadu da hadari......"

Saboda tsabar kiɗima,marshal Omar dake tsaye gaban mirror baisan lokacin da ya saki wayarshi ba,ta faɗi ƙasa,idanuwanshi azazzare yake kallon kanshi ta cikin mirror ɗin gabanshi,tuni jikinshi ya soma kerma kaf kaf kaf,
  Saboda tsabar kiɗima hanyar fita daga dakin ya nufa daga shi sai short ajikinshi,sae da ya ruƙo handle ɗin kopar sannan ya tuna cewa babu kayan mutunci a jikinshi,komawa yayi a hanzarce ya ɗauko jallabiya ya zura ajikinshi,sannan ya dauki wayarshi,
  Gudu gudu sauri sauri haka ya nufo downstairs,Mojar ya kira a waya tunkan yabar falon,ya sanar dashi cewa,An samu matsala su kasance cikin shiri zasu fita,

Da gudun gaske,motoci goma sha biyar na sojoji suka fuce daga cikin gidan,tare da wata irin jiniya mai sautin gaske,

Tracking layin Jahad su kayi har suka ƙaraso inda Motar junaid take,tunkan su fito daga cikin motar jikin kowannansu,yayi mugun sanyi,

A wani irin sukwane marshal Omar ya fito daga cikin Motar,da sauri mutane suka dinga darewa suna basu hanya don su wuce,Lokacin daya ƙarasa wurin da motar junaid take a ƙarmashe,ta lanƙwashe ta dagargaje,Jikinshi a mace ya zube saman guiwowinshi,komai ya tsaya mashi cak!tsit kake ji,
  Girgiza kai ya shiga yi da wata irin razananniyar murya ya shiga faɗin"innallillahi wa'inna ilaihirraji'un"!hannu yasa ya damƙi tokar dake a ƙasan wurin,Nan take ya fashe da wani irin matsanancin kuka,hawaye ne suka soma gangarowa asaman fuskarshi Major dake tsaye akansa,haka zalika sauran Soldiers ɗin dake a wurin kowannansu,idanuwansu cike taf da hawaye,tunda suke a rayuwarsu basu ta6a ganin hawayen Marshal ba sai yau,
   Cikin shessheƙar kuka ya furta"ku faɗamun meya faru dasu?ina ƙanina yake?Ina jahad"?
  Daƙyar ɗan sandar nan ya iya buɗe baki yace"Yalla6ai,A bayanan da muka samu a wurin mai siyar da ice cream ɗin da yarinyar taje,Sun tsayar da motarsu a bakin titin ne,ita yarinyar itace ta fito daga cikin Motarsu,tabar shi Yaron acikin Motar,ta tsallaka titi,kafin ta dawo ne,babbar mota tabi takan Motar,nan take kuma ta kama da wuta,koda muka iso bamu samu komai daga sassan jikinshi ba,
   Hannu Marshal Yasa ya tallabe kanshi,saboda wani irin jiri dake ɗibarshi,sai faman ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yakeyi,Yanke jiki yayi ya faɗi ƙasa a sume,
"yalla6ai!"major ne ya ambaci sunanshi da ƙarfi,tare da zuƙunnawa agabanshi,
  Suna cikin wannan alhinin saiga Motar journalists ta ƙaraso wurin,aikuwa tun kafin ma su sauko daga cikin motar,sojojin nan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login