Showing 159001 words to 162000 words out of 432432 words
Chapter 54 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
acikin gidan!duk irin tsaron dake gareshi,ba ita ba hatta jahad tashiga zargin waye yayi masu wannan zuwan da daddare don ya cutar da hossana,sun jima suna wannan tunanin, a ƙarshe dai bakowa suka fi zargi ba face ɗaya daga cikin security guards ɗin gidan,
Bayan sun gama jimamin nasu,Camilla ta tashi tare da fucewa daga bedroom din ta nufi kitchen don ta shirya masu breakfast,
yayin da ita kuma Jahad,ta taimaka ma hossana bayan ta sanya rigarta sannan ta kaita toilet ta taimaka mata wurin yin wanka da ruwa mai ɗumi yarda jikinta zai ɗan warware,sai da su kayi alwala sannan suka fito daga cikin toilet ɗin,
doguwar riga ta ɗaukko mata acikin wardrobe ta bata ta sanya sannan suka zura hijabansu atare,jahad ta shimfiɗa masu darduma suka hau sama tare da daidaita natsuwarsu suka kabbara sallah,har lokacin jikin hosana sai faman kerma yake yi,a tsananin tsorace take da abunda ya faru da ita adaren jiyan nan,bayan sun kammala sallar jahad tace mata taje ta kwanta tayi bacci,ita zata wuce kitchen wurin Camila,ta taimaka mata suyi aikin breakfast ɗin atare,
Bayan jahad ta fuce daga bedroom ɗin,hossana ta miƙe daga saman dardumar jikinta nata faman kerma ga rawar ɗari da take yi,saboda sanyin da take ji,lalla6awa tayi tare da hayewa saman gadon,takai hannu tare da janyo bargon ta ɗan kakka6e shi zata rufe Jikinta dashi,kwatsam taji sautin faɗuwar wani abu ƙasa,cikin sauri ta leƙa ƙasan gadon tana kallon abun nan daya fado daga saman gadon,
Diamond ring ne ɗan ziriri dashi sai faman ƙyalli yake,gabanta taji ya faɗi rass!ganin zoben da tayi ya faɗo ƙasa,yunkurawa tayi tare da tashi daga zaune sannan takai hannu ƙasan gadon tare da ɗaukko zoban,ɗago shi tayi a daidai saitin idanunta tana ƙare mashi kallo,
Zaro ido tayi hankalinta a matuƙar tashe ta furta"Ya Omar!!!!!!!!!" 😳
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖
Abban sojoji paid book ne,ga duk mai buƙatar karanta cigaban shi yayi mun magana kai tsaye ta number ta 08103884440 Whatsapp only banda phone calls, 300 ne only 🤝
Zuba ma zoben ido tayi tana kallonshi hankalinta a matuƙar tashe,gabanta na faduwa,a hankali take jujjuya shi a hannunta,lokaci guda hawaye suka fara gangarowa daga idanunta cikin shessheƙar kuka take cewa"I can't believe it! Ya omar ɗina ne yayi ƙoƙarin raping dina? Shine yaso rabani da mutuncina?why ya Omar why!?innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah kasa mafarki nake ba gaske ba.......'kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta gaza ƙarasa maganar,nan fa tashiga shararar kwalla,abun ba ƙaramin ciwo yayi mata ba,bata ta6a tunanin haka daga wurin shi ba,wannan zoben nashi ne,shi ya tabbatar mata da cewa Ya omar ɗinsu ne yayi yunƙurin yi mata wannan aika-aikan,amma meyasa!?
tsagaitawa tayi da kukan tashiga girgiza kanta tana cewa"A'a ya Omar ɗina bazai ta6a yi mun haka ba,na yarda dashi sosai,nasan cewa bada son ranshi yayi mun hakan ba,Ya Omar bazai ta6a cutar da hosanar shi ba,ina yi mashi kyakkyawan zato kuma bazan ta6a tona mashi asiri ba,bazan bari kowa yaga zoben shi ba ko jahad bazan nuna mawa ba,saboda nasan ba dole ta fahimce shi ba,kamar yarda ni na fahimce shi,"ƙarasa maganar tayi tare da ƙankame zoben asaman ƙirjinta ta ɗan runtse idanunta hawayen naci gaba da sauka asaman fuskarta,
Dama ance so hana ganin laifi,hosana ta makance akan son ya Omar ɗinta,kuma ta yarda dashi 100%,
tana cikin wannan yanayin taji motsin mutum cikin sauri takai hannu tare da janyo bargo ta ƙudundune acikin shi,6oye zoben tayi acikin aljihun rigar jikinta,sannan ta sanya tafin hannayenta tana goge hawayen fuskarta,
Jahad ce ta shigo hannunta ɗauke da kakkauran tea mai zafi sai faman tiriri yake yi,ƙarasawa tayi tare da samun wuri daga gefen gadon kusa da hosana ta zauna, a hankali tace"ƴar uwata rabin raina ga tea na kawo maki, ki tashi kisha shi da zafi zafinshi karya huce nasan zaki ji dadin shi,'cikin lallami take yi mata magana saboda tasan a halin da take na fargaba tana buƙatar kalamai masu daɗi da zasu sanyata farin ciki,
lamo hosana tayi batare da ta motsa ba abunda yasa tayi hakan saboda tanason ta daidaita natsuwarta don kar jahad ta gano wani abu,
jin shiru yasa jahad,kai hannunta na dama ta ɗan bubbugi kafaɗarta tace"tashi mana hosana ko kinyi bacci ne"?ta tambaya tana kallonta naɗe cikin bargo,
Har jahad ta yunƙura zata tashi,hosana ta soma motsi alamar zata farka,komawa jahad tayi ta zauna tana jiranta ta tashin,a hankali ta yaye bargon tare da tashi daga zaune tana mutsistsika idanunta alamar yanzu ta tashi daga guntun baccin daya ɗauke ta,wartsakewa tayi ta buɗe ido tana kallon Jahad,
Murmushi jahad ta sakar mata tare da cewa"babyn Omar ya jikin naki?nasan har yanxu kina fargaba akan abunda ya faru dake jiya,dan Allah hosana kada kisa damuwa kinji?insha Allah koma wanene asirinshi zai tonu,zamu faɗama ya Omar zai gano koma wane tsinan.........'a firgice Hosana ta toshe ma Jahad baki da tafin hannunta tana cewa"Jahad dan Allah kidaina maganar nan,kina tunamun abunda ya faru jiya,ni banason ma ana maganar nan,gabana faɗuwa yake yi,'ta ƙarasa maganar a sanyaye tare da zame hannunta daga bakin jahad,
Ajiyar zuciya jahad ta sauke tare da cewa"Shikenan mubar maganar,yanzu dae ga tea ɗin kisha,kuma sister camilla tace na tambayeki in akwai abunda kike buƙata a girka maki kici,"
Hannu hosana tasa ta kar6i cup ɗin da jahad ta miƙo mata sannan tace"Bana buƙatar cin komai yanzu,ni dai akira mun ya Omar yazo inason ganin shi,'
Murmushi jahad tayi tare da cewa"kada ki damu babyn Omar,nasan zaizo ne ina ta trying numbarshi amma taƙi shiga still switch off,amma nasan zuwa anjima zai kunna wayar ne,"
Jin haka yasa jikin hosana yin sanyi,don tasan dalilin dayasa Omar ya kashe wayarshi,bata ji daɗi ba saboda tasan zai sanya damuwa sosai aranshi,tausayinshi ne taji ya kama ta,babban abunda take fargaba shine kada ya hana kanshi zuwa wurinsu,
tashi jahad tayi tare da fuce wa daga bedroom din ta koma kitchen,yayin da ya rage hosana ce kaɗai saman gadon tana kur6ar tea ɗin a hankali,duk jikinta yayi sanyi,
After some days
Abu kamar wasa yau almost 1 week kenan ba Omar ba alamar shi,hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,kwana huɗu ba Omar ko layin shi suka kira kullum a switch off suke samun shi,hakan ba ƙaramin tayar masu da hankali yayi ba,sun shiga damuwa sosai na rashin zuwan shi,musamman Hosana duk tabi ta takure kanta,ko abincin kirki bata iya ci,ko isasshen bacci bata samu,kullum cikin kuka take na rashin ganin ya Omar ɗinta,duk bayan ƴan mintina sai taje ta ɗauki telephone ta danna mashi kira,da zarar taji wayar akashe sai ta fashe da kuka,daƙyar jahad ke samu ta lallashe ta,akwai lokacin da jahad ta farka tsakar dare ta samu Hosana saman darduma tana yin sallar dare abunda bata ta6a ganin hosana tayi ba,kuma duk don saboda ya Omar ta tashi yin sallar daren,tana roƙon Allah yasa Ya omar yazo karya rabu dasu,batasan yaya rayuwa zata kasance mata ba,batare da ya Omar ɗinta ba,tana yin addu'ar tana matse kwalla,a wannan lokacin ba ƙaramin tausayi taba Jahad ba,
A washe garin ranar jahad ta yanke shawarar zuwa tasamu Osman ta sanar dashi game da halin da suke ciki na damuwa da rashin ganin ya Omar ɗinsu,ko da Jahad taje ta samu Osman ta faɗa mashi,yayi mata alkwarin cewa zai bincika masu shi,
Bayan tafiyar jahad,Osman ya nemi major a waya ya sanar mashi abunda ke faruwa,na halin da yaran suke ciki akan rashin ganin Marshal da basuyi ba na tsawon kwanaki ,jiki a sanyaye Major yace mashi yaci gaba da kwantar masu da hankali,insha Allah zaizo ne abubuwane sukayi mashi yawa.
Hankalin Omar ba ƙaramin tashi yayi ba,lokacin da major ya sanar dashi halin da su jahad da hosana suke ciki,tsananin tausayinsu ne ya kamashi,musamman hosana da aka sanar dashi cewa ko isasshen bacci bata samu saboda damuwa akan shi,tamkar ya zubar masu da hawaye haka yaji,duk yarda yaso ya daure ya hana kanshi fargabar tunkararsu amma ya gaza yin hakan,ya nisanta kanshi dasu ne, saboda gudun karya ƙara jefa kanshi cikin matsala,shi kanshi daurewa kawai yake yi amma ba ƙaramin cutuwa yake yi ba,yana tsananin son ganinsu yanaso yaga wane hali suke ciki, amma ba yarda ya iya.
A 6angaren Sehrish kuwa ba ƙaramin jiki taji ba,a washe garin ranar da Sgr ya sanyata tsallen kwaɗi,ko school bata je ba,saboda jinyar jikinta da ta tsaya yi,ƙafafunta sunyi suntum,tun da ta lafe saman gadon ko motsi bata son yi,ba ƙaramin jiki taji ba sai da azmee ta taimaka wurin gasa mata ƙafafun da ruwan zafi,tayi mata tausa sannan taji sauƙin jikinta sosai har ta samu ta warware taci gaba da ƙiriniyarta kamar yarda ta saba.
Hayamm taji haushi sosai kamar ta binne kanta saboda tsabar baƙin ciki,tun washe garin ranar da azmee taje gyara part din Sgr,ta fito hannunta ɗauke da tray ɗin kayan abincin da baici ba,jiki na rawa hayaam ta ƙarasa tare da kar6ar tray ɗin tace tabar mata kayan takai kitchen,
tana shiga kitchen dasu ta shiga buɗe kayan don taga idan sgr yaci abincin,sai dae abun takaici bai ta6a komai na abincin ba,yarda sehrish takai mashi shi haka aka dawo dasu bai ta6a komai ba,lemu kawai yasha,kuma ta manta bata zuba gashin acikin abun shan nashi ba,taji takaicin hakan kamar ta aza hannu abisa kanta tayi ihu saboda haushi,amma taci alwashin cewa saita shirya mata wani tuggun tunda ta tsallake wannan.
A 6angaren su Twins kuwa sai dae muce Alhamdulillah,Yara sun zama mazajan gaske,rayuwarsu ta gyaru sosai,yanzu basa wasa wurin yin ibadarsu suna neman tsarin ubangiji,don wani lokacin atare suke tashi suyi ƙiyamun laili da sauran nafilfili,sannan basa komawa bacci bayan sallar asuba,zama suke yi suyi ta karatun alkur'ani mai girma har gari ya waye, Allah sarki rayuwa kenan ayayin da matsalar su jahan ta ƙare, shi kuma junaid wani mummunan al'amari ya soma faruwa dashi batare da sanin kowa ba,shi kaɗae yasan halin da yake ciki,kuma yaƙi sanar ma kowa saboda baison ya tashi hankalin Abbanshi da kuma na ƴan uwanshi,baka ta6a gane halin da yake ciki saboda babu abunda ya canza na daga ƙiriniyarshi, da kuma wannan kyakkyawan murmushin nashi,abun yana damunshi sosai, wannan ɗigon jinin dake fitowa ta ƙopar hancinshi, kullum ne saiya tashi tsakar dare batare da sanin Abbansu ba, ya shiga cikin toilet yana wanke hancinshi, abun sai ƙara gaba yake yi, ga yanayin da yake tsintar kanshi aciki,yanayi mara daɗi wata irin kasala da kuma yawan faɗuwar gaba,da kuma razanar da yake yawan yi,ko kiran sunan shi kayi da karfi sai ya firgita,ba kowa ya lura da hakan ba,tabbas rayuwar Junaid tana cikin hatsari sosai,a cikin jikinshi ciwon ke cin shi batare da sanin kowa ba, hmmmmmmm.
A 6angaren Commandern ƴan iska kuwa wato haroon komai ya gama hargitse masa,kamar wani zautacce haka ya koma wurin neman jakar kuɗin shi,sam ya rasa samun kwanciyar hankali gaba daya plan ɗin da ya shirya na barin nigeria yana shirin rugujewa saboda rashin kuɗin nan,a ƙarshe ya yanke shawarar turo ɗayan videon nan nasu jahan don ya sake yi masu barazana dashi,su ƙara mashi wasu kuɗin da zai samu yabar ƙasar tunkan asirinshi ya tonu,
Wannan kenan👌
Gaba daya an canzama gidan kamanni sai faman gyare-gyare akeyi mashi ta ko'ina,kwararrun ma'aikata aka ɗauko wurin tsara decoration ɗin da za'ayi ma gidan, yarda kasan za'ayi wani shagalin biki haka suka ƙawata gidan,duk wannan shirye shiryen da suke yi na tarbar manyan baƙinsu ne da zasu zo acikin kwanakin nan,a yau dae mutum biyu ne zasu fara zuwa,daga ciki akwai uncle Abusufyan da zaizo daga ƙasar turkey,sai kuma hajiya azeema da zata zo daga lagos,
gaba ɗaya tunanin matasan gidan Abbansu yasa aƙawata gidanne kawai saboda zuwan su Ammin sa ne,abunda basu sani ba shi da wata manufa yasa a gyara gidan, Tofah,
Wuraren ƙarfe 7:00am dai dai sehrish ta kammala shirinta na zuwa school,tana tsaye agaban mirror sai faman feshe jikinta takeyi da turare,bayan ta kammala ta koma wurin gadonta tare da kai hannu ta ɗauki hijab ɗinta data ajiye anan saman gadon ta zura ajikinta,
bata ɗauki school bag ɗinta ba saboda tana so tafara zuwa kitchen wurin su Aunty azmee ta kar6a ma babban yaya breakfast ɗinshi takai mashi,
fitowa tayi daga cikin bedroom ɗin tana tafiya tana ƴan kalle kalle kamar zatayi tuntu6e,decoration ɗin da akayima gidan ba ƙaramin kyau yayi mata ba,don ba ƙaramin ɗaukar ido yake yi ba,
Ƙarasawa kitchen ɗin tayi tare da tsayawa daga bakin kopar tayi masu sallama,Azmee ce kaɗae acikin kitchen ɗin,jin muryar sehrish yasa ta juyowa fuskarta ɗauke da murmushi tace"Ƴan makaranta har an kammala kimtsawa ne?
murmushi sehrish tayi tare da cewa"ina kwana Aunty azmee,ya aiki"? Azmee tace"Alhamdulillah,shigo daga ciki mana in haɗa maki breakfast ɗinki ki ci kafin ki tafi,'
"A'a Aunty azmee bana jin yunwa,idan naje school zanci acan,' har ta ɗanyi shuru, cike da son jin gulma ta kuma cewa"Aunty azmee wai wanene zaizo zo yau"?
Murmushi azmee tayi tare da cewa"Masu kama dake ne zasu zo yau,'
"Masu kama dani kuma Aunty azmee"?ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki,
azmee tace"kwarai kuwa kuna kama da azeema kanwar Abbansu junaid dake lagos,amman kinfi kama sosai da Uncle ɗinsu, Abusufyan dake zaune a ƙasar turkey shima zaizo yau,'
wani irin farin cikine taji ya lullu6eta,saboda ɗokin ganin wannan uncle ɗin nasu da take yawan jin suna ambatar sunanshi,a ƙagare take da ta sanya shi acikin idonta,
"Aunty azmee dagaske muna kama dashi?ko wasa kike yi mun"?
Azmee tace"dagaske nake mana,ban ta6a faɗa maki ba,amma maganar gaskiya kamanninki dashi har sun 6aci,kullum na kalli fuskarki sai ya faɗo mun araina,saboda komai na fuskarki irin nashi ne,tun daga kan idanuwanki,hancinki,da kuma bakinki duk irin nashi ne,ke hatta launin fatarki chocolate colour irin nashi ne,da ace Abusufyan ya ta6a yin aure,zan iya rantsewa cewa ke ƴarsa ce'
tunda azmee ta soma magana sehrish ta saki baki tana sauraronta,
"abun ya jima yana ɗaure mun kai,shiru kawai nayi,amma kamanceceniyarki da wasu daga cikin matasan gidan nan har taso tayi yawa,"
Cika da mamaki Sehrish tace"Aunty azmee wai dagaske"?
murmushi azmee tayi kafin taci gaba da cewa"na ta6a yi maki wasa ne irin haka"?
Girgiza kai sehrish tayi alamar a'a,
Cigaba da magana azmee tayi"kina yanayi da Abbansu junaid sosai kuma kina kama da Auntynsu Azeema,hatta junaid akwai kamanceceniya atsakaninku abunda yasa baza a gane ba saboda hasken fatarshi,amma kina kama da shi,bayan shi kuma sai Marshal Omar,shima akwai kamanninshi atattare dake,da kuma kanal yousouf,na jima da lura da hakan,"
tunda sehrish taji wannan jawabin na azmee take ta faman sakin murmushi,daɗi kamar ya kashe ta saboda ance tana kama da uncle Abusufyan ɗinsu,
"Aunty azmee naƙosa na ganshi,Allah yasa kafin nadawo daga school ya ƙaraso,da kaina zanje inyi mashi sannu da zuwa sannan in kai mashi abun sha,"
Dariya azmee tayi tana cewa"Allah yasa toh,amma kin manta baki ce insha Allah ba,"
cikin sauri sehrish tace"Insha Allah Aunty azmee,"
Suna cikin firar nan tasu,sai ga junaid ya faɗo cikin kitchen ɗin ko sallama babu a firgice suka ɗago suna kallonshi,
daga shi sai gajeran wando fari ajikinshi,sai faman washe baki yake yi,kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna,
"Junaid anya lafiyarka kuwa?kaine yau kake yawo da short ajikin ka?ko ka manta akwai sehrish dani acikin gidan"? Acewar Azmee,
Murmushi ya saki tare da nuna sehrish da hannunshi yace"Wurinta nazo,inason magana dake reesh,in ba damuwa ki biyo ni muje bedroom ɗina,'
Kallon azmee tayi don taji me zata ce,
"kije mana,amma kada ki jima,"
Amsa mata tayi da toh sannan tabi bayan junaid suka fuce atare izuwa bedroom ɗinshi dake a upstairs,
atare suka shiga cikin ɗakin nashi,har wurin gadonshi yakaita sannan ya tsaya tare da nuna mata shaddojin daya jera asaman gadon nashi yace"Pls reeshi ki za6amun ɗaya mai kyau,inaso yau nayi shigar mutunci don na burge uncle Abusufyan yasan cewa na girma yanzu,'ashagwa6e junaid ya ƙarasa maganar,
Sehrish kuwa zuba ma tsadaddun shaddojin ido tayi tana kallonsu,kala biyar ne sun sha uban aiki ajikinsu,hannu tasa tana ɗaɗɗaga kayan tace"junaid ae