Showing 315001 words to 318000 words out of 432432 words

Chapter 106 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

fi ƙarfin ta ko"?
  Yayi maganar ranshi a 6ace,Sgr kuwa ko ajikinshi,yana daga tsaye agaban dressing mirror ɗinshi ya juya ma Abbansu baya,har lokacin bai canza kayan jikinshi ba,babu wanda baizo yayi mashi magana ba akan ya amince da buƙatar mahaifinsu amma yaƙi yarda,hatta Ishaq da Abbas sunyi sunyi har sun gaji sun ƙyale shi,haka Marshal Omar sunyi barambaram dashi,saboda ya 6ata masu rai,
  "Zan tafi na bar maka ɗakin ka,Amma inaso na ƙara tunasar dakai cewa Abusufyan ya baka tsawon wata ɗaya kacal akan ka canza ra'ayinka game da auren yarjejeniyar nan,Zaka iya soke shi in har kana so acikin ƴan kwanakin nan,Amma idan har ka bari wata ɗaya ya wuce baka canza ra'ayin ka ba,duk abunda ya biyo baya kada kayi kuka da kowa ka kuka da kanka!kuma babu ruwana Na zame hannu na aciki,
  A fusace Sgr ya juyo tare da kallon Abban nasu yace"bazan ta6a canza ra'ayi na ba akan hakan!Idan ma yana tunanin hakan to ya daina!Bana buƙatar wani time nayin tunani!wata uku na cika zan sallame ta ne!
  Abba na ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,ta wutsiyar idonshi ya hango mutun atsaye,a ɗan firgice ya juya don yaga wanene,
  Sehrish ce atsaye tana kallonsu,gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa,domin kuwa taji duk abunda suka ce kaf acikin kunnanta,Jikinta har kerma yakeyi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa akan fuskarta,
  Jin shessheƙar kukanta yasa Sgr Juyawa tare dakai idanunshi wurin da take tsaye a ƙopar ɗakin nashi,tun daga ƙasa har sama yabita da kallo,
  A hankali Abbansu ya ambaci sunanta"Sehrish!"
  Juyawa tayi da gudun gaske tabar ƙopar ɗakin nashi,gaba ɗaya tabar part ɗin nashi,saukkowa tayi downstairs,Su fawan ne tsaitsaye acikin babban falon,koda suka ji shessheƙar kukanta sae hankalinsu ya koma akanta,kowa ya shiga tambayarta lafiya,
  Bata tsaya sauraronsu ba,da gudu ta wuce bedroom ɗinsu,tana shiga ciki ta samu junaid da jahad azaune gefen gadonsu suna shan soyayya,jin shigowarta yasa suka mike tsaye hankali atashe suka shiga tambayarta Lafiya,
  Bata basu amsa ba,kai tsaye ta nufi toilet ta buɗe ƙopar ta shige ciki,da ƙarfi ta datse ƙopar,sannan ta tsugunna ƙasa tana kuka tamkar ranta zai fita,

Gaba ɗaya Jahad da Junaid suka nufi ƙopar,Suna kwankwasawa suna kiran sunanta"Sehrish!Sehrish!dan Allah Rishi ki buɗe mana kopa!
  Turo kopar ɗakin nasu akayi,Abusufyan ne tare da hajiya azeema suka shigo ciki hankalinsu atashe,basu jima da shigowa ba,sai ga Abbansu junaid,dama tunda yaga ta watsa aguje tana kuka ya biyo bayanta,
  A bakin kopar shiga toilet ɗin suka tsaitsaya cirko cirko
   "Dama nasan abunda zai biyo baya kenan!"acewar hajiya azeema,
  Abusufyan yace"Ni bansan waya faɗa mata ba,Naso ace ni na fara sanar da ita,"
  Fuskar Abba a yamutse yace"wlh bansan da ita ba!Yanzun nan fa naganta a ɗakin Rafayet,muna cikin magana dashi akan zancen auren nasu,kawai naji shessheƙar kukanta,ashe duk taji abunda muka ce,"
   Jikinsu ba ƙaramin sanyi yayi ba,musamman Abusufyan har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata,
   Ƙoƙarin lallashinta suka shiga yi amma ina,Sehrish taƙi sauraron kowa kuka sosai takeyi kamar ranta zai fita,tana jin muryoyinsu a waje sai faman yi mata magiya sukeyi akan ta buɗe masu ƙopar,
   Junaid duk yabi ya ruɗe sam baisan cewa abun zai ta6a zuciyarta ba har haka,Ita kanta jahad ba ƙaramin tausayin Sehrish taji ba,kowa sai da yasha jinin jikinshi,babban abunda suke ji ma tsoro kada ta illata kanta,

Bakomai ne ya ƙona mata rai ba,Fa ce abunda kunnuwanta suka jiyo mata,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,komai ya fita aranta,tabbas tana son Sgr sosai har cikin ranta,kuma babu abunda ya canza acikin zuciyarta,tayi farin ciki mara misaltuwa na kasancewarta matarshi,wannan babbar kyauta ce agareta,sae dai kash bataso ya aureta batare da yana sonta ba!Sam bata ta6a ra'ayin hakan ba,tafi son ta auri wanda take so kuma yake sonta,bawai wanda takeso ba,Shi baya sonta,bugu da ƙari kuma ya aureta ne don taci gaba da aiki a ƙarkashinshi na wata uku kacal!
    "Idan ba damuwa inaso ku ɗan bani wuri in shawo kanta,"hajiya azeema ce tayi maganar,
   Abusufyan yace"kina ganin zaki iya shawo kanta kuwa?
  "Ku je kawai,Ni nasan yadda zanyi da ita,ku ɗan bamu wuri,"
  Kama hanya sukayi gaba ɗayansu hadasu jahad suka bata wuri,kamar yadda ta bukaci su fita daga dakin,
  Zuƙunnawa hajiya azeema tayi abakin ƙopar toilet ɗin,Saboda ranta ya bata cewar sehrish tana zuƙunne a ƙasa,ta gane hakan ne ta hanyar sautin kukan nata,
  Cikin lallami ta ambaci sunanta"Sehrish,"
  Cikin shessheƙar kuka tace"Na'am,"
  "Inason magana dake!dan Allah ki bani haɗin kai,kada ki bani kunya,inaso kizo ki buɗe mun ƙopar nan!,"
   Miƙewa sehrish tayi,jikinta sai faman kerma yake yi,daƙyar ta iya sanya hannu ta buɗe kopar toilet ɗin,
  Sauke ajiyar zuciya hajiya azeema tayi tare da mikewa tsaye tana kallonta,fuskar nan tayi suntum da ita,gaja gaja da hawaye,idanun sun kumbura,janbakin da ta shafa duk ya 6ata mata fuskarta,mascara ɗin da aka shafa mata asaman eye lashes ɗinta,duk ya jike sharkaf da hawayenta ya 6ata fuskar da baƙin,kayan jikinta ne kawai basu 6aci ba,
  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita daga gefen gadon nasu,itama ta zauna suna fuskantar juna,
"Haba amaryar babban yaya,kuka bana ki bane,Farin ciki ya kamata na gani akan fuskarki,"cike da zolaya hajiya azeema tayi mata maganar hada jan kumatunta,
Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan cikin shesshekar kuka tace"Am...amma..Aunty azeema..meyasa za'ayi mun haka?saboda me za'a ɗaura mun aure tare da babban yayanmu batare da an sanar dani ba?Nasan cewa sun isa dani!Amma yakamata ayi mun adalci,Auren wata uku fa?kawai saboda buƙatar kanshi"?
  Ruƙo hannunta hajiya azeema tayi cikin sanyin murya tace"Inaso na tambayeki wani abu,amsa ɗaya kawai nakeso ki bani,kuma ki faɗamun gaskiya,'
Dakatawa sehrish tayi da yin kukan tare da mayar da hankalinta kan Aunty azeema tana sauraronta,
   "Inaso ki faɗamun gaskiya,Shin kina son Sgr ko bakya son shi ne"?
  Shiru sehrish tayi yayin da idanunta ke akan yatsun hannunta da ta harɗesu wuri guda tana murzasu,
  "Kinyi shiru baki ban amsa ba"?
ƙasa kasa tayi da muryarta tare da cewa"bazan 6oye maki ba Aunty azeema,ina son Yaya rafayet sosai,fiye da yadda nake son kaina,"
   Murmushi hajiya azeema ta ɗan yi,dama saida ranta ya bata cewar tana sonshi,
  "In har dagaske kina son shi bai kamata kiyi kuka ba don an ɗaura maki aure dashi,"
  "Aunty azeema ba baƙin ciki nake yi ba,bakomai ne ya 6ata mun rai ba fa ce irin auren da akayi mun dashi,Saboda kawai nayi  aiki a ƙarƙashinshi,na tsawon wata uku?meyasa za'ayi mun haka?idan aka barni ma zan iya yin aiki a ƙarkashinshi ba sai ansa ya aure ni ba,ba bisa son ranshi ba,tunda ba sona yake yi ba,ni kaɗaice nake ɗawainiya da son shi tun kafin nasan wanene shi,Wahala kawai zansha a hannunshi,Ni ban ta6a son na aureshi ba batare da yana Sona ba,"
  Jinjina kai hajiya azeema tayi tare da cewa"hakane kin faɗi gaskiya,ba'ayi maki adalci ba,Ni kaina bansan dalilin yin auren ba sai daga baya nake ji a wurin Abbanku,Amma kiyi haƙuri dan Allah kada hakan yasa ki bijire ma iyayenki,kiyi masu biyayya in sha Allah zaki ci ribar yin hakan,"
  Batare da musu ba Sehrish tace'Shikenan,in sha Allah zanyi masu biyayya,kamar yadda kika ce,kuma koda baki faɗamun haka ba,Ni bazan yi kuskuren bijire masu ba,"
  Murmushi hajiya azeema tayi tare da sanya hannunta ta shafa gefen fuskar sehrish,
"Good girl,Naji daɗi sosai da kika amince zakiyi masu biyayya,Ni kuma nayi maki alƙwarin cewa atare zamu yaƙi sgr,acikin waɗannan watannin guda uku kacal,Zamu canza mashi ra'ayinshi,don ya gane kuskurenshi,kinsan ance DUK ƘYAN TAKALMI ƘAFA CE KE TAKASHI,So nake ki take mun wannan tsadaddan takalmin da ƙafafun nan naki ya taku sosae,"
Sae lokacin Sehrish ta fashe da dariya,har hakoranta suka bayyana,maganar da hajiya azeema tayi mata ta ƙarshen nan ba ƙaramin dariya ta bata ba,

Cigaba da magana hajiya azeema tayi"domin aikin mu yayi kyau muna buƙatar mu shirya plan A da kuma plan b zuwa c,zamu fara jaraba plan A,idan har akaci nasara akan shi kinga basai mun buƙaci plan B ba,Abunda nakeso dake yanzu shine muna buƙatar satar amsa,kuma ke kaɗae ce zaki iya samo mana wannan satar amsar da muke buƙata a wurinshi,
A tsorace sehrish tace"Ni kuma!"hajiya azeema tace"kwarai kuwa,ba wani abun tashin hankali bane,just akwai bukatar musan me yake so da kuma abunda baya so don mu kiyayesu,Ni dae a iya sanina Sgr mutunne maison abi umarninshi ba'ayi mashi musu,yafi so ayi mashi biyayya abishi sau da ƙafa,sannan mutunne shi mai tsaftar gaske,ya tsani ƙazanta,bayan haka kuma Yana son abinci mai daɗi,shiyasa yake cin girkin azmee saboda tana da tsafta kuma ta iya girki,yakama ki koyi kalar girke girkenta,"
"Ae na fara koyo a wurinta,Kuma na iya waɗansu,amma zanyi mata magana akan ta ƙara koyamun wanda ban iyaba,"
"Yawwa haka nakeson ji,ki dage sosai,Nidae ta 6angarena zan baki gudummuwa sosai,""
Sun jima suna fira atsakinsu tamkar ba uwa da ƴa ba,har sae da aka fara kiran sallar Magrib,sannan aunty azeema tayi mata sallama,
Hankalin sehrish ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ta samu ƙwarin guiwa sosai a wurin Hajiya azeema kuma taci alwashin zata ɗaura ɗamarar zama da sgr,har na tsawon wata ukun

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 12 na dare,tana a tsaye cikin ɗakinsu,sae faman zagaye zagaye takeyi,tana jiran dawowar Sgr,tun bayan sallar isha'e bai dawo cikin gidan ba,har lokacin wedding gown ɗince a jikinta,ta gyara kwalliyar fuskarta,sannan ta daure gashin kanta da ribbom,
Jahad da hosana sun jima da yin bacci ita kaɗae ta rage batayi bacci ba,zuciyarta cike take da damuwa,sam tagaza samun natsuwa babban abunda takeyi ma fargaba shine taya zata fara tunkarar SGR a matsayin Mijinta?shin zata iya jure zama dashi?tasan cewa dole ta fuskanci ƙalubale dayawa a wurinshi,
Tana cikin wannan zancen zucin taji shigowar motocinsu,ajiyar zuciya ta sauke tare da komawa gefen gadonsu ta zauna tana jiran su ƙarasa shigowa cikin gidan,
Almost 30 mins,sannan ta miƙe tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito waje,babu kowa kai tsaye ta nufi kitchen,batare da 6ata lokaci ba,ta shirya mashi dinner ɗinshi a saman ƙayataccen tray ta ruƙo shi da hannayenta,a hankali take tafiya saboda tsinin takalman dake a ƙafafunta,bata saba tafiya da irinshi ba,babu kowa a main palour ɗin hakan yasa ta wuce upstairs part ɗinsa,
Da sallama abakinta tashiga falon,babu kowa aciki sae dae kamshin turaren nan nashi,kama hanyar zuwa bedroom ɗinshi tayi,a bakin ƙopar ta tsaya tare da yin sallama"Assalamu alaikum"
"Who's there"abunda taji yace kenan,
daƙyar ta iya cewa"Ni ce"
"Okey,Come in"
A hankali ta zura ƙafarta cikin ɗakin nashi,samun shi tayin kwance asaman katafaren gadon nan nashi na mulki,ko takalman ƙafarshi bai cire ba,still shaddar ce ajikinshi,
Ƙarasa shiga ciki tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table,kamar wata mara gaskiya ta juya zata kama hanyar fita daga ɗakin muryarshi ta katse mata hanzarinta da cewa"Baki iya gaisuwa bane?"
dakatawa tayi tare da ɗan juyo ta saci kallon fuskarshi,A lumshe ta samu idanunshi tamkar maijin bacci,
Muryarta na rawa tace"Ina yini"
Ta6e la66ansa yayi tare da cewa'zonan""
Jiki asanyaye ta tunkareshi,da hannu ya nuna mata gaban gadon nashi,sannan yace"kneel down"
Tattare rigar jikinta tayi,tare da zubewa saman guiwowinta,
"Kukan me kikeyi ɗazu?ko don saboda kinji abunda muke tattauna da Abba ne?"
Girgixa kai tayi'a'a ba haka bane,""
"Okey,"
Shiru ya ɗanyi na wani lokacin kafin yaci gaba da magana"Na aureki ne saboda inaso ki cigaba da aiki a ƙarƙashin ikona!Idan har bakya ra'ayin hakan zan iya sakin ki,"Ya ɗan dakata da yin maganar yana jiran jin 💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*




_❤Littafin abban sojoji 300 ne,gamai bukata zaiyi mun magana kaitsaye ta layina 08103884440❤_


Not edited,


"zan cigaba da aiki a ƙarƙashin ka,"ta ƙarasa maganar,tana faman sauke ajiyar zuciya,
  "Good,"ya furta hakan tare da miƙe wa daga zaune,Ya jingina bayanshi a jikin pillow,har time ɗin idanuwanshi na a lumshe bai buɗesu ba,
   "Now you are under my control, you must follow my rules,"dakatawa yayi da yin maganar,tare da kai hannu ya zaro hanky daga front pocket na rigar shaddar jikinshi,
  Miƙa mata yayi tare da cewa"Oya,goge wannan fentin dake a saman lips ɗinki,from now bana buƙatar naga make up a face ɗinki,in dai zakiyi aiki a part ɗina,"
   Hannu tasa ta kar6i hanky ɗin,tare da kaishi saman lips ɗinta,a hankali ta shiga goge jan bakin da tasha fa,
   Cigaba da magana yayi"i won't restrict ur life,You still ave ur right,don na aure ki ba hakan yana nufin zaki ɗauki kanki as a married women ba,No just normally zakiyi rayuwarki,Kuma zaki iya kula duk wanda kikeso koda namiji ne i don't care about that,'
  Zaro ido waje sehrish tayi tana kallon fuskarshi,cike da mamakin jin abunda yace mata,Lamarin sgr ya fara bata tsoro,sae ka ce ba musulmi ba!da aurenta kuma ya amince mata ta kula duk wanda takeso?Anya bai fara shaye shaye ba?kodai yana da Iska ne ajikinshi?Abun yayi confusing ɗinta sosai,
  "Idan ma kina da tsafta ki ƙara akan wadda kike da ita,part ɗina ya kasance kullum a tsaftace ya ke,"
  Kasa kunne sehrish tayi tana sauraron shi,guiwowinta har sun fara yi mata raɗaɗi,magana yake yi tamkar baisan motsa la66ansa,balle har yayi sauri ya kammala ko ta samu ta miƙe,
   "Banason wani ya ƙara girkamin abincin da zanci,da hannunki zaki girka mun,sannan ba kowani kalar abinci nake ci ba,Ki nemi bayani a wurin Asmee,"
  Dakatawa ya ɗanyi da maganar,hannu ya miƙa tare da ɗauko wayarshi dake ajiye saman side drawer ɗinshi,ya shiga daddanata,
   Ganin haka yasa sehrish tayi sauri Zama dirshin a ƙasan,kota rage raɗaɗin da guiwarta keyi mata,
     "Where's ur phone"?yayi tambayar tare da ɗan dakawata,da dannar wayar da yake yi,
   Da sauri tace"na barta a bedroom ɗinmu,"
  "Okey,"ya ambaci hakan tare da kai hannu ya buɗe drawer chest,memo ya ɗauko tare da biro,Ya buɗe empty page,a natse ya shiga yin rubutu asaman paper ɗin,.
  Zugudum sehrish tayi,aranta tana tunanin ko taya zata iya gane hand writting ɗinshi?kwanakin baya,daya ta6a yi mata rubutu bata iya gane komai ya rubuta ba,har haroon ya yaudareta,
   Bayan ya kammala rubutun,Yayi tearing paper ɗin tare da miƙa mata,hannu tasa ta kar6a,
   "Phone number ɗina ne,Cos at anytime zan iya kiranki,even in the midnight indai ina buƙatar wani abu"
   Amsa mashi tayi da toh,
"Your work will start from tomorrow!U can leave now,"
  Jiki asanyaye sehrish ta miƙe dakyar take ɗangyasa ƙafarta tana tafiya,har sae da takai bakin ƙopar bedroom ɗin nashi sannan ta ɗan dakata da yin tafiyar,juyowa tayi tare da aza idonta akanshi,a lokacin harya sauko daga saman gadon,yana ƙokarin cire kayan jikinshi,da alama wanka zaiyi,
   Gyaɗa kai kawai tayi tare da sanya ƙafa ta fito daga bedroom ɗin nashi,
  Bata tashi jin hawaye ba,sae da ta hau saman staircase din,tana taka benen a hankali,bakomai yafi ƙona mata rai ba fa ce abunda ya ce mata,Zata iya kula duk wanda takeso koda Namiji ne shi bai damu ba,tsabar takaici kamar ta haɗiyi zuciyarta haka take ji,taci alwashin saita koya mashi hankali,kuma zata jajurce ne wurin ganin ta gudanar da aikinta kamar yadda yakeso,daga baya kuma ta shiga tunanin komai yasa ya hanata shiga part ɗinshi da makeup?mai jan bakinta yayi mashi ne da zaisa ta goge?da alama so yake ya dinga ganinta kamar gardi,shiyasa yayi mata hakan,

Ƙarasa saukowa tayi daga saman stairs din,sannan ta tsaya tare da juyawa tana kallon upstairs ɗin"

In sha Allah,Wata rana Sai kayi kneel down agabana,Kamar yadda ka saba sanya ni in duka agabanka,koda baka zubar da hawayenka ba,zakayi kukan zuciya ne wanda yafi ciwo,Wannan alwashine na ɗaukarma kaina,In har ban tabbatar da faruwar hakan ba,To ni ba jinin Abusufyan bace da abu!!kuma ban cika mace ba,"
  Tana magana hawaye na shararowa akan fuskarta,ranta ya 6aci sosai

  *ATAƘAICE*

Acikin waɗannan ƴan kwanakin Sehrish ba ƙaramin jiki taji ba,domin kuwa sgr baiyi mata da sauƙi,Aiki takeyi tuƙuru,ba ƙaramin ƙoƙari take yi ba wurin ganin ta kiyaye duk wani abu da zai haɗa ta dashi,Aranar monday abusufyan ya mayar dasu school,da kanshi yakaisu acikin motarshi,basu samu matsala ba,sae dai an wuce su abubuwa da dama,Domin kuwa suna dab da fara'a Exams,abubuwa duk sun haɗe mata,ko karatu takeyi hankalinta na akan agogo,don kada ta shiga lokacin aikinta batare da ta sani ba,tun da sanyin safiya take shiga part dinshi tunkafin ma ya tashi daga bacci,ta gyara mashi toilet ɗinshi da falonshi,bayan ya tashi daga bacci ya shiga wanka,ta zauna ta gyara bedroom ɗin nashi,Sannan ta shiga kitchen ta haɗa mashi breakfast ɗinshi,Mafi yawancin lokutta a makare take zuwa makaranta,Saboda aikin sgr,Sae yaga damar sallamarta tukunna,abun ba ƙaramin 6ata ma abusufyan rai yakeyi ba,sae daga baya ya dinga danasanin ƙulla auren yarjejeniyar da sukayi,kullum Shi yake ja masu yin late a school,saboda dole sai sun jira sehrish ta kammala aiki a part din sgr,sannan su wuce school,baiwar Allah suna dawowa daga school da zarar tayi sallah,ko abinci bata ci,indai sgr na a cikin gidan sae ta fara zuwa ta gyara mashi part ɗinshi ta kuma kai mashi lunch ɗinshi,ta kuma yi serving ɗinshi abincinshi har sai ya mula yasha iska tukunna ya sallame ta,sannan fa take samun damar cin abincinta,Cikin lokaci ƙankani sehrish ta soma fita hayyacinta,Duk ta rame,kullum ne sai ta farka tsakar dare,ta zauna tayi ta kuka ba wanda ya sani,ita kaɗae tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta,gashi in tayi kuskuren yi mashi laifi,Hukunta ta yakeyi da tsallan kwaɗi,babu wanda bai fara jin tausayinta ba acikin gidan,shiru kawai sukeyi,bakomai ne ya jawo mata hakan ba fa ce rashin Hajiya azeema domin kuwa tun sati daya da yin auren,Tabar ƙasar izuwa dubai inda tasaba yin harkokin kasuwancinta,Amma tayi mata alƙawarin cewa bazata wuce One month ba zata dawo nigeria saboda ita kawai,Duk da haka kullum sai sunyi waya da ita,kuma tana ƙara ƙarfafa mata guiwa,kullum tana kara tunasar da ita akan cewa Karta kuskura ta karaya tun yanzu,Taci gaba da hakuri wata rana sai labari,mahaƙurci mawadaci ne,Sannan ta dage da addu'a kuma taci gaba da kyautata mashi,sgr bai tsaya a iya nan ba,idan dare yayi dama wannan ƙa'ida ne saita kai mashi coffee da kayan marmari around 12,toh yanzu takai ga,sae tana bacci wuraren 1:30 na dare ko biyu,ringing ɗin wayarshi ke tashinta daga bacci,daga ta ɗaga zaice mata Coffeee,yana furta hakan zai katse kiran,Dolenta ne ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login