Showing 423001 words to 426000 words out of 432432 words
Chapter 142 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
kunama zasu harbeka,anan ya gane cewa Bayan ta fito daga ɗakin Azmee ne ta shigo ɗakinshi,
Jinjina kanshi ya ɗan yi tare da cewa"Kina Zargin Azmee"?
Da sauri abu ta ɗaga mashi kai Alamar eh,
"Meyasa kike zarginta"?
"Saboda na santa,lokacin dana haifi su Sehrish,Itace Ƴar uwar sayyadi wadda tazo yi mun wankan jego,"
Tunkan takai ƙarshen maganar Sgr yace"Kenan ita ƴar uwar shi ce?",
Jinjina mashi kai tayi alamar eh,murmushin takaici Sgr ya saki,
Yana ƙoƙarin buɗe baki ya kuma tambayarta,Yaji Sehrish ta ruƙo hannunshi,da sauri yakai idonshi wurinta,
Da hannu ta dinga yi mashi Alamar ya miƙo mata jotter dinnan zata yi rubutu,
Hannu yasa ya dauki jotter ɗin tare da mika mata,dama biron na hannunta,
Zane yaga tana yi maimakon rubutu bayan ta kammala ta mika mashi jotter ɗin,
Hannu yasa ya kar6a tare da kallon abunda ta zana,Zobe ne ta zana,bai gane me take nufi ba,
"Zan iya ganin me ta rubuta?"abu ce tayi tambayar,
Miƙa mata jotter din
Yayi tasa hannu ta kar6a,koda abu taga zanen sai ta tuna da binciken da Sehrish ke yi dangane da Junaid,dayake ta bata labarin mutuwarshi,baiwar Allah tana so tayi mashi maganar Junaid ɗin ta kasa,Gashi ita kuma abun ta manta bata sanar dashi ba,
"Kin gane me take nufi"?
Jinjina kai abu tayi kafin ta ɗaura da bayani"Ta sanar dani komai daya faru dangane da mutuwar ƙaninku Junaid!"tunda sgr yaji ta ambaci junaid,hankalinshi gaba ɗaya ya koma kanta,
"Akwai wata rana da ta shiga ɗakin Azmee,zatayi sallah tana ƙoƙarin ɗauko hijabi acikin wardrobe ɗin ita azmeen,Sai ga zoben ƙaninku na Diamond ya faɗo daga cikin wardrobe ɗin,A binciken da sehrish tayi ta gano cewa tare da zoben nan Shi Yaron ya fita aranar da al'amarin ya faru kuma abun mamaki Zoben nan nashi baiyi komai ba!babu alamar wuta taci shi!"
Gaban Sgr ne ya faɗi rasss!ya ware idanuwanshi gaba ɗayansu,Abun ba ƙaramin girgiza shi Yayi ba,jikinshi har kerma yake yi,aruɗe yace"Taya akai Ita reesh ɗin tasan cewa tare da zoben Ya fita aranar'?
"Ta hanyar hotunan da suka ɗauka tare da Junaid a wayar Jahad,"
A hanzarce Sgr ya ɗauki wayarshi tare da dannawa Fawan kira,tana fara ringing ya ɗaga kiran,
"Fawan Am sorry na takura ka ko"?
On ther hand fawan yace"A'a babban Yaya,baka takuramin ba,"
"Idan kana kusa,pls inaso ka kira mun Jahad,ka sanar da ita cewa tazo mun tare da wayarta da kuma wayar Sehrish ina buƙatar ganinsu,"
"Toh babban Yaya"yana kai ƙarshen maganar ya ajiye wayar,zuciyarshi sai faman tafarfasa take yi,ita kanta daurewa kawai takeyi saboda maƙoshinta da ake ƙoƙarin shaƙewa ta dage sai ta faɗi gaskiya,koda kuwa Rai zaiyi halinsa,
Bayan wasu mintuna,Jahad ta faɗo ɗakin da sallama a bakinta,jikinta sanye da dogon hijabi,yayin da hannunta ke ruƙe da wayarta da kuma wayar sehrish,
Atare suka amsa mata sallamar,shiga cikin ɗakin tayi,gaba daya idanuwanta na akan Sehrish zaune tana ta murmushi,wani irin farin ciki ne ya lullu6e Jahad,
"Sehrish Ya jikin naki?na damu sosai akan halin da kika shiga"
"Jahad Rishi bazata iya magana ba a yanzu,ki tayata da addu'a,"acewar Oummansu,
Jikin Jahad ba ƙaramin sanyi yayi ba,miƙa mashi wayoyin tayi,Yasa hannu ya kar6a,danna wayar Jahad ya shiga yi,direct ya shiga Gallery ɗinta,
ɗagowa yayi tare da kallon Jahad"Ina hotunan da kukayi keda junaid aranar da kuka fita shan ice cream"?
"Suna acikin Gallery ɗina,daga ka shiga zaka gansu,"
"I did not see anything,ko kin gogesu ne"?
Gaban abu ne ya faɗi rass,Ita kanta Sehrish saida hankalinta ya tashi,
Jahad tace"Wlh ya rafayet ban gogesu ba suna acikin wayata,ko yanzu haka kafin nazo nan hotunan nake kallo"
Miƙa mata wayar yayi"nuna mun su,"
Bayan Jahad ta kar6i wayar,ta shiga neman pictures ɗin gaba ɗaya an goge mata su har vedios din daga cikin wayarta,
Tamkar zata fashe da kuka,"Ya rafayet wlh an goge munsu,bansan ya akai ba,"
"Wani ya amsa wayarki ne"?
Girgiza kai tayi"a'a,duk yinin yau wayata tana a hannu na,"
Mayar da idanuwanshi yayi kan abu"taya zan gane cewa,Junaid ya fita da zoben a hannunshi?ina yin amfani da shaida ne,kafin na yanke hukunci,"
Gaba ɗaya sunyi shiru,jikin kowa yayi la'asar musamman Sehrish domin kuwa harta fara zubar da kwalla,Azmee tayi masu tsiya suna ƙoƙarin fallasa ta ita kuma ta hana hakan,Shi kuma Sgr bai yarda da sihiri ba,koda zasu fada mashi cewa tana amfani da sihiri zaiyi wuya ya yarda,
Hannu Sehrish tasa tare da ta6o shi,juyawa Sgr yayi yana kallonta,Nuna mashi wayarta tayi da yatsanta alamar tana buƙatarta,
Miƙa mata wayar yayi,tasa hannu ta kar6a,
Tana kunna Power din wayar ta kawo haske,Sai ga text message Ya shigo ta layin AMRISH!
Yaushe rabon da ta samu layin Amrish harta manta,kullum in ta kira kashe take samun wayar,Yanzu haka da ta kar6i wayar Amrish take so Ta tura ma saƙo akan ta nemo mata number Ya mu'allim ɗinsu,
Shiga message ɗin tayi,ta ƙura ido tana kallon jagwalgwalon Rubutun da aka turo mata,Na haruffan da aka cakuɗesu,abun ya ɗaure mata kai!Nikaina Boss Ya ɗaure mun kai!
Duk maison Karanta Littafin Abban sojoji Yayi mun magana ta Layina amma whatsapp kawai banda kira 08103884440
💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠
*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*
Ta jima tana kallon haruffan nan bata fahimci me aka rubuta a saƙon ba,layin Amrish ta kira nan take aka sanar da ita cewa wayar a kashe take!sam bata so haka ba,ɗagowa tayi tare da kallon Sgr dake magana da Oummansu,
"Nagode sosai da bayanin da kika bani,duk da ban samu evidence ɗin da nake buƙata ba,but i wll try my best wurin ganin nayi investigation akanta,Zaku iya tafiya,"cikin girmamawa Yayi mata maganar,miƙewa Abu tayi"mun gode sosai Allah Ya taimaka,Ya baku sa'a..."sosai ta shiga yi masu Addu'a yana amsa mata da Ameen,"
Ruƙo hannun Jahad tayi atare suka fuce daga ɗakin,Sae da suka fito palour sannan Oumma tace"Jahad ya akai ba'a ga hotunan a wayarki ba?ko kin gogesu ne batare da kin sani ba"?
"Wlh Oumma ban gogesu ba,Nikaina abun ya ɗaure mun kai,"
Jinjina kai Abu tayi"bakomai akwai Allah,Amma Sehrish ɗin fa?Anan zata kwana?ba ɗakin shi bane"?dama abun ya tsaya mata aranta shiyasa ta tambayeta,
"Bedroom dinshi ne Oumma,kada ki damu mu tafi kawae,"
Bayan fitarsu ɗakin,Sgr ya mayar da hankalinshi kan Sehrish,har lokacin hannunta ruƙe da wayarta yayin da idanunta ke kallon Screen ɗin wayar,
"What are u looking at"jin muryarshi yasa ta ɗago da kyawawan idanuwanta tana kallon fuskarshi,
"If u need something pls lemme know"cike da kulawa yayi maganar,miƙewa tsaye yayi sai da ya fara ɗaukar Laptop ɗinshi sannan ya fita palour,Ji take kamar ta dakatar dashi,Saboda tsoran da take ji,
Yatsun hannunta na kerma Ta shiga danna wayar call log ta shiga ta kara dannawa Amrish kira,Nan take aka kara sanar da ita cewa Layin akashe yake,tamkar ta fasa ihu haka taji,runtse idanuwanta tayi tare da ɗan buɗesu kadan,yanke shawarar zuwa whatsapp group ɗinsu tayi Na Classmates ɗinta,Akwai kuma Na general wanda kowa ke aciki students ɗin da kuma malamansu ne aciki,A Group ɗin teachers kaɗaine zasu Iya tura saƙo banda students,tana fatan Allah yasa Ya Mu'allim yana acikin group ɗin,profile ta shiga daga ƙasa wurin da List ɗin Malaman dake group ɗin suke ta fara duba sunayensu tundaga kan Admins,Gasu nan sunayen birjik amma bata ga Numbar Ya mu'allim ba,Sai dai wasu numbobi da aka rubuta sunansu da harshen Larabci,shiru tayi tana tunanin kowanne ne aciki nashi,A ƙarshe dae duka numbobin masu ɗauke da rubutun Larabci ta turama Saƙon,bayan ta kammala rubuta saƙon ta ajiye wayar a saman bedside drawer,
Wuraren ƙarfe 2:30 na dare Lokacin masu bacci sunyi nisa a baccinsu,kamar yarda suka saba kwanciya a saman gadonsu su ukku,Hosana na a tsakiyarsu Abu na a ta 6angaren hannun dama inda yake fuskantar ƙopa,Jahad nata Can 6angaren hannun hagu,kwatsam Suna cikin Baccin nan,Abu ta soma jin wani irin gurnani gurnani asaman Gadonsu,a hankali ta buɗe idanuwanta tana ƙoƙarin ganin menene,har sai da gabanta ya faɗi rass,Wata Mummunar mage ce baƙa wulik mai Uban gashi ajikinta Hakoranta dogaye irin na Vam pires,Kafin abu tayi wani Yunƙuri Magen nan ta daddage ta kai Mata suka ta dira akan wuyan Abu,wasu Manyan ƙumbuna ta fiddo a hannunta tana ƙoƙarin Caccaka ma Abu akan fuskarta,A firgice Abu ta damƙi wuyan magen,Kokawa ta 6arke a tsakaninsu,duk yarda baƙar magen nan taso ta cutar da abu amma abun ya faskara,Domin kuwa Allah yaba Abu sa'a tunda ta damƙi wuyan magen nan ta dinga Jibgarta batare da jin shakkun wani abu ba,A jikin side drawer abu ta dinga buga kan magen nan bugu bana wasa ba,Har sai da magen ta fara kuka tana faman ambaton Miyau miyau,A faɗace Abu tace"Zaki ci ubanki ne,Baki ga komai ba,Nasan cewa ke ce Azmee,kika zo mun da suffar mage don ki kashe ni,Saboda kinga Asirinki na shirin Tonuwa ko?
Tunda abu ta ambaci hakan sai Magen nan ta bace 6aaat babu ita tamkar bata ta6a bayyana ba,ajiyar Zuciya abu ta sauke tana mai godiya ga Allah,daya bata nasara Akan Azmeee,
Saukowa tayi daga saman gadon,ba ƙaramin daɗi taji ba dasu Hosana basu farka ba,duk wannan badaƙalar da akayi suna ta shan baccinsu,
Toilet ta shiga,Bayan wasu mintuna ta fito ɗaure da alwala,Hijabi ta ɗauko tare da darduma ta shimfiɗa ta kabbara Sallah
A 6angaren Sehrish kuwa kasa samun natsuwa tayi acikin ɗakin,har sai da Sgr ya shigo sannan hankalinta Ya kwanta,ruwa tace mashi zata sha don💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠 paid book
*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*
Not edited👌
Lokacin da suka sauko downstairs,gaba ɗaya kowa Ya hallara akan dining suna Yin break fast,ƙarasawa Su kayi Bayan sun gaishe da kowannansu,Kowa saiyi Mata Ya jiki Yake yi,Taji daɗin yarda Suka nuna damuwa akanta,kusa da oummansu ta xauna,Jahad ma ta zauna a gefenta,a dai dai Lokacin Azmee ta dawo hannun ɗauke da wasu kayan abincin data ɗauko a kitchen,A saman table ɗin Ta ajiye tray ɗin,Atare Sehrish da Abu suka ɗago ido suna kallonta,fuskarta ta kumbura idanuwanta sunyi jawur kamar wadda tasha kuka,a gefen fuskarta hada gurjewa,fatar wurin ta tattare,Abu batayi mamaki ba,don kuwa ta gane cewa Itace ɗin tazo mata da suffar mage a daren jiya,Ga alamu nan Sun nuna,
Zagayawa tayi wurinsu Sehrish,plate biyu ta ɗauko ta zuzzuba masu abinci,tare da tura masu agabansu,Jahad ta hauci,Sehrish kuwa ƙin cin abincin tayi,Miƙewa Tayi daga saman chair ɗin,
"Ina zaki je"?omamnsu ce tayi magana ganin ta miƙe,
Daƙyar ta iya cewa"Kitchen zanje,"ta ƙarasa maganar tare da kama hanyar zuwa kitchen don ta shirya mashi breakfast ɗinshi,tun da ta fara jin sauƙin jikin nata,
Shaf shaf Ta shirya mashi asaman ƙayataccen tray,Ta wurinsu ta gifta cikin main palour,Upstairs Ta haye lokacin data ƙarasa part ɗin nashi tana ƙoƙarin Shiga,tajiyo muryoyinsu suna magana Shi da Omar,
"The same fa irin message ɗin da aka turomin Ni da Abba,da farko da abba ya nuna mun saƙon nayi tsammanin ɗaya daga Cikin friends ɗinshi ne,Aka samu wani Yaron Ya ɗauki wayar mahaifinshi Ya rubuta jagwalgwalon,Amma daga baya dana ga saƙon sai abun Ya tsaya mun araina,kuma sai gashi kaima An tura maka,to wai wanene da wannan aikin"?Yayi tambar yana kallon Sgr,dake a gefenshi,
"Am confused Omar,Nagaza fahimtar me aka rubuta ajikin message ɗin nan,abu 2 nake hasashe akan saƙon nan,kodai ƙaramin Yaro ne Ya rubutoshi,ko kuma wanda baya acikin hayyacinsa,Amma abunda yafi ɗaure mun kai shi ne,Taya akai wanda ya turo saƙon Ya samu special line ɗina,Wanda bakowa ne yasanni dashi ba,"ya kai ƙarshen maganar yayin da idanuwanshi ke akan Omar,
Kafin Omar yace wani abu,Sehrish Ta katsesu da sallama,Atare suka ɗago suna kallonta,
Ƙarasawa tayi gaban table ɗin dake agabansu,ta sauke trayn asaman shi, kafin ta ɗan ɗago tare da kallon Marshal Omar,murmushi ta samu akan fuskarshi,
'Ina kwana Ya omar,ka tashi lafiya,"
"Lafiya Lou Sister,Ya jikin naki"?
"Da sauki ya omar,"_
"Allah ya ƙara maki lafiya,"
"Ameen ngde,"ta amsa mashi,
Cike da Zolaya ya nuna kayan abincin data ajiye masu"Nawa ne ko nashi"?
Duƙar dakai ta ɗanyi tana murmushi
"Naku ne,na kawo maku,"
"Kinsan da zuwana part ɗinshi ne,"?
"A'a,"tayi maganar tare da satar kallon Sgr,Ya tsareta da blue eyes ɗinshi,duk saita shiga kame kanta,
"Ya akai naga ka tsareta da ido?faɗamun menene sirrin kallon nan"yayi maganar yana ɗage mashi gira,da sauri Sehrish Ta juya ta kama hanyar fita ɗakin,
"Kallon Ya isa haka,Its better ka kame kanka malam,saura ƴan satittika,Ka sakar mashi Ƴar shi,Ka koma U.s wurin Eva nasan har yanzu tana jiranka,"
Ɗaure fuska Sgr yayi"Omar bana son wannan joke ɗin,idan kaga nabar ƙasar nan,ƙafata ƙafarta,zan tafi tare da ita u.s don taci gaba da yi mun aiki acan,"
Harararshi Omar yayi"Sannu ko?masu aikin dake garemu a U.s fa,Sallamarsu zaka yi ne"?
"Aikinta daban nasu daban,"
"Kana nufin aikin gyara shimfiɗa"?dariya ce ta kufce ma omar,hakan ba ƙaramin hasala shi yayi ba,
Ganin ya 6ata rai yasa shi cewa"Shikenan nadaina,yanzu dae bari nayi serving ɗinmu ko?nasan kana jin Yunwa,"
Yayi maganar tare da kai hannu yana buɗe warmer,
Sehrish kuwa Bayan fitarta daga part ɗinshi,jiki asanyaye take tafiya,maganar da taji su Ya omar nayi akan saƙon nan ya tsaya mata aranta,Taya akai aka tura masu message iri ɗaya,Amma ita saƙon nata bada new number bane,ta layin Amrish ne,kuma a iya saninta Amrish bata da Number ɗinsu Ya omar,balle ace itace ke tura masu saƙon dagangan,to kodai ta yarda wayarta ne?wani yaron ya tsinta Yake tura masu saƙo,Can kuma ta tuna abunda Sgr yace da Special line ɗinshi aka tura mashi saƙon,Wanda ba kowa ne keda shi ba,
Ƙarasa Zancen zucin tayi a lokacin data sauko palour,bata koma dining ɗinba ta wuce bedroom ɗinsu tana zarya acikin ɗakin nasu,
*Amrish*
lokacin data juya izuwa cikin gidan A sukwane ta faɗa falon,da gudu ta nufi wani Corridor,Gidan Yana da girma sosai,tana da tabbacin cewa anan downstairs Suka rufe shi,haka ta dinga bin ɗakunan dake a gidan kaf tana bincikasu,Tasha wahala sosai,Ga uban gumi data haɗa,fuskarta sai naso take yi,A ƙarshe data gaji ta shiga ƙwala mashi kira ko Allah zaisa Yaji kiran nata Ya amsa mata,
"Junaid!Junaid"tamkar maƙoshinta zai 6allo waje saboda yarda take 6are baki wurin kiran sunanshi,
A galabaice Amrish tayi ruku'e hannunta dafe da guiwowinta,Sae faman haki take yi,runtse idanuwanta tayi gam,yayin da take tariyo ɗakunan data bincika a ƙalla sun kai ɗaki takwas masu zaman banza wanda ba'a amfani dasu,zurfin tunani ta shiga,nan take wani abu ya faɗo mata aranta,Acan backyards ɗin gidan Akwai wani munafukin ɗaki,Wanda tun tana yarinya hajiya Sarat ta hanata shiga ɗakin,ko wurin ɗakin taje saita tsawatar mata,tunda take ita dai bata ta6a gani an buɗe ɗakin nan ba,Akan idanuwanta,Kamar an daina amfani dashi amma akwai wasu surruka da aka 6oye acikinsa,Shiyasa aka hanata zuwa,
Cike da ƙwarin guiwa Amrish Ta miƙe,ta juya tare da kutsawa Can ciki,Ta ƙopar baya ta fita,tsayawa Tayi tana kallon Girman ginin,A hankali ta aza idonta kan ƙopar ɗakin dake fuskantar backyard din,Wani ƙaton ƙwaɗo ta gani an garƙame ɗakin dashi,Wanda duk bala'enta bazata iya cire wannan makullin ba,tsabar baƙin ciki kamar ta haɗiyi zuciya a wurin nan,Gashi window ɗin ɗakin sunyi nesa can sama,matsawa tayi jikin ƙopar ta kanga kunnanta,hannu tasa tana ɗan kwankwasa ƙopar ko zata ji motsinshi,Amma shiru babu wani alamun akwai mutun,cike da takaici ta juya zata bar wurin kenan idonta ya hango mata ɗigon Jini a ƙasan wurin,har sai da ta dafe saitin zuciyarta saboda faɗuwar gaban da taji,wannan Yasa ta ƙara yarda cewa Akwai mutun a cikin ɗakin,tabbas Sun shiga dashi cikin ɗakin,da gudun gaske ta koma cikin gidan,akwai wani ɗaki dake jingine da wannan ɗakin dake a backyard ɗin Amma shi yana fuskartar Cikin gidan,ranta na bata cewar Zata Samu window ɗin ɗakin ta cikin ɗakin dake acikin gidan,cike da sa rai Amrish ta faɗo cikin gidan,gudu gudu sauri sauri Ta shiga ɗakin,kamar Store ne na ajiyar buhun hunan kayan abinci da jarkokin Mai,A jikin ƙopar store ɗin ta samu Key ɗin ɗakin,hannunta na kerma ta murza key ɗin ɗakin,kafin ta hankaɗe ƙopar ta shiga,Gabanta sai faɗuwa yake yi tsoranta kada Mommynta ta dawo,dan Wlh har kashe ta zata iyayi,Dama tasha faɗa mata cewa ita bata damuba don ta rasa ba,ba ɗigon Imani azuciyarta,Kamar arniya hake take,
Ajiyar zuciya ta sauke Lokacin data hango Window mai girman gaske Duk da akwai net ajikinta,Amma batayi nisa ba,in har ta taka wani abu zata Iya hangen abunda ke wakana acan ɗakin bayan gidan,Ga uban duhun da ke cikin ɗakin,Bazata Iya hango abunda ke aciki ba,da gudun gaske ta juya tabar store ɗin,kitchen ta nufa Ta ɗauko wuƙa lafiyayya,Kafin ta ƙarasa saman hannun kujera inda ta ajiye wayar junaid ta ɗauketa,dama ita waya koda security torch ligh na kawoka,Don haka ta kunna fitilar wayar,Ta nufi store ɗin a hanzarce,Rufe ƙopar tayi bayan ta shiga,gaban waɗannan jerin Jarkokin man ta nufa,da yake Allah yayi mata ƙarfi,ɗaukar jarkar Tayi tajata izuwa gaban window ɗin,Sannan Ta hau saman jarkar,Iya idanuwanta ne suka kai Wurin net ɗin tagar,
Wuƙar hannunta ta sanya,ta dinga caccakata jikin Ragar,nan take wurin ya lomatse,Gagara wuƙar ta shiga yi tana Yanka Ragar,har sai da ta cire Rabinta,Tukunna Ta saki wuƙar kasa,Haska wayar tayi tana leƙen ɗakin,Saboda tsabar duhun ɗakin fitilar wayar tayi mashi kaɗan,Amma a haka tadinga ƙura ido tana kallon abubuwan dake cikin ɗakin,Wato wasu tsofaffin makamaine aka ajiyesu acikin ɗakin,ga wasu tuluna kamar na ruwa,A jikin bangon ɗakin Ƙwaryoyi ne aka ratayasu,Samansu an rufesu da faifai,ta kasa ganinshi,har sai da ta fidda rai,tana ƙoƙarin janye wayar ta bar wurin,kawai ta hango ƙurar dake danƙare a ƙasan ɗakin tana motsi,nan take gabanta Ya faɗi Rass,lokaci guda ta gane cewa mutunne kwance ƙasan ɗakin,yayi buɗu buɗu da ƙura,nan take zuciyarta ta karaya batasan Lokacin da ta fashe da kuka ba,Don tana ji aranta cewa Shi ne,Batasan taya zata Iya taimakonshi ba,tunda alamun sun nuna cewa babu ƙwari a jikinshi,balle ya iya takowa wurin Window ɗin Ya biyo ta ciki,tunda tagar tana da girma,
Tana cikin wannan Yanayin,Hawaye shaba shaba akan fuskarta,karaf kunnuwanta Suka jiyo mata dirar Mota a cikin gidan,Zo kaga tashin hankali,A firgice ta duro daga saman jarkar,saboda tsabar ruɗi anan tabar wayar Junaid ƙasa, ta rarumi wuqar data wurgar,ta ruƙota a