Showing 168001 words to 171000 words out of 432432 words

Chapter 57 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

sai don alkawarin da yayi ma sehrish na cewa in zaizo ɗaukarta daga school zai nuna mata wankan da zai ɗauka na shaddar shi,
   yana ƙarasowa cikin gidan bayan yayi parking din motarshi,ya wuce cikin main palour ɗin,a lokacin duk sun fita yin sallar azhar da ake cikin kira,bedroom dinshi ya shige tare da rage kayan da ke jikinshi ya faɗa cikin toilet,shaf shaf yayi wanka cikin minti goma sha biyar,ya fito daga cikin toilet din,jikinshi sanye da bathrobe,
    Gaban dressing mirror dinshi ya zauna,yadda kasan mace haka ya zauna yana gyara jikinshi,sai da yabi ko'ina na jikinshi ya shafe da mai,sannan ya shiga gyara sumar kanshi,bayan ya kammala ya miƙe tare da komawa wurin wardrobe,ya buɗe tare da ɗauko shaddar,a natse ya shiga zura kayan ajikinshi bayan yasa vest da short farare kal,rigar takai masa har guiwarshi,sai wandon,lokacin daya kammala sanya shaddar ajikinshi dawowa yayi tare da tsayawa gaban madubi yana kallon fuskarshi ta ciki ya Allah!shi kanshi sai da ya tsorata da irin kyan da yayi,kamar shiya zana kanshi don kyau,shaddar ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,sae faman salƙi take ajikinshi kamar wani sabon ango,kyakkyawan murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"junaid kenan yakamata ka zama namiji mana,ka cire duk wata fargaba yau ka tunkari sehrish gaba da gaba ka bayyana mata irin son da kake mata batare da jin shakkar komai ba,'
   shiru ya danyi aranshi yana cewa"gaskiya ina jin fargaba fa,anya reesh zata amince da son da nake mata?in tace bata sona fa?tabbas zan iya rasa raina,amma zan jure yau dae na fahimtar da ita tsananin son da nike mata,'
  Ƙarasa maganar yayi tare da ɗauko hula mahadin kayan wadda take tsadaddar gaske sai daukan ido take itama ash colour ya aza saman kanshi,hmmmm abun ba'a magana madarar kyau ba kaman da sumar kanshi ta dan fito daga baya.
  Zura takalmanshi yayi masu kyau da tsadar gaske suma mahadin kayan,sannan ya koma gaban dressing mirror ɗin ya ɗauko turarenshi ya shiga feshe jikin shi dashi ko'ina saƙo da lungu,nan take ƙamshin ya gauraye ko'ina na ɗakin,
  Key ɗin motar shi ya dauko sannan cikin sauri ya fito daga ɗakin nashi ya sauko downstairs,babu kowa a falon duk sun tafi salla,

A hankali yake driving din motarshi fuskar nan dauke da annuri,sae da yafara tsayawa masallaci yayi sallah,sannan ya miƙi hanyar makarantarsu sehrish,shiga ciki yayi tare da yin parking ɗin motar sannan ya fito ya tsaya tare da jingina bayanshi a jikin motar,zuba ido yayi yana jiran fitowar sehrish amma babu ita babu alamarta,ga students sai fitowa sukeyi,wasu na hawa bus wasu kuma ana zuwa ɗaukarsu,
   Gajiya ya fara yi da tsayuwar,
"Wai ina reesh ta shige ne,ta barni tsaye ina ta faman jiranta,'rai aɗan 6ace yayi maganar,
   Juyawa yayi tare da kifa kanshi ajikin motar ya ɗan lumshe idanunshi,
   adai dai lokacin Jahad ta fito hannunta ruƙe da school bag ɗinta,tana neman hossana duk atunaninta zata same tane a wurin da suke jiran osman yazo ɗaukarsu amma babu ita,da alama ma Osman ɗin bai ƙaraso ba,
  guntun tsoki taja tare da juyawa zata koma ciki,karaf idonta suka sauka akan Junaid,cike da mamaki take kallonshi,tana ɗan leƙen fuskarshi daga inda take,

Bakomai ne ya faɗo mata aranta ba,face alƙawarin da tayi ma hosana nacewa zata nemo mata ya Omar,aranta tace"ya Omar yace ƙaninshi ne wannan,kodae naje na tambaye shi ina ya Omar yake,may be ya taimakamun wurin haɗa ni dashi,
  ƙarasawa wurin motar junaid tayi ta ɗan tsaya daga bayanshi,tare da yi mashi gyaran murya don ya juyo,
   jin shiru bai juyo ba yasa tayi mashi sallama"Assalamu Alaikum,"
  Nan ma bai juyo ba,hannu tasa ta ɗan ta6a bayanshi a hankali,aikuwa a firgice ya juyo,ita kanta jahad sae da ta ɗan tsorata taja da baya ganin yarda ya juyo kamar ya tsorata,
    Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"am sorry,naga kamar ka razana,tun ɗazu nayi maka sallama baka ji ba,'
   harara junaid ya watsa mata,har sae da tasha jinin jikinta,rai a6ace yace"yanzu abunda kikayi mun kin kyauta!kinsan tun yaushe nike atsaye nan ina jiranki!"
   Gaba ɗaya jahad ta gama ruɗewa jin abunda Junaid ke cewa,
Cikin sauri tace"dama...am..inaso ne na tambayeka game da yayan.......'
  Kafin ta ƙarasa maganar tuni junaid ya gama hasala,ruƙo hannunta yayi tare da buɗe motar,yace mata wuce ki shiga,
   Murya na rawa jahad tace"bangane me kake nufi ba?
  A tsiwace yace"Ni ki wuce mu tafi,'
  duk yarda jahad taso ta fahimtar da junaid cewar ba ita bace wadda yake nema ba,amma yaƙi fahimta,shi duk atunanin shi sehrish ce,
  Tursasa mata yayi har sae da tashiga cikin motar,sannan ya shiga yaja motar da gudu ya fisgeta suka fuce daga cikin makarantar,

A natse yake driving lokacin daya hau saman shantalelen titin,zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi,ta wutsiyar idonshi yake kallonta,ganin yarda ta zuba mashi ido yasa shi ɗan juyowa tare da sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi,
  mamaki ne ya kama jahad,gaba ɗaya abun ya gama ɗaure mata kai,aranta tace kodae yana da ta6in hankali ne?in ba haka ba, nida bamu ta6a haɗuwa dashi ba amma kuma ya nuna ya sanni har ya tursasa mun na shiga motar shi,yanzu ni bansan ya zanyi na fahimtar dashi ba,kada hosana ta fito tayi ta nemana acikin school,
   "Reesh banji kin yabi wankan nawa ba?ko banyi kyau bane,"yayi maganar a yayin da yake kokarin parking ɗin motar a gefen titi,sannan ya juyo yana kallonta,
  zuru jahad tayi tana kallonshi,hakan ba ƙaramin 6ata mashi rae yai ba,cikin shagwa6a yace"Wai menene haka reesh,duk kin bi kin wani sauya mun,saboda ke fa na ɗau wankan nan don nazo na nuna maki,amma kin zuba min ido kina kallona kamar yau kika fara gani na,'
  A tsorace take da shi,don tagama yarda cewa yana da ta6in hankali,cikin en ina tace"amm...ni fa...ba..' kasa ƙarasa maganar tayi gabanta na faɗuwa,ganin yarda junaid ya matso dab da ita,ya ƙureta gaba ɗaya ƙamshin turaren shi ya gama kashe mata jikinta,
  murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa"kallon ya isa haka reesh,let's talk about serious issue,akwai abunda na jima inason sanar dake,amma inajin fargabar amsar da zan samu a wurinki,'ya ƙarasa maganar yana kallon cikin kwayar idanun jahad amatsayin sehrish,
   a hankali jahad ke bin kyakkyawar fuskarshi da kallo,tun daga kan eye brows ɗinshi,dogon hancinshi da kuma red lips ɗinshi,komai nashi mai kyau ne kuma mai jan hankali,
   Anatse yaci gaba da magana,"reesh,nasan cewa baki ɗauke ni cikakken namiji ba kamar saura,saboda na cika wasa da shiririta da kuma shagwa6a,kuma bani da aikin yi sae zama acikin gida kamar mace, nasan ba kowace mace bace zata so ta aure ni a haka" ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,wannan karon babu alamar wasa a fuskarshi,

  natsuwa jahad tayi tana sauraran shi,
   Hannayenshi yakai tare da ruƙo nata cikin nashi,nan take jahad taji gabanta ya faɗi,
  ɗagowa yayi awani irin yanayi yaci gaba da magana"duk wannan abun da nake reesh zan daina in baki so,idan har kika amince mu kayi aure,xan zama kamar yarda kikeso,nidae burina ki amsa mun cewa kina sona,kuma zaki aure ni,ni ban ta6a son wata ƴa mace ba in bake ba,na shaƙu dake sosai kuma ina da tabbacin cewa in mukayi aure zaki bani kyakkyawar kulawa,pls reesh tell me will u marry me"?
   Tamkar zai yi kuka haka yayi mganar yana jiran amsarta,
  Shiru jahad ta ɗanyi tana yanke shawara da zuciyarta,tunda dae bai da cikakken hankali bari na jaraba biye mashi kona samu mu rabu lafiya
Ƙarasa zancen zucin nata tayi tare da mayar da idanunta akan nashi tace"bana tunanin cewa akwai macen da zata samu namiji kamarka ta nuna bataso,kai na daban ne,kana da komai da mace zata buƙata a wurin namiji,kayi mun sosai kuma ka kwantamun araina,tayin soyayyar da kayimun na kar6a hannu bibbiyu,kuma na amince zan aure ka.....'
   Tsantsar mamaki ne ya kama junaid bai ta6a tunanin cewa rishi zata amince da soyayyarshi ba,cikin sauƙi haka batare da ta wahalar dashi ba,ajiyar zuciya ya shiga saukewa wani irin farin cikine ya lullu6e shi,mara misaltuwa a hankali ya shiga furta"Alhamdulillalh Allah nagode maka daka nuna min wannan ranar,dama sae da raina ya bani cewa reeshi ɗina bazata gujeni ba...."
  Fuskar jahad ɗauke da murmushi take kallonshi har lokacin hannunshi na ruƙe da nata,
   farin cikin da tagani a fuskarshi yasa taji aranta dama dagaske ita yake so,da ta bashi kyakkyawar kulawa,amma da alama akwai wadda yake so,tunda taji ya ambaci sunan reesh wannan ne yasa jikinta yin sanyi,

"Allah yasa ba mafarki nake ba,in ma mafarki nake kada ki tashe ni,'yayi maganar yana dariya tare da zame hannun shi daga nata,ya tallabo fuskarta da tafin hannayenshi,yana ƙare mata kallo,hakanan ya dinga jin kamar ta canza mashi,ƙura mata ido yayi kamar mai son gano wani abu,
  "Reesh kin canzamin sosae,sai nike ganin kamar bake ba,'
   Shiru jahad tayi tana cigaba da kallonshi,sakin fuskarta yayi tare da zura hannunshi cikin hijab ɗin jikinta,ae kuwa a firgice jahad ta ƙanƙame jikinta dake ta faman kerma cike da tsoran abunda zaiyi mata,
   Cikin lallausar suman kanta yakai hannunshi yana shafa gashin kanta yace"meyasa baki ɗaure gashin kanki ba?bai takura maki ahaka?
   atsorace jahad tace"ni na cire shi,yana acikin school bag ɗina,"
   Zame hannunshi yayi daga cikin hijab ɗin nata,
  "Zan ɗaure maki shi,ki ɗauko ribbom ɗin naki,"
  Kamar karta ɗauko mashi amma tunawa da cewar yana da ta6in hankali in ranshi ya 6aci zai iya kai mata bugu,hakan yasa ta janyo school bag ɗin tare da zuge zip ɗin,ta curo mashi ribbom din ta miƙa mashi sannan ta mayar da jakar abayanta,
  kar6a yayi tare da zura shi a cikin hannunshi,sannan ya ƙara matsawa kusa da ita sosai,cire hijabin jikinta yayi sannan ya janyota asaman chest ɗinshi,gaba ɗaya jahad ta gama rikicewa,ba ƙaramin yanayi junaid ya jefa ta ba,
  lamo tayi ajikinshi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarenshi,
  Xuba ma yalwataccen gashin nata ido yayi yana kallonshi,kafin daga bisa ni ya sanya hannunshi tare da tattaro shi wuri guda,ya ɗaure mata shi da ribbom ɗin,
   muryarshi taji acikin kunnanta yana cewa"Reesh,ya akai naga launin gashin kanki ya canza?ba brown colour bane?yanzu kuma naga ya koma dark black,?kodai idona ne ke nuna min ba daedae ba'?shiru jahad tayi batace mashi komai ba,saboda bata da amsar da zata iya bashi,
  jin tayi shiru yasa ya ƙyale maganar,hannu yasa tare da rabata da jikinshi,bin ta da kallo yayi ganin yarda take ta faman lumshe ido kamar mai jin bacci,
  Cikin sanyin murya yace"Reesh,kina jin feelings ɗin da nake ji agame dake"?
  buɗe ido jahad tayi sosai tana kallonshi da wata irin kasalalliyar murya tace"eh,'
   jinjina kanshi yayi tare da cewa"nasani,dama nasan kema zakiji abunda nake ji,pls reesh just for today kawai,kiyimun kiss koda a gefen fuskata ne,inaso naji ya ake ji,'
  Shiru jahad tayi tana tunanin ya zatayi da wannan ɗan tahalikin,gashi duk yabi ya kashe mata jikinta,ita tausayi ma yake bata saboda ta6in hankalin da yake fama dashi,tausayin shi ne taji ya kamata,mutun har mutun amma bai da cikakken hankali tunda inda yana da hankali ai ba yarda za'ai ya kasa gane ba itace wadda yake nufi ba,tunawa tayi da hosana dake fama da irin lalurarshi,amma nashi haukan yafi na hosana,don bata ta6a ganin wanda bata sani ba,ta liƙe mashi da sunan tasan shi,
    bata ƙarasa zancen zucin nata ba,muryar shi ta kuma katseta da cewa"pls reesh,just for today,"
   ajiyar zuciya jahad ta saki tare da kai bakinta zata manna mashi kiss acikin dimple ɗinshi,batayi wani aune ba taji bakinta acikin nashi tsulundum,sakamakon wata mota da ta bugi bayan motar shi,wannan girgizar da motar tashi tayi ne yasa bakinta komawa cikin nashi,gaba ɗaya junaid yabi ya rikice ya zauce ya haukace mata,sosai ya ƙankame ta ajikinshi,yana kissing ɗin bakinta ta hanyar zura tongue dinshi acikin bakin,ita kanta jahad a lokacin ta gaza control ɗin kanta,biye mashi tayi,

Sosai junaid ya shiga romancing ɗinta kamar zai zauce,duk yarda jahad taso ta kwace kanta a hannunshi amma yaƙi barinta,sai da yayi mai isarshi sannan ya zame jikinshi daga nata,cikin sauri jahad ta kifa kanta asaman laps dinta,tana faman sauke ajiyar zuciya,sam tagaza yarda cewa itace da kanta ta ba wani namiji damar kissing lips ɗinta abunda bata 6ata yi ba,to dama dae duk inda mace da namiji suka ke6e irin haka na ukkun su shaidan ne,Allah ya kyauta.

    jikinshi ne yayi sanyi,shi kanshi baisan cewa abun zai kaisu ga haka ba,daƙyar ya iya tashin motar da wata irin kasala ajikinshi yake driving din,ya hau saman titi sosae tare da wucewa dasu gida,
  
_💋Boss Bature💋_

tashin hankali!Lokacin da Hosana ta fito a nan ta samu osman yana jiransu tsaye a bakin motarshi,
   ƙarasawa tayi wurinshi tana cewa"ya Osman Ina jahad ɗin?ina ta nemanta banganta ba,nayi tunanin ta rigani fitowa ne,"
   "Wai kina nufin jahad bata acikin school ɗin naku"?ya tambaya hankali a tashe yana kallonta,.
daga mashi kai tayi alamar eh tace"babu kowa acikin makarantar ya Osman,na duba ko'ina ban ganta ba,"
  Gabansa ne ya faɗi rass,saboda kullum jahad ita ke riga hosana fitowa,yau kuma hosana ta rigata fitowa,tabbas akwai matsala,
  cikin sauri yace"shiga ki zauna bari nashiga cikin classes din na duba ko zan same ta acan,Allah dae yasa ba wani mummunan abune ya faru da ita ba,'
  Ya ƙarasa maganar tare da yin saurin shigewa cikin makarantar,buɗe motar hosana tayi tare da shigewa ciki ta zauna tana jiranshi,
  lokacin da Osman ya shiga cikin classes din yana neman jahad,duk ajin daya duba babu kowa wayam duk sun tafi gida,ko'ina ya dinga bi na makarantar saƙo da lungu yana dubawa amma babu jahad babu alamarta,tun yana sa ran ganinta har ya fidda rae,yafi ƙarfin awa ɗaya da rabi acikin makarantar yana neman jahad amma bai ganta ba,

  Cikin sauri ya fito jiki na rawa ya koma cikin motar,ya zauna a mazaunin driver,
  Ganin ya dawo shi kadae yasa hosana cewa"Ya osman ina jahad din?baka ganta ba"?
   "Na duba ko'ina banganta ba,bansan ina jahad taje ba,bari na fara kaiki gida nasan kin gaji sosai,"
   jan motar yayi tare da fucewa daga cikin gate ɗin makarantar,duk yabi ya ruɗe saboda fargabar kada ace wani abune ya faru da jahad,yana jiyo hosana tana shessheƙar kuka tana cewa"Nashiga uku,Allah yasa jahad bata 6ace ba,bansan ya zanyi ba in na rasata ba,kamar yarda na rasa sehrish,"
    "Kada ki damu jahad tana cikin ƙoshin lafiya,zan nemo maki ita,in ma ban sameta ba,zan kira major na sanar dashi halin da ake ciki,nasan zaiyi ma marshal Magana,"ya ƙarasa maganar a lokacin da yake shiga kwanar gidan Abusufyan,

Yana shiga ciki ya sauke hosana,sannan ya fisgi motar da gudun gaske ya fuce daga gidan,

Abunda ya faru bayan fitar motar osman daga cikin school din,Sai ga sehrish hannunta ɗauke da school bag ɗinta,daƙyar take iya tafiya saboda ciwon da tasha,ta jima acikin toilet din tana juyi kafin Allah ya kawo mata sauƙi harta samu ta fito,
ganin babu kowa acikin makarantar yasa taji gabanta ya fadi,nan tashiga fargabar Allah yasa junaid bai tafi ba,tasan dole ya gaji da jiranta,
Lokacin da taƙarasa wurin gate din taga babu kowa sai security guard din dake tsaron makarantar,tamkar ta aza hannu akai ta fashe da ihu haka taji,
Ganin yarinya tsaye cikin damuwa yasa mai gadin ya ƙaraso wurinta yana tambayar ko lafiya,
muryarta tamkar za tayi kuka tace"Mai ɗaukata nake nema,kuma naga babu kowa acikin makarantar,bansan ya zanyi ba,"
mai gadin yace"meyasa baki fito kin tsaya anan waje ba?me kikeyi acikin makarantar ne"?
cikin shessheƙar kuka tace"bani da lafiya ne,bacci ne ya ɗauke ni kuma babu wanda ya tashe ni,shiyasa bansamu na fito ba akan lokaci,"
"Kuma baki da waya a hannunki"?acewar mai gadin,
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
"Ko numbar wani baki ruƙe a cikin kanki ba,"
"Bani da numbar kowa,ban ruke akaina ba,"
Cike da takaici mai gadin yace"kaji matsalar,ni yanzu bansan ya zanyi dake ba,amma me zai hana ki ɗan fita daga wajen gate ɗin,wata'ƙil shi drivern naki ya dawo daukarki,nasan ma zai dawo ne,da zarar sunji shiru baki ƙarasa ba",
Amsa mashi tayi da toh,sannan ta fice daga cikin makarantar ta tsaya a bakin gate din,tana ta ƴan waige waige ko zata hango motar junaid,

_💋Boss bature💋_

A hankali motar junaid ta ƙetare babban gate din gidan nasu,a lokacin jahad ta ɗago da kanta,ta cikin glass ɗin take hangen katafaren gidan,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,yau gata acikin gidansu ya Omar dinsu,koba komai zata hadu dashi harma ta sanar dashi halin da suke ciki na rashin ganin shi,addu'a tashiga yi acikin ranta Allah yasa Ya Omar na nan,
tsayar da motar junaid yayi tare da buɗewa ya fito sannan ya zagaya ya buɗe ma Jahad motar,cikin sanyin murya yace"Reesh,am really sorry game da abunda ya faru a tsakanin mu,na fita hayyacina ne shiyasa,kinsan cewa ba halina bane.....kuma bazan ƙara ba insha Allah,
Murmushi jahad ta sakar mashi ayayin da take fitowa daga cikin motar tace"just forget about it,komai ya wuce,na yarda dakai sosai nasan cewa bada son ranka hakan ta faru ba,
ba ƙaramin daɗi junaid yaji ba,ya jima yana mamakin nasarar daya samu akan reeshi ɗinsa,farin ciki kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,
Bayan ya rufe motar ya ruƙo hannunta suka shige cikin gidan atare,a ruɗe jahad ke kallon katafaren gidan,jinjina kai kawai takeyi acikin ranta tana cewa"wai dama a wannan daular ya Omar ke rayuwa!gidan yayi mun kyau ya haɗu sosai,Allah yasa yana ciki,inaso na cika ma hosana alƙawarinta na ganin na haɗata da ya Omar dinta,
Babu kowa acikin main palour ɗin,sakin hannunta junaid yayi tare da cewa"bari na shiga ciki na huta,da anjima zan shigo muyi magana,"
amsa mashi tayi da toh,cikin sauri junaid ya wuce bedroom din Abbansu,
tashin hankali,jahad fa batasan ina zata dosa ba,gata dae acikin gidansu Omar,batasan a ina zata ganshi ba,
Tsayawa tayi ƙiƙam batare da ta motsa ba,
Gyaran muryar da taji ne yasa ta yin saurin juyawa don taga wanene,
Azmee ce ta fito sai faman sakar mata murmushi takeyi,jikinta sanye da jallabiya,ta ɗaure kanta da mayafi,ta fito fess abunta,
Gaban jahad ne ya shiga faduwa aranta tashiga tunanin cewa kodae wannan ce mahaifiyarsu?Amma meyasa naga tana sakar mun murmushi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login