Showing 66001 words to 69000 words out of 432432 words
Chapter 23 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
sanya shi tsakiyarsu a lokacin Sehrish da azmee suna a cikin kitchen suna aikace-aikacen girkin dinner ɗin gidan,
Sai da junaid ya tabbatar Ayaan da jahan sun zauna saman dining chairs ɗin sannan yace "ku jira ni, yanzun nan zan kawo maku abinci ku ci," ya faɗi da murmushi a fuskarsa sannan ya wuce kitchen ɗin,
har lokacin jahan dana sani yake yi akan marin da yayiwa junaid,ya gaza yarda cewa shi da kansa ya ɗaga tafin hannunsa ya zabga ma romeo ɗinsu mari, yana ganin abun tamkar a mafarki,😥Kitchen ya wuce yana ganin sehrish ya soma sakin murmushi, sallama yayi masu sannan ya shiga, amsa mashi su kayi gaba ɗayansu, sannan ya matsa wurin sehrish dake agaban chopping board tana yayyanka kayan lambu,
"Reesh idan akwai abun da kuka kammala inaso ki shiryamun a tray zan kai ma yaya Ayaan da Yaya jahan ne, yunwa suke ji ssae," ya faɗi yana yamutsa fuska tamkar shike jin yunwar, zuba mashi ido sehrish tayi tare da cewa "junaid ! meya faru dakaine? waya mare ka har haka"?
Cikin sauri junaid yasa tafin hannunsa ya rufe gefen fuskarsa yane cewa"ki daina ɗaga murya sehrish kada wani yaji, banaso wani yaji kiyi shiru kawai da bakin ki,"
Jikinta ne yayi wani irin sanyi aranta tana mamakin yarda akai har wani ya aza tafin hannunsa a fuskar junaid ga sahun yatsu nan sun bayyana raɗau a fatar fuskarsa yayi jawur wurin,
Jinjina kanta kawai tayi tare da cewa "Shikenan bari na shirya maka abincin ka kai masu," ta faɗi tana kallonsa cikin jin tausayinsa,
Ajiyar wuƙar hannunta tayi sannan ta wuce ciki donta haɗa masa, hannu yasa ya ɗauki knife ɗin da ta ajiye yaci gaba da yanka mata lettus ɗin data bari,
Azmee ce ta taya ta zuba masu acikin warmers duk tana jin magananun da suka yi ita da junaid, aranta tana mamakin marin da taji sehrish ta ambata anyiwa junaid, har satar kallonsa tayi taga yarda fuskarsa tayi jawur gefen da aka maresa ga alama nan tabbas in wani yaji acikin gidan sai an tada husuma,
Ruƙo tray ɗin tayi a hannunta zata wuce takai masu cikin sauri junaid ya ajiye wuƙar ya tare ta da cewa "kawo na kai masu,"miƙa mashi tayi yasa hannu ya kar6a yana kallon fuskarta da murmushi yace "thank u," itama murmushin ta sakar mashi duk tashiga damuwa akan yanayin fuskarshi,
Yana karba ya fuce yakai masu, yadda yabarsu haka ya same su, sunyi zugudun suna kallon junansu, Jahan na ganinsa ya saki fara'a tare da cewa "Yawwa heart beat mun gode sosai da irin kulawar daka ba mu, duk ka damu akan mu," murmushi junaid ya saki a lokacin ya ajiye masu tray ɗin kayan abincin asaman table ɗin,
Jikin Ayaan har kerma ya keyi wurin ɗaukar jug ya zuba lemu mai sanyi acikin cup yana kwankwaɗa, abun ya ɗaure ma junaid kai ashe dai da gaske yunwar suke ji,
Shima jahan jiki na rawa ya shiga zubama kansa abincin, cikin sauri junaid ya wuce wurin freezer ɗinsu ya buɗe tare da ɗuko masu cool drinks ya kawo masu agabansu,
Hannu jahan yasa ya ɗauki bottle water yana kwankwaɗa har yana kusa shaƙewa, agalabaice ya ajiye robar ruwan sannan ya kalli Junaid dake tsaye akansu yace "Allah yayi maka albarka junaid, kaje ka ci gaba da wasan ka,"
Juya junaid yayi ya koma kitchen wurinsu sehrish, tana ganinsa tace "Za'a a ƙara masu abincin ne"? Girgiza kai junaid yayi tare da cewa "zuwa nayi na taya ku aikin, bana jin daɗin zama ni kaɗai ne,"
Azmee tace"so kake kaja mana ko? taya za'a ganka acikin kitchen kana tayamu aiki, kaima kasan ba zaiyiyu ba,"
turo bakinsa yayi tare da cewa "Aunty azmee nifa ba wani abu zanyi mai yawa ba, kawai zan taya sehrish yanka kayan lambun ne,"
"Ban amince ba junaid, wai ni yau ba ka zuwa wurin buga ball ɗinka ne? ina laptop ɗinka ne? kaje ka kunna kallo kayi mana ko ka buga game,"
Ruƙe qugu yayi tare da cewa "Aunty azmee korata kawai kike son yi ne, to Allah ba inda zani ƙafata ƙafar sehrish, tazo mu tafi tare," ya faɗi da shagwa6a
Dariya su kayi gaba ɗayansu, sai lokacin sehrish tace "junaid ɗina shigo ciki ka samu wuri ka zauna, zan haɗa maka Cornflakes, kana sha kana kallon yarda muke girki,"
Murmushi ya saki sannan ya shige ciki tare da samun wuri saman dinning chairs na kitchen din ya zauna yana jiranta,
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Shaƙuwarku fa da junaid ƙara gaba take yi, don na lura kema bakyaso yayi nisa dake,"
Sehrish tace "Aunty azmee yana ɗebe mun kewa sosai, ina jin shi tamkar ƙanina ne shiya sanya.... . '
Muryar junaid ce ta katse ta da cewa "Wanene ƙanin naki"?
Cikin sauri sehrish tace "bafa maganarka muke yi ba" tayi maganar yayin da tasa hannu a cup board ta zaro kofin tare da wuce wa wurin dispenser saboda ta ɗebi ruwan zafin da zata haɗa masa dashi,
"Koma meye dae zanji ne," ya faɗi yana ɗan hararar ta daga inda yake,
Bayan ta haɗa masa takai masa nan ya zauna yana sha suna fira tare dashi,
________________________________
After magrib prayer motocinsu suka dunga shigowa cikin gidan da gudun gaske atare suka yi parking ɗinsu, Abbansu ne tare da SGR suka fito, motar dake bayansu kuma Su irfan ne tare da jabeer da khaleed, kana ganin su kasan sunji jiki, amma su da sauƙi babu alamar rauni ajikinsu sun dai jigata ne,
buɗe motar dake bayan tasu suka yi wadda fawan ne kwance acikinta, gaba ɗaya jikinsa sahun bulali ne ta ko'ina, saboda hasken fatarshi duk zanen bugun da miyagun su kayi mashi ya fito raɗau jawur wani wurin ma harya fashe, amma da yake ya samu emmergency treatment duk ansanya mashi magani awurin, babu riga ajikinsa gajeran wando ne kawai guntu suka barshi dashi, asaman ƙirjinsa hada ɗinki akayi masa, ba ƙaramin jiki ya ji ba yaji gata sosai,
Amstrong ne babban na hannun daman SGR ya fiddo shi tare da Irfan suka tallabo shi sannan suka wuce dashi cikin gidan, har lokacin bai dawo cikin hayyacinsa ba saboda hodar da suka shaƙa mashi,
Suma sauran mutanen da suka halarta domin yi masu jaje duk suka harhaɗu nan suna tayi ma Abbansu Allah kyauta, daga bisani suka haɗu gaba ɗayansu izuwa cikin gidan,
Tun da Sehrish taji dirar motaci tarasa samun kwanciyar hankali burinta taga su wanene suka zo, a lokacin sun kammala aikace-aikacensu na kitchen fitowarta kenan daga wanka, ta buɗe closet dinta ta zura doguwar riga sannan ta matsa jikin window tana leƙensu bata samu damar ganinsu da kyau ba saboda mutanen dake zagaye ta ko'ina,
Jiki asanyayae ta rufe window in gabanta na faduwa tsoranta kar ace wani ne ya rasu, hannu ta aza akanta tana ambaton "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un ya Allah kasa ba wani bane ya mutu,"
Cikin sauri ta bar wurin tare da buɗe kopar ɗakin nata ta fito waje a lokacin itama Azmee tafito daga ɗakinta a ruɗe jikinta na sanye da zumbuleliyar hijabi alamar salla ta kammala yi, ko addu'a bata tsaya yi ba ta fito saboda jin jiniyar shigowar motocinsu,
tsayawa su kayi gaba ɗayansu suna son ganin abunda ke faruwa, gaba daya sun rikice ganin yarda Amstrong da irfan suka shigo da Fawan duk ciwuka ajikinsa saman 3 seater suka zaunar dashi saboda masu zuwa dubiya,
Fitowa Ayaan da jahan sukayi daga ɗakinsu suma jin hayaniyar dake cikin gidan ganin fawan a wannan yanayin yasa su ƙarasawa da gudun gaske suka zube saman guiwowinsu agaban shi cikin tsananin tashin hankali suke cewa "fawan meya faru dakai haka? Waye yayi maka haka? Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,
Daker fawan ke iya kallonsu duk da baya iya tantance su wanene agabansa amma yaji muryarsu, juyawa su kayi suna kallon Irfam da jabeer don son jin ƙarin bayani,
Jabeer yace "Fawan bazai iya yi maku magana ba a halin yanzu baima san ko ku su wanene ba, addu'a kawai zakuyi masa,' jin haka yasa hawaye soma zuba daga idanunsu,
Shigowar da mutane suka soma yi ne yasa su samun wuri ƙasa suka zauna kowa ya zabga tagumi, kana kallon fuskar Abbansu kasan cewa acike take da tashin hankali saboda arayuwarsa ya tsani abunda zai ta6a masa jininsa,
Ganin SGR ya shigo yasa sehrish jin faɗuwar gaba, gaba ɗaya babu annuri a fuskarshi, white shirt ɗin dake ajikinsa duk shedar jini ne daya fallatsar masa hada hannunsa,
ba jinin kowa bane face jinin waɗanda suka farmaki su fawan, mugun bugu sukayi masu na fitar shari'a gaba ɗayansu suna a headquater dinsu an killace su can domin horar dasu da kuma yin bincike akansu,
Tuni jikin sehrish ya soma yin kerma saboda tashin hankalin da tagani ajikin SGR tunaninta ya gama bata cewa ko harbinsa akayine da bindiga shiyasa taga jini, hannu tasa ta rufe fuskarta tana kuka da gudun gaske ta juya ta koma ɗakinta saman gadonta ta faɗa tana cigaba da kukan,"
Abun ya ɗaure ma azmee kai ganin yarda sehrish ta gudu tana kuka kuma tasan ba don komai bane fa ce sai don ganin jini a jikin rigar sgr da hannunsa,
Ganin manyan mutane sun fara cika babban falon yasa azmee komawa cikin ɗakinta jiki asanyaye, zama tayi tana jiran mutane su ragu sai taje ta dubo shi,
Hannu Abbansu yasa ya ruƙo na Ayaan yace "taso ina son magana dakai,"
Tasowa ayaan yayi daga zaunen da suke yabi abbansu suka ɗanyi nisa da mutane sannan ya kallesa yace "Ina junaid yake"?
Ayaan yace "ina ji yana a ɗakinsa bana tunanin ya fita, Amma abba tayaya hakan tafaru da Fawan? Suwaye suka yi mashi haka? ya fadi idonsa cike tab da hawaye,
Dafa kafaɗarsa abbansu yayi shima fuskarshi tamkar zaiyi kuka yace "Ayaan bamu son ko su wanene ba, Babban yayan ku da Omar sune suka je wurin da suka farmake su, kuma sun samu nasarar kashe wasu daga cikinsu, yanzu haka akwai mutun 3 daga cikin miyagun suna a headquater ɗin mu,"
"Abba don Allah karku kyalesu akashe su kawai," ayaan ya faɗi cikin jin ɗaci aransa
"Ba zamu ƙyalesu ba ayaan, mutanene masu haɗarin gaske, babban tashin hankalin ɗaya daga cikinsu da muka aza shi saman kujerar lantarki muka bashi horo ya bamu wasu bayanai nacewa macace take basu Umarni duk wani kashe-kashen da suke yi a ƙasar nan,"!
waro ido Ayaan yayi cikin tsananin mamakin abunda Abban nasu ya faɗa masa, aruɗe yace "What! Mace kuma Abba? mace wannan dana sani?
"Of course Ayaan, ba kai kaɗae ba kowa daga cikin mu yayi mamakin jin hakan, yadda akasan mata da rauni amma har acikinsu asamu wata mai ƙarfin halin haɗa tawagar ƴan ta'adda masu farmakar mutane suna kakkashe su, Amma koma wacece insha Allah zamu ganota bi'iznillah zata ɗanɗani kuɗarta!"
Jinjina kai Ayaan yayi yana cewa "Insha Allah Abba, Allah ya tonu asirinsu aduk inda suke, abun yayi yawa wlh rashin imanin nan har ina? mutun baya tuna cewa shima wata rana zai mutu yabar duniyar ne?shin menene ribarka idan ka kashe wani bayan kai baka isa ka hana kanka mutuwa ba?
Kafin Abbansu yace wani abu muryar kanal yusif ta katse su da cewa "Abba ka matso kusa mutane suna son magana dakai,"
Amsa mashi yayi da "toh gani nan zuwa" sannan ya kalli ayaan yace "Abun dayasa na tambaye ke game da junaid kasan halin shi, muddin ya fito yaga halin da fawan ke ciki tofa zai iya sume wa ko ya zauce, dan Allah kusan yarda za'ae ku hana shi fitowa daga ɗakinsa indae yana ciki,"
Ayaan yace "Shikenan abba bari naje na duba shi," cikin sauri ayaan ya wuce upstairs ɗakin junaid, a hankali ya tura ƙopar ɗakin cikin sanɗa ya shiga, abun mamaki samun shi yayi saman gadon shi zaune ya toshe kunnan shi da headphone yana kallo acikin laptop ɗinsa baya jin duk wata hayaniya da akeyi acikin gidan,
Murmushi Ayaan ya saki sannan ya ƙara ja mashi ƙopar ɗakinsa dakyau ya rufe masa ita, sannan ya juya ya sauko down wurin su,
Har wurin dare mutane suna ta zarya agidan sai wuraren ƙarfe 9:30 sannan suka fara raguwa, tuni Sgr ya wuce part ɗinsa saboda ya gyara jikinsa ga matuƙar gajiyar da yayi idonsa ma kansu daƙer yake buɗesu ga yunwa ga bacci, har lokacin zuciyar shi tafarfasa takeyi duk in ya tuna irin artabun da su kayi tare da miyagun nan, duk da sunci nasara akansu sosai, bakomai bane ya tsaya masa aran shi ba face wannan maganar nace wa macace take ɗaukar nauyin tawagar miyagun dake kashe-kashen, yaci alwashin cewa sai ya gano ko wacece ita,
yanayin salon nata ya nuna cewa hada ɗaukar fansa take yi,' 😳😳😳
A asibiti marshal omar ya barsu hussana a hannun Camila kafin zuwa da safe zaisa a sallame su,
shi da major suka wuce izuwa gida saboda kiran wayarsa da ake ta faman yi ga kuma tsananin damuwar daya shiga game da halin dasu Fawan ke ciki,
daker sehrish tasamu ta fito sam tagaza samun natsuwa ta ko ina, ta damu da yanayin da taga Sgr da kuma halin da fawan ke ciki, a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya sannan ta kwankwasa tare da jiran ta buɗe mata,
tana tsaye azmee ta bude ƙopan tana kallonta tace "kin gama kukan?
Shiru kawai tayi tana wasa da yatsun hannunta,
"hmmmm me kike yi ma kuka ne ɗazu"?
Cikin sanyin murya tace"babu komai Aunty azmee kawai nadamu ne da halin dana ga fawan,'
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "gsky yaji jiki sosai, nima na tausaya masa bawan Allah, Yakamata muje mu duba shi, dama na jira ne mutane su ɗan rage sosai,"
Sehrish tace "ae nagama babu kowa a falon bansan inda suka kai shi ba,"
"Sun kwantar dashi ne, a ɗakin da suke kwantar da mara lafiya, bari nazo mu tafi tare, inyaso in mun dawo sai mu jera masu dinner ɗin duk da nasan abune mai wuya ma a samu wanda zai iya cin abincin, don duk suna cikin damuwa," tana fadin haka tashige cikin ɗakin bada jimawa ba ta fito sanye da mayafi, sannan suka jera da sehrish izuwa ɗakin dake anan downstairs,
A buɗe suka same shi don haka su kayi sallama, muryar kanal yusif ce ta amsa masu tare da cewa "ku shigo ciki mana,"
shiga ciki sukayi sehrish har tsoran kallon jikin fawan takeyi, wanda ke kwance saman gadon idonshi arufe alamar ya samu bacci,
Ayaan da jahad ne zaune daga gefen gadon sai kanal yusif dake atsaye,
Azmee tace "Yusif ashe haka abu ya faru? Mu ba mu sani ba"!
Kanal yusif yace "Wlh kuwa aunty azmee abun babu daɗin ji, ƴan ta'adda ne su kayi masu kwanton 6auna, amma anci nasarar Cafke wasu daga cikinsu,"
Cikin nuna jimami aunty Azmee tace "Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin waɗannan mutanen, wlh duk jikina ya mutu dana ga fawan acikin wannan halin bawan Allah, Allah dae ya tashi kafaɗunsa,"
Suka amsa mata da ameen, sai lokacin sehrish tace "Yaya yusif ya mai jiki"?
Yace "Alhamdulillah da sauƙi sosai harma ya samu bacci,"
Tace "Allah ya bashi lafiya,"
"Ameen ," suka amsa mata
Kanal yusif yace "Aunty azmee ku matso kusa dashi kuyi mashi addu'a yana buƙatarta sosai," matsawa su kayi atare kusa da fawan suna yi masa addu'a tare da tattofa masa, daga bisani su kayi masu sallama suka fito waje
Kitchen suka wuce atare don sun shirya abincin dining azmee tace "bari na haɗa maki, ki kaima babban yayansu nasan zai buƙaci wani abun,"
"Toh," ta amsa mata, suna cikin kitchen ɗin haroon ya shigo cikin babban falon daga waje ya shigo ciki hango sehrish da yayi yasa shi wuce wa cikin kitchen ɗin, kamar yarda ya saba fado masu batare da sallama ba haka ya shiga,
ɗagowa su ka yi suna kallon shi hankalin shi kwance tamkar baisan meke faruwa ba, azmee tace "haroon me kake buƙata ne"?
tsoki ya ɗan ja tare da cewa "tun yaushe nake ta faman zarya ina jiran a jera mana abincin dare amma shiru babu, so ake akashe ni da yunwa ne"? yayi maganar fuska aɗaure yana kallon sehrish wadda tuni ta kawar da kanta,
Azmee tace "kayi haƙuri haroon, saboda halin da su fawan ke ciki ne ga kuma mutane shiyasa ba mu samu damar fitowa ba mun jera,"
Uban tsoki ya kuma bugawa wanda har sai da suka ɗan razana suka kallesa yace "And then so what? Mutuwa fawan ɗin yayi ne da zaku fake da cewa halin da yake ciki ya hana ku jerawa mutane abincinsu"? Ya tambaya a ƙule
Mamakine ya kamasu jin abunda yace yadda ya nuna ko ajikinsa halin da fawan ke ciki,
nuna sehrish yayi da hannu tare da cewa "Ke! ki kawo mun abinci na yanzun nan a bedroom ɗina ina jiran ki,
Cikin sauri sehrish tace "Ni babban yaya zan kai mawa yanzu, sai dai ko in aunty azmee ta jera a dining ka zauna ka ci,'
Zaro ido haroon yayi afusa ce yace "Ke! Ni kike fadama cewa wani wai babban yaya zaki kaima abinci"? Ke ga futsararra ko"? ya tambaya yana faman huci
da ido azmee tayi ma sehrish alamar tayi shiru da bakinta, tsit tayi bata kuma cewa komai ba,
cike da bada umarni yace "Ina jiran ki ki kawo mun idan kuma ba haka ba zaki ga mai zai biyo baya," yana faɗin hakan ya fuce daga kitchen ɗin,
Murya tamkar zatayi kuka tace "Aunty azmee nifa bazan kai masa ba Allah,"
Azmee tace "sehrish ki daure ki kai masa, nikaina na tsorata da yarda yake mana magana, ina tunanin kamar yayi shaye-shaye ne baya cikin hayyacinsa,"
"Aunty azmee nifa bazan kai masa ba,kema da kan ki kince baya cikin hayyacinsa yanzu in naje zai iya kai mun bugu,"
ganin ta dage akan cewa ba zata je ba yasa Azmee cewa "to shikenan bari ni nakai masa, ke kuma ki kaima Sgr nasa," ajiyar zuciya sehrish ta saki tare da cewa "to,"
bayan sehrish ta kammala shirya masa a tray ta wuce upstairs part ɗinsa, sallama tayi ba'a amsa ba don haka tashiga daga ciki, babu kowa acikin falon alamar yana a cikin bedroom ɗinsa,
takawa tayi izuwa ƙopar bedroom ɗin nasa tayi masa sallama kusan sau uku sannan