Showing 72001 words to 75000 words out of 432432 words
Chapter 25 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
kayan maganar haroon ta faɗo mata aranta nace wa ta fara sallar dare domin neman tsari daga sharrin shi, tabbas maganarsa ta girgiza ta saboda tun daga lokacin da ta dawo daki at midnight tafarka tayi nafilfili saboda neman tsari daga sharrin shaiɗanin mutun irin haroon, ta jima tana jin cewa wasu abubuwa zasu faru tabbas acikin gidan!!!!! duba da irin mafarkin da tayi a baccinta na jiya, kuma taci Alwashin cewa ashirye take data fuskanci duk wani abu da zai taso ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wani da zaizo don tarwatsa rayuwarta ko kuma family ɗin SALAHUDDEEN HUSSEIN,
Hakan na nufin SEHRISH ta shirya zama AYYANA wato mai bama family ɗinsu kariyyya daga miyagu irinsu Haroon da kuma ire-irensa masu irin wannan mummunan kuɗirin,nace ba Allah ya ba mai rabo sa'a,
Tana cikin wannan tunanin azmee ta kwankwaso ƙopar ɗakin tana cewa "Allah sa dai kin tashi,"
Murmushi sehrish tayi a lokacin ta kammala sanya uniform ɗin, ba ƙaramin kyau sukayi mata ba tafito ɗass especially skirt ɗin da ya bi shape ɗin jikinta sosai,
ƙarasawa tayi ta buɗe mata ƙopar ɗakin tana cewa "ae tun ɗazu na tashi nama kammala shirya wa,"
Bin ta da kallo azmee tayi tana jinjina kai kafin tace "To fa yau wankan skirt aka ɗauka? masha Allah kinyi kyau ƙanwata, ya maganar breakfast fa? ta tambaya tana kallon ta,
Sehrish dake ta faman murmushi tace "aunty azmee yau a school zanci abinci na gaskiya,amma zansha koda tea ne,"
Azmee tace "okey, shikenan bari na kawo maki tea ɗin,'
gefen gado ta Zauna tana jiran dawowarta,
A 6angaren haroon kuwa bashi ya samu damar barin ɗakin da fawan ya ke ba har sai wuraren sallar asuba bayan abbansu ya kwantar da fawan dake ta faman sharar bacci a kafaɗarsa, sannan ya samu yabar ɗakin don zuwa yin sallah, sir commender haroon na ganin haka ya lalalla6a ya fito ya sungumi pillow ɗinsa daya shigo dashi, sai da ya jinkirta abakin ƙopar ɗakin ya tabbatar da cewa sun harhaɗu sun tafi gabatar da sallar asuba sannan ya koma ɗakin shi, agalabaice ya hankaɗa kopar bedroom ɗin nasa yayi wurgi da filon hannun shi,sannan ya afka toilet don tuni mararsa ta ɗaure saboda fitsarin dayayi ta ruƙo har na tsawon awannni, fitowa yayi daga toilet ɗin har wani biji biji yake gani saboda yarda idanun shi suka galabaita sun kumbura sunyi jawur saboda rashin baccin da baiyi ba, saman gadon shi ya afka batare da tunanin yin sallar asuba ba, sai ma addu'a daya shiga yi yana cewa "ya Allah ka yafe mun,zan ɗan rama baccin da banyi ba da safe in na tashi zanyi sallar anjima,'yana faɗin hakan ya shiga sharar baccin shi,
Babu wanda ya tayar da junaid daga bacci saboda basu son kwata-kwata yaga fawan ko kafin su tafi yin sallar asuba sai da Abbansu ya buɗe door ɗin ɗakinsa ya same shi baje magashiyyan yana sharar bacci rungume da pillow, murmushi kawai yayi tare da rufa masa door ɗin suka wuce mosque,
turo ƙopar azmee ta ƙara yi hannunta ɗauke da tea set ta miƙa ma sehrish cikin sauri sehrish tasa hannu ta kar6a tana cewa "Nagode aunty azmee,"
Azmee tace "ki hanzarta fa kada kiyi late dayawa,"
"Toh," ta amsa mata sannan ta shiga shan tea ɗin,
. har azmee zata fita sehrish tayi saurin cewa "Aunty azmee dama inaso nakaiwa babban yaya nashi kafin natafi school,"
tsayawa azmee tayi hannunta ruƙe da door handle ta juyo ta kalle ta tana ɗan murmushi tace "i knew, raina sai da ya bani cewa sai kinyi magana akan RAFAYET,
,ɗan sunnar dakai sehrish tayi tana kallon tea ɗin dake hanunta yana faman tiririn zafi
"Ni nake maki magana ba tea ɗin dake hannunki ba, naga kin zuba mashi ido,' guntun murmushi sehrish ta saki kafin ta ɗago tana kallonta daƙer ta iya cewa "aunty azmee baya jin daɗi jiyan nan that's why nake so nakai masa breakfast ɗinsa,nasan zai buƙace shi,"
Sakin baki azmee tayi irin mamakin nan tace "to ko dai kece ALEXANDRA ban sani ba,'
shiru sehrish tayi tana sakin murmushi saboda tagane cewa wannan sunan mommynshi ne,shiyasa azmee ta kirata da sunanta,
fuce wa azmee tayi tana cewa "shikenan kiyi sauri kizo ki kai masa breakfast ɗin," tana jin haka tayi saurin ajiye tea ɗin hannunta asaman bedside drawer inda kayan tea ɗin suke,
hijab ɗinta ta ɗauko ta zura ajikinta yar dai² shoulders ɗonta, sannan ta wuce kitchen ɗin tayi mamakin ganin yarda azmee tayi uban aiki duk ita kaɗai, da alama ma tun bayan sallar asuba bata koma bacci ba,saboda tasan cewa dole manyan baƙi su hallara saboda zuwa duba fawan,
..shirya ma sehrish tayi breakfast ɗin SGR acikin ƙayataccen tray sannan ta miƙa mata, ruƙo wa tayi a hannunta sannan ta miƙi hanyar zuwa part dinsa, tana cikin tafiya taji anyi gyaran murya juyowa tayi da sauri don taga wanene junaid ne tsaye jikinsa sanye da shirt pulover tare jeans,
......har ya kammala shiryawar shi cike da ɗaukin kaita makaranta ya fito, sai faman zabga murmushi yake yi sam baida wata damuwa, ɗan dawowa baya tayi dai² saitinsa sannan tace "junaid ! Ya akai naga kana ta faman zabga murmushi, kai bakasan meke faruwa ba acikin gidan nan"? tayi maganar tana kallon shi,
..cikin mamaki junaid yace "kamarya kenan? meya faru ne ni bansan komai ba,"
Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"jiya wani abu ya faru mai matuƙar raxanar wa, zan faɗi maka amma bari nadawo," ta faɗi tare da saurin haye wa upstairs tana murmushi, taso ta faɗama junaid abunda ya faru amma azmee dake tsaye daga kitchen tayi mata alamar karta kuskura ta faɗa masa, shine dalilin dayasa tace mashi ya bari tadawo,
. tuni jikinsa yayi sanyi a ƙagare yake daya ji mai reesh zata sanar dashi,
Kitchen ya wuce wurin azmee da sallama ya shiga sannan ya gaishe ta yana cewa "Aunty azmee a shirya mun breakfast a yunwace nake, gashi inaso nayi sauri nakai sehrish school,
Sakin baki azmee tayi tana kallon shi kanta ya gama ɗaure game da lamarinsu su duka biyun, ita tagaza samun natsuwa saboda son takaima babban yaya breakfast ɗinshi, shi kuma junaid damuwarsa yakaita school,kowa da wanda ya damu dashi kenan,
Zama yayi saman dining chairs yana jiran azmee dake shirya mashi bf ɗinsa ta kawo mashi yaci,
Acan ciki kuwa bayan sehrish ta isa part ɗinsa da sallama ta shiga baya cikin falonsa don haka ta wuce bedroom ɗinsa tsayawa tayi daga bakin door ɗin sannan tayi masa sallama, da wannan sexy voice ɗin nashi ya amsa mata, tare da bata permission din shiga daga ciki,
.a hankali tasa ƙafarta ta shiga ciki tsayawa tayi zuciyarta na faman bugawa ba ƙaramin kyau yayi mata ba,
ya juya bayansa yana tsaye a agaban mirrow jikinsa na sanye da bathrobe white colour wadda ta tsaya mashi dai² guiwarsa,a buɗe rigar take bai ɗaure igiyarta ba, amma akwai shorts ajikinsa,sumar kan nan tashi ta zubo mashi tayi irin Curly ɗin nan dark brown very smooth ta rufar masa abayansa, da alama bai jima da fitowa daga wanka ba,
...gaba ɗaya jikin sehrish ya gama mutuwa murus cos aduk time ɗin da tayi arba da wannan kyakkyawar surar jikin tashi rasa hankalinta take yi gaba ɗaya duk ta bi ta susuce,tana hangen shi ta cikin mirror saboda madubin yana facing dinta,
tabbas yaji alamar shigowar mutun tun da harya bada iznin shigowa daga ciki amma har yanzu baiji an motsa ba, a hankali ya ɗago da blue eyes ɗinsa ta cikin mirror ɗin karaf suka sauka akan na rishi dake tsaye jikinta na rawa ɗan zaro idanun nata tayi tana kallon nashi dake kallon cikin nata ta cikin mirror, hankali atashe cikin tsananin tsoro tayi saurin sunnar da nata ƙasa gabanta na faɗuwa,
gyaran murya ya ɗanyi kafin yace"a ajiye mun shi a palor, sannan agyara mun bedroom dina,' amsa mashi tayi da "toh" sannan ta juya ta fuce tana faman sauke ajiyar zuciya, a saman table ta ajiye masa sannan ta ɗan tsaya tana jiran ya kammala kimtsawa,after some minutes ya fito jikin shi sanye da tunic shirt milk colour tare da trouser, sai ƙamshi yake fitarwa, shiga cikin falon yayi ya samu wuri ya zauna saman royal sofa ɗin sannan ya shiga yin breakfast ɗinsa anatse,
Wuce wa sehrish tayi cikin bedroom ɗinsa ta shiga gyara masa shi komai agyare yake,bedsheet ɗinne kawai da yayi squeezing ya tattare inda ya kwanta, cire shi tayi sannan ta musanya masa wani sabo mai kyan gaske ta shimfiɗa masa, bayan ta kammala gyara ko'ina cikin sauri tafito saboda tunawa da school karta yi late, a lokacin da ta fito samun shi tayi yana yin waya da alama kan fawan suke magana da mutumin daya kira shi awaya,
Kama hanyar fita tayi har takai baƙin ƙopa ta ɗan juyo tana kallon shi gudun kar ace yana buƙatar wani abu gashi zata tafi batare daya bata izni ba, ganin alamar mutun ta wutsiyar idonshi yasa shi ɗan juyawa karaf suka haɗa ido da sehrish dake tsaye tana kallon shi cikin sauri tace "Can i go"? tayi maganar aɗan tsorace,
Lumshe idonshi yayi tare da ɗan jinjina kai alamar eh,
Murmushi sehrish ta saki sannan ta fuce cikin sauri aranta tana cewa "Sannu bata hana zuwa,"😇
Saukowa down tayi cikin sauri adai dai lokacin ta ji saukar motoci cikin gidan alamar sunyi baƙi, kitchen ta wuce anan tasamu junaid zaune saman dinner table harya kammala cin breakfast ɗin shi, yana ganinta yace "dama yanzu nake shirin biyo ki, bansan meya tsayar dake ba gashi har time ya ƙure ma,da ace ana bugu a school ɗin wlh da kinsha bulala yau," dariya sehrish tayi jin abunda yace
"Bari na ɗauko school bag dita," ta faɗi tare da juyawa cikin sauri ta koma bedroom ɗinta,
Sallama junaid yayi wa aunty azmee sannan yabaro kitchen din, jin sallamar Cg Abbas yasa shi ɗagowa cikin tsananin farin ciki yace "Yaya Abbas kaine tare da Aunty Amani !!!"
murmushi suka saki gaba ɗayansu da yake tare suka zo shi da AMANI yana sanye cikin shigar shadda maroon color ita kuma tana sanye da Arab gown white colour mai kwalliya ajikinta na duwatsu tayi rolling veil a kanta, ba ƙaramin kyau tayi ba,
sam junaid ya gaza rufe bakinsa don murna, buɗe mashi hannu abbas yayi cikin sauri junaid ya ƙarasa tare da faɗawa ya rungume shi sosai ajikinsa yana cewa "i really missed u our last born, duk da ina fushi dakai saboda baka son zuwa kawo min ziyara,' yayi maganar a lokacin da ya raba jikin shi dana junaid,
ɗan turo mouth dinsa yayi cikin shagawa6a yace "Yaya Abbas saboda me zaka ce kana fushi dani dan Allah, bakasan yarda na damu dakai ba koda yaushe inason zuwa amma shaiɗan ya hanani zuwa,' dariya sukayi gaba ɗayansu jin abunda junaid yace,
ɗan gyaran murya amani tayi masa tare da cewa"Junaid ni baka ganni bane"?
matsawa yayi tare da kai hannu zai rungumeta ajikin shi, ae kuwa a razane Abbas ya finciko rigarshi tare da janyo shi baya baya yana cewa "Sannu mati na mata,!matar tawa zaka rungume agabana? salon mu koma gida ta juya mun baya ko?"
Fashewa da dariya Amani tayi shima junaid ɗin dariyar yake yi cikin jin kunya ya sunnar dakai, shi aganin shi ba wani abu bane don ya rungume matar yayan shi, duk cikin waye wa ne,
Abbas ya kuma cewa "Oh ni junaid? Yanzu fa in na ƙyale ka sai ka rungume ta ko"?
ɗaga mashi kai yayi alamar Eh, hannu abbas yasa tare da ɗan jan kunnan shi har yayi ƴar ƙara yana faɗin "wayyo yaya Abbas karka cire mun kunne na in rasa na jin magana,"
"Hanzarta ka cire masa kunnan, hukuma ce zata raba ni dakai," acewar Abbansu wanda bai jima da fitowa ba ganin su yasa shi tunkaro su,
Murmushi suka saki gaba ɗayansu, adai dai lokacin Sehrish tafito daga ɗakinta, harta sanya Sandals ɗinta taruƙo school bag ɗinta, ƙarasawa tayi inda suke,
tunkan taƙaraso Amani ke kallonta cikin jin bugun zuciya, shi kanshi Abbas kallon matashiyar yarinyar yake yi cike da mamakin ina aka samu yarinya mace acikin gidan,
Ganin duk hankalinsu yadawo kanta yasa jikinta ya soma yin kerma, dakatawa tayi da tafiya sannan cikin en ina tace "umm....ina kwananan ku,"
atare abbas da abbansu suka amsa mata banda Amani dake tsaye ƙiƙam tana kallonta cikin tashin hankali, ita kanta sehrish atsorace take da kallon da Amani ke yi mata,
"Zonan My daughter nayi missing ɗin ganinki, gashi bakya zuwa kina gaishe da Abbanki ko"? Yayi maganar yana kallonta,
Ƙarasawa sehrish tayi gab da Abban nasu ta tsaya tana faman ƙaƙume hannun jakarta da ta sargafo a kafaɗarta,
Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta yace"yaushe kika fara zuwa school ne ba'a sanar mun ba"?
....daker sehrish ta iya cewa "jiya ne nafara zuwa,"
Jinjina kansa yayi tare da cewa "okey,ki maida hankali sosai akaratun ki kinji ko? Banda biye ma ƙawaye
"Insha Allah Abba," ta amsa mashi,
Baki asake Abbas yace "yakamata a wayar mun dakaina mana, ina aka samu yarinya kyakkyawa kodai daga cikin danginmu ne na damaturu ko zariyya"?
Ya tambaya aɗan ruɗe yana kallon Abban nasu, tunkafin Abban nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa "ƙanwata ce yaya Abbas, sunanta Sehrish kuma abbane yayi mun ƙanwa da ita, itama ƴar Abban mu ce, ba'a jima da haihuwarta ba, nasan zakayi mamakin yarda tayi saurin girma har haka, ka tambayi Abba zaiyi maka bayanin komai,'
yana faɗin haka yaja hannun sehrish suka bi ta gefensu suka fuce,
Dariya kawai Abbansu ke saki hada shi Abbas ɗin,
"Ji wata shiririta irinta junaid,hakanan kawai ya zabga mun ƙarya, ina na ajiye matar bare harna haifi ƴa kamar wannan,'
Ya fadi tare da yi masu alamar su shiga daga ciki, bin shi su kayi tare da samun wurin saman royal sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna, Amani na kusa da Abbas yayin da Abban ke fuskantar su yace "sannun ku da zuwa,nayi mamakin ganinku da wuri haka,"
Abbas yace "tun jiya muka so muzo,amma dare yayi sosai lokacin, wlh sam nagaza samun natsuwa ne game da halin da naga fawan a asibiti, shine nace mata tashirya muzo har gida mu duba shi,"
yayi maganar fuskarshi dauke da damuwa, Amani ma tace "Abba ya mai jiki? sai jiya da daddare yake faɗamun abunda ya faru dasu fawan hankali na ya tashi sosai, tun jiya nima naso ko wayane nakira na tambayi jikin shi amma duk layin dana kira ba'a ɗagawa,"
Abba yace "ae ba zaki same su ba, saboda duk muna cikin damuwa ne,bakowa ma yasan inda ya jefa wayarshi ba,abun ne ya tayar mana da hankali sosai,
Cikin sanyin murya tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya,ya tashi kafaɗun shi, su kuma waɗanda sukayi mashi wannan aika aikan Allah ya toni asirin su,"
"Ameen Ameen," suka amsa mata
Daga bisani Abbas yace "bari mu shiga ciki mu dubo shi,"
Miƙewa su kayi hada Abban yayi masu jagowa izuwa ɗakin da aka kwantar da fawan,
Da sallama suka shiga ciki, har lokacin fawan na kwance sai faman sharar bacci yake yi, Abbas yace "masha Allah jikin nasa yafara sauƙi, tun da harya samu bacci,"
"Ae tunjiya dana shigo ɗakin na same shi yana ta faman fisge-fisge yana cewa sun biyo shi zasu kashe shi,saina zauna wurin shi anan zaune muka kwana ni dashi da asuba ne nabar ɗakin," Abban nasu ne yayi maganar ayayin da yake samun wuri gefen gadon tare da zama yana kallon fawan ɗin dake kwance magashiyyan yana kwasar bacci,
matsawa Abbas yayi shima tare da samun wurin kusa da Abban nasu ya zauna sannan yakai hannun shi ya dafa forehead din fawan yana cewa "Baƙaramin jiki yaji ba gaskiya,sun azabtar dashi sosai bawan Allah, amma asannu zai warware insha Allah,
Kafin Abban nasu ya kuma cewa wani abu wayar Amani dake acikin handbag ɗinta tashiga yin ringing da ƙarfin gaske,
Kallonta Abbas yayi tare da cewa "ki fita waje ki amsa wayar," cikin sauri ta amsa mashi da toh sannan ta fuce,
dama so take ta fita daga ɗakin saboda gulmar data ciyota kunsan mu mata abun ajinin mu yake,da zarar abun gulma ya samu nan take zaka ga jikin mutun har rawa yake yi don ya faɗama ɗan uwansa, (Amma fa ni bana gulma) 😒
Cikin sauri Amani ta sauko down stairs jikinta har rawa yake yi ganin Azmee na jera masu breakfast a dining table, yasa cikin sauri ta wuce wurinta
Azmee naganin ta ta soma sakin fara'a tana cewa "aaa yau kune agidan namu? saukar yaushe,"
Batare da Amani ta amsa mata ba tace "Yawwa Aunty azmee dama akwai abunda nakeso na tambaye ki,"!
Cikin mamaki azmee tace "meke nan"?
"Ga me da Yarinyar dana gani acikin gidan nan, wata ƴar matashiyya shin ita ɗin jinin su Abba ce?
murmushi azmee ta saki aranta tace "Gulma ajali, in ba'ayi ba a mutu," a fili kuma tace "abokiyar aikina ce a aka kawo don ta runƙa tayani aiki,"
yamutsa fuska amani tayi kan ta yagama ɗaurewa ta kuma cewa "ƴar aiki fa kika ce? But i was confused ya akai naganta cikin uniform kuma har junaid na kiranta da ƙanwarshi? Kuma naji Abba ma ya kirata da My daughter,duk kuma a matsayin mai aikin?
dariya azmee tayi ganin yarda amani ta ɗaga hankalinta akan sehrish
"tabbas mai aiki ce itama, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyarsa,bata da banbanci da sauran ƴa'ƴanshi a yanzu, saboda yana son Yarinyar sosai,"
Jin haka yasa Amani ɗan zaro ido waje bata ƙara cewa komai ba saboda wayarta da ta ƙara yin ringing, cikin sauri ta zura hannu tare da buɗe handbag din ta zaro wayarta, tare da duba screen din wayar don taga mai kiranta, sunan Aunty laila ne ya bayyana asama, kallon Azmee tayi tare da cewa "ina zuwa," tayi maganar tare da kama hanya ta danyi nesa da azmee sannan ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta tana cewa "barka da safiyya Auntyna fatan kin tashi lafiya,"
Murmushi Aunty babba tasa ki daga can 6angaren tace "Lapiya lou Alhmdllh my sister, nazo maki da labari mai daɗi ina fata kina da kunnan saurara,"
Amani tace