Showing 207001 words to 210000 words out of 432432 words
Chapter 70 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
baba buzu,ni kake kira da wannan mutumin?ka manta matsayin da nake dashi awurin ƴarka?nifa ne malamin dake koya mata karatun addini,ya kamata ka darajani,kuma abunda abu tayi ba kuskure bane,yaron nan rashin kunya yayi mani dole ranta ya 6aci,dan Allah kaja mashi kunne ya daina yi mana shisshigi saboda ni da abu son juna mukeyi kuma aure zamuyi......'
Tunkan ya ƙarasa maganar baba buzu ya daka mashi tsawa tare da cewa"ubanwa zai auraka maka ita!ko ita take da ikon aurar da kanta ne!Ni ne mahaifinta kuma ni nake da ikon na aurar da ita ga wanda naso,kuma naga ya dace da rayuwarta,don haka tun yau inaso ka cire ta aranka,abu nayi mata miji,kuma ba kowa bane mijin nata ba face ABUSUFYAN!muddin ina numfashi abu bazata ta6a auran wani ba in ba shi ba!!!
Hankali tashe abu ke kallon mahaifinta da idanuwanta da sukayi jawur saboda kukan da tasha,mayar da idonta tayi kan Abusufyan dake ta faman sakin murmushi,girgiza kai tashiga yi tana cewa"baba...ni banason abusufyan,bai dace da rayuwata ba,ba mutumin kirki bane shi,bai da kamun kai,kuma baida ilmin addini,boko kawai yasa agaba,wayewarshi tayi yawa baba.....'
Ganin yarda mahaifinta ya harzuƙo zai rufe ta da duka yasa ta watsa aguje cikin gidan tana kuka,
"Yanzu abunda kayi ya dace baba buzu?yarinyar nan ta nuna tana son malamin addini mahaddaccin al'qur'ani saboda ya tarbiyantar da ƴa'ƴanta,ta san cewa idan ta aure ni zan bata kyakkyawar kulawa kuma zan ilmantar da ita da kuma ƴa'ƴan mu saboda me zaka hana ta aure ni!?kafi son ta auri wannan sangartaccen da baisan komai ba sai yawo da ƴan mata acikin gari?ahaka kake tunanin zai bama ƴarka tarbiyya in ya aure ta?
sayyadi nakai ƙarshen maganarshi baba buzu yace"Ka gama sambatun naka?to kama hanya kabar ƙopar gidan nan tun kafin raina ya 6aci,banason ganinka tare da abu,don ban yarda dakai ba,akwai wata mummunar manufa atare dakai na son cutar da ƴa ta,shiyasa naji baka kwanta mun araina ba,amma abusufyan ya kwantamin araina,duk da ya kasance yana da ƙananun shekaru amma ina da tabbacin cewa yafi ka hankali da tunani........'
Jin wannan maganar ta baba buzu yasa hawaye sauka a idon sayyadi muryarshi a kasalance yace"Wai me nayi maka ne ka tsane ni?me na tsare maka ne?dama tunda na fara zuwa gidan nan ina koya ma abu karatu na lura da irin kallon da kakeyi mun,meyasa baba buzu?ko don na kasance malamin makaranta banda arziƙin da zan iya siyen zuciyarka ne?saboda banda kuɗin da zan dinga baka cin hanci don ka auramun ƴarka zainab,sae shi daya taso gidan naira,kasan cewa idan ka aura mashi abu tattalin arziƙinka zai bunƙasa,baba buzu ka tabka babban kuskure arayuwarka muddin ka aura ma abu wannan sangartaccen yaron........'
Yana kai ƙarshen maganar shi ya tada rugwagwar mashin dinshi yabar wurin,
matsawa baba buzu yayi tare da dafa kafadar Abusufyan cikin rarrashi yace"kayi haƙuri abusufyan,duk sai naji na tsani kaina da abu ta ɗaga hannu ta mare ka,ni ina da tabbacin cewa wannan malamin dake bibiyar rayuwarta ba mutumin kirki bane,ba don Allah yake son abu ba,tabbas akwai wani abu dayake son cimmawa atare da ita,'
Abusufyan yace"baba kada ka damu komai ya wuce,kuma ina baka haƙuri game da kalaman da sayyadi yayi maka,banji daɗinsu ba,'
Baba buzu yace"babu komai yaje don kanshi,Allah na gani ba don komai yasa nakeson ka auri abu ba,sai don saboda in saka ma mahaifiyarku da irin ɗawainiyar da take damu ni da ƴa ta abu,wlh bani da burin daya wuce wani acikin ƴa'ƴanta ya nuna yana son abu ni kuma in aura mashi ita,wannan ce kawai hanyar da nake da ita da zan iya sakamata,'
Murmushi abusufyan yayi tare da cewa"Baba yanzu in na nemi auran abu a wurinka zaka aura mun ita?a yadda nake da ƙananun shekarun nan"?
baba buzu yace"mai zai hana?ni lokacin da iyaye na sukayi mun aure ban kai shekarunka ba,kuma muka zauna da matata lafiya har Allah ya al'barkace mu da samun zainab,abusufyan in har dagaske kana son abu,kuma zaka ruƙe mun ita amana,na amince kayi ma Abbanku magana ya nema maka auranta awurina nikuma zan baka ita,kai tun ma yanzu inaso ka sama ranka cewa abu ta zama matarka,saboda na mallaka maka ita,sadaki kawai zaku biya a aura maka ita,'
wani iri farin cikine ya lullu6e abusufyan,saboda tsabar farin ciki baisan lokacin daya ɗauki baba buzu ba ya daga shi sama yana jujjuya shi,dariya sosai baba buzu yayi yana cewa"Abusufyan ka sauke ni mana!ko nauyi na baka ji!duk murnar na mallaka maka abu ne yasa ka ɗauke ni haka kamar diyar roba,
Sosai sukayi nishaɗi atsakaninsu,
Lokacin da abu ta shiga falon gidan tana faman zabga kuka,hajiya Ameena na ganinta ta tashi daga zaunen da take saman kujera ta tunkareta tana tambayarta lafiya,
adai dai lokacin Mijinta Alhaji nuraddeen yana kan saukowa ƙasa daga saman bene,tun kan yaƙaraso yake tambayarsu me akayi ma abu take kuka,
cikin shessheƙar kuka tace"Baba ne yace zai auramun abusufyan kuma ni bashi nakeso ba sayyadi nakeso in aura......'
Jin wannan maganar ta abu yasa hajiya ameena ta ɗaure fuskarta tace"Abu yanzu saboda mahaifinki ya za6a maki abusufyan amatsayin mijin da zaki aura shine kike kuka!meyasa bakya son shi ne?
Muryar daddy ce ta katse mata hanzarinta"Wannan abun bazai ta6a yiyuwa ba!babu yarda za'ae abu ta auri Abusufyan yaron da bai gama mallakar hankalinshi ba!ban goyi bayan wannan maganarba,zanje na samu mahaifin naki muyi magana dashi,indai aure yakeson yi maki sai dae ya aura maki sayyadi saboda shi ya mallaki hankalinshi zai iya kula dake amma ba abusufyan ba,'
Wurga mashi wani kallo mai kama da harara hajiya Ameenatu tayi tare da cewa"Wannan abun bai shafeka ba alhaji!babu ruwanka da shiga shirgin Abusufyan,tunda ubanta da kanshi ya mallaka mashi ita,babu wanda ya isa ya dakatar dashi daga auranta!aure kamar anyi an gama ne'
murmushi kawai alhaji nuraddenn yayi yana girgiza kai yace"oh kema kin goyi bayan Abu ta auri abusufyan?bayan kinsan halin shi sarai bai jin magana,kuma yarinyar nan ta nuna cewa bata son shi,dan Allah karku takura rayuwarta,ku bari ta auri za6in ranta karku tilasta mata!kuma sannan ke kin manta da cewa Yayarki hajiya Aishat bazata bari abusufyan yayi aure da ƙuruciyarshi ba!kuma kin manta da tsarinta na ƙin auren bare"?
ta6e baki hajiya ameenatu tayi kafin tace"ni wannan bai dame ni ba,ba'a auran bare ita ta auri amininka salahuddeen?ko tana da alaƙa dashi ne?ba haɗuwar barikin sojoji bace,'tayi tambayar tana kallonshi,
Cigaba da magana tayi,"idan kuma kuruciyarshi kake magana,kai kamanta kana da shekara nawa na aure ka?wasan ƴar 6urun 6urun muka dinga yi dakai adaren farkon mu ko ka manta da wannan"?
Bakin Alhaji fa ya mutu shiru yayi bai tanka mata ba,don bai da amsar da zai bata,
guntun tsoki taja kasa² tare da mayar da idanunta kan abu dake tsaye hankali tashe tana kallon mommyn jin ta goyi bayan auranta da abusufyan,
"Abu,kiyi hakuri ki bi za6in da mahaifinki yayi maki,ni ina da tabbacin cewa bazaki ta6a dana sanin auran abusufyan ba!nasan kina yi mashi kallon mutumin banza ne saboda son mu'amalarshi da mata,amma inaso ki sani abusufyan ɗina ba ɗan iska bane,kuma shima yana da ilmin addini fiye da tunaninki,shigar ƙananun kaya da yake yi da kuma yawan manne ma matan da yakeyi hakan ba yana nufin cewa shi mutumin banza bane,zainab abunda nakeso ki sani,bata suttura kota kalaman baki ake gane mutumin kirki kona banza ba,wannan azuciya yake,zaki iya ganin mutum malamin addini mai haddar al'qur'ani kanshi kullum sanye cikin jallabiya yana wa'azi bainar nasi,alhalin zuciyarshi baƙa ce yana aikata wasu muna nan abubuwan a6oye batare da sanin kowa ba sai mahalincinshi ,haka zalika zaki iya samun mutumin da kullum yake ɗabi'u irin na turai,sanya ƙananun kaya,hulɗa da mata rashin jin magana da sauransu amma kuma zaki samu zuciyarshi kyakkyawa ce tsarkakakkiya bai sa6ama ubangijinshi,ki daina yarda da abunda idanuwanki suke nuna maki abu,tun farko kinyi ma abusufyan mummunan zato shiyasa kika tsane shi,amma ni nasan cewa kina sonshi kamar yarda yake sonki,bansan me malamin can ya faɗa maki agame dashi ba,dayasa har kika za6e shi akan jini na,to inaso ki sani muddin kinason ganin farin cikina,tun daga rana irin ta yau ki cire soyayyar wancan mutumin aranki,ki fara koyama kanki soyayyar Abusufyan,kafin aɗaura auranku.,.......'
Murya na rawa abu tace"..mo..mommy..ke ma kin amince in auri abusufyan in rabu da sayyadina?
Jinjina mata kai hajiya Ameenatu tayi alamar Eh,
Fashewa da kuka Abu tayi tare da watsa wa da gudu ta shige ɗakinta saman gado tana kuka tana faɗin"Ni bani sonshi bana son abusufyan bazan aure shi ba,sayyadi nakeso,'kamar zautacciya haka tashiga sambatu har bacci ya ɗauketa,
Alhaji dae bai ƙara tanka masu ba saboda baisan 6acin ran matarshi,ya zuba ma sarautar Allah ido,yana kallon ikon Allah,
Batare da 6ata lokaci ba,hajiya Ameenatu ta biya sadakin abu dubu ɗari ta damƙa ma mahaifinta,shi kuma ya damka ma zainab kuɗin a hannunta,daƙyar ta kar6i kuɗin,ko da ta koma ɗakinta dasu,wurgi tayi dasu asaman gadonta,ta koma tana sharar kwalla,
Duk wannan budurin da akeyi,iyayen Abusufyan basu son da zancen auren abusufyan ba,tun lokacin da Hajiya ameenatu ta kira Ammi awaya take sanar da ita cewa Abusufyan yaga yarinyar mai gadin gidansu yana so,tun kafin ta rufe bakinta ammi ta katseta a fadace tace"Kar na sake jin wannan zancen,ki rabashi da yarinyar don karya sama ranshi ita,ni bazan ta6a aura mashi yar mai gadi ba mara asali,ƴa'ƴana bazasu auri bare ba,auran zumunci zanyi masu,"tun da hajiya Ameenatu taji wannan zancen na yayarta ta tabbatar da cewar bafa zata amince abusufyan ya auri abu ba,saboda ita kaifi ɗaya ce in ta furta abu babu wanda ya isa ya dakatar dashi!
Koda Hajiya ameenatu ta sanar ma Abusufyan abunda mahaifiyarshi tace na ƙin amincewa da aurenshi da abu,ranar har zazza6i yayi yaƙi cin abinci kuma,duk yabi ya hargitse ya shiga damuwa sosai,hakan yasa hankalin hajiya yayi mugun tashi saboda ta mutu akan son Abusufyan,batason ganin damuwarshi,shiyasa ta yanke shawarar aura mashi abu batare da sanin iyayenshi ba,ko wani daga cikin danginsu don kar Ammi ta samu labari,a wata ranar juma'a ne bayan an kammala salla,aka ɗaura igiyoyin auransu dubban jama'a suka shaida,daga ciki hada ni hafsat bature muhammad,da kuma makaranta wannan littafin,
Tun lokacin da labarin auren Abu da abusufyan yaje kunnan sayyadi,tun daga ranar bai ƙara takawa yaje gidan ba,abun ya ɗaure mashi kai,yarda suka shirya komai batare da saninshi ba,suka aurar da yarinyar da yake mutuwar so,har gadon asibiti sai da ya kwanta yayi jinya,
Bayan aurensu da sati guda hajiya Ameenatu ta ware masu katafaren ɗakin da zasu zauna anan cikin gidansu,ta zuba masu duk wani abu na more rayuwa acikinshi,duk don ta faranta ma abusufyan dinta,hatta lefen kayan abu duk ita ta siya mata komai da kayan ɗakinsu,
Duk yadda abusufyan yaso ya shawo kanta ta amince suyi rayuwar aurensu amma abu taƙi amincewa dashi,har yau ganinshi takeyi tamkar ba mijinta ba,saboda bata son shi ita sayyadi takeso,kullum Abusufyan yayi yunƙurin ta6a ta,hana shi takeyi tana cewa ba tayi tanadin kanta saboda shi ba sai don sayyadinta,'wannan maganar ba ƙaramin ƙona mashi rai takeyi ba,gashi Allah ya jarabce shi da tsananin sonta,duk wulaƙancin da abu keyi mashi,bai ta6a sanarma kowa ba,jurewa kawai yake yi donnya rufa mata asiri,yasan muddin ya sanar ma mommyn shi aminatu ko mahaifinta baba buzu sae ranta yayi mugun 6aci don mahaifinta har bugunta zai iyayi,saboda ya tsani yaji tana maganar sayyadin nan,
Wuraren ƙarfe sha biyu na dare,tana kwance saman gadonsu tana bacci,ta dinga jin shessheƙar kukan mutum akusa da ita,buɗe idanunta tayi masu ɗauke da bacci,tare da miƙewa daga zaune tana kallonshi,
Ya tasa ta gaba ya zabga uban tagumi yana ta faman zubda hawaye,gabanta ne taji ya faɗi rass ganin abusufyan na kuka da idanunshi,zuba mashi ido tayi tana kallonshi batare da tace mashi komai ba,
Cikin shesshekar kuka yace"Abu dagaske baki sona?meyasa kika tsane ni ne?
buɗe baki tayi tare da cewa"ba kaine ke bana so ba,ɗabi'unka da halayanka ne ke bana so,na tsani naganka kana mu'amala da wasu matan da sunan abokantaka,kuma natsani naganka kana sanya irin waɗannan kayan ajikinka,kuma baka da kunya abusufyan agaban kowa kake faɗin duk abunda yazo bakin ka,ni nafison kamilin mutun natsastse mai ilimin addini,'
cikin sanyin murya yace"zan canza halaye na saboda son da nake yi maki ne kawai,'
"Kayi mun alƙawarin bazaka ƙara kula wata mace ba in ba ni ba?
ɗaga mata kai yayi alamar eh yace"Nayi maki alƙawari abu,zan daina,daga rana irin ta yau bazan ƙara hulɗa da mata ba,zan kame kaina kamar yarda kikeso,zan zama irin mutumin da kikeso,'ya ƙarasa maganar yana kallon cikin idanunta,
Jinjina kai tayi tace"idan kuma ka sa6a fa?ka yadda na yanke duk hukuncin dana ga dama akanka"?
"Na amince"ya bata amsa,
Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙa hannunta ta ɗauko al'qur'anin dake ajiye asaman side drawer dinta ta miƙa mashi,yasa hannu biyu ya kar6a cike da mamakin me zaiyi da al'qur'anin da ta bashi,gabanshi ne ya shiga faɗuwa tsoranshi kar tace ya rantse da al'qur'ani don bazai iya rantsuwa dashi ba,
"Me kike nufi da wannan qur'anin da kika bani,"
Murmushi ta saki kafin tace"so nake ka rantse dashi cewa ba zaka ƙara hulɗa da wata ƴa mace ba aduniyar nan in ba ni ba,babu ruwanka da mace indai ba ƴar uwarka bace sai kuma ni da nake matarka,in kuma harka sa6a hakan na kama ka tare da wata ƴa mace zaka sake ni saki ukku!ka amince da hakan!!"
Shiru abusufyan yayi gabanshi na faɗuwa,aranshi yana zullumin amincewa da maganarta,saboda baisan halin da zai tsinci kanshi ba anan gaba,tsautsayi zai iya afkawa dashi a lokacin da baiyi tsammani ba,
"Dan Allah abu ki janye maganar rantsuwa da qur'ani,banaso kuma ma babu kyau yin rantsuwa dashi,kiyi haƙuri pls,wlh nayi maki alƙawarin bazan ƙara kula mata ba,komai zan daina,"cikin sanyin murya yayi maganar yana kallonta,
ɗaure mashi fuska tayi tare da cewa"Abusufyan dole fa sai ka rantse mun da qur_'anin nan sannan zan yarda dakai!ƙin amincewa da hakan zaici gaba da haddasa rashin zaman lafiya atsakaninmu!"
babu yarda ya iya da ita,saboda aƙagare yake da su fara kasancewa amatsayin ma'aurata tare da ita,baison 6acin ranta ko kadan,baida burin daya wuce yaga suna zaman lafiya da ita,wannan dalilin ne yasa shi yin rantsuwar da har yau yake danasaninta,
Hannu tasa tare da kar6ar qur'anin ta maida shi saman drawer ta ajiye shi,
"Yanzu zaki bani haƙƙina kenan"?ya tambaya yana kallonta,
jinjina mashi kai tayi alamar eh,kafin ta sanya hannunta tare da cire rigar jikinta,ya rage daga ita sae bra,nan fa hankalin Abusufyan ya tashi haikam da ganin surar ƙirjinta,gaba daya ya afka mata,suka manne ma juna,gaba daya suka zautar da junansu,sosai Abusufyan ya biya bukatarshi da ita,sai lokacin ta gane ba ƙaramin cutar kanta takeyi ba,na ƙin amincewa dashi tun ranar farko da aka ɗaura masu aurensu,ba ƙaramin so ya nuna mata ba awannan daren,kuka sosai abusufyan yayi mata saboda tsantsar farin cikin da yaji na kasancewarshi mutun na farko daya fara kar6ar budurcinta,
Tun daga wannan lokacin soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninta dashi,saboda irin tarairayar da yake yi mata,da kuma irin kulawar da yake nuna mata,kullum yana tare da ita yana faranta mata,da kanshi yake kaita school sannan ya wuce tashi makarantar,idan an tashe su shi yake zuwa yaje ya ɗaukota ya kaita gida,tamkar romeo da juliet haka suka koma,har acikin mota soyayya suke sha,idan tana aiki a kitchen haka zai bita yana tayata aiki,gyaran ɗakinsu duk shi ke yi in yana gida,hatta gugar kayan makarantarta shi ke zama ya goge mata su,duk wannan soyayyar da suke sha akan idon Hajiya Ameenatu,dama itace ta bama soyayyar tasu wurin zama,in taga sunyi kwana biyu basu fita yawon shakatawa ba,da kanta take ɗauko kudi tabasu tace su tafi shan ice cream,ko suje suyi siyayyar abunda suke so,shi dai Alhaji nuraddeen har lokacin zuba masu ido kawai yake yi,mahaifin abu kuwa baba buzu mai gadi,hankalinshi ba ƙaramin kwanciya yayi ba,ganin yadda Abusufyan ke kular mashi da yarinyarshi,yanzu baida sauran damuwa sae fatan cikawa da kyau da IMANI,
Bayan wata guda da sati uku da yin auransu..................
Suna zaune a cikin class ɗinsu na islamiyya,ƙawayenta na kewaye da ita,tana basu labarin irin soyayyar da suke sha ita da abusufyan ɗinta,dama bata da wata magana sai ta Abusufyan,suna cikin firar nan sai ga malamin nan nasu sayyadi ya faɗo cikin ajin a fujajen yana ta faman huci,suna haɗa ido da abu ya kwaɗa mata kira"Zo nan zainab,"
ƙin zuwa tayi sai da wata ƙawarta tace mata"Abu kije ya sayyadi na kira,"ba don taso ba ta miƙe tare da zuwa inda yake,waje suka fita daga gefen ajin nasu,
"Yanzu abu kin kyauta abunda kikayi mun?kawai sae dai naji agari an ɗaura auranki da abusufyan"? Muryar shi tamkar zaiyi kuka yayi maganar,
"Dama Allah ya ƙaddara cewa kai ba mijina bane Sayyad,Abusufyan shine mijina,don haka ina baka haƙuri kuma ina yi maka fatan Allah ya baka mace tagari wadda ta fini,"tana faɗin hakan ta juya zaka koma class cikin sauri yasha gabanta tamkar zai rungumeta,ɗan ja da baya tayi tana kallonshi a tsorace,
Rai amatuƙar 6ace yace"Zainab!kada kiyi mun haka kin manta alƙawarin da mukayi ma juna,zamu yi aure mu haifi ƴa'ƴa mu tarbiyantar dasu atare?abu ni fa kikeso ba Abusufyan ba?me zakiyi da namiji mai bin mata?ke da kanki kika sanar dani cewa Abusufyan mutumin banza ne mai hulɗa da mata,kuma bai da tarbiyya sannan baida ilmin addini rayuwar turae yasa agaba bai damu da addinin shi ba....'
Abu tace"hakane ni na faɗa maka haka da bakina,tabbas munyi alƙawari dakai sai gashi Allah bai nufa ba,tunda bani ke iko dakaina ba,mahaifina shiya za6amun Abusufyan kaga dole nayi masa biyayya,malam kaida kanka kake yi mana nasiha akan mubi iyayenmu muyi musu biyayya,don haka bai kamata kaga laifina ba,don nabi umarnin mahaifina ba,sannan zancen cewa abusufyan na bin mata,rashin sani ne yasa nayi mashi mummmunar fahimtar nan,amma ni mijina baya bin mata,abusufyan mutumin kirki ne,yana mu'amala da mata amma bai ta6a kusantar su da sunan aikata zina ba,iya friendship yake yi dasu,maganar ilmin addini kuwa abusufyan shima malami ne mai zaman kanshi,da farko na dauka boko ya sanya agaba,amma yanzu nagane cewa yana da ilmin addini sosai,bai cika bayyanawa bane agaban mutane,amma shi da kanshi yake ƙara mun karatun hadda in aka bani a makaranta,kuma yana tashi na muyi sallar dare dashi,kuma muyi karatun alƙur'ani atare.......'
Tunda tasoma magana sayyadi ke