Showing 162001 words to 165000 words out of 432432 words
Chapter 55 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
ni nama rasa wadda zan za6a maka acikinsu,saboda kowacce kasa acikinsu kyau zatayi maka,bakasan cewa kaine keyi ma kayan kyau ba"? Tayi maganar tare da ɗan juyawa tana kallon junaid dake tsaye yana ta faman sakin murmushin jin daɗin yarda sehrish ke hura mashi kai,
ta jima tana ruwan ido kafin ta cankar mashi wata haɗaɗɗiyar shadda gezner Ash colour sai faman salƙi take yi, mika mashi tayi tare da cewa"Wannan tayimun sosai kuma ina da tabbacin cewa in har ka sanyata ajikinka,sai uncle abusufyan ya razana da ganin irin kyan da zakai,'
Kar6ar shaddar yayi daga hannunta yace"thank u so much reesh,amma fa ba yanzu zan sanyata ba,sai zuwa anjima in zanzo ɗaukarki daga school zaki ga kalar wankan da zan ɗauka,"
murmushi tayi tare da kama hanyar fita daga cikin bedroom ɗin nashi tana cewa"Allah ya kaimu lafiya,yanzu dae zan jiraka,in ka kammala shirin ka fito mu tafi kar nayi late,'
Amsa mata yayi da toh,bayan ta fita ya tattara shaddojin duka ya mayar acikin wardrobe ɗinshi, ya zaro wasu jeans da t-shirt ya shiga zura su ajikinshi
_💋Boss Bature💋_
Lokacin da sehrish ta koma kitchen ɗin bata samu Azmee ba,sae dae Hayaam ta samu acikin kitchen ɗin,tana atsaye ta ruƙe qugunta kamar mai jiran wani abu,
Ganin sehrish yasata cewa"Sannu ko"
firgit Sehrish tayi tare da kai idonta inda hayaam ta ke atsaye tana sakin wannan shu'umin murmushin nata,
"Yawwa"ta amsa mata atakaice tare da wucewa wurin trayn da azmee ta ajiye mata saman table wanda ta shirya ma sgr breakfast ɗin shi aciki,hannu biyu tasa ta ɗauki tray ɗin sannan ta kama hanya tare da fucewa daga kitchen din,hakanan ta dinga jin kamar bata yarda da hayaam ba,anya ba wani abu takeyi acikin kitchen ɗin ba?in ba haka ba meyasa ta tsaya atsaye ruƙe da qugu,kamar mai jiran wani abu,
haka tayi ta wasiwasi acikin zuciyarta har ta ƙarasa part ɗin sgr,
Sallama ta fara yi mashi,jin shiru ba'a amsa mata ba,yasa tayi tunanin ko yana acikin bedroom ɗinshi ne,
A hankali tasanya kafarta tare da shigewa cikin palourn komai agyare tsaf ta same shi,asaman table ta aza mashi tray din sannan ta tsaya tana jiran fitowarshi ko zai bukaci wani abu,
tana cikin tsayuwar nan tajiyo muryarshi daga cikin bedroom ɗinshi yana tambayar wanene anan!"
Cikin sauri tace"Ni ce,dama breakfast ne na kawo maka,"
kusan minti biyar da yin maganarta sannan taji yace"A shigo min da coffee shi kawai nake buƙata,"
murmushi ta ɗanyi tare da mika hannu ta ɗauki cup of coffee ɗin dake acikin kayan breakfast ɗin nashi,ta nufi bedroom ɗin hannunta ɗauke da cup ɗin,
sai da ta tsaya abakin ƙopar shiga Sgr ya bata izini sannan tasa kai tashiga,wani irin daddaɗan kamshin turarensa ne ya bugi hancinta,nan take taji wani irin yanayi atattare da ita,
lumshe donta tayi tare da buɗesu a hankali ta kallo inda sgr yake, a hakimce ya ɗan kishingiɗa daga gefen katafaren gadon nashi,
Gaza janye idanunta tayi daga kallon kyakkyawar surar jikinshi,wankan daya ɗauka ba ƙaramin fisgarta yayi ba,white trouser ne na suits amma bai sanya coat ɗin sama ba,iya vest ɗin ciki ya bari tabi shape ɗin jikinshi,daga ƙasan vest ɗin ta ɗan tattare hakan ya bayyana farar fatar shafaffen cikinshi, ya harɗe kafafunshi wuri guda yayin da idanunshi ke a lumshe,
tafiya take tana tunkarar inda yake idonta akanshi har ta ƙarasa tare da ajiye mashi cup ɗin asaman bedside table ɗinshi tace"Gm sir,ga coffee nan na kawo maka,ko akwai wani abu da kake buƙata"?
Bai amsa mata ba,a hankali ya dan buɗe idanunshi sannan ya yunƙara tare da miƙewa daga zaune ya sauko da ƙafafunshi ƙasa,
Zaki iya tafiya,ya ambaci hakan ayayin da yakai hannu tare da ɗaukar kofin coffeen yakai bakinshi yana kur6ar shi anatse,
Juyawa sehrish tayi ta kama hanyar fita daga bedroom ɗin a hankali,ji take kamar karta tafi ta barshi,don bata gaji da kallon kyakkyawar fuskarshi ba,
Yana cikin shan coffeen nan wani abu ya sarƙe mashi adaidai saitin throat ɗinshi,a hanzarce ya ajiye cup ɗin tare da zura fingers ɗinshi guda biyu cikin bakin cikin sa'a ya ruƙo siririn abun,
Lokacin daya fiddo da abun daga bakin nashi yayi arba da dogon gashi,ware idanunshi yayi, hankali a matukar tashe yana kallon gashin yace"in my coffee...!
Jin wannan maganar tashi yasa sehrish saurin juyawa don taga menene,a lokacin har tasa ƙafa zata fita daga ɗakin,
Gabanta ne taji yayi wani irin mugun buga ganin siririn gashin da Sgr ya ruƙo a hannunshi,
Yunkurin amai yashiga yi,nan take ya miƙe da saurin gaske ya faɗa toilet,kai tsaye ya ƙarasa gaban basin yana kwarara aman,tamkar ƴan hanjin cikinshi zasu fito,kasancewar shi mutum mai tsaftar gaske ga ƙyanƙyami ya tsani ƙazanta a rayuwarshi duk mun ƙankanta,ranshi ba ƙaramin 6aci yayi ba,gashi a abun shansa kuma har ya shiga bakinsa!!,a wannan lokacin komai zai iya aikatawa he can't even control him self, cos he has a very bad temper,kuma ta motsa.
Tap ya kunna,ruwa yashiga zubowa yana kora vomitting ɗin da yayi,sannan ya tarba tafin hannayenshi biyu tare da ɗebo ruwan ya watsa su a fuskarshi yana faman sakin huci,
Sehrish dake atsaye abakin kopan bedroom ɗin nashi,jikinta sai faman kerma yake yi,gaba daya tabi ta rikice kan ta ya gama ɗaurewa,taya akai aka samu gashi acikin abun shan Sgr?ita dae tasan cewa ba gashin kanta bane,saboda ta sanya hijab ajikinta,hasalima ba ita bace ta shirya mashi kayan breakfast ɗin nashi ba,tunkan taga hukuncin da zaiyi mata har tafara matsar kwalla,don tasan bazai ƙyale ta ba,dole ya hukunta ta,
A fusace ya fito daga cikin toilet ɗin,sai faman huci yake yi,ɗagowa yayi da idanunshi yana kallon inda sehrish take atsaye jikinta sai kerma ya keyi,tunda taga zufa na gangarowa a gefen fuskarshi, ta ƙara tsorata sosai,
tamkar wani zaki haka ya tunkaro ta,a tsananin tsorace sehrish ta shiga ja da baya tana girgiza kai cikin shessheƙar kuka take cewa"wlh bani da masaniya akan gashin nan,banawa bane bansan ya akai ya shiga cikin abun shanka ba,'
wata irin tsawa da Sgr ya daka mata nan take sehrish ta firgita agigice take zazzare ido tana kallon fuskarshi,
biting lips ɗinshi ya shiga yi,yama rasa wane irin punishment zaiyi mata,
Nuna ta da dogon yatsan sa yayi tare da cewa"as from today!bana son na ƙara ganinki a part ɗina!'
Cikin shessheƙar kuka sehrish tace"Am really sorry babban yaya........ba laifi na bane bada sani na gashin ya faɗa aciki ba..........'tun kafin ta ƙarasa maganar ya ɗaga hannunshi da nufin ya sharara mata mari,runtse ido sehrish tayi tana jiran jin saukar marin nashi a kuncinta,
ji yayi bazai iya ba saboda tunda yake arayuwarshi bai ta6a gigin ta6a jikin wata ƴa mace ba da sunan bugu,tun suna yara Abbansu ya hane su da yin wannan,kullum yana tunasar dasu akan su dinga daraja ƴa mace,
Dunkule hannunshi yayi tare da yarfar dashi gefe guda,sannan yace"Get out from my bedroom!since before I show u my true colour!,
ya ƙarasa maganar tare da juyawa yabarta tsaye anan tana faman shessheƙar kuka,
Ji tayi bazata iya jure hukuncin da Sgr yayi mata ba, na hanata aiki a ƙarkashin shi ba,
gaba ɗaya jikinta ya gama yin sanyi, a wani irin yanayi ta zube asaman guiwowinta,cikin sanyin murya,muryarta na rawa tace"nasan na 6ata maka rai sosai,na cancanci kowane irin hukunci daga gare ka,amma ina neman alfarma a wurin ka........'dakatawa tayi da maganar tana kallon bayan shi daya juya mata,
ganin ya tsaya da yin tafiyar yasa ta gane cewa ita yake sauraro,
anatse taci gaba da magana"ka yanke mun kowane irin hukuncin daya dace da laifin dana aikata,amma kada ka hanani yin aiki a ƙarkashinka,wannan horon yayi mun tsauri sosai,bazan iya jurewa ba,tun da nake maka aiki banta6a yin irin wannan gangancin ba,ina kiyaye wa sosai wurin ganin na tsaftace duk wani abu da zan kawo maka kaci ko ka sha,ba zanso wani abu da zai cutar dakai ba,wannan ma bansan ya akai hakan ta faru ba,don Allah kayi haƙuri ka yafe mun............'ƙarasa maganar tayi cikin shashsheka yayin da hawaye ke cigaba da zuba a idanunta,
shiru Sgr ya ɗanyi na wani lokaci batare da ya motsa ba,hakan yasa ta fidda rai da cewar zai yafe mata,
Hannu tasa tana sharar hawayenta tana kallon bayanshi,cigaba da tafiya sgr yayi kai tsaye ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,hannu yasa tare da janyo drawer chest din dake ajikinshi,sabon scissors ya ɗauko cikin ledarshi, ya fiddo dashi yana kallonshi,
lokacin daya juyo hannunshi ɗauke da almakashin nan,hankali atashe sehrish ta zaro ido tare da miƙewa tsaye daga kneel down ɗin da tayi tana ja da baya tana girgiza mashi kai,alamar karyayi mata haka,
Gadan gadan Sgr ya tunkare ta,hannunshi ɗauke da almakashin nan sai faman salƙi yake yi,hannu sehrish ta aza asaman kanta tana cewa"Nashiga uku!innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..........dan Allah kada ka datse mun gashin kaina ......'tana magana tana ja da baya yayin da shi kuma yake tunkararta,abu kamar wasa haka suka shiga zagaye ɗakin yana binta tana ja da baya,a ƙarshe daya fusata a zafafe ya damƙo hijabin dake jikinta tare da tun6uke ta daga jikinta yayi wurgi da ita gefe guda,yarda ya fusge hijabin daga jikinta gaba ɗaya ta tafi zata faɗi kasa,yakai hannu tare da janyo ta ta faɗo saman wide chest ɗinshi,kuka take kamar ranta zai fita saboda ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nan nata ba,ta kwallafa rai akanshi shiyasa kullum take ƙokari wurin gyara shi,har tasamu tatara shi da yawa bayan yanke shin da akai da zata fara aiki gidan,gashi yau akan kuskuren da ba ita ta aikata ba,za'ayi mata aski tana ji tana gani ba yarda zata yi,
tunda sehrish ta faɗa jikinshi gaba ɗaya ya rasa duk wani kuzari na jikinshi,ƙamshin turaren jikinta ba ƙaramin kashe mashi jiki yayi ba,abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,a hankali yakai hannunshi tare da Cire ribbom ɗin da ta ɗaure gashin kanta dashi,ya warwaro shi duka tare da yin wurgi dashi gefe guda ya fadi kasa saman hijab ɗinta,
Nan take lallausar suman kan nata mai laushin gaske ya tarwatse abayanta yayi mata tamkar hijabi,
Ai ina baku labari tunda boss man ɗin nan ya zura hannunshi acikin sumar kanta nan fa yashiga murza gashin acikin hannunshi,laushin gashin kan nata ne yake fisgarshi har yayi hakan batare da saninshi ba,
A hankali ya russinar da kanshi tare da kai tsinin hancinshi saman sumar kanta yana shaƙar daddaɗan kamshin dake fitowa daga cikin sumar kan nata,wani irin bugu zuciyarshi tashiga yi da sauri sauri take harbawa,
ƙankame shi sosai sehrish tayi ta hanyar zagayo da hannayenta abayan waist ɗinshi ta ruƙo shi sosai kamar wani zai kwace mata shi,ba ƙaramin yanayi ta jefa Sgr ba ta kara sanya mashi kasala ajikinshi,kamar yarda itama ta shiga yanayin,tunda ta lafe mashi ajikinshi tayi lamo,wata irin natsuwa ta ji
da bata ta6a ji ba atattare da ita,shessheƙar kukan nan da takeyi gaba daya ta neme ta ta rasa,tsit tayi tana sauraron heart beat ɗinshi,
Suna cikin wannan yanayin na shauƙi sai ga Abbansu ya faɗo cikin part ɗin nasa yana neman shi,ganin baya acikin falon yasa ya wuce izuwa bedroom ɗin shi,tunkan ya ƙarasa ya hange su manne da juna kamar tip da tyre, adaidai ƙopar shiga bedroom din nashi,abban nasu ya tsaya cike da mamaki yana kallon wannan abun al'ajabin,ko motsi basa yi,bakomai yafi ɗaure mashi kai ba,face yarda sgr yake cakuɗa sumar kan yarinyar acikin hannunshi sai faman murzar gashin kan nata yake,ga kuma hancinshi daya cusa asaman kan nata yana shaƙar kamshin da sumar kan nata ke badawa mai daɗin gaske,
Ita kuma ta ƙankame mashi qugunshi da hannunta,ta kwantar da kanta asaman chest ɗinshi,
baki asake Abbansu ke kallon wannan tashin hankali,jinjina kai ya shiga yi cikin ranshi yana cewa"Oh ni hussein!tun yaushe wannan al'amarin ya soma faruwa acikin gidan nan batare da sani na ba!Hmmmm yanzu haka zare mata ido yakeyi yana tsoratar da ita don ya samu abunda yake so,nasan maganinka Rafayet,"ya faɗi hakan tare da kama hanya yabar part ɗin nashi fuskarshi ɗauke da murmushi,don shi wannan abun farin ciki ne awurinshi,ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don tsabar farin cikin ganin rafayet tare da mace,baida burin daya wuce wannan arayuwarshi,shi dae yaga Sgr yafara kula mace da sunan soyayya,yau dae gashi Allah ya nuna mashi,
Janye hancinshi yayi daga cikin sumar kan nata,sannan ya tattaro gashin nata tare da sanya almakashin ya datse mata shi,sosai ya yanke gashin,yabar mata guntu wanda ko kafaɗarta bai sauko ba,'
hankali a matuƙar tashe sehrish ta raba jikinta da nashi, da sauri takai idonta akan hannunshi dake ruƙe da dogon gashin daya yanke mata,kamar a mafarki take kallon gashin nata daya yanke mata,
A hanzarce takai hannu tare da shafo kan nata don taji sauran daya rage mata,
Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita,dakyar takai hannu tare da ɗaukar hijab ɗinta, sannan ta juya tare da watsawa aguje tana kuka ta fuce daga cikin ɗakin nashi,
ajiyar zuciya ya sauke tare da takawa izuwa gaban dressing mirror ɗin nashi ya mayar da scissors ɗin aciki tare da gashin kan sehrish daya datse,duka ya tura shi aciki ya ajiye,sannan ya maida drawer chest ɗin ya rufe,
Komawa yayi tare da haye wa saman gadonshi ya kwanta,yanayin da bai ta6a ji ba atattare dashi ba yake ji,tsananin tausayinta ne ya kama shi,har ya dinga jin tamkar baiyi mata adalci ba daya datse mata gashin kanta,ya lura ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nata ba,lumshe idanunshi yayi a hankali yana tariyo abunda ya faru tsakaninta dashi,especially lokacin da ta watsa da gudu tana kuka,duk baiji daɗi ba saboda shi baiyi mata hakan da nufin ya 6ata mata rai ba.
*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖
Saboda masu complain, nacewa nace zan tura da safe ban turo ba,Allah ne bai nufa zan tura da safen ba,
Ga half page nan,later zan tura sauran
komawa cikin bedroom ɗinta tayi tana ta faman sharar hawaye ranta na kuna,wuri ta samu ta zauna daga gefen gadonta tana ƙarashe kukan nata,babban takaicinta guntun gashin da Sgr ya bar mata da kyar in zaiyi parking da ribbom,koma yayin ba lalle ribbom din ya tsaya ba,ta jima tana azaune tana matsar kwallar bakin ciki,kafin daga bisani ta miƙe tare da nufar wurin dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta acikin madubin,cikin shessheƙar kuka tace"Meyasa bai aske gashin duka ba yabarmun kwalkwali?me zanyi da guntun gashin nan daya barmun?ban son gashin!na tsani ganin shi,'ita kaɗae take ta faman sambatu rai atsananin 6ace,
Kwankwasa ƙopar ɗakin nata akai,a tsiwace tace"Wanene"!
Muryar junaid taji daga waje yana cewa"It's me junaid,tun ɗazu fa nake jiranki,ki fito mu tafi na sauke ki,'a ƙagare yake maganar don ya gaji da jiranta,
Ita gaba ɗaya ma ta manta da batun zuwa makarantar,sai da junaid ya tunasar da ita,
hannu tasa tana share hawayenta tace"junaid ka jira ni,acikin mota yanzun nan zan fito,"
Amsa mata yayi da"Okey," sannan ya juya tare da barin kopar dakin nata,
Sai da tafara shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fito tare da ɗaukar hijab ɗinta dake ajiye gefen gadon ta zura ajikinta
Cikin sauri ta fito ɗauke da school bag ɗinta,ta fice waje wurin harabar ajiye motocinsu,hannu tasa tare da buɗe motar junaid ta shiga daga ciki ta zauna,
ɗan kallon fuskarta yayi tare da cewa"Reesh,na jima ina jiranki,bansan me ya tsayar dake ba,gashi ma har kinyi late,ina fata dae lafiya?"
daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa"lafiya lou ba wani abu,mu tafi kawai ina ƙara makara,"
ajiyar zuciya ya sauke tare da jan motar suka bar gidan.
Ita kuwa Hayaam dama tunda taga Sehrish ta nufi part din sgr da coffeen ta sulale ta shige dakinta don kar a gano abunda ta aikata.
*HOSSANA*
Zaune take saman gadonsu ta takure kanta sai faman shessheƙar kuka takeyi,ta sanya uniform ajikinta amma taƙi tashi ta zura hijabin,ta hana kanta duk wani jin daɗi,
Fitowa jahad tayi daga cikin toilet tana kallonta gwanin ban tausayi tace"Hossana,dan Allah kidaina wannan kukan,duk kinbi kin takure kanki,ni nasan cewa ƴa omar ba hakanan ya daina zuwa wurin mu. Ba,Abubuwane suka yi mashi yawa shi ya sanya bai samu halin zuwa ba,'
muryarta na rawa tace"jahad ba zaki gane bane,bazan ta6a samun kwanciyar hankali ba in har bansa ya omar a idona ba,Allah in har baizo ba yau,zanci shinkafar 6era ne na mutu kowa ya rasa,'
dariya jahad ta fashe da ita,hakan yasa hosana ɗaure fuskarta tana jifarta da harara tace"jahad dariya kike mun ko?
tsagaitawa tayi da dariyar tana girgiza kai tace"hosana dole nayi dariya,shinkafar 6era fa kika ce?
ɗaure fuska tayi tana murguɗa mata baki,
Murmushi kawai jahad tayi tare da komawa wurin closet ɗinsu,ta buɗe tare da ciro uniform ɗinta ta shiga zura su ajikinta,shaf shaf ta kammala shiryawa,ta ɗauko school bag ɗinta,sannan ta dawo wurin hosana tace"tashi mu tafi kada mu makara,"
Girgiza kai hosana tayi tace"Jahad ku tafi kawai,ni zan zauna a gida,saboda ko naje ba gane karatun zanyi ba,'
Zuƙunnawa jahad tayi agabanta tace"pls hosana ki daina sa damuwa aranki kinji?ni da kaina yau zan nemo maki ya Omar,'
jin abunda jahad tace yasa hosana sakin murmushi tace"dagaske Jahad"?
ɗaga mata kai tayi alamar eh tace"nayi maki alkwarin,duk inda yake indae yana acikin garin nan saina nemo maki shi,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hosana,jiki na rawa ta tashi ta ɗauko hijabinta bayan ta zura safarta da takalmanta suka fuce atare,
A waje suka samu motar osman na jiransu,bayan sun shiga ya tashi motar ya fuce dasu daga cikin gidan,hosana sai murna take jahad tace zata nemo mata Omar,batasan cewa ita da wasa ta faɗa mata ba don ta sanyata farin ciki ne