Showing 93001 words to 96000 words out of 432432 words
Chapter 32 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
pink lips dinta saboda shock ɗin da takeji na sofwan dake bin jikinta da hannun shi yana shafa ko'ina,Auntyna indae ni ce just karki samu damuwa,ki ƙaddara cewa gani can ma acikin gidan ina watayawa ta,ita kuma wannan yarinyar da kika sanar mun cewa tana zaune a gidan tuni zansa su yi mata checking out badai ni bace ba hmmmmmm,
Dariya aunty babba ta saki tare da cewa"har naji sanyi araina,burina na dab da cika,"
Download>>> Yar Harka Complete Document
Sun jima suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama da junansu,
Buge hannun sofwan tayi tare da cewa"duk kabi ka takuramin wai kai wani irin jarababben mutun ne mai nacin tsiya haba mtwww,"taja dogon tsoki
Baki asake yabi ta da kallo tare da cewa"ni kike ma tsoki wai?wato wannan haɗamammar auntyn taki takira duk ta tunzuraki akan abunda bazai ta6a faruwa ba,duk naji mai kuka tattauna da ita,
ya fadi yana faman sakin hucin 6acin rai,murmushi hayaam ta saki tare da cewa"Sofwan zamana dakai ya ƙare!!!!!!!
�?
Zaro ido waje yayi yana kallonta hankali atashe yace"saboda me hayaam?kada kiyimun haka don Allah!amma dae nasan wasa kike mun ko?
ƴar dariya tayi kafin tace"na ta6a maka wasa irin wannan?zanje na nemi namijin duniya ne!cikakken namiji jarumin gaske wanda ya kasance burin kowace ƴa mace ne shi bazanyi gangancin rasa cikar burina ba sofwan.......
Bata ƙarasa ba ya dauke ta da mari ji kake faaaauuuu!
Rai a 6ace yace"Wlh baki isa ba hayaam ki katse mun jin daɗina ba!!saboda ke dakikiya ce sam bakisan meke maki ciwo ba wannan wani irin abun kunyane zaki kwasa kawai ki koma gidan surukanku da zama?Anya kuwa yayarki ba mahaukaciya bace.....
bata bari ya ƙarasa maganar tashi ba ta zame hannunta data dafe kuncinta dashi ta daddage ta zabga mashi zafafan maruka har guda uku sannan tace"karka kuskura ka ƙara kiran auntyna da sunan mahaukaciya!!maganar tafiya kuma ba fashi sofwan inka ga ban tafi ba to wlh numfashi na ne ya tsaya don ko ba ƙafa saina je,😳
Tuni sofwan ya rikice ganin yarda hayaam ta zabga masa mari batare da jin komai ba,duk irin yarda yake tarairayarta don karya rasa ta amma lokacin guda auntynta ta canza mata tunaninta,
Kallonta ya shiga yi yana girgiza mata kai yayin da idonshi suka cicciko da kwalla muryarshi a kasalance yace"Hayaam kada kiyimun haka dan Allah!saboda ke na wulaƙanta iyayena na baro komai nawa don muyi irin rayuwar da kikeso,wannan gidan fa duk don saboda ke na gina shi hayaam,ki duba gidan da iyaye na suke ciki duk ya rakwakkwa6e amma saboda ke na gidan wannan katafaren gidan ko don saboda wannan pls hayamm kada kibarni komai kikeso zanyi maki shi," yayi maganar tare da zubewa saman guiwowin shi a gabanta yana faman sharara hawaye,amma maimakon yaga alamun tausayi a idonta saima ta fashe mashi da dariya tashiga tafa hannaye tana cewa"sofwan kaifa dakanka kace ka wulaƙanta iyayenka saboda Ni?shin ni wacece a wurinka?mutumin da bai daraja iyayensa ba musamman uwarsa data tsugunna ta haifeshi taci baƙar wahala kanshi!ga kuma mahaifinsa daya fitar da gumi wurin nema masa kyakkyawar rayuwa duk bai duba wannan ba,burinka kawai ka farantama wasu can waɗanda basu son ciwonka ba,waɗanda ko yau ka faɗi ka mutu wlh shewa zasu yi suce Allah raka taki gona,shine har kake mun kwatance da ka wulaƙanta iyayenka don saboda wata banza can Ni?hanyar Aljanna nake sanya ka kota wuta?ko zan taimake ka ne ranar lahira?sofwan haƙƙin iyayenka ma kawai ya isa ya tarwatsa dukkan wani farin ciki na rayuwarka!!idan ma naci gaba da ra6arka nima zan shiga matsala ne don haka kawai muyi break up kawai kowa yayi rayuwarshi,"
ta ƙarasa maganar tare da ruƙe waist dinta tana kallon shi a tsiyace,
Miƙewa yayi daga kneel down din da yayi ya kalleta da fuskar tausayi yace"kada kiyi mun haka hayaam indae alaƙata da iyayena ne zan gyara komai...'
girgiza mashi kai tayi tare da cewa"na yaushe sofwan?hmmm ba don Allah zama kayi masu ba sai don saboda ni abanza kam,shiyasa koda yaushe soyayyar SGR take ƙara ninkuwa araina duk da irin tarin dukiyar dake gare shi hakan baisa ya canza ma iyayenshi ba ko wani nashi,zokaga Namijin gaske mai tsananin biyayya ga iyayensa wanda yasan darajarsu yake binsu sau da ƙafa kaifa? Har yau mahaifinka bai daina siyar da kifi a gefen titi ba, ga Mahaifiyarka cen kullum safiyar Allah sai tafito da murhu kopar gida tana suyar ƙosar da kunu,taya ma zan cigaba da kasancewa dakai!!? Kana da arziƙin da zaka iya ciyar da karuwai ka gina ma iyayensu gida ka kuma gina masu su kansu Amma iyayenka fa!!!?
shiru Sofwan yayi yana kallonta idanun shi sunyi jawur dasu ga wani ƙululun baƙin ciki daya tsaya masa a maƙoshinsa,
Wuce wa hayaaam tayi wurin wardrobe dinshi saboda anan kayanta suke nasawa, hannu tasa ta buɗe wurin kayanta tana raira waƙar nan ta namej dayake cewa"ko babu mota ba abun hawa wlh saina jee,"
A wani irin fusace Sofwan ya cafki hannunta data ruko bra dinta dashi,dakatawa tayi da yin waƙarta ta tace"Malam sakarmin hannu na,"
Yana wani irin huci yace"Hayaam baki isa kibar gidan nan ba, batare da kin mayar mun da duk wani abu dana kashe maki ba!!wlh bazaki ci bulus ba,duk kin taƙaitani duk ƙarshen wata saina kawo maki kayan abinci kwalin indomie kwalin taliya da sauran kayan abinci, sannan duk ƙarshen sati muna zuwan shopping mall dake nayi maki siyayya kuma mu fita restaurant cin abinci,ga kuma kuɗin mayukan da nake siya maki su kansu kudinsu yakai na dubu dari biyar,in kin ga kin bar gidan nan to ki tabbata kin haɗa mun kuɗaɗe na kin mayar mun dasu," ya ƙarasa maganar yana jifanta da wani irin kallo,
ta6e baki tayi tare da cewa"Naji duk zan biyaka ni kuma da me zaka biyani jikina da kayi amfani dashi?donni ma bazaka Ci bulus ba tunda ba uwar mutun ta haife ni ba,ka biyani budurcina nima saina biyaka kudinka"A shagale take maganar tana faman sakin murmushi,
Shiru sofwan yayi yana faman mazurai aransa yana tunanin taya zai biyata virgin dinga da take magana akai?
tsoki taja tare da buge hannunshi tabar shi tsaye a wurin ta koma daga gefe tana zura brazier dinta,
Muryarshi ce ta kuma katse ta da cewa"naji wannan tabbas bazan iya biyanki budurcinki ba,amma inaso ki sani bazan bari ki ɗauki ɗaya daga cikin abunda nasiya maki ba da kudina,daga ciki kuma hada kayan sawa don dama a tsiyace kikazo gidan nan,
Download>>> Babban Yaya Complete Document
harara ta wurga mashi tare da cewa"Matsalarka ce wannan!ae ni abun kunya gaba na bashi ba baya ba,in ka hanani sa sutura sai in tafi a zir abuna,"
ganin tana shirin ɗaura mashi hawan jini yasa shi buga jikin wardrobe din da hannunshi yana kallonta idonshi jawur rai a tsananin 6ace ya fuce yabar mata ɗakin gaba daya,
Murmushi tasaki tana cizon la66anta aranta tace"ƙaramin ɗan duniya har ni zakayi wa barazana,"
*******************
Tsare ta da ido hafsat tayi wadda shigowarta kenan bedroom din ta,
Ta jima a la6e tana sauraron firar da mommyn nata keyi da Hayaam a waya, sai da tabari ta kammala sannan tashiga daga cikin ɗakin tana kallonta, tunkan tace wani abu aunty babba tayi saurin cewa"to ƴarsa ido uban me yakawo ki dakina?
murmushin takaici hafsat tayi kafin tace"narasa meke damunki mommy!gaba daya naji wayar da kikayi da aunty hayaam,saboda me zaki ce ta tattara kaya ta koma gidansu Abbana da zama?wannan wane irin abun kunya ne ace ƙanwar matar yayansu tana rayuwa acikin gidansu? menene alaƙarta dasu?gsky wannan tsarin sam baiyi ba mommy yakama ki dakatar da hayaam daga zuwan gidansu........'
tunkan taƙarasa aunty babba ta kwatsa mata tsawa tare da cewa"munafuka!!ashe la6e kikeyi mun ni narasa gane meke damunki hafsat!!tunda waɗancan yaran da omar yakawo mun suka zo gaba ɗaya duk sun canzamin ke, yanzu bakya goyon bayana......' Tana magana tana yin nuni da hannunta dake ruke da wayarta,
ta6e baki hafsat tayi tare da cewa"Mommy kenan,mgnr da kika faɗa gaskiya ce,Jahad da hossana ba ƙaramin sauyani su kayi ba saboda akansu na fara tausayin wani dan adam a duniya,sun goga mun kyawawan ɗabi'unsu da halayansu waɗanda ke baki ta6a gwadamun ba,haƙiƙa nayi rashinsu sosai kuma ina fata Allah ya ƙara hadani dasu wata rana.....' murya asanyaye tayi maganar,
Sakin baki Aunty babba tayi tana kallonta kamar me son gano wani abu can dae tace"Hafsat kodae kece kika sa Abbanki ya hanani zuwa abuja ganin jikin fawan?ina zargin hakan!!
kaitsaye tace"Nice mommy!ni nasame shi na roƙe shi akan cewa kada yabari ki tafi ke kaɗai sai tare dani saboda bana jin daɗi yanzu bazan iya zuwa ba,"
a fusace tace"Meyasa"!
Murmushi hafsat tayi tare da cewa"Saboda ba don Allah zakije ba!bakuma don kije duba jikin fawan ba face donki je ganin yarinyar da Aunty Amani ta sanar dake, ni kuma gsky bana son ma ki ganta balle har kiyi yunƙurin cutar da ita, don kuwa bazan sake bari ki cutar da wani ba saboda wani buri can da kike dashi wanda bazai ta6a cika ba.......'
Da gudu hafsat ta fuce daga dakin ganin yarda Aunty babba ta zabura zata cafkota takai mata bugu,'
bedroom ɗinta ta koma tana faman tiƙar dariya hadasu dafe ciki,
Ita kuwa aunty babba tuni idonta sunyi jawur saboda 6acin rai,tama rasa me zatayi ta huce,ashe hafsat ce ta hana ishaq barinta taje abuja yau lallaikam zata ci ubanta ne dani take magana,
Ta fadi tana faman huci,
*********AFTER 2WEEKS************
*Bayan Sati uku*
Tuni jikin fawan ya ɗan murmure yaji sauƙi sosai har yana iya miƙewa ya taka yaje inda yake so hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,a 6angaren su twins kuwa murna har ba'a magana saboda alert ɗin kuɗin da mommynsu ta turo ta wayar jahan a cikin dollar acct dinsa, a tsakar dare alert din yashigo a lokacin suna maƙale da juna kamar yadda aka saba,gaba ɗayansu suka buga shewa cikin jin daɗi ba don komai ba sai don zasu rabu da matsin Haroon su huta,a daren ranar har nafilar dare sukayi atare suka roƙi Allah akan ya yaye masu masifar dake damunsu, sun sha kuka kamar kamar me,sannan kuma sun shirya zuwa bank domin su kar6o masa kuɗinshi miliyan tamanin su damƙa mashi,😣 dama sai zarya yake yi masu kullum safiyar Allah yana musu barazana,ba don sun nuna mashi kuɗin ba dake cikin acct dinsu ba ya gani awayarsu, da bazai ƙyalesu ba,
DOWNLOAD: "HARIJI BOOK 1 COMPLETE DOCUMENT"
A 6angaren Hossana da Jahad kuwa hmmmmm just speechless,wata irin rayuwar hutu da jin daɗi suke gudanarwa acikin hamshaqin gidansu,babu ruwansu da kowa su biyu abunsu sai Camillah dake yawan zuwa dubasu wani lokacin takan tsaya ta kwana ma acikin gidan,ba ƙaramin gyarasu tayi ba,domin kuwa sun canza fiye da tunanin mai tunani,fatarsu kanta abun kallo ce, ga wasu irin surorin kyau da suka bayyana ajikinsu,sun koma rainon Madara rainon bonvita 😂
Ƴancin da su hossana suka samu ko mutanen nigeria a 1960 basu samu makamancin shi ba,hossana fa har wasu kumatun jin daɗi tafara ajiyewa🤣 dama bata wasa da abinci gashi Omar ya cika masu store da kayan abinci kala kala, ga freezer dinsu dake shaƙe da kayan sha,kullum in jahad tayi mata maganar tadinga ci ahankali sai tace"ina ruwanki!In suka ƙare yaya Omar zai siya mana wasu," 🥱
Marshal omar bai barsu hakanan ba, sai da ya ƙara masu security guards har mutun huɗu, Osman kuma shine a matsayin drivern da zai dunga kaisu School da wuraren shaƙatawa,tuni ya cike masu form na school koda akazo wurin sanya sunan uba ya tambayesu sunan mahaifinsu sai cewa suka yi "kasa mana sunanka kawai ya omar,mu bamu da uba," wani irin kallo yayi masu tare da cewa"ban shirya haramta ma kaina ɗaya daga cikin ku ba,don haka zan sanya maku sunan Uncle ɗina ne a matsayin Mahaifinku amma banawa ba,'
Sam basu gane mai ya omar ɗinsu ke nufi ba da cewa bai shirya haramta ma kanshi ɗaya daga cikinsu ba,sun dai bar abun ne kawai azuciyarsu,
Alhamdulillah Omar ya kammala cike masu form da sunan Uncle dinshi,JAHAD ABUSUFYAN da kuma HOSSANA ABUSUFYAN,ba ƙaramin daɗi suka ji ba saboda jin ya saka masu sunan mutumin nan da goggon katsina ta ƙaƙaba masu amatsayin Ubansu,
sunan makarantar da suka fara zuwa D.A International acadermy wato makarantar da Sehrish ke zuwa🤔
_💋Boss Bature💋_
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
11:30 na dare
Fitowarta kenan daga toilet jikinta ɗaure da towel,ba ƙaramin canzawa tayi ba gaba daya ta sauya saboda hutun da take samu ga kuma kwanciyar hankali,tun daga kan natural skin colour dinta zaka gane hakan,yanzu bata wasa da tsaftace jikinta kullum cikin ƙamshi take,
Ƙarasawa tayi gaban mirror tana cigaba da tsane jikinta da towel ɗin hannunta,bayan ta kammala tayi hanging dinsa daga gefen mirror din,sannan ta kai hannunta jikin drawer chest na mirror,janyowa tayi tare da zura hannunta ta ɗauko hand dryer,jona ta tayi ajikin socket nan take ta soma buso da iska, cikin sauri ta kanga ta saitin kanta taci gaba da busar da gashinta,cikin nishaɗi take yi saboda ta mayar da abun tamkar na wasan yara, natsuwa tayi tana tunano abunda suka tattauna da Azmee acikin kitchen bayan ta sanar da ita maganar da sukayi da abbansu nacewa tafara kamun ƙafa tun daga yanzu,
dariya sosai azmee tayi tare da cewa"Abba da zolaya wato in marks dinki yazo da F shine zai aura maki haroon gsky kwara ki dage,"
Murmushi sehrish tayi tare da cewa"Amma aunty azmee ya akeyin kamun ƙafa inaso na iya"?
ɗan gyaran murya azmee tayi kafin tace"Kyautatawa mana,kinsan ita zuciya nason mai kyautata mata,kamar abbansu atlease yakamata ace duk safiyar Allah kina zuwa har bedroom ɗinshi kina miƙa gaisuwa hakan zai ƙara maki daraja a idanunshi kuma zai tabbatar da cewa kina da tarbiyyya sosai,sannan 6angaren girki yakamata ace ma yanzu kinfi ni iya girki,tuntuni dama inaso nayi maki magana akan koyon girki,saboda maza nason macen da ta iya girki,kin ga mazan gidan nan basa wasa da abinci akwai son cin mai daɗi,shiyasa nake da kusanci dasu sosai saboda yarda nake masu girki,don haka kema daga yanzu ki fara trying bafa dole sai irin nawa ba a'a salo na daban yakamata ki koya,bari na baki satar amsa kamar abincin gargajiya haka namu na hausawa saboda a gidan nan sunfi sabawa da abincin turawa,yakamata ki fara jaraba yi masu shi,ki koyi sarrafa abinci kala kala hada abunsha da kuma irin kayan makwalashe haka da sauransu,sannan 6angaren tsafta domin kuwa itace gaba da komai,idan ma kina da tsafta to ki ƙara akan wadda kike da ita,saboda mazan gidan nan basa son ƙazanta ko miskala zarratin,tun daga kan tsaftar jiki yakamata ki fara kulawa,wurin yin shaving na armpit dana under,da kuma kula da teeth dinki wurin yin brush akai akai banda barin datti ajiki,da kuma kula da gashin kanki wurin gyare shi,hatta nails ɗinki ki runƙa kula wurin yankesu banda tara akaifa,ina fada maki wannan ne domin amfanin kanki,don ita mace da tsafta akasanta da son ado,inaso kema ki kasance haka.........
Sosai azmee ta koyar da ita abubuwa da dama na rayuwa waɗanda zasu amfane ta,kuma tun daga lokacin duk in suka shiga kitchen suna aiki tana ƙara ilmantar da ita,hakan yasa sehrish ta soma canzawa sosai, yanzu kullum cikin gyara kanta takeyi,sannan bata wasa wurin koyon girki dalilin hakan yasa tashiga whatsapp grp na koyon girki,kullum tana cikin ɗaukar videos ɗin girki tana kallo donta koya,a hankali a hankali yanzu harta fara jin zata iya jaraba yi masu abinci acikin gidan 😇
murmushi ta saki bayan ta kammala tunanin a fili tace"bansan da wasu kalmomi zan iya godema aunty azmeena ba,saboda tagama yi min komai a rayuwa ina jinta tamkar mahaifiyata ne,Ya Allah ka barni da aunty azmee na,"�?
jin alamar shigowar motocinsu yasa ta yin saurin cire hand dryer ɗin daga socket ta mayar da ita inda ta ɗaukota, sannan ta taka izuwa wurin wardrobe ta buɗe tana neman kayan da zata sanya,wurin jerin kayan baccinta ta duba,wasu riga da wando ta dauko ƴan qasar indonesia masu matuƙar kyan gaske ga laushi jikinsu,launinsu maroon colour ne masu ɗigon baƙi baƙi ajikinsu, cikin sauri ta zurasu ajikinta sannan ta ɗauki mayafi tayi rolling dinsa akanta, sai da ta tabbatar da cewa sun shigo ciki kusan 15 mins ta ƙara sannan ta buɗe ƙopa tare da fitowa daga ɗakin nata,ƙafarta na sanye da flat shoes,miƙo hanya tayi tana tafiya a hankali ta biyo ta main palour din babu kowa har sun wuce ciki,kitchen ta wuce don ta haɗa mashi tea tare da kayan marmarin dayake buƙata kamar kullum,
Tare da Marshal Omar suka bar gidan,amma SGR ne kawai ya dawo saboda Omar ya wuce wurin su Hossana,tun akan hanya suka rabu dashi,
a galabaice ya shiga part dinsa saboda rashin jin daɗin jikinshi dayake yi,tun safe bai da lafiya amma saboda juriya irin tashi da ƙarfin hali ba wanda ya lura da hakan,wani irin sever headache tare da zazza6i mai zafine ya rufe shi,
Jikin shi na sanye da Army trouser tare da shirt light green colour,kai tsaye yana shiga bedroom dinsa ya faɗa saman bed dinsa batare da ya rage kayan jikinshi ba,saboda rashin ƙarfin jikin shi da yake ji,abun yazo mashi wani iri saboda kafin yayi ciwo da wuya mutun ne mai cikakkiyar lafiya,sam bai sanarwa kowa ba saboda baya son tayar masu da hankali kuma baison aga raunin shi,
Sehrish
Fitowa tayi daga kitchen ɗin hannunta ruƙe da tray mai ɗauke da ƙayataccen plate na fruits sai cup mai ɗauke da Hot tea sai faman tiririn Zafi yake yi,a natse take tafiya kai tsaye ta nufi stairs ɗin tana cikin tafiya kamar daga sama taji muryar haroon yana cewa"Wurin Namiji za'a ne"? A wani irin firgice ta juya tana neman ta inda zata ganshi,
Yana zaune saman 3 seater shi kaɗai abunshi jikin shi