Showing 48001 words to 51000 words out of 432432 words
Chapter 17 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
ka bari muji da wanda muke ciki," shiru jahan yayi yana faman sakin Huci ji yake tamkar ya tashi ya shaƙe wuyan Haroon,
Hannu haroon yasa abaki irin mamakin nan yace "Wow wai meyasa kowa yake ma junaid irin wannan zazzafar soyayyar har haka? Gaskiya anyi mun nisa kaina na cikin duhu, farin jinin junaid yayi yawa ina kishi da hakan," ya faɗi yana dafe saitin zuciyarshi
. Ayaan yace "Ba son junaid muke ba, Ƙaunarsa muke yi saboda shi ɗin jinin mu ne,"
ta6e baki haroon yayi tare da ɗan jinjina kai yace "hmmmm ni wannan ba damuwata bace ba, abu biyu nake buƙata daga gare ku, inaso ku gamsar dani acikin daren nan, saboda inji irin naku salon, Sannan abu na biyu kuɗi nake so kimanin naira miliyan 50, in kun mun hakan zaku zauna lafiya,
Wani irin kallo suke bin shi dashi, Jahan yace "50m fa kace? Ina zamu same su? ka ruga da kasan iya salary ɗin mu, kuma ba tarawa muke yi ba, kashewa muke yi,"
haroon yace "Wannan ba damuwa ta bace, in kun so there's many way da zaku samu waɗannan kuɗin ! Yayan ku fa billionare ne! Mahaifiyarku ma billionaire ce, yadda take son ku ɗin nan, da zarar kun mata waya kunce kuna son Ƴan silalla zata turo maku,"
Murya a sanyaye Ayaan yace "mun ji zamu samu kuɗin mu baka amma dan Allah kada kace zaka aikata wannan abun damu, wlh bazamu iya ba, iya mu biyu ne kawai ba kowa muke bi ba, ka faɗi mashi jahan kada ya cutar da rayuwarmu bazamu iya jurewa ba........................"
bugun ƙopar da akayi ne ya hana Ayaan ƙarasa maganarsa, Cikin sauri Haroon yayi tsalle yashige bayan labule ya 6oye,
tashi su kayi atare suna faman sa hannu suna goge hawayen dake fuskarsu, sannan jahan yayi ƙoƙarin cewa "Wanene?
Sehrish dake tsaye ruƙe da tray a hannunta tace "Ni ce sehrish,"
Ayaan yace "Shigo ciki,"
Tura ƙopar tayi da tray ɗin hannunta mai ɗauke da food wermers tare da kayan tea ta shiga ciki, tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki ganin yadda fuskokinsu sukayi Jawur, idanunsu sun Canza launi alamar sunsha kuka,
Muryarta na rawa tace "Dama.............' bata ƙarasa ba Jahan ya katse ta da cewa "Ki barshi kawai, bazamu iya cin komai ba, ki koma da kayan,"
Shiru tayi aranta tana mai mamakin jin yadda Jahan ke mata magana cikin sanyin Murya, shi da kullum atsiwace yake mata magana,
Jinjina kai tayi tare da yin juyi zata futa karaf idonta suka sauka kan ƙafafun haroon dake 6oye bayan labule, tana ganinsu tagane cewa ƙafafunsa ne kamar na shebur haka suke, tsananin tsoro da mamaki ne suka kamata daker ta iya fuce wa daga ɗakin,
Kai har ta futa tana waiwayen ɗakin nasu, cikin mamaki take cewa "Meke faruwa ne? Naga fuskar Ayaan da jahan jawur alaman sunsha kuka, kuma menene yakai ƙafafun haroon ɗakin, hakan na nufin shine 6oye bayan labule? ko uban me yakaisa ɗakin hada su 6oyewa abayan labule, gaskiya akwai wani mummunan abu dake faruwa, Nashiga ukuna Allah yasa dae Haroon kada ya cutar dasu don nasan halinsa ba ƙaramin shaiɗani bane...........' ta ƙarasa zancan Zucin nata ayayin da take saukowa down daga saman stairs ɗin,
Kitchen ta shiga ta ajiye tray ɗin, sannan ta wuce bedroom ɗinta cike da zullumin abunda tagani,
A daren ranar haroon sai da ya tabbatar ya wulaƙantar da rayuwar Ayaan da jahan domin kuwa har sai da Ayaan Ya sume sannan ya ƙyalesu ya fuce yana ƙara jaddada masu maganar kuɗinsa, bayan ya fita jahan ya fashe da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali yana jijjiga jikin Ayaan dake sume aƙasa 😭
[9/15, 9:20 AM] 💋BOSS LADY💋: *💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
~🔥The father Of Soldiers🔥~
*Episode 25-26*
*Story & Written by*💫
*Hafsat Bature Moh'd* *BOSS LADY*
cikin sauri Jahan ya miƙe fitowa daga ɗakin yayi ya sauko down kai tsaye freezer ɗin dake a babban falon nasu ya tunkara, buɗewa yayi tare da zura hannu ya ɗauki robar ruwa mai sanyi, sannan ya juya ya koma ɗakin nasu, bayan ya buɗe robar ruwan ya ɗebo ya yayyafa masa a fuskarsa, wata irin doguwar ajiyar zuciya Ayaan ya saki tare da buɗe idonsa da sukayi jawur dasu yana kallon jahan dake zuƙunne agabansa, ganin Ayaan ya farka yasa jahan faman sauke ajiyar zuciya, yayin da hawaye ke sintiri a fuskarsa yana kallon ɗan uwan nasa,
Buɗe baki Ayaan yayi zaiyi magana, nan take wani irin yunƙurin amai yazo masa, a hanzarce ya zabura ya miƙe duk jikinsa ba ƙwari da gudun gaske ya faɗa toilet agaban basin ya tsaya yana faman kwarara aman, biyo sa jahan yayi cikin toilet ɗin tsayawa yayi kusa dashi ya sanya hannunsa yana ɗan bubbuga bayan Ayaan cikin muryar kuka yake cewa "Ayaan kayi haƙuri ina mai takaicin wannan ranar, naji natsani kaina Ayaan saboda nagaza ceton ka a hannun wancan fasiƙin, tabbas Haroon bai da Imani ko misƙala Zarratin kashe mu kawai yake son yi, ni ina kokwantan cewa Anya haroon JININ MU NE !!!!!!!!!!
dakyar Ayaan yasamu ya dakata da Aman hannunsa yasanya yana tarbo ruwan dake kwararowa daga jikin fanfon yana kuskure bakinsa, bayan ya kammala ya kashe Tap ɗin,
Sannan ya ɗago da shanyayyun idanuwansa ya kalli jahan yace "Haroon bai da Imani, Ƙazamin banza mugu macuci kuma Azzalumi wlh Allah bazai ta6a ƙyalesa ba sai ya bi mana haƙƙin mu, Jahan ni sam bana jin kunyar videon tsiraicin mu ya fita, babban abunda nake jimawa shine Mutuncin mahaifin mu da kuma na Babban yayanmu, jahan dole mu nemi mafita akan wannan Baƙin Shaiɗanin...........' ya ƙarasa maganar yana faman sakin Numfashi mai zafi, don tuni zazza6i yakama jikinsa,
Jahan yace "yanzu dare yayi Ayaan,Gobe sai musan Abunyi amma gaskiya bazan ƙara bari haroon ya ƙara kusantar ɗaya daga cikin mu ba, ko nawa yakeso muyi ƙoƙari mu biyasa shine kawai !!!
Sun jima suna jimamin abunda yafaru dasu kafin daga bisani suka sake sabon wanka don tsarkake jikinsu, bayan sun fito suka zura jallabiya ajikinsu, sai da Jahan ya canza musu bedsheet sannan suka kwanta, sun juma idonsu a buɗe kafin daga bisani bacci ya ɗauke su 😥
(Arayuwa kowa da irin tashi jarabtar, babu wanda Allah baya jarabta, kuma bawai don baya son mu bane a'a face don ya jaraba imanin mu)
**************Morning***********************
tun da sassafe sehrish ta farka daga baccin da ta koma na asuba, fuskar nan awashe yau zata fara shiga school, jiki na rawa ta faɗa toilet shaf-shaf tayi wanka ta fito jikinta ɗaure da farin towel,
Uniform ɗinta ta curo daga cikin wardrobe duka ukun, ta jera su saman gadonta tana tunanin wanne zata sanya, duk kala ɗaya ne amma na farkon riga ce da mini skirt ɗan dai-dai guiwa shafa su tayi tare da girgiza kai tace "Ba wannan zansa, basu son cewa ni musulma bace, taya zansa wannan gajeran skirt ɗin cinyoyi awaje kamar ƴar christiana," tayi maganar tana yatsina fuska, buɗe na biyun tayi riga ce tare da skirt pencil ba ƙaramin ɗame jikin mutun zaiyi ba,
"Kamar dae wadda zata club," ta faɗi tana ƴar dariya, na ƙarshen ta buɗe riga ce tare da dogon wando, duka uniform ɗin suna da Top wadda ake sanyawa daga sama bayan an zura rigar sai kuma guntun hijab wanda daƙyar ya dire kafaɗa,
"Kwarama wannan zasu fi dacewa dani," ta faɗi tare da hanzarin komawa gaban mirror sai da ta kammala shafe jikinta da body oil tabi ta feshe shi da turare ko'ina yakama ƙamshi sannan ta koma gaban gadon tana zura uniform ɗinta, lokacin da ta kammala zura kayan duka ta kalli kanta a mirror sai da taji gabanta ya faɗi saboda yadda kayan suka hau jikinta su kayi mata wani irin kyau,
Rigar white colour ce wandon kuma Maroon colour launi ɗaya da Top ɗinta, jujjuyawa tayi agaban mirror ɗin sannan ta sakarwa kanta murmushi, sai da tagama shiriritar sannan ta ɗauko takalmanta,
tsayawa tayi tana ƙoƙarin zura safa a ƙafarta, ta aza ƙafar asaman kujerar gaban mirror tana gyaggyara safar, Azmee ta shigo ɗakin da sallama tana yin arba da sehrish ta soma washe baki tana cewa La!la! Irin wannan kyan haka, Masha Allah gaskiya uniform ɗin nan ba ƙaramin kyau su kayi maki ba Sehrish sai kace donke akayi su,"
Murmushi kawai Sehrish ke saki tana ɗan kallonta a lokacin ta kammala sa safar da takalmin a ƙafar daman ta, saura ta hagun zata sanya mawa,
"aunty azmee ina kwana fatan kun tashi lafiya," ta faɗi tana aza ɗayar ƙafar saman kujerar ,
Azmee tace "Lafiya lou Alhamdulillah, naga sai faman shiri kike yi, maganar breakfast ba?
"Aunty azmee lokaci zai ƙure ne, idan nadawo zanci," ta faɗi tana zura safa a ƙafar hagunta,
Azmee tace "Kin ta6a ganin inda akaje ɗaukar karatu da yunwa? gaskiya bazaiyiyu ba, akwai sauran miyar jiya na ɗumamata saina haɗa maki da dankalin dana soya kici, bari na kawo maki"
ta fadi tare da juyawa ta fuce cikin sauri bayan wasu mintina sai gata ta dawo hannunta ɗauke da plate, soyayyan dankalin ne aciki tare da jar miya, ajiye mata tayi asaman side drawer ɗinta, sannan ta koma ta ɗauko mata kayan tea don ta haɗa tasha,
"Nagade sosai Aunty azmee da kulawarki," sehrish ta faɗi a lokacin ta baro gaban mirror ɗin, wuri ta samu gefen gadon ta zauna tana cin breakfast ɗinta, yayin da azmee ta fuce tana cewa "ki hanzarta ki shirya kafin Junaid ya fito,"
ta amsa mata da "Toh,"
A can ciki kuwa tuni junaid ya farka saboda ya tashi da wuri ya sanya alerm a wayarsa, shaf shaf yayi wanka ya fito ya kimtsa cikin pakistani riga da wando farare amma anyi masu ado da stone launi daban daban ajikinsu, ba ƙaramin kyau yayi ba, bin jikinsa yayi ya feshe shi da Spice bomb, sannan ya gyara sumar kanshi, gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa yace "Nima kaina nasan cewa Ni kyakkyawa ne, Son kowa ƙin wadda ta rasa, Allah kaɗai yasan ƴan matan da suke crushing akaina," ya faɗi yana tsumbula yatsansa na tsakiya a dimple ɗin fuskarsa daya Lotsa,
daga bisani ya ɗauki key ɗin motar shi tare da wayarsa ya fito daga ɗakin, cikin hanzari ya sauko down babu kowa saboda duk basu tashi daga bacci ba, wuri ya samu asaman Royal sofa ɗin dake a falon mai mazaunin mutun 3 ya zauna yana jiran fitowar sehrish, wayarsa ya shiga daddanawa, message ya tura mata cikin wayarta, na cewa yana jiranta ta fito,
a lokacin ta kammala kur6ar tea ɗin data haɗa, message ɗin junaid ya shigo mata karantawa tayi "Am waiting for u reesh,' murmushi ta saki cikin sauri ta miƙe tare da ɗaukar guntun hijabin ta zura ajikinta, sannan ta ɗauki School bag ɗinta ta ɗan sagala hannun jakar a kafaɗarta, sai da ta ɗauki wayarta sannan ta fito daga ɗakin, kai tsaye ta nufi falon tunkan ta ƙarasa junaid ke kallonta baki asake,
Ganin hakan yasa ta sakin dariya, ƙarasa wa tayi wurinsa tare da tsaya agabansa ta ruƙe waist ɗinta tace "Nayi kyau,"?
Cikin mamaki yace "Reesh irin wannan kyau haka? Anya karfa malaman makarantar su rikice? innalallahi," ya faɗi tare da aza hannunsa akansa,
ɗan bubbuga ƙafarta tayi tare da cewa "ka tashi mu tafi junaid har 8:30 fa tayi,"
Mamaki tayi ganin yarda yake kallonta hannunsa yakai tare da cafko wutsiyar gashinta da ta sauko har tsakiyar bayanta yace "Sehrish jibi fa? Babu wani dogon hijabin ne sai wannan? Taya zaki bar gashin nan haka bainan nasi? Kowa ya kalla?
Sai lokacin ma ta ankara sam ta manta bata sanya ribom ba ta ɗaure gashin, dafe kanta tayi tare da cewa "kash ! Wlh mantawa nayi ban ɗaure gashin ba, kuma fa in na sanya ribbom gyaran gashin da akayimun zai 6ace,"
tashi junaid yayi tare da ruƙo hannunta yace "Mu shiga cikin ɗakin na ɗaure maki shi, nasan yarda zanyi batare dana 6ata maki gyaran gashin ba,"
bin shi tayi suka wuce ɗakin nata, duk wannan abun dake faruwa akan Idon haroon sam basu ankara dashi ba, tun fitowar sehrish yake tsaye ruƙe da qugu daga shi sai gajeran wando fuskar nan a murtuke kamar ta shanu, jinjina kansa yayi tare da cewa "Wato ni waccen ƴar shilan zata raina ma wayau, in na ta6a jikinta taita ƙyamata amma gashi junaid har wani ruƙe hannunta yake yi, hada su shiga ɗaki ko uban mi zasu yi aciki,"? Ya tambayi kansa can kuma ya saki wani irin shu'umin murmushi yace "Wannan babbar dama ce agare ni ! Zanyi amfani da ita wurin gur6ata sunanta acikin gidan nan, Zan ƙala mata sharrin cewa ta koyama junaid lalata, kuma na kama su hannu dumu-dumu, " fashe wa yayi da wannan mahaukaciyar dariyar tasa kafin ya juya ya nufi hanyar komawa dakinsa yana cewa "Yarinya kin gama yawo acikin gidan nan, sai kin gane baki da wayau !," yana tafiya yana sambatu har ya shiga ɗakinsa,
Junaid kuwa bayan sun shiga ɗakin sehrish ta cire hijabin nata agaban mirror suka tsaya, ribbom ɗinta dake ajiye saman mirror ta ɗauko tare da miƙa masa, hannu yasa ya kar6a sannan yashiga kiciniyar tattara gashin kanta donya ɗaure mata,
Murmushi ta dunga saki saboda jinsa yadda junaid ke faman nishi aranta tace"junaid ba ƙaramin rago bane, yanzu gashin kan nawa ma yagaza ɗaure wa, shi dai sai kace ba namiji ba, sam babu wannan karsashin na maza atattare dashi......
Muryarshi ce ta katse ta da cewa "Gulma ta kike ko"? Cikin sauri tace "a'a ni na isa,"
Murmushi kawai yayi, daƙyar yasa mu ya tattara sumar kan sehrish ya ruba ta biyu ya haɗa ya ɗaure," sannan ta mayar da hijabin nata,
"Gaskiya junaid ka iya dabara, gashi nan yanzu babu gashin bai leƙo ba,"
ruƙo hannunta yayi tare da cewa "Mu tafi ko," cikin sauri ta bishi suka fito da hanzari suka fuce,
Buɗe mata motar yayi ta shige sannan shima ya zagaya yashiga ciki, yana a driver seat ita kuma tana a gefensa, tayar da motar yayi sannan suka fuce daga gidan,
A natse yake yin driving ɗin sehrish na satar kallon shi tace acikin ranta "koya akai ya iya driving yanzu yadda yake shagwa6a66an nan karfa wata rana ya tunkari babban mota damu kwatsam ta rotse damu duk mu mutu.....'
"Matsalar ɗan nigeria kenan, duk wani bala'e shike fara kira ma kansa, yanzu ko menene na wannan tunanin"? Cikin mamaki tace "Acikin Zuciya fa nayi maganar" ta faɗi tana kallonsa
Junaid yace "Eh nasani, ae muddin zaki yi gulmata acikin zuciyarki to fa saina ji don haka ki kiyaye," ya faɗi yayin da yake shan kwana dasu,
Shiru tayi tun daga lokacin bata sake maganarsa ba acikin zuciyarta amma fa tayi mamaki don ita tasan cewa acikin zuciyarta tayi maganar amma gashi yaji,"
Tunkan su ƙarasa sehrish ke hangen katafariyar makarantar motoci sai shiga suke yi ciki suna sauke ɗalibai, tsayawa zayyana kyawun makarantar 6ata baki ne, gashi bani da isasshen lokacin yin wannan bayanin 😆
A parking space dinsu junaid ya sauke sehrish tare da cewa mun iso, atare suka fito gaban sehrish ne ya faɗi ganin tsala-tsalan ƴan mata young ladies irinta sun ɗau wanka, ƴa'ƴan masu kuɗi wayayyun gaske tun daga shigarsu zai tabbatar maka da cewa An sangarta su da yawa, saboda majority ɗin matan Mini skirt ne ajikinsa sai santala santalan cinyoyi awaye, kuma mafi yawancinsu babu hijab ajikinsu gyaran gashi ne kawai iri-iri, wasu kuma skirt ɗin nan ne ajikinsu waton pencil yabi shafe ɗin jikinsu, iya guiwar ƙafarsu ya tsaya,
waro ido waje sehrish tayi tana cewa "kai!kai!!kai!!! Junaid mu koma gida, gaskiya bazan iya zama a school ɗin nan ba, wannan sunfi ƙarfi na Allah,"
Fashewa da dariya junaid yayi ganin yarda sehrish duk ta dabarbar ce, hannunta na kerma ta ruƙo rigarsa tana 6oyewa abayansa tana faman yi masa sambatun su koma gida, abu kamar wasa har hankalin wasu students ɗin suka dawo kansu ganin yadda Yarinyar ta ƙanƙame jikin dan uwan nata hada su hawaye a fuskarta,
Shima kansa junaid sehrish ta rikita shi hankali atashe yake cewa "dan Allah sehrish ki daina, karki bani kunya mana kalli yarda hankalinsu yafara dawowa kan mu innalallahi, yanzu da ace school bus ce ta kawo ki bansan ya zaki ƙare ba,"
"Junaid nidai mu tafi gida, Allah bazan zauna anan ba" ta faɗi tana shesshekar kuka 😆
dariya kamar zata kashe junaid ba shi kaɗae ba hada wasu daga cikin ɗaliban dake a wajen,
Wasu gungun ƴan mata ne suka ƙaraso kusa dasu, ɗaya daga cikinsu tana cewa " Wow friends kalli wani handsome guy nan ya burgeni sosai,"
Jin hakan yasa sehrish dakatawa da kukan tana ɗan kallonsu kai kana ganinsu kaga jarababbu,
Murmushi ta gefenta ta saki tare da cewa "Kamar nasan shi a tiktok fa,