Showing 57001 words to 60000 words out of 432432 words

Chapter 20 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

ƙaraso akan Lokaci batare daya kai ga Cutar da ita ba" huci kawai yake yi yana kallonsa da idanuwansa waɗanda suka canza Launi bakomai yake tunawa ba fa ce yarda Baba alamu ya yayyaga ma Husana rigar jikinta, in ya tuna wannan abun zuciyarsa Tafarfasa take yi saboda 6acin rai, muryar major ce ta katse shi da cewa" Allah ya huci zuciyarka yakamata mu hanzarta barin gidan gonar nan domin muyi gaggawar kai su asibiti,

Jin hakan yasa shi yin saurin zura hannu tare da curo wayarsa daga aljihun wandonsa, nan take ya shiga camera tare da saita gawar baba Alamu ya ɗauke ta hoto da kyau, bayan ya ammala ya mayar da wayar cikin aljihun sannan ya kalli Major yace "Duba min aljihun wandonsa kona rigarsa kaga ko za'a samu waya,"


Cikin hanzari Major ya zura hannunsa cikin aljihun baba alamu daker ya lalubo wata ƙaramar waya nokia, taji duniya don bala'e batteryn wayar saida aka sanya robali sannan aka ɗaure shi baya cikon da akayi masa,duk ta rakwakkwa6e wayar,

"Sir ga wayar," ya faɗi tare da miƙa masa, bai kar6a ba bin wayr yayi da kallo kafin yace "Major cewa nayi ka ɗauko mun wayarsa ba wannan abun ba," ya faɗi yana nuna wayar hannun major ɗin

Ƙiris ya rage major ya fashe da dariya saboda ya lura cewa Boss Man ɗin nasa baya cikin hankalinsa,


"Sir wannan itace wayar, ka duba da kyau ta tsufa ne sosae shiya sanya ka ganta hakan,"

Ajiyar zuciya ya saki tare da cewa "Keep it in ur place, zan neme ta," yana faɗin hakan yakama hanyar fita daga ɗakin,

Muryar Major ce ta dakatar dashi da cewa "yalla6ai rigar fa? zan iya ɗauko maka ita," ya tambaya yana jiran amsa ,

Bai amsa mashi ba ya fuce kawai cikin sauri major ya ɗauko Jacket ɗinsa da yayi wurgi da ita sannan ya fito daga ɗakin ruƙe da ita a hannunsa a lokacin har yakai wurin motarsu da suka zo da ita, kai kana ganin yarda sukayi parking ɗinta kasancewa a tsiyace suka shigo da ita, domin kuwa har katakon ƙopar gidan gonar duk sun tarwatsa shi,


Cikin sauri Major ya rufa masa rigar abayansa shi kuma ya ƙara gyarata ajikinsa sannan ya zuge zeep ɗinta, buɗe motar yayi sannan ya shige back seat ɗin shikuma major ya shige driver seat sannan ya tayar da motar yayi baya² da ita kafin ya karya kwana ya fito daga gidan gonar da gudun gaske yake driving ɗinsu,

Sam ya gaza ɗauke idonsa akan hosana dake langwa6e asume kusa dashi, duk gashin kanta ya gama tarwatsewa dama a hargitse yake sai kuma aka ƙara hargitsar dashi, duk ya rufe mata fuskarta, lumshe idonsa kawai yayi har lokacin yana mamakin yarda akai wannan Lamarin ya afku amma yana da tabbacin cewa major yana da masaniya akan hakan,"


adai dai hanyar da baba alamu yayi wurgi da jahad Major yayi parking ɗin motar, cikin sauri ya buɗe motar ya fito gabansa ne kawai ke faɗuwa tsoranshi kar ace ta mutu,

wani saurayi ne zuƙunne a inda jahad take yashe, da alama ba ƙaramin taimako yayi mata ba, domin kuwa ya ciccire mata ƙayoyin da suka soki ƙafarta sannan kuma yayi amfani da Mayafinta wurin kekketa shi izuwa kashi uku, ya ɗaure mata goshinta sannan kuma ya naɗe mata ƙafafunta dake zubar da jini,

Fitowa major yayi shima yana kallonsa,

"Major karfa ace yarinyar nan ta mutu," ya faɗi a tsananin tsorace

"Sir she's still alive, suma ce kawai," ya bashi amsa,

saurayin yace"yalla6ai tana buƙatar taimakon gaggawa saboda jinin dake bleeding a goshinta da kuma tafin ƙafarta,"

Cikin tsananin tashin hankali ya ƙarasa tare dasa dukkan hannayensa ya tallabo JAHAD ya ɗaukota da sauri Major ya buɗe masa motar ya shigar da ita a kusa da Hossana ya zunar da ita a sume, sannan shima yashiga motar, zuge glass ɗin yayi tare da kallon saurayin yace"Ka shiga mu tafi tare,"

saurayin yace"yalla6ai machine ɗina fa"?

tunkan ya bashi amsa major yayi saurin cewa"daraban kayima arziƙi ƙulli ana maganar arziƙi wake ta wani machine"?

Jin haka yasa saurayin tasowa sai da ya bari major yashiga, sannan shima ya shiga kusa dashi ya zauna, rufe motar su kayi sannan da gudu suka bar dajin suka miƙi santalelen titin da zai sadasu da inda suka dosa

Kallonsu kawai yake yi ransa na ƙara ƙuna ganin irin jigatar da yaran su kayi yaran daya kai Amana, sam kwalwarsa ta rikice yarasa gane ma wannan lamarin ba komai yake son ji ba face yarda akai har tsohon can ya ɗauko yaran izuwa cikin gidan gonarsa don ya lalata rayuwarsu! taya akai ya fito dasu daga gidan general Ishaq? taya akai Aunty laila tayi gangancin da har wani zaizo ya ɗauki twins ɗinsa? da sa hannun wa akayi wannan ƙulla-ƙullar, tabbas kowaye bazai ƙyale shi ba, muddin ya gano gaskiyar lamarin!!, ya ƙarasa zancen zucin nasa adai² lokacin da suka ƙetaro Abuja, kai tsaye suka wuce dasu izuwa katafaren asibitin SGR,

***************SEHRISH***************

Sam bata gane mai ake koyarwa acikin class ɗin saboda wata irin yunwa dake jibgarta ga wani irin bacci da take ji, sai faman hamma take yi tana lumshe ido,

Wuraren ƙarfe tara da rabi, time ɗin break yayi gaba ɗaya ƴan class ɗin sai fita suke yi don suje cin abinci, Sehrish na kwance saman desk ɗin gabanta sai faman sharar bacci takeyi,

juyowa Amrish tayi daga seat ɗinta tana kallonta, murmushi ta saki tare da sa hannunta taɗan bubbigi bayan sehrish tace "Get up baby ! time ɗin break yayi, yakamata mu fita,"

daker sehrish ta buɗe ido tare da ɗago kanta daga saman desk ɗin tana kallonta biji², miƙewa Amrish tayi ta fito daga seat ɗinta, sannan ta ruƙo hannun sehrish tana cewa"Get up mana Let's go,ko bakya jin yunwa ne"?

ta tambaya tana kallonta, miƙewa sehrish tayi tare da biyota suka fito daga Class ɗin gabanta nata faɗuwa tsoranta kar ace siyen abincin zasuyi don ko sisi bata fito dasu ba, babu wanda ya bata kuɗi,

saukowa sukayi daga saman benen duk inda suka bi sai an samu wanda zai yi ma Amrish magana, kuma yawanci akan Sehrish suke tambayarta ko ƴar uwarta ce, sai dae kawai tace musu eh, saboda tasan son jin gulma ne kawai,

Hanya suka miƙa bada jimawa ba suka ƙaraso Lunch room ɗin makarantar wurin cin abincinsu, lokacin da suka shiga wurin mamaki ya kama sehrish ganin ɗalibai aciki kowa zazzaune saman dining tables masu mazaunin mutun 4, kowa wanne gabansa cike shaƙe da abinci sai ci suke yi,

Ruƙo hannunta Amrish tayi adai² wani tebur da bakowa tace ma sehrish tazauna sai faman zare ido take yi gabanta na faɗuwa tsoranta kar ace tabada kuɗin abinci,

"Me kike so na amso mana muci"? Amrish ta tambaya tana kallonta daga tsaye, zuru sehrish tayi tana tunanin yarda za tace ma Amrish bata da ko sisi,'

"Kin yi shiru baki ce komai ba"? Amrish ta tambaya a ƙagare, murya na rawa Sehrish tace "Ni bana jin yunwa, a ƙoshe nake,"

Cikin mamaki amrish tace "but alamu fa sun nuna cewa kamar kina jin yunwa? Yakamata ko Coffee ne kisha taya zaki zauna da yunwa acikin ki"?

sehrish tace"kada ki damu bana jin yunwa ne kawai," jinjina kai amrish tayi tare da cewa "its ok bazan takura maki ba, tunda kince bakya jin yunwa, ni bari naje na amso abunda zanci," tana faɗin hakan ta wuce wurin masu zuba masu abincin,

ɗagowa sehrish tayi tana kallon students ɗin dake zazzaune suna faman cin abinci hankalinsu akwance, haɗiyar miyau tashiga yi ganin yarda suke Cusa pancakes da zuma abakinsu,

sunnar da kai tayi gaba ɗaya tarasa yaya zatayi ga yunwa tana ji amma tana tsoran taci musu abinci ba kuɗin biya, tana cikin wannan tunanin sai ga Amrish tadawo hannunta ɗauke da plate guda biyu da murmushi afuskarta, ta ajiye su saman table ɗin sannan ta juya ta koma domin amso masu abunsha,

Zuru sehrish tayi tana kallon plate ɗin mai ɗauke da banƙararriyar kaza ta gasu sosai hada ƙaramar knife wadda mutun zai yanka yaci, ɗayan plate ɗin kuma Snacks ne acikinsa shaƙe, runtse ido tayi tana ji tamkar takai ma plate ɗin hari, sai faman cixon la66a takeyi,

dawowa Amrish tayi hannunta ruƙe da Laca sera mai sanyin gaske roba biyu, wuri tasamu tana fuskantar sehrish tazauna tana cewa "Wai haryanzu kina akan bakan ki na ba zaki ci komai ba"? tun yanzu zamu fara haka dake?

ɗan murmushin yaƙe Sehrish ta saki tare da cewa "ba haka bane just bana jin yunwa ne shiyasa," ta faɗi tamkar zatayi kuka, Ido ya gani rai naso,

Murmushi kawai Amrish tayi kafin tasa hannu ta ɗauki ƙaramar wuƙar dake ajiye saman kazar tashiga yankar naman tana ci,

Ƙiris ya rage sehrish tasaki miyau saboda tsabagen kwaɗaituwa da tayi cikin sauri ta gyara natsuwarta gudun kar tayi abun kunya agaban sabuwar ƙawarta,

Muryar amrish ce ta katse ta da cewa "Ko lemun ba zaki sha ba"? Cikin sauri tace"eh a ƙoshe nake," giɗa kai tayi sannan taci gaba da cin abunta, suna cikin zaman nan sai gasu Naja'at da parveena sun shigo, kai tsaye wurinsu suka nufa suka samu wuri suka zazzauna,

Naja'at tace "Wlh da wata irin yunwa na fito Class ɗin can, sam bana gane ma karatun, dama can nifa ba gane math nake ba,' tayi maganar tare da sa hannu ta ɗauki robar lacasera tare da buɗeta ta kwafa abakinta tana kwankwaɗa, hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba ganin tashanye mata lacasera ɗin da Amrish ta kawo masu, Ana cikin haka parveena ta tsoma hannu suka cigaba da cin roasted chicken ɗin da Amrish ta kawo masu, kafin kace mai tuni sun kwamushe komai, duk tana zaune tana faman haɗiyar yawu, sai da suka kammala sannan ma suka lura da ita, parveena tace "Au! Wai dama Yarinyar nan tana a wurin nan? Yo aini yunwa tasa nagaza gane ku nawa ne zaune a table ɗin muka tarar," ta faɗi da mamaki Naja'at ma tace"ko ni ban lura da ita ba, sai da kikayi magana Allah, sannu ko? Meyasa ke bakici komai ba ne,"

Tamke fuska sehrish tayi rai a6ace tace "bana jin yunwa," jinjina kai su kayi atare naja'at tace "halan kinyi breakfast dayawa ne a gida"?

A ƙule sehrish tace "Bansani ba," acikin zuciyarta tayi maganar a fili kuma tace "eh,"

daganan suka ci gaba da firar su har Parveena ta ƙaro masu abincin duk tana zaune suka zauna suka lamushe suka bar rishi da tanɗar baki, da lokacin komawa Class yayi kowa ya wuce Ajinsu naja'at da parveena class ɗinsu ɗaya don haka suka wuce atare, ita kuma tabi Amrish izuwa nasu Class ɗin,



Sehrish ba ƙaramin jiki taji ba, saboda azabar yunwa har wani jiri take gani, dishi² ta runƙa gani a idonta sam batasan me aka koya masu bama,

Lokacin da suka taso daga school tunani ta soma yi wa zai zo ya ɗauke ta, ga school bus tashigo cikin makarantar amma tsoranta kar ace kuɗi za'a biya,tsayawa tayi hannunta ruƙe da school bag ɗinta sai faman lullumshe ido take yi, suna cikin tsayuwar nan sai ga drivern Amrish ya iso, sallama tayi ma sehrish sannan ta shige cikin motar suka tafi,

Hankalin Sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba, ganin sai zuwa ake ana kwashe sudents ɗin ita gatanan tsaye zugudum babu alamar wani zaizo ya ɗauke ta,

tana cikin wannan tunanin motar JUNAID tashigo cikin makarantar adai² inda take tsaye yayi parking ɗin motar tare da zuge glass ɗin motar yace "madam muje ko," ajiyar zuciya ta saki ba ƙaramin daɗin zuwan shi taji ba, buɗe motar tayi tashiga sannan yaja motar suka fita daga makarantar,

Miƙar hanya yayi dasu yana cikin driving ɗin yaji sehrish ta faɗo masa a kafaɗarsa ta langwa6e, saboda shock ɗin daya ji har saida yaɗan ci burki a tsakiyar titin, aza idonsa yayi akanta, wani irin wahalallan bacci ne ya ɗauke ta batare da saninta ba, shine ta faɗo masa a shoulder ɗinsa, gaza janye idonsa yayi akanta yadda take ta faman sharar baccin ta ba ƙaramin kyau tayi masa ba, ya jima yana kallon kyakkwawar fuskarsa, sam.ya manta cewa a tsakiyar titi suke, sai go slow suke haɗawa batare da saninsa ba, har sai da wani babban mutun yayi masa magana ta waje, sannan ya tashi motar yaci gaba driving ɗinsa cikin kasala,

har suka ƙaraso gidan adai² parking space ɗinsu ya ajiye motar, sannan yajuya ya kalli sehrish tare dasa hannunsa ya shafa gefen fuskarta tare da ambaton sunanta"Sehrish mun iso gida fa, wake up pls ," ya furta yana kallon yadda take motsi da idonta alamun zata tashi,

daker ta iya buɗe idonta tana kallon shi sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa, junaid yace "reesh kamar baki lafiya fa? Look at ur eyes fa sun janza kala,

A kasalance tace "yunwa nake ji sosai banci komai ba tunda naje school, ga wani wahalallan bacci da nake ji," ta ƙarasa maganar tana faman yin hamma, har time ɗin suna acikin motar,

Tun da tasoma magana junaid ya saki baki yana kallonta har sai da takai ƙarshen maganarta sannan yace "Kina nufin wai baki ci komai ba a school to saboda me? Ya tambaya yana kallonta

Yamutsa fuska tayi tare da cewa "junaid ban fa da ko sisi balle na sayi abinci, shiya sanya,"

Wani irin kallo junaid ke bin ta dashi kallon na tausaya maki, ga takaicin daya hanasa yin magana,jin yayi shiru yasa ta cewa "ka tashi mu shiga ciki, kuma naga kana kallonta,"

A ƙule yace "Haushi kika ban ne,shiyasa nagaza magana, reesh waya ce maki sai kin biya kuɗi zaki ci abinci? An fa riga anbiya kuɗin komai na school ɗinki, tun daga school fees har kuɗin abincin ki dana school bus da zaki dunga hawa har na tsawon 3 months fa,"

Jin haka yasa sehrish zaro ido waje baki asake tana mamakin ashe itace shashashar batasani ba ta hana kan ta cin haƙƙinta, ashe an biya kuɗin komai ita kanta takaicin ne yasa ta yin kasaƙai,

Fitowa sukayi daga motar atare suka shige cikin gidan a babban falon suka rabu ta wuce bedroom ɗinta shi kuma ya wuce upstairs ɗakinsa, babu kowa acikin gidan abunda ya ɗaure mata kai,

tana shiga ciki tayi wurgi da school bag ɗin sannan tashiga tu6e uniform ɗin suma duk nan tayi watsi dasu saman gadonta, bayan ta kammala ya rage daga ita sai half vest da gajeran wando, toilet tashige shaf shaf tayi wanka tare da ɗauro alwala tafito, cikin hanzari ta buɗe wardrobe ɗinta ta zumbula doguwar riga, sannan ta zura hijabi tare da shimfiɗa darduma ta kabbara sallar, tana kammala sallar ko addu'a bata tsaya yi ba, ta haye saman gadonta ta baje tashiga sharar bacci maganar yunwa kuma wata'kil saita tashi sannan tashiga neman abinci,



Turo ƙopar Azmee tayi ta sameta tana ta jan minshari bin ko'ina tayi da kallo ganin yarda tayi wurgi da school bag ɗinta ga uniform ɗinta data watsar saman gadon, murmushi kawai tayi tare da girgiza kai tace "ƴan makaranta kenan, tun yau anfara wurgi da shool bag ga uniform a watse saman gadon maimakon ta ninke su," ta faɗi da murmushi a fuskarta sannan taja mata ƙopar ta fuce,

ta jima tana bacci sai wuraren sallar la'asar sannan tafarka da wata irin matsiyaciyar yunwa ba arziƙi ta fito ta wuce kitchen, har time ɗin babu kowa, roƙon da take yi Allah yasa babban yaya ba us suka koma ba,

Acikin tray ta haɗa abincinta sannan ta zauna a kitchen ɗin tana ci tana tunanin duniya,'



**********Twins***************

Duk yinin ranar ba inda suka je saboda tashin hankali sam sun rasa inda zasu tsoma ransu, tun da sanyin safiya bayan sun dawo daga sallar asuba, haroon ya faɗo masu ɗaki domin ya ƙara jaddada masu akan buƙatun daya nema a wurinsa, Jahan ya tsawatar masa akan cewa ko nawa yake so zasu bashi amma kada ya sake yayi kuskuren cewa zai ƙara kusantar ɗaya daga cikinsu, da jin wannan maganar sai haroon yace ya amince amma bisa sharaɗin cewa zasu ƙara mashi miliyan 80 in har suna son ya daina bibiyarsu Kuma cikin sati guda kacal ya basu in ba haka ba zai tona masu asiri 😥😳

tun safe basu ci komai ba, ko fitowa ba suyi ba daga bedroom ɗinsh, kuma babu wanda ya lura da hakan illa junaid da yayi ta tambayarsu har ɗakinsu sai da yazo yayi ta faman knocking yana kiran sunan su, suna jin shi tamkar zasu yi kuka amma basu amsa mashi ba,ƙarshe yayi tunanin cewa basa nan yayi tafiyarsa,

Ayaaan ya sha kuka aduk lokacin daya tuna abunda ya faru dasu daren jiya sai yayi yunƙurin amai, yanzu haka ma yana zaune gefen gadon idonsa jawur ya ɗago ya kalli jahan dake ta faman safa da marwa acikin ɗakin yace "Dan Allah jahan mu hanzarta mu sama mashi kuɗin daya buƙata, if not wlh so yake ya kashe mana rayuwa," ya faɗi yana faman matse hancinsa da yayi jawur saboda matsar daya sha da hannunsa,

Jahan ya dubesa cikin damuwa tare da cewa "Ayaan bansan ya zanyi ba ! Wa zan fara tunkara game da kuɗin nan? duk wanda zamu tambaya acikin brothers ɗin mu ko Abban mu dole sai sunji me zamuyi dasu kafin su bamu, daga baya ma zasu tambaye mu ina abunda muka siya dasu, don haka Mommy ce kawai nake tunanin zata iya bamu kuɗin amma matsalar shine tana fushi da mu saboda bama kiranta a waya muna gaishe ta," Jahan ya ƙarasa maganar tare da samun wuri ya zauna kusa da Ayaan ɗin,

"Jahan mom ita kaɗai ce solution, mu jaraba kiranta kawai mu sanar mata mu ji mai zata ce,"

"Video call zamu kira ta, may be tafi tausaya mana in taga yanayin mu" Acewar jahan, yayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login