Showing 426001 words to 429000 words out of 432432 words
Chapter 143 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete
hannunta Da gudu ta rufe ɗakin,Ta nufi kitchen,ƙiris Ya rage ta shiga kitchen ɗin,Muryar Hajiya sarat ta katse mata hanzarinta
"AMRISH"!a gigice Amrish Ta juya tana kallonta,Material ne ajikinta,Ta kashe ɗaurin kallabin nan na rashin mutunci,hannunta ruƙe da hand bag ɗinta,
Wani irin fitsari ne ya matsi amrish,Sai faman haɗiyar yawu take yi,idanuwan nan wuri wuri dasu na mara gaskiya,
"Naga kamar bakiyi farin ciki da dawowata ba ko"?
Shiru bata amsa mata ba,
"Ko har yanzu fushin kike yi dani ne"?nan ma shiru Amrish bata Amsa mata ba
Sai lokacin Hajiya sarat ta lura da wuqar dake hannunta,cike da mamaki tace"Ke!me kikeyi da wuqa a hannunki?Ya akai naga hawaye sharkaf akan fuskarki?wai meke faruwa ne"?
Ajiyar Zuciya Amrish ta sauke,Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Albasa nake yankawa a kitchen,ina girka abinci ne,saboda Yunwa nake ji,"ta ƙarasa maganar tana shafa cikinta,
Dariya Saratu Tayi"Manya Na girki,kinga yarda kika canza kamanni?Sai kace bada Gass kike girki ba?Yo wanna ae koda murhu kike girki baza ki yi irin wannan galabaitar ba,Fuskarki ta ca6e sosai kamar ma hada kwalliya kikayi ga janbaki nan dama dama har akan kumatunki"Tana magana tana dariya,
Murmushin yaƙe Amrish tayi tareda sanya hannu tana goge zufar goshinta,Ba ƙaramin daɗi taji ba,Ganin bata Ganota ba,
"Nasan ban kyauta maki ba,Nayi maki alƙawarin zamu fita shopping,Banji daɗi ba daughter,Wani emergency call ne aka yi mun Shiyasa na fita batare dana sanar maki ba,"
"Kada ki damu mommy,Ni yanzu ma ta cikina nake yi,bari na shiga na ƙarasa Yanka Albasar,"
"Okey,Zan shiga ciki na ɗan watsa ruwa,inaso na kwanta na huta,don wlh na gaji,Amma idan na tashi,Zuwa anjima kaɗan sai mu fita Shopping ɗin"
"Toh mommy,A huta Lafiya,"daga haka ta shiga kitchen ɗin,Hajiya Sarat kuwa Upstairs ta wuce,
Ajiyar zuciya Amrish ta sauke,A dole ta ɗauko albasa ta shiga yayyankata,can kuma ta ajiye yankar albasar,ta soma zarya acikin kitchen ɗin tana tunanin Ta yadda za'ae Ta taimaki Junaid Ya koma wurin Iyayenshi,In ba haka ba kashe shi zasu yi,in ma basu kashe shi ba,Wannan daƙyar zai kai labari,
Tunanin kiran Sehrish Tayi a waya,Domin kuwa Ta haddace numberta,Babbar matsalar shi ne Babu wayar da zata Kirata,Wayar Junaid akwai security,duk ta gaza samun natsuwa,a ƙarshe ta ajiye yankar Albasar,ta fito daga kitchen ɗin ta nufi upstairs,A bakin ƙopar ɗakin mommy ta tsaya,tura ƙopar ɗakin tayi a hankali ta leƙa,bata same ta aciki ba,amma taji saukar ruwa alamar wanka Take yi,
Jiki na rawa ta shiga cikin ɗakin cike da fargabar karta kamata,handbag ɗinta ta buɗe anan ta samu wayoyinta guda biyu,ƙaramar nokia da kuma Infinix,duka ta haɗa wayoyin,Sannan ta ɗauki key ɗin ɗakin data gani saman side drawer,fitowa tayi daga cikin ɗakin,Ta garƙame Hajiya Saratu da mukulli,gudu gudu sauri sauri ta sauko downstairs,tana ƙoƙarin kunna ƙaramar wayar kenan,Infinix ɗin hannunta ta soma ringing,ƙura ido tayi tana kallon Sunan daya bayyana akan screen ɗin wayar,Daddyn Amrish,
Maimaita sunan Tayi"daddyn Amrish!"da mamaki akan fuskarta,
"Dama amrish nada uba,"ta tambayi kanta sai kace ba ita bace Amrish ɗinba
Picking call ɗin tayi tare da kara wayar akan kunnanta,
"Kina jina saratu,Wlh karki kuskura kibar yaron nan araye,Don na lura Yaya bazata ta6a bari A ɗauki fansa akanshi ba,Abunda nakeso dake shine,ki ƙwaƙule mashi idanuwanshi nasan zaki iya,Sannan ki binne mun shi da ranshi in bai mutu ba,"
Wata irin zufa ce ta wanke mata fuskarta,Lokaci guda tsananin tsoro ya bayyana akan fuskarta,mutumin bai jira amsarta ba,Yaci gaba da magana duk a tunaninshi da Saratun Yake magana,
"Banaso Ya wuce Yau araye,Kawai ki aiwatar da abunda nace maki,"a gigice Amrish tayi rejecting ɗin kiran,don bazata juri bata lokaci ba wurin sauraron munanan kalaman mutun daya kira wayar,Amma fa tajima tana nanata sunan da Mommynta tayi mashi saving a wayarta,wai daddyn Amrish,A rasa wa za'a sanya ma suna daddyn Amrish sai wannan Mugun,me kashe ƴa'ƴan mutane,
Dogon tsoki Taja,taso ace zata Iya buɗe infinix ɗin don tayi bincike akan wayar,Sae dai kash akwai security ajikin wayar,ƙaramar wayarce kaɗai babu security ajikinta,Call log ta shiga tare da dialling number ɗin Sehrish ta danna mata kira,Sai faman tsuma take yi,don ta qagara Sehrish ta ɗaga kiran ta sanar da ita cewa Yayanta na a gidansu,Suzo su dauke shi,
Almost 3 times Kiran nashiga,amma Sehrish bata ɗaga ba,sakamakon Wayarta dake a silent,tana cikin aljihun doguwar rigar Jikinta,
A ruɗe amrish ta shiga faɗin"Nashiga Uku!Sehrish dan Allah ki ɗaga kiran!Ya zanyi in bata ɗaga ba,Yanzu idan suka kashe shi fa,Wayyo Allah na,"tana cikin wannan zullumin,
A can ɗakin Hajiya saratu kuwa,tana fitowa daga toilet,daga ita sai towel ɗaure a chest ɗinta,kaitsaye ta nufi handbag ɗinta donta ɗauki wayarta,tana zura hannu taji wayamm babu wayoyinta,Zazzage kayan cikin jakar tayi nan ma wayaam babu su dagaske dai an ɗauke mata wayoyinta,da farko tayi tunanin cewa ko a wurin meeting ɗin da taje ne aka dauke mata waya,Amma daga baya kuma sae ta tuna cewa tayi waya acikin mota lokacin da take shigowa cikin gidan,kodai Amrish ce ta ɗauke su!Nan take gabanta Ya faɗi rass,Sae lokacin ta tuna da wayar Junaid data bari asaman gadon,itama wayar babu ita,tun lokacin da tashigo ɗakin tayi noticing ɗin hakan amma bata kawo komai aranta ba,saboda ranta ya bata cewa ko ba anan ta ajiye wayar tashi ba,
A hargitse ta nufi ƙopar da dukkan ƙarfinta tasa hannu ta tura ƙopar,aikuwa taji an rufeta da mukulli,bubbuga ƙopar tashiga yi tana ƙwala mata kira
"Amrish!Amrish!wlh karki kuskura kice zakiyi mun bincike acikin wayata!kizo ki buɗe ƙopa tunkafin in buɗeta dakaina,"
Ƴan hanjin cikinta ne suka kaɗa lokacin da tajiyo Muryar Mommynta,.
Tabbas in bata yi hanzarin kawar da junaid daga cikin ba,su duka biyun zasu iya rasa ransu,
Duk da halin da take ciki hakan bai hanata mayar ma mommynta martani ba,.
"Wlh bazan buɗe ba mommy,Allah ya kamaki,Yau saina tona maki asiri,"
Kamar ƴar dambe haka Hajiya saratu ta dinga bubbuga ƙopar,
"Amrish wlh idan har kika kuskura kika tona mun asiri,Saina kashe shi acikin gidan nan,"ita duk a tunaninta Amrish a iya binciken wayarta ta tsaya batasan cewa ta gano inda suka 6oye shi ba,
Ganin taƙi zuwa ta buɗe mata ƙopa yasa ta nufi cikin ɗakin tana neman ɗayan key ɗin ɗakin,Gaba ɗaya ta hargitsa ko'ina,
Amrish kuwa yatsun hannunta na kerma Ta shiga ƙoƙarun rubuta ma Sehrish saƙo,Bayan ta tura mata text message ɗin,ta jefar da wayoyin saman Sofa,dabara ce ta fado mata,In har ta shiga ta cikin tagar dakin nan data cire ragarta,Zata Iya ƙoƙarin ku6utar dashi,
Da gudun gaske ta koma Store ɗin nan,Ta janyo jarkar man zuwa saitin tagar,ta haye samanta,hannuwanta ta sanya da dukka ƙarfinta ta ƙarasa yayyaga ragar jikin tagar,dama ta tsufa sosai daga taja saita kece,gaba ɗaya ta yakice ta,saukowa tayi daga saman jarkar ta dauko wayarshi da tayi wurgi da ita a ƙasa ɗakin,ta kunna torchlight ɗinta,Sannan ta koma saman jarkar,Da ƙarfin gaske ta kutsa kanta Cikin tagar,ba ƙaramar wahala tasha ba,Saboda girman jikinta don ma Allah yasa Tagar tana da girma,tana jin sauran ragar dake agefe da gefen tagar tana kartar jikinta amma haka ta jure,gaba ɗaya ta rubza cikin ɗakin,ta faɗo ƙasa timmm cikin ƙurar nan,duk ta 6ata mata fuska,A galabaice ta ɗago tare da sanya hannunta,Tana kakka6e ƙurar dake akan fuskarta,ɗago da wayar hannunta tayi tana haska ɗakin,Ga tsoro ga furgici,miƙewa tayi tana haska ƙasan ɗakin har Allah yasa ta gano inda yake kwance,numfashinshi na fita sama sama,zubewa tayi saman guiwowinta,Ta sanya dukkan hannayenta tare da ɗago dashi,yayi buɗu buɗu dashi,ƙurar duk ta rufe fuskarshi,har cikin hancinshi,baka iya ganin komai daga fatar jikinshi,fashewa amrish tayi da matsanancin kuka,kamar ranta zai fita,ya raunata sosai,Alamun sun nuna cewa yana akan hanyar gangara,daƙyar zai iya rayuwa,rungumeshi tayi ajikinta yayin da zuciyarta ke bugawa,Tunawa da Mommynta yasa Ta yunƙura tare da ɗaukarshi asaman kafaɗarta,Yayin da hannunta ke ruƙe da wayarshi,miƙewar da zatayi kenan hasken fitilar hannunta ya hasko mata Wayarta dake dadda6e da ƙura,bata bi ta kanta ba,don a halin yanzu tafi buƙatar Rayuwar Junaid,Ita dai koda gawarshi ce takai masu su ganshi,dole ta tagar ta fara turashi kamar tsumma haka ya faɗo ƙasan ɗakin,ita ma ta biyo ta window ɗin, a hanzarce ta ɗauke shi,saman kafadarta ta kama hanya,fitowa tayi daga cikin ɗakin ɗauke dashi,Ƙura duk ta buɗesu,musamman shi,kamar dodo haka ya koma,ya rame ya shanye ya bushe Ya ƙanjame bawan Allah
Adai dai Lokacin Hajiya saratu ta samu ɗayan mukullin ɗakin dake a cikin drawer chest,jinjina kai tayi tana huci tamkar zakanya haka ta Nufi bakin ƙopar,Ta murza key ɗin.........
*Masu buƙatar karanta Abban Sojoji har zuwa Takun ƙarshe yayi mun magana Ta Layina whatsapp kawai 08103884440*
*Ayi hakuri da wannan*
⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐�?
*_MACE MAI GYARA KANTA BATA BORANCI_*
*DOMIN. DAWO DA MARTABAN NONONKI*
Shin ko kinsan nono yanada matukar muhimmanci a wajan mai gida ,? Shin ko kinsan babu abunda namiji yafiso yafi daukar hankalinahi kamar cikar k'irji , ? To nono shine babban Martaban mace a wajan mijinta , don babu namijin da zaiso mace mai yakunannen nono kamar silifas ,wannan yasa Nazo maku da sahihi kuma ingantaccen maganin nono Wanda bashida wata matsala hadin gargajiya ne , acikin lokaci kalilan zakisha mamakin yadda nononki zai ciko sosai Wanda wannan cikowar ita zata bashi damar da zai tashi sosai ta yadda kema zaki Shiga cikin jerin mata masu aji agaban mazajensu ........kedai hanzarta ki nemi mmn Yusuf mai kayan mata yar mutan sokoto zaki samu ingantattun kayan mata masu tafiyar da hankalin maigida.......don neman Karin bayani 07069711327 ......💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋
𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠
*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*
Har ta kusa Fita palourn ta tuna da wayar Mommyn nan Nokia,Sehrish zata iya kira Kuma in har tabar wayar za'a samu matsala,Juyawa tayi ɗauke dashi ta koma saman Sofa ɗin ta ɗauki nokia ɗin ga wayar Junaid duka ta haɗasu Sae faman nishi takeyi,tana ƙoƙarin kama Hanya ta fuce,Hajiya Sarat ta bude Ƙopar A fujajan ta fito,waro ido waje Amrish tayi a wani irin Firgice ta watsa da gudu tamkar ba mutun ta ɗauko a kafaɗarta ba,Lokacin Da Hajiya Sarat ta ankare da Junaid dake sa6e a kafaɗar Amrish,Wani irin kukan Kura tayi da dukkan ƙarfinta ta watso a guje irin gudun nan na fitar hayyaci,Cikin Rashin sa'a tana Sanya ƙafarta saman benen,Tamkar an ja ƙafarta gaba ɗaya ta burkice,a jirkice ta sulalo daga saman benen,kanta yayi Mugun buguwa,Qugunta kuwa sae dai muce Allah ya kyauta,
Amrish kuwa tsabar tsoro ko waiwaye batayi ba,lokacin data faɗo entry hall na gidan,Da gudu ta nufi gate,A lokacin baba mai gadi yana yin alwalar sallar Azhar da aka fara kira,Koda yayi arba da Su Amrish Baiyi tsammanin mutane bane,Wurgi yayi da butar hannunshi ya watsa da gudu zai shige ɗan ɗakinshi Ya ɗauko sandar shi,
Daƙyar Amrish ta iya buɗe baki tace"Baba Mai gadi ni ce,Dan Allah kataimake ni,Ka tsaida mana Taxi mu kaishi asibiti kada ya mutu,"dakatawa baba mai gadi Yayi a sukwane ya juyo yana kallonta,Sae lokacin Ya gane ta,kuma ya gane yaron nan ne na jiya ta ɗauko,ganin zai 6ata mata lokaci yasa ta fashe da kuka tana faɗin"Baba mai gadi kashe mu zatayi,In har bamu bar gidan nan ba,"
A hanzarce Baba mai gadi ya buɗe mata ƙopa suka fita,har zai tsaya ya tuna cewa Shine yaba Amrish Labarin Yaron,kenan shima Yana cikin hatsari,aikuwa da gudu ya bi bayan Amrish suka miƙi hanya suna neman Abun hawa,A ƙarshe daya ga ta jigata shi ya kar6i Junaid ya ɗaura shi a kafaɗarshi,Babban tashin hankalin tunda suka fito Unguwar babu kowa wayaam dama haka unguwannin ƴan gayun nan suke,Da ace irin geto ne da tuni jama'a sun agaza masu,ɗaiɗaikun mutanan dake wucewa duk wanda yayi arba dasu Amrish saiya watsa da gudu kamar sunga Aljanu,saboda ƙurar da ta 6ata masu jiki,
Da iya ƙarfinta Na ƙarshe ta daddage ta miƙe,ɗago kan da zatayi keda Wuya haƙorinta ɗaya ya 6allo jaga jaga da jini,qugunta ya ruƙe sosai,wani irin azababben raɗaɗi,daƙyar ta samu ta fara jan jiki a galabaice ta nufi wayarta dake ajiye saman sofa,jikinta sai tsuma yake yi,daƙyar ta iya cire password ɗin wayar,Call log ta shiga ta kira wani layi da akayi mashi saving da ƙare kukanka,Daƙyar take magana saboda ciwon bakinta,
"Duk yarda za'ae karku bari yarinyar nan tabar cikin unguwar nan,Nasan zaiyi wuya su samu abun hawa,da ita da yaron Gawarsu kawai nakeso ku kawo mun...."tana magana tana goge zufar goshinta,ga wani irin huci dake fita abakinta,.
"Akwai ƙaramar nokia ɗita a hannunta,Zan tura maku Lambar wayar kuyi tracking ɗinta,"ta ƙarasa maganar tare da yin rejecting ɗin kiran,Gaba ɗaya Amrish ta ɗaure mata kai,saboda ta ɗauketa Shashasha,A irin rainon da tayi ma Amrish irin sangartattun nan ne,bata da wayau haka,Sai gashi yau ta bata mamaki,wai har tasan ma inda suka 6oye shi,koya akai duk tasan wannan?
Lokacin da Su Amrish suka haura saman titi,suna neman abun hawa,duk mai motar da suka tsaida sai yaƙi tsayawa,Baiwar Allah duk tabi ta ruɗe gashi sam taƙi tunanin yarda nokia ɗin Hajiya sarat data ɗauko,kuma ta hanyar bin diddigin layinne kaɗai za'a san Location ɗin da suke,
Suna cikin wannan tsayuwar,wata danƙareriyar mota ta shawo kwana da gudu,bata tsaya a ko'ina ba sai agabansu Amrish,mutuwar tsaye tayi lokacin,shi kanshi baba maigadi ya firgita da ganin motar,Jim kaɗan mamallakin Motar ya fito jikinshi sanye da fararen kaya hatta takalmanshi,Facemask ɗin fuskarshi Ya hana Amrish ta gane shi,
Yayi mamakin ganinsu cikin wannan halin,bai tsaya tambayarsu Lafiya ba Kawai ya buɗe masu bayan motar,badon ta yarda dashi ba hakanan dai kawai suka shiga cikin Motar tunda ba yarda zasu yi,a back seat na motar ta shiga baba mai gadi ya jinginar da junaid a tsakiya kafin shima ya shiga,Mai motar ya fusgi motar da gudu,a dai dai Lokacin motoci guda uku masu blank tunted ƙirar Range rover suka bi bayan motar shi,da wani irin mahaukacin gudu mutumin ke tuƙa motarshi,yarda kasan filin ƴar tseral haka motocin nan suke gudu asaman titi,
Amrish sai kuka takeyi tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin tashin hankali ba irin na ranar,ba komai ya ƙara tsoratar da ita ba fa ce Harbin bindiga da taji a bayan motarsu,Ya salam!gashi hanyar da suka biyo babu ƴan sanda balle su samu taimako,
Ɗaya daga cikin Ƴan ta'addan da suka biyosu wanda ya buɗe murfin motar ya miƙe a tsaye hannunshi ruƙe da irin wannan bingidar mai fitar da bullet kamar bomb,kwakkwaran Saiti Yayi ma Motarsu,Yana sakin Bullet ɗin mai girman gaske nan take Ya hau saman motarsu Ya fashe gaba ɗaya Wuta ta kama ci a bayan boot ɗin Motar,Hakan yasa motar ta dakata da tafiya,ganin sun ci nasara akansu yasa suka tsayar da motocinsu,Suka diddiro daga cikinta kusan Su takwas ne,Ƙirar jikinsu gwanin ban tsoro,babu ɗigon imani akan fuskarsu,kowanne hannunshi ruƙe da manyan makamai,
Suna ƙarasowa gaban motar,ɗaya daga cikin samudawan nan ya damƙi murfin motar ya 6alleshi,hannu yakai tare da damƙo rigar mutumin dake acikin motar ya wurgoshi waje,basu tashi ankara ba,Sae da Mai tuƙin motar ya fito yana faman ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'una,Leƙa cikin motar sukayi Wayaam basu ga Amrish da yaron ba,Ashe Ba motarsu bace,Sunyi mistake Saboda mai wannan motar da suka kama iri ɗaya ce da motar da suka bi su Amrish,
Da sauri Suka koma cikin motocinsu,A guje suka ja motar,Sunbar bayin Allah da aikin neman taimakon kashe masu wutar motarsu,don ma Allah yasa babu wanda ya raunata acikinsu,
A 6angaren Su Amrish kuwa,mutumin dake tuƙa motarsu ne ya umarce ta data jefar da wayoyin hannunta gaba ɗayansu,nan take ta zuge glass ɗin motar ta wurgar dasu waje,Bayan ta jefar dasu sai ya Canza hanya da wani irin gudu yabar titin,Su kuma waɗannan miyagun da suka fara yin tracking ɗin Layin wayar Hajiya sarat na ƙaramar nokia ɗin da aka basu,Ta hanyar laptop ɗin dake a hannun wani kwararre acikinsu,Sae location ɗin ya dinga nuna masu hanyar da Amrish ta jefar da wayoyin,Nan fa suka miƙi hanyar cike da sa ran zasu kamasu,Lokacin da motarsu ƙare kukanka ta ƙarasa inda Location ɗin Ya basu,Sai suka tsayar da motocinsu,A zafafe suka fito suna waige waigen neman inda suka ajiye motarsu,Sai da suka gama shan wahalar nemansu a Area ɗin wurin abun takaici sai ga wayoyin sun tsinta yashe a ƙasa,Rai a matuƙar 6ace suka hanzarta komawa cikin motocinsu batare da sun ɗauki wayoyin ba,Nan fa suka ruɗe saboda hanyoyi ne guda uku,Ta hannun dama da kuma ta hannun hagu,Ga kuma wadda ta mike straight,To fa sun ruɗe a wannan lokacin,Basu san ta wace hanya su Amrish suka bi ba,A ƙarshe kawai suka raba motocinsu dama guda uku ne ɗaya tabi straight,ɗaya tabi Left ɗayar kuma tabi Right,Don sunsan Dole a ɗaya daga cikin hanyoyin suka bi,
*Boss Bature*
Wuraren ƙarfe 2 na rana,
Wayar Ishaq ta soma ringing,A lokacin dawowarshi kenan daga wurin aiki,Buɗe mashi mota sergeant Yayi Ya fito daga cikin motar hannunshi ruƙe da wayarshi,picking call ɗin Yayi tare da kara wayar a kunnanshi,
Fuskarshi ɗauke da murmushi ya soma magana"Mutanan Damaturu,Sai yau ake jinku"?
On the other hand Hafsat tace"Wlh Daddy fushi nake dakai,you forgot about me,"
"Nima ae fushi nake dake,tunda na baro damaturu kin ƙara kirana ne?Ko irin Morning message ɗin nan babu ko,Yanzu da ace ban kiraki ba da shikenan bazaki neme ni ba,"ya ɗanyi maganar yana ɗaure fuska kamar tana agabanshi,
"Shikenan na ɗauki laifin,Am so sorry,Amma daddy meyasa ka canza Layinka?in na kira wancen Mtn ɗin bana samun shi"
"Kinga yanzu na dawo daga wurin aiki,Agajiye nake,bari na ɗan samu natsuwa I will call u later,"
A ɗan shagwa6e tace"dan Allah Daddy,idan ka huta kada ka manta ka kirani akwai maganar da nakeso nayi dakai,"
"Toh,"ya amsa tare da kashe kiran Ya nufi cikin gidan aranshi yana faɗin"yanzu haka saboda Mommynta ne yasa ta kira ni,lokacin daya shiga gidan ya yi mamakin yarda aka gyara mashi ko'ina fess,murmushi ya dinga saki don ya san cewa aikin hajjaju ne,wani irin ƙamshi ke tashi acikin palourn,
Ga lafiyayyen abinci An jera mashi asaman dining,Dama da wata matsiyaciyar yunwa ya dawo,A hanzarce ya haura upstairs ya shige Bedroom ɗinshi,Bayan ya rage kayan jikinshi ya faɗa cikin toilet,Within mins Ya fito Ya kimtsa kanshi cikin jallabiya,Saukowa Downstairs Yayi kaitsaye ya nufi dining ya zauna,Da kanshi Yayi serving ɗin abincin ya zauna yana ci yana murmushi kamar wani zautacce,Sai da ya kammala cin abinci,tukunna ya koma saman Sofa ya zauna tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,
Wayarshi ya ɗauko ya