Showing 63001 words to 66000 words out of 432432 words

Chapter 22 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

salwantar da yaran,ina da tabbacin cewa so suke su zubar dasu kaci gaba dasa musu ido,daga yanzu banaso ko bacci ka dunga yi osman, saboda wannan lokacin ne mafi haɗari, aduk lokacin da maƙiyin ka ya canza maka salo na soyayya to kaji tsoransa halakar dakai zaiyi,"

Tun daga lokacin da Major ya sanar dashi haka, bawan Allah osman bai ƙara yin bacci ba, koda bashi ke akan duty ba, yana nan yana lura da shige da ficen da hafsat keyi dasu hossana,



A ranar da baba alamu zai tafi dasu hossana, akan idon osman Aunty babba ta fito tare dasu jahad da hossana,ta buɗe masu motar hafsat suka shiga, duk yana kallonsu, daga bisani kuma sai yaga hafsat tafito hannunta ɗauke da trolley hakan na nufin wani ne zaiyi balaguro, bayan hafsat ta shiga cikin motar taja motar tafito dasu daga cikin gidan, cikin sauri osman ya hau mashine ɗinsa da yake ajiyesa acikin gidan yabi bayansu a hankali yake tuƙa mashin ɗin don kar su ganshi, da hafsat ta tsayar da motar abakin titi tana jiran ƙarasowar baba alamu, sai osman ya dakata da tukin mashin ɗinsa, cikin sauri ya sauka tare da samun wuri ya cire rigar jikinsa ta kakin sojoji ya 6oyeta a ƙarƙashin wani benci dake agaban wani shago dake rufe, sannan ya tu6e wandon jikinsa ma, ya ajiyesa a ƙarkashin bencin bakomai yasa shi yin hakan ba face don karsu ganshi da kakin sojoji yana binsu, Asirin shi zaiyi saurin tonuwa ne,


Sai daya rage daga shi sai farar shirt da gajeran wando ajikinsa a lokacin motar baba alamu taƙaraso,cikin sauri Osman ya zuƙunna agaban mashin ɗin tamkar ya samu matsala yana gyaransa, alhalin nan duk salon dabaru ne na jami'ae,

yana gyaran mashin ɗin yana satar kallonsu, akan idonshi hafsat ta buɗe ma jahad da hossana mota suka fito sannan ta ɗauko masu trolley ɗinsu da food basket ɗinsu ta basu,bayan hafsat ta tafi, baba alamu ya amshi akwatin Su hossana da jahad ya wurga cikin boot ɗin motarsa, daga nan jahad da hossana suka shiga cikin motar, shima ya shiga tare da tashin motar suka tafi, cikin sauri Osman ya haye mashin ɗinsa tare da tashinsa yabi bayan motar baba alamu da gudun gaske amma bai bari ya ƙurewa motarsa ba kasancewar Motar baba alamu glass ɗin jikinta duk ya fashe, muddin osaman ya ƙurewa motar tofa zasu iya hango shi, hakan yasa ya basu tazara sosai, yana cikin tuƙin mashin ɗin ya ɗan jinkirta tare da zura hannu cikin aljihun wandonsa ya zaro wayarsa tare da bugama major kira, bayan ya ɗaga yake sanar dashi duk abunda ke faruwa,

Hankali tashe major yace "Osman kada ka bari ya kubce maka, kaci gaba da bin motarsa, sannan kabar wayarka a kunne zamu biyo diddigin layinka, mu zo inda kuke," bayan osman ya amsa masa, ya mayar da wayar, sannan ya ƙara ma mashin ɗinsa gudu, a lokacin da motar baba alamu tashiga dajin da gudun gaske, jahad na ƙoƙarin fitowa tana ihu bayan ta samu ta harba murfin motar ya buɗe, sai baba alamu ya girgiza motar da mugunta, ta faɗo ƙasa timmmm goshinta ya bugu, ta taso da gudu tana bin motar tana kiran sunan hossana daga bisani ta yanke jiki ta faɗi, adai-dai lokacin shi kuma osman ya ƙaraso ba komai yasa shi yin jinkiri ba fa ce wayar da yayi da major shiyasa bai ƙaraso akan lokaci ba har baba alamu ya kubce mashi,

ganin jahad da yayi yashe a ƙasa ta sume ga jini, ba ƙaramin razana yayi ba, cikin hanzari yayi wurgi da mashin ɗinsa ya nufe ta hankali atashe, ya zuƙunna gabanta yana faɗin "ke!ke!! tashi ki tashi dan Allah, kada ki mutu,"

Adai-dai lokacin kuma motarsu Marshal Omar ta faso cikin dajin ta hanyar tracking layin osman da sukayi yasa har suka ci nasarar cimma inda yake,

Osman na ganin motarsu Marshal yasan cewa sune aciki, a lokacin omar ya zuge glass ɗin motar a tsorace ganin jahad kwance duk jini a goshinta, harya harzuƙa zai fito daga cikin motar, cikin sauri Osman yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar, gashi can ya miƙi hanyar dama da ita, don Allah ku ceci rayuwarta," jin haka yasa Omar fasa fitowa daga cikin motar, cikin sauri major yaja motar da gudun gaske suka bi motar baba alamu a lokacin ya ɗanyi masu nisa, hayaƙin da bayan motar baba alamu ke fitarwa shine yasa suka gane hanyar da yabi,

suna isa basu tsaya buɗe kopar katakon gidan gonar ba, kai tsaye major yabi ta ƙopar atsiyace ya tarwatsa katakon gidan gonar suka shige,

Tamkar zaki haka omar ya fito daga cikin motar ya afkawa ɗakin da baba alamu ya shige da hossana,



*Wannan shine abunda ya faru taƙaice kenan*



"Ya omar ina hossana take ita'? Omar yace"hossana tana cikin ƙoshin lafiya, itama ƙarin jini akeyi mata, yanzu haka bacci take sha tana a kusa da ɗakin nan," ajiyar zuciya jahad ta saki kafin ta kuma cewa "ya omar kullum hossana saita ambaci sunanka, komai akayi sai tace "ya Omar fa," ita bata son rabuwa da yaya omar ɗinta,"

Murmushi Omar ya saki jin abunda jahad tace,

"Amma ya Omar ba zaka ƙara rabuwa damu ba ko? dan Allah kada ka haɗamu da kowa kabarmu kawai a wurin ka, kai kaɗai ke son mu," tayi maganar idonta akansa tana jiran amsar shi,

Omar yace "ko wancan time ɗin bada son raina nabar ku ba, jahad you're always in my mind ina jin ku araina,amma yanzu komai ya wuce just forget about the past, ku ƙaddara cewa wani abu bai ta6a faruwa da rayuwarku ba na ƙunci, saboda yaya omar ɗinku ya shirya maku kyakkyawar rayuwa ta jin daɗi da walwala, masarauta ce wadda ku kaɗai zaku mulketa sai yadda kuka ga dama zakuyi acikinta, hatta yaya omar ɗinku zai zama tamkar bawa agare ku,"

dariya kawai jahad ke faman tiƙa saboda murnar jin abunda omar ke cewa, hatta dr Emran da Camila dake tsaye murmushi kawai suke saki, shima major dake tsaye daga ƙopar ɗakin murmushi ne a fuskarsa, ƙarasa shigowa ciki yayi yana cewa "Sir idan ba damuwa inaso a bani muƙami acikin masarautar nan, zanso na zama sojan dake kula da princesss ɗin dake acikinta, bama ni kaɗai ba ga abokina osman nan shima yana roƙon gimbiya jahad da ta bashi damar zama ɗaya daga cikin masu kula dasu,"

Abun sai ya zama tamkar shirin wasan kwaikwayo gaba ɗayansu dariya ce a fuskarsu, hakan ba ƙaramin farantawa omar rai yayi ba ganin yadda jahad ke faman tiƙar dariya, sai yaji sanyi aransa sam ya gaza janye idonsa akanta,

Muryar Camila (kameela) ce ta katse su da cewa "Yalla6ai nima idan ba damuwa ina neman alfarmar zama ɗaya daga cikin masu yi ma gimbiya jahad hidima, ko da a matsayin jakadiya ne mafi kusanci dasu,"

Fashewa da dariya jahad ta ƙara yi daga kwancen da take har omar na cewa "Bi a sannu my baby, kada ki shaƙe,"

gaba ɗayansu sun natsu sai raha akeyi, suka ji Muryar hosana kamar daga sama tace"YA OMAR,"

Atare suka juya suna kallonta, tsaye take a bakin ƙopar ɗakin daker take buɗe idanunta tana kallonsu, hannu tasa ta murza idonta sannan ta ƙara buɗe su da kyau donta tabbatar da abunda idonta ke gane mata, tabbas kuwa shine wato yaya Omar ɗinta,

tsananin farin ciki ne yasa hossana ƙarasa shigewa ciki da gudun gaske tana isa inda Omar yake ta zube saman guiwowinta tare da kifa kanta asaman laps ɗinsa tana kuka,

Shiru su kayi gaba ɗayansu na wani lokaci suna sauraren kukan da hossana ke yi, gaba ɗaya jikin omar ya gama mutuwa saboda yasan yarda yarinyar ke tsananin ƙaunarsa dole tayi kewarsa, hannu omar yasa tare da shafa gashin kan hossana cikin muryar lallashi yace "Am so sorry hossana,nasan nayi laifi ban ma san da wane baki zan iya baki haƙuri ba,"

Maimakon ta ɗago sai ta daddage ta gartsa mashi ciwo a laps ɗinsa, runtse ido omar yayi saboda yaji zafin cizon, babu wanda ya lura da abunda ke faruwa sai jahad, tun da taga omar ya runtse ido tasan cewa Hossana Cizon shi tayi,



tayi mashi hakan ne don yasan irin raɗaɗin da suka ji acikin zuciyoyinsu na ƙin zuwan da yayi ya tafi dasu,

buɗe idonsa yayi a hankali yana sauke ajiyar zuciya ya kalle ta, a lokacin itama ta ɗago tana faman huci ta ɗaure masa fuska tare da haɗe masa girar ƙasa da sama tana kallon shi,

Cikin sanyin murya ya sake maimaita "Am sorry again," ya furta tare da kai hannunsa a fuskarta yana share mata hawayenta dake kwaranyowa daga idonta,

Cikin kuka tace "Ya omar yanzu ka kyauta abunda kayi mana? ka tafi kabarmu cikin tashin hankali ko waiwayon mu, ba kayi ba yanzu da mun mutu shikenan bazan sake ganin Ka ba sai dai a lahira ko?

ƴar dariya omar yayi tare da cewa "Amma ae yanzun baku mutu ba ko? Kuna raye kuma ga yaya Omar ɗinku atare daku, mai yayi saura yanzu"? ya tambaya yana kallonta

Hossana tace "sai ka kaimu gidan ku inda kake rayuwa, don wlh duk inda zaka je, ƙafarka ƙafarmu, mu da kai mutu ka raba takalmin kaza," ta ƙare maganar tana zumbura baki,

Gaba ɗayansu na cikin ɗakin dariya kawai suke yi, Kallon dr emran omar yayi kafin yace "yanzu mai ya rage dr?yaushe kake tunanin za'a sallame su, in yaso sai acigaba da basu kulawa acan gida?

dr emran yace "zuwa night, ae jikinsu yayi ƙarfi yanzu saboda ƙarin jinin da akayi masu, idan ma ba damuwa Camila zata iya cigaba da kula da lafiyarsu, in har kana buƙatar hakan, tunda dama naji tace tana son zama hadimar princess ɗin naka,"

Murmushi suka saki gaba ɗayansu banda hossana don batasan zancen ba, tuni ta mayar da kanta akan laps dinsa tana faman sauke ajiyar zuciya,



dukkan tsanani yana tare da sauƙi, mahaƙurci kuma mawadaci ne wata rana, babu wani yanayi na rayuwa da yake kasance wa na dundundun, Innallaha ma'assabirin tabbas wannan haka yake, iya haƙuri dae su hossana sunyi kuma sun jurema duk wata jarabawa da suka fuskanta na ƙuncin rayuwa, basu fasa yin addu'a ba suna kai kukan su ga Allah ba kuma basu fidda rai da cewa Allah zai kawo masu ɗauki ba, idan muka sa haƙuri kowa zai cimma nasara, gashi yanzu zamu iya cewa Masha Allah 😍👑



**************Twins *******************

daker suka samu suka yi wanka suka canza kaya izuwa jeans da t-shirt suka fito wuraren ƙarfe 5 na yamma, tafiya suke yi gabansu na faduwa tsoransu kar suci karo da haroon don yanzu ya zamar masu tamkar dodo, suna cikin tafiya sai ga Junaid ya fito daga upstairs yana ganinsu ya ɗan zaro ido cike da murna yace "Yaya Jahan ina kuka shiga inata neman ku, naga da safe ko breakfast ba kuyi ba, duk na shiga damuwa," ya yi maganar tare da ƙarasa saukowa down ɗin yayi ya tunkaresu, suna tsaye baki asake suna kallon shi saboda neman shi suke yi ruwa a jallo,

yana ƙarasawa yabi su ɗaya bayan ɗaya yayi hugging ɗinsu tare da manna musu kiss a gefen fuskarsu, irin gaisuwar da suka saba,

Ganin sun zuba mashi ido batare da sunyi mashi magana ba yasa shi bubbuga ƙafarsa tare da cewa "Dan Allah wai menene haka duk kun Canzamin, ko magana ma ba zaku iya yi mun ba why pls? ya faɗi tamkar zaiyi kuka,

gyaran murya jahan yayi tare da cewa "no ba haka bane junaid, ba mu jin daɗi ne, ni da Ayaan shiyasa ka ganmu a haka, yanzu haka ma kai muka fito nema akwai maganar da muke son yi dakai, amma ba'a nan ba, acikin ɗakin ka,"

junaid yace "magana kuma dani? Allah yasa ba laifi nayi ba"

Murmushi Ayaan ya saki tare da cewa "ba laifi kayi mana ba junaid taimako ne ma zakayi mana,"

ruƙe ƙugunsa yayi sannan yace "Naji toh, amma kafin nan sai naga kun ci abinci tukunna, saboda baku ci komai ba tun safe ina sane da hakan, bayan na hana ku zama da yunwa,"

Yadda yayi maganar tamkar wani yayansu, alhalin sun girme shi,



Murmushi suka saki atare sannan jahan a ruƙo hannunsa tare da cewa "Zamu ci abincin ne,amma kafin nan, mu shiga daga ciki muyi magana,

tasa ƙeyarshi su kayi har cikin ɗakinsu, suka tsaya daga tsaye suna fuskantar shi, gaba ɗaya sun rasa ta inda zasu soma neman alfarmar nan a wurin junaid,

Ganin sun tsayar dashi sun zuba mashi ido yasa shi hasala tare da cewa "Yaya Jahan nifa bansan menene ma'anar zuba mun idon nan da kuka yi kuna kallona ba," ya faɗi yana hura hanci,

Ayaan ne ya soma magana "am...junaid ka gane, dama wata alfarma ce muke nema awurin ka,

"Am listening to u," junaid ya faɗi yana kallonsu

Jahan ya daura da cewa "junaid sabo da mu zakayi wannan abun, so muke ka kira Mommy a waya video call ka bata haƙuri sanna ka ambaci sunanta ka kirata da Mommy, dan Allah junaid.........' tunkan jahan ya ƙarasa maganar tasa junaid yabi ta gefensu zai fuce daga ɗakin yana cewa "da nasan wannan alfarmar zaku nema awurina, wlh da ban 6ata lokacina wurin sauraronta ba,

Cikin sauri suka ruƙo rigar jikinsa har suna haɗa baki wurin cewa "Janaid dan Allah ka taimaka ma rayuwarmu, kai kaɗai ne a yanzu zaka iya fitar damu daga halin da muke ciki pls junaid do this favour for us"

a fusace junaid ya fusge rigar shi daga hannunsu yace "Wlh bazanyi ba, ni bazan ta6a kiran wannan matar da sunan mommyna ba, saboda bata sona ta tsane ni, Yana faɗin hakan ya kama hanyar fita, Ayaan yayi sauri sake cafko rigarsa, aikuwa a fusace junaid ya sanya hannunsa tare da buge na Ayaan, rai a6ace jahan ya janyo shi tare da kwashe shi da mari, zaro ido junaid yayi yana kallonsu yayin da ya sanya hannunsa ya dafe kuncinsa saboda zafin marin da jahan yayi masa, tunda yake arayuwarsa zai iya cewa ba'a ta6a bugunsa ba, ko da wasa wani bai ta6a yin gigin ta6a fatar jikin junaid ba da sunan bugun, amma sai gashi yau an samu wasu daga cikin yayyansa da yake matuƙar ƙauna yasa hannu ya mare sa, tuni idonsa sun ciko da kwalla red lips ɗinsa har rawa suke yi wurin cewa "Yaya jahan ! Yau kai da kanka, kasa hannu ka mare ni? Saboda na bijire ma buƙatarku? akan abunda yake haƙkina nifa aka cuta, abun har yanzu yana yi mun ciwo azuciyata bana faɗi ne kawai..............' kuka ne yaci ƙarfinsa har ya gaza ƙarasa maganar tasa yaci gaba da sharar kwalla, tuni jikinsu yayi mugun sanyi musamman jahan daya mare sa, baisan lokacin da shima ya fashe da matsanancin kuka ba, hakan yasa junaid dakatawa da kukansa ganin yarda Yayansa jahan ke kuka agabansa tamkar ƙaramin yaro, nan take hankalinsa ya tashi cikin sauri yasanya hannayensa a fuskar jahan yana share masa hawayensa yana cewa "dan Allah yaya jahan ka daina kuka, bana son ganin hawayen nan naka, in dai ni ne na sanya ka, yin kuka wlh zan baka hakuri ka yafe mun bazan ƙara,

Cikin shessheƙar kuka jahan yace "junaid naji na tsani kaina fiye da tunaninka, wai yau ni ne na kasance mutun na farko daya fara ta6a lafiyar jikin ka, da wannan mummunan hannun nawa, ina danasanin wannan ranar kuma bazan ta6a yafe ma kaina ba..........' gaba ɗaya tausayin jahan ya gama kama junaid cikin sauri ya janyo shi ajikinsa tare da rungume shi sosai yana ɗan bubbuga bayansa, cikin muryar rarrashi yake cewa "Ba laifinka bane yaya jahan, Laifina ne nayi rashin kunya, na buge hannun ayaan duk da raina ne a6ace bansan nayi hakan ba, amma ku yafe mun abisa kuskuren da nayi maku bazan ƙara ba,'

gaba ɗayansu sun shiga cikin wani kalar yanayi, Ayaan kam tuni jikinsa ya gama mutuwa saboda tausayin junaid da kuma kansu daya kama shi,

Bayan sun tsagaita jahan ya janye jikinsa daga na junaid sannan yace "Junaid dan Allah kayi mana wannan alfarmar na roƙe ka kai kaɗae ne zaka iya fidda mu cikin halin da muke ciki, kuma nason kana tsananin son mu ba zaka so wani abu ya cutar damu ba,' ya ƙarasar maganar yana kallonsa da idanunsa da suka gama runewa,

Jiki a mace Jahan ya kalli Ayaan cikin tsananin damuwa, ganin junaid yayi shiru baice komai ba yasa su yin saurin zubewa agabansa saman guiwowinsu suna roƙonsa,

Cikin tsananin tashin hankali shima junaid ɗin ya zube saman guiwowinsa agabansu tare da fashewa da wani sabon kukan yana cewa "meyasa zakuyi mun haka?yaya Ayaan da ya jahan saboda me zaku duƙamin nifa ƙaninku ne, ku kuma yayyena ne dan Allah kudaina mun hakan banaso! banaso!!bana so!!" ya ƙarasa maganar tare da cewa "naji na amince zan kirata, Amma ba yanzu ba,"

ajiyar zuciya suka sauke gaba ɗayansu nan take suka ji wani irin sanyin ya ratsa zuciyoyinsu,

Ayaan yace "yaushe zaka kirata"? Junaid yace "an jima kaɗan," ya faɗi a shagwa6e

Murmushi suka saki gaba ɗayansu har haɗa hannu suke yi wurin goge masa hawayansa da suka wanke masa fuska, har lokacin suna a zuƙunne su duka ukun suna fuskantar juna,

Jahan yace "Am Sorry junaid, ka yafe mun marin da nayi maka, nayi dana sani sosai," ya faɗi cikin sanyin murya,

Junaid yace "gsky bazan yafe ba yaya Jahan har sai kunci abinci sannan nagani da idona tukunnan,

Ayaan yace "shikenan junaid komai kake so zamu yi,"

Murmushi ya saki sannan ya ruƙo hannayen su suka miƙe tsaye atare, bayan sunyi wiping tears ɗinsu, Sannan suka fito daga ɗakin nasu,

Ajere suka jera suna tafiya sun

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login