Showing 114001 words to 117000 words out of 432432 words

Chapter 39 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

abunda ya faru jiya,amma yarda take motsi da siraran la66anta tana karanta addu'oi'n neman tsari hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba, sai ya samu kan shi da shagala wurin kallon bakinta, tunanowa yayi da ranar daya turketa amatsayin mace yarda ta tsorata har ta sume mashi, shi kuma rayuwarshi mace mai shegen tsoro ba ƙaramin burgeshi takeyi ba,ba don komai ba sai don ya ruƙa tsorata ta don ya samu nishaɗi,
    ɗan gyara muryarshi yayi tare da cewa"jiya kin ban allura nayi ma kaina har nayi ƙoƙarin yin raping ɗinki, ko ba haka akayi ba? ya tambaya fuskarshi a ɗaure,. 
   hankali tashe sehrish ta shiga furta"innalallahi wa'inna ilaihirraji'un. Nashiga uku, kasan Allah ni bani bace na ɗauko allurar ba  bansan komai akai ba,. 
   shiru sgr yayi yana kallonta har lokacin taƙi buɗe idanunta, abunda bata sani ba shi guessing yayi bai tuna komai ba, amma yayi mata rijiya ta faɗa,
   cigaba da magana yayi anatse"then tell me who brought it to u"?
    shiru tayi lamo saboda tasan ba zata iya furta sunan haroon ba, ganin taƙi magana yasa shi daka mata tsawa tare da cewa"ba magana nake maki ba!!," wannan tsawar da yayi mata ne yasa ta sume mashi, dama sai da ranshi ya bashi,
  Saukowa daga saman gadon yayi tare da fucewa izuwa palour dinshi, kai tsaye ya wuce wurin fridge ɗinsa tare da buɗewa ya ɗauko bottle water mai sanyi, sannan ya koma cikin bedroom ɗin nashi,zama yayi daga gefen gadon tare da sanya hannu ya buɗe roban rubar saida ya fara sha sannan ya ɗebo a hannun shi ya yayyafa mata a fuskarta, a gigice ta ware idanunta kai tsaye suka shiga cikin nashi a lokacin ya mayar da  bottle din abakin shi yana ƙara shan ruwan, tamkar a mafarki take ganin abun har lokacin jikinta bai daina kerma ba, cire roban ruwan yayi daga bakin shi sannan ya mayar da murfin ya rufeta tare da ajiyewa saman side drawer ɗinshi,
    sannan yayi mata nuni da hanyar fita yace"zaki iya tafiya," cikin sauri ta sauko daga saman gadon nashi, hanyar fita ta nufa da sauri da sauri, jinkirtawa tayi tare da ɗan juyawa don ta saci kallon shi, samun shi tayi a kashingiɗe saman gadon ya aza head dinsa asaman pillow, eyes dinshi a lumshe tamkat zasu rufe amma hasken kwayar idonshi blue ya ɗan fito alamar bai runtse idanun duka ba,
   Muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa"akwai wani abu ne"? Cikin sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta fuce daga ɗakin, sai da tafara ɗaukar mayafinta dake zube a ƙasa, ta yafa shi akanta sannan ta fuce daga part ɗin nashi, tafiya take anatse fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi tayi mamakin yarda akai Sgr bai tuhumeta ba,bayan ya tuna duk abunda ya faru atsakaninsu jiya, tayi tunanin zata sha mari ne a wurin shi amma sai gashi abun yazo mata da sauƙi, har yau tana mamakin sauƙin kai irin nashi da ba kowa zai fahimta ba, amma tabbas bai da girman kai ko kaɗan, jan ajine kawai dake gare shi ko jinin sarauta bazai nuna mashi wannan ba, Domin kuwa shi kanshi Sarki ne mai cike da ƙarfin iko👑

  a hankali take taka steps ɗin down stairs zata sauko, jin alamar shigowar mutun cikin babban falon yasa ta tsagaitawa da tafiyar tana kallon shi, jahan ne ya shigo cikin falon hannun shi ruƙe da jakar kuɗin da zasu ba haroon, ganin yarda yake tafiya cikin sanɗa yasa ta gane cewa bai son wani ya ganshi cikin sauri ta ja da baya tare da samun wuri ta la6e,
   sai faman ƴan waige waige yake yi yaga ko akwai mutun amma wayaam ba kowa hakan yasa cikin sauri ya wuce bedroom ɗinsu, ajiyar zuciya sehrish ta sauke tare da lalla6awa ta fito kai tsaye ta nufi kitchen tana zullumin ko menene Jahan ya ɗauko acikin jakar hannunshi, da alama dae wani mugun abunne tunda har yake sanɗa don kar aganshi, ta faɗi acikin ranta a lokacin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin don ta zuba ma kanta abincin da zata ci,

   turo ƙopar yayi a hankali yashiga daga cikin ɗakin nasu, jin alamar shigowar mutun yasa ayaan dakatawa daga zirga zirgan da yake yi acikin ɗakin,
  Cikin sauri ya nufe shi yana cewa"Jahan ka tabbata babu wanda ya ganka"? Amsa mashi yayi da cewa"eh babu da alama duk sunyi bacci, kazo yanzu mu hanzarta mu kai mashi kuɗin," 
  Atare suka fito daga bedroom ɗin nasu,  duka suna sanye cikin jallabiya, ɗakin haroon suka nufa, koda suka ƙaraso ƙopar ɗakin a rufe take, kwankwasawa Jahan yashiga yi a hankali,
  "Su waye ne"? Ya tambaya daga ciki,
Har suna haɗa baki wurin cewa "twins ne ",
   kwance yake daga saman gadonshi,daga shi sai shorts ajikinshi ba riga, tasowa yayi tare da nufar kofan yasa hannu ya buɗe masu tare da cewa"ku shigo daga ciki," kallon juna su kayi kafin daga bisani suka shiga daga ciki,
  tunda haroon yayi arba da jakar kuɗin dake hannun jahan yashiga sakin murmushin nan na shu'umanci yana cewa"ince dae kuɗina ne acikin jakar nan ko"? yayi maganar tare da miƙa hannu zai kar6i jakar,janye ta jahan yayi tare da cewa"ka fara goge  video ɗin tukunna mu damƙa maka su," 
  ta6e baki yayi yana kallon su,kafin ya juya ya nufi saman gadonshi inda wayar shi ke ajiye ya ɗaukota, yatsan shi yasa ta buɗe sannan ya shiga wurin videos ɗinshi ya lalubo nasu daya ɗauka sannan ya miƙa masu tare da cewa"Gashi nan ku goge da kan ku,ina ga hakan zai fi ko"?  Kallon juna suka sake yi duk jikinsu yayi sanyin, tsoransu karya cuce su,ayaan ne ya kar6i wayar tashi yayi deleting ɗinsa gaba ɗaya, sannan ya kalli haroon ɗin dake ta faman sakin murmushi yace"ka  tabbata babu wani videon namu dake gare ka bayan wannan!? 
 ɗaga mashi gira yayi alamar eh, jahan yace'laptop ɗinka fa babu wani aciki"? nan ma ya sake cewa"babu wannan ne kawai gare ni," 
  ajiyar zuciya suka saki gaba ɗayansu,
 Miƙa mashi wayar Ayaan yayi, sannan jahan ya damƙa mashi jakar kuɗin, kar6a yayi yana cewa"kun tabbatar  cewa miliyan 80 ɗinne"?
  ayaan yace"ka ƙirga su mana sai kaga in sun cika," 

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
�?

Zuƙunnawa haroon yayi tare da zuge zeep ɗin jakar, sai ga bandir bandir ɗin ƴan dubu dubu, dami dami shaƙe acikinta, hannu yasa tare da curo bandir guɗa ɗaya yakai a saitin hancin shi yana shinshinasu yace"Anya wannan ba kuɗin ganye bane?harara suka watsa mashi jahan yace"a'a na bishiya ne," dariya haroon yayi yana faman shaƙa kuɗin a hancin shi,
  gaba ɗaya ransu ya gama 6aci burinsu ya ƙirga kuɗin yaga in sun cika, amma ya tsaya yi masu shegantaka,
   tass ya fiddo da kuɗin ya ƙirga su, duk dami ɗaya na dubu ɗari ne, a haka yayi counting ɗinsu 80 millions ne bayan ya kammala ƙirgasu, ya shiga cusa su acikin jakar kaf ya kwashe su, sai da ya zuge zeep ɗin sannan ya ɗago ya kalle s u cike da shaƙiyanci yace"Au na manta ban baku la'ada ba," 
  atare suka haɗa baki wurin cewa"mun fi ƙarfinsu,kai ke buƙatarsu kai daga ganin mu kasancewa ba matsiyata bane," 
  "Wow," ya furta yana tafa hannunshi "abu yayi kyau ƴa'ƴan billionaire,karfa kuce zaku gayamin magana!ku fuce mun daga ɗaki cikin salama," 
  Jahan yace"ba sai ka kore mu ba, mukan mu aƙagare muke da mu fita mubar maka wannan ƙazamin ɗakin naka wanda ko numfashi mutun daƙyar yake iya fitarwa!!kuma inaso ka sani Haroon baka ci bulus ba, zamu rama duk wani wulaƙancin da kayi mana!!
  yana kai ƙarshen maganar tashi ya ruƙe hannun ayaan suka juya zasu fita daga ɗakin karaf idonsu ya sauka akan mutumin dake shigowa cikin ɗakin, A wani irin firgice suka ja da baya gaba ɗayansu, shi kanshi Haroon ya sha jinin jikin shi saboda basu son da mutun ba, gaba ɗaya duk abunda suka tattauna acikin kunnanshi kaf ya gama naɗar komai, 
  hankali tashe suke kallon shi,kamar yarda shima hankali atashe yake kallon su 



Follow my tiktok acct 👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

Atare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da suka shaida cewa junaid ne,sai faman murza idanunshi yake yi da hannunshi,da alama magagin bacci ne ya shigo dashi,hakan ya basu tabbacin ba lallai in ya fahimci komae ba,
    cikin sauri Jahan yace"junaid tun yaushe kake anan?me kake yi har yanzu baka yi bacci ba"? 
  Cikin shagwa6a yace"nima bansan ya akai na shigo ba,dan Allah kutaimaka mun ku kaini ɗakin abbanmu in kwanta,wurin shi nake son zuwa,"
 Shu'umin Murmushi haroon yasaki yana kallon shi,
  ganin yarda yake binshi da kallo yasa su twins saurin ruƙe hannun junaid suka fuce dashi daga ɗakin,
    "Ayaan kaje kawai ka kwanta,ni bari nakai shi ɗakin Abban namu,"
Amsa mashi yayi da toh,sannan ya wuce bedroom ɗinsu,
  Shi kuma jahan zuƙunnawa yayi tare da ce mashi"ka hau na goya ka karka faɗi,"
   daddagewa junaid yayi ya haye bayanshi tare da ƙanƙame shi,sannan jahan ya miƙe ɗauke dashi abayansa ya wuce bedroom ɗin Abban nasu,
   A hankali ya tura ƙopar bedroom ɗin Abban nasu,yana kwance sai faman sharar bacci yake yi asaman royal bed ɗinshi,shiga da junaid ciki yayi a hankali ya sauke junaid saman gadon daga gefen abban nasu,
     gyara kwanciya junaid yayi tare da rungumo Abban nasu da hannunshi sannan yace ma Jahan"thank u,"
  murmushi jahan yayi ba ƙaramin burge shi yayi ba,sam junaid bashi da wata damuwa,sai yaji dama shine ke irin rayuwar shi,
   "Sleep well," ya furta tare da juyawa ya fuce daga bedroom ɗin yana sauke ajiyar zuciya,ɗakinsu ya koma lokacin daya shiga a kwance ya samu Ayaan har bacci yayi awon gaba da shi,shima wucewa yayi tare da haurawa saman gadon ya kwanta daga gefenshi,
Yaushe rabon da suyi bacci irin na daren nan harsun manta,saboda fargabar haroon kullum da damuwarshi suke kwana,yau dae sun huta ma rayuwarsu tunda sun sallame shi,

A 6angaren haroon kuwa tun bayan da suka fita ranshi ya raya mashi cewa tabbas akwai alamar tambaya game da zuwan junaid bedroom ɗinshi,saboda tun da yake junaid bai ta6a faɗowa ɗakinshi ba irin haka,duk irin magagin baccin da junaid yake yi bai ta6a zuwa ɗakin shi ba,amma sai yau kwatsam zai faɗo mashi ɗakin shi adai² lokacin da suke tattaunawa dasu twins kuma? Anya ba turo shi akayi ba�?
   zama yayi daga gefen gadon nashi yana tunani,dakyar ya iya tashi yakai hannu ya kinkimi jibgegiyar jakar kuɗin,wuri yayi mata acan cikin ɗakin nashi ya 6oyeta,
   Sannan ya koma tare da hayewa saman gadonshi ya kwanta,

     *********************
Washe gari 

A hankali ya buɗe idanunshi da su kayi mashi nauyi saboda bacci,hannu yasa tare da yaye blanket ɗin daya lullu6a dashi,miƙa hannu yayi tare da ɗaukar wayarshi dake ajiye saman bedside drawer dinshi,missed calls ya gani nasu hossana da jahad,tashi yayi daga zaune yana kallon screen ɗin wayar tashi,jiya yaso yaje ya duba su amma bai samu time ba,
   danna musu kira yayi tuni tashi ga ringing,
  A lokacin Jahad ce acikin falon zaune saman 2 seater tana ta jiran kiranshi,hossana kuwa tana can tana sharar bacci,
    har ta fidda ran cewa zai kirasu saiga kiran nashi ya shigo,cikin sauri ta miƙe ta nufi telephone ɗin tasa hannu ta dauka tare da karata a kunnanta,
   Cikin sanyin murya tace"Assalamu Alaikum ya Omar an tashi lafiya,"
  murmushi yasaki tamkar yana agabanta yace"lafiya lou Alhmdlh,nayi laifi ko?jiya banzo na duba ku ba,ayi mun afwa ina busy sosai,amma kuna araina,"
   "Babu komai ya Omar,dama mun damune akan rashin zuwan naka,kuma mun kira wayarka jiya da safe,baka a kusa sai dai matarka Aunty zainab ta ɗaga kiran," 
   "What!matata kuma? Wacece kuma aunty zainab?pls explain to me ni bangane me kike cewa ba,"
   murmushi jahad tayi tare da cewa"Ya omar meyasa ba ka sanar damu cewa kana da aure ba?baka so mu sani ne?
  Sam Omar baisan inda zanjen nata ya dosa ba,
   "Jahad nifa bansan me kike cewa ba! Wacece kuma matata?
  kafin jahad tace wani abu,sai ga hossana ta fito da saurin gaske jikinta sanye da kayan bacci,tana ƙarasowa tasa hannu ta kar6i telephone ɗin tare da karata a kunnanta cikin shagwa6a tace"eh mana ya omar ashe kana da aure,jiya da safe mun kira wayarka,mace ta ɗaga kiran tace mana kai mijinta ne kuma baka a kusa,sannan kuma tace mana tana ɗauke da juna biyu,kuma sunanta zainab amma kana kiranta da Hayaty,"
   tunkan ta ƙarasa maganar Omar yashiga 6a66aka dariya,natsuwa su kayi gaba dayansu suna sauraron sautin dariyarshi,
  "Ya omar kayi shiru baka ce komai ba," muryar hossana ce ta katse mashi dariyar tashi,daƙyar ya tsagaita tare da cewa"Am sorry na fahimci abunda kuke cewa,bazan iya yi maku bayani anan ba,insha Allah bayan na kammala breakfast dina zan shigo sai muyi magana ta fahimta ko? 
  Atare suka haɗa baki wurin cewa"Eh muna jiran zuwanka,sannan in ka tashi zuwa kazo mana tare da Hayati ɗinka muganta,"
   murmushi kawai yayi tare da rejecting call ɗin,sai lokacin ya duba kiran nasu da sukayi mashi jiya acikin wayarshi,cike da mamaki yaga kiran da sukayi mashi jiyan da safen kuma already an ɗaga kiran,natsuwa yayi yana tunanin wanene ya daga mashi kira harya tsara wannan ƙaryar,tabbas junaid zai iya yi mashi wannan aikin,.  
  Miƙewa yayi tare da saukowa daga saman gadon nashi,ya wuce cikin toilet dinshi,within 15 mins ya fito ya wuce wurin closet ɗinshi,tsaf ya kammala shiryawa cikin shadda purple colour ba ƙaramin kyau tayi mashi ba yabi jikinshi duka ya feshe shi da turare,
  Bayan ya ɗauki wayar shi ya fito tare da wuce wa part ɗin Rafayet,da sallama ya shiga ciki,baya acikin falon shi don haka ya wuce cikin bedroom ɗin shi,
  Yayi mamakin ganin shi a kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi,jikin shi na'a sanye da bathrobe da alama bai jima da fitowa daga wanka ba,
   Shiga ciki omar yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna sannan ya ambaci sunan shi a hankali"Rafayet wai haryanzu bacci kake yi?
   Yamutsa fuska yayi alamar idonshi biyu sannan yace"Omar,yau lalaci nake ji ajikina,duba fa ka gani tun ɗazu nayi wanka amma nagaza tashi in shirya kaina,"
   sakin baki Omar yayi yana kallon shi tare da jinjina kai yace"nasan meye matsalarka,wato har yanzu abun nan bai bar jikinka ba ko?

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
�?

   "Mekenan"? Sgr ya tambaya yana kallon shi daga kwancen da yake,
   Murmushi Omar yasaki batare da yace komai ba,
   Miƙewa Sgr yayi tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna shi da Omar yace"Na fa tuna duk abunda ya faru jiya a tsakanina da yarinyar nan,"!
  "dagaske"? Omar ya faɗi da ɗan mamaki a fuskarshi,
  "yeah,amma bakomai na tuna ba,so nake ka faɗamun gaskiyar abunda ya faru,time ɗin da ka tarar damu asaman gadon nan,shin na cire shorts ɗin jikina ko ban cire ba"?
   tunkan ya ƙarasa maganar omar ya soma sakin dariya,
  Ɗaure fuska sgr yayi tare da cewa"pls Omar banason wasa,just tell me the truth,cos banaso yarinya ta raina ni,"
    tsagaitawa omar yayi sannan ya zayyana mashi dukkan abunda ya faru tsakanin shi da Sehrish,

   hannu sgr yasa tare da dafe forehead ɗinshi yace"OMG!Omar ashe kaine ka katse mun jin daɗina a wannan lokacin!meyasa baka bari na ƙarasa aikina ba"? ya ƙarasa maganar yana jifar shi da harara,
   dariya omar ya kuma yi kafin yace"nifa taimakonka nayi,kisan kai fa zakayi,"
   tsuke fuska yayi tare da cewa"babu wani nan,ni narasa meyasa kake mun haka,"
  Yayi maganar tare da kai hannu ya dauki pillow ya wurga mashi shi a fuskarshi,tarbe pillow ɗin Omar yayi a hannunshi tare da cewa"Am sorry bro,bansan abun yayi hurting ɗinka ba,amma ae ko yanzu bata 6aci ba,kasan inason farin cikin ka,bari natashi naje na kira maka yarinyar sai ka ƙarasa aikin naka,"
  Yana kai ƙarshen maganar tashi ya mike tare da nufar  hanyar fita daga bedroom ɗin  yana  karashe dariyar shi,yana jiyo muryar sgr cike da zolaya yana cewa"Am waiting,"

Kai tsaye bayan Omar ya fito daga sashen sgr down stairs ya sauko tare da fuce wa daga main palour din,ko breakfast din bai tsaya yayi ba ya wuce wurinsu hossana,

Wuraren ƙarfe tara kiran Amrish ya tashe ta daga dogon baccin daya ɗauke ta tun bayan sallar asuba,dakyar ta iya buɗe idanunta da sukayi nauyi saboda bacci,hannu takai tare da daukar wayar dake ajiye asaman side drawer ɗinta,picking call ɗin tayi tare da kara wayar a kunnanta a kasalance tace"Assalamu alaikum Amrish irin wannan kira haka tunda sanyin safiya"?
   daga can 6angaren Amrish tace"Sleeping sickness wai kina nufin har zuwa yanzu baki tashi daga bacci ba?duba time ki gani kusan 9 fa yanzu,"
  Jin haka yasa sehrish sa hannu tare da janye blanket ɗin jikinta ta tashi daga zaune tana kallon clock, ɗan xaro ido tayi tare da cewa"subhanallahi wai har 9 tayi?meyasa aunty azmee bata tashe ni ba,ya ilahi," 
  dariya amrish tayi tare da cewa"kin cika bacci reeshi yakama kije kiga psychiatric doctor ya duba brain ɗinki,"
   ɗaure fuska sehrish tayi kamar tana agabanta tace"oh ashe dama kallon da kike mun kenan ko?
     muryarta cike da dariya tace"no ba haka bane inason lafiyarki ne shiyasa na baki shawarar kije aduba ki,"
   "Okey thanks for ur advise amma fa ni ba inda zanje,da raina da lafiyata bazan kwasa na tafi asibiti ba,salon su ja man bala'e," 
ƙarasa maganar tayi tare da cewa"pls inason zan shiga kitchen yanzu,i wll call u later bye," 
   sallama su kayi da amrish sannan ta mayar da wayar saman side drawer ta ajiyeta,
saukowa tayi daga saman gadon cikin sauri ta wuce cikin toilet, brush tayi tare da wanko fuskarta sannan ta fito ta wuce wurin wardrobe ɗinta,buɗewa tayi tare da ɗauko mayafi ta daure shi akanta kamar ɗan kwali,

Lokacin da fito har azmee ta kammala jera masu breakfast ɗin asaman dining,junaid ta samu tare da fawan zaune suna yin breakfast dinsu,kamar waɗanda yunwa ta koro sai faman turawa suke yi abakinsu suna ci,
   dagowa junaid yayi tare da kallonta nan take ya sakar mata murmushi tare da kiran sunanta"sehrish," 
  Juyowa fawan yayi tare da kallonta yace"ke zo nan," 
  nan da nan taji gabanta ya faɗi dama basu ta6a magana dashi ba,
  jiki asanyaye ta ƙarasa inda suke dai dai kusa dashi sannan ta tsaya tana faman ƴan kame kame,
   cikin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login