Showing 393001 words to 396000 words out of 432432 words

Chapter 132 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

Ga uban Ga kuma ƴa'ƴansu,"ya ƙarasa maganar yana dariya,
Alex tace "U'r Highly welcome, Abusufyan's Family,Am glad to see guys "ta yi maganar tare da ƙarasawa ta rungumo Abu ajikinta,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,

Sun jima a waje suna gaisawa kafin daga bisani suka koma babban falon gidan,Kowa dake acikin gidan sai da ya hallara A falon,Abusufyan ya shiga gabatar ma abu kowa,Sun yi farin ciki sosai,duk da tashin hankalin da suke ciki hakan bai hanasu yin Murnar dawowar Uncle ɗinsu ba tare da Oummansu rishi,Abusufyan ya lura da yanayin fuskokinsu,abun ya ɗaure mashi kai,mutanen gidan duk sun rame sunyi duhu,bashi kaɗai ba hatta Sehrish ta ankara da canzawar da mutanen gidan su kayi,Sai faman wurga ido takeyi taga ko junaid zai fito amma shiru babu shi,Ranta ne ya bata cewar ko sun fita tare dasu Babban yaya ne tunda bata gansu ba acikin gidan,

Basu tashi sanin halin da Family ɗin suke ciki ba,Sai da suka huce gajiyarsu,tukunna Abba ya sanar da Abusufyan shima ɗin don ya matsa mashi ne akan son ganin junaid,Hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin anyi garkuwa dasu Junaid,baima son lokacin da ya rufe Abba da faɗa ba saboda ƙin sanar dashi da sukayi,Don me zasu 6oye mashi abunda ke faruwa acikin gidan,abun ya ƙona mashi rai,Har cikin ranshi baiji daɗin hakan ba,har ƙwalla saida ya zubar,

Yinin ranar Abu na tare da ƴan ukunta a bedroom ɗinsu,Sun sha firar yaushe rabo,har bacci ya ɗaukesu atare saman gadon,basu suka farka ba sai wuraren Sallar Magriba,

Bayan kowannansu yayo alwala Jahad ta shimfiɗa masu darduma suka jera atare da Oummansu,a tsanake sukayi sallar har suka kammala,basu tashi daga saman dardumar ba,ɗaga hannayensu suka yi sama suka shiga karanto addu'o'a abakunansu suna masu kara mika godiyar su ga Allah(S.W.A),

Allah Allah Sehrish take yi su kammala Sallar taja jahad gefe saboda ta tambayeta ina junaid yake sannan kuma ta bata Labarin Artabun da suka yi tsakaninsu da ya sayyadi,ita ma jahad ɗin a ƙagare take dasu ke6e ita da Sehrish,Don ta bata labarin mutuwar junaid,kota samu ta rage raɗaɗin dake acikin zuciyarta,bazata iya 6oyema Sehrish ba,duk da An gargaɗeta akan karta fadama kowa,

Basu suka samu lokacin kebewa da junansu ba,Sai bayan sallar Isha'e,kowa ya hallara a dining area,Suna cin abincin darensu,

Su biyu suka rage acikin bedroom ɗinsu,Zaune daga gefen gadonsu,kowa yayi tsit,na wani lokaci kafin Sehrish tace"Jahad,tun ɗazu nakeso na tambayeki game da canzawar dana ga mutanen gidan nan sunyi,kowa ya rame yayi duhu,musamman ke kamar kin yi ciwo,"
Cikin sanyin murya Jahad tace"Labari ne mara daɗin ji Sehrish,Zan faɗa maki amma ina gudun na jefa ki cikin tashin hankali,"
"Kada ki damu jahad,ki faɗamun koma menene,in sha Allah zan jure bazan tashi hankali na ba,"
"Shikenan zan faɗa maki Amma kafin nan inaso ki yi mun alƙawarin cewa bazaki faɗa ma kowa ba"
..Sehrish tace"I promised you jahad,babu wanda zaiji abunda muka tattauna dake,"
Shiru jahad ta ɗan yi yayin da take yin wasa da yatsun hannunta,
"Ina sauraronki jahad,"ta faɗi hakan ne don a ƙagare take da ta ji abunda jahad zata sanar da ita,
"Sehrish!munyi babban rashi,wanda ya raunata zukatanmu,"
..tunkan ta ƙarasa maganar sehrish taji gabanta ya faɗi rasss,
Aruɗe tace"Jahad kada ki ce mun junaid ya mutu......!"
Hawaye ne suka fara saukowa daga cikin idanun Jahad,bata 6oye mata komai ba game da mutuwar Junaid,Abun mamaki sai taga Sehrish na Zabga murmushi kamar wata zautacciya,
Bata karaya ba,cigaba da magana tayi"Babu wanda yasan ainihin abunda ya faru,daga ni sai su ya Omar sai kuma Jami'an ƴan sandan da suke je wurin da kuma Sojojin dasu ya Omar suka je dasu,"
Dakatawa tayi da yin maganar tare da kallon Sehrish,wadda ke ta sakin murmushi,
Fashewa da kuka Jahad tayi tare da cewa"Sehrish meyasa kike yin murmushi?na faɗa maki ne don in rage raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata,wlh da kinsan halin da muka shiga ni dasu Ya Omar da baki yi mana dariya ba,"tana kai ƙarshen maganar ta ƙara sautin kukan nata,
Sai lokacin Sehrish ta tsagaita da yin dariyar,Sannan ta soma magana"Haba Jahad,taya zaki ce mun Junaid ya mutu farat ɗaya in yarda?bazan ƙaryata ki ba,mutuwa na akan kowa babu wanda yafi ƙarfinta,Amma ni dai ban yarda cewa junaid ya mutu ba,tunda banga gawarshi ba,"tuni hawaye sun cicciko acikin idanuwanta,
Cikin Shesshekar kuka jahad tace"Taya za'ae kiga gawarshi!nace maki ko ƙashi ba'a samu ba daga sassan jikinshi,Saboda ya ruga da ya ƙone ƙurmus ya zama toka,"
"Jahad ni ban yarda ba,Allah Junaid ɗinmu bai mutu ba,ki daina wahalar da kanki wurin faɗa mun,"
Rai a6ace Jahad tace"Wlh dole ki yarda Sehrish!meyasa zakiyi mun haka!Maimakon ki tayani jimamin rashin shi amma shine kike ƙara jefa ni cikin damuwa,"
Girgiza kai sehrish ta shiga yi tana faɗin'wlh bazan yarda ba,"tashin hankaline yasa Sehrish ta burkice mata,
"Ko kin ƙi ko kin so dole ki yarda Sehrish,Junaid has gone forever,"
Miƙewa Sehrish tayi jiki ba ƙwari ta nufi toilet,Shigewa ciki tayi tare da jan ƙopar ta rufe,
Zuƙunnawa tayi ajikin ƙopar,sai lokacin ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,
"Allah sarki Junaid,Allah ya jiƙanka,bazan ta6a mantawa da halarcin da kayi mun ba,

💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*




Zuƙunnawa tayi ajikin ƙopar,sai lokacin ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,

"Allah sarki Junaid,Allah ya jiƙanka,bazan ta6a mantawa da halarcin da kayi mun ba,Allah yasa ƙarshen wahalarka kenan"

Sai da tayi mai isarta,Sannan ta miƙe ta nufi basin,Fanfo ta kunna ta wanke fuskarta,bayan ta kashe shi ta fito daga toilet ɗin,Har lokacin Jahad na zaune tana matsar kwalla,
Wuri sehrish ta samu gefenta,ta zauna yadda kasan ba ita bace tasha kuka acikin toilet ba,tayi hakan ne saboda batason jahad taga rauninta,hakan zaisa itama jahad ɗin ta ƙara shiga damuwa,
"Jahad,kuka bashi ne magani ba,Allah ya jiƙanshi ya gafarta mashi,bazan iya misalta raɗaɗin dana ji acikin Zuciyata ba,Allah sarki junaid,Yayi mun abubuwan da bazan ta6a mantawa ba,"dakatawa ta ɗan yi da yin maganar,yayin da take tariyo rayuwarsu ta baya ita da junaid,
"Muna da kusanci da juna dani dashi tamkar abokai muke,ashe ɗan uwana ne shi," tana magana hawaye na zuba akan fuskarta,jurewa kawai take yi,Zuciyarta tayi mata nauyi sosai ga wani raɗaɗi da take ji,daga ta runtse idanuwanta fuskarshi kawai take gani,
Sai lokacin Jahad ta tsagaita da yin kukan nata,kallon sehrish tayi da idanuwanta waɗanda suka yi jawur dasu sun ƙankance saboda yawan kuka,
"Yaya rafayet da Ya Omar suna cikin tashin hankali Sehrish,baki ga yadda suka koma ba,Nafi jin tausayinsu akaina,ba don son ransu ba suka 6oye mutuwar junaid,sunyi hakan ne saboda su ceto rayuwar Abba daga rasa shi,sai gashi kuma abun ya fara damunsu,Yanzu kullum mutanen gidan nan suna sa ran dawowar junaid bansan ya zasu ƙare ba duk ranar da suka ji cewa junaid ya mutu ba garkuwa akayi dashi ba,"ƙarasa maganar tayi tare da sanya tafin hannunta saman fuskarta,ta sake fashewa da wani kukan,
Jikin sehrish ba ƙaramin sanyi yayi ba,abun ya ta6a mata zuciyarta sosai,
"In sha Allah,Zamu tayasu da addu'a akan Allah ya kawo masu mafita,"Acewar sehrish,
Sun jima suna jimamin mutuwar junaid,kafin daga bisani Jahad tace"Baki fadamun labarin rayuwarku a kano ba?Rashin kwanciyar hankaline ya hana in kiraku,Ni ban ma san inda na yarda wayata ba,"
Nan sehrish ta labarta mata abunda ya faru zuwansu kano har zuwan ya sayyadi,"
Murmushin takaici jahad ta saki kafin tace"Allah ya tsine ma la'anannan mutumin nan,Dama saida raina ya bani cewa shine ke bibiyar rayuwarmu,ta Allah ba tashi ba,ƙarshen shi ne yazo shiyasa yake bibiyar ajalinshi batare da ya sani ba....."
"Jahad,Nifa ina zargin cewa su ne suka kashe Junaid,tabbaci ma nake dashi,tunda yace Family ɗinmu a tafin hannunsu yake,kuma duk motsin mu akan idonsu yake wannan ya tabbatar mun da cewa,Suna Atare damu,"
Jinjina kai jahad tayi"Nima yanzu shi nake zargi,bayan shi kuma ina tunanin akwai wani mai take masa baya,ko kuma wanda yake take ma baya,Dole akwai wani a kusa damu,Lamarin ma ya fara bani tsoro Rishi,ɗan adam ba abun yarda bane,Ke dai kawai ki kalli mutum,"
cike da takaici sehrish tace "Wlh ji nake da ina da halin da zan iya taimaka masu Babban yaya dana taimaka masu,Amma zamu tayasu da Addu'a dare da rana,That's the only solution......"

Turo ƙopar da akayi ne yasa suka dakata da yin maganar,atare suka ɗago don suga wanene
Hosana ce atsaye sai faman lasar hannunta take yi,bakinta duk maikon abinci tace"Waiku ba zaku zo muci abinci ba"?
A fusace Jahad ta warci pillow tare da wurga mata shi ya sauka akan fuskarta,
"Sakarya kawai,Ci kaɗai kika sani,Ba za'aci abincin ba,sai kace bakisan Halin da ake ciki ba,"
Harara hosana ta jefa mata,kafin tace"Ae bani na kar zoman ba,Rataya aka bani,"guntun tsoki taja tare da jan ƙopar ta fuce tana raira waƙa,
Girgiza kai Sehrish tayi tare da cewa"Allah ya baki lafiya Hosana,"
"Ameen,"jahad ta amsa a yayin da take gyara kwanciyarta saman gadon,



Wuraren ƙarfe Goma Sha biyu na dare,Kowa ya yi shirin kwanciya,A saman gadonsu Abu ta kwanta tare da Hosana da Jahad,Gadon yayi masu kaɗan su kwana su huɗu hakan yasa ta sanar dasu cewa zata wuce ɗakin Aunty Azmee ta kwana acan,fitowa tayi daga cikin dakinsu jikinta sanye da jallabiya,

Babu kowa A main palour ɗin,Da alama duk sunyi bacci koda basuyi bacci ba,to suna a bedrooms ɗinsu Ne,

Upstairs ta wuce Part ɗin Sgr,hannu tasa ta tura ƙopar tare da shigewa ciki,sai da gabanta ya faɗi ganin irin dattin da falonshi yayi,komai a hargitse,wannan ya ƙara tabbatar mata da cewar babu Lafiya,Mutun mai tsafta irin Sgr bazai bar part ɗinsa da dauɗa ba irin haka,

Ashe bata ga komai a falon ba,Sai da ta shiga bedroom ɗinshi,Tashin sense,tun A ƙopar ɗakin ta fara cin karo da robobin lemun da ya sha yayi wurgi dasu a wurin,a hankali take tafiya izuwa cikin ɗakin,haɗaɗɗen gadon nan nashi ya canza kamani,Zanin gadon yayi uban squeezing,komai ya fita hayyacinshi,Pillow har a ƙasa anyi wurgi dashi,tausayinshi ne ya kamata,tuni hawaye sun fara saukowa saman kuncinta,gefen gadonshi ta zauna tana shessheƙar kuka sai da tayi mai isarta,Sannan ta mike tare da cire mayafin dake akanta ta ɗaure ɗamara dashi,toilet ɗinshi ta fara shiga,yayi datti sosai,hada ƙura kamar ba mutun ke amfani da shi ba,batare da 6ata lokaci ba,within 30 minutes Sehrish ta gyara mashi ko'ina ya dawo fes dashi,taci baƙar wuya don ba ƙaramin aiki tasha ba,bayan ta kammala da toilet ta dawo bedroom ɗin ta gyara mashi,ta canza mashi bedsheet da blanket,komai tayi arranging ɗinshi,after ta gama da bedroom ɗin ta Koma falonshi,Nan ma ta gyara mashi shi,Ƴan share share ne,ƴan goge goge ne babu abunda ta bari,

A galabaice ta fito daga part ɗinshi lokacin da ta kammala gyaran,saukowa downstairs tayi tana tafiya kamar an zare mata lakar jikinta,kitchen ta wuce da niyyar ta ɗaura mashi girki duk da jahad ta sanar da ita cewa bai cika cin abinci ba,kuma bata da tabbacin zai dawo gidan ko bazai dawo ba,

Within 30 mins,ta kammala shirya mashi dinner ɗinshi,fitowa tayi daga kitchen ɗin ta koma bedroom ɗinsu,A hankali ta tura ƙopar ɗakin ta shiga ciki,
Murmushi ta saki yayin da idanuwanta ke kallon Oummansu dake rungume da Jahad suna bacci,Hosana ma na manne da ita,ta rungumeta ta baya,
"Allah sarki,Rayuwa kenan,ko kusa banta6a tunanin zanga wannan ranar ba,Ya Allah ka ƙara haɗa kan zuri'armu,"
Na amsa mata da Ameeen,
Wall clock ta duba kusan ƙarfe 1:30 na dare,toilet ta wuce,within few mins,ta watso ruwa,

Fitowa tayi da ɗaurin gaba,Gaban dressing mirror ta zauna saman front chair ɗinshi,har lokacin Junaid na faɗo mata aranta,jin mutuwarshi take yi kamar ba a gaske ba,

Hannu takai jikin drawer chest na mirror ɗin gida na ƙarshe ta janyo shi,kayan da Aunty Azeema ta aiko mata dasu ne,a nan ta jerasu,tare da wasu daga ciki ta tafi kano na gyaran jiki,amma bata fara amfani da turarurrukan ba,

Ɗauko turaren tayi hadi da wasu haɗaɗɗun mayukan shafawa na jiki ta ajiyesu agaban madubin
Ko'ina na jikinta tabi ta mulke shi da mayukan,bayan ta gama kuma ta feshe jikinta da turarurrukan,powder ta shafa a fuskarta,Sannan ta murza man baki mai ƙyalli asaman la66anta,Wow ta yi kyau ba kaɗan ba,kamar Aljana haka ta zauna tana kwalliya,ko tsoro bata ji ita kaɗai cikin daren nan,

Ta ƙwallafa rai akan son ganin Sgr,ta damu sosai akan rashin baccin da taji Ance baya yi,da kuma rashin cin abinci,Yafi kowa shiga damuwa akan rashin Junaid,

Miƙewa tayi tsaye tare da nufar wardrobe ɗinsu,buɗewa tayi tana laluben kayan baccin da zata sanya a jikinta,Night gown ta ɗauko red colour,tsayin rigar bazai wuce dai dai guiwarta ba,launinta kuma maroon colour ce,

Zura rigar tayi ajikinta,ta ɗauko mayafi ta yafa asaman kanta,komawa tayi gaban mirror ɗin,turarurrukan ta ƙara fesawa ajikinta,wani irin fragrance mai sanyaya zuciya jikinta ke fitarwa,

Zirga zirga ta soma yi acikin bedroom ɗin har ta fara fidda ran zasu dawo cikin gidan,Gaban window ta koma ta janyen labulen tare da zuge glass ɗin tana leƙen harabar gidan,

Gajiya tayi da tsayuwa ta koma daga gefen gadon ta zauna,gyangyaɗin bacci ta fara yi,a hankali ta ɗan kwanta a takure daga gefen gadon,in a short time bacci ya ɗauke ta,


Minti goma sha biyar da fara yin baccinta,Sai ga Motocinsu sun shararo da gudun gaske cikin gidan,motarsu marshal Omar ce farko,Sai Motar Sgr dake biye da tasu,Da alama dai wani bincike suke yi wanda yasa har sukayi dare a waje,

Parking ɗin motocin suka yi,At same time Major da Armstrong suka fito tare da buɗe masu motar,

Atare suka fito kowannansu na sanye da army trouser,tare da Long sleeve shirt green colour,sallama suka yi masu Armstrong kafin suka Nufi ƙopar shiga Main palour ɗin,hannunsu ruke cikin na juna,Upstairs suka haye bayan sunyi sallama da junansu,kowa ya wuce part ɗinshi,

Tunkan ya shiga falon ya fara jin daddaɗan kamshin na kai mashi ziyara cikin hancinshi,Tura kopar yayi slowly ta buɗe,Shiga daga cikin falon yayi abun yayi matuƙar ɗaure mashi kai,Ganin an gyara mashi falonshi an canza mashi kamanni,ko'ina yayi fess,da farko yayi tunanin ko Azmee ce ta gyara mashi ɗakin,afterwards ya fara doubting ko Yarinyarshi ce ta dawo,Cos ya hana Azmee yi mashi aiki ko part ɗinshi ma bata Zuwa,ranshi ne ya bashi cewar Uncle ɗinsu ya dawo,

Walking slowly ya nufi bedroom ɗinshi,Lokacin da ya shiga cikin ɗakin nan ma yaga angyara mashi ɗakin,Har cikin ranshi yaji daɗi sosai,ƙarasawa ciki yayi tare da rage kayan jikinshi,Ya shiga toilet domin yayi wanka,cikin minti Goma sha biyar ya fito jikinshi sanye da bathrobe,hannunshi na ruqe da short towel fari yana tsane ruwan dake acikin sumar kanshi,bayan ya kammala ya koma gefen gadonshi ya Zauna,ya jima ahaka kafin ya gyara kwanciyarshi asaman gadon batare da ya cire Bathrobe ɗin ba ya sanya night dress ɗinshi, damuwa tayi mashi yawa,a kowace daƙiƙa gabanshi faɗuwa yake yi,saboda gudun da lokacin keyi,yau har ya rage saura 1 week da ƴan kwanaki su bayyanar da Junaid agaban Abbansu,
_Ya Allah makes it easy for me_Ya furta hakan yayin da idanuwanshi ke kallon Ceiling,ya ƙura mashi ido fuskar junaid kawai yake gani tana yi mashi gizau,babu alamun bacci a idanuwanshi don kuwa tuni ya ƙaurace mashi,
"Assalamu Alaikum,"kamar daga sama yaji muryarta acikin kunnanshi,Wurga eyeballs ɗinshi yayi akanta batare da ya ɗago daga kwancen da yake ba,tun daga ƙasa har sama yake bin ta da kallo,.
Tsaye take abakin ƙopar ɗakin,hannunta ruƙe da tray wanda ta shirya mashi dinner ɗinshi,
Amsa mata sallamar yayi tare da bata izinin shiga daga cikin ɗakin,
Ƙarasawa cikin ɗakin tayi,asaman table ɗin gadonshi ta ajiye mashi tray ɗin,
Lumshe idanuwanshi yayi,ƙamshin turarenta sai kai mashi attack yake yi,
Gaisar dashi tayi"Ya rafayet,how are u and how work" batare da ya buɗe idanuwanshi ba yace"Alhamdulillah,Am well,"iya abunda ya furta mata kenan,
Jiki asanyaye ta juya zata bar ɗakin,bai tanka mata ba sai da takai bakin ƙopar fita daga ɗakin sannan taji yace"wannan food stuffs ɗin fa?wa kika ajiye mawa"?
Dakyar ta iya bashi amsa da cewa"Kai na kawo mawa,".
"Okey,bana jin yunwa,Zo ki kwashe su,".
Sam bata ji daɗin jin hakan daga gare shi ba,at least koda ace yana cikin damuwa bai kamata ya yi mata haka ba,how many days basa atare almost 2 weeks,ko irin sannu da zuwa babu,tayi mashi uziri ne kawai saboda tasan halin da yake ciki,
komawa cikin ɗakin tayi idonta cike tab da ƙwalla,tasha wahalar girka mashi abinci don ta damu da halin da yake ciki,amma ya watsa mata ƙasa a ido,
Hannu tasa zata ɗauki tray ɗin kayan abinci,a hankali ya ɗan buɗe idanuwanshi ya saci kallon fuskarta,kallon ta ya shiga yi batare da ta sani ba,especially lips ɗinta dake matuƙar jan hankalinshi,tunawa yayi da halin da yake ciki,tabbas yana buƙatar natsuwa sosai,kuma yana jin cewa a wurinta ne kawai zai iya samun wannan natsuwar da kwanciyar hankali,harma da Lafiya,"Hold On!ya dakatar da ita da hannunshi a lokacin har ta juya zata tafi,
"ajiye mun,ki tsaya ki yi serving ɗina before ki tafi," juyawa tayi asanyaye tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table,
Yunƙurawa yayi ya tashi daga zaune,ya saukko da ƙafafunshi ƙasa,
"Me zan zuba maka,"?
"Abunda kika san ya dace naci,"
A tsanake ta soma yin Serving ɗinshi,sosai ya ci abincin, yaushe rabon da ya sanya abincin kirki acikinshi har ya manta,sai da yaci ya ƙoshi,Sannan ya kalleta yace"faɗamun meya faru tsakanin ki da wannan bastard ɗin a Kano"?
Gabanta ne ya faɗi rasss,mamakinta taya akai zancen yazo kunnanshiWayyo Allah!
Girgiza kai ta ɗan yi "babu komai,babu abunda ya faru tsakanina dashi",
"Ƙarya zaki yi mun"?rai a6ace yayi maganar tare da miƙewa tsaye,aikuwa a tsorace sehrish tace"wlh baiyi mun komai ba,ba ƙarya nake yi maka,bazan iya yi maka ƙarya ba,"
Wani irin kallo taga yana yi mata,tarasa gane kallon menene,ganin yana ƙoƙarin zagayowa ta gabanta yasa ta soma ƙoƙarin ja da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login