Showing 411001 words to 414000 words out of 432432 words

Chapter 138 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

daya suka zuba mata ido suna kallonta cike da mamaki a fuskokinsu,banda Amani dama ita tasan tsakaninta da Jahan,
  Murmushi Amani ta saki tare da cewa"Nima wasa nake maki,Ae Amal ta gama zaman maiduguri in ba dai zuwa kai ziyara ba,daga Abuja sai ƙasar waje ko ba haka ba?'cike da zolaya tayi mata maganar,
Murmushi Amal tasaki,tare da juyawa da gudu tabar falon tana dariya
Tashin sense,jikinsu Abra ba ƙaramim sanyi yayi ba,duk irin burin da suke dashi na zama surukan Alexandra ya tashi abanza,Sai gashi Yarinyar da suka raina,Suke wulaƙantawa ita ke da rabon auran jinin Alexandra,Abun ba ƙaramin ta6a masu zuciya yayi ba,sunyi danasanin rayuwarsu,zuba masu ido Amani tayi tana kallonsu ganin yadda kowa tasha jinin jikinta,

*General Ishaq*

Fitowarshi kenan daga cikin toilet,Jikinshi sanye da jallabiya,tun yana acikin toilet yaji ringing ɗin wayarshi,ƙarasawa yayi tare da kai hannu ya ɗauki wayar,New number ce aka kirashi da ita,Bin kiran yayi kiran na shiga aka ɗaga wayar"Assalama Aleekum"muryar wani inyamurin mutunce,
  "Wa'alaikum salam,ko zan iya sanin dawa nake magana"?
On the other hand mutumin yace"Yalla6ai dama wani bawan Allah ne keson magana dakai,Shine yace in taimaka in kira mashi layinka,"
  "To bashi wayar,"tsayawa yayi yana jiran jin muryar mutumin da akace yana son magana dashi,
  Abun mamaki sai yaji kukan Laila Acikin wayar,ya cika kunnanshi,cikin shessheƙar kuka ta wanda ya galabaita ya jigata sosai ta soma magana"Abban hafsat ni ce laila,dan Allah akawo mun ɗauki,ina cikin mawuyacin hali,"
  Murmush Ishaq ya ɗanyi tare da cewa"Bangane wake magana ba?kodai wrong number ne aka kira"?
  Jin haka yasa ta ƙara sautin kukan nata"Ishaq kada kayi mun haka,Wlh ina cikin masifa,gani nan a Enugu yashe gefen bishiya,sai an bani sadaqa sannan nake samun abunda nake sawa acikina,Wlh Ishaq na tuba nabi Allah,Akawo mun agaji ƙafata ta lalace ta ru6e...."tana magana tana kuka,
  Handsfree ya sanya don yaji daɗin sauraronta,Sai da takai ƙarshen maganarta sannan yace"the number you're trying to call is switch off,pls try again Later"yana kai ƙarshen maganar,yayi rejecting kiran yana dariya,ko kaɗan baiji tausayin kukanta ba,Don tafita aranshi kwata kwata,Yayi mamakin jin wai tana a Enugu ko ubanme yakaita enugu?ta6e le6enshi yayi tare da faɗin"I don't care Allah ya raka taki gona,nasamu na rabu da jangwamgwam,"
  Ƙarar shigowar message yaji,da sauri ya duba screen din wayar ya soma karanta saƙon
  _Ishaq ka taimaka ka ceci rayuwata,wlh ina cikin masifa,naga tashin hankalin da banta6a gani ba Ishaq,wayar ma aronta nayi a hannun wani inyamuri,kayi taimakon musulunci ishaq karka duba halina,dan Allah zakayi,ataimaka a dauko ni daga Enugu ko maiduguri ne a mayar dani in mutu acan_
  Guntun tsoki ishaq yaja,tare da yin deleting ɗin saƙon,a karshe ma blacklist ya tura number,yadda ko an kira baza a same shi,"
  Murmushi ya saki lokacin daya tuna da hajjaju,macen da yake burin aure,duk da taƙi amince mashi amma kullum saita kirashi ta tambayi lafiyarshi,Wannan ya tabbatar mashi da cewar tana sonshi,tunda ta damu dashi,sannu a hankali Zai samu yayi Wuff da ita ya kawota Cikin gidan shi,

*Boss Bature*

Yinin Ranar Sehrish da Ciwon kai Tayi shi saboda tsabar tunane tunanen da take yi,ta kasa tsaye ta kasa zaune,Har magani tasha amma kan yaƙi lafawa kamar ana kunna wuta acikin ƙoƙan kan nata,abun ya ɗaure mata kai yadda Azmee ta share zancen bata Labarinta,Har lokaci suka samu amma bata tada zancen ba,kuma ko tayi yunƙurin zata tuna mata sai tayi saurin Canza zancen,hakan ne yasa Sehrish ta fara accusing ɗinta,Ta sanya mata ido sosai duk wani motsinta akan idanuwan sehrish take yinsu,

Wuraren ƙarfe 9;30 na dare,gidan yayi tsit da alama wasu daga cikinsu sunyi bacci,Oummansu kaɗai ta rage a ɗakinsu,Zaune saman sallaya tana tasbihi,Yayin da su sehrish ke kwance saman gadon,hosana da jahad sunyi Bacci banda Sehrish wadda idonta biyu,ta kasa runtsawa,jira take yi Oummansu ta kammala Sallar ta dawo saman gadon ita kuma ta koma ɗakin Azmee,

Tana cikin Jan cazbahar nan wani abu ya faɗo mata aranta,abunda ta jima tana ƙoƙarin tunanawa,a hanzarce ta miƙe jiki na rawa ta tunkari gefen da sehrish take kwance saman gadon,Hannu tasa tana ɗan bubbuga kafaɗarta"Rishi!rishi!ko kinyi bacci ne,"yatsina fuskarta ta ɗan yi daƙyar ta iya huɗe idanuwanta,
  "Tambayar da kika yi mun game da wannan Auntyn taku Azmee,Na tuna inda nasanta.."tunkan takai ƙarshen Maganar,jiki na rawa Sehrish ta tashi daga zaune tana kallonta"Oumma a ina kika Santa?
  "Zan faɗa maki Sehrish amma fa karki kuskura ki sanar da ita cewa nasanta,tunda bansan da wata manufa take zaune acikin gidan nan ba,"
  "Bazam faɗamata ba Oumma"
Jinjina kai abu ta ɗanyi"Wannan matar da kike gani,Lokacin da na haifeku babu wanda yazo yi mun wankan jego,Sai daga baya Ya sayyadi yazo da ita amatsayin ƴar uwarshi da zata yi mun wankan jego...."
  Jin wannan maganar yasa hankalin Sehrish yayi mugun tashi,Saboda tsabar kiɗima gaba ɗaya idanuwanta suka firfito waje,Hannu tasa ta daki ƙirjinta"Ƴar uwar Ya sayyadi!"ta ambaci hakan a tsorace
  Abu ta lura da Yanayin da Sehrish ta shiga,bata dakata da yin maganar ba taci gaba da cewa"Wlh Sehrish matarcan da kike gani,Ba ƙaramar shu'uma bace!abun tsoroce ita,Dalilin dayasa nace maki haka,Lokacin da sayyadi yazo mun da ita don tayi mun wankan jego,Kamar kurma haka ta koma,duk in naso na bugi cikinta don ta sanar dani wani abu game da danginsu,Sae taƙi tanka mun,Nasan dai ta bani kyakkyawar kulawa a lokacin amma gaskiya ba abun yarda bace,saboda nayi mamaki dana ganta acikin gidan nan,Kuma sai surutu take yi kamar ba ita ba,Sa6anin a yadda nasanta lokacin da tazo gidanmu ko uffan bata cewa,daga um sai um um shine abunda ke fitowa daga bakinta,"
Hannu sehrish tasa tare da dafe kanta dake jujjuya mata,a hankali tashiga furta"Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un!Amma Azmee ta gama damu!indai abunda nake zargi ya tabbata to tabbas Azmee Itace Ƴar leƙen asirinsu dake fitar da surrukan gidan nan......"
Cike da mamaki abu ke sauraron kalamanta sae da takai ƙarshen maganarta Sannan tace"Meyasa kika ce haka?Dama kina zarginta ne?Amma naga kamar kuna zaman lafiya da ita,'
Hawaye na kwaranyowa akan furkarta ta shiga faɗin"Oumma,muna cikin tashin hankali in har ya kasance AZMEE itace take shirya maƙarƙashiya acikin gidan nan...."dafa kafadarta abu tayi"ki sanar dani abunda yasa kike zarginta inaso inji,ko Zan iya taimaka maku"
  Duk da tana cikin mawuyacin hali na firgici,haka ta zauna ta kwashe dukkan abunda ke wakana acikin gidan ta sanarwa Oummansu,abun mamaki tana kai ƙarshen maganar sai taga Abu na murmushi gami da girgiza kanta,
  "Oumma ko kin gano wani abu akanta ne?naga kina murmushi,"
  "Akwai wani abu da nakeso na sanar dake sehrish!Shi ɗan adam ba abun yadda bane,Bakomai zaisa kiyi kokwanto akan azmee ba fa ce Yardar da kukayi da ita,Ta ko'ina azmee ta gama daku,Ta siye zuciyoyinku ta hanyar kyautatawar da take yi maku,Shi mutun maison ɗaukar fansa,Zai iya yin 6adda kama ya shiga jikin maƙiyansa har na tsawon shekaru Yana yi masu bauta batare da gajiyawa ba,yayin da yake shirya masu maƙarkashiya batare da sun ankare ba,Har sai ranar da ya tarwatsa su gaba daya tukunna zai bayyana kanshi,Yanzu kinga gaba ɗaya ta gama sanin surrukanku......"dakatawa abu tayi da yin maganar,Ta jinjinawa azmee sosai,ta iya shirya tuggu
  "Gaskiya sehrish dole kiyi taka tsantsan,don wlh in har ya kasance zargin da muke yi ya zama gaskiya,To fa Azmee ba ƙaramar shu'uma bace,Kuma zata iya kashe duk wanda yayi gigin tona mata asiri,a yadda ta faro shirinta tsawon lokaci yanzu bazata bari wani Ya fallasa ta ba,"
  "Amma Oumma,nibansan ya zanyi ba,abubuwa sunyi mun yawa akaina,"tayi maganar damuwa ƙarara a kan fuskarta,
  Dafa kafaɗarta abu tayi"Ni dai shawarar da zan baki shi ne,Ki samu wani babba ki sanar dashi komai dangane da ita....."
  A ruɗe sehrish tace"Wazai yarda dani Oumma!idan har na faɗi cewa Azmee ƴar uwar sayyadi ce,kuma ina zarginta da mutuwar Junaid"
  "Tabbas kuwa babu wanda zai yarda dake a halin yanzu,a ƙarshe ma reshe zai iya juyewa da mujiya,Zata iya ɗaura maki laifin kinsan fa shi mugun mutun hatsari ne shi,balle su da suke da tsafi,duk da dai mu mun dogara da Allah ne,babu ja da baya Allah shi zai bamu kariya,"
  "Yanzu ya zanyi!inaso naci gaba da bincike akanta,Saboda inaso na tambayeta dangane da zoben Junaid dake a wurinta me yakai shi cikin kayanta,"
  "Nace maki karki kuskura ki ce zaki nuna cewa kinsan wani abu game da ita,in ba haka ba zatayi maki mummunar illane,Nidai shawarar da zan baki A yanzu ki damƙa binciken nan a hannun ɗaya daga cikin mutanen gidan nan,Zaifi ma ki sanar da Daddynku,Zan ma yi mashi magana,nasan zai yarda dani sosai'
Shikenan Oumma,Yanzu zan iya zuwa ɗakinta in kwanta"?
  "Me zai hana amma dai ina ƙara jan kunnanki akanta,karki kuskura ki tsananta bincike akanta,Don zata ganoki ne,"gyaɗa kai Sehrish tayi tare da saukowa daga saman gadon ta nufi hanyar fita daga ɗakin,ruƙo handle ɗin ƙopar tayi,bayan ta fita taja ƙopar ta rufe,gyara kwanciya Oummansu tayi saman gadon,ita kanta abun ya razanar da ita,Ta yadda akai har ƴar uwar sayyadi ke aiki acikin gidan,daƙyar bacci yayi awon gaba da ita,

Tafiya sehrish takeyi kamar wadda aka zarewa lakar jikinta,komai ya tsaya mata Cak,don abun ya girmi tunaninta,a ƙopar ɗakin Azmee ta tsaya gabanta na faɗuwa a hankali ta furta"La'ila ha illa anta subhaka inni kuntu minazzalimin,tana kai ƙarshen addu'ar ta tura ƙopar ta shiga daga ciki,abun mamaki bata samu kowa ba acikin ɗakin,Ranta ne ya bata cewar kodai ta shiga toilet ne,
A wauta irin na Sehrish,maimakon tabi abunda Oummansu ta sanar da ita,Sai ta soma tunanin Yin bincike acikin ɗakin don a qagare take da ta gano gaskiyar wacece AZMEE,

Agaban bedside drawer ɗinta ta zuƙunna jikinta na kerma,ta shiga bubbuɗe drawer chest ɗin,Yawanci duk tarkace ne na magunguna sai ƴan ƙulle ƙulle kamar na maganin Zafi,gida na ƙarshe ta bincika anan ne taga abun daya ɗaure mata kai,Ƙura ido tayi tana kallon Galleliyar wayar dake ajiye a wurin,Ƙirar i phone 13pro

Batasan lokacin da ta furta"Ya Allah!dama Aunty Azmee tana da waya?Amma meyasa ban ta6a ganin wayarta a hannunta ba,"ta ƙarasa maganar tare da zura hannunta ta ɗauki wayar,ta kunna power ɗinta,Nan take haske ya kawo,Gabanta ne ya faɗi Ganin Hoton dake ajikin Wallpaper ɗinta,bakowa bane face Fuskar HAROON,da ƴar ƙuruciyarshi,nan fa tashiga ruɗanin abun al'ajabin da take gani,Menene Alaƙarta da haroon da har ta ɗaura hotonshi a fuskar wayarta?dama ta jima tana zargin haroon ba mutumin kirki bane,kodai hadashi atare suke shirya maƙarƙashiyarsune?

Tana cikin wannan wasi wasin,kira ya shigo cikin wayar da baƙuwar lamba,kwata kwata babu sautin ringing an sanya wayar silent,Yadda ko an kira baza'aji ƙararta ba,

Sehrish da karanbani sai ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta,
Shiru tayi tana jiran jin wanene zaiyi Magana,
Cikin harshen fulatanci taji ana magana,gashi ita bata iya yaren ba,Tunani ta shiga yi dama azmee bafullatana ce?dama ta ta6a ganin Zanen kalangu a gefen fuskarta,

  Tana cikin wannan zancen zucin tajiyo takun tafiyar mutun yana tunkaro ɗakin,Ba shakka Azmee ce,A tsananin tsorace Sehrish ta katse kiran,gashi wayar akwai password,babu yarda za'ae ta goge kiran da akayin,dole idan aka shiga Call log agane cewa An ɗaga kiran da akayi,
A matukar firgice Sehrish ta tura wayar acikin drawer ɗin,Duk tabi ta ruɗe ta rasa inda zata dosa,A ƙarshe ta faɗa toilet ta rufe,tana faman sauke ajiyar zuciya,jijiyoyin wuyanta duk sun fito saboda tsabar tsoro,Tayi danasanin ɗaga kiran wayar Azmee da tayi,

A hankali Azmee ta turo ƙopar ɗakin ta shigo,Jikinta sanye da baƙaƙen kaya,Jallabiya ce tare da mayafinta,kamar wadda taje anguwa,zama tayi daga gefen gadon,tare da kai Hannu jikin drawer ɗin ta ɗauko wayarta,dannata ta shiga yi,kafin ta danna call,

Sehrish dake la6e acikin toilet ɗin da alama mutumin da ya kira Sehrish ta ɗaga shi Azmee ta kira,Addu'a sehrish tashiga yi hannunta na kerma ido ya raina fata,tuni zufa ta wanke mata fuskarta,Ga fitsari daya matse,ta kasa tsugunnawa tayi futsarin gudun kada azmee taji ƙarar fitarshi,
  Ba ƙaramin haushi Sehrish taji ba lokacin da Azmee ta soma Magana Cikin harshen fulatanci,taso ace da yaren hausa tayi maganar don ta samu taji abunda zata ce,yanzu ta ƙara ƙarfafa zarginta akan Azmee,

*Boss Bature*

Around 10pm

Jami'an da Sgr ya sanya su tsare grave ɗin Junaid,sunyi 6adda kama yadda kasan ba Sojoji ba,kowannansu na sanye da Kaya namu na hausawa,riga da wando na yadi,ɗaya daga cikinsu yana zaune saman dogon benci yayin da ɗayan ke zuƙunne agaban bencin gefenshi kayan Shoe shiner ne,Yana goge ma na saman bencin Takalminshi,dayake akwai hasken street light,Bakomai suke jira ba fa ce wannan mai zuwa yana yin zarya a ƙabarin nasa,bisa Command ɗin da Sgr ya basu nasu sanya ido akanshi idan ya ƙaraso,Su sanar dashi yana so yaga ko wanene,Suna zaman jiran zuwanshi,Aikuwa cikin sa'a ƙarfe goma na bugawa,kamar yadda ya saba zuwa,Sai motar nan ƙirar Venza ta shararo da gudu izuwa titin,tunkan ya ƙaraso ɗaya daga cikin sojojin wanda ke zaune saman Bencin yace"Gashi nan!yakamata mu sanar da Sgr,tun kafin ya kufce mana"
  Wanda ke goge mashi takalmin yace"sai munyi taka tsantsan if not zai gudu ne,"

Koda ya ƙaraso wurin ƙabarin slowly yayi parking ɗin Motar a gefen titin batare daya fito ba,

A hankali Sergeant ɗinnan dake zaune saman bencin ya ɗauko wayarshi tamkar yana dannata,message ya turawa Sgr,bayan ya kammala tura saƙon Ya mayar da wayar cikin trouser ɗinshi,

Buɗe murfin motar yayi tare da saukowa daga cikinta,kamar yadda ya saba zuwa haka yau ma yazo,Ya sanya face mask a fuskarshi yayin da idanuwanshi ke sanye da glass baƙi,Jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da T-Shirt purple,tafiya ya soma yi har izuwa gefen bishiyar nan inda aka kewaye ƙabarin Junaid,tsayawa yayi kamar mai neman wani abu,hada ruƙe qugu,kusan minti 5 kafin ya soma zagaye bishiyar yana jinjina kanshi,

Miƙewa ɗaya daga cikin Sojojin nan yayi,A hankali ya nufe shi batare daya ankara ba,koda matashin nan Ya lura da cewa wani na tunkaroshi,Aikuwa da gudun gaske yabar wurin bishiyar,Sojojin nan suka bishi a guje,duk yabi ya rude ko motarshi bai tsaya ɗauka ba,a rikice ya faɗa saman titin yana gudun ceton rai kamar zai tashi sama,da gudu suma suka bi bayanshi don karya kufce masu,yana gudu yana waiwayen bayanshi,Unfortunately Yana ƙoƙarin karya kwana,Adai dai Lokacin Motarsu Sgr ta shawo kwanar,Kwatsam ya faɗama motarsu ta bugeshi sosai,ya saki wata irin razananniyar ƙara tare da zamewa ya faɗi wanwar ƙasa,Ƙarasowa Sojojin suka yi suna faman sauke ajiyar zuciya,Ta kwana gidan sauƙi,

Fitowa Sgr yayi daga cikin motar,Armstrong ma ya fito,Atare sojojin suka sara mashi,Kafin ɗaya daga cikinsu ya nuna saurayin dake a kwance ƙasa yana bullayi"Sir,Wannan shi ne wannan matashin dake zarya a ƙabarin ƙaninka,rashin gaskiya yasa yana ganinmu ya zabura zai gudu",

Zuba mashi ido Sgr yayi yana bin shi da kallon ƙurulla,tun kafin ma Ya cire mashi face mask ɗin fuskarshi,Ya shaida shi,zuƙunnawa yayi saman guiwarshi ɗaya,tare da kai hannu Ya zame face mask ɗin saurayin tare da cire glass ɗin fuskarshi Yayi throwing dinshi saman titin,runtse idanuwanshi yayi jikinshi sae kerma yake yi,

A hankali Ya furta sunanshi"HAROON" kamar bashi ba,Ya rame,yayi baƙi,jin muryar Sgr yasa haroon ware manyan idanuwanshi masu kama dana mujiya,koda yayi tozali Da Sgr a hargitse Ya tashi daga zaune yana kallonshi yayin da yake faman zazzare ido,wata irin zufa ce ta soma tsastsafo mashi agefen fuskarshi,. 
  "Dama kaine"?cike da mamaki Sgr yayi tambayar,
  Shiru Haroon yayi bai tanka mashi ba,
  "Me kake yi a wurin grave ɗin Junaid"
  Daƙyar ya iya furta"ƙabarin junaid kuma?yayi maganar tamkar baisan akan me suke magana ba,
  ɗagowa Sgr yayi tare da kallon sojojin dake tsaye suna ta faman haki"Zaku iya komawa bakin aikinku,"juyawa su kayi da sauri suka bar wurin,
  "U will explain it don ubanka,I have been suspecting you for a while,Zuba maka ido nayi kawai inga ƙarshen gudun ruwanka,abunda ka aikata ne yasa ka gaza samun natsuwa acikin ranka That's why kazo kana zarya akan ƙabarinsa"?

Waro ido haroon yayi amatuƙar tsorace Yayi yunƙurin miƙewa ya gudu,damƙar ƙafarshi Sgr yayi hakan yasa ya gaza motsawa,
  "Amstrong,ɗaukarmun shi ka sanyamun shi acikin mota,"

Gadan gadan Amstrong ya tunkareshi,Yadda kasan ƙaramin Yaro haka ya ca6eshi asaman kafaɗarshi,Ya turashi cikin motar Sgr,Front seat suka shiga,Sgr da Amstrong Tada Motar yayi da gudun gaske ya fisgeta,
"Wai ina zaku kaini ne?Motata fa?kun barta a wurin"shiru su kayi mashi babu wanda ya tanka mashi,
  "Wlh kada kuce zaku ta6ani,Rafayet ku sauke ni in kama gabana!Ni bansan akan me kuke magana ba"Sai faman sambatu yake yi,zufa duk ta wanke jikinshi"
  Har Lokacin basu tanka mashi ba,ƙoƙarin buɗe motar yayi donya buɗe,amma yaji ƙopar adatse ta ko'ina babu hanyar da zai gudu,

Da gudun gaske motarsu ta shigo cikin gidan A lokacin Sehrish na la6e cikin toilet ɗin Azmee,Har cikin kunnanta tajiyo sautin Shigowar Motar Sgr,kamar ta fasa ihu haka take ji ga Azmee taƙi yin bacci bare ta lalla6a ta gudu,Sae dannar wayarta take yi,Yadda kasan tasan da zaman wani acikin ɗakin,

Window ta hango acikin toilet ɗin,Da gudu ta nufe ta,so take ta leƙa window ɗin don taga idan shi ne ya dawo dagaske,net ne ajikin tagar,kuma tagar tayi nesa,Tsawon sehrish bazai kai ta leƙa tagar ba,Lalla6awa tayi cikin sanɗa ta ɗauko bokiti,Ta kifa shi ajikin bangon,Sannan ta daddage ta haye saman bokitin cike da tsoran karya fashe bokitin,

Ƙura idanuwanta tayi tana leƙan wajen gidan daƙyar take hangen wurin da motar Sgr take,fitowa yayi daga cikin motar tare da zagayawa ya Shaƙo wuyan rigar haroon ya wurgo shi waje,gaba ɗaya ya kife ƙasa a susuce,Gabanta ne ya faɗi rass!lokacin da taga Ya damƙo rigar haroon,Tabbas ranta na bata cewar Sun kamoshi ne a matsayin me laifi!tsoranta kada Sgr yayi kuskuren raunata shi,wata'ƙil Sunji kalamanshi ne dayake cewa zai kashe Farin cikin mutanen gidan Shiyasa suke tuhumarshi,kamar ta bur6a tagar ta fito haka take ji,

Ɗaukarshi Sgr yayi asaman kafadarshi Ya wuce dashi cikin gidan Amstrong na biye da bayanshi,ɗakin horon nan nasu Ya shiga tare dashi,ɗakinda idan aka rufe ƙoparshi ko ihun mutun ba'aji,

Sauke shi yayi yana tangal tangal Zai faɗi ƙasa,Nuna mashi ɗaya daga cikin kujeru biyu dake kallon juna yace"Ave a seat,magana nakeso nayi dakai,"
  "Nifa bansan komai ba!meyasa ka shigo dani wurin nan"?
Wani irin kallo da Sgr ya wurga mashi yasa shi lalla6awa ya zauna,jikinshi nata kerma,kai cike da iskanci ga shegen tsoro

Zama Sgr yayi suna fuskantar juna yayin da Amstrong ke atsaye yana kallonsu,

  Sai faman mazurai haroon keyi,irin na marasa gaskiyar nan,
  "Meyasa ka aikata hakan"?girgixa kai ya shiga"Ni wlh ban aikata komai ba,Nifa bansan komai ba,bansan akan me kake magana ba"
  Tsabar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login