Showing 186001 words to 189000 words out of 432432 words

Chapter 63 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

"Okey,"ya ambaci hakan tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,
  Komawa azmee tayi tare da zama daga gefen sehrish tana kallonta gwanin ban tausayi,Ba ƙaramar wahala tasha ba,ta jigata sosai,ta wani 6angaren kuma taji daɗi da Sgr ne zai dubata,don tasan cewa zata samu kyakkyawar kulawa awurinshi,zaiyi mata abunda ya dace ne,"
  15mins da fitar shi,sae gashi ya dawo cikin ɗakin hannunshi ɗauke da Allura har ya ɗura ruwan allurar acikin sirinjin,
   Ganin shi yasa azmee mikewa daga zaunen da take gefen gadon ta bashi wuri don ya samu damar yi mata allurar,
  Zama yayi daga gefen gadon tare da ruƙo hannun sehrish da ta fito dashi daga cikin bargon da azmee ta rufa mata ajikinta sae faman hargowa take tana ambaton cikinta,
   Yana ƙokarin tsira mata allurar,ta ware idanunta sosai kai tsaye suka sauka akan Syringe ɗin dake hannunshi,duk da bata acikin hayyacinta amma ta gane cewa Allura ce fa za'ayi mata,
  a firgice sehrish ta fusge hannunta tare da yin wurgi da bargon da azmee ta yafa mata,gefe guda ta jefar dashi,matse kanta tayi ajikin headboard na gadon tana faman shesshekar kuka tana cewa"banaso!dan Allah ku kyaleni kada kuyi mun allura,"gaba daya duk tabi ta firgice dama ta tsani allura arayuwarta mugun tsoranta take ji,
    sanin cewa Sgr yana da bad temper bazai iya jure koke-koken da sehrish keyi mashi ba,muddin taƙi tsayawa zai iya kwashe ta da mari,don ta dawo dai dai,
  Cikin sauri azmee tace"Zan iya ruƙe maka ita?
  "E" ya bata amsa ataƙaice,
Wucewa saman gadon azmee tayi tare da rurruke sehrish,aikuwa a gigice sehrish ta shiga kokawar kwace kwanta hada gartsa mata cizo a hannunta,
    Cire hannunta tayi daga ruƙon da tayi ma sehrish,saboda taji zafin cizon da tayi mata,
  Ganin haka yasa sgr bata Umarnin ta fita daga ɗakin,
   Saukowa azmee tayi daga saman gadon,tare da kama hanya ta fuce daga cikin dakin,
  A waje ta samu junaid atsaye sae faman zagaye yake yi a wurin ɗakunan nasu,bawan Allah duk ya rasa natsuwarshi tunda yaji cewar Sehrish bata da lafiya,
  "Junaid," jin an ambaci sunanshi yasa shi yin firgit ya juya yana kallon azmee dake tsaye a kopar dakin,
  Ƙarasawa yayi wurinta fuskarshi ɗauke da damuwa yace"Aunty azmee wai meya faru da sehrish ne?ina taje ne?duk nabi na ruɗe wlh,bansan ta yadda akai ta sanya ƙafa tabar gidan nan ba,nifa dakaina na ɗaukota daga school na kawota gida,"
  ruƙo hannunshi azmee tayi taja shi daga dan gefe suna fuskantar juna tace"Junaid ka kwantar da hankalinka,ba abunda ya faru da sehrish,stomach pain ne kawai kuma insha Allah zata ji sauƙi ne,sannan maganar fitar sehrish daga cikin gidan nan,kada kayi confusing kanka,ka manta da wannan kawai,komai ya wuce,"
  ajiyar zuciya ya shiga saukewa,har cikin ranshi yaji daɗin bayanin da azmee tayi mashi,
  "Yanzu kaje ka kwanta mana,zuwa da safe in yaso sae kazo ka dubata ko"?
  cike da shagwa6a yace"Aunty azmee kona koma ɗaki bazan iya bacci ba,in har ban sanyata acikin idanuna ba,'
  Murmushi azmee tayi tace"ummm romeo kenan shugaban ƴan soyayya,dama tunda na ganka nan tsaye nasan cewa abunne ya motsa,"
  Sunnar da kai ƙasa junaid yayi yana faman sakin murmushi,
    A nan suka tsaya suna cigaba da yin fira atsakaninsu,janye mashi hankali azmee ta dinga yi saboda ta lura da yadda yake firgita duk in yaji sautin kukan sehrish,daƙyar tasamu junaid ya wuce bedroom dinshi itama ta wuce nata ɗakin,
  suna barin wurin hayaam ta fito daga ɗakinta,cikin sanɗa take tafiya harta ƙaraso wurin kopar ɗakin sehrish,anan ta tsaya tare da jingina kanta ajikin ƙopar ta kasa kunnanta tana sauraran kukan da sehrish keyi,duk atunaninta ita kaɗaice acikin ɗakin take kuka,hakan yasa taji daɗi acikin ranta har tana cewa"Shegiyar Allah yasa ta mutu kowa ya huta,wlh bazan shiga in taimaketa ba,koda ciwon zai kashe ta,

acan cikin ɗakin kuwa duk yadda sgr yaso sehrish ta tsaya yayi mata allurar abun ya faskara,taƙi bashi haɗin kai,sae faman yawo take mashi da hankali,wannan ne yasa shi fusata har ya daka mata tsawa,wannan tsawar da sgr ya daka ma sehrish yasa ta dawo cikin hayyacinta sosai,waro ido waje tayi hankalinta a matuƙar tashe take kallon sgr,abun kamar a mafarki take kallonshi,wai dama shine!taya akai ya shigo ɗakinta?
a tsananin tsorace take binshi da kallo,jallabiya ce fara ajikinshi mai gajeran hannu,hakan ya bayyana damtsen hannun nan nashi,
   zazzare ido tashiga yi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,
  Matsawa sgr yayi kusa da ita,suna facing din juna face to face,a hankali yake bin fuskarta da kallo yayin da itama take ƙare ma tashi kallo,har lokacin kokwanto takeyi anya shine da kanshi ya shigo ɗakinta,Sgr sukutum da guda yau a bedroom ɗinta zaune gefen gadonta,a kusa da ita?
  Hmmmmm ina labarin Hayaam dake la6e ajikin ƙopar ɗakin tana sauraron kukan Sehrish,ae tun lokacin da taji muryar sgr ya daka ma sehrish tsawa,jinjina kai ta shiga yi tana faman sakin huci kamar wata zakanya saboda tsabar 6acin rai da takaici,acikin ranta tashiga cewa"lallaima yarinyar nan,wato harta samu matsayin da sgr zai dinga takawa da ƙafafunshi yana shiga ɗakinta,'
  ɗagowa tayi tare da aza hannunta asaman kanta tana cewa"nashiga uku ni yau hayaam bansan ya zanyi da yarinyar can ba,tana shigar min gonata!tabbas dole nayi wani abu akanta,bazan ƙyaleta ba tayi nasara akaina ba,
  Tana cikin wannan zancen zucin nata ta jiyo muryar sgr yana magana daga cikin ɗakin,cikin sauri ta kasa kunne tana sauraron me yake ce ma sehrish ɗin,
   "Bana son wannan koke koken da kikeyi mun,kamar zan rabaki da ranki ne,"!. 
  tsit Sehrish tayi tana sauraranshi,yayin da take bin pink lips ɗinshi da kallo,
  Cigaba da magana yayi anatse yace"idan kika natsu,ba da zafi zan maki ba,a hankali zanyi maki,batare da kowa ya ji mu ba,"
   tashin hankali tunda hayaam taji wannan zancen da Sgr yakeyi ma sehrish nan take taji gabanta ya faɗi rass,zullumi ta shiga yi gabanta na faduwa,duk atunaninta wani mummunan abunne sgr da sehrish ke aikatawa,gaba daya ta rasa natsuwarta,kamar ta fada cikin ɗakin  taga me suke aikatawa haka take ji aranta,zuciyarta sae faman azalzalarta takeyi tana tunzurata akan ta shiga taga me sukeyi,
  Yanayin yarda sgr keyi mata magana cikin sanyin murya,yasa taji wani irin yanayi atare da ita,da kanta ta miƙa mashi hannunta don yayi mata allurar,
  Hannunshi yasa tare da ruƙo wrist din hannunta,sannu a hankali ya zura allurar a cikin jijiyar hannun nata,lokacin da tsinin allurar ya ratsa cikin jijiyar,a ɗan razane sehrish ta saki ƴar ƙara tare da runtse idanunta tana faman cizon la66anta,
  a hankali sgr ya ɗago da blue eyes ɗinshi yana kallon fuskar sehrish,zuba mata ido yayi yana kallon eye lashes ɗin idanunta masu tsayin gaske,kafin ya mayar da idanun nashi akan la66anta dake ta faman kerma,tana ɗan cizon gefensu da Teeth ɗinta,
  gaba daya ya gaza control ɗin kanshi,har ya gaza janye idanunshi daga kallon la66anta da yake yi,ba ƙaramin yanayi ta jefa shi ba,cos she looks so sexy a wannan lokacin komai tayi bashi sha'awa yake yi,
  siraran hawaye ne suka shiga gangarowa daga cikin idanunta,batare da saninshi ba yakai hannu zai share mata hawayen,buɗe idanuwan da tayi ne yasa shi dakatawa tare da janye hannunshi,
ya kawar da kanshi gefe guda a lokacin ya kammala yi mata allurar,
   tayi danasanin buɗe idanuwanta da tayi,taso ace ya sanya hannayen shi ya share mata hawayen,ko ba komai zata ajiye wannan ranar a matsayin ɗaya daga cikin ranakun da suka kafa tarihi a rayuwarta,
   Ganin ya miƙe tsaye tare da kama hanyar fita daga cikin bedroom ɗin nata yasa tayi saurin cewa"ngd da taimakon da kayi mun,"
  Batare da ya juyo ya kalleta ba yace"get well soon"
Yana ƙarasa maganar tashi yasa hannu ya ruƙe handle ɗin ƙopar zai buɗe door ɗin ɗakin,jin motsin shi yasa jiki na rawa hayaam ta watsa da gudu izuwa cikin bedroom ɗinta,
Upstairs ya nufa ya wuce part ɗinshi a wani irin yanayi ya faɗa saman katafaren gadonshi,yayin da idanunshi ke kallon saman ceiling ɗin ɗakin nashi,

   Wani abu ne ya faɗo mashi aranshi,lokacin suna da shekaru goma sha wani abu a duniya,a katafaren gidansu dake a los angeles California,su shida suke rayuwa acikin gidan bayan masu aikin dake kula dasu,Uncle donald tare da matar shi wadda suke kira da Mommy,sae Ƴa'ƴansu mata guda biyu Eva da jessy,Sae shi tare da Omar,wata irin rayuwar farin ciki sukeyi acikin gidan,saboda tarairayar da suke samu a wurin matar uncle ɗinsu kamar ita ta haifesu,Allah ya jarabceta da son su,ko ƴa'ƴan data haifa batayi masu irin son da takeyi ma Sgr da Omar,A wannan lokacin Uncle Abusufyan ya ta6a yi masu zuwan bazata,sunyi murna kamar kamar me,suka manne mashi suna tambayarshi ina tsarabar da yazo masu da ita,
  Hannu yasa tare da ciro wasu hotuna biyu daga cikin aljihunshi,ya aza hotunan asaman table ɗin gabanshi,ya kifa hotunan yarda bazasu iya tantance hotunan menene ba,
   yana daga zaune saman 3 seater,su kuma suna atsaye ruƙe da qugu suna jiran ganin wannan tsarabar da yazo masu da ita,maimakon suga chocolate suga iyayen shan zaƙi sae suka ga Hotuna guda biyu,nan take suka ɗaure fuskokinsu,atare suka haɗa baki wurin tambayar shi menene wannan yake 6oye masu acikin hotunan
  Abusufyan yace"so nake kowanne daga cikinku ya za6i ɗaya daga cikin hotunan,kuma duk abunda mutun ya za6a dole ya rungume shi hannu bibbiyu,kun amince da hakan"?
  "Yeah,"suka amsa mashi,,
"Waye zai fara canka acikin ku"?
Shiru rafayet yayi tare da maƙe kafaɗarshi alamar bazai fara ɗauka ba,Kallon Omar Abusufyan yayi yana jiran jin shi mai zaice ko zai fara ɗauka ne,
  da yake shi mai sauƙin kaine,baiyi gardama ba,ya sanya hannu tare da ɗaukar ɗaya daga cikin hotunan,juyo da hoton yayi ta gaba yana kallon shi,
  Kyakkyawar yarinyace,ƴar ƙarama bazata wuce 5 years ba,tana tsaye akayi mata hoton,'
  Murmushi Omar ya shiga saki yana kallon hoton,
  "Saura kai Mr arrogant,pick d other one,"yayi maganar cike da zolaya yana kallon Sgr,
  tsuke baki yayi tare da miƙa hannunshi ya ɗauki ɗayan hoton daya rage asaman table ɗin,ɗago dashi yayi tare da juyo da gaban hoton yana kallonshi,
Koda yayi arba da hoton yarinyar daya dauka nan take ya ɗaure fuskarshi ya haɗe girar idanunshi alamar ranshi ya 6aci,
    Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace uncle I don't like her, she's ugly, she doesn't have even shoes on her feet,ko gashin kanta ma bata iya gyarawa,ƙazama ce"
  Fashewa da dariya Omar yayi hada dafe cikin shi,hakan ya ƙara fusata sgr,
  Abusufyan kuwa,ruƙo hannunshi yayi cikin sanyin murya yace"Look rafayet,itama ba laifinta bane kuma bada son ranta ta kasance haka ba,kai kana da gata ne shiyasa kake ganin cewa ita da son ranta ta kasance hakan,Bata da wanda zai gyara mata gashin kan nata ne,babu wanda zai janyota ajikinshi yayi mata wanka ne,kuma kaga ƙarama ce bata da hankalin da zata iya gyara jikinta da kanta,dole sai an nuna mata ga yadda zatayi sannan tayi.....'
  Shiru Sgr yayi yana faman hura hanci shi an haɗa shi da mahaukaciya,ɗago da hoton yayi yana ƙare mashi kallo kafin ya kuma kallon uncle ɗin nasu yace"Ita bata da Mommy ne?ina daddyn ta yake ne?ko basu raye ne"?ya jera mashi tambayoyin yana jiran amsar su,
  Abusufyan yace"bata dasu, marainiya ce,amma yanzu ta samu,in har ka amince zaka aureta,kaga shi kenan zaka ruƙe ta amana,kuma zaka dinga gyara mata gashin kanta,kana sanya mata takalma,har ma wanka sai kayi mata....'tun kafin abusufyan ya ƙarasa maganar Sgr ya bubbuga ƙafafunshi rae a6ace yake cewa"Uncle I can't marry her,but since I hv a lot of money i will give her to buy whatever she wants"
Murmushi Abusufyan yayi yana kallon shi,wato shi bazai aureta ba,amman tunda yana da kudi da yawa zai bata kuɗi ta sayi duk wani abu da take so,yaji daɗin jin maganarshi,koba komai yaron yana da tausayi ta wani 6angaren,dama ya jarabasu ne don yaga reaction ɗin kowannansu,kuma ya samu abunda yake so,
Har kawo yanzu,wannan hoton da uncle abusufyan ya basu,yana nan a wurinsu kowannansu ya adana hoton kamar yarda uncle ɗin nasu ya roƙesu akan su ajiye hotunan a wurinsu,karsu yadda su,'
"Har yau uncle abusufyan,bai faɗamun wace yarinya ce ajikin photon nan ba,inason nasan kowacece ita,saboda in taimaketa,kamar yarda nayi niyyar taimakonta," Sgr ya fadi hakan.
Lumshe idanunshi yayi tare da gyara kwanciyarshi,nan take bacci ya ɗauke shi,
*su wanene acikin hotunan da Uncle abusufyan ya basu*!
 
  
  _Ayi mun uziri,in bansamu damar yin posting gobe ba,abubuwa sunyi mun yawa sosai,bansan ya zanyi ba,amma koda ace banyi a gobe ba zan yi ƙoƙarin biyan bashin wanda banyi ba,tunda ina ƙoƙarin ganin na Kammala littafinn ne insha Allah Zan yi kokarin sanya maku long pages,sannan kuma Labarinsu sehrish da nake tacewa za'ayi za'ayi lokacin shi yazo dama akwai abunda nake jira ne_



*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃


*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*


*LOCATION KANO*

08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku


Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
A*💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖


*Ga duk mai buƙatar littafin abban sojoji,from book one zuwa book two har inda muka tsaya,300 ne idan yayi payment za'a tura mashi duka sannan za'a sanyashi a grp da zai cigaba da samun cigaban shi akai akai,ga mai buƙata yayi mun magana kai tsaye ta whatsapp ɗina 08103884440 pls banda phone call,ban san meyasa wasu suke kirana a waya ba,Only message nace,kuma insha Allah mutun yayi mun magana bazan share shi ba,zan bashi amsa ne akan lokaci indae ba busy nake ba,sannan masu cewa suna som Book 3,pls su daina abun yana 6ata mun raina,cos ni ban rubuta book 3 ba,wasu can sarakan iyayi ƴan shisshigi suka haɗamun document ɗinshi,to abunda nake so na sanar daku,Abban sojoji dae Iya book two zai ƙare insha Allah,babu wani book 3,🤗*



*Kada ku manta muna acikin takon ƙarshe ne🔥🔥🔥*

_Father Of soldiers❤story and written by Hafsat Bature Mohamed Boss Lady_

❤🤍❤

Gagarumar Walima Abba ya shirya masu awashe garin ranar,na murnar dawowar Abusufyan Nigeria,tun da wuri aka soma shirye shiryen gudanar da ita,basu yi inviting ɗin kowa ba,anan cikin gidan kawai za'ayi ta,yasu yasu batare da wani bare ya shigo ba,don nasan halin sumayyer yanzu ta kwaso ƙafa tace zata,

Gaba ɗaya ko'ina na gidan ya karaɗe da ƙamshin dadɗaɗan girkin dasu azmee ke yi acikin kitchen ita da Hayaam,tun da sanyin safiya suka fara aikin girke girken,tun bayan da  Abbansu junaid ya sanar da ita game da walimar,suka soma gunadar da aikin batare da 6ata lokaci ba,


Matasan gidan kuwa wankan shadda zasu ɗauka gaba ɗayansu,kamar yarda Abbansu ya basu Umarnin su sanya shadda ajikinsu in kuma ba shadda ba kowane kalar kaya zasu iya sanyawa ajikinsu indai namu ne na hausawa,duk sun amince da hakan,


"Azmee wai ita yarinyar can bazata fito ta tayamu aiki bane?tun safe muke ta faman aikace aikace ko leƙowa batayi ba,"Hayaam ce tayi maganar yayin da take ta faman kwa6a fulawa acikin roba,duk ta haɗa gumi a fuskarta,'

Azmee tace"kema ae ban matsa maki ba,naga kamar kina son aikin ne shiyasa ma nayi maki magana,amma idan kin gaji ko yanzu ma zaki iya tafiya,"

Rae a6ace tace"yanzu me ya kawo wannan maganar Aunty azmee?nifa ina magana ne akan waccen yarinyar sehrish ya kamata ta fito ayi aikin da ita,na lura kamar bakiso inayi maki magana akanta,kin gatanta yarinyar sosai,shiyasa bata da aikin yi sai dae ta zauna tayi ta sharar bacci kamar matacciya,bata tsinana uban komai acikin gidan nan hakanan take sunan yar aiki...."

juyowa azmee tayi daga tsayen da take agaban gas cooker,ta kalli hayaam dake ta faman hura hanci ga uban gumi ta haɗa,
  "Hayaam!sehrish ba tada lafiya,shiyasa ban tashe ta daga bacci ba,tun jiya da daddare take fama da raɗaɗin ciwon ciki daƙyar ma aka samu tayi bacci,wannan dalilin ne yasa banyi yunƙurin tashinta daga baccin ba,"
   ta6e baki hayaam tayi tare da cigaba da aikin da takeyi cikin ranta tana fadin"ta dai gama iskancinta tayi bacci,

Marshal Omar

Tun yana cikin toilet wayar shi ke ta faman ringing,cikin sauri ya fito daga cikin toilet ɗin,jikinshi ɗaure da towel,ƙarasawa yayi inda ya ajiye wayar asaman pillow,ya miƙa hannunshi ya ɗauki wayar yana duba mai kiran nashi,murmushi yayi aranshi yace"Allah yasa jiya sun samu bacci,don na lura da yadda suke ta faman ɗokin son ganin ƴar uwar nan tasu,nima kaina a ƙagare nake dana haɗasu wuri guda,don su cigaba da rayuwa atare,
  Picking call ɗin yayi ya kara wayar a kunnanshi,
  Tun kafin yayi sallama muryar hosana ta katse mashi hanzarinshi da cewa"Ya omar!yaushe zaka zo ne!kai muke ta jira,jiya fa ko bacci ba muyi ba,
  Tana kai ƙarshen maganarta Jahad ta kar6e da cewa"ya Omar dan Allah ka tausaya mana,wlh ko breakfast ba muyi ba,kuma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login