Showing 180001 words to 183000 words out of 432432 words

Chapter 61 - Abban Sojoji Book 2 Hausa Novel Complete

ni ban faɗa maki hakan don na 6ata maki rai ba,kawai banji daɗin maganganun da kika faɗi bane agame da rishi,koba komai ita mutunce mai daraja,kuma yarinya ce dole mushiga damuwar rashin.....'.
  Bata bari azmee takai ƙarshen maganarta ba,ta buga uban tsoki tare da cewa"Ni bangan abunda damuwa ba anan,Ita tasan inda takai kanta,wama ya sani ko tana ɗakin hotel Kwance tare da kwartonta,ku kuna nan kun tashi hankalinku a banza"
  Waro ido waje Azmee tayi jin abunda hayaam tace,
  Shu'umin murmushin nan nata ta saki tare da juyawa ta nufi hanyar bedroom dinta,tabar azmee atsaye baki a sake tana bin ta da kallo,
  Lokacin da hayaam ta shige cikin ɗakinta,wani irin farin ciki ne ya lullu6eta ba don komai ba,sae don jin 6atar sehrish,addu'arta Allah yasa karsu ganta,
A fili ta dinga cewa"Allah yasa mota ta take kanta ta mutu kowa ya huta,dama natsani ganin yarinyar nan acikin gidan nan,"ta ƙarasa maganar tare da faɗawa saman gadonta hankalinta kwance,

Azmee kuwa lamarin ya fi ƙarfinta,ta jijjiga sosai da jin kalaman hayaam akan sehrish,tabbas ba ƙaramin tsanarta tayi ba,wannan ma in ta samu dama da alama zata iya halakar da ita gaba ɗaya,'

*Boss Bature*


Abun da ya faru lokacin da Sojojin nan suka bi sehrish a guje suna ƙoƙarin kamata ta kubce masu,ta hanyar faɗawa wata corner,kafin da gudun gaske sojojin suka bi ta cikin kwana din don su kamota sae dae kash,lokacin da suka ƙarasa cikin lungun tuni sehrish ta jima barin shi,da sauri suka bi lungun har ƙarshen shi,anan suka tarar da dogon titi,ko'ina sun duba babu ita,hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba,basu ga ta zama ba haka suka karaɗe ko'ina na garin wurin neman Yarinyar,

Yayin da suke ta yawan neman sehrish,ashe tana ƙarƙashin teburin mai siyar da kayan marmari a bakin hanya,lokacin da ta faɗo lungun ta futo aguje tarasa inda zata sanya kanta,kwatsam ta hango teburin nan na mai kayan marmari,babu wanda ya lura da ita lokacin da ta saɗaɗa cikin sanɗa,ta shige ƙarƙashin teburin jikinta nata faman kerma,gaba ɗaya duk tabi ta rikice ta ruɗe,ta razana kuma ta firgita sosai,sanadin wannan uban gudun da tayi ne,ya ƙara mata raɗaɗin ciwon cikinta ya dawo sabo,a can ƙasan mararta ta dinga jin wani irin zogin ciwo mara daɗin ji,kuka sosai takeyi ƙasa ƙasa duk tabi ta takure kanta a ƙarkashin teburin,ta ƙankame jikinta saboda wani irin Sanyi dake shigarta,ba ƙaramin kamu sanyin yayi mata ba,ko'ina na jikinta sae faman kakkarwa yakeyi,hatta teeth ɗinta gamewa sukeyi da juna,Sehrish taji jiki sosai fiye da tunaninku,baiwar Allah tama rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi,don ta jigata sosae ga uwar yunwar dake cin ta don ma ciwo da fargaba sun hana ta fahimci tana jin yunwar,gaba daya ta fita hayyacinta,wuraren ƙarfe sha ɗaya lokacin kowa ya watse babu mutane a wurin mai kayan marmarin,A hankali ta fito daga ƙarkashin Teburin tare da miƙar hanya tana tafiya tana tangaɗi akan hanya kamar wadda tasha Giya,da ƙyar take takawarma don jan kafa kawae take,a lokacin ita kanta batasan inda ta dosa ba,saboda ta fita hayyacinta,

Tana cikin wannan tafiyar agefen titi,wata mota baƙa ƙirar Rav 4,tayi parking adai dai inda sehrish take,wasu matasa ne kusan su Huɗu jigunannun ƴan iska,Zubin ibliss ne suka fito daga cikin motar,dukansu suna sanye cikin Riga da wando crazy jeans,Kallo guda zakayi masu kasan cewa ba Allah aransu,fitsararru ne na ƙarshe,wani ɗan iskan gyaran gashi ne akansu,na tantirae wanda suka haura matakin deegre a6angaren Tashanci,
   Jin motsin mutane yasa Sehrish yin firgit agigice ta juya tana kallonsu hankali a matuƙar tashe,kafin tayi wani yunƙuri tuni suka ɗauketa tare da toshe mata baki da tafin hannu suka turata acikin motarsu,back seat suka wurgata ciki,sannan suka shige ciki,tare da jan motar da gudun gaske suka fisgi Motar,
   kokowa sehrish ta shiga yi tana ihu tana hargowa tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!ku rabu dani!ku ƙyale ni!ku barni na tafi gida,nashiga uku,Wayyo Allahna,
  daya daga cikinsu ne ya sanya hannunshi tare da toshe mata baki ya daka mata tsawa yace"Ke!yi mana shiru anan,kin cika mu da hayaniya,its better ki rufa mana baki,don babu mai taimakonki anan,"
   Ba ƙaramin tsorata tayi ba,kankame jikinta tayi tana cigaba da ambaton sunan Allah acikin bakinta,
   Da gudun gaske suka shigar da motar cikin wani ƙayataccen garden tare da yin parking dinta,
  Buɗe motar sukayi gaba dayansu suka fito,na ƙarshen ne ya fito hannunshi ɗauke da sehrish yayi wurgi da ita,gaba daya ta gangara goshinta ya bugu jikin wata bishiya,dafe wurin tayi tana faman shesshekar kuka,ba ƙaramin buguwa tayi ba,dakyar tasamu ta ɗago daga kwancen da take aƙasa,
   buɗe idanunta tayi waɗanda suka kumbura suka ƙankance saboda kukan da tasha,a firgice taja da baya ta ƙure ma bishiyar dake bayanta tana kallonsu,idanunta azazzare hankalinta yayi mugun tashi,
  Su duka huɗun suna tsaye agabanta,kowannansu na kwance belt din wandonshi,girgiza masu kai tashiga yi tana cewa"dan Allah kuyi hakuri.. ..kada ku cutar dani....kada ku rabani da mutunci na....ku ƙyale ni na tafi gida ..bani da lafiya..."
  Abun nasu babu imani kwata kwata,duk wannan magiyar da sehrish keyi masu hakan baisa sunji tausayinta ba,
  A wulakance daya daga cikinsu yakai hannunshi tare da Fisge hijabin dake jikinta yayi wurgi dashi gefe guda ya faɗi ƙasa,
  Cikin sauri sehrish ta ƙankame rigar jikinta,saboda ta matse ta kirjinta ya fito sosai,

   gaba daya sun kwaɗaitu da ita,musamman da sukayi arba da kyakkyawar surar jikinta,mai matuƙar jan hankali,
   tamkar zata shige ma bishiyar haka ta manne tana kara matse kanta ajikinta,hawaye sae faman sintiri sukeyi a fuskarta,cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah ku ƙyale ni na tafi gida!bansanku ba bansan su wanene ku ba,bansan me yasa kuka ɗaukoni ba......'ƙasa karasa maganar tayi saboda jin daya daga cikinsu ya cafko gaban rigarta,da ƙarfi yajata nan take ta tashiga yagewa Allah yaso akwai farar half vest da tasanya daga ciki,daddagewa tayi ta gartsa mashi cizo asaman hannushi,a gigice ya saki rigarta,tattare wurin tayi da hannunta,jiki na rawa ta yunƙura zata tashi ta gudu,
   Wani daga cikinsu yasanya kafarshi tare da taɗiyo kafarta,nan take sehrish ta kife ƙasa,ta bugu sosai saukin ma ciyayi ne awurin ba duwatsu ba,.
   fashewa sukayi da dariyar sheƙiyanci suna kallonta,kafin daga bisani ɗaya daga cikinsu,ya afka mata yana ƙoƙarin keta mata haddinta,
  fashewa da kuka sehrish tayi mai sautin gaske saboda tarasa yarda zatayi ta kwaci kanta ahannunshi,
   Damƙa yakai ma wandon jikinta yana ƙokarin zame shi kenan,

dai dai lokacin wata danƙareriyar mota jeep ta kunno kai cikin garden ɗin atsiyace mai motar ke driving ɗinta,

motar na tsayawa yasa hannu tare da buɗewa ya fito daga cikinta,gaba ɗaya matasan nan guda ukun dake awurin zuba mashi ido sukayi atare suna tunanin wanene wannan ya faɗo masu acikin garden ɗin lokacin da suke tsaka da jin dadinsu,ya rufe fuskarshi da face mask,sannan ya manna baƙin glass a fuskarshi,wannan yasa ba zasu iya tantance ko wanene shi ba
  Jin sautin kukan yarinyar a cikin kunnanshi yasa shi juyawa cikin sauri yakai idanunshi akan wanda ke ƙoƙarin rabata da kayan jikinta,a wani irin zafafe ya tunkare shi,kwakkwaran damƙa yakai ma wuyar rigar shi da hannu ɗaya,ya ɗago shi tare da yin wurgi dashi gefe guda,
  Kallon juna sauran suka shiga yi,hankalinsu tashe ganin yarda ya ruƙo shi da hannu guda,duk girmanshi yayi wurgi dashi,
Kafin yayi wani yunkurin tashi daga wurgin da yayi dashi,ya dunƙule hannunshi tare da kai mashi naushi agefen fuskarshi,Nan take haƙora guda biyu suka 6allo tare da fadowa daga cikin bakinshi ɗauke da jini,
  Koda sauran matasan nan guda uku suka ga wannan tashin hankali,maimakon suyi ta kansu,rabon wahala sae suka tunkareshi suna naɗe hannun riga alamar zasu yi mashi rubdugu,
   Kamar jira yake su ƙaraso wurinshi,dukkansu ya haɗa yayi masu shegen duka,gaba ɗayansu babu wanda bai raunata shi ba,sae faman juyi sukeyi a ƙasa suna fadin Wash!Ash!
   Juyawa yayi tare da kallon Yarinyar dake kwance ƙasa sai faman burgima takeyi tana fadin kada ku rabani da mutuncina,ku ƙyale ni na tafi gida,banaso!banaso ku daina ta6amun jikina,gaba daya sehrish bata a cikin hayyacinta juyi kawai takeyi tana sambatu,
  juyawa yayi batare da yaje wurinta ba,dama taimako ne ya kawo su cikin garden din,Hanya ce ta biyo dasu ta saman titin shine suka ji sautin kukan mace acikin baƙar motar dake a gabansu wannan ne dalilin dayasa suka biyo bayan motar har suka gano inda suka shiga,cikin sa'a kuma suka tarar da abunda suke zargi,

  Karasawa yayi wurin motar tasu tare da buɗewa ya shiga ciki ya zauna yana faman sauke ajiyar zuciya,
   "Sir,yarinyar fa"? Drivern dake driving ɗinshi ne yayi maganar,
    Muryarshi a kasalance yace"Armstrong,muje gida kawai,am very tired,so i need some rest,'
   Armstrong yace"Sir,ya kamata ka ƙarasa aikin ladar da ka fara a taimaki yarinyar asan daga ina take"
  "Banyi niyya ba!,why ta fito wannan lokacin almost midnight,zata tashi ta koma inda ta fito ne"ya bashi amsa,
  Sam baiji daɗi ba,bai so Sgr yaƙi amincewa dasu taimaki yarinyar ba,yana ji yana gani zasu bar yarinyar kwance acikin garden ɗin cikin wani hali na neman agaji,ba yarda zaiyi,
  Tashin Motar armstrong yayi tare da janta baya baya sannan ya karya kwana suka fuce daga cikin garden din,
   Lumshe idanunshi yayi yana faman sauke ajiyar zuciya wani irin bacci ne ke fisgarshi,kwanakin nan yana stressing kanshi sosae,matsaloli sunyi yawa a kasar daga wnn sai wnn,abunda ma yafi bashi haushi yadda aka bar yarinya mace kamar wannan ta fito a irin wnn lokacin.
  Yana cikin wannan yanayin,ringing din wayarshi ya karaɗe kunnansu,cikin sauri yakai hannu cikin aljihun wandon jikinshi ya curo wayar tare da duba sunan mai kiran nashi,My Own Father,sunan da ya bayyana akan screen din wayar tashi kenan,
   ganin Abbansu ne yasa shi yin saurin picking call ɗin tare da kara wayar a kunnanshi yana sauraronshi,
  On the other hand abban nasu yace"Rafayet!kana ina ne"?
  Sgr yace"Abba yanzu muna kan hanyar dawowa gida ne,akwai wani abu ne"?ya tambaya yana jiran amsar da zai bashi,
  Cikin tashin hankali Abban nasu yace"Rafayet!yarinyar nan fa,ta 6ace an nemeta ko'ina acikin garin nan ba'a ganta ba"
   "Abba,I don't understand what u'r talking about,wace yarinya ce ta 6ace"?
  Kora mashi bayani abban nasu ya shiga yi game da 6atan sehrish,"
   Cikin sauri Sgr yayi rejecting kiran abban nasu tare da dakatar da Armstrong daga yin driving din da yake yi yace mashi"mu koma garden din nan,kayi sauri,"
"okey sir,"ya amsa mashi tare da karya kwana ya miki hanyar da zata maida su can wurin da suka baro,
  Tunda Abbansu ya sanar dashi 6atan sehrish,yake ji aranshi cewa kamar itace yarinyar da waɗannan matasan suka kai cikin garden din nan suna ƙoƙarin lalata mata rayuwarta,tabbas yana ji aranshi cewa itace yarinyar,duk da bai kalli fuskarta ba,amma yana ji aranshi cewa itace,

Bayan sun shigar da motar cikin garden ɗin,da sauri sgr ya fito daga cikin motar tare da nufar inda Sehrish take kwance bata iya ko motsi,sai numfashi da take fitarwa sama sama,Kuma har lokacin matasan nan guda huɗu da yayi masu bugun mutuwa suna nan baje ba wanda ya iya tashi,

  Ƙarasawa sgr yayi tare da zuƙunnawa wurin da sehrish take kwance,ya sanya hannunshi tare da juyo da fuskarta da kyau yana kallonta,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,taya akai yarinyar takai wannan lokacin awaje bata koma gida ba?da alama daga school take tunda ga uniform nan ajikinta,runtse idanunshi yayi tare da cizon la66ansa, buɗe idanun yayi gwanin ban tsoro sun canza launi saboda tsananin 6acin rae,aranshi yace wai dama ita ce!?
  Wurga idanunshi yayi yana kallon matasan nan dake baje ƙasa suna ta faman juyi,yunkurawa yayi a zafafe ya nufesu,naɗe hannun jacket din jikinshi yayi,One bye one ya bisu sae da ya canza masu kamanni yarda ko uwar da ta haifesu in ta gansu bazata ganesu ba,sae da ya tabbatar cewar bazasu ƙara amfanuwa ba,sannan ya haƙura ya ƙyalesu,
   dawowa yayi wurinta ya sake zukunnawa tare da sanya hannayeshi biyu,ya ɗaukota tamkar yar baby ya nufi motar da ita,
  Tun kan ya ƙaraso Armstrong ya buɗe masu mota,shiga ciki sgr yayi tare da ita,sannan armstrong ya koma ciki yaja motar suka bar cikin garden din,
   asaman kafadarshi sehrish ta kwantar da kanta,tare da ƙankameshi sosai jikinta nata faman kerma,yayin da idanunta ke a rufe la66anta nata faman kerma,
  gyaran murya ya ɗanyi tare da ce ma armstrong ya kashe na'urar A.C,'
  "Okey sir,"ya amsa mashi,batare da 6ata lokaci ba,ya kashe sanyin ac na motar gaba ɗaya,ya kunna masu warmer,na'urar dake dumama yanayi tamkar room heater,nan take cikin motar yayi ɗumi mai daɗin gaske,
  A hankali jikinta ya rage kermar da yake yi,zuba ma fuskarta ido yayi yana kallon yadda la66anta keta faman kakarwa,har lokacin bata daina wannan sambatun da takeyi ba,kawar da idanunshi yayi daga kan fuskarta ya mayar dasu saman wuyanta,kafin yayi ƙasa da idanun nashi izuwa saman ƙirjinta,cikin sauri ya kawar da idanunshi gefe guda,saboda wani irin bugu da zuciyarshi tayi,
   Janyeta yayi daga jikinshi ya jinginata ajikin seat na motar,sannan ya sanya hannunshi tare da cire jacket ɗin jikinshi,janyo sehrish yayi ya zura mata rigar sanyin tashi ajikinta,bayan ya kammala sanya mata rigar,ya janyo ta ajikinshi sosai ya ruƙota,saboda kermar da jikinta keyi,a firgice take har lokacin,ƙara ƙanƙame shi tayi sosai tana mutsistsike rigar jikinshi da hannunta,bai yi wani aune ba yaji hannunta asaman mararshi,ba ƙaramin gigita yayi ba,wani irin shock yaji ajikinshi,lokaci guda ta jefa shi cikin yanayi,sam ya gaza janye hannunta daga wurin,duk wannan abun da sehrish takeyi mashi bada saninta ba,saboda bata acikin hayyacinta,batasan wanene shi ba,raɗaɗin ciwo ne kawai ke fisgarta,
   Kafin Sgr yayi yunkurin zame hannunta daga saman mararshi tuni ta zarce da hannunta inda ba'ason zuwa,a gigice ya damƙo hannunta cikin nashi yana faman jan numfashi,runtse idanunshi yayi yana cizon pink lips ɗinsa,ware idanun nashi yayi a hankali sun canza launi izuwa dan ja,
   ƙasa ƙasa yaji muryarta tana cigaba da cewa"kada ku cutar dani dan Allah,ku barni na tafi, karku raba ni da mutunci na.....'
  lumshe idanunshi yayi a yayin da yake cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta,jacket ɗin da ya sanya mata ba ƙaramin kyau tayi mata ba,duk da tayi mata yawa sosai,
   yarda take motsi da tausasan la66anta tana sambatu ba ƙaramin burgeshi tayi ba,gaba ɗaya ya tsinci kanshi da bin su da kallo ko ƙyaftawa baiyi,
  Murmushi kawai armstrong ke saki yana driving ɗinsu anatse,ta cikin mirrow yake satar kallon Sgr daya kura ma sehrish ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi, Kasancewar akwai hasken fitilun motar daya haskaka ko'ina na cikinta, wannan ne ya bashi damar ganinsu sosai,sun burgeshi sosai,bai ta6a ganin Sgr nama wata ƴa mace irin  kallon daya kamashi yanayi ma ƴar tahalikar ba,tabbas kowacece wannan ba ƙaramar mai sa'a bace,ya fadi hakan acikin ranshi,
  ƙoƙarin kwantar da kanshi yayi agefen wuyanta,gyaran muryar da yaji ne yasa shi ɗagowa,kumshe dariya armstrong yayi,bakomai yasa shi yi mashi gyaran murya ba fa ce don ya tunasar dashi cewa bafa su kaɗae ne acikin motar ba,yana a kusa kar Ogan nashi ya sa6a number a gabanshi,
  Harara sgr ya wurga mashi tare da miƙa hannunshi ajikin motar,ya danna wani wuri,nan take Labule ya sauko daga sama,ya raba tsakaninsu da armstrong ya kasance bai iya hangensu,balle ya san meke wakana,
  Dariya sosai armstrong ya shiga yi,abun ba ƙaramin ƙayatar dashi yayi ba,bai so sgr ya sanya labule atsakaninsu ba,yaso yabarshi yaci gaba da kallonsu don ba ƙaramin kyau sukayi mashi ba,
  a hankali motar ta ƙetare babban gate din gidan nasu,bayan sun ƙarasa ciki wuring parking space,tsayar da Motar armstrong yayi sannan ya fito cikin sauri ya zagaya tare da buɗe mashi mota,
  A lokacin Hayaam na a tsaye gaban window tana leƙen motar tasu,dama tun ɗazu ta tsaya ajikin windown tana jiran dawowarshi,don takai mashi abinci tunda sehrish ta 6ace,tasan cewa yanzu dole ya haƙura ita taci gaba da kai mashi,cike da zumuɗin ganinshi,hayaam ke washe baki tana leƙo motar tasu,fitowar shi kawai take jira daga cikin motar,ta baza idanuwanta kamar na mazuru tana jiran ganin shi,ganin ya zuro kafarshi daga cikin motar yasa Hayaam lumshe ido tana sakin murmushin nan nata,
  Lokacin da ya ƙarasa fitowa daga cikin motar,hannu shi ya sanya tare da ɗauko sehrish gaba daya ya azata asaman kafadarshi,
  Nan take murnar hayaam ta koma ciki,hankalinta a matukar tashe take kallonsu,har hannu take sanyawa tana murza idanunta wai ko idonta ne ke nuna mata ba dae dae ba,lokacin da ta tabbatar da abunda idanunta ke nuna mata,na ganin Sgr ɗauke da Sehrish a kafaɗarshi,nan take ta fashe da matsanancin kuka tana bubbuga ƙafa,bakin ciki kamar ya kasheta,wani rin ƙululun baƙin ciki ne taji ya tokare mata a maƙoshinta,kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka ta dinga ji,
  cikin shessheƙar kuka take cewa"Wlh na tsani yarinyar nan!bansan ganinta!ƙoƙari take ta rabani da abunda nake hari!ni bansan ma ya akai ya ganta ba,harya ɗaukota acikin motarshi!Allah bazan barta ba saina illata ta,tunda har ta sanya na zubar da hawayena akanta!saina ga bayanta kafin ita taga bayan nawa"!
  Haka hayaam taci gaba da sambatu tana zagaye dakin nata kamar wata zararriya,
  Atare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da Sgr ya shigo cikin main palour din,kafadarshi ɗauke da sehrish,gaba dayansu sunyi mamakin ganinshi tare da ita,yarda akai har ya hadu da yarinyar,
  fuskar Abbansu dauke da farin ciki ya shiga furta"Alhamdulillah!Alhamdulillah Allah mungode maka,ba rabon asha wahala!"
  Wani irin farin ciki ne ya lullu6e junaid ganin sehrish dinshi,duk da ya ɗan tsorata da ganin yarda sgr ya daukota kamar bata numfashi,suma sauran duk sunyi tsaitsaye suna jiran jin bayani daga wurinshi,
Ƙarasawa ciki yayi tare da kwantar da ita saman 3 seater,
  Muryar Abbansu yaji a bayanshi yana cewa"Meya same ta ne?a ina kuka ganta"?
  Bai bashi amsa ba sae da ya fara juyawa ya kalli su fawan dake atsaye suna kallonsu yace"Tsayuwar me kuke anan,ba kuje kun kwanta ba,"?
"Sun shiga damuwa ne na rashin ganinta da akayi,shiyasa suka gaza runtsawa suma,"abban nasu ne ya bashi amsa,
  "Kowa yaje ya kwanta,"cike da bada umarni yayi maganar,nan da nan kowa ya kama hanyar zuwa bedroom ɗinshi ba tare da sunji wani bayani ba,
  Mutum uku ne suka rage atsaye suna sauraron jin bayani daga wurinshi,Abbansu da kuma marshal omar sae kanal yousouf,
   Matsawa omar yayi kusa da sgr dake atsaye ya dafa kafadarshi tare da cewa"Bro,a ina kuka same ta ne?
da kyar Sgr ya iya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login