Showing 33001 words to 36000 words out of 270744 words

Chapter 12 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2931

Areef mikewa ya yi yana faɗin "Momma bari na je na ɗauko matata, dan ba iya jurewa zan yi ba". Ya kai karshen maganar tare da wucewa da sauri. Kafin ta yi wani magana ma ya fice abinsa.

Dawo da kallonta a kan Lion ɗin ta yi tare da fara magana a nutse. "Ina Muhammad, Sudais da kuma A'isha suke?". Wato su Uncle Herry take nufi kenan.

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Just call them Herry, Josephine, and Tyson, because all of them are Kristen now, ba yanda kike tunani bane".

Zaro idanuwanta waje sosai ta yi, cike da mamaki ta ce "Harda Josephine ɗin?". Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba.

Shiru ta yi tana al'ajabin wannan al'amari, katse mata shirun ya yi da cewa "Momma forget about them, saboda babu mai gaskiya a cikinsu, ko kin tanbayesu, karya za su yi maki, kamar yanda suka yi mana, dukkansu bakinsu ɗaya, so forget about them, I will do something about da case, now abin da nake so da ke, kada ma ki sake yin maganar, kada kuma ki sake tambayar kowa komai a kan labarin baya, ki rufe babin kawai!".

Tabbas ta sha jinin jikinta na jin abin da ɗan nata ya faɗa, ta kuma sha ruwan mamakin yanda aka yi gabaɗaya su Dr William ya zama bakinsu a haɗe, ya aka yi Josephine mace mai hankali ta biye masu? Wai menene yake faruwa ne?.....

"Momma zan iya tafiya?". Ya faɗa cikin sanyin murya.

"Ina zaka je?".

Kai tsaye ya bata amsar gidan uncle zai je, kamar zata tambaye shi wani uncle ɗin daga ciki, sai kuma ta fasa, dan ta lura baya son yawan magana, hannu ta kai ta shafi kansa tare da fara kwararo mashi ruwan albarka da adduo'in masu ratsa jikin duk wani mumini.

Wani abin sai uwa, babu wanda ya taɓa yi mashi makamancin hakan, hakan tasa ya ji wani mugun sanyi tana ratsa zuciyarsa, Allah sarki, wata kila da ace gwaggo ta rayuwa da su, da ba zai yi zafin zuciya har haka ba, da ko ma yaya ne zai rage wasu abubuwa, uwa, uwa, uwa, haka Allah ya kirata sau uku kafin ya kira uba, Allah ka karawa iyayenmu lafiya da nisan kwana, waɗan da suka rigamu gidan gaskiya kuma, Allah ya jikansu da Rahman, ya kai haske cikin kabarinsu, ya sadasu da manzon rahma.

Miƙewa ya yi ya kara mastowa kusa da ita sosai, a saman cinyarta ya kwantar da kansa, a can cikin zuciyarsa kuma, yana jin tamkar ya haɗiyeta, saboda so da kauna. Ita kuwa, ta cigaba da kwararo mashi ruwan addu'a ba kama hannun yaro, tana yi tana shafa lallausan gashin kansa, ya yi shiru yana sauraronta, abin gwanin birgewa, kowa ya gansu a haka, sai ya matsa kwallar farinciki, haka ta yi wa Areef ma da ya shigo ɗazun, dan shi tun karfe 6 yana wajenta, sai hira suke yi har lokacin da Lion ɗin ya shigo.

Sai da ta kai karshen addu'ar ne ya ɗago kansa tare da kai ɗan bakinsa saitin kumatunta, sumbata ya manna mata a wajen yana faɗin "I really more appreciate and happy da ya kasance kece mahaifiyarmu, i love you so much my momma". Ya kai karshen maganar tare da sake manna mata sumbata a kumatun nata.

Shafa lallausan sajensa ta yi, tare da manna mashi sumbata a goshin tana faɗin "Na fika farincikin kasancewarku ƴaƴana, ina alfahari da ku, je ka wajen uncles ɗin naka ka dawo, idan ka dawo, sai ka gaya mani aikin me kuke yi? Akwai wanda ya gaje mu a karatu ne a cikinku? Ko dai babu Dr a cikinku?".

Jinjina mata kai ya yi tare da miƙewa ya nufi kofar fita ba tare da ya sake cewa komai ba. Da kallo ta bishi tare da fatan alkhairi har ya fice. Yana fita Mark ya shigo mata da abinci, dan Areef ya gaya mashi ya kawo mata abinci kafin su dawo, sai su ci a tare gabaɗaya.

A can gidan daddyn Rimsha kuwa. Sai misalin karfe 8:30 daddy ya fito cikin shirin kananan kaya, waje gabaɗaya ya fita, restaurant ya wuce, abinci ya sawo masu ya dawo. Kafin ya dawo mum ta jera plates da komai a saman table, tana zaune tana jiransa.

Ko da ya dawo, saman table ɗin ya wuce yana faɗin su Rimsha basu tashi daga barci bane? E ta amsa mashi da shi. Jinjina kai ya yi kafin ya ce "Okey ki kyalesu duk time da suka tashi, sai su zo su ci nasu breakfast ɗin". Okey ta amsa mashi da shi.

Wani irin daddaɗar kamshi perfume ne ya daki hancinsu, a tare suka ɗago kai dan ganin wanene. Jehan ce take saukowa daga saman bene, ta shirya cikin ɗaya daga cikin kayan da ta samu a cikin walldrop na bedroom nata, doguwar riga ce mai kama da baya, blue color, kaya sun yi mata matuƙar kyau, abinku da farar mace, ta haɗu da blue color, ai kunsan dole ta haska. Ta yafo gyalen kayan a kanta, light make up ne a fuskarta, sai lips gloss da ta sanya a kyawawan lausasan kananan lips nata, duk wanda ya ganta, sai ya sake waigawa ya kalleta, saboda ta fita ta yi kyau over.

Kusa da su daddy ta zo ta tsaya tare da ɗaga masu gaisuwa. Cikin tsantsar so da kauna suka amsa mata gaisuwar tare da tambayarta irin wannan uban kyau haka waye ta yi wa kwalliya.

A takaice ta ce "Daddy zan je naga gwaggona, ba zan iya zama ba tare da ita ba!" Ta kai karshen maganar tana yamutse fuska.

Kallon mum ya yi yana murmushi kaɗan kaɗan, ya sani, ba wata gwaggon da take son zuwa ta gani, Areef take son ta je ta gani, yana ganinta da asuba da ta ɗauka mashi waya tana kallon hoton Areef ɗin, kawai bai kula ta bane, duk yana ganinsu, kuma ya yi alkawarin ba zai saka baki a maganar ba, idan suka ji uwar bari, za su mayar da kansu kamar yanda suka kawo kansu gidan, nasu wasa ne, har yanzu su yara ne, ba su san sharrin so ba, ita dai Rimsha ga idanu sun kunbura luhu luhu kamar ba lafiya ba, Akila kam ba'a magana.

"Mummy ki saka baki mana, daddy ya kaini wajen gwaggona da wuri, Allah ji nake ba zan iya kara minti goma ban kalleta ba". "Gwaggo ko ko Areef surikina zaki je gani?". Mummyn ta tambaya tana ƙoƙarin zuba abincin a cikin plate.

Ɗaure fuska ta yi tamkar irin basawan nan, cikin fushi ta ce "Mummy waye kuma Areef?".

Galala daddyn ya saki baki yana ganin ikon Allah, Jehan akwai taurin zuciya kamar gwaggon nata, ai wanna yarinyar ba in da ta baro halin Lion, dan shi ma ya ɗauko gwaggon ta wani fannin, kamar taurin zuciyar da sauransu, tana kewar Areef kamar ta mutu a cikin zuciyarta, amma a fili ta wani dake kamar bata ma san shi ba, bayan kuma harda satan hotonsa ta yi tana ta kallo har barci ya ɗauketa.

Kawar da zancen mum ta yi da cewa "To zauna mu yi breakfast tukun nan, idan kin ƙoshi, sai a kaiki wajen gwaggo naki ". "Mum nifa ba zan iya cin komai ba tare da na kalli gwaggo ba". Ta kai karshen maganar tana matsowa kusa da daddyn, shi dai sai kallonta yake yi, ƴar karama da ita wai zata yi masu wayo, kamar ba su suka haifeta ba.

Mum zata sake yin magana Areef da ya shigo yanzu ya ce "Mum don't west your time, ba zata iya cin abinci ba har sai taga mijinta farincikinta, to gani na zo, nima dai na kasa cin abincin har sai na zo na ganki rigimammiya kawai".

Nan take daddaɗar kamshi perfume nasa ya bule ko'ina a palon, fuskarsa ɗauke da murmushi ya kariso cikin palon.

Wani irin nauyayyar ajiyar zuciya Jehan ɗin ta sauke tare da sunkuyar da kai kasa tana satar kallon shi, ya yi kyau matuka over, ji take yi tamkar ta je ta rungume kayanta, amma ina jiji da kai ba zai barta ba.

Yana karisowa wajen yasa hannu ya ɗan ja kumatunta yana faɗin "Sarkin rigima, da sanyin safiyar nan ma sai kin tasa mum a gaba da rigima ko? To gani nan na zo, sai ki kyale mani mum ɗina ta huta".

Harara ta wurga mashi tare da sa kai da nufin ta kowa sama abinta. Cikin sauri ya riko hannunta tare da jawowata jikinsa yana faɗin "Good morning my uncle, mum good morning".

Mummy dai kunya ya hanata ta ɗago idanu ta kalle shi, kun san Jehan ce ƴar farinta, ga shi babu kunya Areef ɗin ya zo ya wani rungumeta a gabansu ko a jikinsa, dole mum ta ji kunya, shi kuwa daddy, ko a jikinsa, shi da ya kalli fin haka ma, sau nawa yana kallon Aseef yana ɗaukar Akila cancak a gabansa, sau nawa yana kallon Lion da Rimsha a garden suna sha'aninsu, Areef da Jehan ɗin ma me basu yi a gabansa? Ai shi ya ga komai, dan haka basu wani bashi kunya.

"Ni ka sakeni Hai!". Ta faɗa cikin fushi, da tsawa kuma. Saketa ya yi dan shi ma baya son ya ja magana sosai a tsakaninsu, kasancewar yaga mum ta takure waje guda, duk sai ya ji wani iri.

Zama ya yi a saman ɗaya daga cikin tables chars ɗin, ita kuma Jehan ɗin ta haura sama da gudu abinta. Miƙewa mum ta yi dan ta basu waje, a cewarta, ba zata iya cin abinci tare da Areef ba, dan yana surikinta, miji ga ƴar fari.

Ta zo dai'dai zata hau step na stair case ta haura sama, kamar daga sama suka ji voice ɗin Lion da ya shigo yanzu yana faɗin "Ke where is my wife?".......BABBAR MAGANA, LALLAI LION DA SAURANKA, MUM ƊIN CE KE! KAI LALLAI KUWA.

Baki Areef ya saki yana kallon Lion ɗin da mamaki, a cikin zuciyarsa yana faɗin "Yau Lion ne yake cewa ina matarsa? Da bakinsa yake tambayar, bama ina Rimsha ba, ina matarsa kai tsaye? Wato yanzu kenan ya yarda matarsa ce? Kenan ya yarda yana sonta? Lallai kuwa abin da mamaki, ko da yake, dama duk ɗa na halak idan ya ji irin kyautatawa da daddyn Rimshar ya yi wa mahaifinsa, to dole zai so su Rimshar suma, ko dan daddyn nasu, ai dole ma Lion ya yarda da cewa yana sonta, kuma dole soyayyarta ta karu a cikin zuciyarsa over.

Sai dai sam Areef ɗin bai ji daɗin yanda har yanzu Lion baya girmana kowa ba, ya shigo musu har cikin Palo, sallama ma kasa kasa ya yi ta yanda babu wanda ya ji, ko sannu bai ce masu ba, babu gaisuwa a matsayinsu na kannen mahaifiyarsa, kawai yana wani yi masu magana tamkar shi ne ubansu, kai Lion har gobe dai akwai izzar bala'i, wato yafi karfin ya ce wa mummy mum ina kwana?! Tab lallai har yanzu da sauran aiki.

Shi dai daddy, da yake yasan izzar da ta fi hakan ma Lion zai iya nuna masu, sai bai ce komai ba, idan da sabo, ai ya saba da halinsu. Mum da bata saba ba, sai abin ya ɗaure mata kai, ya yi mata wani irin banbaraƙoi, amma haka ta daure ta nuna mashi a in da ɗakin Rimshar yake.

Bai sake cewa da su komai ba, ya wuce ya nufi saman tamkar shi ya gina masu gidan, akwai shi da bala'in nuna isa na wuce misali.

Matsa mashi a hanya mum ɗin ta yi, ya wuce abinsa, da kallo suka bi shi, Areef yana mamakin irin tsantsar nuna wannan uban isa na ɗan uwan nasa, tamkar baza'a mutu ba.......... GASKIYA DAGA KAN LION AN RUFE ISA DA IZZA, IN DAI NUNA ISA DA IZZA NE, TO SHI KARSHE NE, SHI FA JI YAKE YI TAMKAR KOWA DOLE YA KASANCE A KARKASHINSA, KUMA DOLE AYI MASHI BIYAYYA, KO ANA SO KO BA'A SO, KAMAR SHI NE UBANSU!!.

Bayansa mum ɗin ta bi, ita ma ta haura saman kenan, a in da ta wuce bedroom nata.

Rimsha tana zaune a saman tsakiyar bed nata, sai kuka take yi kamar ba gobe, kayan barcin jiya ne a jikinta, wando guntu zuwa santala santalan cinyoyinta, sai ƴar riga mai siririn hannu zuwa cibiya, fararene kal kal kayan, sun yi mata kyau over, gashin kanta a sake, duk ya barbazu kamar mahaukaciya, saboda kukan da ta rinƙa yi tana burgima a saman bed ɗin, shi ne yasa gashin nata ya bazu haka, ko wanka ta kasa tashi ta je ta yi, fuska ta yi jajir kamar tumatir nunanne.

A hankali ya turo kofar ya shigo, bakinsa ɗauke da sallama kasa kasa. Kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo, a zabure ta ɗago kanta tare da kai kallonta izuwa bakin kofar.

Ganin da gaske shi ɗin ne yasa ta miƙe da sauri tare da dirowa kasa daga saman gadon, da sauri ta nufe shi da nufin ta rungume shi, ko me ta tuna, sai kuma ta ja birki. Yana tsaye a bakin kofar yana kallonta.

Zubewa kasa ta yi a saman gwiwowinta tare da sake rushewa da wani sabon kukan. Yau ga ikon Allah.

Ya ɗan ɗauki ƴan mintoci kamar biyar haka, kafin nan ya tako a hankali izuwa cikin ɗakin.

A kusa da ita ya tsaya, hannun rigansa ya gyara kafin ya ɗauketa cancak izuwa saman bed ɗin. Zama ya yi da ita a jikinsa, yama rasa me zai ce mata, shi dai bai san kukan me take yi ba, bai kuma san ta ya zai tambayeta ba, sai ya ɗan zuba mata idanu yana kallonta.

Goga fuskarta ta fara yi a saman kirjinsa tana ɗan bubbuga kirjin nasa da hannunta ɗaya, tamkar wadda ta aikata mummunar laifi kuma tana babbar danasani.

"Meesha". Ya ambaci sunanta a hankali.

Kamar jira take yi ya yi magana, cikin kuka ta ce "Yaya Saif me ya kawoka gidanmu? Me kazo yi to? Ni ka tafi!". Tana kuka tana surutan.

Jinjina mata kai ya yi tare da sauketa daga jikinsa, ya kuwa mike da gaske zai tafi ɗin, kofar futa ya nufa, yana taku a nutse cikin kwanciyar hankali.

Da gudu ta diro kasa daga gadon, ta baya ta zo ta rungume shi tana mai cigaba da kukanta.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juyo gareta, dama yasan ba zata iya jurewa ya fice daga ɗakin ba, ai yasan irin tsananin son da take yi mashi, da gangan ya nuna mata cewa komawar zai yi kamar yanda ta ce bata son ganin shi.

Juyowa ya yi ya rungumota yana ɗan bubbuga bayanta a hankali, alamar rarrashi. Kara saka mashi kuka mai sauti sosai ta yi. Ɗaukarta ya yi suka nufi waje, dan ba zai iya jurar kukan nan nata ba.

A haka ya zo ya wuce daddy da Areef a palon, ya nufi waje da ita a saman kafaɗarsa.

Kai tsaye sai cikin mota, a gidan baya ya sakata, shi ma ya shiga gidan bayan, Donal ne dama ya ja motar suka zo. Har lokacin sai kuka take zuba mashi. Umarni ya yi wa Donal ɗin a kan ya fita ya basu waje. A hanzarce ya fice.

Rungumota sosai ya yi a jikinsa, sai a lokacin ne ya tambayeta meyafaru take yin wannan uban kuka haka. Kankame shi ta yi, ta kasa magana, sai yii, yi, yi, take yi tamkar wata ƴar baby.

"Meesha, meyasa kike son sakani a cikin damuwa ne? Kin san halin da nake ciki kuwa a yanzu?". Ya yi maganar yana ɗago haɓarta.

Subhanallahi zaro idanu sosai ya yi yana kallon yanda face nata ya dawo saboda kuka, idanu a kumbure. Nan take shi ma face nasa ta sauya, ɗaure fuska sosai ya yi, cikin nuna isa da magana kai tsaye ya ce wani mai karan kwanan ne ya taɓata da har ya sakata wannan irin kuka haka? Meya sameta?.

Jin yadda ya yi maganar babu wasa a tattare da shi ne yasa ta tsayar da kukan nata cak, da sauri ta waro jajayen idanun nata waje. Wani irin mahaukacin razana ta yi na ganin yanda fuskarsa take, ya ɗaureta tamau, ya haɗe geran sama da kasa, sam babu wasa ko ɗigo a tattare da shi.

Nan take wani irin tsoro ya kamata, dan bata san me zata ce mashi ba, ga shi ya ɓata rai over. Narai narai ta fara yi da idanu. Tsawa ya daka mata a kan wanene ya taɓata? Me aka yi mata da har zata yi irin wannan uban kuka haka?.

Kokarin barin jikinsa ta fara yi, dan ta gudu, ta koma cikin gida. Damko wuyar rigar jikinta ya yi, kasancewar rigar ɗan ƙaramin ne zuwa cibiya, sai gabaɗaya tula tulanta suka bayyana a waje. Da sauri ta koma jikin nasa ta kwanta tana mayar da numfashi, nan take ta nemi kukan nata ma ta rasa...... NI KO NACE AU, DAMA ASHE IYA SHEGE NE, DA KI GAYA MASHI ME YA SAMEKI MANA! KIGA YANDA ZAI YI BALL DAKE, DAN WLH IN DAI KIKA CE MASHI BAKI SON SHI NE SABODA DADDYNSA NA CI AMANAR GWAGGON, ZAKI YABAWA AYA ZAKINTA KUWA

Wani irin shock ya ji na komawa jikinsan nan da ta yi. Kankame shi ta yi, murya a dashe ta ce "Yaya Saif ni babu wanda ya taɓani".

Kai tsaye ya ce karya ne, ta gaya mashi wanda ya ɓata mata rai har ya sakata kuka haka, ko kuma ita ma ya hukunta ta, ya fara ta kanta. Shiru ta yi yana tunanin me zata yi mashi ne ya sauko? Me ya kamata ta yi mashi.

Can sai ta ce "Yaya Saif ciwon ciki ne fa yasa nake kuka, tun jiya da daddare cikina yake yi mani ciwo, kuma na kasa gayawa su daddy ne, dan a lokacin suna barci, da safe kuma na kasa iya fitowa waje, kuma muryata bata fita sosai bare na yi kuka da karfi su jini".

Hannu ya ɗaura a saman cikin nata. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, hankalinsa ya ɗan kwanta, da ya yi tunanin ko wani ne ya taɓata, da yanzun nan ya karɓi hukunci.

Shafa shafaffen cikin nata ya fara yi yana kallon face nata, gam ta datse idanunta, dan ma kada su haɗa ido, sai sauke nauyayyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login