Showing 237001 words to 240000 words out of 270744 words

Chapter 80 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2956

dayawa, kawai jiran goben nan suke yi ta zo, akwai shagali, ga hjy Rimsha First Lady da kanta, sai wani kara kyau ita ma take yi, ta yi wani dumur mur da ita, tana tafiya abubuwa suna juyi, kullum cikin rikita mana our Lion bawan Allah take yi, tasa ya yi ta biye mata kamar ba under 15 years da 32 years ba.........😂

Ganin Akila tana da ciki yasa gwaggo ta ce dukka sauran ma su zo a gwada su, irin wannan ciki na bazata haka, waya sani kila saura ma suna da shi.

Da sauri Brr Naurat ta ce haka za'ayi kam, duk su zo a gwadasu.

Da Anaya aka fara bayan gwaggon tasa an canzawa Akilar gado, ta ce Dr William ya ceci cikin Akilar kada ya fita, so yana ta fama da ita, shi kuma Lion ya koma gefe ya zauna yana tunani, shi dai har ga Allah baya son yara, bai shirya masu a yanzu ba, a cewarsa kuma babu ranar shirya masu ɗin, dan yara basu a tsarin rayuwarsa, ya kuwa yi sa'a dukka matan da aka gwadasu Rimshar ce kawai babu cikin a jikinta, Jehan and Anaya duk suna da ciki for two two months, cikin Akila yafi girma, ashe ba'a banza Jehan ta rinƙa yin zazzaɓi kwanaki ba, ashe cikin ne ita ma, ita dai Rimsha babu shi babu labarinsa, hakan yasa Lion ya yi farinciki ba kaɗan ba.

Gwaggo kuma ta yi bakin ciki ba kaɗan ba, dan tana da burin son ganin yaran Lion and sir Safwan, saboda sune masu kama da masoyinta Dr William, tana son ta sake ganin an haifa mata Dr William again, tana son ganin yarantar mai kama da Dr William, hakan yasa sam bata ji daɗin rashin samun cikin Rimsha ba, bugu da kari tun ranar da ta haifi QUADRUPLE soyayyar Lion da sir Safwan suka fi ninkuwa a cikin zuciyarta, ta fi sonsu sama da kowa, saboda wannan kama dai da suka yi da fist love ɗin nata wato Dr William.

Wani irin tattali da kulawa na musamman aka fara bawa Akila, Anaya and Jehan, ta kowani ɓangare samun kulawa na musamman suke yi, Aseef kam nasa ba'a magana, tamkar zai koma cikin cikin Akalar, saboda tsananin son da yake yi wa wannan ciki, kowani bayan ƴan lokuta kaɗan sai ya zo ya kwantar da kansa a saman cikin nata wai ko zai ji motsin babynsa, kowani lokaci aikin kenan, shi ma Areef hakan yake fama.

Shi kam Lion ya rungumi Meesharsa sun cigaba da gashi abinsu, sai zuba love kamar wasu tattabaru, basu da damuwar komai.

Josephine ta tare a part ɗin Aseef mai gabaɗaya, dan kula da Akila, saboda ita Josephine ta fi kaunar Aseef sama da kowa a cikin gidan, tana bala'in kaunarsa na wuce misali, shiyasa ma ta tare a part nasa, dan ta tabbatar da babu abin da ya samu Akila ko ɗigo.

Washegari kamar yadda yake a dokance aka rantsar da Lion a cikin........

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA🔥🌹)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581 ban da kira*



E48



Washegari kamar yadda yake a dokance aka rantsar da Lion a cikin fadar shugaban kasa da yake a cikin white house, su ba'a EAGLE SQUARE suke rantsar da shuwagabanninsu ba, saboda they're DEVELOPED COUNTRIES, so komai nasu ba na kanana bane ba, basu wuce su ɗauki 10 mins wajen yin abin da zasu yi a wuce waje, saboda suna ɗaukar lokaci da mahimmanci fiye da komai a Rayuwarsu, basu wasa da lokaci, dan in ya wuce ya wuce kenan ba zai dawo ba, hakan tasa suke daraja lokacin fiye da komai nasu, sai dai kuma sun shirya party a cikin fadar shugaban kasar, wanda iya ƙusoshin gwamnati da iyalansu ne kawai zasu halakta, party ma ta shiryawa Lion ɗin wani shagalin, ga su Areef sun shirya mashi a gefe wanda bai san da shi ba.

Dukka wasu masu muƙaman gwammanati sai da suka harci cikin fadar shugaban kasar.

Kamar yadda kuka sani ne a bisa ka'idarsu Lion ko in ce shugaban kasar zai je wajen ne tare da matarsa, to hakance ta kasance, tare suka shirya da shi da Meesharsa. Duk da cewa kowa yasan da cewa Lion ya musulta, domin ya yi editing na komai da komai nasa ya cire sunansa na Romeo William Jacob izuwa Saif William, duk da sun san da hakan, dan kafin ya yi hakan sai da sanin ƴan jarudu kamar yadda yake a dokance, amma kuma abin ya yi matuƙar basu mamaki na ganinsa tare da Rimsha kuma cikin shiga irinta addinin musulunci, sun sha mamakin ganinta cikin complete shiga ta rufe komai nata.
Sanye take da farar abaya mai bala'in kyau da tsada, sai ɗaukar idanu yake yi tsabar kyansa, ta yi rolling na veil ɗin abayar a kanta, sannan ta sanya face mask mai bala'in kyau irin na mijin nata a face nata, hannayenta da kafafunta dukka suna sanye cikin safa fara kal, ta yi kyau iya kyau duk da tana cikin face mask, watch da Lion ya ɗaura mata a hannunta kawai ya ɗauki idanun duk jama'ar da suke wajen, wani dankareren diamond watch ne wanda sai Allah kaɗai yasan a ina ya sawo mata shi, kuɗin wannan watch ɗin kawai ta isa ta sayawa mutun dankareriyar gida a malali Abuja, ga shi watch ɗin ɗan dai'dai da hannunta, duwatsun da aka yi wa wannan watch ɗin kwalliya ba ƙaramin ɗaukar idanu kyallinsu yake yi ba, daga wuyarta zuwa kunnenta dukka wasu shegun gwala gwalai ne wanda Josephine ta sanya mata, dan ita Josephine ɗin ita ce ta yi mata kwalliya yau, sai tashin kamshin perfume ɗin Lion ɗin take yi, sai dai kuma ta kara zama baka sosai a cikin masu jajayen kunnuwar.

Shi kuwa Lion sanye yake cikin wasu shegun tsadaddun suit masu bala'in kyau launin white color irin kalar kayan jikin Rimshar, ya tara kyakkyawar dark black curly hairnsa a baya ya ɗaure, sai face nasa ta fara fitowa sosai, sai dai kuma duk wannan uban kyau da ya yi fa fuska a ɗaure tamau kamar hadari, yau ya sanya siririn glass mai bala'in kyau a face nasa, sannan ya sanya face mask, cover shoes ce a ƙafarsa, kuɗin duwatsun dake jikin cover ɗin nan kawai ya isa ya buɗewa mutun katafaren mall mai cike tab da kaya, kusan takalmar kafarsu iri guda dana Rimsha, ita ma cover ce mai kwalliyar duwatsu masu bala'in kyalli a jiki, sai dai nata na mata ne nasa na maza, komai na jikinsu from up to down farare ne kal kal, tsadarsu kuwa baki bai isa ya faɗi kuɗinsu ba.

Tun da suka shigo white house Lion yake ruke da hannunta, ya kuma ɗan mannata da jikinsa dan ma kowa ya sani cewa ba son wasa yake yi mata ba, kuma ita Rimsha ma bata iya tafiya sosai, kafarta yana ciwo, shi ne ma yasa Josephine ta ce ta sanya cover shoe plat wanda Lion ɗin ya saya masu a tare, da ita Rimshar a yarintarta high heels zata saka, ita da kafa yake ciwo, Lion ya ragargajeta jiya, hakan yasa bata iya tafiya sosai, karfin hali ne ma kawai irin nata, da farko ma cewa ta yi ba zata je white house ɗin ba, sai da ya lallaɓata sannan ta yarda da cewa zata je.

Ita dai mummyn Rimsha kunya abin yake bata, yadda Lion ya wani rungume matarsa kamar ance za'a kwace mashi ita, gwaggo kam ko a jikinta, hannunta ita ma yana a cikin na Dr William kamar wasu taurari, kusa hasken fatar Dr William dana gwaggon ɗaya, da kaɗan ya fita, sun fito a iyayen QUADRUPLE ɗin da gaske, sai haskawa suke kamar wasu sabbin taurari.

Sam mummyn Rimsha taki yarda daddy ya riko hannunta a bainnar nasi, sai dai suka nufi cikin a jere kawai, saboda tana kunyar su brr Naurat. Shi kam Aseef da akwai dama ma ai ɗaukar Heartbeat cancak zai yi ya saɓata a shoulder ɗinsa su shiga ciki, dan baya son ta sha wahala, kada ta jijjiga mashi baby.

Areef da Jehan ma haka suka jero gwanin birgewa, yana ƙanƙame da hannunta. Sir Safwan da Maryam haka suka jera rike da hannun juna, duk kuma shirin Josephine ne, Uncle T tare da Aafia, Mahhir tare da Adiva, Dr Salman and Brr Naurat suna rike da hannun Pinky, Mark tare da Anaya, sai aikin turo baki Anaya take yi wai bata son zuwa, da kyar ita ma ya lallaɓata ta yarda ta biyo shi.

Tamkar wasu taurari haka familyb Dr Salman and Familyn Dr William suka shigo white house, a kalla dankara dankaran motoci sama da guda hamsin ne suka ɗaukosu daga gida, hakan zai tabbatar maka da Lion ya shirya abubuwa sosai, dan motocin gabakiɗaya sababbi ne gal gal, babu tsoho na gida ko ɗaya a ciki.

His Excellence ma yazo taya Lion murna, kuma dama dole ya zo, dole ya kasance yana wajen, dan shi ne zai miƙawa Lion ɗin mulkin.

Manyan shuwagabannin kasashe da dama sun halakci taron rantsarwar. An kawata white house ɗin nan na wuce misali, baki ya yi kaɗan ya zayyana yadda kawatuwarsa ya kasance, har shi kansa speaker room dake a cikin fadar shugaban kasar, komai sai dai mu ce masha Allah, billions of dollars aka narka wajen sake kawata white house ɗin, saboda sabon shugaba zai shi ga, tsadaddun motocin da aka zuba na fitar President a cikin white house ɗin ma kawai kuɗin su ya kai kuɗin budget ɗin wata ƙasar, dollars sun yi kuka, sun ci uwarsu a wannan lokaci, ita kanta kujerar da His Excellence Saif William zai zauna kuɗinta ya fi kuɗin budget na state.

Dollars da aka kashe wajen shirya kujerun zaman bakin da zasu taya Lion murna ma kawai ta isa wata kasa ta inganta kanta, shegun tsadaddun kujeru aka zuba, bafa wani zama zasu yi su jima ba, amma a haka aka narka waɗan nan shegun dollars ɗin kawai dan a kawata wajen, abin dai baki ya yi kaɗan ya faɗe shi.

Wani irin azababben fitinannen daddaɗar kamshin ne yake tashi a gabaɗaya ilahirin white house ɗin, ga wasu jiga jigan security's masu jini a jika dake aikin fesa perfume ta ko'ina. Dubbannin zaratan sojoji masu jini a jikka ne suka kewaye ko'ina a faɗin cikin white house ɗin, ta ko'ina idan ka juya kaki zaka gani rike da jiga jigan bindigu masu rai da lafiya, ƴan'sanda ta ko'ina suna shawagi, ga wasu haɗaɗɗun helicopters da suke shawagi a sararin samaniya dan kara tabbatar da tsaro, apart from helicopters da akwai wasu na'urori da suka tasa sama dan kawai su tattabar da tsaro, ga wasu kananan jirage masu amfani da computers, duk wasu Generals na sojoji sun hallara a wajen, a ɓangaren ƴan'sanda ma I.G da D.I.G na kasa bakiɗaya ma sun bayyana a wajen. Duk wasu Ministers sai da suka zo, ga manya manyan lauyoyi ma dukka a wajen.

Kowa daga cikinsu ya samu waje cikin tsadaddun luntsuma luntsuman sofas da aka jeresu a cikin fadar suka zauna, daga gefe guda kuma shuwagabannin kasashen da suka zo taya shi murna ne a wajen.

Dukkansu suna saman sofas Lion and Rimsha ne kawai suka hau saman stage ɗin da aka kawata shi da ado mafi tsada a duniya, shi kansa speaker da Lion zai yi magana a wajen da diamond aka yi shi.

Meesharsa tana gefensa, ga wasu jiga jigan lauyoyi ta kotun duniya da suke tsaye a gefe da gefensa, sanye suke cikin kayan lauyoyi masu kyau da tsada, ga su jajir dasu kamar ka taɓa jini ya zuba. Ta ko'ina hasken Cameras wanda ƴan jaridu suke ɗaukarsu ne yake tashi, daga ɗan bayansu Lion ɗin kuwa lieutenant General na sojoji ne, sai Major General and Brigadier General, su ne suka tsaya a bayansa ta gefe guda rike da jiga jigan bindigu, ta gefe guda kuma I.G and D.I.G na kasa ne tsaye a wajen.

Wani hamshakin shararren lauya ne ya kawo wa Lion wata takarda wanda zai karanta a wajen domin ya sanar da al'umma irin alkawarin da ya yi masu da kuma aikin da zai yi masu, takardar tana kunshe da abubuwa sosai na bayani da zai yi. Sai dai kuma, ko da suka kawo mashi bai karɓa ba, ya ɗaga masu hannu a kan baya buƙata.

Rimsha ta ƙanƙame shi sosai saboda tsoron waɗan nan jiga jigan sojoji dake tsaye a bayansu, ga taron jama'a dukka idanu naa kansu, hakan yasa ta kasa sukuni, baiwar Allah bata saba ba, duk sai ta shiga damuwa ta ƙanƙame shi sosai, shi ma ɗin bai saki hannun nata ba duk da sun hau saman stage ɗin, yaki sakinta, dan yasanta da shegen tsoro. Har mamaki jama'a suke yi, waɗan da basu gani su kyale har sun fara tofa albarkacin bakinsu, sai maganarsa ake yi, na farko ga shi sun ra'ina matar tasa, ƴar ƙarama da ita, na biyu ga shi sai biye mata yake yi, ya wani ƙanƙameta kamar sun ce zasu kwace mashi ita, hakan yasa ƴan jaridu suka kara ɗaukarsu hotuna sosai da kyau da kyau dan su sami abin yaɗawa a tashoshinsu.

Live aka kunna a fadar, gabaɗaya faɗin ƙasar har ma da na ketare ana kallon me yake gudana, kowa ya sha ruwan mamakin kin karɓar takardar nan da Lion ya yi, hakan tasa kowa ya nutsu domin ya ji menene dalilinsa.

Wani hamshakin alkali ne dake tsaye a wajen nasa speaker ne ya fara magana cikin ƙwararriyar turancinsu wadda tamkar a bakinsu aka kerata. Sallama irin tasu ta Kristen ya yi kafin ya fara da karantowa Lion ɗin abubuwan da ya shafi doka da kuma alkawarin da zai yi ma'ana ya fara karanto mashi cewa "Ni Saif William Jacob, a rana irin ta yau, a gaban dubbanin al'umma, na yi alkawarin rike kasa ta da gaskiya da amana, na yi alkawarin kawo mata dukkan wani cigaba, na yi alkawarin tallafawa talakawa da kula da rayukansu". Irin abubuwan da alkalin yake karanto mashi kenan, Lion ɗin yana maimaitawa cikin wannan cool voice ɗin nasa, tamkar baya son yin magana, da alama ma duk jikinsa a mace take, kuma hakan ce, zuciyarsa tana buga mashi, yana jin tamkar wani abin zai faru da shi, hakan ce ta kashe mashi jiki sosai.

Gabaɗaya ko'ina ya yi tsit, tamkar babu kowa a cikin wajen, duk sun kasa sunne suna sauraton zazzaƙar muryarsa yana maimaita abin da wannan alkalin yake faɗa.

Bayan wannan alkalin ya gama jawabinsa, sai aka buƙaci da Lion ɗin ya faɗa da bakinsa abin da yake so da kuma muradin yi wa kasarsa, wanda kuma dama shi ne a rubuce a jikin takardar da wancan lauya na ɗazun ya bashi yaki karɓa, shi kuma yaki karɓa ne domin ba'a aiki a takarda yake da buƙata ba, baya son kowa ya rubuta mashi abin da zai yi, zai faɗi kayansa da bakinsa, kuma zai jaddada hakan a aikace da izinin Allah, hakan yasa yaki karɓar takardar da lauyan ya bashi, sai kawai ya gyara tsayuwarsa tare da kara matso da Rimsha jikinsa sosai, sannan ya fara magana a daf bakin speaker tasa cikin kwarewa tare da sanyayyar muryarsa.

Daga nan ya buƙaci daddyn Rimsha ma ya zo ya yi nasa alkawarin a matsayinsa na vice president. Haka kuwa aka yi, suka iso wajen shi da mummyn Rimsha, duk da cewa face ɗin Rimsha na sanye da face mask, amma tsabar gulma irin na jama'a sai da suka iya gane cewa sir Nawazuddeen da mummy iyayenta ne, dan kuwa duk wanda ya ga kwayar idanun mummyn Rimsha ya ga na Rimsha sai yasan jini guda ne, yanzu duniya an daina kiwon dabbobi, an dawo kiwon mutane, tsabar gulma da sa ido har sun iya gano cewa vice president dai mahaifin First Lady ce, abin ya yi mugu mugun basu mamaki, wasu kuma abin ya burgesu sosai, musamman ƴan mata, sun ji matuƙar daɗi yadda Lion ya kasance a tare da surkunayensa inuwa ɗaya, a haka ma basu san cewa uncle nasa bane, su dai sun gansu kawai, kuma basu isa su tunkari wani daga cikin familyn da nufin su tambaye shi ba, sai kawai suna ta canki canka.

Cikin ƙwararriyar turanci daddyn Rimsha ya fara magana, dayawa daga cikin jama'ar wajen sun yi mamakin yadda aka yi harshen daddyn Rimsha bata da banbanci data Lion ɗin wajen magana, turancinsu iri ɗaya, ga shi dai suna yi wa daddyn kallon bakin fata, basu san cewa shi ma daddyn harshen nasa duk irin nasu bane, zaman Nigeria yasa ma harshen ta fara sauyawa, domin zamansa a Nigeria yaruka dayawa sun hau kan harshen, ba dan haka ba ai da duk ɗaya ne.

His Excellence ne ya kariwo wajen a in da ya miƙawa Lion ɗin hannu suka gaisa kafin daga bisani ya miƙa mashi takardun gwammati, waɗan nan files ɗin su ne suke nuna cewa ya miƙawa Lion ɗin mulki kenan kamar yadda doka ta tanada!! Sai kallon juna suke yi, His Excellence dai nasa kallon kamar da biyu, kamar ya shirya wani abin, shi kuma Lion nasa kallon tamkar wanda yake isar wa da kakan nasa sakon cewa lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login