Showing 174001 words to 177000 words out of 270744 words
tsayawa zayyana maku haɗuwarsa ma sam ba zai yiwu ba, dan baki ba zai iya zayyano haduwarsa ba, ga uban ma'aikata dayawa sosai, sai ɗan wane da wane ne suke iya kwanciya jinya a cikinsa, saboda tsada da kyau, kwararrun likitoci ta duniya ne ke aiki a cikinsa.
Kai tsaye kyakkywar elevatornsu Lion ya nufa, hawa na 10 ya nufa kai tsaye, da alama yasan address na in da zai je ɗin tun kafin ya tako kafarsa izuwa cikin kasar. Sai wani girmama shi suke yi, ko da ya isa hawa na gomar ya fito daga cikin elevator, duk wata likita da zai wuce sai ta duƙar da kai ta girmama shi, tun abin yana bashi mamaki har ya dai'na.
Kai tsaye office na babbar likita wato Dr Cherish ya nufa, yana taku cikin nuna isa da ƙasaita, sak yadda Sir Arvin yake tafiya, dan shi ma akwai shi da nuna isa da izza, ga ɗan banzan girman kai kamar me, yana kallon mutane kamar kashi, abin nasu a jini yake!! Babu in da Sir Arvin ya baro Lion, tamkar a waje guda suka yi rayuwa, tamkar a tare suka girma, suna kasashe daban daban, amma komai nasu kusan iri ɗaya ne, kama daga halayya ɗabi'u, komai dai, sak TRIPLETS sir Arvin yake!!.
Babu ko excuse ya danna ciki office na Dr Cherish abinsa, manya manyan security's uku dake tsaron kofar office ɗin babu wanda ya yi yunkurin hana shi, saboda a tunaninsu sir Arvin ne, dan yana zuwa hospital ɗin time to time, so sun san shi, basu isa su hana shi ganin Dr Cherish ba.
Tana hakimce a saman dankareriyar office chair ɗinta, A.c na bugata ta ko'ina, idanuwanta na sanye da wani shegen tsadadden farin glass, ga wani tsadadden laptop a gabanta saman table, daga gefe uban tulin files ne na majinyata, kyau iya kyau ta yi, kayan jikinta dukka masu uban tsada ne, watch dake ɗaure a hannunta sak irin watch dake ɗaure a hannun Lion ɗin, tamkar daga company guda suka saya, da yake yau ba watch nasu na TRIPLETS na sanya ba, wata ce daban, sai aka yi sa'a ta yi iri ɗaya sak dana Dr Cherish ɗin, ta dake tare da hakincewa a saman chair, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ga wasu tsadaddun waya har biyu a gefenta, daga dukkan alamu tana cikin kwanciyar hankali na wuce misali. Kowa dai yasan yadda office na babban Dr yake da haɗuwa da tsantsar kyau, ba sai na tsaya ɓata lokacina wajen zayyano maku haɗuwarsaba.
Tana ganinsa ta cire glass ɗin face nata tana faɗin "Arvin what are you doing here? Is there any problem? Kai da na bari a gida kana barci, ka ce mani fa yau ba zaka fita ba, ba zaka je office ba, to me kazo yi a nan?".
Saman chair ya zauna ba tare da ya amsa mata maganar tata ba. Lion akwai nuna tsantsar isa, ya shigo mata kai tsaye kawai, ya samu waje ya yi zamansa ba tare da izini ba, yanzu kuma me next our Lion?........... Alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana ce kawai zata gaya maku me next...❤️
Kallonsa ta fara yi from head to toe, yanayin kayan jikinsa sam ba irin dressing na Sir Arvin bane ba, Sir Arvin bai cika sanya jeans and t-shirt ba, ya fi yawan sanya suit kullum, sai kuma kayan ƴan kwallo da kuma pajamas, saboda shi tun safe yana office sai yamma yake dawowa gida, idan kuma ya dawo ya yi wanka kayan shan iska yake sanyawa, shiyasa kullum yake a cikin shigar suit kala kala masu tsada, bugu da kari sai yanzu ta lura da Lion ya fi Sir Arvin cika, sannan dark black curly hairnsa ya fi na sir Arvin yawa, kuma sir Arvin bai taɓa shigowa har ya zauna ba tare da ya yi mata magana ba, amma Lion har ta yi mashi magana ma bai amsa ba, daga haka sai ta fahimci wannan kamar ba sir Arvin bane, suna da banbanci, amma sai mutun ya tsaya ya lura sosai ne zai gane banbancin nasu.
"Who are you?". Ta faɗa a ruɗe tana zaro idanuwanta sosai a kansa.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
Date: 17/5/2024
E34
"Who are you?". Ta faɗa a ruɗe tana zaro idanuwanta sosai a kansa.
Shiru ya yi mata almost na 10mins, sannan ya ɗago kai a nutse tare da cire face mask dake a face nasa, a saman table nata ya ɗaura face mask ɗin.
Wani ruɗewa ta kara yi, saboda kara kamanceceniya da sir Arvin da ya yi, da ya cire face mask ɗin ma sai ainahin kamar tasu ta bayyana, in dai ba wai ka yi wa sir Arvin or Lion ɗin farin sani sosai ba, to bazaka taɓa iya banbantasu ba, ita kuma ita ce mahaifiyar sir Arvin, ita ta rene shi, ta san shi ciki da waje, so dole ne ta iya banbantasu da Lion, dole ta gano banbanci a tsakaninsu, dan ba ta yadda za'ayi ace sun fita abu ɗaya sak, dole da akwai banbanci, saboda duk duniya babu dai'dai sai Allah, Allah shi kaɗai ne dai'dai!!.
Jikinta har kerma ya fara yi, saboda tun da take a duniya bata taɓa kallon irin wannan tsananin kamanni a zahiri ba, sai dai a film, ashe akwaisu da gaske a zahiri? Abin ya ruɗar mata da ƙwaƙwalwa sosai, hakan yasa cikin hanzari ta ɗauko wayarta, number sir Arvin ta fara kira jikinta na wani kerma sosai.
Yana gida yana ta zuba barcinsa abinsa, hankalinsa a kwance, banda tunanin Lion da ta kutso mashi cikin rayuwarsa, da babu komai da yake damunsa.
Bugu ɗaya ya ɗauka, idanuwansa duk barci, a tsananin tashin hankali ta ce "Son where are you now?!".
Shiru kaɗan ya ɗan yi mata kafin ya ce "Mum am sleeping you know that, amma sai da kika tasheni, what do you want again? Before ki bar gidan nan sai da kika tashe ni fa, yanzu ma kika sake". Cikin muryar barci sosai ya yi maganar.
"Son come to our hospital now!". Ta faɗa words ɗin ta basu fita sosai, sai haɗesu take yi.
"Mum are you okey? Why are you talking like that? Is there any problem?". Ya yi maganar yana miƙewa zaune, saboda yadda ya ji tana magana sam bai yi kama da wadda take a cikin hayyacinta ba, ya fi kama da wadda aka sanyawa bindiga a kai aka sanyata yin magana dole, bai san cewa bama bindiga ce aka sanya mata ba, nuclear makamin kare dangi ce mai gabaɗaya zaune a gabanta, dan Lion shi kaɗai gayyace mai tarwatsa tawagar azzalumai, tamkar nuclear yake, idan ya shiga gungun azzalumai komai yawansu sai ya tarwatsasu, ga karfin halin bala'i, ga dakiya na wuce misali, ga kwarin gwiwa full a tattare da shi, baya sarewa kuma baya ja da baya idan zai dimfari waje, so abin da yake a gabanta yanzu yaci uwar bindiga, dole ta yi in'ina a magana, dole ta kasa fitar da words yanda ya kamata, a hakan ma bata san wanene a gabanta ɗin ba, ita dai kwarjinin dake a saman face nasa ne kawai ya razanata, bata riga ta ji waye shi? Kuma meya kawo shi ba?.
"Arvin i said come to our Hospital now!". Ta faɗa cikin ɗaga murya, tana kai karshen maganar ta katse kiran jikinta na ɓari, duk kuma maganar da take yi tana yin shi ne idanuwanta na a kan Lion ɗin, ko kyaftawa ta kasa yi.
Shi kuwa tun da ya shigo kallo ɗaya ya yi mata ma ya kawar da kansa gefe guda, dan baya da buƙatar sake kallonta, idan baku manta ba, shi baya ɗaga idanu ya kalli abu, tama yi sa'a ne da ya yi mata kallo gudan.
Tana son kiran security's su shigo dan tsoron kada Lion ɗin ya cutar da ita, amma ta kasa iya kiran nasu, saboda azababben tsoro da kuma kwarjininsa da take gani, ta kasa kiransu, dan a yadda take kallon Lion ɗin nan babu wani securitynta da zai iya ɗaga mashi yatsa ma bare har ya iya dakatar da shi idan ma zai cutar da ita ɗin ne, saboda shi a tsaye yake, kuma Lion irin mutanen nan ne da suke a buɗe sosai, hakan ma tana ɗaya daga cikin abin da yasa mutane suke tsoronsa, saboda Lion chest nasa a buɗe take sosai, zakin ne da gaske, ya ci sunansa na Lion ɗin.
Tamkar wata marainiyar biranya haka Dr Cherish ta koma saman chair nata ta zauna, duk da sanyin A.c dake dukanta, to zufa take haɗawa, ta yi wani fiki fiki da ita, ga idanuwan nata na ƴan China kanana da su, sai suka kara ƙanƙancewa.
Shi dai Lion saboda karfin hali ko sannu dai har yanzu bai ce mata ba, kuma yaki sake ɗago idanu ya kalleta.
Almost 30 mins suna a haka shiru kafin sir Arvin ya turo kofar office ɗin ya shigo bakinsa ɗauke da excuse, tun daga kan wannan excuse ɗin ta gane shi ne ɗanta, dan shi baya shigo mata babu excuse, saboda ya girmama mahaifiyar tasa, shi kuma Lion mai gayya mai aiki, bata kai ya ce mata excuse ba........... 😂
Wlh idan kana neman ƴan duniya idan ka samu Lion da Areef to shikenan ka gama komai.
Cikin tashin hankali sir Arvin yake faɗin "Mum what's happening?".
Subhallahi, ai sai a yanzu ne ma Dr Cherish ta shiga ainahin tashin hankali, saboda yadda mutane biyu suka haɗe suka zama mutun ɗaya saboda kamanni, sai dai fa shi Sir Arvin ɗan siririr ne kamar Aseef namu ɗan soyayya, dama na gaya maku Lion ya fishi cika.
Kasa magana ta yi sai dai ta nuna mashi Lion da yake zaune da hannunta. Karisowa cikin office ɗin ya yi yana cikin shigar suit ash color masu bala'in kyau da tsada, sai tashin kamshi yake yi.
Wani irin uban jan birki ya yi lokacin da idanuwansa suka sauƙa a kan Lion ɗin, duk da cewa tun jiya ya ga hotonsa, amma ya tsorata da ganinsa a zahiri, saboda hoto ma ta ɓoye wasu abubuwa, a zahiri ainahin kamar tafi fitowa sak.
Ganin yadda ya ja birki ne yasa Lion ɗin ya ɗago idanuwansa tare da saukesu a kansa. Kara waro idanuwan nasa waje shi ma ya yi, wani irin mamaki ne ta kama shi, sai dai bai bayyanar da mamakin tasa ba, saboda abin da ya kawo shi ba karamar abu bace, so ba zai bari su fahimci ya yanayinsa ma yake ba bare har su kawo mashi wata wargi, ya yi bincike a kan Dr Cherish sosai kafin ya zo, so ya yi mata farin sani, makira ce ajin karshe.
Kawar da kallonsa daga kan sir Arvin ɗin ya yi tare da mayar da shi izuwa kan Dr Cherish ɗin, calmly cikin wata iriyar nutsuwa ya ce "Where's Dr William?". Shi ne kalma ta farko da ta furta tun shigowarsa cikin office ɗin kenan.
A zabure ta miƙe tsaye tana kallonsa.
Kara ja da baya sir Arvin ya yi, saboda jin harta voice ɗin Lion sak irin tasa take, yadda suke magana a hankali sak iri ɗaya, yadda suke magana cike da class da nuna isa da tsantsar izza, shi ma sak iri guda, abin ya kara bashi mamaki.
Kallon kallo suka fara yi a tsakaninsu wato sir Arvin da Dr Cherish ɗin.
"Bana magana biyu, idan nayi na farko shikenan, in aka matsa sai na yi na biyu, to sai dai hannuna ya sake maimaitawa mutun, so is better for you da ki bani amsa ba ɓata lokaci, because i have a lot of things to do, time nawa yana da mahimmanci a gareni!". Cewar Lion, cikin wannan sexy voice ɗin nasa dai ya sake yin magana, hankalinsa a kwance.
"Who are you? And what do you want?!". Sir Arvin ya tambaye shi cikin ɗaga murya.
Tamkar bai san da tsayuwarsa a wajen ba, dan bada shi yake magana ba, kuma kunsan halin Lion, idan ba da kai yake abu ba to ko kai uban waye baya bi ta kanka, bama ka ishe shi kallo ba, so yanzu dai da uwarsa Cherish yake yi ba da sir Arvin ɗin ba, saboda haka bai ga dalilin da zai sa ya kula sir Arvin ɗin ba!! Babbar magana.
Ganin kamar bata da niyar yin magana ne yasa ya miƙe tsaye tare da harɗe tafukan hannayensa ɗaya cikin ɗaya yana ɗan shafe juna, kafin ya saci kallon sir Arvin ɗin dake ta gefensa ta wutsiyar idanu, sannan ya ɗauke Dr Cherish ɗin da wata iriyar mari wadda ta sanyata komawa saman chair ɗinta ta yi wani irin zaman ƴan bori.
Nan take ta fara ganin wani irin duhu duhu da wasu yana suna gifta mata ta cikin idanuwanta, kunnenta ta gefen da ya mara dai ya tashi a aiki, dan ta dai'na jin sautin komai ta gefen yana tashi, duk da tana zaune sai da ta kalli wani irin ajijiya mai karfi yana wani kwasan chair ɗin nata, da alama ta leƙa lahira ne ta dawo, tama yi ƙoƙari da bata suma ba, saboda zaratan maza ma basu iya shanye marin Lion bare ita mace, ko da yake dama ba zai mareta kamar yanda yake marin maza ba, zai sassauta mata, dan kada ta mutu bai sami amsar da yake so ba!!.
(Oh ni PRINCESS FATEEMA ya zan yi da karfin hali irin na Lion ne?🤔 Kasamu mata ka bata lafiyayyen mari a cikin office nata dake kewaye da security's babu ko ɗar ɗar? Bugu da kari a cikin kasarsu? Sannan a gaban ɗanta? Tana matsayin babban likita uwa ga jama'a?😒 Dole mu nemawa Lion sauki wajen Ubangiji, in dai karfin hali da nuna isa da izza ne daga kansa an rufe kofa, wato shi ko shakkar shiga cikin kasar tasu ma bai yi ba?🤔 Kai lamarin Lion sai shi wlh, sai kuma Rimsharsa ƴar baiwa, dan idan baka da baiwa ba zaka iya ɗaukar zama na minti goma da shi bama)
A fusace sir Arvin ɗin ya yi kansa, dama kuma yasan za'ayi hakan, shiyasa ma ya saki kallonsa kafin ya mari Dr Cherish ɗin, ya kalle shi ne dan ya ga a yadda yake, saboda ya ji daɗin bashi nashi marin da kyau idan ya nufo shi, dan yasan ɗan nata ba bari zai yi ba.
Sai da ya bari sir Arvin ɗin ya iso gare shi da nufin ya bashi mari shi ma, sai ya rike hannun nasa tare da ɗauke shi da marin shi ma, dan idan ba hakan ya yi masu ba, ba zasu yi mashi abin da yake so ba. Babban magana Lion da marin sir Arvin.
Bayan ya mare shi ɗin ma sai da ya haɗe hannayensa dukka biyu ta baya ya rike da hannunsa ɗaya, dama na gaya maku shi sir Arvin kamar Aseef yake, bashi da cika sosai, hakan yasa Lion ɗin ya rike hannayensa da hannunsa guda, cikin wata iriyar murya a kwance cikin nutsuwa ya ce "Ka nutsun mani, idan ba haka ba zan turaka in da ba'a dawowa, da uwarka nazo yin magana ba kai ba, so be careful!".
Turo kofar office ɗin da aka yi ne yasa Dr Cherish ta dawo cikin hayyacinta, shi kuma Lion hannu ya kai ya ɗauko wani kyalle fari da yake kusa da Dr Cherish ɗin ya ɗaure hannun sir Arvin ɗin ta baya, har lokacin sir Arvin ɗin bai dawo dai'dai na marin da ya sha ba, jiri ma yake gani, sai ya ji kamar ba shi ba, kamar ba'a duniya yake ba, ya maru ba karya, bawan Allah wannan jajir ɗin kumatun nasa bata taɓa shan mari ba sai yau, yau ɗin ma kuma marin Lion, ai dole ya faɗa wani yanayi na fita cikin hayyaci.
Bayan ya kammala ɗaure shi ta wutsiyar idanu ya kalli wanda yake shigowa ɗin. A dubu ɗari ya saki sir Arvin ɗin tare da juyowa da kyau ya kalli mutumin da ya shigo ɗin, shi kuma sir Arvin saboda yana ɗaure zubewa kasa ya yi a saman gwiwowinsa da Lion ɗin ya sake shi.
Cikakken Dr ne, kyakkyawan Bature tas da shi, yana sanye da suit masu tsada launin white color, ya ɗaura rigar aikinsa a sama, idanuwansa na sanye cikin white Medicated glass mai shegen tsada, hannunsa na ruke da wasu files dayawa, dark black curly hairnsa a ɗaure a bayan wuyarsa, sai sheƙi yake yi. From head to toe Lion ya fara kare mashi kallo, bai tsayar da kallon nasa a ko'ina ba sai a cikin dara daran blue eyes na wannan Drn, ɗan ciza lips nasa ya ɗan yi kafin ya dukar da kansa kasa yana wani irin sauke numfashi mai wuyar fassaruwa.
"Cherish what's happening here?". Cewar wannan Dr da ya shigo yanzu, ya yi tambayar yana mai do da kallonsa a kan Lion, cikin hanzari ya sake kai kallonsa a kan Arvin da yake durkushe a saman gwiwowinsa.
Zaro idanuwa waje sosai ya yi, cikin sauri ya ce "Cherish who is this guy that look like our Arvin over?".
Kasa magana