Showing 9001 words to 12000 words out of 270744 words

Chapter 4 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2923

William". A hanzarce ta miƙe daga jikinsa jin abin da ya ce, bata taɓa tunanin shi krista bane, duba da yanayin irin fuskarsa, yana da face mai kyalli sosai, idan ka ganshi, zaka yi tunanin yana sallah.

"Why are you avoiding me like that dan na ce am a Kristen? Shin da kika ce mini ke musulma ce did i do something like that to you?".

Girgiza mashi kai ta yi, sai kuma da ya yi magana ta fahimci ta yi kuskure na irin gudunsa da ta yi lokaci guda haka, yin hakan zai sanya ko da yana son shiga addinin musulunci ma, sai ya fasa, saboda zai ce dama haka musulmai suke? Dama basu son wani addini idan ba nasu ba?. Bai san mu musulmai kowa ma muna kaunarsa ba, kuma muna zaman lafiya da shi, addininmu mai sauki ne, addininmu mai ni'ima ne wanda ya bamu damar zama waje ɗaya da wanda ba musulmi ba, mu yi zaman mutunci, kamar da ƴan uwanmu musulmai muke tare, musulmai ne kawai za'a ci hakkinsu kuma su hakura, su yafe, su cigaba da zama da mutun, ai addinin musulunci babu biyunsa a duniya, ya yi ne kawai babu mai musawa sai dai wanda baya son gaskiya.

Shiru ta ɗan yi tana ƴan kame kame, ta rasa abin yi. A lokacin sam bata da wani ilimin addini sosai, haddan Alqur'ani mai girma ne kawai gareta, shi ɗin ma ba dukka ba, kuma bata san fasarar ko sururori biyu daga ciki ba, so hakan yasa ta rasa me zata ce mishi, sai dai ƴan kame kame, ilimin boko ya fi yawaita sosai fiye da misali a kanta sama da na addini, matsalar da aka samu kuma shi ne, ita bata wani zauna da su Brr Naurat sosai ba, secondarynta ma, boarding school ta yi, so bata sami lokaci da iyayenta sosai ba, shi ne yasa.

Ganin haka yasa shi ya miƙe ya koma saman sofar da take zaune. Kusa da ita ya zauna tare da ɗan riko hannayenta, cikin sanyin murya ya ce "Please kada ki gujeni, kin ji? I really love you the way you are, please love me the way i am, don't be angry because am a Kristen my angel, you hear?".

Wani sanyi ta ji a ranta na jin kalamansa, ta ji daɗi sosai, hakan yasa ta ji cewa zata iya janyo shi a jiki har ya karɓi addinin musulunci. Dan haka sai ta juyo da kyau suna fuskantar juna, cikin sanyin murya ta ce "I really love you the way you are, so don't worry!".

Sakin hannayen nata ya yi tare da buɗe mata hannu alamar ta zo gare shi. Ba musu ta faɗa jikinsa tana ɗan murmushi, shafa bayanta a hankali ya fara yi yana mai jin daddaɗar yanayi a tattare da shi.

"What is your name?". Muryarsa ya daki dodan kunnanta.

"A'isha". Ta bashi amsa, ɗan ɗago haɓarta ya yi yana faɗin "Nice nema, but can i call you my angel or my beauty?". Jinjina mashi kai ta yi alamar e. Ɗan kara matseta a jikinsa ya yi tare da sumbatar goshinta.

Haka suka kasance suna ta hira dan sanin juna har wajen karfe ɗaya na dare. A nan ne ta ce mishi barci take ji, zata je ta kwanta. A kunne ya raɗa mata a kan cewa tare zasu kwanta a gado ɗaya, Okey ta ce mishi.

Miƙewa ya yi da ita a jikinsa a in da ya gyara ɗaukarta da ya yi, ya zamana ya ɗaurata a saman kirjinsa, suka nufi cikin bedroom ɗin nata. Bai sauketa a ko'ina ba, sai a saman gadonta, murmushi ta sakar mashi kafin ta ce ta gode.

Hayewa gadon shi ma ya yi, daga ɗan gefen da shi ta kwanta, ya so tambayarta me yasa har yanzu take gudun shi, amma sai kuma ya basar bai tambaya ba, sai ma ya juya mata baya, dan ya lura tamkar tana cikin damuwa na kwanansu gado guda.

A can gidansu kuwa, su Uncle Herry sai neman shi suke yi, sun je bedroom nasa baya nan, hankalin daddynsu ya tashi, ga shi ya bar musu wayarsa ma a gidan, mum ɗinsa har da kuka ta rinƙa yi, tamkar yaro ne karami William ɗin, mutumin da ya kai 24 years a duniya, amma sun ɗaga hankalinsu har haka, da yake shi gaskiya ba mai yawan fita bane na farko, na biyu idan ma zai je party ko gidan rawa, yana gayawa mum ɗin nasa shi fa ya tafi waje kaza, kuma ba zai dawo ba sai time kaza, idan ya ce hakan, to time ɗin na yi zai dawo abinsa, hakan tasa suka ɗaga hankalinsu sosai da basu gan shi ba.

Shi kuwa shiru ya kwanta ya kasa yin barci, baya son gaya mata ne or ta gane, amma ji yake yi tamkar a cikin keji yake, gidan nata ya yi mishi ƙarami over, duk ya takura, dan fa su gidansu, gida ne na madarar kuɗi, babban yayan daddynsu shi ne president mai ci a yanzu, ga uban kuɗi da suke da shi na wuce misali, gidansu aljannar duniya ce guda, bedroom nasa kawai ya kai girman gidan nata gabaɗaya har da palo da kitchen, so bai saba da ƙaramin waje haka ba, duk sai ya takura.

Ita ma ta kasa barci saboda tsananin tsoronsa, sai taga kamar idan ta yi barci, zai yi mata wani abin, dan fa gani take yi kamar fyaɗe ya zo yi mata kamar yanda ya nuna mata tun farko.

After some minutes, can duniya ta kara yin shiru sosai. Lallaɓawa ta yi ta miƙe zaune, a hankali ta matso kusa da shi, cikin sanɗa ta ɗan leƙo fuskansa, dan ta gani ko ya yi barci. Tana so ne ta yi barci, amma ta kasa, saboda tsoro, shi ne ta zo ta gani ko dai ya yi barci ita ma ta samu ta yi.

Ganin idanuwansa a rufe yasa ta ɗan koma ta zauna zuciyarta na yi mata wasi wasi a kan bai yi barci ba, yana jiran ta yi barci ne kawai ya hake mata. Jin abin da zuciyarta yake raya mata ne yasa ta sake lallaɓawa ta leƙo face ɗin nasa.

Duk abin da take yi yana jinta, sai dai bai motsa ba, dan shi ma yana son ta sami nutsuwa ta yi barci. Amma ina abin ya ci tura, sake leƙo face nasa a karo na uku ta yi, dan ta kasa sakin jiki ta kwanta, ta kasa yarda da ya yi barci.

Jin haka yasa ya bari time da ta leƙo face ɗin nata a karo na ukun, sai ya jawo hannunta da ta kafa a jikin mattress ɗin ta gaban face nasa dan ta sami damar leƙa shi da kyau. Jawo hannun ya yi tare da juyowa gareta ta faɗa saman kirjinsa. Rungumeta sosai ya yi tare da juyowa da ita da kyau da kyau suna fuskantar juna. "My beauty, why zuciyarki bata yarda da ni ba?". Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin ba komai.

"Seriously babu abin da zan yi miki, idan ina son na yi miki wani abin, ki sani tsab zan iya yi ba tare da son ranki ba, amma i can't do that, so feel free and sleep kin ji?".

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗaura kanta a saman gefen kirjinsa, a hankali ta lumshe idanu bayan ta ɗaura hannunta a saman wuyarsa, ta ɗan saƙalo kenan.

Shi ma nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, sai a yanzu ne ya ji zai iya yin barci, ji ma ya yi tamkar kwanciyar nan da ta yi a jikinsa, kamar ta karawa ɗakin nata faɗi da girma ne, so sai ya ji yanzu yana normal.

Hannu ya ɗaura a saman bayanta tare da lumshe idanu shi ma. Ba jinawa barci ya yi awon gaba da su.......ASUBA TA GARI.

Da yake bata yi barci da wuri ba, har wuraren uku suka sami barci, sai bata iya tashi sallar asuba, makara ya kamata, shi dama ba sallah yake yi ba!.

Sai misalin karfe 7 na safe ta farka, a hankali ta waro idanunta, kai tsaye sai saman kyakkyawar face nasa. Sai zuba barcinsa yake yi hankalinsa a kwance, ɗan shafa lallausan kumatunsa ta yi tare da yunkurawa zata mike. Duk motsinta yana ji, dan sam bashi da nauyin barci, tun farkawarta ya farka shi ma.

Jin zata bar jikinsa ne yasa ya waro idanunsa a hankali shi ma, kai tsaye sai saman face nata.

Kasa kasa da murya irin na mai barci ya ce "Good morning my beauty". A hankali ya motsa laɓɓan nasa wajen furta maganar.

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta amsa mishi da "Morning my Dr, how was your night?".

Bai amsa mata ba, sai dai ya tsareta da idanu yana kallonta. Ganin hakan yasa ta yunkura zata miƙe, matsowa ya yi kusa da ita sosai tare da rikota. Can kasan makoshinsa ya furta "Can i have a one kiss my beauty?".

Ɗan ɗaga idanunta sama tamkar mai tunani ta yi.
Bai jira ta bashi amsa ba ya matso kusa da ita sosai tare da haɗe fuskokinsu, kafin ta yi wani yunkuri ma har ya fara kissing nata abinsa.

Wani irin duniya suka lula dukkansu biyu, Baturen mutun akwai shegen iya soyayya, ya yi mata wayo sai bata hot kiss yake yi.

Haka ya matseta a jikinsa tare da fara shafa mazaunanta da tun jiya suka tsole mashi idanu, kuma suke ɗaukar hankalinsa, cikin kwanciyar hankali yake yin komai.

Karar danna kararrawar kofa ce ta dawo da shi daga duniyar da ya afka. Da kyar ya iya raba bakinsa da nata, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta, murya kamar wanda ya yi shaye shaye, a hankali kasa kasa ya furta yana zuwa bari ya duba wanene.

Okey ta amsa mashi tare da miƙewa ita ma ta nufi toilet jiki ba kwari. A nata tunanin Cherish ce ma, ta san ita kaɗai ce take zuwa mata gida without a permission.

Toilet ta shige, shi kuma ya sauko ya nufi palo. Yana buɗe kofar suka yi ido huɗu da daddynsa, mummynsa, Uncle Herry da kuma ƴan'sanda guda biyar, masu sanye da kakinsu a jiki, jajir da su kamar tsada. A lokacin mummynsu tana da cikin Tyson, wato Tga kenan.

Hakika babu maraba a tsakanin face ɗin Dr William da mummynsa, harta blue eyes ɗin nata ne ya ɗauko, kyakkyawar mace ce na wuce misali, shiyasa dukkansu suke kyawawa tamkar su suka yi kansu, tana da tsawo sosai, har ta ɗara daddynsu tsawo, a takaice dai wannan blue eyes da tsantsar kyau na wuce misali, tsawo zara zara da su, a wajen mummyn Dr William suka gado shi, ga black cuirly hair sosai, gashin nata kuma har kugunta ta baya.

Da sauri mum ɗin nasa ta ce "My son, what brought you here? What are you doing in this dirty place? What happened to your eyes?".

Harara ya wurgawa uncle Herry dake tsaye a gafe kafin ya ce "What are you doing here Herry?".

Tun bai gama rufe baki ba Uncle Herry ya juya ya bar wajen, dan fa yasan ɗan uwan nasa sam bashi da sauki.

Dawo da kallonsa a kan dad da mum ɗin nasu ya yi, ɗan ɗaure fuska ya yi yana faɗin "Mum why are you disturbing your self like that? Ni fa ba yaro ba ne, you have to be.........." Katse shi ta yi da cewa lallai shi yaro ne a wajenta, kuma ya zo su tafi gida.

Make mata kafaɗa ya yi a kan shi dai ba zai tafi ba, daga karshe ma sai ya ce suje gidan yana zuwa. Sun yi sun yi ya gaya musu me yake yi a cikin wannan kurkukun gidan, local da shi. Amma ina, sam yaki faɗa, sai ce musu ma ya yi, idan basu tafi ba, shi zai yi kuka tun da haka ne.

Basu da zaɓi, dole su tafi, dan suna mugu mugun son farincikin ɗan nasu fiye da komai a duniyarsu, su ne nan suka ɓata shi da kuɗi, suka sanya yana yin abin da ya ga dama, ya taka kowa, babu wanda ya isa ya taka mashi birki.

Bayan sun tafi sai ya dawo cikin ɗakin, saman bed ɗin ya koma ya zauna yana tunanin abubuwan da suka faru a tsakaninsa da gwaggo tun daren jiya zuwa yanzu, mamakin kansa yake yi, tamkar ba shi ba, mace ta canza shi a lokaci guda. A haka ta fito ta same shi, jikinta na ɗaure da towel white color mai ɗan girma zuwa gwiwa.

Binta da kallo ya yi babu ko kyaftawa. Har ta kammala shafa Lotions nata yana ta kallonta, da yake sam ita ma bata san kunya ba, sai ya zamana ko a jikinta, bata damu dan yana cikin ɗakin ba, haka ta shafa duk abin da zata shafa a gabansa kafin ta nufi dressing room na cikin ɗakin nata. Sai da ya ga shigarta dressing room ɗin ne ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da jingina kansa da jikin headboard na bed ɗin yana sauke numfashi a hankali hankali.

After some minutes. A haka ta fito ta same shi. Shirye take cikin wandon jeans baki da riga mai ƙaramin hannu pink color, ta yi matuƙar kyau sosai, ta ɗaure gashin kan nan nata a tsakiya, sai tashin fitinannen kamshi take yi. Kamshin perfume ɗin nata ne ya daki hancinsa ya sanya shi ɗagowa yana bin in da ya ji kamshin da kallo.

Wow ya furta da ɗan karfi tare da ɗaga mata gera ɗaya. Murmushi kaɗan ta yi hannunta na rike da dadduma da hijabi. Ta kusa da mirror ta je ta shimfuɗa daddumar tare da sanya hijabi ta tsaya ta tada sallah. Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take sallar babu ko kyaftawa.

Har sai da ta kammala kaf a kan idanunsa tamkar mai karanta wani abin, bayan ta kammala ne ta miƙe tare da naɗe daddumar ta nufo in da yake zaune. Cikin sanyin murya ta ɗaga mishi gaisuwa tamkar mijinta na sunna.

Fuska ba yabo ba fallasa dan baya dariya, haka ya amsa mata. Duba kyakyawan ƙaramin watch dake ɗaure a hannunta ta yi tana faɗin "Dr muna da class karfe 9:30 fa, yanzu kuma 8:30, remain 1 hour, ya kamata ka je gida ka shirya, sai mun haɗu a school ko?".

Nisawa ya yi tare da miƙewa tsaye, nan take ta dawo tamkar Rimsha a gaban Lion, dan ya fita tsawo sosai shi ma, kamar dai Lion da Rimsha, gara ma Dr William da gwaggo, ratar shekaru babu yawa a tsakaninsu, shi kuwa Lion ratar shekaru dake a tsakaninsa da Rimsha suna da yawa. 31 to 32 years Lion yake da shi, ita kuma Rimsha 14 to 15 years, kun ga kuwa da akwai rata sosai a tsakaninsu, so gara Dr William da gwaggo.

"Bana jin zan iya tafiya na barki, dan ban gaji da ganinki ba". Ya faɗa a sanyaye, shi kansa baya sanin time da wasu kalamai suke fitowa daga ɗan bakinsa nan, bawan Allah ya faɗa tarkon mace lokaci guda, ji yake yi tamkar ba zai iya tafiya ya barta ba.

Juya idanunta sama ta yi tamkar mai tunani. Shiru ya yi yana ta kallonta.

"Ai zamu haɗu a school ko?". Gera ɗaya ya ɗaga mata ba tare da ya yi magana ba, idanuwansa a shanye kamar wanda ya yi shaye shaye.

"Tom shikenan ka je kawai kada ka damu ka ji my Dr?". Dogon numfashi ya ja tare da buɗe mata hannayensa a kan ta zo su yi bye bye.

Da sauri ta faɗa jikin nasa tana ɗan murmushi, rungumeta gam ya yi na ƴan mintuna kafin ya ɗan sassauta riƙon nata da ya yi tare da ɗago haɓarta suna fuskantar juna.

Rankwafowa kanta ya yi tare da haɗe fuskokinsu. Cikin nutsuwa ya fara kiss nata tamkar matarsa ta sunna. Ko da yake su a wajensu ai lafiya lou ne yin haka, ba wata matsala ba ce. Ya Ubangiji ka hanemu da aikata duk abin da ya zamana ka haramta shi, ka tsaremu da faɗawa taka dokokinka. DA AKWAI DARUSA DA DAMA A RAYUWAR DR WILLIAM DA GWAGGO, HAKA ZALIKA A GABAƊAYA LITTAFIN TRIPLETS KEWAYE YAKE DA DARUSA DA DAMA A CIKINTA MASU AMFANI GA AL'UMMAR MUSULMAI, WANDA DUK ZAN KAWO MUKU SHI A KARSHEN LITTAFIN NAN IN SHA ALLAH, A YANZU MA NASAN KUN KOYI DARUSA DA DAMA SOSAI DA SOSAI, AMMA AKWAI ABUBUWAN DA TUNANINKU BA ZAI KAI KANSU BA HAR SAI NA WARWARE MUKU, KU DAI KAWAI KU KASANCE DA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA DAN KU JI KOMAI DALLAH DALLAH. ALLAH KA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN LAFIYA, KASA NA CIGABA DA RUBUTA MAKU LABARAI MASU AMFANI DA FAƊARKAWA, ILMANTARWA, WA'AZANTARWA, HAR MA DA NISHAƊANTARWA, NA RUBUTA MAKU LITATTAFAN WAƊAN DA BABU SHIRME KO SHIRIRITA A CIKINSU, NA GODEWA ALLAH DA BAIWAR DA YA YI MANI NA RUBUTU, HAKIKA NA SAN LITATTAFAINA BABU SHIRME A CIKINSU, SAI FAƊAKARWA DA ILMANTAR, KUMA SAIDA NE KO MY READERS?.

Mayar mishi da martanin kiss ɗin ta fara yi ita ma babu kama hannun yaro, nan take tasa ya fara ficewa daga cikin hayyacinsa. Ba sai na sake faɗa ba, kunsan Turawa da soyayya, akwai iya madarar soyayya zallah.

Daga ita har shi kasa tsayuwa a kan kafafunsu suka yi, hakan tasa suka faɗa saman bed ɗin. Mirginawa ya yi a in da ya yi mata rumfa da kirjinsa. Hannu ta tura cikin gashin kansa tana shafawa, shi kuma hannu ya ɗaura a saman breast nata ya fara matsa mata su ta saman riga.

Haka suka kasance na tsawon mintuna 20, sosai ya yi romancing nata, sai dai bai yi yunkurin kusantarta ba, dan ta ce mashi bata son hakan, amma ba shakka yana son kusantar tata, kasancewar ya kamu da sonta da tasa baya son ɓacin ranta ne yasa ya hakura ya jure, suka yi iya romance kawai.

Da kyar ya iya kyaleta ba dan ya so ba, sai dan time ya tafi, mikewa ya yi daga kanta idanuwansa tamkar wuta saboda ja. Palo ya nufa yana yi mata bye bye tamkar wanda yake cikin maye. Ita ma jiki duk a mace ta mike ba tare da ta canza kaya or something like that ba, ta gyata jikinta kawai ta karisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login