Showing 42001 words to 45000 words out of 270744 words
yake?". Areef ya sake tambaya.
Kasancewar daddyn bashi da burin da ya wuce yaga matarsa ta dawo, sai ya basu labarin tsamar da take a tsakaninsu da baban Muneer ɗin, bai ɓoye masu ba, harda videon da ya yi mashi na sharri duk ya gaya masu.
"Aina yake to yanzu?". Areef ne ya sake tambayarsa, nan ma basu amsa ya yi da shi dai a Kano ya barosa, so bai san a ina yake ba yanzu.
Kallon Imran Areef ɗin ya yi yana faɗin "Zamu je wajen yanzu ko prof?". Jinjina mashi kai Imran ɗin ya yi.
Nan take hankulan kowa ya kara tashi, ganin da gaske Ayla fa ta ɓata ne, babbar magana.
Areef, Imran, da kuma Irfan ne suka nufi Kanon tare da tallafawan daddyn Jelly da ya basu number wayar babban yaronsa, wato engr Muhammad Imam, a kan idan sun je Kanon su nemesa, zai yi masu karin bayani a kan wanene Baban Muneer, zai ma kaisu har companynsa. Da farko daddyn Jelly ya ce da wuya idan baban Muneer ɗin ne ya ɗauketa, dan shi a Kano yake, sai da Areef ya gaya mashi cewa, ai zai iya turowa a ɗauko mashi ita, dan wlh mai son abinka, ya fi ka sanin hanyar kula da shi, dan ya ɗauka, shi ne sai hankalinsa ya yarda a kan hakan.
Da kyar Abba ya lallaɓa matan suka koma cikin palo, su kuma mazan, wato su Abbi, sai suka fita gari nemanta, ko Allah zai sanya a ganta, daga nan su kai report station da sauransu........NIMA PRINCESS TEEMA INA TAYAKU DA ADDU'AR ALLAH YASA A GANTA ƊIN, AMMA ƁATAR AYLA BA KARAMIN ABU BANE, DAN DOLE DAI HANNU NE YA ƊAUKETA, SABODA BAIWAR ALLAH NAN KO HARABAR GIDA BATA FITA, TO WAYE YA ƊAUKETA? ALLAH SARKI, GA KARAMIN CIKI, GA UBAN LAULAYI.
A ɓangaren Lion kuwa. Bayan sun kammala cin abinci, Rimsha ta kwash kayan abincin ta fitar, ta gyara wajen tsab, sai ta dawo ta haye saman bed nasa, a kusa da shi ta kwanta, tare da lumshe idanu, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita, saboda daren jiya bata samu damar runtsawa ba.
Shi kuma Lion, yana can yana aikin latsa laptop nasa, Tyrone ya ɗauko mashi wannan memory da camera ta naɗi komai, sai dai, da kyar aka samu memoryn, dan ma dai babu nai shiga gidan nan, kuma dama ana ajiye storyn camera irin haka sosai, so suna nan a ɗakin computers ɗin, an dai ci kwakwa ne kafin a nemosu.
Miƙewa Lion ɗin ya yi tare da ficewa daga bedroom ɗin. Ɗakin gwaggo ya koma, tambayarta ya je ya yi a kan zata iya tuna ranar da abin ya faru a tsakaninta da Dr William, ma'ana ranar da ta kai mashi TRIPLETS ɗin gidansa. Cikin sauri ta ce ai bazata taɓa manta wannan rana ba, biyu ga watan biyu ne.
Jinjina mata ya yi da ƙoƙarinta na ruke komai na tsawon shekaru a kanta, sannan ya juya ya koma bedroom nasa. Cewa Tyrone ɗin ya yi da ya saka memoryn a laptop, ya duba mashi videon biyu ga watan biyu a shekaru 32 baya.
Okey ya amsa mashi tare da fara aikin babu kama hannun yaro. Cikin ƙanƙanin lokaci ya samo video ya turowa da Lion ɗin.
A hanzarce ya buɗe video, dan dama jira kawai yake yi. Shiru ya yi ya zubawa video idanu yana ganin komai kamar a gaske a gabansa ake yin komai. Tun daga shigowar gwaggon gida, tun wayewar garin ranar, har shigowar gwaggon da TRIPLETS ɗin, yanda ta faɗa, ga yanda ta kwantar da su a saman sofa, komai da komai yana gani kamar a zahiri.
Dai'dai lokacin da Dr William ya bugawa jariri ɗaya santa, sai da Lion ɗin ya datse idanunsa, saboda har cikin ransa ya ji saukar wannan sandar, babu irin azabar kalolin kisa da Lion bai gani ba, amma ba zai iya jure gani ko ɗan ƙaramin bulala ne ya taɓa TRIPLETS nasa ba, shiyasa lokacin da ya ga Dr ya kwalawa ɗaya ɗaga cikinsu sandar, sai da zuciyarsa ta amsa, ji ya yi tamkar shi aka bugawa.
A hankali ya waro idanunsa ya cigaba da kallon video, yana ganin gwaggo ta fice waje da gudu, shi kuma Dr William ya yi kan yaran da gudu bayan ya jefar da sandar, ita ma Josephine da gudu ta kariso cikin palon.
Ɗaukar jaririn Dr ya yi, da gudun gaske ya nufi waje da shi, sai zubar da jini kansa yake yi, kai tsaye asibiti ya nufa shi da Uncle Herry, ita kuma Josephine, kan sauran jarirai biyun ta nufa, da sauri ta ɗauko ɗaya ta ruke a hannunta tana shafa ɗayan da yake kwance a saman sofar da hannunta, dan ta tabbatar da lafiyarsu.
Sai ruwan hawaye take yi. Kamar daga sama wani mutun ya faɗo cikin palon, wani dogo da shi, yana sanye da bakaken kaya, long cut ce baka a jikinsa, daga ta cikin kuma T-shirt ce mai karamar hannu, ita ma baka, ya sanya wata hula mai gashi a kansa, fuskansa na a sanye da black mask, hannayensa dukka biyu suna sanye a cikin hands gloves bakake kirin suma, kafarsa na'a sanye cikin Booth baka kirin, baka iya ganin komai na daga jikin mutumin nan fa ce idanunsa da suke ashe color masu tsananin haske kamar glass, tamkar ba na mutun ba.
Hannunsa na ruke da jariri sabon haihuwa cikin towel baka kirin, ga jaririn fari kal da shi, kasancewar yana jikin bakar towel ga shi fari kal, sai ya haska sosai.
Kai tsaye Josephine mutumin ya nufa, yana zuwa ya miƙa mata jaririn da yake a hannunsa, karɓa ta yi, ita kuma sai ta miƙa mashi ainahin cikon TRIPLETS da yake a hannunta, tana yi tana shafa kan baby ɗaya da yake kwance. Juyawa mutumin ya yi da ainahin cikon TRIPLETS ɗin a hannunsa, ta kofar da ya shigo, ta nan ya fita, ita kuma Josephine, sai ta cirewa jaririn da mutumin ya kawo waɗan nan bakaken kayan da suke jikinsa, sai ta ɗauko wani towel fari daga cikin ɗaki ta rufe shi da shi, sannan ta kwashi bakaken kayan ta nufi waje da su.
Jim kaɗan ta dawo, kusa da jariran ta dawo ta zauna tana kare masu kallo, babu wanda zai iya banbanta su, babu wanda zai iya cewa su ba TRIPLETS bane, wancan ɗin ya saje da ɗayan.
Wani irin datse idanuwansa gam Lion ya yi da karfin gaske, tamkar zai fashe idanun nasu, karo na farko a rayuwarsa da ya fara danasanin gani abu, da ya sani, da bai kalli video nan ba, dan wlh ba zai taɓa yarda ace ɗaya daga cikinsu ba cikon TRIPLETS nasa bane, da bai kalla ba, da ya rufe maganar sun tafi a haka har su mutu, ba zai iya taɓa rabuwa da ko ɗaya daga cikin TRIPLETS nasa na yanzu ba, yau an zo gaɓar da ya kasa, ba zai iya ba. Toma a cikinsu wanenen jaririn da mutumin nan ya kawo? Kuma ina shi wanda aka ɗauka? Me aka yi da shi? Meyake faruwa ne? Josephine ta sadaukar da shi kenan? Ko yaya ne? Wanne ma wannan mutumin? Meyasa dukka hakan ta faru?. Wannan shi ne tashin hankali.
Cikin tsananin zafin rai Lion ɗin ya ɗauki laptop ɗin ya makata da jikin bangon ɗakin, ji kake yi war, ta tarwatse, dafe kansa dake yi mashi barazanar tarwatsewa ya yi, cikin fitar hayyaci ya miƙe tsaye, wani irin azababben jiri yake gani, duniya juya mashi take yi, gara ace mashi mutuwa ɗaya daga cikinsu ya yi da wannan bakin abin da ya gani, wlh sai dai ya rufe maganar nan, amma ba zai taɓa iya rabuwa da Areef ko Aseef, su ne bugawar zuciyarsa, shi kam ya yarda sune TRIPLETS na sa, a bar mashi su kawai........ Ba shakka da akwai ciwo na wuce misali a cikin rayuwar TRIPLETS tamkar yanda Malika ta gayawa Rimsha a baya, to a hankali dai ga shi abubuwa sai bayyana suke yi, mu je zuwa dai, ku kasance da PRINCESS TEEMA, dan ni kaɗai ce zan iya warware maku wannan babbar al'amari, kun dai ga abin da Dr William ya karyata na cewa bai san gwaggo ba, to ga gaskiya ta fito, ga komai kamar yanda gwaggon ta faɗa!! Lallai akwai wani abu wai shi ruɗanin kwakwalwa a cikin TRIPLETS!!.
Waje ya nufa, sam baya ganin gabansa, dan wani irin jiri da uban duhu da yake gani, ji yake tamkar zai haɗiye zuciya ya mutu kawai ya huta. Ɗakin gwaggo ya nufa, da hannu biyu dukka ya dafe kan nasa da ƙarfin gaske, yana tafiya yana huci tamkar ransa zai fita, iska mai tsananin zafi ce take fitowa daga bakinsa, ya ilahi ya lillahi!!.
Da sauri gwaggo ta mike tana tambayarsa lafiya. Ina ai bai kai ga karisowa in da take ba, ya zube kasa wanwar, baya numfashi!.
A dubu gwaggon ta kariso wajen da yake kwance, shi ma Aseef da yake kwance yana aikin zuba shagwaɓa, a ɗari ya sauko daga saman bed ɗin, bai ma san time ɗin da ya iso wajen ɗan uwan nasa ba.
Sunansa suka fara kira babu kama hannun yaro, ina ko motsawa bai yi ba, tamkar rai ne ya yi halinsa. Fridge Aseef ya nufa da sauri.
Ruwa mai bala'in sanyi ya ɗauko, tsabar shiga tashin hankali har kerma jikinsa yake yi, da kyar ya iya ɓalle bakin robar ruwan. Tashin hankali ya hana shi ma ya iya tarbo ruwan a hannunsa, da bakin rofar ya fara zazzagawa ɗan uwan nasa, ita kuma gwaggo, sai ambatar sunansa SAIF!! SAIF!! SAIF! take yi.
Tas Aseef ɗin ya zazzaga mashi ruwan, amma ina ko motsawa bai yi ba.
Ganin duk wannan uban ruwa mai bala'in sanyi da ya zuba mashi bai farka bane yasa ya zunduma uban ihu tare da fara jijjiga shi da karfi yana kiran sunansa da ya tashi, kada ya mutu ya barsu, ba zai iya rayuwa babu shi ba, dan Allah ya tashi.
Wannan ihun da ya zunduma ne yasa Uncle T ya shigo ɗakin a guje. Ganin abin da yake faruwa ne yasa ya kariso ciki da sauri. Sai kuka Aseef yake yi tamkar ransa zai fita, bawan Allah!.
Babu ɓata lokacin TGA ya naɗe hannun rigar jikinsa tare da sanya karfi ya saɓi Lion ɗin a kafaɗarsa, kai tsaye sai waje ya nufa. Da sauri suka rufa mashi baya.
Bai tsaya tambayarsu me ya faru ba, kawai ya sanya shi a cikin mota tare da bawa Mark umarnin a kan ya ja su zuwa asibiti. Kafin su gwaggon ma su iso harabar gidan, har Mark ya tashi motar. Gabaɗaya sojojin da suke gidan, kowa ya nufi sauran motocin dake cikin gidan dan su rufa masu baya.
Donal Aseef ya kira cikin kuka, ya ce mashi ya ɗauko mota su bi su TGA, sai ringin wayar Aseef ɗin take yi, amma ina hankalinsa baya a tattare da shi, kuma Areef ne yake kiransa, dan ya kira wayar Lion yafi sau a kirga, amma bai ɗauka ba, shi ne ya kira Aseef ɗin dan ya ji ko lafiya, saboda a jikinsa yana jin tamkar basu lafiya, kamar akwai wani abin. Amma ina Aseef ɗin ma yaki ɗaukar kiran, shi burinsa kawai Lion ya tashi....... MASU KARATU, WANNAN SHI NE ASALIN CAKWAKIYA, LITTAFIN TRIPLETS YANZU ZAI ƊAUKI ZAFI JAU KAMAR WUTA, KADA KU MANTA BOOK 4 MUKE, KUMA SHI NE LAST IN SHA ALLAH, TO MUNA FATAN AYI KOMAI A NAN A GAMA, HAR KULLUM PRINCESS TEEMA TAKU CE TA AMANA.💋
Gwaggo babu ko mayafi a kanta, daga ɗankwalin doguwar rigar jikinta, shikenan, haka ta bi su a motar Donal ɗin. Bayansu TGA suka bi, Uncle Herry kuwa, yana can yana kula da Dr William, bai ma san abin da yake faruwa ba, John da Jay kuwa basu ma a gidan gabaɗaya, sun tafi yawonsu!. Rimsha sarkin rigima, tana can tana barci ga Noorish nata tamkar rai ya yi halinsa!
WANNAN KENAN, ABIN DA YAKE FARUWA A GIDAN LION, BARI MU LEƘA GIDAN ABBO, WATO WAJENSU DR NAWID, WATA KILA KAFIN MU DAWO, ABUBUWA SUN ƊAN YI SANYI, GIDAN ABBA BA SAUKI, AYLA TA ƁATA, GIDAN LION KUMA YA MA KAMA DA WUTA BAL, BAL NE MA GABAƊAYA, SABODA BALA'IN TASHIN HANKALI DA SUKE A CIKI, TO BARI MU JI GIDAN ABBO KUMA KO DA ƊAN SAUKI SAUKI.
GIDAN ABBO.
Gabaɗaya familyn Abbo, wato Ummi, Dr Nawid da Aafia, suna a cikin tsananin tashin hankali, suna tsaka mai wuya, yau tsawon kwana uku kenan Dr Nawid yana kwance rai a hannun Allah, ko motsawa baya yi, ga idanuwansa a buɗe garau, amma baya iya ko motsawa, likitoci daban daban Ummi ta kira, amma kowa ya zo, sai ya ce babu wani abin da yake da munsa, su basu ga ciwon komai ba, ga shi Abbo dai baya nan, shiru babu shi babu labarinsa, haka Ummi ta daure ta fara shirye shiryen fitar da Nawid ɗin kasar waje.
Abin da ya faru shi ne, suna tsaye a kitchen suna aiki shi da Aafia, ranar bai je office ba, sai ya bita kitchen yana tanaya aiki kamar dai yanda suka saba, sai zuba soyayyarsu suke yi kamar ba gobe, bawan Allah lafiyarsa lou wlh, babu ko ciwon kai a tattare da shi. Haka kawai ya yanke jiki ya faɗi kasa, sai wani bakin ruwa ya fara fito mashi daga bakinsa, abin ya yi mugu mugun girgiza su Ummi, Aafia ba'a magana, ta yi mummunar rama yarinyar nan, dan kun sani, tun farkon littafin nan, tana bala'in son Dr Nawid, Ummi kuwa, shi kaɗai ne ke gareta, bayan shi bata da wani yaro, dole ta shiga tashin hankali na wuce misali, bayin Allah, wannan shi ne abin da ya faru.
Sai shirin fitar da shi kasar waje suke yi. Yau ta kasance ranar Friday, bayan an sauko daga sallar jumma'a, Aafia tana zaune a gefensa a saman bed nasu, ta yi mashi alwala dan ya yi sallah ko da da idanu ne, dama haka take yi mashi kullum, tana yi mashi alwala idan lokacin yin sallah ya yi, ita kuma Ummi bata nan, tana gidan Abbin Irfan, dan suma sun san abin da yake faruwa, Abbin ne ma yake shirya masu fita kasar waje dan neman lafiyar Nawid ɗin, so ta je su yi magana da Abbin.
Shiru Aafia ta zauna tana ta kallon mijin nata, shi kuma sai kallon sama yake yi, dan ko juya idanun nasa ma baya iya yi. Hawaye masu matuƙar zafi ne suke gangaro mata daga cikin idanunta, duk ta bushe ta yi wani irin baki tamkar mai cutar kanjamau, sai idanu kawai zaka gani dara dara a face nata, duk wanda ya ganta sai ya matsa mata kwallah.
Yau tsawon kwana uku Dr baya motsawa, ta yi nisa cikin tunanin da take yi, kamar daga sama ta ji voice nasa yana faɗin "Aafia ba zan tashi ba, mutuwa zan yi, ki yafe mani idan na taɓa yi maki wani laifi, sannan ki roka mani gafara a wajen Ummi, ta yafe mani, ina tsananin sonku, amma ba zan rayu da ku ba, sannan ki sani wannan cuta da ta kamani........" Bai kai karshen maganar ba ya sake yin shiru ɗiff tamkar an ɗauke wutar nepa.
Tun da ya fara magana, a tsakanin razane Aafia ɗin ta ɗago tana kallonsa, still idanuwansa suna kallon sama, sun kafe, bai iya motsasu, kuma bakinsa ma bata motsawa, kawai dai ga muryarsa nan tana fitowa ana magana da ita, amma sam sam babu wata gaɓa da ta motsa daga jikinsa!. Toh fa!!
Ta tsorata sosai na ganin hakan, sunansa ta fara kira, Yah Nawid, Yah Nawid, amma ina shiru bai amsa mata ba, tana ƙoƙarin ta sake yi mashi magana, sai ta ga idanuwansa sun sauya color izuwa purple eyes. Zaro idanu sosai waje ta yi, tamkar idanun nata za su fito su faɗi kasa, tana ƙoƙarin gudu ta sauka kasa, sai ta sake ganin idanun nasa sun sake sauyawa izuwa bakin kirin, babu ɗigon fari ko kaɗan a cikin idanun nasa, wani irin hayaki ne mai matukar warin gaske ya fara fitowa daga bakinsa, bakin ruwa mai kaurin gaske ya fara zuba mashi daga hancinsa, haka zalika kunnuwansa ma hayakin ne ya fara fitowa.
Wani irin uban ihu ta zunduma tare da sauka kasa da uban gudun gaske, a dubu ta nufi waje. Tamkar zararriya haka ta bazama izuwa harabar gidan, dai'dai lokacin kuma motar Ummi ya danno kai, ta dawo daga gidan Abbi, ta je ma bata samu ganawa da shi ba, saboda suna cikin tsananin tashin hankali na ɓatar Ayla, so suma yau ba'a zaune suke ba.
Ganin yanda Aafiar ta fito a gigice tana zunduma ihu ne yasa Ummi ta dakatar da motarta ba tare da ta karisa parking space na gidan ba. A hanzarce ta fito daga cikin motar, Aafia kuwa bata ma bi ta kanta ba, ta nufi waje da gudu, tamkar ƙwaƙwalwarta ya taɓu ne, da alama ta zauce.
A hanzarce Ummin ta ce mai gadi ya rufe gate ɗin, kada ya bari ta fita, sannan ta yi maza ta rikota tana ambatar sunanta, amma ina banda wannan ihu da take zunduma, babu wani abin da take yi.
Da kyar Ummin ta jata izuwa cikin palo, ɗaki ta sakata ta rufe kofa, sannan ta ɗauko wayarta, cikin tsananin tashin hankali ta kira Abbi dan ta sanar da shi abin da ta zo ta tarar a gidan again.
Ta yi sa'a ya ɗaga kiran, bayan ta gaya mashi, sai ya ce mata to Akil yana zuwa yanzu, daga haka suka yi sallama, sannan ta kira ƴan uwanta a Katsina ta gaya masu halin da yau kuma suke a ciki.
A palonta ta zauna, ta kasa shiga ta sake duba Aafiar, shi dama Dr Nawid bata san me yake faruwa da shi ba, bata san me Aafiar ta gani ta haukace haka ba, baiwar Allah, tana zaune ta buga uban takumi tana jin yanda Aafiar take yi mata watsi da kayan ɗaki har Akil ya kariso.
Tana ganinsa ta miƙe a hanzarce tana kara yi mashi bayanin abin da yake faruwa. Ina Aafiar ya tambaya, da sauri ta nuna mashi ɗakin da take, ba ɓata lokaci ya nufi cikin ɗakin.
Yana buɗe kofar Aafiar tana gefo mashi kwalbar perfume