Showing 150001 words to 153000 words out of 270744 words
daga azabar da Queen ta ɗanɗana masu ba, sai jinyar Dr Salman ake yi, ya sha allurai da karin ruwa tare da magunguna, shi ne yasa sam suka ki sanar da su halin da ake ciki.
❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉✷❉
Lion ya isa Washington lafiya lou masha Allah, gabaɗaya airport ɗin cike yake da jami'ai, ƴan jaridu da kuma ƴan siyasa, dan kowa so yake yi ya yi magana da Lion ɗin, a ƙage suke, dama idan baku manta ba, a yanzu almost tsawon 2 month kenan jama'a suna neman ganinsa ruwa a jallo ko da da ido ne kawai, ƴan jaridu suna haukar nemansa, dan su yi mashi tambayoyi, amma babu wanda ya iya samun damar ganinsa, sai yau da ya shigo kasar, da yake ba tafiyar sirri ya yi ba, shi ne yasa suka sami masaniya a kan dawowarsa tasa.
Shi kuwa ko a jikinsa, dan bai ga uban da ya isa ya sanya shi ya buɗe bakinsa ya yi magana bai yi niya ba, haka ya fito daga cikin jirgin yana takunsa na nuna isa da izza, duk ƴan jaridun babu wanda ya iya tunkararsa, saboda basu ga fuska ba, dama already fuskarsa a ɗaure tamau take kun sani, yau kuma ya kara tamketa babu alamar wasa a tattare da shi, hakan yasa kowa ya ji matukar tsoro da shakkar tunkararsa da wata magana. Duk sun tsaya cirko cirko kamar masu jiran sadaka. Suna ji suna gani har ya je ya shiga motar Areef dake jiransa su wuce. Ga Generals nasu na sojoji duk nemansa suke yi, yau ga shi sun gan shi ido da ido amma sun kasa iya tunkararsa.
Suna ji suna gani ya bar airport ɗin suka wuce gida, sai tsokanarsa Areef yake yi a kan wai ya je Nigeriar ya ci angwancinsa, ya tura yarinya doguwar suma ya dawo ya barta a wahale ko farfaɗowa bata yi ba. Ko sannu bai ce mashi ba, ya bar shi ne sai sun je gida ya shake shi da kyau, dan Areef yana takura mashi ba kaɗan ba, dole ya yi mashi koda shaƙa ɗaya ne wata kila zai bar shi ya sarara, tun da ya yi dis virgin ɗin Rimsha ya saka shi a gaba da tsokana, idan suka yi waya maganar kenan, dama da abin a ransa ya dawo, sai ya wahalar da Areef ɗin nan sosai wannan karon kam. (Ni ma dai na ce ya shake shi da kyau, Allah Areef akwai tsonana, ya saka mana Lion a gaba😂)
"Lion kaki ka bani labarin ya kaji ko? Serious dole na ɗauko my baby ni ma, dan naji me ka ji, saboda naga ka yi wani kyau ne". Yana magana yana kara gudun A.cn motar, cikin zolaya kuma ya yi maganar.
Banza da shi dai Lion ɗin ya yi bai tanka ba. Har suka isa gida sai tsokanarsa yake yi bai kula shi ba. Yana yin parking na motar a parking space na gidan, ya fito ya nufi ciki abinsa, dan aikin da ya kawosa ba karamar aiki bace ba, so baya bukatar ɓata lokaci koda second ɗaya ne.
Yana shiga palon sama suka yi four eyes da daddyn Rimsha dake zaune a saman sofa mai zaman mutun uku yana latsa waya. Already kunsan basu shiri kamar wuta da audiga, amma kuma ya iya zubawa ƴarsa soyayya ya ce kuma baya son ubanta. (Wlh Lion ɗan duniya ne, baya shiri da uba, amma kuma yana son ƴa, anya hakan zata yi wu kuwa?🤔)
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
Date: 9/5/2024
Kallo ɗaya ya yi wa daddyn ya kawar da kansa tare da wucewa ya nufi bedroom nasa. Shi ma daddyn bin shi da kallo kawai ya yi, Lion halisna sai shi, ba dai abin da ya canza a tattare da shi, Rimsha kawai ya canzawa, bayan ita kowa a yanda ya san shi yake ganinsa.
Yana shiga bedroom nasa wanka ya yi, kayan shan iska ya sanya a jikinsa tare da hayewa saman bed nasa ya kwanta, dan a tsananin gajiye yake sosai, ga uban tunanin Meesharsa da ya sako shi a gaba.
Shi kuwa Areef juya kan motar ya yi izuwa gidan Sheikh Sultan, dan dama ya ce yau zai je ya ɗauki Aseef ɗin, da izinin Allah ya sami lafiya sosai da sosai.
A ɓangaren Tga kuma, shopping nasa ya je ya yi abinsa, ba shi ya dawo gidan ba sai misalin karfe 11 na rana. Yana shigowa ya nufi bedroom nasa, har lokacin still Aafia bata motsa ba, shi sam ya mance ma da tana a cikin bedroom ɗin. Da ya ganta sai da ya ɗan yi mamakin mantawa da ita da ya yi, bai bi ta kanta ba ya wuce izuwa toilet, dan ya shirya abubuwan da ya sawo a mazauninsu.
Daya kammala wanka ya sake yi tare da shiryawa cikin wandon jeans three cuter baka, da T-shirt mai ɗan shara shara.
Fita ya yi daga bedroom ɗin ya nufi saman benen, ɗakin gwaggo ya nufa, a bakin kofa ya tsaya tare da yi mata excuse. Jim kaɗan ta fito. Cikin girmamawa ya gaishe da ita kafin ya faɗa mata abin da ya kawosa na ya buge wata yarinya da mota ne a daren jiya, kuma yaga yarinyar tana kama da su Imran, ta zo ta ganta ko ƴar uwarsu ce.
Da yake tasan da batun ɓacewar Aafia ɗin, sai bata ɓata lokaci ba wajen ce mashi "Tabbas Aafia ce ma In Sha Allah, mu je bari na ganta".
Wucewa gaba ya yi ya sauke kasa. A hanzarce ta bi bayansa, kai tsaye bedroom ɗin nasa suka nufa.
Tana ɗaura idanu a kanta ta ce "Dama na ce ita ce, tun daren jiya muke nemanta, bari na kira su Deen ɗin a waya mun sameta, sai wahala suke ta sha, ashe gata a gida ma". Ta kai karshen maganar tare da kai hannunta a saman kumatun Aafia ɗin.
"Meyasa me ta? Suma ta yi ne?". Ta tambaye shi.
"Na yi mata alluran barci ne tun daren jiya ɗin, amma kuma yakamata ace alluran ya saketa izuwa yanzu ai".
Kai kallonta a kan in da ya sanya mata bandeji da plaster bayan ya wanke wajen ta yi, kamar zata yi magana, sai kuma ta fasa tare da juyawa ta nufi waje. Bedroom nata ta koma ta ɗauko wayarta. Number Abbi ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a hanzarce ta sanar da shi cewa ga Aafia nan a gida Tga ya bugeta da mota. Murna sosai suka yi da Allah yasa tana gidan, sai dai kuma sun shiga damuwa ta wani ɓangaren a kan bugeta da motar da aka yi, ba ɓata lokacin Abbin ya tambaya ta ji ciwo ne?.
"E ta ji ciwo amma kaɗan ne, kuma a iya kai ne kawai". Gwaggon ta bashi amsa. "Okey tom bari na sanar da su Abba, gani nan zuwa gidan yanzu". Okey ta amsa mashi da shi, sannan suka yi sallama. Fitowa ta sake yi ta koma bedroom ɗin na Tga.
Tana zuwa ta ce mashi ya kai mata Aafiar ɗakinta, iyayenta suna zuwa yanzu, zata cigaba da jinyarta a can, sun gode da taimakon da ya yi mata.
Gwaggo ta tara majinyata kam, ga Rimsha, ga Jehan, yanzu kuma Aafia, ɗakinta ya koma kamar clinic.
Ba ɓata lokaci ya ɗauketa zuwa ɗakin gwaggon kamar yanda ta buƙata, sannan ya dawo ya cire bed sheet dake shunfuɗe a saman bed ɗin nasa, ya canza wata.
Ita kuma gwaggo kula da Aafiar ta cigaba da yi har Abbi da Abba suka ƙariso cikin gidan. Sai a lokacin ne Brr Naurat ta sami labarin abin da ya faru, jajanta masu ta yi, sannan ta ce to a bar Aafia ɗin a wajen gwaggon ta cigaba da kula da ita. Haka kuwa aka yi, duk suka amince, sannan suka koma gidajensu, kwananta biyu a wannan suma da ta yi Allah yasa ta farfaɗo tare da taimakon gwaggon, sun kuma yi sa'a ta farfaɗo lafiya lou ba tare da buguwar da ta yi a kai ya taɓa mata ƙwaƙwalwa ba, sun yi sa'a sosai.
Sai kula da su gwaggon take yi, bata da wata nutsuwa sosai a tattare da ita, Rimsha kam har yanzu tana a bedroom na mijinta.
After some days.
Washington. Sun yi primary election lafiya ba tare da wata tangarɗa ba, Lion shi ne na farkon ma, shi ne a sahun gaba na cin primary election ɗin, dan jama'a suna yinsa ba karya, kowa yana son mutumin kirki mai adalci ai dama, abin ya kara razana mutane sosai, ya tada tarzoma a majalisan dattawa, tashin hankalin da His excellence ya shiga ma baki ba zai iya faɗarta ba, shi kuwa Lion tamkar bai san meyake faruwa bama, yana gida tare da ƴan uwansa hankalinsu a kwance, sai tunanin Meesharsa da yake yi, yana tsananin kewarta sosai, ji yake yi ba zai iya zama ba tare da ita a kusa da shi ba, ga wani azababben sha'awarta da take takura mashi kwana biyun nan, komai yake yi ita ce a cikin tunaninsa, zazzaƙar zumarta ya tsaya mashi a rai over. Da yake Areef ya san komai, sai ya yi ta tsokanarsa.
Yau ma dai yana zaune a saman luntsumemiyar sofarsa mai zaman mutun uku dake wajen balcony, sanye yake da pajama launin milk color mai matuƙar kyau da tsada, tsadaddiyar sabuwar laptop nasa ne a gabansa, aiki yake yi a azahiri, amma a baɗini ba aikin yake yi ba, ya yi shiru yana tunaninta ne kawai, hankalinsa sam baya a kan laptop ɗin, da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan yana cikin matsananciyar azababbiyar sha'awa, waɗan nan fararen idanuwan nasa sun sauya launi izuwa jajir, kwayar idanuwansa har wani kara blue suka yi, sai kyalli idanun nasa suke yi, alama ce dake nuna a hannu yake, ga shi kuma yau tsawon kwana 29 kenan Rimshar bata farka bama bare kuma su san tana lafiya ko dai kwakwalwarta ta taɓu, tun abin baya damun gwaggo sosai har ya zo ya fara damunta, har ƴar rama ta yi, ita kanta mummyn Rimshar ta rame sosai, bata fito ta nuna damuwarta a fili ba, amma kullum ta shiga cikin ɗaki sai ta yi wa ƴar tata kuka, abin ya tsaya mata a rai, ta tausayawa ƴaƴan nan nata kamar me, babban damuwarta ɗaya shi ne, kada ace Rimsha mutuwa ta yi, ƴaƴa biyu kawai Allah ya bar mata, ya karɓi sauran dukka, tana son ƴaƴan nan kamar ta yi masu numfashi, musamman Rimsha da suka fi shakuwa da ita, idan ta mutu ya zata yi? Ina zata sanya ranta? Ga shi bata zuwa duba Rimshar sosai, a rana sau ɗaya take zuwa, saboda Rimshar tana bedroom na Lion ɗin ne, ita mummyn bata son shiga bedroom na sirikin nata, kuma bugu da kari bata son ganin ƴar tata cikin halin doguwar sumar ne, hankalinta yana tashi matuƙa, ga shi daddy baya nan bare ya rinƙa kwantar mata da hankali, abin ya yi mata yawa sosai, shiyasa har rama sai da ta yi, da Allah yasa ma ciwo bai kayar da ita ba, haka ita ma gwaggon, tsoronta ɗaya kada ace Rimsha mutuwa zata yi, ba zata iya jurar hakan ba, abin ya ɗaga mata hankali da har ta sa a ranta idan su Areef suka dawo a gaskiya sai ta ja masu kunne sosai a kan su Jehan, su bi komai a sannu, su Jehan yarana, dan Allah su rufa mata asiri su taimaketa su taimaki mum su yi masu komai a sannu. (Gwaggo ta ji papper😂 dole baiwar Allah ta ce su Areef subi komai a sannu😂 waye ya ce mata Borno a gabas take?)
Baki ɗauke da sallama Areef ya shigo cikin balcony ɗin, jikinsa na sanye da three cuter sky blue, daga ta sama kuma farar singlet ce a jikin nasa, sai zuba uban kamshi yake yi, hannunsa na ruke da wani kyakkyawan cup mai ɗauke da green tea, sai tiririn hayaki yake yi, ya saki gashi har baya, kyawawan fararen kafafunsa na sanye cikin bedroom slippers masu matuƙar laushi kamar audiga, ga kyau farare tas da su, kusan iri ɗaya ne da na kafar Lion ɗin, sai dai na Lion up white ce.
Kusa da shi ya zo ya zauna yana faɗin "Our Lion good evening". Yadda ya yi maganar cike da nuna tsantsar so da kauna. Sam Lion ɗin bai kula shi ba, dan shi kaɗai yasan meyake ji.
Areef ɗin zai sake yin magana sai ga Aseef ya shigo hannunsa rike da waya ya manna a kunne, ɗayar hannunsa na ruke da cup irin na hannun Areef, jikinsa na sanye da short zuwa iya santala santalan cinyoyinsa, daga ta sama babu riga, dukkansu sun kara wani irin kyau na musamman, bare ma shi Aseef da dama ya fisu samun hutu, su suna ta busy game da Election, shi kuwa kome za'ayi yana kwance a gida manne da waya, baya leƙa ko palon kasa, hakan tasa ya fisu hutu, jikinsa ya fi nasu fito da wata sihirtatcen kyau na daban. (Yo dama Aseef ai sai dai ya kwanta ya mannewa wayar😂 ina zai iya yin minti 30 bai ji muryar Heartbeat ba? Ai ko sun saka shi aiki ma ba zai yi ba😂 jibge masu kayansu zai yi, dan shi dai iya wuya Heartbeat kawai😂)
A ɗayar gefen Lion ɗin ya zo ya zauna, ya zama sun saka Lion ɗin a tsakiya.
"Heartbeat Allah ni ba zan yarda ba, kawai video call nake so". Cewar Aseef. Ya faɗa yana ajiye cup ɗin hannun nasa a saman table dake gaban Lion wanda ya ɗaura laptop nasa.
Harararsa Areef ya yi yana faɗin "Allah ya nuna mani ranar da Aseef da Akila zasu canza hali". (Ni kuwa na ce nima ina jiran wannan rana,😂 su sam basu da wani aikin yi sai kashe juna da love da shagwaɓa, ko gajiya ma basu yi?🤔😂)
Da yake ya saba da abin ta bi jininsa, ko da aka yi mashi magani ƙwaƙwalwarsa ta warke garau shagwaɓar bata rabu da shi ba, kun san sabo, ya rigada ya saba, kuma haɗuwa da Akila yasa shagwaɓar tasa ta yi yawa, saboda shagwaɓarta da take zuba mashi yana biye mata yasa shi ma nasa ta karu sosai, da ace bata da shagwaɓa, da nasa ba zata kai haka ba, kuma da izuwa yanzu ya dai'na yinta ma, amma da yake ita shugaba ce, sai ta kara shagwaɓa shi kawai abinta.
Shi dai Lion ko sannu bai ce masu ba. Akilar ce ta cikin wayar ta ce "Heartbeat yanaji kamar maganar Yah Areef?".
"Shi ne mana". Ya bata amsa. "Yanzu a gabansa muke dukka wannan hiran dama?". Ta faɗa tana zaro idanu, tana daga kwance a saman bed na bedroom nasu.
"No yanzu na shigo wajensu, to idan ma a gabansu ne sai me? Ina ruwansu da mu?".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "A'a ni ina jin kunyarsu". "Ke gara ma ki dai'na wannan shirmen, su basu san wannan ba". Ya faɗa yana kwanto da kansa a jikin Lion.
Hannu Lion ɗin ya kai yana shaga face ɗin Aseef ɗin cike da tsantsar so da kauna, waɗan nan bayin Allah baki ya yi kaɗan wajen bayyana yadda suka kaunar junansu. Cigaba da zuba hirarsa Aseef ɗin ya yi, ba ko kunya yake zuba kalaman da ya ga dama, idan ta ce mashi ita yana bata kunya, sai ya ce mata yanzu dai shi mijinta ne, idan a da time da take gida tana taka mashi burki a kan wasu kalai, saboda basu yi aure ba, to yanzu dai hakura zata yi ta barshi ya zuba kalamansa son ransa, dan yanzu mallakinsa ce ita ɗin, ko hoto ba kaya ya ce ta yi mashi dole ta yi ta tura mashi, dan haka shi ta kyale shi ya ji da abin da ma yake ji na kewarta.
Areef kam dariya kamar ya mutu, saboda yadda Aseef da Lion ɗin dukka suka zama wasu jugum jugum kamar wasu marayu, duk saboda kewa da kuma sha'awar matansu, yana son ya tsokanesu, amma yana tsoro, dan a yadda suke ɗin nan, idan ya taɓosu lallasa mashi jiki zasu yi son ransu, haɗuwa zasu yi su bashi a jikinsa, so is better for him da ya ja bakinsa ya rufawa kansa asiri ya yi shiru. Sai dai shi ma fa yana jin azababben kewar babyn tasa, abin da yasa shi ta shi tafi yi mashi sauki shi ne, na farko kun dai san bai saba kwana da Jehan ɗaki ɗaya ba, na biyu bai saba wasanni da ita ba, kullum cikin dirama suke, na uku dama ko ya kirata a waya ba wasu kalamai na soyayya take gaya mashi ba, so bai wani saba ba, shiyasa abin bai taɓa shi sosai kamar su ba.
Shi kuma Aseef ba sai na faɗa ba, kun san ya fi kowa tsotsewa Heartbeat baki da tula tulanta, ya fi su dukkansu murzar matar tasa son ransa, kullum suna manne da juna, ɗaki ɗaya suke kwana, shi ne yasa abin ya taɓa