Showing 15001 words to 18000 words out of 270744 words
ko'ina da kallo, ta kasa nutsuwa waje guda, gani take yi tamkar Dr William zai cutar da ita ne a irin wannan gida, ta tsorata da ganin wannan uban daular more rayuwar.
Shi kuwa, riko hannunta ya yi suka nufi saman wata luntsumemiyar sofa mai matuƙar laushi da kyau, fara kal tamkar yanzu aka cirota daga kwalinta. Komai na cikin palon sai kyalli yake yi, yana ɗaukar idanu, gal gal da su, nera ta yi kuka ta kuma zauna da kyau a wajen.
Ko da suka shigo palon, sam iyayen Dr basu nuna mata komai ba, sai ma karramata da suka yi, da fara'a mummynsu ta tarbeta, shi ma daddyn nasu, fuska ba yabo ba fallasa ya tarbesu, dan gwaggo dai baturiya ce ba bakar fata ba, sak Naurat take!. Josephine ta fi kowa murnar ganin gwaggo, saboda dama yayan nata yana yawan korinta a kusa da shi, a tunaninta tun da yanzu ya fara son mata, zai dai'na abin da yake yi mata. Su Uncle Herry duk sun yi tsantsar murna ba kaɗan ba.
Sam Dr William bai ɓata lokacin wajen sanar da iyayensa wace ce gwaggo a wajensa ba. A nan ne tsananin farincikinsu ya kara bayyana, sun ji daɗi sosai da ɗansu ya kawo macen da zai aura, nan take mum nasu ta ce gwaggo ta dawo kusa da ita ta zauna, tamkar za su cinyeta saboda so, sai tambayarta suke yi me take so ci a kawo mata?!.
Kan ka ce me an cike mata gabanta da lodin kayan cima kala kala, masu aiki sun fara zarya a cikin palon, suna kai kawo na kayan cima. Yau dai Gwaggo taga abin mamaki, abincin ma a baki suke ƙoƙarin tura mata, saboda so, kuma duk aikin mum ce, sai wani ririta take yi.
Ta ɗebo abinci a cikin spoon zata kaiwa gwaggon a baki kenan, cikin hanzari Dr ya ce "Mum kada ki bata, dan ita bata cin irin abincin mu, ba komai take ci ba!".
Ɗan zaro blue eyes nata mum ɗin ta yi kafin ta ce "Why?". Ko a jikinsa ya amsa mata da cewa "Be cause she is a Muslim, so ba komai take ci ba, akwai abin da ya zamana haramun a cikin addininsu su ci, haka idan muka je restaurant cin abinci ma, sai ta faɗi abin da za'a bata, bata cin irin nawa!". BABBAR MAGANA.
A tsananin razane mum da dad ɗin dukka suka mike tsaye, tamkar sun ga wani abin tsoro. Nan take kuma suka canza fuska tamkar ba su ne suke dariya a yanzu ba, sun wani uban ɗaure fuska tamkar hadari, shi daddy ma har da wani zaro idanu. Cikin tsawa mum ɗin ta ce "To musulmar zaka aura ne?!".
Sosai gwaggo ta yi wani mahaukacin razana!, Ta tsorata na ganin canjin da suka yi lokaci guda, tamkar ba su ba.
Shi kuwa Dr, ko a jikinsa ya amsa musu da "Yeah mum, ita nake so, ita zan aura, kuma yanzu ma da muka zo, na zo ne na gaya muku zan musulta nima, be cause we're prepared to get a marriage together, so shi ne abin da ya kawo ni!". TASHIN SENSE!!!
Wani uban tsawa dad ya daka musu wanda ya sanya gwaggon mikewa da sauri. Shi ma Dr William mikewa ya yi tare da yi mata alama da hannunsa a kan ta zo. Da sauri ta tafi izuwa wajensa, jikinta sai kerma yake yi. Dr kuwa ko a jikinsa ya rumgumeta yana ɗan shafa bayanta, alamar ta kwantar da hankalinta.
Mum ce ta katsesu da cewa ya sake wannan yarinya ko kuma wlh yanzu ransa ya ɓaci. A zahirin gaskiya tun da yake da iyayensa basu taɓa ɗaga mashi murya a magana bama bare har a kai ga tsawa, lalaɓa shi suke yi sosai kullum. Hakan tasa ya ji wlh yana kaunar shiga musulci, dan shi duk abin da ba'a so, to fa shi yake so. (Idan baku manta ba a baya dama Dr William ɗin ya faɗa, wannan kalma ta abin da ba'a so, shi Lion yake so, a wajensa ya gaji kalma, to hakan take!.)
"Mum why are you shouting like that? You already know that idan na ce zan yi abu fa, to sai na yi, so don't west your time to say something about that issue, be cause confirm sai na musulta, dan ina son A'isha, she is my life, my everything!!". BABBAR MAGANA!! YAU AKE YINTA!!
"William are you out of your sense?!" Cewar mum ɗin. Dad ne ya karɓi maganar da cewa "In dai har ka ce zaka musulta, to confirm zaka bar mani gidana! Kuma sai dai ka mance da mu a matsayin iyaye, ka nemi wasu!!".
A takaice ya ce "That's good daddy, i chose A'isha and Muslim religion, wai daddy ka manta abin da ba'a so shi nake so ne? To ko dan nunawa da kuka yi baku so, confirm sai na yi!!".
Ya kai karshen maganar tare da juyawa tare da gwaggon a jikinsa. "William don't go anywhere, come back and say sorry to your dad!". Cewar mum, ta yi maganar tamkar zata fashe da kuka, idanuwanta duk sun cika taf da kwallah, Allah ya gani a duk cikin ƴaƴanta, ta fi son Dr William, kuma ta san halinsa sosai, tun da ya ce sai ya musulunta, to fa babu chanji sai ya yi ne, sai dai duk abin da zai faru ya faru. TIRKA SHI.
A ɓangaren shi ma daddyn, kirjinsa sai dukan uku uku yake yi, dan shi ma, ya fi son Dr William sama da kowa a cikin ƴaƴansa, ba zai iya rabuwa da shi ba, ba kuma zai iya ganinsa a cikin addinin musulunci ba, dan su irin kristocin nan ne masu tsauri a kan addininsu, ba za su iya yafe ɗansu ya musulunta ba! Gara su kashe shi da su barshi ya musulta.
Hakan tasa daddyn zuciya ta ɗebe shi ya yi yunkurin kashe gwaggo da wukar da mum take yanka ganyayyakin da take ci. Cikin ɓacin rai Dr William ya tare daddyn nasa, tare da kwace wukar, har ya ɗaga a zuciye zai cakawa daddyn nasu a ciki, gwaggon ta rike shi tana kuka tare da girgiza mashi kai a kan kada ya yi hakan, kada ya kashe daddynsa.
Wurgi ya yi da wukar tare da rungumeta suka nufi waje. Dafe saitin zuciyarsa dad ɗin ya yi, kan su yi wani yunkuri ya zube kasa sumamme, abin ya taɓa mishi zuciya over, kuma dama dole ya taɓa shi over, ace ɗa mafi soyuwa a gareka, ka fifita shi fiye da kowa, ka shagwaɓa shi, rana tsaka wata mace ta shiga tsakaninku, har yaron ya yi yunkurin kashe ka, saboda mace, ba dan macen da yake son ɗin ta rike shi ba, da tsab zai iya kashe ka saboda zuciya ta ɗebe shi, dole wannan abin ya taɓasu over, dan zuciyar iyaye ya wuci tunanin mutun, in ma musulmi ko Kristen, duk wanda aka ce shi ya haifi mutun, to wlh ya wuce abin wasa, zai so ɗan nan ne fiye da tunanin mai tunani, koda kuwa ba zai nunawa kowa ba, ba zai taɓa yuwuwa ace iyayen da suka haifeka ba su sonka ba, sai dai idan ba zasu nuna maka son ba, amma zuciyar iyaye daban yake da kowa, suna iya sadaukar da duk abin da suka mallaka saboda ƴaƴansu, ba'a banza da Allah ya ce bayan Allah da Manzonsa sai iyaye ne kawai za'ayi wa biyayya a shiga aljanna kai tsaye ba, so iyaye sun wuci wasa koma ya ya suke!! Fatanmu dai Allah Ubangijin ya bamu ikon bin umarninsu tare da kyautata musu!!.
Ko kaɗan Dr William bai juyo ba, duk da yana jin zafin rabuwarsa da iyayen nasa, amma hakan bai hana shi dagewa dan cika burkinsa ba. Ficewa ya yi daga gidan abinsa.
Shi kuma dad su Uncle Herry suka yi ƙoƙari tare da taimakon ma'aikatan gidan, suka nufi hospital da shi.
Ko awa ɗaya bai yi a asibiti ba rai ya yi halinsa, dama already yana da hawan jini, sara ce ta zo a kan gaɓa. Mutuwarsa ta sanya mum nasu shiga tsananin tashin hankali, wanda har sai da ya jawo mata bugawar zuciya, ita ma ba'afi awa uku da mutuwar dad ba rai ya yi halinsa, ta bi daddyn.
Hakika familyn Roshan su ga tashin hankali a wannan rana, harta yayyun daddyn da suke rike da mulki, a wannan rana sun sha kuka, an yi musu hotuna da videos suna kuka da hawayensu na rashin kaninsu da matarsa tamkar wasu yara ba adadi.
Sam Uncle Herry da Josephine sun ki gayawa jama'a gaskiyar abin da ya kashe Jacob da mum nasu, sun ɓoye ne saboda suna tsananin son Dr William, kuma suma sun ji suna son su musulta, sun san cewa idan har suka sanar da jama'a gaskiya, to ba shakka yayan daddy da yake kan mulki zai sanya a kashe Dr William, dan su basu yafe jininsu, ko yaya ka taɓosu sai sun rama, koda kuwa a cikinsu kake.
A lokacin da za'ayi jana'izarsu su mum, za'a kaisu mutuware, wato jana'izar kiristoci, an buƙaci da Dr William ya zo ya wuce gaba a matsayinsa na babban ɗansu, amma sam baya wajen, hasalima bai san da zancen mutuwar ba, duk da cewa labarin ya baza gari, abin ku da manyan mutane, sai dai shi bai sami labari ba, dan yana babbar masallaci jumma'ar musulmai dake garin, tun da ya bar gidan suka wuce can da gwaggon, kafin ya tafi kuma sai da ya kashe wayarsa, a cewarsa kada ma su mum ɗin su kira shi, dan confirm sai ya musulunta. TASHIN SENSE.
Kasancewar ba'a sami Dr William ko a waya ba, haka aka ce Uncle Herry ya wuce gaba, Josephine ta bi bayansa, dan da aka tambayesu ina Dr William, sai suka cewa jama'a ai Dr William baya nan, sun dai ki faɗar gaskiya. Haka aka kai gawarwakinsu mum ɗin mutuware, sai kuka su Josephine ɗin suke yi tamkar ransu zai fita.
A ɓangaren Dr William kuwa, suna fita Masallaci ya wuce da gwaggon, a in da ya je ya gayawa liman ga abin da yake tafe da su, ya gaya mashi aure suke son yi, kuma iyayensu basu son aure, saboda iyayensa sun ce a'a, kuma sun hana shi musulta.
Duba da yanayin kasar tasu, ba musu limamin ya bashi kalmar shahada tare da tambayar gwaggo shin da gaske tana son Dr William, sosai ta tabbatar musu da hakan, ba ɓata lokacin limamin ya ɗaura musu aure bayan an fito sallar azzahar, a cewarsa, ai sun fi shekaru goma sha takwas, dan haka suna da ƴanci da kansu, suna da ƴanci su yi abin da suka ga dama, shi ne yasa aka ɗaura musu aure bayan musultar Dr.
Ita kuma gwaggon a lokacin idanunta sun rufe, tana ganin kamar iyayen Dr William za su zo su rabata da shi, ba zata iya rayuwa babu shi ba, shi ne kawai yasa duk abin da liman ya ce mata, sai ta ce mishi e, dan a lokacin bata da burin da ya wuce Dr William ya musulunta, a ɗaura musu aure, su mallaki juna, shi ne yasa ta yarda, bata bi ta kan iyayenta ba, dan tana ganin suma zasu tsaya ɓata mata lokaci ne har a rabata da Dr.
Bayan an ɗaura musu aure, kai tsaye gidan Gwaggon suka wuce abinsu, yau sun zama sabbin mutane. Ko da suka je gidan, komai na kayan kallo a kashe, basu sami labarin abin da yake wakana a gari ba. Rungume juna suka yi suna tsananin murna da farinciki, yau sun mallaki juna na har abada.
Kissing nata ya fara yi, cike da so da kauna ta fara mayar mishi da martani. Sun ɗan yi nisa cikin abin da suke yi, tamkar wanda aka muskula ta miƙe tana faɗin "My Dr bari na kira mum ɗina na gaya mata yanda aka yi komai, dan kada asamu matsala ka ji?".
Idanuwansa a runtse ya jawota jikinsa yana faɗin "A'a kada ki gaya musu yanzu, kada suma su rabani da ke, ki bari sai mun sami hutu a school, sai mu je gidan a tare ko?".
Jinjina mashi kai ta yi cike da gamsuwa da kuma yarda da shi ɗari bisa ɗari, dan ta faɗa makauniyar soyayya, baiwar Allah, ba laifinta bane, laifin so ne, da bashi da adalci idan ya shiga mutun.
"My Dr ka bari, bari na je nayi wanka nazo ko?". A kunne ya raɗa mata yau kam a tare za su yi. Bata yi mashi musu ba, dan sun mallaki juna, kafin su mallaki juna ma, dama wani lokaci ko tana toilet yana shiga ya yi abin da zai yi, bare kuma yanzu, ai sai abin da hali ya yi.
A tare suka wuce cikin toilet ɗin. After some minutes suka fito rungume da juna, tamkar wani ya ce zai kwace musu junansu. Yau dai a tare suka yi komai, kama daga shafa lotions, shiryawa cikin kananan kaya, da yake da akwai kayansa sosai a gidan, dan idan baku manta ba, wani lokaci a gidan nata yake kwana a baya, hakan tasa ya sayi wasu kaya ya zuba a dressing room nata. Komai suke yi suna yi ne suna wasan masoya cike da so da kauna.
Da zata shiga kitchen ma, a tare suka shiga da shi. Duk da cewa bai iya aikin komai na kitchen ba, amma ya tayata da hira na kalaman soyayya masu daɗi, tare kuma da tana aiki yana rungumeta, ko ya shafi mazaunanta. Kayan kwalama ta haɗa musu tare da green tea mai zafi sosai.
A palo suka baje abinsu, a lokacin kuma har an kaisu Jacob mutuware an dawo, duk basu da labari. Sai da suka fara shan tea ne ta ɗauko wayarta tare da kunna data dan ta yi wa Cherish massage a Whatsapp na yau sun yi aure da Dr, sun mallaki juna, ta zo ta tayata murna.
Tana kunna data sakon Cherish ɗin ya shigo wayar nata na tayata alhinin rasa iyayen saurayin nata Dr William wanda yake a matsayin mijinta a yanzu kenan. Wani irin ihu ta kurma wanda bata san time ɗin da ya fito daga bakinta ba, jikinta na kakkarwa ta yasar da wayar kasa.
Cikin tashin hankali ya riko kafaɗunta yana tambayarta lafiya? Ihun me take yi. Kasa magana ta yi, nan take hawaye suka cika mata idanuwa, domin tasan Cherish ba zata taɓa yi mata karya ba, tun da ta yi mata wannan massage ɗin, to gaskiya ne, iyayen Dr William sun mutu. TASHIN SENSE!!!.
Ganin taki amsa mishi tambayar da yake yi mata ne, yasa ya ɗauki wayar tata dan ya duba me ta gani take wannan ihu. Dubawa da zai yi bai san time da ya saketa ya wani irin mikewa a razane ba.
Ita ma mikewa ta yi tana hawaye jikinta duk sai ɓari yake yi, abin mamaki yanzu bai fi awa biyar da suka rabu da su ba, amma ace sun mutu dukkansu biyu? Wannan dole bawa ya shiga tsananin tashin hankali.
A hanzarce Dr ya wuce ya ɗauko wayarsa, cikin tashin hankali, idanuwansa suna gani bibbiyu, ya fara ƙoƙarin kunna wayar. Ya kasa saboda kerma da jikinsa yake yi, wayar ta kasa tsayuwa waje guda a hannun nasa.
Daga karshe ita ta karɓa ta kunna mashi. Number uncle Herry ya fara kira, bugu ɗaya ya ɗauka. Cikin tsananin tashin hankali da razana ya fara magana yana haɗe word, a in da ya tambayi uncle Herryn ɗin ina dad da mum.
Ba ɓoye ɓoye ya gaya mashi sun mutu. Ya ilahi ya lillahi, bai san time ɗin da ya saki wayar tasa ta faɗi kasa ba. Kasa tsayuwa waje guda ya yi a in da ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen, yana wani irin numfashi mai kama da gurnanin zaki.
Tsugunnawa ta yi a kusa da shi tare da ɗan rungumo shi a jikinta, sai ruwan hawaye take yi. Muryarsa tamkar mara lafiyar da ya yi shekara cikin mawuyacin hali ya ce mata. "My.....my beauty.... Don't tell me that what i heard now about my dad and mum is true, say it's not a true to me".
Rarrashinsa ta fara yi tare da kara mashi karfin gwiwa. Ina ai kasa hakura ya yi, zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba, idanuwansa sun yi jajir da su. Ta yi ta yi a kan ya tashi su je gidan, amma ina ya kasa koda motsawa, dan yana bala'in kaunar iyayen nasa fiye da tunanin mai tunani, sune duniyarsa, duk abin da yake yi musun nan yana tsananin sonsu, ace lokacin guda ya rasasu? Kai abu ne wanda zuciyarsa ba zata iya ɗauka lokaci guda ba, dan ma dai yana da taurin zuciyar ce, ai da abin ya wuce hakan.
Sai da ya ɗauki almost 1 hour a durkushe a wajen, sannan ne ya iya ɗan motsawa. Da kyar ya mike. Da dafa bango ya fito palo. Da sauri ta ɗauki bakullin mota ta biyo bayansa.
A takaice ita ta ja motar suka nufi gidan. Har lokacin jama'a na cike taf a gidan. Bai kula kowa ba ya wuce ciki, yana tafiya tamkar zai faɗi kasa, ya rike hannun gwaggo gam dan kada jama'a su rabasu, ta je ta ɓace mashi kuma.
Kai tsaye hawa na biyu suka wuce, a nan suka sami su uncle Herry da su yayyun dad ɗin nasu, sun sha kuka tamkar ba gobe, shi kuwa Dr William ya daure, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta, amma sam bai yi kwallah ba.
Sai bayan sati biyu da mutuwar iyayen nasu ne ya fara gane kansa, nan ma da taimakon gwaggo da take kwantar mashi da hankali, ba karya ya shiga tsananin damuwa da tashin hankali na wuce misali, har wata iriyar mummunar rama ya yi, tamkar ba shi ba, iyaye ba wasa ba! Kuma dukkansu a lokacin guda, a hakan ma su Uncle Herry basu gaya mashi cewa sanadiyarsa ne yasa hawan jinin dad ɗin nasu ya tashi har ya mutu ba, sun ɓoye mashi, wata kila da sun gaya mashi shi ne sula, tashin hankali ne shi ma zai kashe shi.
Haka suka kasance a daddafe har tsawon wata da rasuwar iyayen nasu, sannan ne ya ce shi ba zai iya zama a wannan