Showing 249001 words to 252000 words out of 270744 words

Chapter 84 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2994

riga shi ne, wanda ake haifarsa yana zuwa da wani abu mai kamar yana da yake rufe mashi fuska, wanda idan ba'ayi saurin cirewa ba yana kashe yaro nan take, dan yana tare mashi numfashi ya hanasa yi, hakan ce tasa Lion ɗin ya ɗauke shi cikin jinin ya yi saurin yage abin ya cire.

Da gudun gaske Rimsha ta shigo cikin ɗakin, kan Jehan ɗin ta ƙariso tana ambatar sunanta da karfi.

"Get out Meesha". Shi ne abin da Lion ɗin ya ce da ita yana ƙoƙarin janyo duv dake saman bed ɗin dan ya kwantar da babyn dake hannunsa.

Kasa fita waje ta yi, sai ma kara matsowa da ta yi tana ƙoƙarin riko Jehan ɗin.

Wani irin nishi Jehan ɗin ta sake yi tare da riƙo wuyar rigar Lion ɗin, dan ya fi kusa da ita a kan Rimshar, Rimsha tana ta gefenta ne, shi kuma yana tsungunne ne a ta gabanta in da ya ɗauki baby, hakan yasa da azaba ta yi azaba bata san lokacin da ta damko wuyar rigarsa tana sakin wani irin numfashi mai matuƙar razanarwa ba, tamkar mutuwa zata yi, baiwar Allah.

Cikin zafin nama Lion ɗin ya janyon duv ɗin a dubu ya kwnatar da babyn tare da kai hannunsa dukka biyu ya riƙo shoulders ɗin Jehan ɗin yana mai dakawa Rimsha tsawa a kan ta fita a ɗakin kamar yadda ya faɗa mata tun farko.

Wannan tsawa da ya daka mata ya yi dai'dai da faɗowar baby a karo na biyu, ita kuma Rimshar tsabar tsorata da tsawar, sam bata san lokacin da ta kwasa a guje ta bar room ɗin ba, daga ita sai towel a kirji.

Yau dai Lion da baya kaunar yara a rayuwarsa, saboda kaunar Areef da yake yi tasa ya karɓi haihuwar Jehan da kansa, shi da ya ce ko kallon yaran baya son yi, sai ga shi da Allah ya tashi kamasa a hannunsa aka haifo yaran Areef, daga karshe ma gabaɗaya jikinsa ta yi dama dama ta yi wanka da jini, dan kuwa ba ƙaramar damka Jehan ta rinƙa yi mashi ba, saboda azaba, babynta na uku dana huɗu kam ma kusan a jikin Lion ɗin ta haifosu, duk ta fita daga cikin hayyacinta, hasalima bata san waye ne a wajen ba, Allah ya bata haihuwar QUADRUPLE a saukake, dan kuwa a saukake za'a ce, duk wannan azaban da ta sha wlh ya zo mata da sauki, saboda ba kowace mace ba ce zata iya haihuwa ƴan uku da kanta ba ma bare QUADRUPLE, wannan sai ikon Allah da ya bawa gwaggo da Jehan ɗin damar yin hakan, idan baku manta ba, ita ma gwaggon hakan ce, Jehan ƴar ɗakinta ta yi gado sosai sosai, a komai ta gaji gwaggon, bata rage komai ba abinta.

Duk taurin zuciya irin ta Lion wlh sai da idanunsa suka ciko da kwallah, ya yi matuƙar tausaya mata, dan daga karshe ma sai da ya bata iskar bakinsa ta iya cigaba da numfashi, a haihuwar na karshe ta kasa samun numfashin da zai riketa ta iya haifar baby, sai da Lion ɗin ya tallafa mata, ga shi su gwaggo basu kusa, dan gwaggo ma tana can sama hawa ta karshe ita da Josephine suna tsara yadda tafiyarsu Nigeria and Dubai zai kasance, sam bata kawo cewa haihu zai zowa Jehan ɗin a satin nan ba, a nata kissafin sai cikin next week, shi ne yasa suka ɗan matsa kusa da ita.

A lokacin da Rimsha ta fita daga bedroom ɗin, kai tsaye bedroom na gwaggon ta nufa, sai dai ko da ta je bata sami kowa ba, abin ku da yarinta, a maimaƙon ta fita ta nemi gwaggon a cikin gidan, dan ta gaya mata halin da ake ciki, sai kawai ta haye gado tana kuka tare da addu'ar Allah yasa kada Jehan ta mutu, Allah yasa ba mutuwa zata yi ba.

Kada kuga laifin Rimsha, ita bata san menene haihuwa ba, yarinya ce, ko cikin ma bata san ya ake ji idan aka ɗauke shi ba bare kuma tasan zafin haihuwa, ita dai kawai addu'a take yi Allah yasa kada Jehan ɗinta ta mutu.

Shi kuwa Lion babu halin ya fita ya bar Jehan ɗin ya je naman gwaggo, duk dakiya irin tasa ya ji ba zai iya matsawa daga kusa da Jehan ɗin ba, dan yana ganin kamar idan ya matsa daga kusa da ita ya karya amanar da ya karɓa daga hannun Areef, yana ganin kamar yana barin wajen zata mutu kafin ya dawo, dan haka sai ya dakata kawai ya kasa tafiya, ya cigaba da riketa har ta haife cikin nata complete QUADRUPLE.

Baby na ƙarshe yana faɗowa ta saki jiki ta sume a jikin Lion ɗin, baiwar Allah.

Shi kansa Lion ɗin wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sake shoulders ɗin nata tare da zareta daga jikinsa.

A kasa saman duv ɗin kusa da baby's ɗin nata ya kwantar da ita, sannan ya miƙe tsaye, gabaɗaya ya yi wanka da jiki tamkar shi ne ya yi naƙudar.

Har zai bar ɗakin idanuwansa suka sauka a kan yaran, complete QUADRUPLE, suna kwance shiru. Lokaci guda ya ji wani irin tsananin son yara ya kama shi, barema yadda ya kalli yaro ɗayan nan mai matuƙar kama da Areef ɗin, sai ya ji ba zai iya tafiya ba, juyowa ya yi tare da sake tsugunnawa a gaban baby's ɗin.

Tamkar mai tsoron taɓa abu, haka ya kai hannunsa zai taɓa kumatun wannan baby mai kama da Areef ɗin, ga yaran da cibiya a jikinsu.

Ai kuwa yana taɓa fuskar yaron ya fara tsallara mashi ihu, a hanzarce ya miƙe kamar wani mara gaskiya, da sauri ya fice daga cikin ɗakin.

Kai tsaye bedroom nasu ya koma. Yana shiga ya hau cire kayan jikinsa, sam bai nemi Rimsha ba, saboda bata kanta yake ba a yanzu.

Sai da ya cire kayan ya rage daga shi sai short ne, ya ɗauko wayarsa ya rubutawa Sir Safwan sako a kan ya kira gwaggo Jehan ta haihu. Yana tura sakon ya wuce toilet abinsa, zuciyarsa a cike tab da tunanin baby's ɗin, sun yi matuƙar shiga ransa ba kaɗan ba.

Har ya yi wanka ya fito tunanin baby's ɗin yake yi, sake sabon shiryawa ya yi, har lokacin kuma bai nemi Rimsha ba, yama mance da cewa ya daka mata tsawa.

Bayan ya kammala shirin nasa ne ya zo ya tsaya a gaban Tv dake manne a bangon yana kallon yadda su gwaggon suke ɗawainiya da baby's ɗin, yaran kawai yake ta kallo, ji yake yi kamar ya je ya sake taɓa yaron nan mai kama da Areef ɗin, tunanin Areef ya dawo mashi sabo gal.

Ya jima sosai yana kallon su gwaggon, har suka gama shirya baby's ɗin suka kwantar da su a saman bed, sannan suka hau gyara Jehan ɗin, gwaggon a tare da Josephine suke aikin.

Ganin cewa sun kawar da yaran daga idanun Camerar zasu fara gyara Jehan ɗin ne yasa ya kawar da kallonsa tare da juyawa ya bar wajen.

Sai a lokacin ne kuma ya tuna da cewa ashe Rimsha bata a cikin ɗakin, dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya sa kai ya nufi waje.

Kai tsaye bedroom na gwaggo ya nufa, dan yasan a can kawai zai sameta.

Akila kuwa tana bedroom na Josephine ne, kada ku manta Aseef dai na Josephine ne, hakan yasa Josephine ɗin ta ce a bedroom nata matar Aseef ɗin zata zauna ta yi jego, dole gwaggo ta bar mata Akilar, Anaya kuma tana wajensu Brr Naurat, a can tafi yawan zama, su Aafia kowa tana part na mijinta.

Tana kwance kamar yadda ta shigo ta kwanta, bata motsa daga wajen ba sai ruwan hawaye da take yi.

Kasa kasa ya yi sallamar da babu wanda zai iya jinta face shi da ya yi kayansa, sai zuba uban kamshi perfume nasa yake yi tamkar ba daga ɗakin haihuwa ya fito yanzu ba jimawa ba.

Tana ganinsa ta miƙe zaune tana mai cigaba da kukanta, hawaye suna gudu a saman face nata kamar ruwan famfo aka buɗe.

Ɗan tsura mata idanu ya yi kafin ya ƙariso wajen nata.

Kasa ta yi da kanta tana shesshekar kuka.

Yana isowa wajen ya miƙa mata hannunsa. Ɗago kai ta yi ba tare da ta yi magana ba, kuma bata iya miƙa mashi nata hannun ba.

Ganin hakan yasa shi ya kamo hannun nata tare da jawota a kan ta sauƙo kasa, dan baya jin kamar zai iya hawa saman bed ɗin gwaggon.

Ba musu ta sauko kasan. Cak ya ɗauketa ba tare da ya yi magana ba. Bedroom nasu suka koma.

Bai direta a ko'ina ba sai a saman katafaren bed nasa. Zama shi ma ya yi a bakin bed ɗin tare da jawota jikinsa yana faɗin.

"Ya isa kukan nan haka, calm down sarkin rigima".

Cikin dashewar murya ta ce.
"Noorish ina Jehan ɗita take? Bata mutu ba ko? Ya take?".

"Jehan ɗinki bata mutu ba, sai dai ma haifa mana kyawawan baby's har guda huɗuda ta yi, juya ki ganta a jikin Tv". Ya kai karshen maganar yana shafa kanta.

A dubu ɗari ta zaro idanuwanta tana kallon Tv, su gwaggo kawai ta gani suna aikin gyara kasan wajen, Jehan ɗin tana saman bed suka mayar da ita, saboda har lokacin tana sume ne, hakan yasa suka mayar da ita saman suna aikin gyara kasan kafin su koma ta kanta.

"Noorish ban ga Jehan ɗin ba, in je bedroom ɗin in dubata?". Ta yi maganar muryarta cike tab da zumuɗi.

Kai kawai ya gyaɗa mata tare da sakinta a kan ta je. Da gudu ta miƙe da nufin ta fita.

A hanzarce ya riƙota yana faɗin. "Saka kayanki tukun nan mana".

Nisawa ta yi tare da nufar dressing room nasa. A gaggauce ta zura abaya a jikinta tare da fitowa da sauri, har tana haɗawa da gudu.

Da kallo kawai ya bita da shi har ta fice abinta, sai zumuɗi take yi.

Bayan ta fita ne ya miƙe da nufin ya fita waje shi ma, zuciyarsa cike tab da tunanin baby's ɗin nan, da hannunsa yau ya karɓi haihuwa, Allah mai iko, idan ba dan Areef ba yaushe zai yarda ya kusanci mace mai ciki ma, amma sai ga shi ya kusanceta har ya karɓi haihuwa, Allah da ikonsa kuma har soyayyar yara ta dasu mashi a cikin zuciyarsa, dama ance wani sanadi shi yake kawo wani, to shi dai sanadin ya karɓi haihuwa Jehan, ta haihu a hannunsa, wannan sanadi tasa ya fara son yara, Allahu Akbar.

Parlourn kasa ya sauko, babu kowa a ciki, dan ƴan gidan nan wasu suna kaiwa 12 na rana basu tashi barci ba wani lokaci, so babu kowa a parlourn.

Waje harabar gidan ya nufa. Yana fitowa motocin jiga jigan sojoji masu ɗauke da jini tamkar zasu ruguje garin, tamkar zasu yaki kowa da komai na duniyar ne suka danno hancinsu a cikin gidan, ji kake jiniya ta karaɗe ko'ina a faɗin arear wajen tana tashin kai.

Zubawa motocin idanu ya yi yana kallonsu har suka iso cikin tsakiyar harabar gidan.

Tun basu gama yin parking ba wasu jiga jigan zaratan sojoji turawa farare kal kal dasu ne suka fara dirowa kasa daga saman bayan motocin.

Ji kake dib, dib, dib, suna dirowa, ga wasu shegun jiga jigan bindigu a hannayensu.

Suna dirowa kuma suka fara aikin bubbuɗe kofofin motocin.

Tga ne ya fara fitowa daga ɗaya daga cikin motocin, cikin zafin nama yake taku izuwa wajen motar dake kusa da wanda ya fito.

Yana zuwa ya ɓalle marfin bayanta, hannu ya zura ciki ya saɓo Areef dake kwance kamar gawa a saman shoulder ɗinsa.

Ai a dubu ɗari Lion ɗin ya nufosu, sojojin suna ganinsa suka ja da baya, cikin girmamawa suka hau sara mashi.

Sam bai bi ta kan kowa ba, bai kalli in da suke ba ya nufi Tga ɗin kawai. Yau idanuwan Uncle T kamar wuta saboda tsananin ja da suka yi, da alama sun ji wuya ba kaɗan ba, fuskar nan tasa kawai idan mai ƙaramar zuciya ya gani sai zuciyar ta buga ya mutu.

Lion ɗin yana isa wajensu ya kai hannu ya karɓi Areef ɗin. Saura kaɗan ya sake shi ya faɗi kasa, saboda yadda ya ji jikin ɗan uwan nasa a sake kamar gawa, abin ya yi tsananin girgizasa. Amma sai ya daure ya rikesa da kyau ya wuce da shi cikin gida.

Shi kuma Uncle T ya koma ya fito da mummyn Rimsha da ita ma take kwance kamar gawa, shi kuma Mark ya tallafawa daddyn Rimsha da baya iya tafiya a miƙe, saboda ya jima tsawon watanni a ɗaure cikin sarkoki yana tsugunne a saman gwiwowinsa, hakan yasa baya iya miƙewa ya taka kafafun nasa, su Anderson sun kai tsinannu azzalumai wlh.

Cikin gida suka wuce su ɗin ma, jinin Uncle T yau a tafashe take over.

Waɗan nan jiga jigan sojojin ne suka fito da dattijo Anderson and His Excellence, duk jikkunansu ciwuka ne, sun sha ɗauri kamar wasu huhun goro, daga ganin wannnan azzalumin baƙin ɗaurin na rashin imani uncle T ne ya ɗaure su, da gani babu tambaya shi ne nan ya ɗauresu, dan tsabar sun ɗauru har ta wuyarsu bai bari ba, duk ya kanannaɗesu da wata shegiyar igiya mai kaifin gaske, kamar wasu dabbobi, sai yankar jikinsu igiyar take yi, uncle T babu imani ba tausayi idan ya kamaka da laifi.
Da kyar da makyarkyata suke iya yin numfashi, duk sun zama wasu iri da su, shi His Excellence ma har da kumburi a tattare da jikinsa, saboda rashin samun isasshen gudun jini da yake fama da shi, dan sun ɗauru ne over ta yadda yasa har jinin jikin nasu baya ratsa sassan jikinsu da kyau, da alama kuma sun ɗauki tsawon kwanaki suna a cikin wannan hali na ɗaurin, dan kuma ga su nan sun yi fari pat kamar wasu farin fenti, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo?.

Wani shirgegen soja ne ya fito da Uncle Herry wanda shi ma ya samu harbi da bingiga a shoulder ɗinsa ta dama, da alama ya yi ƙoƙarin yi masu gardama ne uncle T ya harbesa, dan da alama uncle T shi ne ya karisa wannan yaƙin duba da yadda Areef yake kamar gawa, Allah ne kaɗai yasan ya mutu ne ko yana raye.

Cikin gida wannan shirgegen sojan ya wuce da Uncle Herry ɗin ma, a lokacin tuni Lion ya wuce da Areef word room nasu, a saman sofa ya kwantar da Uncle Herry ɗin, sannan ya juya ya fice abinsa.

Yau dai gida suna farinciki kuma suna bakin ciki, farincikin Jehan ta haifo QUADRUPLE ne, bakin ciki kuma na dawo da gawar su Areef da mummyn Rimsha...........

NASO NA HAƊE MAKU COMPLETE LAST PAGES YAU, AMMA BAN SAMU DAMA BA, SABODA WANI UZURI, KUMA KUN SAN DAMA BA ISSHASSHEN LAFIYA NE DA NI BA, WLH KAWAI KARFIN HALI NE DA KUMA BANA SON BARINKU A CIKIN KEWA TASA NAKE DAGEWA NA YI MAKU POSTING ƊIN!!. MA'ASSALAMA.

FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA CE.....✍️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*



E52



Yau dai gida suna farinciki kuma suna bakin ciki, farincikin Jehan ta haifo QUADRUPLE ne, bakinciki kuma na dawo da gawar su Areef da mummyn Rimsha.

Saman ɗaya daga cikin bed dake room ɗin Lion ya kwnatar da Areef, su Uncle T gabaɗaya sun biyo bayansa, a saman wata bed ɗin ya kwantar da mummyn Rimsha da ta yi wani irin bala'in haske, tamkar jinin jikinta aka zuƙe, da alama ma hakan ce.

"Call dad". Cewar Lion, ya sanar da Uncle T kenan a kan ya kira masu Dr William.

Da sauri uncle T ɗin ya fice daga cikin ɗakin.

Da Areef da mummyn Rimshar tamkar an zuƙe masu jini ne, dan kuwa ciwo iri guda ne yake damunsu.

Ko da Dr William ya zo, kallo ɗaya ya yi masu ya ce ai waɗan nan babu rai a jikinsu, sun mutu, dan kuwa ga shi nan har jinin jikinsu ya dena motsawa.

Cikin dakiya tare da kwarin gwiwa Lion ɗin ya ce. "No dad, basu mutu ba, suna raye, idan har da gaske Areef ya mutu, to dole dukkanmu zuciyoyinmu zata tsaya da bugawa na ɗan lokaci, sannan kuma idan har da gaske Areef ya mutu dole zamu ji a jikinmu cewa babu shi, kuma dole wasu abubuwanmu zasu ragu, gaskiya bai mutu ba". Ya kai karshen maganar wani irin zufa tana tsastsafo mashi daga gefe da gefen kunnensa.

Shiru Dr William ɗin ya ɗan yi kafin ya ce. "Haka ne, in dai Areef ya mutu to dole zasu ji a jikinku, haka su Anderson suka ji lokacin da daddyna ya mutu".

"Kana nufin Jacob suma QUADRUPLE ne?". Cewar uncle T. Wato shi uncle T ba zai ce daddyn bama, sai dai Jacob kai tsaye, dan ya jefasu a cikin bala'i.

Jinjina kai Dr William ɗin ya yi tare da tabbatar masu ai ainahin haifar QUADRUPLE ya samo asali ne daga kan su Jacob, da Jacob da su Anderson ƴan huɗu ne masu masifar kaunar junansu, shi ne yasa suka kasa yafe mutuwar Jacob ɗin da Dr William ɗin ya zama sanadi, sun kasa hakuri, amma kuma rashin imaninsu ya yi yawa da har suka iya raba jarirai guda huɗun nan, ai shi Jacob sai da suka girma aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login