Showing 75001 words to 78000 words out of 270744 words

Chapter 26 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2953

ta ɗaure shi, ko motsi baya iya yi. Su kuma sauran sojojin ɗakunan da aka kai'su da akwai haske, suna iya ganin komai, kuma bata ɗaure su ba, kawai an zubasu a saman tiles ne aka barsu.

Tsawon kwana biyu suna a sume, Queen kuwa tana ta harkar gabanta, bata bi ta kansu ba tukun nan.

A can gida kuwa, sai adduo'i ake ta yi masu babu kama hannun yaro, kowa hankalinsa a tsananin tashe sosai, Rimsha kam har da zazzaɓi take fama da shi, ko sallar dare bata iya tashi ta yi, saboda rashin lafiya, abin kamar ba lafiya ba, sam ta kasa yi wa Noorish ɗin nata addu'a, ta zama tamkar kurma, ciwon nata ma akwai ayar tambaya a kansa, dan fa ko kallonta mutun ya yi sai ta daka mashi tsawa, ta zama tamkar ba ita ba........

Wannan shi ne abin da ya faru a cikin kwanaki biyun da suka wuce, dan haka mu koma kan story.

Yau shi ne kwana na uku na kasancewar su Lion a Daular Mutuwa, sai a yau kuma Queen ta waiwayesu, a in da ta fara yi masu ɗauki ɗai'ɗai tana bawa dodan tsafinta, wayewar garin yau, ta kashe sojoji biyu daga cikinsu, kafin ta kashe su kuma, sai da ta dawo masu da hankulansu jikinsu cif, a kan idanunsu tasa aka ɗauresu, suna ji suna gani ta sanya aka fasa cikinsu, ta ɗebi abin da zata ɗeba, jininsu kuma kamar yanda kuka sani ne, an kaiwa dodan tsafi, sauran sassan jikinsu kuma tasa aka wuce da shi izuwa wajen da suke kulla harkokinsu da sauran gidajen matsafa dake a duniya, dan ta sayar masu da abubuwan da suke buƙata daga ciki....... Innallilahi wa Inna ilahirrajiun, ya ilahi ya lillahi, wannan musifa dame ta yi kama?.

Mutun na uku a yanzu shi ne a kan layi da za'a kashe, ba kowa bane kuma face Areef na Jehan, shi Lion ma sai Allah ne kaɗai yasan halin da yake a ciki, shin yana raye ne ko ya mutu?.

Ɗakin da Areef ɗin yake kwance yana sume suka nufa, babu Queen ɗin a cikinsu, waɗan nan zaratan kyawawan matasan igbo ɗin ne, sune masu aiwatar da komai, ita Queen idan an gama fasa cikin mutun, da tsafinta take ɗaukar abin da take so dan gane da sassan jikin wanda aka kashe, a takaice dai, ita bata fitowa, komai tana daga cikin faɗarta take aiwatarwa.

Kamar yanda suka kwantar da Areef ɗin tun ranar da suka kawo su, haka suka zo suka same shi, bawan Allah, ko motsawa bai yi ba.

Turo wannan gadon da suke yanka mutun a kai ɗin suka yi izuwa tsakiyar ɗakin. Zaratan maza biyu ne suka ɗauko Areef ɗin, suka kwantar da shi flat a saman bed ɗin, sannan suka zura hannayensa a cikin lock na bed ɗin, suka rufe, ta yanda ko an dawo mashi da hankalinsa, ba zai iya yin yunkurin komai ba, haka kafafunsa ma suka zurata a cikin lock suka datse gam. Sannan ɗaya daga cikinsu ya fito da wata sharɓeɓiyar wuka, sai kyalli take yi, har wani ɗaukar idanu take yi, ga kaifin bala'i, dama su shidda ne zaratan mazan, da mai rike da wukar sun haɗu bakwai dai'dai kenan.

Tsayuwa suka yi shiru a kan Areef ɗin suna jiran Queen ta dawo mashi da tunaninsa, dan bakar zalinci da mugunta, sai mutun yana cikin hayyacinsa ma suke yin duk abin da za su yi, yana ji yana gani babu yadda ya iya da su, a da can baya, sai sun gusarwa da mutun hankali suke yanka shi, yanzu kuma tun bayan fitar su Rimsha suka kawo sabbin tsare tsare da wasu abubuwa na tsubbace tsubbacensu.

Cikin ƴan sakannin da basu fi 30 ba, sai ga Areef ɗin ya buɗe ash eyes nasa, tamkar wanda aka tasa daga barci, idanuwansa sun kumbura sosai, saboda kwana biyu yana sume.

Dishi dishi ya fara gani, saman ɗakin yake ta kallo, su kuwa waɗan nan maza, suna tsaye a kansa, suna jiran ya gama dawowa dai'dai su yanka shi, dukkansu kyawawan gaske ne, farare tas da su, sai dai shi mai ruke da wukar nan, haskensa na daban ne, ba hasken Nigeria ba ne, haka zalika kyansa na daban ne, ya sanya wata bakar handkerchief ya ɗaure daga hancinsa izuwa bakinsa, dan kada jini ta yi mashi fallatse, kuma yafi gabaɗaya matasan wajen tsawo, ya fisu cikar halitta ta kasance cikakken namiji.

A hankali kallon Areef ɗin ta washe. Ya sha ruwan mamakin ganinsa a cikin wannan ɗakin, a hankali ya fara juya kallonsa, ya fara bin ɗakin da kallo.
Cak ya tsayar da idanuwansa a kan waɗan nan matasan, da mamaki yake ganinsu, ya san dai sojojin Lion ba haka suke ba, fararen Turawa ne, waɗan nan kuma hasken Nigeria ke garesu, bakake ne ma a idanun Areef ɗin. To suwaye su kuma? Ya tambayi kansa da kansa.

Yunkurawa ya yi zai mike, sai ya ji ko motsi ba zai iya yi ba, kokarin juyar da kansa ya yi dan ya kalli abin da ya hana shi tashi, ina shi ma kan nasa ba zata iya motsawa daga in da suka kwantar da shi ba, abin ba ƙaramin ɗaure mashi kai ya yi ba, ya yi yunkurin yin magana, nan ma abin ya ci tura, tamkar an ɗaure mashi harshensa ne, ya gagara ambatar sunan Allah, ga shi yana son ya tambayi mutanen su waye su, amma ba hali, Queen ta rufe mashi baki.

Sake juya idanuwansa ya yi, dan idanun ne kawai suke motsawa a gabaɗaya jikinsa, sake fara bin waɗan nan zaratan mazan da kallo ya yi.

Cak ya tsayar da kallonsa a kan wanda yake ruke da wukar, sosai ya zaro idanuwansa waje yana kallon matashin, shi ma matashin shi yake kallo. A dai'dai wannan lokaci Queen ta turo masu da sakon ta bada umarni a datse kan Areef ɗin.

Hannu wanda yake rufe da wukar ya kai saman face nasa, a hankali ya janye wannan handkerchief ɗin daga face nasa, ya buɗe fuskar tasa kenan, sannan ya ɗaga wukar sama dan ya aiwatar da umarnin Queen.

Tsabar shiga tashin hankali da ruɗu Areef bai san lokaci da waje baki da iya karfinsa ba, nan take harshensa ta sake, da iya karfinsa na karshe ya furta sunan Aseef, ya yi maganar yana kallon matashin dake ruke da wukar yana ƙoƙarin cire mashi kai. Ba shakka Aseef ne, ko mutuwa ya yi ya dawo, ba zai taɓa mance Aseef ba, idan zai kasa gane kowa a duniya, to banda TRIPLETS nasa, meya kawo Aseef Daular Mutuwa? Yanzu kenan Aseef kashe mutane yake yi? Me haɗinsa da su Queen? Menene gaskiya? Shin ma wanenen Aseef ɗin?!!! Idan baku manta ba Josephine sun canza ɗaya daga cikin TRIPLETS, kuma Lion yana zargin Aseef ne, hakan na nufin Aseef ɗin ne da gaske? Kenan shi ba mutun bane? Kada fa ku manta a gida suka baro shi yana kukan rabuwa da su! Kenan dama Aseef zai iya kashe TRIPLETS nasa? Ko dai yaya ne, wai wanenen shi!!!!!!!!!!!!!!, Ko dai ba shi bane? Amma dai Areef ba zai taɓa iya kasa gane Aseef ba gaskiya, tun da ya ambaci sunansa, to ba makawa shi ɗin ne!!!! Tirkashi, yau ake yinta, wata sabuwar cakwakiya mai ƙulle kai🧠. Na barku lafiya, har kullum taku ce PRINCESS TEEMA ta amana mai salon ban mamaki da ruɗa kwakwalwa!.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*


E13


Date: 23/4/2024



"Aseef what are you doing here?". Ya yi maganar cikin tsananin fitar hayyaci, da ruɗu, dan ko a mafarki bai taɓa tunanin zai ga Aseef a Daular Mutuwa ba, kuma a nan ɗin ma yana ƙoƙarin kashe shi, wlh zai iya rantsuwa har ga Allah wannan Aseef ne ba gizo ba.

Shiru Aseef ɗin ya yi bai amsa mashi ba, sai ma sanya hannu da ya yi ya mayar da handkerchief ɗin face nasa, sannan ya ɗaga wukar da gaske zai datse mashi wuyar, cikin kwanciyar hankali da kwarin gwiwa yake aikwatar da komai nasa, ga kuma tsantsar nutsuwa a tattare da shi, ba zaka taɓa cewa Heartbeat na TRIPLETS da ya kasance rago mai shagwaɓar tsiya bane, a nan ya zama mai taurin zuciya, mara imani da tausayi.

"Aseef before you kill me, talk to me fist pls, duk da nasan cewa kai ne, amma ka kara share mani tantama kafin ka yi abin da zaka yi".

In a cool voice ya ce "Yeah Areef, it's me, what's next that you want me to tell you before the time of your death". Cikin kwarin gwiwa, jarumta, da nuna isa ya yi maganar, sam babu shagwaɓa ko ɗigo a muryarsa.

Tashin hankali, ai shi Areef ganin Aseef ɗin da kuma tabbatarwa da shi ɗin ne yafi kashe shi ɗin da za'ayi ɗaga mashi hankali, yanzu dai da gaske Aseef ɗin me babu tantama, kuma da kansa zai kashesu? Innallilahi wa inna ilahirrajiun, ya ilali ya lillahi. Godiya ga Allah Areef ɗin ya fara yi da Allah yasa shi ne ya kalli Aseef ɗin ba Lion ba, da Lion ne zuciyarsa zata buga, yanda yake tsananin kaunar Aseef ɗin fiye da kansa, sai dai bai san cewa Lion ɗin ma yana a kan hanya ba.

"Babu wani abin kuma da nake son sake sani face na ce maka kada ka cutar da Lion, kome zaka yi mana ni ka yi mani ni kaɗai, please ka bar Lion ya huta, ya wahala a kanmu ɗan tahalikin nan, tun muna yara, a kanmu ya koyi faɗa, a kanmu ya koyi zafin zuciya, ka fi kowa sanin cewa saboda kai Lion ya koyi faɗa, a primary school shi yake tare mana faɗa, komai muka kwaso shi yake tare mana, ya tsaya mana a kan maraicinmu na rashin uwa, ya bamu farinciki fiye da kansa, ya kula da mu fiye da rayuwarsa, burinsa kawai ace muna yin yanda muke so, please Aseef ka kashe iya ni kaɗai, ka bar Lion, ka barshi ya huta, kada ka ci amanarsa". Ya kai karshen maganar idanunsa sun yi jajir tamkar jini.

Cool murmushi Aseef ɗin ya saki, daga bisani kuma ya ɗaure fuska tamau, cikin muryar shagwaɓa tamkar yanda yake magana a gida ya fara magana yana turo baki "I can't kill you my Areef, i can't do anything to you my TRIPLETS, ku ne ni, kune bugawar zuciyata, kune farincikina, haka zalika ba zan iya bari ko kuda ya taɓaku ba, kamar yanda Lion ya tsaya mana tun muna yara har izuwa yanzu, bai yarda ko kuda ya taɓamu a rashin son ranmu ba, to nima a yanzu Allah ya ara mani lokaci da dama na taimake ku, na ceceku my TRIPLETS!" Ya kai karshen maganar tare da juya wukar hannun nasa ya datse kan ɗaya daga cikin matasan dake tsaye a gefe da gefensa, nan take matashin ya zube kasa bai shura ba, sai jini dake malala a kasa kamar an buɗe bakin fanfo.

Kafin sauran su yi wani yunkuri, ya sake datse kan ɗaya. Cikin zafin nama sauran suka yi kansa, ita kuwa Queen dake kallonsu, a zabure ta mike tsaye, dan bata taɓa tunanin cewa ba mutuminta dake yanka mutane bane, tambayar kanta take yi ina wancan mutumin nata mai yanka mutanen kenan? Tashin hankali, wato gaba ma da gabanta, wai aljani ya taka wuta, Queen ta iya bibiyar su Lion tun da suka baro Kaduna, har suka shiga Enugu, har izuwa Daular Mutuwa, amma bata iya gane ya aka yi mutuminta mai datse kan mutane ya sauya ba, bata iya gane shi ɗin ina yake ba, bata iya bibiyar Aseef ba, shin ta yaya aka yi Aseef ma har ya shigo cikin Daular Mutuwar ba tare da ta sani ba? Ya aka yi har ya kashe ainahin mutuminta mai kashe mutane ba tare da saninta ba? Ya akayi har ya shiga cikin tawagar mutanenta ba tare da saninta ba? Wanenen shi ɗin to? Wai wanenene Aseef?!!!!!!.

Idan kuwa da gaske Aseef ya zo taimaka masu ne, to kenan hakan yana nufin da wata manufa na daban Josephine ta sanya shi a cikinsu? Ke nan ba ta canza ɗayan TRIPLET'S ɗin bane dan ta cutar da su? Ko dai yaya abin yake ne? Amma to tun farko ma menene makasudin canza TRIPLETS ɗin? Manene yasa suka kawo Aseef suka ɗauki na ainahi? Ina na ainahin yake? Shi Aseef ɗin su waye iyayensa? Dole dai akwai wani dalili mai mugu mugun karfi na yin hakan, akwai babbar cakwakiya da kulla kulla a wannan lamarin, wanene mai gaskiya a cikinsu Josephine? Alkalamin PRINCESS TEEMA ce kawai zai warware maku gaskiya, dan haka ku kasance da ni taku PRINCESS TEEMA mai abin ban mamaki.

Babbar magana, a tsananin razane Queen ta mike daga saman kujerar mulkin nata, sai dai kafin ta yi yunkurin yi wa mutanenta dake faɗa da Aseef ɗin wani tsafi, tuni Aseef ɗin ya kashe su dukka, babu imani babu tausayi ko ɗigo a tattare da shi, haka ya yi masu kisan kiyashi, tamkar ba Heartbeat namu ba. Babban abin da ya girgizata ya kuma jijjiga tunaninta, bai wuce yanda ta ga Aseef ɗin ya buɗe Areef daga lock da suka sanya shi ba, ita dai tasan cewa bayan ita babu wanda ya isa ya buɗe waɗan nan locks ɗin, to ya aka yi Aseef ya buɗe shi? Kuma dai da tsafi ake buɗewa, hakan na nufin shima yana da tsafi kenan?.

Ta saki baki tana mamaki, bata ankara ba sai gani ta yi dukkansu biyun sun miƙe tsaye, Areef sai tambaya yake yi ina Aseef ya samu karfi haka? Shi kuma Aseef ɗin sai tambayarsa yake yi ina Lion nasu yake? Wannan shi ne cakwakiya....... JAMA'A NI KAI'NA INA SON SANIN WANENE ASEEF FA? DAN A GASKIYA WANNAN ABIN AKWAI ƊAURE KAI.

Ganin Areef ɗin zai ɓata masu lokaci wajen tambayarsa wanene shi, sai ya riko hannunsa tare da jansa suka fita, har sun fita ɗakin, sai kuma Aseef ɗin ya dawo ya ɗauki jakar da Areef ya zo da ita. Ita kuwa Queen sai kallonsu take yi ta cikin ruwan tsafin, bata ɗaga hankalinta dan sun fito daga ɗakin ba, dan a cewarta, ai tana da zararan mukarrabanta da za su yi gunduwa gunduwa da su, su cinye namarsu ɗanya, dan haka sam bata wani damu ba, bata san cewa abin ba haka yake ba, ko a tsafin ma ai akwai iyayenka wajen yin shi, gaba ne da gabanta, ita har yanzu a iya Africa take tsafinta, su kuma tsafinsu bugawa suke yi da manyan kasashen duniya masu faɗa aji, su ba kananan kwari irinta bane, iyayenta ne a iskanci da bala'i. E KAM BABU SHAKKA IYAYENTA NE, GA ALAMA TA FARKO, ASEEF YA IYA SHIGOWA HAR YA KASHE MUTUMINTA MAI YANKA MUTANE, YA KUMA SHIGA CIKIN JAMA'ARTA DUK BATA IYA GANEWA BA, BABBAN ABIN TAMBAYAR MA SHI NE, TA YAYA YA SHIGO CIKIN DAULAR?.

Suna fitowa harabar wajen, wasu jiga jigan maza masu kama da su barbushi ne suka kewayesu, zaratan maza ne majiya karfin gaske, yanayin nunfashinsu ma kawai abin tsoro ne, dan suna numfashi yana fitar da hayaki tamkar waɗan da aka ɗaurasu a saman garwashin wuta mai tsananin zafi, wasu jibga jibga da su, ga gashin kansu kamar jijiyar bishiya, a tsai tsai kamar kawon shaiɗan, idanunsu kawai abin tsoro ne, tamkar ba idanun bil adama ba, wasu jajir dawu tamkar sun zuwa jini ne a ciki, hannunsu kawai abin kallo ne, wasu dama dama da su, kirjin nan nasu a tsaye tamkar bishiyar kuka, sam yanayin halittarsu ya fita daban da ta mutane, kai daga gani kasan da tsafi suke amfani, da tsafi suka mayar da halittarsu hakan, jikkunansu babu riga, sai dai ta kasa ne kawai suka rufe, sun kasance su goma ne cif.

Hakika Areef ya tsorata da ganin waɗan nan halittu, ya girgiza na ganin munin halittarsu, sai dai bai sare ba, bai ji sanyin gwiwa ba, dan hukumar C.I.A idan ba gani suka yi an kashe su ba, to wlh basu taɓa tsarewa a kan abu, komai gani suke yi za su iya, haka Areef yake ganin kamar zai iya faɗa da su, yana ganin mutane tamkar gunguma gungumar kumaka da aka sassaka da dafaffiyar karfe, amma hakan bai sa ya ji ba zai iya yakarsu ba.

A tare waɗan nan gunguma gungumar mutane suka nufesu, suna taku kasa na amsawa da dib, dib, dib. Su kuwa suna tsaye suna kare masu kallo.

Sai da suka isa wajen ne Aseef ya ciro da wata sharɓeɓiyar wuka daga kugunsa, shi kuma Areef ya yi bismillah dan su fara yaki, sai kuma me? Yana ambatar wannan bismillahi gabaɗaya dakarun Queen ɗin suka ja baya da su, tamkar waɗan da aka janye da tsafi.

Ita dai Queen tana cikin faɗarta har wa yau, sai kallon abin al'ajabi da mamaki take yi, wani irin zaro shegun idanun tan nan ta yi na ganin yanda mukarraban nata suka ja baya daga tunkarar su Areef ɗin, irin wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login