Showing 156001 words to 159000 words out of 270744 words
mashi, sai Mark ɗin ya ce masu su kyale mashi ita ta yi mashi.
Kusa da bed ɗin ya ƙariso, a takaice ya tambayi Mark ɗin ya yake jin jikin nasa a yanzu?.
"Alhamdulillah sir". Ya bashi amsa cikin girmamawa. Anaya ta koya mashi faɗin Alhamdulillah.
Jinjina kai Lion ɗin ya yi tare da tambayar Dr ba wata matsala. Babu ya amsa mashi da shi cikin gaggawa shi ma. Sallama ya yi masu tare da ficewa ya koma bedroom nasa.
Saman bed ya haye ya kwanta, shiru ya lumshe idanuwansa tamkar mai yin barci, a haka Areef ya shigo ya same shi, saman bed ɗin ya nufa yana faɗin "His Excellence what is wrong with you? Since in the evening naga like you're not in a good mood".
Ɗan waro idanunsa waje ya yi, in a cool voice ya fara magana "Areef am in too much of missing Meesha, abin ya kai ni makurar da i can't control myself, I can't stop myself daga kai kai'na gareta".
Shiru Areef ɗin ya ɗan yi. Hakika ya yi mugu mugun tausayawa Lion ɗin, dan yasan wanene ɗan uwan nasa, abin da zai sanya shi ya buɗe baki ya ce ya yi missing na wani abin, this thing is not be small thing ooo, duk sai ya ji ya shiga damuwa sosai, ya tausayawa Lion ɗin sosai da sosai.
"Do you know something our Lion?". Shiru ya zuba mashi idanu ba tare da ya amsa ba.
"Ka sanya a ɗauko maka ita, this is the only solution we have, zaman ta a kusa da kai ma zai taimaka maka sosai a kan duk wani abin da zaka yi, and then lastly Rimsha she is so special, she is very very smart, sometimes idan ta faɗi wani magana, zaka yi tunanin mace mai 30 years old ne ta faɗe shi, tana da hankali, nutsuwa and bata da yawan magana bare ka ce zata dameka da surutu ta hanaka yin aiki, so just ka ɗauki kayarka kawai, ta dawo kusa da kai, now she is your power and she is your weakness".
Harara ya wurgawa Areef ɗin kafin ya ce "Meeshar ce so silent?". "Yeah Lion, Meesha she is so silent girl, ga hankali, ko da baka yi sex da ita ba, zaku yi wasa, zata na rage maka abin da kake ji sosai, ni bana goyon bayan ka sake kusantarta a yanzu, because idan ka sake kusantarta nan kusa zaka kasheta ne kawai, amma ka ɗaukota dan ta rage maka feeling da kake ji ta hanyar wasa".
Har lokacin harararsa ya sake yi, sannan ya ɗan yi shiru na tsawon mintoci kafin ya ce "Meesha she isn't like you're thinking, she isn't silent at all, and them I can't control myself idan na ganta a kusa da ni, you can't understand anything Areef, you can't understand who is Meesha, even if i explain to you, you can't understand anything, what i know dai shi ne Meesha ce kawai zata iya kashe mani abin da nake ji that's all".
"Lion why are you saying I can't understand who is Rimsha? I think na fika ma sanin wacece ita, kai fa baku jima da fara shiri ba, bata jima da fara zama kusa da kai ba, she is so silent, very very cute and smart girl".
Girgiza kai kawai Lion ɗin ya yi, Areef fa ba zai gane komai ba, she a wajensa Rimsha ba shiru shiru bace, su ne take yi wa shiru shiru, shi a wajensa banda kuka da shagwaɓa babu abin da take yi mashi, and then yadda ya ɗanɗani zumar nan tata ba zai iya hakura ya kyaleta kamar yadda Areef ɗin ya faɗa ba, ba zasu gane me yaji ba, kawai su kyale shi da abin da yake ji, shi kaɗai yasan wace duniya ya shiga, shi kaɗai yasan wacece Rimsha, a yanzu ko iyayenta sai dai ya kallesu da ido, amma ba dai su gaya mashi sanin wacece Rimsha ba, saboda Areef bai san komai bane yake wani cewa ya fishi sanin Rimsha, to abin da bai sani ba ita dai Rimsha kamar mutun biyu ce a jikin mutun ɗaya, saboda acting biyu take yi, a wajensu Areef tana nuna masu true colornta, shi kuwa Lion ko magana zata yi mashi na serious a kan abu, ba zaka taɓa jin ta buɗe murya ko kuma ta yi magana da asalin voice nata ba, cikin shagwaɓa take yi mashi magana, yanzu da za'a cewa Areef tana da saurin kuka, ba zai taɓa yarda ba, saboda bata taɓa yi masu ba, amma shi kuma Lion, da ya yi mata abu kaɗan zata sa mashi kuka, sai ya yi ta aikin rarrashi, so sanin da Areef ya yi mata ya mata ne a kan Rimshar ta na ainahi, shi kuma Lion Meesha uwar shagwaɓa da soyayya ya sani, suna da banbanci sosai.
"Areef you don't know who's Rimsha, that's all kawai". Ya faɗa tare da jawo wayarsa dake ɗaure a saman bedside drawer tana ringing.
Shiru Areef ɗin ya yi yana tunanin halayen Rimshar, shi dai yasan shiru shiru ce Rimsha, ga shiga hankali sosai.
Ganin kiran mommansa ne yasa ya katse kiran tare da gyara kwanciyarsa haɗe da jawo pillow izuwa saman Lion chest nasa, sannan ya bi kiran. Bugu ɗaya suka ɗauka. Cikin sanyin murya ya ce "Assalamu alaikum, good evening Momma".
Daga ɗaukar ɓangaren ta amsa mashi da "It's not Momma, it's Meesha, wai Noorish ina ka tafi ne? Tun ɗazun gwaggo ta ce ka fita, kuma baka dawo ba, ni fa gaskiya........" Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon jin yanda ya ambaci sunanta da ɗan sauti kuma cikin sarkewar murya, yana daga kwance bai san time da ya miƙe zaune ba, kwata kwata bai kawowa ransa cewa ta farfaɗo ko zata farfaɗo a yanzu ba, kuma dole ya shiga mamaki na jin yadda ta kirashi babu wata alama da take nuna cewa ya yi mata laifi, ko tana fushi da shi, bai san ita bata san komai da ya faru ba, bai taɓa tunanin zata farfaɗo ta yarda da shi ba, bai taɓa tunanin zata yarda ko a waya su yi magana ba, abin ya yi matuƙar bashi mamaki.
Love period ❤️🥲😌
"Noorish lafiya kuwa?". Ta faɗa a ɗan tsorace.
A hankali ya koma ya kwanta tare da kara jawo pillown nasa ya rungume yana faɗin "My Meesha is it you?". Ya faɗa cikin wata iriyar murya da take nuna tsantsar kaunarta da yake yi.
Mamaki ne ya kamata, ita tarasa wannan abin da me ya yi kama, su mummynta sai su rinƙa lallaɓata suna ta ce mata sannu, sannu yaki karewa, ga maganganun da zasu kwantar mata da hankali wanda gwaggo da mum ɗin suke gaya mata, sannan ga kula na musamman da suke bata, sun hanata zuwa ta je ta yi wanka, da ta motsa za su ce mata sannu tana bukatar wani abin ne? Yanzu ta ce zata yi magana da Noorish gwaggo ta kira mata shi a waya, shi ma yana ɗaukar kiran ya ruɗe daga jin voice nata, tunani ta fara yi anya wani gagarumin abu bai faru ba kuwa? Anya babu wani abin da suka ɓoye mata kuwa? Tasan cewa gwaggon da mum ɗinta duk tun fil azart suna nuna masu kauna da kulawa, amma ta yau ɗin nan ta yi yawa over, sun saka mata kai a duhu, sun kuma saka mata kwakwalwa a cikin tunani.
"Meesha meyasa kika yi shiru?". Ya faɗa yana kallon Areef da ya tsare shi da ido. Sai mamakinsa Areef ɗin yake yi, bai taɓa tunanin ko da sunan wasa zai ga Lion cikin zumuɗin jin muryar mace irin haka ba.
Hannu ya kai ya kyastawa Areef ɗin kyawawan yatsunsa a dai'dai saitin face nasa yana sauraron abin da Meeshar tasa take faɗa.
Kasa sosai ta yi da murya, dan gwaggo tana a cikin ɗakin nata, mum ta koma nata ɗakin zata je ta yi sallah, so bata son gwaggon ta ji hiranta da mijin nata, dan wani azababben kunyar gwaggon take ji a yanzu.
"Noorish kafaɗa mani me kayi mani please? Naga su mum sai sona suke kara yi".
(Rimsha zata kashe mutun da dariya, wai su mum sai kara sonta suke yi😂)
Shiru ya ɗan yi, sai yanzu ya gane dalilin da ya sanya ta yarda ta kira shi a waya, wato bata san abin da ya faru ba? No wonder mana, da ta sani ai da sun yi hannun riga kenan.
Nisawa ya yi tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya kafin ya fara magana in a cool voice. "Meesha babu abin da na yi maki face soyayya kawai, know lest do a video call, I want to see your beautiful face my life".
Shi kam Areef ai gabaɗaya Lion ya kwance mashi lissafin ƙwaƙwalwa, ko da sunan wasa bai taɓa tunani Lion ya iya kalamai masu daɗi haka ba, basu taɓa jin sa ko da sunan wasa ya furta makamantansu ba, ko a mafarki basu taɓa zaton ganin irin wannan rana ba.
"Noorish Allah kunyarka nake ji, ni kawai ka dawo gida sai muga juna". A shagwaɓe sosai ta yi maganar.
Kamar zai ce mata baya kasar, amma sai ya tuna da cewa ta ce mashi gwaggo ta ce mata ya fita yana zuwa, hakan na nufin sun ɓoye mata baya nan kenan, tuna hakan yasa ya ce mata "Meesha ba zaki yi mani abin da nake so ba? Ina son kallon face naki fa na ce? Before na dawo ɗin ne nake son ganinki, do you know how much i love? Do you know what am feeling about you now danaji voice naki kuwa?".
Kwace wayar Areef ya yi tare da sanyata a hand-free, dan ya tabbatar wa da kansa Rimshar da ya sani ce, ko dai wata ce, so yake ya ji yau dai ya suke magana, me Rimsha take gayawa Lion da har shi ma yake gaya mata kalamai irin haka.
(Areef akwai shegen son jin gulma, ga sa ido, ko ina ruwansa da su?🤔 😂 Amma dai gara ya jiyo mana me suke faɗa da kyau 😂)
"Noorish kome kake so zan yi maka mana, in dai bai saɓawa Allah, ka manta cewa kai ne farincikina? Amma dai ni gaskiya sai ka rufe ido, idan na kalli kyakkywar face ɗin nan naka da kyau da kyau, sai na kawar da kallo na, sai ka buɗe idon, dan ina jin kunyar ganin cikin idonka ne fa". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai.
Salati Areef ɗin ya fara yi a cikin zuciyarsa, yana mamakin yaushe Rimsha ta zama haka shi bai da labari? E lallai dole Lion ya rinƙa zuba mata kalamai ba tare da ya san yana zuba su ba, irin wannan zallar madarar shagwaɓa da kalamai da take zuba mashi, ga muryarta a kwance kasa kasa, idan ba ka yi mata farin sani bama, ba zaka taɓa cewa ita bace, gaskiya bai ga laifin Lion ba, dole ne ma ya shiga zuba kalamai ba dan ya shirya ba. Daga kasan zuciyarsa kuma tunani yake yi ko yaushe shi kuma zai sami irin wannan soyayya haka? Yaushe Jehan zata fara nuna mashi soyayya haka?. Bawan Allah duk sai ya ji babu daɗ, Rimsha dai har da wani sunan soyayya mai azababben daɗi tasakawa mijinta, wai Noorish, Noorish ɗin ma idan zata kira da salo mai matuƙar jan hankali take kira, amma shi ƴar diramar nan tasa tasan komai, kuma ta iya komai sai wahalar da shi take yi, kuma a haka saboda rashin adalci irin na zuciyarsa kara sonta ma yake yi, baya son ya ji an faɗi laifinta, bawan Allah.
Karɓar wayar tasa daga hannun Areef ɗin ya yi tare da katse kiran ya kirata video call.
Bugu ɗaya ta ɗauka.
Wani irin doguwar numfashi ya ja lokacin da idanuwansa suka sauka a kanta, a hankali ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Ita ma tana ɗaukar kiran ta sauke idanunta a saman face nasa, wani irin daddaɗar ajiyar zuciya ta sauke, sai dai kuma ta canza fuska sosai na ganin shi kwance a saman bed, ina yake to? Ta tambayi kanta.
Ganin ta ɗaure fuska sosai ne yasa ya ɗaga mata gera ɗaya alamar lafiya?.
"Yah Saif ina kake yanzu haka?". Ta faɗa kamar zata saka mashi kuka. Shiru ya ɗan yi, ya lura da ita sosai, idan ya yi mata abin da bai yi mata daɗi ba, zai ji ta kirashi da Yah Saif saɓanin Noorish, hakan na nufin ranta ya sosu kenan, yarinya mai hankalin manya.
"Meesha i want you to understand me, and ki yi mani uzuri, I'm not around, I'm not in Nigeria now, ina U.s, but zanzo ba da jimawa ba kin ji?".
Kuka mai sauti ta saka mashi tare da kifa wayar a saman bed, da gaske take kukan, hawaye zafafa ne suka fara bin kuncinta.
Da sauri gwaggo dake zaune a saman dadduma ta miƙe ta nufota tana tanbayarta lafiya, shi ma Lion ɗin sai hello, hello yake ce mata, amma ina ta kifa wayarma a saman bed ɗin, baya iya ganinta bare yasan ta yadda zai shawo kanta, yana dai jin voice nata tana kuka, yana kuma jin voice na gwaggo tana magana a kusa da ita, shiru kawai ya yi yana sauraronsu.
Tari ta fara yi mai sauti sosai tamkar makoshinta zai fashe, tana mai cigaba da yin kukan nata da iya gaskiyarta. Matsowa gwaggon ta yi ta rungumota tana tambayarta lafiya?.
Kasa yin magana ta yi, saboda kukan ya ci karfinta, ga kuma tarin da take yi sosai da sosai.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
Date: 13/5/2024
E30
Kasa yin magana ta yi, saboda kukan ya ci karfinta, ga kuma tarin da take yi sosai da sosai.
Hankalin gwaggo idan ya yi dubu to ya tashi a wannan lokaci, kiran sunanta take yi, amma ina ko kulata Rimsha taki yi.
Shi kuwa Lion ganin ba zasu ji shi bane yasa ya katsi kiran ya sake kira, dan wayar ta yi ringing ta sa su dawo da hankalinsu a kanta, duk hankalinsa a tashe bawan Allah, a yanzu a duniya, idan akwai abin da ya tsana, to bai wuce yaga ɓacin ran matarsa ba, sam baya son yaga antaɓa mashi ita, zai iya yin komai a kanta.
Yana sake kira gwaggo ta kai hannu ta ɗauki wayar, ganin shi ne yasa ta yi picking da wuri, dan dama ko bai kirata ba, tana da niyar ta kira shi, dan ta ji me ya yi wa Rimsha da har take irin wannan kuka da tari haka.
Ita kuwa Rimshar, kwanciya ta yi tare da rungume pillow tana mai cigaba da yin kuka kasa kasa, hawaye bibbiyu take zubarwa.
"Assalamu alaikum". Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Wa'alaikumussalam". "Good evening momma". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Firstly me ka yi wa Rimsha take irin wannan kuka haka?".
"Nothing momma, kawai dai dan na ce mata am not around ne yasa ta yi fushi, please Momma ki rarrasheta ta yi shiru, kinga bata da lafiya, and if that's the case ki yi mani izini na sa a ɗauko mani ita kawai, because ba zata iya zama babu ni ba, nima kuma haka". Ya kai karshen maganar yana jan dogon gashin kan Areef da yake ta yi mashi dariyar mugunta, saboda Rimshar tana fushi da shi, duk ya bi ya rikice, shi ne Areef ɗin yake yi mashi dariya dan neman tsokana.
"Meyasa zaka gaya mata baka kusa? Kasan wahalar da muka sha kafin ta farfaɗo kuwa? Ka san wahalar da ƴar tahaliƙar nan ta sha? A yanzu Rimsha farinciki take so ba wai a kara ɓata mata rai ba, ba zan ji daɗi ba idan har ka sake yi mata abin da ba daɗi, ka yi magana da ita, idan har tana son zuwa wajenka shikenan ka tura a ɗauka maka ita ɗin". Ta kai karshen maganar tare da sanyawa Rimshar wayar a kunne, sannan ta juya ta fice abinta.
Shiru ya ɗan yi yana sauraron kukan nata da take rerawa, yana kuma tunani a cikin zuciyarsa, lallai uwa uwace, tun da yake babu wanda ya iya tunkararsa ya ce mashi Saif abin da ka yin nan baka kyauta ba, ba'a taɓa samun wanda ya kwatanta kwantankwacin haka ba, wasu ma da yin magana da shi kawai tsoro yake basu, yana yi masu kwarjinin da ba zasu iya ba, amma yau kai tsaye gwaggo ta ce ya yi laifi, kuma bai ji zafin faɗar hakan da ta yi ba, sai ma daɗi da ya ji da ta yi mashi faɗa, to gaskiya dai uwa ta wuce abin wasa, dole ya kara jinjinawa duk wasu iyaye jajirtattu a kan ƴaƴansu.
"Meeshana". Ya faɗa a sanyayye. Tana jinsa ta ki amsawa, cigaba da kukanta ma ta yi.
"Am so sorry, please stop crying mana, kina nema ki sanya zuciyata ta ɗau zafi ba? Ni nasan ke mai hakuri ce kuma mai yi wa mutane uzuri, amma meyasa kika kasa yi wa mijinki uzuri?".
Cikin kuka a ƙule ta ce "Saboda ina sonka mana, babu wani uzuri da zan yi