Showing 192001 words to 195000 words out of 270744 words
nasa ta yi ita ma ta buɗe kofar nata side ɗin ta fito. Kallon wajen suka fara yi, sun rasa ta ina zasu fara tinkarar wajen, abin mamakin ma a nan shi ne, ya aka yi mutane suke rayuwa a irin wannan wajen? Anya wajen nan babu wata ayar tambaya a kanta kuwa? Dan waje ne mai haɗari, bil adama mai gaskiya ba zai taɓa zuwa ko kwatan wannan waje ba!.
"Baby waiting for me inside the car am coming". Ya faɗa tare da wucewa gaba ya nufi dutsen, babu ko tsoro a ransa, cikin jarumta yake tafiya, tamkar ba'a kungurmin daji suke ba.
"No Yah Areef, ni zan bika, ba zan iya zama ba". Ta kai karshen maganar tare da bin bayansa da sauri, tana zuwa kuma ta riko hannunsa dan ma kada ya hanata binsa ɗin.
Shi kuwa tun daga kan yanayin hanyar da suka biyo suna zo wannan waje ya fahimci ba waje ne na lafiya ba, tun daga lokacin yake danasanin zuwa da ita da ya yi. Bashi da zaɓin da ya wuce ya kama hannunta su nufi wajen dutsen, dan baya son ɓacin ranta kuma baya son barinta a cikin motar ita kaɗai, bai san me zai iya faruwa ba, gara mashi suna a tare.
Tsit kake jin wajen babu motsin kowa, sai kukan tsuntsaye da suke ta faman shawagi daga can nesa da wajen.
Kamar zasu shiga cikin wannan kogwan dutsen, sai kuma suka fasa ya ce da ita su fara duba kewayen dutsen su gani, dan su tabbatar da ya haɗarin wajen yake kafin su afka. Ita dai da to kawai ta bishi.
Bayan dutsen suka nufa, tafiya suna rinƙa yi mai ɗan nisa kafin su isko wani abin da zukatansu suka kasa yarda da abin da idanuwansu suke gani, kallon juna suka yi kafin su sake mayar da kallonsu a wajen. Wani katafaren gida na alfarma ne a wajen, gini ne wanda ya amsa sunansa gini, tsabar kyan wannan gida sai ka ɗauka aljanu ne suka kera shi ba mutane ba. Tashin sense!! Waye zai zo cikin wannan kungurmin daji ya yi wanna tampatsetsen gida haka? Shin gidan mutane ne ma ko na al'janu? Dan dai wannan gini tsarinsa bai yi kama da tsarin gine ginen gida nan Nigeria ba.
Buɗe baki ta yi zata yi magana, cikin sauri ya rufe mata bakin da tafin hannunsa, a kunne ya raɗa mata ta yi shiru kawai su je. Ba musu ta ja bakinta ta yi shiru, hannunta ya riko cikin nasa, sannan suka nufi cikin gidan babu ko alamar tsoro a tattare da shi.
Tamkar wani jarumin sadaukin yaki ya sa hannu ya buɗe tampatsetsen gate ɗin wannan gida. Gida ne dai tamkar gidan sarauta, komai na more rayuwa da akwai a cikinsa, sai dai kuma a tsakiyar dokar daji yake!!.
Ciki suka shiga, tsorata iya tsorata Jehan ta yi, sai dai bata nuna mashi ta tsorata ba, ta daure tare da dakewa suka kutsa har can cikin gidan. Katafaren parlourn ya ji komai na more rayuwa. Fasa shiga can cikin parlourn Areef ɗin ya yi, saboda ya hango wata ɗaki mai matuƙar abin tambaya a tattare da ita daga ɗan can gefe a harabar gidan ta wajen flowers, ko'ina a gidan fentin yellow da fari ne, amma shi wannan ɗakin fentinsa baki ne da jajir kamar jini, daga ta sama rabin ginin ɗakin fentin jajir ne kamar jini, daga ta kasa kuma bakin kirin kamar zunubi. Hakan yasa Aseef ɗin ya dasa ayar zargi a kan wannan ɗakin, shi ne yasa ya fasa shiga cikin parlourn ya juyo suka nufi wajen ɗakin.
Yana zuwa babu ko shakka bare tsoro yasa hannu ya wangale tampatsetsiyar kofar ɗakin wadda take baka kirin kamar zunubi. Saman ɗakin ma dakin ne ba kwano bane ba, hakan yasa ɗakin yake da duhu sosai, ga kuma babu Windows a cikinsa. Suna buɗe kofar wani irin haske ne ya kauraye cikin ɗakin.
Ɗakin empty yake babu komai, floor nasa ma siminti ne ba tiles ba, tamkar irin waɗan nan gingima gingiman storys na manyan kasuwanni da ake yi dan ajiyar kayan hatsi kada su lalace.
Can suka hango mace a kwance zindir babu kaya a jikinta a kasar floor ɗin, gashin kanta a barbaje kamar wata mahaukaciya, ko motsi bata yi, ga jini dake zuba ta karkashinta, kamar wadda aka yi wa fyaɗe, jikinta ya yi wani irin green color tamkar wadda ta jima da mutuwa ta fara ruɓewa, kafafunta duk a kumbure tamkar ruɓaɓɓen alala, sam babu numfashi a tattare da ita.
Ihu Jehan ta kurma tana faɗin "Adiva!! Adiva!! Wlh she's.........". Bata kai karshen maganar ba ta kwasa a guje ta afka cikin ɗakin, ba tare da yin wata tunani ba.
A dubu ɗari Areef ɗin ya yi ƙoƙarin dakatar da ita, sai dai ina ta rigada ta shige ciki da gudun gaske. Nan take ɗakin kuma ya fara wani irin kururuwa tamkar kukan zaki a lokacin da yake jin yinwa, wani irin kura mai haɗe da hayaki ne ya bule gabaɗaya cikin ɗakin, daga ita Adivar har Jehan ɗin da ta afka cikin ɗakin Areef ɗin ya dai'na ganinsu, saboda wannan turnukin hayaki da kuma kura, ga kurar da shiga hanci da ido, shi kansa a haukace ya ja da baya, saboda wani irin azababben tari da yafara yi, kan kace me jini ya fara fitowa daga cikin bakinsa da hancinsa na wannan tari da yake yi.
Daga ina wannan hayaki da kura suka fito⁉️bayan kuma kasar ɗakin siminti ne ba kasa ba bare ace dama akwai kasa za'a iya samun kura! Gidan wanenen a dokar dajin nan⁉️ ina su Jehan ɗin suka yi da suka bacewa Areef ⁉️ meyasami Adivan⁉️ ta mutu ne ko tana a raye⁉️.
Kai, kai, kai TRIPLETS dai ba zai dai'na cazamun kai ba sai ranar da na ajiye alkamanina, ma'ana na dasa aya a littafin kenan, ina ga a ranar ne zan huta da cakwakiyarsa🥲 irin wannan cakwakiya haka?! Duk fa wannan daɗi, sugar da karɗi tare kuma da cakwakiya na littafin TRIPLETS wasa ne a kan next book nawa da zan sakar maku! Kada kuma fa ku manta na gaya maku shi littafin TRIPLETS tamkar ina barci haka na rubuta shi, shi kuma next book nawa da zai zo maku idan Allah ya kaimu na kammala littafin TRIPLETS, shi sai da na waro idanuna,👀 na nutsar da kwakwalwata🧠 na taushi zuciyata🫀 sannan na iya fara typing nasa, saboda na daban ne, idan nace maku na daban ne, to fa ina nufin na daban ɗin ne, salonsa ya sha banban da kowani story, tafiyar ta manyan kai ce,🔥 dan za'ayi ɓarin wuta🔥dan haka kada ki yarda baki karanta wannan book ɗin ba, ayi babu ke, idan littafin TRIPLETS yazo da zafinsa, to shi kuma wancan da tafasa yake tafe, tafasa yake yi bul bul bul!🙃 Yana hayaki mai tashin kai!!🔥 Ba zan gaya maku sunansa a yanzu ba😂 sai a karshe littafin TRIPLETS sunansa da ɗan takaitaccen bayani a kansa zai zo maku❤️🔥 MA'ASSALAMA, TAKU HAR KULLUM FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA ZERO TENSION❤️🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
Date: 23/5/2024
E38
Tari sosai Areef ɗin yake yi tamkar maƙoshinsa zai fashe, wannan kura da kuma hayakin sai kara yawaita a wajen yake yi.
Sun ɗauki a kallah 5 mins a haka kafin wannan kura da kuma wannan hayaki ya dakata cak, haka zalika shi ma Areef ɗin tarin nasa ya tsaya cak, abin mamakin kuma jinin dake fita daga bakin nasa shi ma sai ya ɓace ɓat, nan take ya koma normal kamar babu komai. A wani irin zafafe ya nufi ɗakin gadan gadan.
A sume ya isko Jehan ɗin, ta sume kwance kusa da Adiva ɗin. A zafafe ya karisa cikin, kai tsaye kanta ya nufa, cikin zafin nama ya kai hannu yana ƙoƙarin taɓata, tamkar daga sama wata halitta mai kama da shanuwa ta bayyana a gabansu. "Hasbunallahu wani'imal wakil ". Ya furta tare da ɗago da kallonsa izuwa kan wannan halitta.
Nan tane wannan Halitta ta kurma wani irin kururwa mai matuƙar doɗar da kunnuwar mai sauraro, kururuwar sai da ta amsa a gabaɗaya ilahirin dajin, wani irin amon sauti mai bala'i kara mara daɗin ji take fitarwa, bakinta na fitar da wata iriyar bakar hayaki, ko kaɗan wannan halinta bata da kyan gani, tsabar muninta ma sai idan kana da karfin imani ne zaka iya ganinta, ga wani ɗan iskan kaho a tsakiyar hancinta tamkar kawon shaiɗan, hancin nata kam sai dai mu ce subhanallahi, saboda wani irin bala'i muni, ga wasu garman hakwara tamkar kopaton doki. Duk wannan hayaki da kurafa kenan alama ce ta bayyanar wannan halitta.
Sake furta hasbunallahu wani'imal wakil Areef ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye suna fuskantar juna da wannan halitta, ko kaɗan bata bashi tsoro ba, saboda yasan abu ne na tsafi, shi kuma ya riki Allah, yana da kwarin gwiwa, sannan yana jin zai iya karawa da kowa da komai, dan haka ko a jikinsa.
Wani irin kururuwa wannan halittar ta sake zunduma tare da durkushewa kasa a saman gwiwowinta. Kafin Areef ɗin ya yi wani yunkuri halittar ta daka uban tsalle! Ta haye kansa.
Kokawa suka fara yi da gasken gaske, cikin ikon Allah, Allah ya bawa Areef ɗin dama ya samu ya murɗe wuyar halittar, nan take ta kurma wani ihu wanda sai da ya sanya Jehan ta farfaɗo daga sumar da ta yi, shi kuma Areef ya yi maza ya toshe kunnuwarsa da hannayensa, saboda bala'in karar wannan halitta.
Kasa wanwar halintar ta zube, nan take ta rikiɗa ta koma ainahin halittar mutun. Cikakken namiji ne kuma babban mutun, ba kowa bane kuma face Abbon Nawid!! Tashin sense, dama kenan nan ne wajen tsafinsa kenan? Meyake yi da ƴan matan idan ya kawosu nan? Ga dai Adiva ko me ya yi mata? Ta mutu ne ma ko tana raye?.
Kawar da kallonsa daga kan Abbon Areef ɗin ya yi, ya mayar da kallon nasa a kan Jehan da ta miƙe tsaye cikin fitar hayyaci, gabaɗaya a birkice take, waje ta nufa da gudu. A hanzarce ya rikota tare da jawota jikinsa yana ambatar sunanta kasa kasa. Baiwar Allah wannan kururuwar da Abbon ya kurma lokacin da yake wannan halintar ne ya birkita mata kwakwalwa.
Jin ya ambaci sunanta yasa ta dawo dai'dai, ƙanƙanme shi ta yi tare da sakar mashi kuka mai tsuna zuciyar mai sauraro, rarrashinta ya fara yi cikin nutsuwa yana mai da numfashi.
Wani irin jijjiga ɗakin da suke ɗin ya fara yi, almace na yana son rugujewa. Saketa ya yi a hanzarce tare da cire mayafin jikinta duk da babu girma ya rufe Adiva ɗin da shi, sannan ya ɗauketa cak ya ce da Jehan ɗin zu je, su yi sauri su fita gidan zai ruguje, domin Abbon ya mutu duk wasu kambun tsafi ya karye, so dole gidan ya ruguje.
A takaice dai da kyar suka iya sha daga cikin wannan gida, saura kaɗan ginin ya ruguje da su, Allah ya taimaka suka fito. A gidan baya na motar ya kwantar da Adiva ɗin, sannan suka shiga gidan gaba, a guje ya figi motar suka ɗauki hanyar da suka bi suka zo. Gidan tsafin Abbo kuwa ya ruguje gabaɗaya da gawarsa a ciki.
A can gida kuwa, gwaggo, Rimsha, Akila da kuma Aafia, sun shirya tsab suka nufi wajen gyaran jiki tare da kunshi haɗe da wankin kai. Tga ne zai kai'su, sai kallon Aafia yake yi, yana tuna sumar da ta yi a jikinsa a garden, bayan farfaɗowarta da yadda ta zaro mashi idanu da ta farfaɗo ta gan shi a gabanta, ta tsorata sosai shi ne ta tashi ta gudu cikin gida, bai hanata ba dan kada ta sake sume mashi.
Yau sun ci kwalliyar Abayas, sun yi matuƙar kyau da su, Rimsha dai sai ɗingisa kafa take yi, tun da suka fito Tga ɗin ya tsare Aafiar da idanu, sun zo zasu shiga cikin motar a gidan baya, ya yi maza ya buɗewa gwaggo karfin motar yana faɗin Aafia ta shiga gaba ba sai sun yi mota biyu ba, su tafi a ɗayar ma ya wadatar.
Cikin hanzari Aafiar ta ce "A'a ni ba zan shiga gaba ba gaskiya, sai dai Akila ko Rimsha su shiga gabar, ni a baya zan zauna".
Why ya tambayeta yana tsareta da idanu.
Kawar da kanta daga kallonsa ta yi tana jin zuciyarta na bugawa da sauri sauri.
"Ni matar mutun ce, dan haka ba zan shiga gabar mota da mijin wata ba, dan Heartbeat bai yarda da hakan ba". Cewar Akila, ta kai karshen maganar tare da wucewa ta shiga gidan baya abinta, tana ta aikin latsa waya.
Guntun tsaki Rimsha ta ja kafin ta ce "Uncle T gaya masu ni haramun ce ma shiga gabar mota idan ba motar yaya Saif ba, kuma ko motarsa ɗin ma sai dai idan shi zai tuƙa ne zan shiga gaba". Cikin masifa ta yi maganar, kamar mai jin haushin wani.
Me gwaggo zata yi idan ba dariya ba? Su Rimsha manya, akwaita da iyayi idan ya gameta, barema yanzu da take jin haushin Lion, sai abin ya shafi kowa, kowa masifa take yi mashi, yanzu shi dai Uncle T uncle nata ne fa, tun da Uncle ɗin Lion ne, amma har da shi yau ya sha masifar, dan hawai tana jin haushin Lion.............😂
"A'a Rimsha ai dama ko da kowa zai shiga gabar motar wani ai banda ke". Cewar Tga ɗin, dan ya san halin Lion sarai, ya san shi da bakar kishi, dan haka shi ko da sunan wasa ma baya fatan Rimsha ta shiga mashi gabar mota, yana da tabbacin yanzu ma ba dan gwaggo ba, da wlh Rimsha ba zata tako ko tsakar gidan nan ba, saboda Lion fa karshe ne a ɗan banzan bakin kishi.
"Aafia to ki shiga gaban mana kawai". Cewar gwaggo, ta yi maganar ita ma tana shiga cikin motar gidan baya kenan.
Ɗan turo baki kaɗan ta yi. "A'a gwaggo ni nafi son baya ne". "Meyasa to?". Gwaggon ta tambaya.
"Saboda ni uncle T tsoro yake bani". "Meyasa nake baki tsoro?". Ta tambaya yana rufe Kofar motar gidan bayan, dan su gwaggon sun kammala shiga, saura ita kaɗai suka bari a waje tsaye kamar mara gaskiya.
Tsareta da ido ya yi yana jiran amsa, ƴan kame kame ta fara yi mashi. "Okey now sai ki shiga kawai tun da baki da wani sauran option". Ya faɗa tare da buɗe mazaunin driver zai shiga.
Turo baki ta yi kamar ta ce ta fasa zuwa, amma saboda tana son ayi mata gyaran jiki da kuma kunshi, sai ta hakura ta shiga, tun da Dr Nawid ya rasu bata sake yin kunshi ba, har ta gama takaba da jimawa, kafin Dr Nawid ya rasu kullum cikin yin kunshi da gyaran jiki take, Allah sarki rayuwa kenan.
Tun da ya fara tukin motar yake aikin kallonta ta cikin mirror motar, jefi jefi ita ma tana satar kallonsa ta gefen idanu, sai dai tafi mayar da hankalinta a saman titi.
Wajen gyaran jikin da suka je last time, nan suka je yauma, har cikin wajen ya bisu, gwaggo tana ganin yadda yake ta aikin kallon Aafia kamar wadda aka bashi gadinta, daga nan ta ce tafiya da Aafia U.s ya kamasu, dan ko basu tafi da ita ba sai Tga ya dawo ya ɗauketa, gara ma kawai su sassautawa bawan Allah kawai su wuce tare da ita, idan sun je komai ya dai'dai ta sai ya musulta kawai a ɗaura masu aure a can, dama bai kamata su bar Aafiar a Nigeria ba, duba da abubuwan da suka rinƙa faruwa da ita a baya, bare kuma yanzu da ta yi aure mijinta ya rasu, ai tana bukatar kulawa ne fiye da can baya, kowa kuma yasan Aunty dai ba zata iya rike Aafia ba, saboda suna ganin bata yi wani karatun kirki ba, so bata waye ba a ganinsu, ita kuma Hjy Hadiza ai bama sai na sake faɗa ba, kun sani tana can tana yawon ta zubar ɗinta, so bazata bi ta kan Aafiar ba, Abbi ba zama yake yi ba, shi ma daddyn Jelly zai koma Kano abinsa, dama a can ya fi wayo, Irfan ya koma school, gidan yanzu babu kowa, dama solution dai kawai gwaggon ta ɗauketa ko kuma su mayar da ita gidan Abba wajen Ammie, tun da ita ma Ammien ba baya ba, ta iya bada tarbiya kuma tana da zafin sosai, ita ce zata iya zama da Aafiar duk da ba ita ta haifeta ba, amma yanzu tafiya da ita U.s ma ai dole ne, dole ayi mata password da komai da komai duk a yau ɗin nan!.
Yau ma dai kamar ranar, kusan wuni zumbur suka yi a wajen gyaran jikin, sai dai fa sun sha gyara, Rimsha dai bata fasa ba, sai dai aka yi mata flowers na zane har wuya abinta, a tafin hannunta ma ta bada kalar zanen da take so ayi mata, ta yi wani irin fitinannen kyau,