Showing 78001 words to 81000 words out of 270744 words

Chapter 27 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2963

jan baya kamar an janyesu haka? Abin ya ɗaure mata kai. Amma bata sare ba, sai ta sake yin amfani da tsafinta ta sake turasu suka tunkari su Areef ɗin.

A karo na biyuma bismillahi Areef ya yi, dan su TRIPLETS komai za su aikata, to fa da bismillah suke farawa, sunan Allah shi ne a farko kafin su yi komai, kun tuna lokacin da Lion zai shiga gidan Queen? Sai da ya yi bismillah, ko zama za su yi a saman sofa, sai sun yi bismillah, ta yanda koda akwai wani abin da aka kullah masu, to wannan sunan Allah da suka kira, zai zama sanadiyar warwarewar komai, idan suka yi bismillah za su zauna a waje, to duk wasu shaiɗanun dake zaune a wajen za su watse, kowa zai kama kansa, hakan zai sa da wuya su zauna a waje kuma kuga sun yi faɗa ko makamancinsa, saboda da sunan Allah suka fara zama, babu wani shaiɗani a wajen da zai iya zugasu su yi faɗa, shiyasa kuke ganin kullum cikin Kaunar juna suke, babu faɗa babu kyaran juna.

A karo na biyu da ya yi bismillah ma, a dubu ɗari jakarun suka sake ja da baya, abin ya yi matuƙar girgiza Queen ba kaɗan ba, dan haka sai ta miƙe tsaye, cikin nuna isa da izza ta sanya hannu a saman ruwan tsafin nata, tare kuma da fara surutansu irin na matsafa, nan take ruwan nata ya fara juyawa kamar fanka.

Shi ma Aseef ya yi mamakin ganin yadda mukarraban Queen ɗin suka kasa iso su, sai dai bai nuna ba, kuma already shi ma kun san musulmi ne, akwai dai wata a kasa, amma ban da haka, duk wata addu'ar da Areef zai yi, shima zai iya yinta, so dama kunsan already shi bai yi nisa a karatun addini bane, bai san ma'anonin wasu adduo'i ba, ya dai iya karantawa ne kawai, ita kanta bismillahi bai san me ma'anar yinta ba, ya dai san sunan Allah ne.

Wannan surutai da Queen take yi ba komai bane face karawa jama'ar tata karfi, da kuma dakiya. Haka kuwa aka yi, bayan ta gama surutanta, sai ta sake turasu ga su Areef ɗin, bayin Allan, su kuma suna tsaye gam, babu alamar tsoro ko sarewa a tattare da su, sai ma kwarin gwiwar da suka sake ji mai karfi yana kara ratsasu.

Da wani irin mahaukacin zafi mukarraban Queen ɗin suka nufosu a karo na uku, dafe kai Areef ya yi yana faɗin "La ilahaillah anta subahanaka inni kuntunminazzalumin, wai ku idan za ku zo mu kashe juna kawai kuzo mana, amma saboda walaƙanci sai ku tinkaro mu, sai mun shirya kuma ku sake ja da baya, wannan abin fa ya fara kona mani rai, wani irin abu ne wannan? Ku yi maza ku karisu in ma kashe juna ne sai ayi komai a wuce wajen, ban son jan rai, zuciyata ta fara hasala".......faka faka kenan.

Bai kai karshen surutan nashi ba ya ji an taɓa shi, da sauri ya ɗago kansa, Aseef ne ya taɓa shi, yana ɗagowa ya ce mashi "To ai sai ka dai'na surutun haka ko? Mutanen da sun ɓace kamar haske, kai katsaya sai wani zuba magana kake yi kai kaɗai".

Zaro idanu ya yi yana faɗin "Ban gane sun ɓace ba? Ina kuma suka je? Ba kashe mu suka zo yi ba wai? Yaushe suka ɓace?". Duk waɗan nan tambayoyi ya jerosu ne da mamaki a saman face nasa.

Shiru Aseef ɗin ya yi na ƴan sakanni kafin ya ce "Oho time da ka fara surutanka mana, ni muje hai". Shiru Areef ɗin ma ya yi yana tunanin to a kan me za su ɓace kuma?. Bai san cewa wannan kalma ta lailahaillah anta subahanaka inni kuntuminazzalumin da ya faɗa bane yasa gabaɗaya suka yi wani irin ɓacewa ɓat, ita kanta Queen ɗin sai da kalmar ta sanyata ta yi wani irin baya baya ta faɗa a sama kujerarta na mulkin, karo na farko a rayuwarta da har wani jiri jiri take gani, kanta har wani sara mata yake yi...........

My peoples, wannan shi ne banbancin duk wata shirka da kuma sunan Allah, idan mutun zai yi shirka, ko wani saɓon Allah, to ba makawa sai ya ɗauki lokaci yana haɗa abubuwa, sai ya sha wahala kafin ma ya iya aiwatarwa, kuma ko da ya yi bata taɓa ɗorewa, misali, mushiriki, sai ya haɗa abubuwa da dama ya sha bakar wahala kafin ya iya yin tsafin nan nasa, ya azabtar da kansa ta hanyar shan jini da sauransu, kuma koda sun yi tsafin, baya taɓa tabbata, haka za su yi ta shan wahala, amma ba zai tabbata a jikin wanda suka yi wa ɗin ba, domin annabi ya ce tabbas tsafi bata tabbata a jikin bawa, dole akwai time da zai warware, lokaci gare shi, ɓarawo, sai ya sha wahala wajen yin sata, yana yi zuciyarsa tana bugawa da karfi karfi, saboda yana tsananin tsoron kada a kama shi, idan rana ta ɓacin mashi, to fa har kashe shi ana iya yi, idan kuma ya tsira, to abin da ya sata ɗin ba zata taɓa yin albarka ba, kamar iska haka zata wuce, kunga a nan ya sha bakar wahala sosai a banza, mazinaci, yana yin zina zuciyarsa na dukan uku uku, tsoron kada a kama shi, ko kuma wani abin ya faru yake yi, sannan idan har ya yi zina sau ɗaya, to kofa ce ta wahala da talauci a rayuwarsa take buɗe mashi, mashayin giya, idan ya sha giya, ya shiga cikin maye, ya fita a hayyacinsa, zai iya zuwa ya hau babban titi mota ta take banza ma ba tare da ya sani ba, babban musiface mutun ya gusar da hankalinsa daga jikinsa, masu yin luwaɗi, su maɗigo da sauransu, duk suna kasancewa cikin mufisa da wahala, masu yin lesbian a hankali hankali za su fara wari, ana tafiya ana tafiya har gabansu ta lalace, saboda sun kauce hanyar yadda Allah ya ce ayi, masu bada bayansu ayi zina da su ta wajen, su lalacewarsu ma tafi munin gani, dan har tsutsa suna yi, Allah ai ba abin wasa bane, Allah yana son bayinsa fiye da yanda suke son kansu, dan haka ba zai taɓa hana bayinsa wani abin na jin daɗin rayuwa ba, duk abin da kuka ji Allah ya haramta, to ba makawa wannan abin cutarwa ce ga bayinsa, masu yin bleaching wlh har wani irin wari suke yi, suyi ta zuba turare a jiki, amma kamshin perfume ɗin daban, warin jikin nasu daban, komai za su yi wa jikinsu, wlh ba za su dai'na wannan wari ba, saboda me? Saboda sun kauce hanyar Allah, Ubangiji ya fi kowa sanin abin da zai dace da bawansa, bai yi ki a bakar fata haka kawai ba, haka zalika bai halicci fararen fata haka kawai ba, yasan da cewa shi ne yafi dacewa da kowa daga cikinmu, amma ku ƴan iya, ƴan bani na iya, fit kin daka tsalle kina baka kice sai kin dawo fara, Allah yasan da farar fatar, amma ya baki baka, sai ki gode mashi ba wai ki ra'ina yanda ya yi maki har kina ƙoƙarin canzawa ba, a takaice dai duk masu aikata aikin saɓon Allah, to wlh a wahale suke, su kuma waɗan da suka ce Allah ya isar masu akan komai, wlh ko barci suke yi Allah yana isa masu ɗin, nafi jin daɗi a koda yaushe na yi maku misali a aikace ba wai da baki ba, dan ta hakan ce kawai za su fi ganewa, yanzu misali, ita dai Queen kunsan ba karamar wahala ta sha wajen gina waɗan nan dakarun nata ba, ko da ido ku kunsan dakare ɗaya ya isa ya kashe TRIPLET'S gabaɗayansu, ya isa ya cinyesu gabaɗaya, amma su TRIPLETS ɗin kuma sun ce Allah ya isa masu a kan komai, kuma ga shi ya isa masu ɗin, ƴar ƙaramar kalma ce a baki wajen faɗa, amma babbace a aikace, wato bismillahi munfara da sunan Allah kenan, ga shi su basu sha wahala ba, da iya bismillahi suka ruguje dakarun, ku sani bawai kankantar kalmarce abin dubawa ba, girman abin da ta kuntsa ce abin dubawa, bismillahi, mun fara da sunan Allah, tun da kuwa suka fara da sunan Allah, to ba makawa Allah zai tsaya masu, dan shi suka sako a gaba, shi ne kuma zai shige masu gaban a komai, abin da nake son nuna maku a nan shi ne, duk wani mai aikata saɓon Allah, to wlh a wahale yake har karshe raywuarsa idan bai tuba ba, idan ka ruke Allah, ka gama komai, ba zaka taɓa shan wahala ba, babu wanda zai iya kareka a kan komai a duniyar nan sama da Allah, to ni dai PRINCESS TEEMA na ce Allah ya isa mani akan komai da na saka a gaba a duniyar nan, kuma shi ne a kan gaba a komai nawa, shi na ruke babu wani ja in ja, saura ku kuma my READERS?.

STORY.

Wucewa gaba Aseef ɗin ya yi yana faɗin "Kai Areef ka cika tambaya". Ya yi maganar a tsananin shagwaɓe, yadda dai yake yi masu magana a gida.

Harararsa Areef ɗin ya yi yana faɗin "Kai ni kazo ka gaya mani ta yaya aka yi kazo nan wajen, ba zan yi mamaki da wannan karfin da ka samu ba, dan nasan kai jininmu ne, dole dama kana da karfi, shagwaɓa ce kawai ta cinye karfin, amma ya aka yi kazo nan? Shi nake son sani".

Miƙa mashi jakarsa Aseef ɗin ya yi, ba tare da ya dakata daga tafiyar da yake yi ba ya ce "Kai kanka fa baka san ta yaya ka zo nan ba, amma kake tambayar wani ta yaya ya zo? To ta sama na faɗo, ni ka ruke jakarka na gaji ba zan iya ba, ya fi karfina". Ya kai karshen maganar tamkar zai saka kuka.

Duka Areef ɗin ya kai mashi a dantsen hannunsa. "Ba wani nan sai ka gaya mani ta ya aka yi kazo nan".

Kukan shagwaɓa ya sanyawa Areef ɗin yana faɗin "Kai fa mugu ne, to nima na san tayaya na zo ne? Kawai na ganni ne a kusa da kai, daga haka kuma sai ban sake ganina ba".

Jinjina kai Areef ɗin ya yi yana faɗin "Sarkin rainin wayo na duniya ba, yanzu Aseef ni zaka kalla ka yi wa wannan tatsuniyar na cewa kawai ka ganka ne, sai kuma daga baya baka sake ganinka ba, to yanzu kuma da waye nake magana kenan?".

Turo baki ya yi kamar zai sa kuka ya ce "Da Heartbeat na TRIPLETS kake magana mana, ni ka karɓi jakarka ya yi mani nauyi, ba zan iya rukewa ba". "Amma kuma ai ka iya kashe mutane rai shidda ko? Jaka ce ba zaka iya rukewa ba?".

Kuka ya saka yana ƙoƙarin fara bubbuga kafa a kasa, da sauri Areef ɗin ya karɓi jakar yana faɗin "Rigimamme kawai, ni bani kayana". Ya karɓi jakarsa tare da wucewa gaba abinsa.

Haka suka cigaba da tafiya, Areef yana gaba, shi kuma Aseef yana baya, sai wuce ɗakuna suke yi suna neman sojojinsu da kuma Lion.

"Aseef wai ina Lion ne?". Areef ne ya tambaya.

Shiru Aseef ɗin bai amsa mashi ba, ko da ya juyo dan ya ga meyasa ɗan uwan nasa bai amsa mashi ba, sai ya kalli wajen wayam, babu Aseef babu dalilinsa. Da mamaki ya juyo da kyau yana kallon hanyar, babu wata kofa dai da za'ace Aseef ya bi ya tafi, hanya ce doguwa, sai ɗakunan mutane da suke a rufe ruf. Shiru ya yi yana al'ajabin ina Heartbeat nasun kuma ya yi?.

Ina da tantanma a kan Aseef sosai wlh!!.

Ya jima a tsaye a wajen ya kasa motsawa, tamkar wanda ruwa ta cinye. Almost 20 mins yana tsaye yana ta tunanin abin yi, kwatsam sai ji ya yi daga ta bayansa an taɓa shi.

A razane ya juyo. Cool murmushi Aseef ɗin ya sakar mashi yana faɗin "Muje".

"Aseef ta ina kabi ka bar nan wajen?". Ya yi maganar on a serious note.

Turo baki Aseef ɗin ya yi tare da wucewa gaba ba tare da ya bashi amsa ba. Kamar ba lafiya ba Areef ɗin ya ji ya mance da tambayar da ya yi wa Aseef ɗin a yanzu, kuma ya mance da tambayar da zai sake yi mashi, haka ya sake bin bayansa suka cigaba da tafiya a wannan shegiyar doguwar hanyar, suna tafiya Areef yana ambaton sunan Allah a cikin zuciyarsa, dan shi dama baya rabuwa da yin tasbihi, wannan tasbihi da yake yi kuma shi ne ya yi mugu mugun taimaka masu wajen kubcewa daga kan idanun Queen, kwata kwata ta dai'na ganinsu a yanzu, gabaɗaya sun fita daga idanun tsafinta, dan haka sai ta tashi ta fara gagarumin sabuwar shiri, dan ta lura abin da take gani ƙaramin abu, to yana neman ya zama babban abu, gara ta miƙe tsaye.

A takaice dai sun yi tafiya mai nisa kafin su samu su fita daga cikin wannan waje, suna fita kuma wata duniya suka sake gani, dan faɗawa wani ɓangare na gidan suka yi, gani suke yi tamkar a wata sabuwar duniya suke, Daular Mutuwa gidan akwai girman gaske, babu abin da basu da shi a ciki, Daular ce ta gasken gaske kuwa.

"Areef yana da kyau mu raba hanya a yanzu, zan je neman fadar wancan tsinanniya, dan ita ce kawai zata nunamana gidan uwar da ta kai Lion, kai kuma ka nemo su kaka, Heartbeat da sauransu". Cewar Aseef. Ya kai karshen maganar tare da matsowa sosai kusa da Areef ɗin, a kunne ya raɗa mashi "Ka nemomini Heartbeat tawa da wuri, dan ko a yau muka koma gida sai na yi dis virgin nata, bafa zan kyaleta ba". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi ɓangaren hagunsa.

Areef ɗin yana son ya yi mashi magana, amma ya kasa, yana son yi mashi tambayoyi sosai, amma sai ya ji ya kasa, harshensa ta yi nauyi, hakan na nufin kenan shi Aseef bada tsafi yake amfani ba? Ko dai yaya ne? Wannan abin akwai ruɗu da ɗaure kai.

Areef bawan Allah ya jima tsaye a wajen kafin daga bisani ya nufi nasa hanyar, dan su aiwatar da abin da ya kawosu da sauri su fita a cikin gidan, sai dai kuma zuciyarsa cike take fal da tunanin irin jarumtar Aseef ɗin, tashi ɗaya ya zama jarumi na gasken gaske, kuma ga dai shagwaɓar bai barta ba, idan ta motso mashi yana yi, ga kuma karfin bala'i da yake da shi tamkar wani shararren sadaukin mayaki.

Haka dai suka rabu kowa ya yi hanyarsa, suka bazama neman ƴan uwansu, ita kuma Queen tana can tana shirya masu gagarumin shiri ta yadda za ta kashesu gabadaya lokaci guda, tana ta ƙoƙarin taga ta haɗesu waje guda ta konesu ta huta......

Mu leka gida kuma muga me yake faruwa.

KADUNA.

Wasa wasa Rimsha rashin lafiya sai karuwa yake yi, da mummynta da gwaggo dai kamar yanda kuka sani ne, sun ɗauka laulayin ciki ne, saboda kusan duk abin da take yi a yanzu, ya yi kama da mai ƙaramin ciki, a koda yaushe tana zaune shiru tamkar gunki, bata son hayaniya, kuma ga masifar tsiya idan ka yi mata abu, duk zafi da tsiwa irin na Jehan, to fa yanzu ta shafawa Rimsha lafiya, dan yanzu Rimshar ta fita iya bala'i, jiya ma saura kaɗan su buga dambe, dan Jehan ɗin ta kalleta da ido kawai.

Gwaggo da daddy kuma sun hana ayi wa Rimshar abin da bata so, dan gwaggo ta gayawa daddyn wai ciki ne da Rimshar, so dole a kula da ita a lallaɓata.

(Kai jama'a ana al'amura a littafinTRIPLETS, wai Rimsha ce mai ciki?🤔 Ita da ko...... Ba ayi ba🤔)

Daddy kam murna a wajensa ba'a magana, sai wani ririta suke yi, Jehan kuwa kamar zata fashe saboda haushi, sai Rimsha ta yi mata laifi, amma haka tana ji tana gani su gwaggo za su hanata ɗaukar mataki, abin yana bakanta mata zuciya ba kaɗan ba.

A ɓangaren ita kuma Aafia, ta farfaɗo, ko da ta farfaɗo sai ta farfaɗo masu a kurma mara magana, sam sam bata cewa komai, da idanu kawai take bin mutane baiwar Allah, kome aka ce mata, da idanu kawai take kallon mutu, ba um bare umm.

Daddyn su Lion ma ya sami lafiya sosai, sai dai har yanzu yana a kan bakarsa na cewa shi wlh bai san gwaggo ba, yana fitowa har palo ya zauna da su Uncle Herry, amma baya ko ɗaga idanu ya kalli gwaggon, ita ma bata bi ta kansa, dan Lion ya gaya mata kada ta kula kowa, ya ce mata kusan kowa da take kallo a gidan, to fa ba yin kansa ne yasa yake yin wasu abubuwa ba, akwai wata gagarumar matsala a kasa, dan haka ba ruwanta da kowa, shi idan ya dawo, zai binciko koma mecece ainahin wannan matsala bakiɗaga. Hakan tasa sam bata ko ɗaga idanu ta kalli Dr William ɗin, ita ma ta nuna kamar bata san shi ba, uncle T kuma Lion ya aike shi Usa, ba da shi suka tafi Daular Mutuwa ba, Jay ya koma Washington abinsa, yanzu saura John kawai, suna rayuwarsu iya su uku, Dr William uncle Herry, sai John, sam basu shiga harkar su gwaggo, suma su gwaggon, basu shi ga harkarsu.

Jehan ce kwance a saman bed ɗin gwaggo, dama idan baku manta ba, ɗakin da daddynta ya zauna, shi ne ɗakin gwaggon a yanzu, ta lafe shiru a saman bed ɗin tana tunanin duniya da kuma mijinta. Kamar daga sama tunanin gidan Hjyr daɗi ya faɗo mata cikin ƙwaƙwalwarta, a hanzarce ta miƙe zaune, cikin sauri ta fara leke leke a bayan gadon gwaggon.

Jim kaɗan tasa hannu ta fito da wayoyi guda biyu da ta taɓa ajiyewa a wajen tun lokacin da ta zo gidan kafin ta ta fi prison. Ɗaya wayar Abubakar Salahuddeen ne, ɗayar kuma wayar Adiva. Ganin wayar Adivan nan ya sanya idanunta sun ciko tab da kwallah, tunaninsu ya dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, addu'a take yi Allah Ubangiji hasa Hjyr daɗi bata lalata masu rayuwa ba, Allah sarki Maryam baiwar Allah, yanda ta sha fama da wahalar rayuwa, idan dai Hjyr daɗi ta lalata mata rayuwa wlh sun gama zaluntarta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login