Showing 117001 words to 120000 words out of 270744 words
tsab zata shake Sultan ɗin ma da kansa, amma ta ruketa gam, ta ki barinta ta yi borin.
Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo cikin ɗakin. A tare suka amsa mashi da gwaggo da Brr Naurat. Waro idanu ya yi yana kallon Sultan dake ta faman yin tofi. Cike da mamaki ya ce "Shaikh is it you?" Ya yi maganar yana kara waro idanu waje.
Sultan ɗin bai amsa mashi ba sakamakon yana addu'a, sai bai amsa ba. Kusa da gwaggo ya zo ya zauna yana faɗin "Momma am feeling hungry". Hannu ta kai ta ɗan shafi kansa, cikin sanyin murya ta ce "Sannu da tashi, let me bring food for you ko?".
"No momma just leave it, I can't eat anything without my heartbeat, bari ta tashi sai muci a tare, zan jirara".
Jinjina kai ta yi, rigimar Aseef tana da yawa, shi fa ya ce yana jin yunwa, za'a kawo mashi abinci kuma ya ce sai da Akila zasu ci a tare, ya iya rigima kala kala.
"Momma what happened to Rimsha?". Ya yi maganar yana kallon Sultan da ya dafa kanta yana yi mata karatu a fuska.
"She isn't feeling fine". Ɗan zaro idanu ya yi tare da cewa "What? Momma kuma shi ne ba'a gaya mani ba? What is wrong with her?".
A takaice gwaggon ta ce mashi aljanune suka taɓata. Shiru ya ɗan yi yana maimaita kalmar aljanu, shi sai yau ma ya taɓa jin wannan suna, wai aljanu, abin ma dariya ya bashi, ko meye aljanun? Ya tambayi kansa. Da yaga dai shi ba wani ganewa zai yi ba, sai ya miƙe yana faɗin "Let me go and see uncles".
A takaice gwaggon ta ce mashi "Is good, suna ma shirye shiryen wucewa gidajensu yanzu ne". "Why zasu koma gidansu?". Ya tambaya da mamaki a saman face nasa.
Brr Naurat ce ta ce "E mana zasu koma gidansu, shi ne dai'dai, a nan sun takura sosai ne". Turo baki ya yi yana faɗin "Amma without uncle Hossain ko? Dan ni Allah ba zan yarda ya je ko'ina ba, dole duk in da zamu je mu tafi da shi tare, i don't want him to stay out of us". Ya kai karshen maganar kamar zai yi kuka.
Da sauri gwaggo ma ta ce "You are right! Nima gaskiya ba zan iya yin nisa da Nawazuddeen ba, dan haka shi dole ya zauna a tare da mu, dole na gayawa Saif, ina son mu kasance a tare da Nawazuddeen".
Juyowa ya yi ya dawo ya sumbaci gwaggon a kumatunta yana faɗin "That's my momma, that's why I love you, uncle babu in da zai je, we are together with him". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya fice daga ɗakin.
Ita dai Brr Naurat da idanu kawai take binsu, Aseef ɗan rigima.
A takaice sai da Sheikh Sultan ya shafi kwana uku yana yi wa Rimsha addu'a tare da magunguna irin na addinin musulunci, sannan ne suka sami nasarar cetota ta dawo dai'dai, amma fa anci kwakwa, an wahala ba kaɗan ba, tsayuwa zayyana maku irin wahalar da aka sha ma sai mu cike wannan book 4 ɗin fam, da akwai sauran story a gaba, so ba zan tsaya ɓata lokaci na sosai a wajen zayyano maku ba, just ku yi imagine ya bakar wahala take a ranku, akwai abubuwa da yawa a gabana, ba zan tsaya ɓata lokacina ba!.
A cikin waɗan nan kwanaki ukun fa abubuwa da dama sun faru, wanda suka haɗa da dawowar Tga Nigeria, dan Lion ya ce mashi ya dawo Nigeria zai biyo shi, sannan su Abba kowa ya koma gidansa lafiya lou, yanzu gidan ya rage daga gwaggon, Brr Naurat da Dr Salman, sai Jehan, Rimsha and Akila, matan TRIPLETS kenan, sai Sheikh Sultan mai yi wa Rimsha magani, ita kuma Anaya sun wuce Washington da Mark ɗinta, Lion yasa an mayar da shi can, dama already kunsan Brr ta ce ya karɓi kalmar shahada sai a aura mashi Anayar su tafi a tare, to hakan aka yi, su Abba ne suka ɗaura auren a cikin palo bayan ya musulunta, yanzu sun wuce Washington yana asibiti bawan Allah, yana shan wahala sosai da sosai, sai daddyn Rimsha, shi ma yana nan a gidan bai koma gidansa ba, dan gwaggo ta ce babu in da zai je ya barta gaskiya, shi ne Lion ya ce to ya zauna sai ya dawo kawai, Aylar daddyn Jelly kuwa tana asibiti a kwance, saboda ta samu matsala a cikinta har sai da aka yi mata aiki, ta sha wahala ne, cikinta ya zube, ta zubar da jini, sannan ta ɗauki tsawon kwanaki a sume, ga kuma wahala da jijjiga da cikin nata ya sha, abin dai ba'a cewa komai, Allah ne ma ya kaddara tana da sauran numfashi a gaba, ai da ta jima da mutuwa, yanzu dai shi ne yasa sai da aka yi mata aiki, yanzu haka tana gadon asibiti tare da Aunty matar Abbi, dama kunsan sun koma gidansu. A ɓangaren su Aafia kuma, Abbo ya dawo, ya sakata a gaba, tun da ya dawo ya makale yana zarya a tsakanin gidansa da gidan Abbi, Ummi tana Katsina wajen ƴan uwanta, bata san ya dawo ba baiwar Allah, kuma bai bari ta san ya dawo ɗin ba, dan ba ta ita yake yi ba a halin yanzu, hankalinsa ya karkata a kan Aafia, dan ita ya dawo dama, ana buƙatar ta a wajen tsafin nasu, shi ne ya dawo ɗaukarta, sai safa da marwa yake yi a tsakanin gidajen biyu, sai dai Allah da ikonsa, duk zuwa gidan Abbi ɗin da yake yi baya samun ganinta, ko sau ɗaya bai haɗa idanu da ita ba, shi kuma burinsa kawai su haɗa idanu, suna haɗa ido shikenan ya sami kaso 60 a cikin ɗari na abin da yake so, Allah sarki, so suke yi su hallakata kamar yanda suka hallakar da Dr Nawid, Abbo shi ya bada Dr Nawid, sai dai ba'a son ransa ya bada shi ba, dole suka tilasta mashi, da farko ma ya ce ba zai bayar ba, sai da ya ji matsa da wahala ne ya yarda ya bayar, abin da yasa suka ce sai ya bada Dr Nawid ɗin kuma shi ne, idan baku manta ba Dr Nawid ɗin ya hana shi yin amfani da Jelly, to shi ne abin ya ɓata masu rai, suka ce tun da ya rushe masu shirinsu a kan jelly, to za su yi amfani da shi a madadinta, shi ne yasa suka kashe shi.
To a takaice dai Abbo ya dawo, yana neman ta yadda zai yi ya ɗauki Aafia ido rufe.
A ɓangaren Lion kuwa, a cikin waɗan nan kwanaki uku da suka wuce, ya aikata abubuwa da dama, ciki kuma har da rubuta takardar ajiye aikinsa na soja da ya yi, wannan abin ya yi mugu mugun ɗagawa jama'ar kasar hankali, saboda Lion soja ne wanda kowace kasa take buƙatar jarumi kuma jajirtartce irinsa, tsayayye namiji ne kuma jajirtartce a kan aikinsa, yana da adalci da gaskiya, ga rikon amana, babu zancen cin hanci a lamuransa, kuma babu ɗaga kafa a wajen yanke hukunci, ko kai ɗan uban waye idan ya kamaka da laifi, ba shakka sai ya hukuntaka, babu uban da ya isa ya taka mashi burki, ko his excellence baya ɗagawa kafa, kaifi ɗaya ne shi, babu mai iya tankwara shi, rashinsa a hukumar soja babbar ci baya ne ga kasar U.s gabaɗaya, yana da matuƙar farinjini, al'umma suna tsananin kaunarsa saboda gaskiyarsa, da sama masu kwanciyar hankali da cigaba da yake yi, kowa begensa yake yi, jin cewa ya ajiye aiki yasa wasu har suma sai da suka yi, saboda shiga tashin hankali, wasu kuwa har da rashin lafiya, kowa sai tambayar dalilinsa na ajiye aiki yake yi, amma sam yaki yarda ya fito daga gida ma bare ya yi hira da wasu, duk sojojin dake gidansu ya tarkatasu ya mayar da su headquartersu, sannan ya ɗauko wasu jibga jibgan bodyguards lafiyayyu masu jini a jika ya jibge a cikin gidan nasu, bodyguards ne masu lafiya karfafa masu kiran samudawa, abin ya ɗaurewa jama'a kai, his excellence ya shiga ruɗe sosai, yasan Lion sarai, shi mutun ne da baya yin abu haka kawai, dolen dole sai da kwaƙkwaran dalili, to menene dalilinsa na ajiye aiki? Meyasa? Wannan shi ne tambayar da His excellence ɗin yake ta yi wa kansa, ya haɗa taron gaggawa a white house, ya kuma turawa Lion ɗin saƙon gayyata, amma ya ki zuwa, ko kallon takardar gayyatar ma bai yi ba, dan ya ce bata da amfani a wajensa, his excellence yana tsoron ya sanya karfin mulki ya tursasa Lion ɗin a kan yazo taron dole, dan shi dai yasan waye jikansa, idan ya gwada mashi karfin mulki, to shi kuma ba shakka zai gwada mashi karfin jini, dan Lion baya barin ko ta kwana, dan haka sai His excellence ɗin ya haɗa malaman jikinsa, bai tursasawa Lion ɗin zuwa taron dole ba, haka suka ɗan yi maganganunsu suka watse, anyi anyi da Lion ɗin ya fito ya yi magana a kan meyasa ya kashe kakansa, nan ma yaki buɗe bakinsa, da his excellence ya ga dai Lion fa wani abin yake shirya masu, sai ya lallaɓa ya wankesa a kan zagin kashe kakan nasa da ake yi mashi, duk Lion ɗin yana ganin komai da yake faruwa, amma sam bai yi yunkurin saka baki ba, ya tada kura, a jijiiga gari ya koma gefe ya lafe shiru kamar babu shi, daga shekaran jiya zuwa yau ko'ina idan ka zaga a cikin birnin Washington da kewayenta, maganar Lion ake yi, ko ta ina zancensa ne kawai yake tashi, gidan jaridu kafafen yaɗa labarai, da ko'ina, ya tada tarzoma ba kaɗan ba.
Ya koma gefe guda ya yi shiru kamar ba shi ba, abin da ya sanya ya ajiye aikin soja, saboda ya san ta hakan ne kawai his excellence zai yi ƙoƙarin horar da shi, yasan cewa zasu yi ta ce mashi zasu tuɓe mashi kaki, ko kuma su saka shi yin wani abin a gwammatance, to shi ne yasa kafin ma su fara wannan diramar ya ajiye aikin, yanzu ba kaki da gwamnati ce zasu yi faɗar ba, farar hula ce da gwamnati. Wannan shi ne cakwakiya, shi ne ake kira da ainahin game. Tsafinsu ba zai iya kama shi ba, babu abin da suka isa su yi mashi, dole ne sai sun ajiye tsafi sun yi ta kulla mashi manakisa, shiyasa shi kuma ya biyo masu ta karkashin kasa, Allah ne kaɗai yasan shirin da yake shirya masu!!.
His excellence ya so haɗuwa da Lion ɗin a koma ina ne, sai dai ina bai samu damar haɗuwa ba, hasali ma Lion ɗin ko waje baya fita, yana cikin gida abinsa, gabaɗaya faɗin U.s ta ɗauka a kan ajiye aikin nan nasa, ta girgiza kasar girgiza mafi girma, amma shi ko a jikinsa, sai ma barci da yake shararawa, yana hutawa, har wata ƴar kiba ya kara abinsa, ban da tunanin gwaggo, TRIPLETS nasa da kuma Meeshansa, to baya tunanin komai a rayuwarsa, hankalinsa a matuƙar kwance, kai daga gani kasan ba karamar abu yake shiryawa ba, komawa da baya ga zaki ba tsoro bane, shirin yaki ne, his excellence ya san da hakan, shi ne yasa hankalinsa ya yi mummunar tashi, shi kansa Anderson a tsorace yake.
Wannan shi ne kaɗan daga cikin abubuwan da suka faru a cikin wannan kwana uku da suka wuce, yau ta kama kwana na huɗu, Sheikh Sultan ya kammala aikinsa, Rimsha ta samu lafiya sumul, tamkar bata taɓa yin ciwo ba, yau ta dawo cikin hayyacinta fes, tana dawo dai'dai kuma abinci ta tasa a gaba, ci take yi babu kama hannun yaro, sai kallonta su gwaggo suke yi, baiwar Allah ciki ya buɗe, a kallah yau ta ci abincin da ya kai kusan ukun wanda take ci a baya, sai kallonta Dr Salman da Sheikh Sultan suke yi.
Bayan ta kammala ɗirkar abincin ne ta ɗago idanuwanta tana faɗin "Gwaggo ina yaya Saif? Ko basu dawo daga Daular Mutuwar bane?".
Shiru gwaggo ta ɗan yi kafin ta ce "Sun dawo, amma shi baya nan, sai dai ki kirashi a waya".
Shiru ta ɗan yi tana ji tamkar wadda ta yi tafiya ta je ta yi kwana biyu a wata duniyar.
"Gwaggo ina wayata? Jiya da daddare na barta a nan, bani bari na kirashi". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi saman bed ɗin, ta bar kayan abincin da ta ci a wajen.
Mikewa Dr Salman da kuma Sheikh Sultan suka yi, suka fita suka basu waje, sai Hamdala suke yi ga Allah an samu nasara Rimsha ta dawo dai'dai. Ɗakin ya rage daga gwaggo sai Brr Naurat da kuma Jehan dake ta zuba barci ta tada kai da cinyar gwaggon, ita kuma Akila tana can tana gyaran bedroom nasu, Aseef da Areef basu nan, kwana biyun nan ma sam basu zama a gidan, da alama wani aiki Lion yake saka su, dan a tare da Tga suke fita, idan suka fita tun safe, sai dare suke dawowa, da sun dawo kuma zasu yi barci, dan zasu sake fita da sassafe, mummynsu Rimsha kuma tana can boys quarters tana barci, daddynta baya nan, ya fita zuwa gidansu Abban Imran.
Kusa da gwaggo ta zo ta zauna tana faɗin "Gwaggo ina wayar tawa take? Ina so ne na ɗan yi abu da ita". Miƙa mata sabuwar wayarta da Areef ya saya mata gwaggon ta yi, tana faɗin "Nasan Saif zaki kira, to ki kirashi da wayata, numbersa ita ce a farko, dan ba jimawa muka yi waya da shi".
Okey ta amsa tare da karɓar wayar tana wani sunkuyar da kai na rashin kunya. Miƙewa ta yi ta nufi waje, da idanu suka bita suna mamakin yadda ta dawo dai'dai cikin hukuncin Ubangiji.
Kai tsaye bedroom na Lion ɗin ta nufa, ko'ina a gyare tsab tamkar yana nan. Saman bed nasa ta haye tare da rungumo pillow a kirjinta tana danna mashi kira. Wayar tana fara ringing ya katseta, dan ya ɗauka gwaggoce, shi bai san Meesharsa ta dawo dai'dai ba, yana kwance a saman katafaren bed nasa, daga shi sai singlet fara kal and short, sai wani lumshe idanu yake yi tamkar mai jin sha'awar wani abin, ya kara yin fresh da shi over, bin kiran ya yi tare da manna wayar a kunnansa...........
Kiran na shigowa ta ɗauka cikin zumuɗi, a nutse ta ce.........
*KADA KU MANTA BABU POSTING A WEEKEND, NA YI CANCEL NASA, IYA MONDAY TO FRIDAY ZAN RINƘA YI KAWAI YANZU.*
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E21
Date: 1/5/2024
Kiran na shigowa ta ɗauka cikin zumuɗi, a nutse ta ce "Hello Noorish". Yana kwance bai san time da ya mike zaune ba, kasa yarda da abin da ya ji kunnuwansa suka ji ya yi, anya ba gizo kunnuwansa suke yi mashi ba kuwa? Anya ita ce kuwa?.
Katse mashi tunanin nasa ta yi da cewa "Noorish ka fara ko? Sai mutun ya yi magana kaki amsa mashi da wuri ko?". Ta yi maganar a tsananin shagwaɓe sosai.
Calmly ya furta "My Meesha". Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin voice nasa ta yi tamkar an zuba mata zuma a baki, saboda daɗi, wani irin sanyi ne ya ratse zuciyarta, kara kankame pillow hannunta ya yi, cikin sanyin murya ta fara magana a shagwaɓe. "Noorish ka dawo daga Daular Mutuwa kuma ka fita baka tasheni daga barci ba, to ni yanzu kawai ka dawo gida ina son ganinka". Tana magana tamkar zata sanya mashi kuka.
"Meesha bana kasar ne, amma zamu rinƙa yin waya kin ji?".
Jin abin da ya ce yasa ta fashe mashi da kukan shagwaɓa tana faɗin "Shi ne ka tafi ka barni ko? Allah ni ban yarda ba, koma ina kake ka dawo na ganka, kewarka nake yi sosai". Tana magana tana kuka hawaye bibbiyu.
"My Meesha why kike son yin kuka ne? Do you know how sad am feeling idan kina kuka kuwa?".
Girgiza mashi kai ta yi. "Sorry Noorish, amma ai ina son ganinka ne".
Nisawa ya yi kafin ya ce "Same here, nima ina kewarki sosai my wife".
"To Noorish ka dawo mana kawai". Shiru ya ɗan yi mata kafin ya ce "My Meesha, dawowata yanzu ba zai yiwu ba, kuma zamanki a Nigeria yafi mani sauki da samun kwanciyar hankali, ina son kasancewar ki kusadani matuƙa, amma dole na barki a can".
Hawayen da suka cika mata idanu ne suka cigaba da gangaro mata a saman face nata, yanzu ta yaya zata iya yin barci ita kaɗai a wannan ɗakin? Ta tambayi kanta da kanta.
Jin ta yi shiru ne yasa ya ce "Meesha kuka kike yi ko?".
Da sauri ta kai hannunta tana ɗan goge hawayen nata, cikin shagwaɓa da sanyin murya ta fara yi mashi