Showing 90001 words to 93000 words out of 270744 words
kewar ɗan, Allah mai iko, abin mamaki dai baya karewa, sam babu kunyar gwaggo a tattare da Jehan, babu wani abin da ya sauya a yadda suke da, ita bata yi mata ma kamar gwaggonce ta haifi TRIPLETS ɗin ba, ita dai iya abin da ta sani shi ne, Gwaggo, gwaggonta ce, kuma abokiyar rigimarta, ta zuba mata shagwaɓa san ranta, ita kuma gwaggon ta biye mata, bayan haka ita bata wani san da cewa ana jin kunyar uwar miji ba.
Da kyar da suɗin goshi gwaggon ta samu ta shawo kanta, da kyar ta yi shiru, ta hakura ta dai'na kukan, sai dai fa na ciki na ciki, kewar dai babu abin da ya ragu, har wani zazzaɓi take ji.
Haka suka kasance har Anaya ma ta shigo ta same su, ita ma nata sabon babin kukan ta zo ta buɗe masu, yau dai suna ganin ikon Allah, haka suka fara rarrashinta ita ma, har sai da ta hakura ta yi shiru, daga haka kuma barci ne ya yi awon gaba da ita. Ba su suka farka ba har sai da gwaggo ta tashe su a kan lokacin sallar mangariba ta yi, su tashi su yi sallah su yi wa mazan nasu a addu'a. A nan ne Gwaggo ta ga abin mamaki abin al'ajabi. Wannan abin mamaki ba komai bane face Rimsha, tana tashi ta barci da aka ce ta je ta yi sallah, buɗar bakinta sai cewa ta yi menene kuma Sallah? Babbar magana.
Zaro idanu suka yi, gwaggon zata daka mata tsawa, Brr Naurat ta yi saurin dakatar da ita, saboda ta lura tamkar da kawai matsala a tattare da Rimshar, abin ku da manya, ƙwaƙwalwarsu da tunaninsu ba irin na yara bane, har ta harbo da akwai gagarumin matsala a tattare da jikar tata, wanda su gwaggon kuma basu gane ba.
Dan haka sai ta ce kowa ya je ya yi sallah, ita kuma Rimsha ta kwanta ta cigaba da yin barcinta, su kyaleta kada su sake yi mata magana. Da mamaki cike fal a fuskar gwaggon ta ce "Mummy sallah fa zata yi, kuma kice a barta kada ta yi? Ya haka kuma? Ai Rimsha yanzu idan ta ce ba zata yi sallah ba, to wlh da itace zamu karya mata kafa, dan ai ba yarinya bace tun da har da ciki a jikinta, uwa fa take shirin zama".
Jama'a ina ganin ikon Allah, karfi da ya ji gwaggo ta mayar da Rimsha mai ciki, ko me ta gani a jikinta da har ta dage a kan lallai ciki ne da ita? Ku tayani dubawa my readers, ita dai Rimsha bata taɓa yin sunna da Lion ba, har yanzu virgin ce ita, amma an zage a kan tana da ciki, to koma me dalilinsu na cewa hakan, lokaci zai nuna mana komai.
"Aisha tun da na ce ku bar Rimsha, to ku kyaleta kawai, idan kika cika matsawa, to ba makawa zaki tabka danasani mai girma, dan haka ku kyaleta ki je ki yi sallarki". Cewar Brr Naurat.
Okey kawai gwaggon ta amsa mata da shi, sannan ta miƙe tsaye tare da nufar toilet, ita kuma Brr Naurat ta karisa tashin su Jehan a kan su je su yi sallah.
In takaice maku wannan labari, Rimsha dai bayan wannan uban barci, to bata iya aikata komai, ko wanka bata yi, baiwar Allah, sai Allah ne kaɗan yasan menene matsalarta!.
Haka Brr Naurat ta rinƙa lallaɓata tana ririta ta, sai dai kuma ba abin da take cewa face su gaya mata su waye su? Bata sansu ba. Abin ya ƙullewa gwaggo kai, ita kuwa Brr Naurat sam bata damu ba, dan izuwa yanzu ta gama yardanwa kanta cewa jikar tata ba lafiya take ba, da akwai gagarumin matsala a kasa, hakan yasa bata wani damuwa.
Su Abba kuwa, suna can hankalinsu a tashe, sai adduo'i suke yi tare da bincikar ina Aseef, securitynsa Abban Imran ya kira a waya, ya sanyasu suka je suka shigar da report a kan ɓatar na Aseef, su kuma suna gida Lion ya hana fita.
A ɓangaren Aafia dai babu wani sauki, sai ma abin da ya cigaba na rashin lafiya, duk ta kara ramewa, ta bushe sosai, ta yi wani irin duhu mai munin gaske, abin gwanin ban tausayi, kuma har yanzu bata amsawa kowa komai, daga ido sai ido.
Akil, Imran da Irfan gabaɗaya tarewa suka yi a masallaci suna zubawa TRIPLETS addu'ar fatan nasara a tafiyarsu, Allah ya karesu ya dawo da su lafiya.
A ɓangaren Katsina gidansu Sadiq kuwa, Allah mai iko, shagon Yusuf dai sai kara bunƙasa take yi, yanzu har da fridge ya sanya a ciki, yana sayar da kayan sanyi, abubuwa sun cigaba, shi ma Sadiq Alhamdulillah, abubuwa suna tafiya mashi yadda ya kamata, sai dai kuma kullum yana cikin tunanin Jehan, bawan Allah, yana tsananin sonta, bai san cewa matar wani ce a yanzu ba. Maman Sadiq a yanzu abubuwa sun saukaka mata, girkinta har da nama da kifi, sau uku take girki a rana, gabaɗaya ta fita daga harkar baban Sadiq ɗin, dan dama baya tsinana mata komai, yanzu Allah yasa ƴaƴanta sun fara tsayuwa gam da kafafunsu, abu dai sai dai muce Alhamdulillah, wani lokaci har kaji biyu Sadiq yake sayo mata, ya yanka mata, ta gyara masu, ta zuba mashi miya mai shegen daɗi, Allah ya taimaketa ya bata ƴaƴan masu zuciyar nema da kuma zuciyar taimaka mata dukka biyu, dan wani yaron yana da zuciyar nema, amma kuma kuɗinsa bata ciwuwa, ba zai taimaka ba, ita dai ta yi sa'a, daga Sadiq ɗin har Yusuf ɗin burinsu kawai suga sun yi mata abu, su ganta a cikin tsananin fariniki suna kyautata mata, shi ne muradinsu, kuma hakan ce tasa Allah yake taimaka masu, komai suka saka a gaba, sai sunga dai'dai, dan uwa ba wasa ba!!! Uwa ba wasa ba!!! Uwa ba wasa ba!!! Ku ruke wannan da kyau, duk mai son yaga dai'dai, to ya sanya mahaifiyarsa farinciki, ko da iya murmushi kawai kasanya mahaifiyarka a rana, to ba makawa wannan rana ba zata wuce ba har sai wani abin alkhairi da zai sanyaka farinciki ya wanzu a gareka, bare kuma ace ka yi wa mahaifiyarka abin da har zata buɗe baki ta zuba maka albarka da ruwan adduo'i, haba ai ranar abin alkhairi da zaka fuskanta sai Allah ne kawai zai san adadinsa, ina mai kara jan hankulanku ƴan uwa, a kula da uwa, abi umarninta koda babu daɗi matuƙar bai kaucewa dokar Allah ba, hakan zai sanya muga dai'dai a dukkan al'amuranmu, mu jikanta, mu tausaya mata, iyayenmu sun yi mana komai a duniyarnan, komai muka yi ba zamu taɓa biyansu ba! Sai dai mu kwatanta iya abin da zamu iya sanyasu farinciki kawai.
To haka dai rayuwar su Sadiq take a yanzu, shi kuma baban nasu, gaula wanda ya rako maza duniya, yana can har iyanzu yana tare a gindin amarya, sai yadda ta ce haka za'ayi, yadda ta dama haka zai sha, naira na aiki, duk zaginsa da ƴan unguwa suke yi, wlh ko a jikinsa, haka Amarya zata yi mashi ɗinki, ko kunya baya ji zai saka kayan a jikinsa yana washe baki, Sadiq bakinciki kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu, yana ji yana gani idan baban nasa ya yi wa Amaryar ba dai'dai ba, a tsakar gida zata kwashe mashi duk wasu albarka dake a tattare da shi, ta tsine mashi, ta yi mashi zagin kare dangi, amma dan rashin zuciya, zuciya ta mutu, haka zai yi ta bata hakuri, kuma bata hana shi ya sake komawa gindinta ya tare, abin dai ba'a cewa komai, Sadiq dai ba dan mamansa ba, da yaronnan ya haɗiyi zuciya ya mutu, saboda kunci da bakin cikin irin wannan hali na babansa, yarinya karama kamar amaryar nan da bata wuce sa'arsa a wajen shekaru ba, ta tsaya tana cin mutuncin mahaifinsa, ai kunsan dole zai ji zafi, dan fa uba uba ne komai lalacewarsa, Allah Ubangiji ka bawa kowa iyaye masu zuciya, masu sanin yakamata, masu sanin darajar kansu, masu sanin mutuncin kansu, ba masu kwaɗayin duniya ba, Allah ka karawa namu muku iyayen lafiya, ka kuma saka masu da mafificin alkhairi.
Wannan shi ne rayuwar su Sadiq kuma. Idan muka dawo Kaduna kuwa, bayan sallar issha, Brr Naurat ce ta taka da kanta har izuwa part nasu daddyn Rimsha.
A lokacin suna tare da mum suna hirar duniya. A palo ta zauna tare da yi masu sallama. Jin cewa ita ce yasa dukkansu har su Abba basu ɓata lokaci ba wajen fitowa. Da mamaki suke kallonta har suka kariso izuwa in da take, a saman sofa kowannansu ya zauna, sai binta da idanu suke yi, suna jiran karin bayani.
Ta ɗan ɗauki mintina da a kallah za su kai biyar tana tunani ba tare da ta yi magana ba. Can kuma sai ta fara magana a nutse. "Nawazuddeen a gaskiya Rimsha tana cikin gagarumin matsala, kuma ga halin da muke ciki a yanzu, babu wanda aka yarjewa ya shiga gidan nan ko ya fita sai su Imran, Akil da kuma Irfan, suma dan tarewa da suka yi a masallaci ne, amma yana da kyau mu san matakin da zamu ɗauka, ba zai yi wu mu barta a cikin ciwo har haka ba, babban tashin hankalin ma shi ne rashin sallah, ba zai taɓa yiwuwa mu barta bata sallah ba har zuwa su Saif su dawo, dole kafin su dawo mu san abin yi". Ta kai karshen maganar tana jan doguwar numfashi tare da saukewa a hankali.
Har suna haɗa baki wajen cewa "Me kuma yake damunta?".
Nan ma shiru Brr ɗin ta ɗan yi, sai jinjina al'amarin a ranta take yi, abin ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai. "To bana ce ba, amma yanzu abin da za'ayi kuzo muje ku yi mata karatun Alqur'ani mai girma, ko Allah zai sa a samu sassauci, dan fa ikirari take yi ma na cewa ita bata sanmu ba, mun ce mata to shikenan mun ji bata sanmu ɗin ba, kuma mun yarda, amma ta tashi ta yi sallah, shi ne ta ce bata san shi ba, kunga kuwa ai akwai gagarumin matsala, da farko ma na ɗauka dukka laulayin cikin nata ne yasa ta ce bata sanmu ba, amma da ta ce bata san menene sallah ba, sai na fahimci ba batun laulayin ciki bane, wata matsa ce ta daban".
Shiru daddynta ya yi yana tauna zantukan na Brr, shi kuma Abban Imran cewa ya yi. "Gaskiya wannan matsala ce babba, bata san me sallah ba kuma? A dole mu nemi mafita, yanzu dai ina take? Muje sai muga me yakamata mu yi mata".
Haka suka rankaya izuwa ɗakin gwaggon, suka baro su mum ko wacce a ɗakin mijinta, bama su san me yake faruwa ba.
Har lokacin barci Rimshar take yi, tun abincin safe da ta ci, ƴar tahalikan nan bata sake sanya komai a cikinta ba, ko ruwa, da alama ciwon bayan ta yi breakfast ne ya bugeta, dan ba shakka ta yi sallar asuba lafiya lou.
Tana barci basu tasheta ba, dan Brr ta ce kada a tashe ta, su yi mata addu'ar a haka, dan haka sai suka fara yi mata topi ta ko'ina, duk suka haɗu a kanta. Ko motsawa bata yi ba, tamkar wadda babu rai a jikinta, ba dan sauƙar numfashi kaɗan kaɗan da suke ji nata ba, to da sai su ce babu rai a tattare da ita.
Sun ɗauki tsawon lokaci suna tofa mata addu'a, amma ko motsawa bata yi ba. Abin ya ɗan bawa daddynta mamaki, sai dai bai bayyana hakan ba, ya dai cigaba da yi mata topin kawai. Daga karshe Brr Naurat ta ce su barta kawai, zuwa gobe da safe In Sha Allah sai a kirawo su Imran a waya, su dawo gida a san abin yi.
Okey suka amsa mata, shi dai daddynta ya amsa ne kawai saboda mahaifiya ba wasa ba, basu ja da maganarta, amma ba dan haka ba, a daren nan ya so ya ɗauketa su je neman magani, dan abin ya ɗaga mashi hankali!!, Barema yanda ya ga fuskarta ta kara wani irin haske, ita da take chocolate color, to ta kusa kai Jehan haske a yau, ga face ɗin nata ya ɗan kunbura kaɗan, abin dai ba'a cewa komai, tana a cikin matsala ainun.
Da haka suka koma ɗakunansu, ita kuwa Brr Naurat ta gyarawa Rimshar kwanciya tare da rufa mata bargo, sannan ta ce gwaggo ta koma ɗakinsu Rimshar ta kwana da Jehan, su barta da Rimshar a nan.
Okey gwaggon ta amsa tare da cewa "Zan je ɗakin Saif na kwana kawai, kyale Jehan ɗin nan, ba zan iya rigimarta ba yau ɗin nan, dan sam yau bana jin daɗi". Ta kai karshen maganar tare da nufar kofar fita.
Kiranta Brr ɗin ta yi a kan ta dawo. Ba musu ta koma ta zauna, nasiha mai ratsa jiki Brr ɗin ta yi mata, dan tasan cewa ba wani rashin jin daɗin jikinta da take ji, kawai tunanin TRIPLETS nata ne ya sakata a gaba, ba dan Brr ɗin ma tana yi mata faɗa da nasiha a kullum ba, ai da abin sai ya fi haka. Sosai ta ji nasihar mahaifiyartata, ta kuma yi alkawarin In Sha Allah zata cire damuwar a ranta, za kuma ta kara tsananta masu addu'a sosai. Da haka suka yi sallama, ta wuce ɗakin Lion dan ta kwanta, ita kuma Brr Naurat ta gyara ta kwanta a kusa da Rimshar, baiwar Allah sai barci kawai take ta zubawa ba ci ba sha.
A ɓangaren Daular Mutuwa kuwa.
Sunci bakar wahala na kin karawa, sun azabtu kafin nan su kai wajen da Dr Salman ya ce masu hanyar take. Sai dai kuma ko da suka je wajen babu wata hanya a wajen, wayam wajen take.
Jugum jugum suka tsaya suna mayar da numfashi, ga kuma gine ginen gidan cigaba da rugujewa yake yi, idan har basu hanzarta nemo hanya ba, to har in da suke ma sai ya ruguje ya rufta da su.
Sauke Ayla daga bayansa Areef ya yi, sannan ya fara kewaye a wajen yana nema masu ko da akwai wata makama da zata nuna da alamar hanya ta sama ko ta kasa a wajen.
Ita kuwa Aylar, yana sauketa ta zube kasa a saman gwiwowinta, cikinta ne yake wani irin murɗa mata, tamkar cikin yana son fita daga jikinta ne, ta wahala ne aihun.
Sauke Akila shi ma Aseef ya yi, ita ma yana sauketa ta zuba kasa a saman gwiwowinta, tana mai da numfashi. Shi ma Dr Salman zama a wajen ya yi, saboda wajen tiles ne fari tas da shi, babu alamar kazanta a wajen.
Ganin hakan yasa duk sauran jama'ar da suka biyusu, suma sai suka zauna a kasa a wajen ɗin kawai.
Wasa wasa cikin Ayla na kara tsananta mata ciwo, tun tana dannewa har ta fara ruwan hawaye, sam Areef ko Aseef babu wanda ya lura da halin da take a ciki, sun tafi dubawa ko za su ga hanya a wajen.
Da AKILA ta ga yanda ta dafe cikin nata tana murkusoso, sai ta daure ta matso kusa da ita, cike da kulawa ta rungumota, daman kunsan ita Akila akwaita da son ƴan uwanta da dangi, tana da tausayi sosai. Haka ta rungumo Aylar tana tambayarta meyake damunta take kuka.
Kasa yin magana ta yi, Dr Salman ma matsowa kusa da ita ya yi, sun zaci wahalar hanya ce, sai suka fara ƙoƙarin rarrashinta. Sai kuma me, jini suka fara gani ya fara bin kafafunta. Sosai Akila ta tsorata, hakan yasa ta zunduma ihu tana faɗin "Heartbeat jini, jini matar bappa Maik take zubarwa sosai". A tsananin rikice ta yi maganar, saboda bata taɓa ganin jini na fita dayawa daga jikin mace har haka ba, shi ne abin ya tsoratata.
A tare Aseef ɗin da Areef ɗin suka juyo da kallonsu a kansu, da yake shi Areef ya fi su tausayi, a dubu ɗari ya nufo in da suke, dan ya duba me matsalar. Sai dai kuma bai kai ga karisowa ba, a dai'dai tsakiyar wajen, filin ta ɓurma da shi ya zurma kasa. Tashin sense, shikenan Areef ya rufta!.
Kafin Aseef ɗin ya yi wani yunkuri, ilahirin wajen gabaɗaya ya fara wani irin jijjiga yana ƙoƙarin ruftawa da su.........
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E16
Date: 26/4/2024
Kafin Aseef ɗin ya yi wani yunkuri, ilahirin wajen gabaɗaya ya fara wani irin jijjiga yana ƙoƙarin ruftawa da su.
Da Aseef ɗin ya ga haka, sai ya yi amfani da nasa tunanin, cikin ƙanƙanin lokaci ya binciko ƴar hanyar da take a wajen, a hanzarce yasa karfi ya buɗe kofar hanyar, ta cikin kasa take. Ya sha bakar wahala kafin ya buɗe masu, sannan ya ce su zo su fita ta wajen.
Ayla ba zata iya miƙewa ba, dan haka sai ya kamata ita da Akila da Dr Salman, ya ce da sauran mutane kuma su bi ta hanyar su tafi.
Da sauri suka fara dira a hanyar, shi