Showing 27001 words to 30000 words out of 270744 words

Chapter 10 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

4598

ɗin ya yi na ɗan tsawon lokaci kafin Brr Naurat dake zaune saman sofa ta ce "To yanzu ina son sanin wani abu guda a kan wannan case ɗin".

Ɗago kai dukkansu suka yi tare da kai kallonsu gareta. Lion ne ya amsa mata da cewa "No, just ki bar maganar nan a yanzu, ki bari sai gaba". Jinjina mashi kai ta yi, dan ta lura dukkansu basu a cikin nutsuwarsu.

Ɗago idanu da gwaggon zata yi ne idaunta suka sauka a kan chain dake wuyar Lion ɗin, wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa TRIPLETS ɗin suka ɗago suna kallonta. Su daddyn Rimsha har suna rige rigen haɗa baki wajen tambayarta lafiya.

Cool murmushi ta sakarwa daddyn Rimsha tana faɗin "Ina Jehan?". Da hannu daddyn ya nuna nata Jehan ɗin dake zaune kusa da Rimsha dake kusa da Brr Naurat.

Alama ta yi wa Jehan ɗin da hannu a kan ta zo. Da sauri ta miƙe ta zo. Tsabar iya shege irin na Jehan ɗin a saman cinyar gwaggon kusa da Aseef ta gefe ta zauna tare da saƙalo wuyar gwaggon da hannunta ɗaya, tana wani kwaɓe fuska, tana kuma raɗa wa gwaggon magana a kunne. Binsu da idanu Areef ya yi yana tunanin irin tsiyar da ya rinƙa yi mata a kan daddynta a baya, yanzu reshe ta juye da mujiya kenan........ E NIMA PRINCESS TEEMA NA CE RESHE TA JUYE DA MUJIYA KUWA, DAN GWAGGO DA JEHAN 5 AND 6 NE, LALLAI JEHAN ZATA RAMA ABIN DA KA RINƘA YI MATA NA HANATA ZUWA WAJEN DADDYNTA😂 YANZU WASAN ZAI FARA😂 KAI ABUBUWA SUNA YI MANI DAƊI😂 AREEF KA JIRA ƊAUKAR FANSA😎🥳 DAN WLH GWAGGO DAI TANA BAYAN JEHAN💃🥳

Kome Jehan ɗin ta raɗa mata sai ga gwaggon ta fashe da dariya tana kallon Areef. Daga gani yasan gulmarsa ta kai, da wani idanunta kamar ball a cewarsa. Hannu gwaggon ta kai ta ciro sarkar dake wuyar Jehan ɗin, dama kun san nasu Jehan mai round ne, na su Lion kuma mai tambarin heart, sannan na su Jehan ɗin yana da faɗi fiye da na su Lion ɗin, kuma na su Lion zallar zinari ne, na su Jehan iya igiyar ce kawai zinari.

Ciro sarkar Jehan ɗin ta yi a in da ta sanya karfi cikin dabara ta buɗe kan round na sarkar. Nan take wani tambarin ɓari na heart ya bayyana a cikin round ɗin, sai kyalli yake yi har yana ɗaukar idanu. Ciro heart ɗin ta yi sannan ta mayar da sarkar ta rufe tare da mayarwa da Jehan ɗin abinta.

A hankali ta ambaci sunan Lion, ɗagowa ya yi yana kallonta. Kama sarkar wuyarsa ta yi tare da sanya ɓarin heart ɗin da ta ciro daga sarkar Jehan ɗin, ta mayar ta jona. Nan take chain ɗin ya koma tamkar ba'a taɓa raba shi biyu ba, ya zama kamar yanda yake. Sam Lion bai yi mamaki ba, dan yasan ita ce mahaifiyarsu, kuma dama yasan a wajenta kawai za'a sami rabin sarkar nan, dan har company ya je sun kasa buga mashi ɓarin da zai yi dai'dai da chain ɗin, daga karshe dai ya hakura ya bar zancen kawai, ashe yana jikin sarkar Jehan, gwaggo ta iya ajiya a in da kowa ba zai zata ba, kuma duk in da za su je yana tare da su.

Cikin shagwaɓa Jehan ɗin ta ce "Gwaggo dama ashe abu kika ajiye a ciki kenan? Shi ne har da wani cemini ko za'a kasheni kada na yarda na bada sarkar nan ko? Wato yanzu dama a kan wannan abin ne har da cewa ko za'a kashe ni ko? Allah na ɓata dake". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa dan ta bar wajen.

Sake baki Areef ya yi yana kallon ikon Allah, mamaki yake yi, ashe dama ƴar rigimar nan tasa ta iya shagwaɓa kenan? Ashe da gangan take yi mashi abu kamar wata boss? Ai kuwa zai yi maganinta, ya faɗa a ransa. Bai san cewa da iya gwaggo kawai take shagwaɓar ba, bayan gwaggon ba wanda yake ganin hakwaranta ma bare shagwaɓa, sai daddynta da shi ma ba koda yaushe ba, sun fi shiri da gwaggon, mum nasu kam dama kun sani basu wani shaku ba, dan ita ta gwaggo ce.

"Haba babyn gwaggo da daddynta, zo kiji wata magana". Cewar gwaggon. Kin zuwa ta yi ita a dole ta yi fushi, fuuu ta wuce zata bar wajen.

Da hannu ɗaya Areef ya rikota yana faɗin "To ƴar rigima, ke kowa sai kin yi mashi ne? Sai kin nunawa kowa halinki ko?". Gwaggon ce ta ce "A'a babu ruwanka da babyna, tare ka ganmu, ka kyale mani ita, kada ka takura mata, ba wani rigimar da tayi, haka take dama".

A takaice ya ce "Momma to ai ni kuma matata ce, kin ga yanzu na kwace maki ita kenan".

Zaro idanu ta yi tana faɗin "Jehan ɗin tawa ce matarka? Waye ya baka ita? Wlh ba zata saku ba, a kan me? Ni ni zan bada auren Jehan, duk wanda ya bayar ba ni ba, to auren bai ɗauru ba".

Jawo Jehan ɗin ya yi ya faɗa jikinsa yana faɗin "Momma uncle nane mana nima ya bani ita, ƴar rigima ba, kuma aure ya ɗauru, dan ma kin dawo da wuri ne, ai da sai dai ki zo ki ganta da ciki ko baby's".

Salati gwaggon tasa, sam ƴaƴan nan nata basu da kunya ko kaɗan, shi ko kunyar iyayen Jehan ɗin su Abba da suke cike a wajen bai yi ba, kawai ya faɗi son ransa ne.

Cikin fushi Jehan ɗin ta ce "Ni ka sake Ni!" Yanda ta yi maganar on a serious note, babu wasa a cikin maganarta, ya sha mamaki na jin abin da ta ce, sai dai bai kawo komai a ransa ba, kuma bai saketa ɗin ba, ita ma Gwaggo yanda Jehan ɗin ta yi maganar yasa ta fahimci da akwai matsala kenan a tsakaninta da Areef ɗin, kowa da yake palon harta daddyn Rimsha ya sha ruwan mamakin yanda Jehan ɗin ta dakawa Areef ɗin tsawa, ko a baya da take cewa bata son shi, bata taɓa yi mashi irin wannan magana a gatse har haka ba, ita kuwa ita kaɗai tasan dalilin da yasa ta yi mashi wannan magana.

Gwaggon na ƙoƙarin kara yin magana Aseef ya katse su da cewa "Areef ka tuna mini ma, na ce yau zan yi wa Heartbeat surprise, har kasa na ji saukin jikina da ka tuna mani". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana wani mustsuke idanu kamar wanda ya sha wani abin na maye.

Shi dai Lion kamar babu shi a wajen, ya dukar da kai kasa kawai yana tunani.

Da mamaki gwaggon ta ce da Aseef ɗin "Au kaima matar gareka?". Jinjina mata kai ya yi tare da matso da bakinsa saitin kunnenta yana mata raɗan akan ai yau ma yake son bawa matar tasa baby.

Hasbunallahu. Kasa juyowa gwaggo ta yi bare ta haɗa idanu da shi, a hakan ma bata san cewa ya yi mata raɗan ne dan kada Akilar ta ji ba, ba dan Akilar tana wajen ba, ai da afili zai faɗi maganarsa, yo su ina ruwansu? Ina suka san me kunya? Ai sam basu san shi ba. Turawa ma da suke wasu abubuwa marasa ɗa'a a kan tsakiyar hanya, ai su nasu ma mai sauki ne, turawa ai iskancinsu a bayyane yake.

Kawar da zancen gwaggon ta yi da cewa "To gaskiya wannan aure dai bai ɗauru ba, dan ni ban bada Jehan da Rimsha ba!".

Areef zai yi magana daddyn Rimsha ya katse shi da cewa "A'a ni ai na bawa ɗana, kuma aure ya ɗauru, dan haka ba wani sharhi, Jehan matar Areef ne".

Kafewa gwaggo ta yi a kan ita sam bata bayar ba, dole a zo a tsugunna a gabata a nemi aure Rimsha da Jehan, kuma sai ta tantance masu neman auren zata ba su, sai ta yi musu jarabawa masu tsanani tsauri, idan sun ci, sai a basu mata, idan ba su ci ba, shikenan ta rike ƴaƴanta, ta nema masu miji na gari.

Ganin Lion yana ƙoƙarin mikewa ya bar wajen ne yasa gwaggon ta ce "Saif zauna mu yi magana ko?".

Ba musu ya koma ya zauna yana faɗin "Mummy my head is penning me to much, bana son hayaniya, idan kuna yawan magana bazan iya zama a wajen ba, that's why nake son baku waje!".

Hannu ta kai ta shafa kan nasa tana faɗin "Tom shikenan zamu yi maganar anjuma, je ka huta yanzu ga ji?". Ba tare da ya amsa ba ya miƙe ya fuce daga ɗakin abinsa.

Shi kuwa Areef raɗa ya fara yi wa Jehan a kunne bayan ya matseta a jikinsa. Babu kunya a gaban gabaɗaya iyayenta. Ita kuwa ko kallo bai samu ta ɗago ta yi mashi ba, haushinsa ma take ji, burinta kawai ya saketa, shi kuma yaki, ya kankameta gam kamar wani ya ce zai kwace mashi ita.

Nan fa hira ya ɓarke a cikin bedroom ɗin, ga Brr Naurat a wajen, ai sai ta fara basu labarin rayuwarta a Russia, su kuma suka gaya mata bayan tafiyarta Dr Salman ya rasu. Nan take ƴar tsohuwa ta fara kuka. Taruwa suka yi a kanta suna bata hakuri. Jikokin nata kuma sai dariya suke yi mata, wai ta tuna da tsohon zuwa, Imran da Irfan sai tsiya suke yi mata.

Lallaɓawa Anaya ta yi ta fice daga cikin bedroom ɗin. Tamkar wata ɓarauniya haka take sanɗo. Palon kasa ta sauko, sai waige waige take yi tana neman Mark, dan ɗazun da suka shigo da daddynta, ta gan shi a palon kasan, ba halin ta yi mashi magana ne saboda daddynta. Shi kuma bai ganta ba, yana latsa waya, ba sai na sake gaya maku ba, irin halin Lion ne da Mark, abin da yake gabansu kawai suke yi, so ko mutun zai wuce ta kusa da su, sam basu ɗago kai bare su kalle shi, hakan tasa har su Anaya suka haura sama bai ɗago kai ba.

Ta zo zata nufi waje ta hango shi a cikin kitchen yana aiki, wani irin tsantsar farinciki ne ya rufeta, sai sakin cool murmushi take yi. Cikin sanɗo ta lallaɓa izuwa cikin kitchen ɗin.

Sarai ya ji alamar mutun, dan su suna amfani ne da sautin numfashi mutun, dan sun iya yakin sunkuru. Amma bai kawo cewa ita ba ce, ya yi tunanin Rimsha ce ko Jehan or Akila, dan sune kawai masu shigowa cikin kitchen ɗin.

Hatta kariso kusa da shi bai juyo ya kalli wacece bane. Hannu ta sa ta tsaƙalo wuyarsa tare da ɗale jikinsa ta baya tana murmushi. A tsananin fusace ya juyo tare da damko wuyarta, ya dawo da ita ta gaban fuskarsa.

Ta yi matukar razana na ganin yanda ya shaketa ɗin, nan take idanunta suka firfito waje, ta tsorata ainun, kirjinta sai dukan uku uku yake yi.

Yana kawota saitin face nasa ya ga ashe ita ce, ga shi ta zaro mashi idanu tamkar za su faɗo kasa. Ai a dubu ya sake wuyar tata yana ɗan sunkuyar da kai kasa. Sam bai taɓa tunanin ita ɗin ba ce.

Ganin tana ƙoƙarin zubawa kasa ne yasa a hanzarce ya rikota tare da jawowata jikinsa yana faɗin sorry. Ya yi maganar tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya, wani irin sanyi ya ji na jinta a jikinsa.

"Haba my shi ne kake son kashe ni? Dan kawai nazo ganinka ko?". Ta yi maganar tamkar zata saka mashi kuka, tana yi tana turo baki.

Cikin sanyin murya bawan Allah kasa kasa ya ce "Sorry my Queen, ban san ke ba ce ai, am so sorry". "Ni gaskiya ba zan hakura ba".

Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin daga bisani ya matso da face nasa daf da tata, kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Zaki fara ko? Wai har yanzu ba zaki dai'na wahalar da ni ba? Haba mana, kullum fa a waya sai kin yi ta yi mani kuka, kuma kin san bana son hakan, sai ki yi ta bani wahala, yanzu a zahiri ma ba zaki barni na huta ba?".

(My peoples yau ga Mark ma da cewa mace sorry 🤔 duniya kenan😂 kai waye ya taɓa tunanin Mark da Lion za su furta wannan kalma ta sorry ga wani ma ba wata ba?🤔 Lallai mata mun ciri tuta, mu ɗin duniya ne, duk giman namiji da karfi izza da isarsa, muna iya juya shi son ranmu😂 dan haka dole a bimu 😂)

Turo ɗan bakinta ta yi har sai da ta taɓa nasa, kasa kasa ita ma ta ce "Ai kai ne, sai ka yi ta yiwa mutun wani irin hali na basawa da bana ganewa". "Am so sorry zan dai'na duk abin da baki so kin ji ko? Amma a dai'na yi mani fushi da kuka please".

Tana ƙoƙarin sake yin magana suka ji motsi a bayansu. Da sauri ya saketa, suna juyowa a tare, dan su ga wanene.

Brady ne ya zo taya Mark ɗin aiki. Ajiyar zuciya Anayar ta sauke tare da wucewa da sauri, dan ta fice daga kitchen ɗin kada ma daddynta ko wani daga cikin family ya ganta.

A hanzarce ya riko hannunta yana faɗin "Haba mana, ina kuma zaki je?". A takaice ta ce mashi cikin ɗaki zata koma, dan kada ma a nemeta, dama ta zo ganin shi ne kawai, tana tsananin kewarsa.

Sake jawota jikinsa ya yi yana faɗin "Haba my Queen, bari na ɗan ganki tukun nan mana, kin san yanda nake kewarki kuwa? Please ki bari na ganki ko da na 1 hour ne".

Sakalo wuyarsa ta fara kokarin yi, amma ina bata kai shi tsawo ba, ko ta sakalo ba zata iya tsayuwa a hakan ba, dan ko ta ɗaga kafa ba zai yi mata dai'dai ba.

Ganin hakan yasa shi ya ɗan rankwafo mata da kansa kaɗan yana faɗin "Ƴar karama da ita a wajen, ba tsawo". Turo baki ta yi tare da jan gashin kansa ta wajen bayan wuyarsa.

Wash ya ɗan furta kafin ya matseta a jikinsa da karfi. A can cikin bedroom ɗin Lion kuwa, sai hira ake yi, tamkar za su cinye junansu saboda tsantsar so da kauna, sai dai ko kaɗan basu taɓo hirar abin da ya faru a baya na dan gane da rayuwarsu Abba, ma'ana rayuwar gidan Dr Salman na baya, sam basu taɓo wannan hiran ba, saboda yau suna cikin tsantsar farinciki, ba su son tuna abin bakinciki. Shi dai Aseef ya makale a jikin mommansa abinsa yana ta zuba mata shagwaɓa, shi kuma Areef sai tsokanar Jehan yake yi bayan gwaggo ta gama gabatar masu da gabaɗaya uncles nasu. Shi kuma daddyn Rimsha da daddyn Anaya tamkar za su haɗiye juna, saboda kauna.

Haka suka kasance har tsawo good 2 hours, kiraye kirayen sallar mangariba ne ya tashe su daga hirar ta su.

Mazan suka wuce masallaci, matan kuma suka nufi bedrooms na su Rimsha. Ƴan matan kuma wato su Rimsha, suka wuce bedroom na daddynta dan su yi alwala a can. Gwaggo dai a nan ɗakin Lion ɗin ta yi alwala. Shi kuwa Lion tun da ya bar ɗakin, basu sake jin ɗuriyarsa ba.

Rimsha tana shiga cikin toilet dan ta yi alwala, ta samu waje a saman chair, ta zauna ta fara tikar kuka kamar wadda aka yi wa sakon daddynta ya mutu.......... To fa kukan me kuma take yi hakan? Mu je dai zuwa.

Ita ma Akila lokacin da ta shiga toilet ɗin da nufin tayi alwala bayan Rimsha ta fito, sai da ta yi kuka kamar ba gobe. Ita dai Jehan ko a jikinta, alwalarta ta yi ta fito. Umaisha ciki ya fara girma sosai, sai tura abinta take yi.

Bayan sun yi sallah sun dawo ne aka haɗu gabaɗaya a palon sama. Nan fa su Abba suka ce za su wuce gida, kuma za su wuce da Brr Naurat. Suna cikin yin magana sai ga Lion ya shigo. Kusa da gwaggon ya zauna, kasa kasa ya tambayeta ya ta wuni?. Da fara'a ta amsa mashi da lafiya. Dawo da kallonsa a kan Areef ya yi kafin ya ce "Where is dad?".

Yana bedroom nasa Areef ɗin ya bashi amsa. Jinjina kai ya yi ba tare da ya sake yin magana ba.

Gwaggo ce ta gaya Lion ɗin uncles nasu za su koma, amma tare da ita za su tafi, kuma za su tafi da Brr Naurat. Girgiza kai ya yi yana faɗin "No momma, ke kina nan, kuma ita ma grandma a barta a nan!".

Abban Imran ne ya karɓi zancen da cewa "A'a ita A'isha ta zauna a nan ɗin, dan kuna da bukatarta fiye damu, amma ita Brr zamu tafi da ita, dan mun fiku bukatarta muma, muna da bukatar mu zauna da ita, akwai abubuwa da dama da zamu tattauna da ita".

Shiru ya yi bai sake cewa komai ba, gwaggon ce ta sake cewa, to shikenan hukuncin da Abba ya yanke ya yi. Miƙewa Lion ɗin ya yi tare da wucewa bedroom nasa abinsa. Cikin hanzari Areef ya bi bayansa, shi kuwa Aseef har wa yau yana kwance ya tada kai da cinyar gwaggon abinsa.

Shiryawa su Abba suka yi, gabaɗayansu suka wuce izuwa gidan Abba, Jehan, Rimsha, Akila, duk sun bisu, sun bisu ba tare da su Abba sun sani ba, dan a motar Imran suka shiga, shi kansa Imran ɗin bai lura ba, dan familyn dukka sun haɗu, kuma shap ya mance da cewa su fa matan TRIPLETS ne.........

Bayan anyi sallar isha, gwaggo ta idar da sallah a bedroom ɗin Lion, tana zaune a saman dadduma, su kuma sun tafi masallaci.

Tana zaune a wajen har suka dawo, bakinsu ɗauke da sallama suka shigo cikin ɗakin. Su ukun dukka gwanin ban sha'awa. Fuska ɗauke da murmushi ta amsa masu sallamar tana mai binsu da kallo. Wani irin tsantsar farinciki na wuce misali take ji a tattare da ita, har wani ji take yi kamar ta mayar da su cikin cikinta, dan so da kauna.

A bakin bed Areef da Lion suka zauna, shi kuwa Aseef saman bed ɗin bakiɗaya ya haye ya kwanta. Zubawa mahaifiyar tasu idanu suka yi suna ta kallonta. Sai zuba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login