Showing 24001 words to 27000 words out of 270744 words
yake yi, ran maza ya ɓaci!.
Shi kuwa Aseef miƙewa ya yi daga kwanciyar da ya yi daga saman cinyar daddyn Rimsha, ya kifa kansa da jikin hannun sofa yana hawaye, sam baya son ganin abin da yake faruwa.
Sosai Lion ya shake daddy har sai da idanunsa suka juye, harshensa ya zazzago waje, yana daf da bakontan lahira. Ga shi Lion ɗin yaki ko da sassauta mashi, kuma ya ki yin magana, saboda tsananin ɓacin rai, dan daddy yana neman raina masu wayo.
Can kuma cikin tsawa ya ce da daddyn nasa. "Tell us the truth, if not I'll make you regret! Me muka yi maka da zaka yi mana haka? Me bamu yi maka ba? Saboda kai muka ɓoye cewa mun musulta na tsawon shekara ɗaya yanzu, duk gudun kada mu sa ciwonka ya tashi, dan mun sanka da kishin addininka, zaka iya mutuwa idan ka ji mun zama musulmai, saboda kai muka ɓoye hakan! Duk dan mu faranta maka rai, mu kuma sauke hakkin iyaye da yake a kanmu, amma kai kuma ka gaya mana meyasa ka yi mana haka? Meyasa ka bari muka taso cikin kafurci? Ka yi mana karya! Ka ɓoye mana ainahin mahaifiyarmu, ka haɗamu da wata banza a matsayin uwa, bayan kuma sisterka ce uwa ɗaya uba ɗaya! Ka cutar da rayuwarmu! Ka cusa mana tsanar abubuwa da dama a rayuwarmu wanda bai kamata mu tsanesu ba! Ka ɓoye mana gaskiya, amma da yake, ita gaskiya komai daren daɗewa sai Allah ya bayyanata, sai ga shi Allah ya haɗani da Imran, na kaunace Imran sosai! Bana son kowa bayan TRIPLETS na, amma rana tsaka na tsinci kaina da son Imran, ta dalilinsa na dawo ainahin addinina, ta dalilinsa na tako kafata na zo Nigeria, wanda a baya ban taɓa tunanin zan zo ba, da Allah ya tashi kamaka daddy, kai ma da kafarka ka tako kazo Nigeria, ba wanda ya sanyaka dole, daga kan Imran kuma ban sake kaunar wani ɗan adam ba sai Uncle ɗin James, haka kawai shi ma rana tsaka na kaunace shi, har mamaki nake yi wani lokaci, na kasa banbance da shi da Imran wa ye na fi so a cikinsu, ashe dan Allah ya gwada mana wani aya ne yasa muke kaunarsu......". Da kyar ya kai karshen maganar saboda wani tukukin bakin ciki daya tokare mashi maƙoshi. Daga haka ya yi shiru bai sake yin magana ba, sai dai sauke dogon numfashi tamkar gurnanin zaki da yake yi, ya kuma kara shake daddyn da karfi sosai!!.
Kallon Areef Abban Imran ya yi cike da tsananin tashin hankali ya ce "Areef ka dakatar da ɗan uwanka, idan ba haka ba, zai yi kisan kai, dan daddynku dab yake da ya mutu!".
Ganin da gaske hakan ne yasa Areef ɗin ya nufi Lion ɗin da sauri dan kuwa da gaske ne daddyn nasu na dab da mutuwa.
"Lion wlh zai iya mutuwa, dan girman Allah ka sake shi haka nan ya isa, ba kaga yanda yake numfashi ba ne?".
A wani irin haukace ya damko wuyar Areef ɗin ma, da ɗayar hannunsa, ya haɗesu su dukkansu biyu yana jin wani bakin azaba a cikin zuciyarsa, tafarfasa zuciyarsa take yi tamkar an ɗaura dalma a wuta! Sam baya ji kuma baya gani, idanuwansa sun rufe, yau ne ya fito da ainahin zuciyarsa fili! Duk wajen an rasa mai iya gigin yi mishi magana, dama Areef ɗin ne kawai yake da ɗan kwarin gwiwar tinkararsa a irin wannan yanayi da yake ciki, to shi ma ga shi ya haɗa da shi ya shake. Aseef kam dama tun ɗazun daya kifa kansa da jikin hannun sofa, bai sake ɗagowa ba, duk abin da suke yi yana jinsu, amma ba zai iya ɗagowa ba, bakinciki zata iya sanyawa ya haɗiyi zuciya ya mutu idan ya ga halin da suke ciki, to gara mishi ya cigaba da runtse idanuwansa kawai zai fi mashi alkhairi, Rimsha, Jehan da Akila dukkansu guduwa suka yi, suka fita daga palon, ko wace ta san halin masoyin nata sarai, sun san me zai biyo baya idan suka tsaya, gara musu su gudu abinsu.
Yau su Abba sun ga tashin hankali, an rasa mai bakin magana a cikinsu, su Imran duk sun haɗa malaman jikinsu waje guda, dan faɗar ta manya ce!!, TGA da yake jarumi ma, kirjinsa sai dukan uku uku yake yi, cikinsa na murɗawa, bare kuma saura, ai su tsoronsu a tsananin bayyane ma yake.
Daddyn Rimsha ne kawai mai ɗan kwarin gwiwan da ya kalli Gwaggo ya ce mata ta yi wa Lion magana wata kila zai ɗan sassauto ya sakesu, idan ba haka ba to tabbas dukkansu zasu mutu, wlh har Areef ɗin, dan ba shakar wasa ya yi musu ba.......
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E5
Daddyn Rimsha ne kawai mai ɗan kwarin gwiwan da ya yi ta maza, ya kalli Gwaggo ya ce mata ta yi wa Lion magana, wata kila zai ɗan sassauto ya sakesu, idan ba haka ba, to tabbas dukkansu zasu mutu wlh har Areef ɗin, dan ba shakar wasa ya yi musu ba.
Ganin da gaske har da Areef zai iya mutuwa ne yasa ta miƙe da sauri ta isa wajen nasu.
Shi kuwa Areef ɗin sam bai yi ƙoƙarin kwatar kansa ba, dan yasan duk bala'i Lion ba zai taɓa kashe shi ba! In yaga zai mutu da gaske, dole ya sake shi, sai kawai ya zuba mashi idanu yana kallonsa, kuma dama hakan shi ne dai'dai a cewarsa, ya kamata su koyawa Lion ɗin tausayi ne, idan Areef ɗin ya zuba mashi idanu yana kallonsa, to zai ji tausayinsa ya sake shi, a haka zai koyi tausayi sosai a cewarsu.
Daga ɗan bayan Lion ɗin ta tsaya, gabaɗaya idanun jama'ar palon yana a kansu, kowa so yake ya ga ya Lion zai yi idan gwaggo ta yi mashi magana....... Ni ma PRINCESS TEEMA so nake yi naga ya zai yi😂
"Saif" ta ambata a hankali, tamkar bata son yin magana, kuma kamar tana jin tsoron yi mashi maganar.
Hakika ya ji sunan har cikin ransa, duk fushi da yake ciki bai hana ya ji muryar mahaifiyar tasa ta ratsa dukka ilahirin jikinsa ba, dama shi already zuciyarsa ta yardan mashi cewa ita ce mahaifiyarsu!.....
Ganin bai amsa ba, kuma bai sakesu bane, yasa ta ɗan kara mastowa, gabaɗaya a tsorace take da ganin yanayin da ɗan nata ya shiga, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, amma hakan bai hana ta daure ta dafa kafaɗarsa da hannu ɗaya ba. Cikin sanyin murya ta ce "Saif ka sakesu, kada ka yi masu illa ka ji ko?".
Wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, har cikin kashi da ɓargonsa ya ji sakonta! Ya ji sautin muryarta!. Ba musu ya zame hannayensa daga wuyoyin nasu. Nan take suka zube kasa, shi daddy ya suma already dama, shi kuma Areef tari ya fara yi da karfi karfi ba kakkautawa.
Uwa kenan, yau Lion ne yana cikin tsananin fushi haka har ayi mashi magana, kuma ya ji maganar ta ratsa shi? Lallai dai kam, uwa ta wuce wasa wlh!!.
Da sauri daddyn Rimsha ya yi kan Areef ɗin bayan ya ɗauko mashi ruwa a cikin fridge mai sanyi. Cike da kulawa ya dafa shi tare da kafa mashi robar ruwan a baki yana yi mashi sannu.
Shi kuwa Lion juyawa ya yi da nufin ya bar wajen, ya nufi bedroom nasa. Riko hannunsa ɗaya gwaggon ta yi, tana mai sake ambatar sunansa kirjinta na bugawa, dan tana tsoron kada su ce ba za su karɓeta a matsayin uwa ba, idan hakan ta kasance ba makawa zata iya mutuwa, dan tana bala'in sonsu, ko wani rana na duniya sai ta yi masu addu'a da fatan alkhairi tare da fatan Allah ya tsare mata su a duk in da suke, daidai da second guda basu taɓa barin cikin tunaninta ba, suna ranta fiye da tunanin mai tunani..... Allah sarki abin tausayi!.
Juyowa ya yi gareta cikin natsuwa, zuba mata idanu ya yi na ƴan sakanni kafin kuma ya tsinci kansa da rungumeta a jikinsa.
Rungume shi ita ma ta yi, tare da sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya mai cike da tarin abubuwa kala kala a cikinsa. Nan take kuma ta fara ruwan hawaye. Wani irin sanyi shi kuma ya ji tana ratsa zuciyarsa da ya rungumeta, hakan ce ta kara tabbatar mashi da cewa lallai ita ce mahaifiyarsu, domin kuwa tun da ya taso har izuwa yau, ba'a taɓa rana guda da ya shiga cikin fushi da ɓacin rai, ace zuciyarsa ta yi sanyi lokaci guda ba, ba'a taɓa ba! Wani lokaci ma, idan ya fusata sai ya zubawa tsakiyar kansa ruwan mai tsananin sanyi, saboda ya sami sauki, dan tamkar ci da wuta zuciyarsa take yi idan ransa ya ɓaci. Amma yau rana ta farko, ya shiga ɓacin rai, daga jin voice na gwaggo kuma ya sauko cikin sauki haka, dole ba'a banza ba! Dole ita ce mahaifiyarsu ta gaskiya! Ya sami nutsuwa sosai a kanta! Yana tsananin jinta a ransa ne fiye da tunanin mai tunani! Ji yake yi tamkar ya ɗauketa a saman kafaɗarsa su yi ta kewaye duniya kawai, saboda tsantsar so da yake yi mata, ashe ba'a banza yake kaunar Rimsha ba! Ashe ba'a banza ba duk da basu son mutane, amma suka yarda da daddyn Rimsha ya zauna a wajensu, sannan kuma suka kaunace shi sosai! Ashe ba'a banza ya ji cewa dole ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya kwatarwa da daddyn Rimsha hakkinsa na zaluntarsa da aka yi ba. Ba'a banza su Areef suke tsananin kaunar daddyn Rimsha ba, ko dan kula da mahaifiyarsu da ya yi tamkar ba gobe, ai dole ma su ji kaunarsa, uwa ta wuce wasa!!. Daddyn Rimsha ya kula da gwaggon over, shiyasa Allah dan ya saka mashi, ya jarrabi TRIPLETS ɗin da kaunarsa over!. Allah sarki rayuwa kenan, Allah mai kyauta mai kari, mai saka maka ta in da baka yi zato ba, Shiyasa ake son komai zaka yi, to ka yi shi domin Allah, dan idan ya tashi saka maka, zai yi maka babbar sakayyar da baka taɓa zato ba, a gaskiya daddyn Rimsha ɗan uwa ne na kirki da kowa zai yi fatar samun irinsa, duk bakinciki da kunci da su Abban Imran suka jefa shi a ciki, suka raba shi da mahaifinsa da Hassan nasa da suka kwanta ciki ɗaya, duk da hakan bai hana shi yana taimaka masu ba, kuma dan Allah yake yi, shiyasa da ya gamu da jarabawa na rabuwa da familynsa, sai Allah ya kare mashi familyn nasa, suka shiga hannun na gari, duk in da suka je, an rukesu hannun biyu tsakani da Allah, dan shi ma ya ruke mutane da yawa tsakani da Allah, bugu da kari, sai Allah ya bashi surukai ɗaya tamkar da million, wanda ko wani uba zai yi wa ƴaƴansa fatan samun mazajen aure irinsu, Allah ka cigaba da dafa mana, kasa komai zamu yi, mu yi shi domin ka, dan mu samu rahamarka a koda yaushe.❤️
STORY
A hankali ya kwantar da kansa a saman kafaɗar gwaggon, yana sauke numfashi mai kama da gurnanin zaki. Hannu ta kai ta fara shafa lallausan gashin kansa, da yake ya rage tsawonsa ne, ya ɗan kwanto a kafaɗarta, to tana iya taɓa kansa.
Jin sautin kukan gwaggon yana tashi a hankali hankali ne yasa ya ɗan ɗago kan nasa daga saman kafaɗar tata. Ganin da gaske take kuka ne yasa ya sanya hannu ya fara goge mata hawayen nata ba tare da ya yi magana ba.
Tamkar jira take yi wani sabon kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ne ya kubce mata. Zafafan hawaye ne wasu suna bin wasu a kuncinta. Hakika an cuceta ba kaɗan ba, an cutar da rayuwarta ba karya, kuma a duk wannan abin da ya faru, sam bata da laifi, duba da yanayin karantar shekarunta a lokacin, ga ƙarancin ilimin addini, sannan bata wani rayuwa da mahaifiyarta sosai ba, bata taɓa haihuwa ba sai a kan TRIPLETS ɗin, a lokacin da ta mayarwa da Dr yaran, bata gama sanin zafinsu ba, sannan zuciya ce ta ɗebeta, wanda kuma dama wannan dole ce, tama yi namijin kokarin da ta hakura ta haife cikin, duk cin amanar da ya yi mata, ta daure ta haife cikin, gaskiya ta yi namijin kokari, abin a jinjina mata nema!!.
Ganin haka yasa ya ɗan raba jikinsu kaɗan tare da ɗan duƙawa ya ɗauketa cancak tamkar karamar yarinya, ya nufi bedroom nasa da ita. Gabaɗaya palon binsu da kallo suka yi, shi ma Areef binsu da kallo ya yi ya kasa motsawa, dan shi kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyarsa. Shi dama Aseef bawan Allah sam bai ɗago kai ba ma, bare yasan me suke yi, yana kife yana kuka, Allah sarki bayin Allah!.
Ita ma Brr Naurat sai bin su da idanu take yi, tana jin abin tamkar a mafarki ne!.
Lion bai sauke gwaggo a ko'ina ba, sai a bakin katafaren bed nasa da yake shinfiɗe da white bed sheet mai matuƙar kyau da tsada, kamar yanda kuka sani ne, sai zuba uban daddaɗar kamshi bedroom ɗin nasa yake yi, ko'ina a gyare tsab, tsab, fes, fes!!.
A gefenta ya zauna tare da ɗan juyowa suna fuskantar juna. Hannayenta ya riko cikin nasa, har lokacin zubar da hawaye take yi tamkar famfo aka bude. Cikin nutsuwa da sanyi murya ya ce "Ba zan hanaki kuka ba, ki yi sosai, dan yana rage raɗaɗi, na san duk raɗaɗin da muke ji a yanzu, ba mu kai kwatan naki ba, so just cry, cry more!". Ya kai karshen maganar tare da sakin hannayen nata ya rungumota a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya.
Kankame shi sosai ta yi tana mai cigaba da kukanta yana sauraronta, dan yasan kukan shi ne zai sa ta sami sassaucin abin da take ji a cikin zuciyarta, yau ta tuna baya, an cutar da ita over baiwar Allah.
A haka gabaɗaya familyn suka shigo bedroom ɗin suka samesu, har da su Rimsha da Brr Naurat, duk sun biyo sahunsu, sun baro Dr William da yake sume, sai dai Areef ya ɗauke shi ya kwantar da shi a saman sofa, sannan suka biyo Lion ɗin. TGA da Uncle Herry suna wajen Dr William ɗin, su kuma su John wucewa suka yi nasu bedroom ɗin, wai ba za su zo ɗakin ba!.
A ɗayan gefen gwaggon Areef ya zauna, ya zamana sun sakata a tsakiya. Shi kuma Aseef saman bed ɗin gabaɗaya ya haye, ya kwanta, kansa tamkar zata fashe mashi saboda ciwo, har wani jiri yake gani, yana ganin dishi dishi.
Ɗago kai daga saman kirjin Lion ɗin ta yi tare da juyowa zuwa ga Areef dake gefenta. Hannu Areef ɗin ya kai ya fara goge mata hawaye yana faɗin dan Allah ta yi shiru, kukan ya isa haka nan, ba ya son ganin kukan nata, dan ba zai iya jura ba, zuciyarsa tana yi mashi zafi sosai idan yana ganin kukan.
Yana magana yana goge mata hawaye, shi kuwa Lion ya dukar da kansa kasa yana tunani a kan abubuwan da gwaggon ta faɗa daga farko har karshe, yana nazari a kansu.
Muryar gwaggon ne ta daki dodan kunnuwansu, a in da ta ce "Ina ɗayan ɗana? Ina cikon TRIPLETS ɗin?". Juyawa Areef ya yi izuwa ga Aseef dake kwance tamkar zai mutu, idanunsa sun yi jajir kamar jini. A sanyaye ya ce mata ga shi nan.
Cikin ruɗu ta ce "Me ya same shi ya kwanta haka?". Ta yi maganar tare da kai hannu tana taɓa kansa. Turo baki ya yi tamkar yanda kuka sani ne, gidan shagwaɓa ba, ko a gadon asibiti yake sai ya yi ta, yanzu ma dai cikin shagwaɓa ya ce "Please ku dai'na taɓani, Allah idan ba haka ba in na fara kuka ba zan dai'na ba!". Shiru kawai gwaggo ta yi, dan kuwa yanda Aseef ya yi maganar sak Dr William time da suke zuba soyayya, sai ya tuna mata da baya.
"My son mommarka ce fa take taɓaka, tashi ka gaya mini menene yake damunka?". Cewar gwaggon. Kara turo baki sosai ya yi yana faɗin "Ni momma to ki barni mana, bana so ne a taɓani".
Girgiza kai kawai Areef ya yi, yanzu ya dai'na mamakin halin Aseef, tun da ya ji cewa daddynsu ruwa biyu ne, ɗan shagwaɓa ne ta wani fannin, ta wani fannin kuma ɗan bala'i, mafaɗaci, to kun ga kuwa shi Aseef ai shi ya yi gado, dan kuwa shi ma ruwa biyu ne, idan ka taɓo shi, ya iya faɗa, sai dai kawai ya fi Dr yawan shagwaɓa ne, dama kuma, ɗan na gada, ya fi ɗan na koya.
"Tashi to ka zo na goyaka". Cewar gwaggon, ta yi maganar cikin zolaya. Ɗan ɗago kansa ya yi. A hankali ya matso kusa da ita yana faɗin "Kwanciya a saman cinyarki ma is okey my Momma".
Matsa mashi waje kaɗan Areef ya yi, a nan ne ya samu dama ya kwantar da kansa a saman cinyar tata yana mai cigaba da turo ɗan bakinsa abinsa.
Shiru bedroom