Showing 57001 words to 60000 words out of 270744 words
in takaice maku ita kanta amaryar sai da ta zo ta kaunace ni fiye da ƴarta Batula, ta soni tamkar ta yi mani numfashi, a gidansu Abba na cigaba da rayuwata har muka yi aure, ƴan uwansa dukka suna kaunata sosai, barema Dr Salman bawan Allah, yana sona sosai, a lokacin ya ce mani yana son matarsa Naurat, amma bai isa ya je kasar Russia ya ce zai ɗauketa ba, idan ya je, ƴan uwanta za su kashe shi, dole ya hakura da ita, sosai a lokacin suka nemi ɗan uwansu Nawazuddeen wanda ni banma san shi ba, na dai ji labarin ya bar gida, amma basu gan shi ba, bayan aurenmu da Abban Imran, daga nan abubuwa suka fara faruwa, haɗarin da Dr Salman ya yi shi da amarya, ina da tabbacin da sa hannun Queen, a lokacin na cewa Abban Imran zan sake komawa ruwa, wato zan haɗa kayan tsafina, dan na yi maganin Queen, saboda idan ba fito na fito muka yi ba, in dai ban rushe Daular Mutuwa ba, to ba zata barni ba, dan ba zata iya yafe ni ba, sosai Abba ya yi mani nasiha, ya kuma yi mani faɗa a kan ko bayan ransa bai yarda na sake komawa tsafi ba, kamar yanda na barta, to ya zamana na barta kenan har abada, sosai naji nasiharsa, dan haka sai na hakura, muka cigaba da rayuwa muna karatunmu cikin farinciki, amma mutuwar Dr Salman ya girgizani, ina tuna bawan Allah nan, mutun mai farar zuciya, sai dai fa har gobe ina jin kamar bai mutu ba, ina ji kamar wata sharrin Queen ta haɗa mana, amma dai Allah masani.
(Masu karatu i hope yanzu kun fahimci dalilin kasancewar Dr Salman a Daular mutuwa?)
Tun daga wannan lokacin muka cigaba da yin rayuwarmu cikin farinciki, na rike kannan Abba kamar kannena, na mance da tawa kanwar da mahaifiyata, na sami sabuwar ahali, a haka muka kasance har Abbi wato Deen shi ma ya yi aure, ya auro wata ƴar Katsina da suka haɗu ita ma a school, ita ce mahaifiyarsu Irfan, mafadaciya ce sosai, da ta nemi ta kawo mani wargi, na taka mata burki, akwai wata rana da na yi mata dukan mutuwa har sai da aka kai ta asibiti, daga lokacin aka rabamana gida da ita, Abbin ya ɗauketa zuwa ɗaya daga cikin gidajen Dr Salman, in takaice maku labari ni ban sake waiwayar iyayena ba har rana mai kanata yau, na rufe babinsu, kuma nasan wlh Queen ba zata rabu da ni ba, ba shakka ita ce nan ta ɗauki Akila, kuma ita ce ta ɗauki matar Maik, sai dai fa sun canzawa Daular Mutuwa tasu waje, bata a in da na santa da, tun kafin na bar gida dama na ji suna shirye shiryen kara mata wasu matakan tsaro, sannan kuma su canza mata mazauni, a yanzu ita Rimsha ita kaɗai ce zata iya gaya maku in da Daular Mutuwar take, saboda ita ce ta shiga cikin ta kwanannan, amma kuma a gaskiya duk wanda ya shiga Daular Mutuwa ya fito da rai, to dole a jinjina mashi!! Dan duk yanda kuke tunanin Queen ta wuce hakan wlh, sam bata san menene imani or tausayi ba!!.
Masu karatu yanzu kun fahimci dalilin da ya sanya waɗan nan dodannin suke zane su Abba? Kun fahimci menene ainahin tushen matsalar? Bari na kara maku wata haske, a duk shekara dama already kun san da cewa dodannin suna zuwa gidan Abba, abin da yasa suke zuwa kuma, saboda tun bayan haihuwar Akila, lokacin sauka daga kan karagar mulkn Queen ya yi, kuma dole sai Ammien su Imran ɗin ce zata karɓi mulkin, dan ita ce babbar ƴarta, ita kuma kunga ta musulta, tama ki yarda ta sake haɗa hanya da su, wannan karya doka da ta yi ne yasa mukarraban Queen ɗin suke zuwa su zaneta, Queen ɗin ma tana zuwa gidan, amma ana ɗaukar lokaci sosai kafin ta zo, har ga Allah tana kaunar Ammien su Imran, shi ne ma yasa bata kashe ɗin ba, ta ke bata wahala dai kawai, kuma tun da Queen ɗin take zuwa kawowa Ammien ziyara, bata taɓa haɗuwa da su Akila ba, saboda rikonsu da addini, sai dai mukarraban tane suka taɓa haɗuwa da Imran, shi ma an samu akasi ya shigo ba tsarki a jikinsa ne, ya gama shan lemon tsaminsa bai yi wankar tsarki ba ne ya shigo cikin palon, kun tuna lokacin da suka taɓa zane shi ko? To lokacin ne suka san Imran ɗin, ai kunga shi Akil yana shigowa suka gudu, saboda yana da tsraki, kuma a lokacin ƙira'ar karatun Alqur'ani mai girma yake sauraro. Abin da ya faru a yanzu a wannan shekara Queen ɗin ta zo kawowa Ammien ziyara da kanta ne, a nan ne kuma taga Ayla, dama kunsan already tana neman Ayla, Rimsha, da kuma Kausar, shi ne yasa ta ɗauki Aylar, da ace Rimsha tana wajen, da ba makawa har da ita za su ɗauka, ita kuma Akila abin da ya sanya Queen ɗin ta iya ganinta har ta ɗauketa duk da tana karatun Alqur'ani mai girma, anyi katari ne da Queen ɗin ta kawo ziyarar dai'dai lokacin da Akilar take period, wato bata da tsarki, shi ne yasa ta samu damar ɗaukarta, ita Kausar dama already sun ɗauketa da jimawa, dan ba wani riko da addini ke gareta ba, yanzu Rimsha, Imran, Akil, su Queen take hari, ita Rimsha kun sani saboda karya mata record na gidanta da ta yi ne yasa suke son kamata, su Imran kuma, saboda ƴaƴan Ammie ne, idan baku manta ba dama Queen ɗin ta ce ba zata taɓa barin Ammie da duk wanda ya goya mata baya or yake kaunarta su zauna lafiya ba, shi ne yanzu dataga su Imran, sai take son ɗaukesu gabaɗaya, kuma dukkansu tsafi take da niyar yi da su............. (Jama'a za'ayi tsafi da Shaikh Akil fa😂mahaddacin Alqur'ani mai girma, mu gayawa Queen ba zata iya bane? Ko kuma mu bari duniya ta gaya mata? Dan in har ta ɗauki waɗan nan malamai guda biyun, wato Akil da Imran, to tana tsaka mai wuya, dan fa Alqur'ani mai girma ba wasa ba!!)
Allah sarki Ammie duk zaneta da dodannin nan suke yi, ba zata iya tuna wannan ba, saboda goge mata shi ake yi a cikin ƙwaƙwalwata, baiwar Allah, ita ma ta sha kuncin rayuwa ba karya, kuma hakika Allah yana sonta da rahma, har ta fito daga kabilar igbo, kuma matsafiya, sannan ta musulta, ta kuma rike addinin da kyau, kai gaskiya ta zama zakarar gwajin dafi! Ba abin da zamu ce mata face Allah ya daɗa kareta daga sharrin Queen! Amma dai Ammie ta yi kokari na wuce misali!".
Salati su gwaggo suka sanya, abin gabaɗaya ya sanya sun rasama ina za su kama, sun rasa abin faɗe. Ita kuwa Ammien, kuka take yi sosai tana faɗin wlh a dawo mata da Akilarta, ta san ba makawa kasheta Queen zata yi, dan ba imani ne da ita ba, in kuma ta kashe Akila, to wlh ba zata rabu da su ba! Shi ma Aseef kuka ya saka masu a kan wlh shi dai a nuna mashi ina ne wannan Daular Mutuwa ya je ya ɗauko matarsa, dan wlh shi ba zai yarda ba, in suka taɓa ko da mayafinta ne, duk sai ya kashe su........... E LALLAI ASEEF BAI SAN SUWAYE NE A CIKIN DAULAR MUTUWA BA, JAMA'A MU GAYA MASHI NE, KO DAI MU BARSHI YA JE ƊAUKO AKILA?😂 HAR DA WANI CEWA ZAI KASHESU HMMM QUEEN TA WUCE TUNANIN NAI TUNANI.
ita kuwa Rimsha, ganin Ammien Imran tana zaune kusa da Abba dake kusa da daddyn tane, yasa ta bar jikin daddyn nata da gudu, a dubu ta je ta ƙanƙame gwaggo tana ihu a kan tashiga ukunta, su taimaketa, tun da an ɗauki Ayla, yanzu ita kenan za'a ɗauka next, wlh bata son koma Daular Mutuwa, kashe mutane ake yi a can! Umaisha ma dai guduwa ta yi daga kusa da Ammien, saboda sun tsorata da jin labarin Daular Mutuwa. Yau Ammie ta zama dodo a wajensu, har surukanta suna gudunta.
Rimsha baiwar Allah, tamkar zautatciya ta zama masu a cikin palon, sai surutai take zubawa marasa kan gado. Riketa sosai gwaggo ta yi tana ambatar sunanta, ina ai tun da ta ji Queen na kawo wa Ammie ziyara, shikenan kuma ta birkice, zunduma ihu take yi tsakaninta da Allah, ita kaɗai tasan bala'in Daular Mutuwa, su dan basu sani bane, bata fatan ta sake komawa can baiwar Allah......GA ABIN DARIYA, GA ABIN TAUSAYI.
Karin wani haske, zaman Rimsha a gidansu Imran, Malika ce ta taimaka mata har tasa Queen bata ganta ba, Malika ce tasa Ammien ta ce bata son Rimshar, ta yi hakan ne kuma dan bata son Rimshar ta zauna da Ammien inuwa ɗaya har Queen ta kawo ziyara ta ganta su ɗauketa, to kun ji yanda aka yi da kuma dalilin da yasa Ammien ta ce bata son Rimshar, Malika ce sila, na san kowa yana son sanin ainahin wacece Malika, to muje dai zuwa, lokacin sani ya kusa..........
LALLAI AKWAI CAKWAKIYA, AYLA TANA TSAKA MAI WUYA, NA FARKO SUN KARYA RECORD NA QUEEN, NA BIYU KUMA TA ZO TA SHIGA CIKIN FAMILYN DR SALMAN A MATSAYIN SURUKA, FAMILYN DA QUEEN TA FI TSANA FIYE DA KOWA A DUNIYA, ITA MA RIMSHA TANA TSAKA MAI WUYA, DA CAN BAYA QUEEN BATA SAN CEWA RIMSHA ƊAYA DAGA CIKIN FAMILYN DR SALMAN BANE, KAWAI TANA NEMANTA NE DAN RECORD NATA DA SUKA KARYA, YANZU KUMA, TA GANE TANA ƊAYA DAGA CIKIN FAMILYN DR SALMAN, KUNGA KUWA BA ZATA KYALETA BA, LALLAI AKWAI CAKWAKIYA, AKILA KAM BA'A MAGANA, GATA ƳAR AMMIE, GATA JIKAR DR SALMAN, TAB AKWAI CAKWAKIYA, ITA KUMA RIMSHA, GA SU JOSEPHINE A GEFE SUNA HARINTA, WASAN YANZU ZAI ƊAUKI ZAFI JAU, HAR YANZU AKWAI SAURAN RINA A GABA BA KAƊAN BA, DAN HAR YANZU BASU SAN CEWA DR SALMAN YANA RAYE BA, GA KAUSAR ƳAR YARABAWA MA QUEEN TA DAUKETA, TA YI TSAFI DA SUNE KO SUNA RAYE? ALLAH MASANI, SAI KUMA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA, WAI SHIN YANZU A INA MA DAULAR MUTUWA TAKE? RIMSHA ZATA SAN HANYA NE? KADA KU MANTA DAJI SUKA BIYO, SU KANSU BASU SAN WANI HANYA BANE, TSAWON KWANAKI SUKA SHAFE SUNA TAFIYA, ZATA IYA SANIN TA INA SUKA FITO NE MA? WAYE ZAI JE ƊAUKO AYLA DA AKILA? NA BARKU HAKA NAN, KADA NA KARA CAZA MUKU KAI, MA'ASSALAMA!!.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E10
Date: 20/4/2024
Ihu sosai take zunduma, sai ƙoƙarin dannanta gwaggo take yi, amma ina, taki tsayawa. Da dai Lion ya lura ita fa Rimsha sam bata a cikin hayyacinta, ta ruɗe masu ne sosai, ga shi sai tumurmusa masu jikin mommansu take yi, kamar wadda ake hurawa wani abin a kunne, haka take tsalle tana ihu, sai ya kai hannu ya rikota da hannu ɗaya, a lokacin kuma su Abba duk sun yunkura zasu karɓeta daga hannun gwaggon, saboda gwaggon ba zata iya riketa ba.
Ganin Lion ya riketa ne yasa kowa ya fita harkarsu, dan duk wanda ya kwana ya tashi a wannan gidan, to yasan waye Lion, so basu ma son wani abin ya haɗasu, basu yarda hanya ta haɗasu.
Jawota jikinsa ya yi, ya haɗa hannayenta dukka biyu da take ta faman yarfarwa tana ihun nan, haɗesu ya yi ya rike da hannunsa ɗaya yana tofa mata addu'a, saboda ya samu ta nutsun mashi.
Shiru palon ya yi na ƴan mintoci, ban da kukan Rimshar da yake tashi kasa kasa, babu wani motsi da zaka ji a palon, tamkar babu mutane, kowa ya zubawa Brr Naurat idanu, ita kaɗa suke jira ta yanke hukunci, daga nan sai a san abin yi.
Shi kuwa Lion, sai da ya tabbatar ta dawo dai'dai, sannan ya dakata da tufa mata addu'a yana kallon face nata, idanunta a rufe ruf, da alama ma barci ya ɗan yi awon gaba da ita. A hankali ya ɗago da kallonsa izuwa kan Brr Naurat dake ta kallon shi ita ma.
Kowa binsu da idanu yake yi sosai, sun ƙagu su ji menene abin da zata ce. Ita kuma shiru ta yi tana nazarin maganganun Ammien, ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta fara magana cikin nutsuwa. "Tun farko kune ma muka yi kuskure, ko in ce shi Abba shi ne ya yi kuskure, tun da ka san ga daga in da ka ɗauko mace, ai da sai ka san irin babban matakin da ya kamata ka ɗauki, wani faɗan ai baka isa ka yi shi kai kaɗai ba, tun kafin ka shiga gidanka da kuka zauna, sai ka sanya ayi maka saukar Alqur'ani mai girma, ayi walima ayi maku adduo'i, ta yanda zaku ɓacewa ita Queen ɗin gabaɗaya, karfin addu'a zai taimaka maku Allah ya tsareku, sauran ƴan uwanka ma, sai ka gaya masu su ga halin da ake ciki, sai suma su shirya su tsananta addu'a, tun da a gaban idanunka Queen ɗin ta sha alwashin ba zata rabu da kai da familynka ba, sai baka yi hakan ba, ka ɗauka abin wasa ne, yanzu koma me ya faru da ƴan uwanka, to laifinka ne, dan su basu san ma daga ina take ba, suna rayuwarsu ne yanda suka saba, kuma shi karatun Alqur'ani sai wanda yake da kokari sosai ne yake iya yinsa kullum, saboda shaiɗan ba zai barsu ba, amma kaga idan sun san da wannan matsala, dole za su yi taka tsantsan sosai, dole zasu yi ƙoƙarin yin addu'a sosai, za su kula da askar, dan su kare kansu daga irin wannan musifu haka". Ta kai karshen maganar tana mai kara jinjina wannan al'amari, dan ita wlh sam bata taɓa tunanin ire iren waɗan nan matsafa akwaisu a gaske a zahiriya ba, kun san Turawa dama, su sam basu damu da irin waɗan nan shirme ba, to yau dai ga shi ta samu gagarumar matsafiya a cikin surukanta!.
(Anya da Brr Naurat tana nan a lokacin zata yarda Abba ya auri Ammien kuwa?🤔 Shiyasa Allah ya kawar da ita a lokacin, ta koma kasar Russia, domin rabon su Imran da yake a tsakanin Abba da Ammien, kun san shi fa rabo har kisa yanayi, to Allah ya ƙaddara akwai auren ne, shi ne ya matsar da Brr Naurat, dan yasan ba zata taɓa yarda da auren ba!!)
A hankali sautin zazzaƙar muryar Rimsha ya fara tashi, kasa kasa take magana ta lafe a jikin Noorish nata. "Noorish Allah ni bana son komawa Daular Mutuwa, please kada ka bari Queen ta ɗauke ni, Allah Duna ya ce mani cinyeni zata yi idan na sake komawa". Tana magana wasu siraran hawaye suna zubo mata a kuncinta.
Shafa face nata ya yi tare da goge mata hawayen, a hankali ya motsa laɓɓansa, ba sai na sake faɗa ba, dama kun sani already shi idan yana magana, kasa kasa yake yinta, idan ba kana kusa da shi sosai ba, to ba zaka taɓa jin meyake faɗa ba, a yanzu ma haka ne, duk cikin palon ban da Areef dake zaune kusa da shi sosai, to babu wanda ya ji abin da ya ce mata, kasa kasa ya yi maganar.
"Babu wanda ya isa ya mayar mani dake can, just calm down kin ji ko?"
"Noorish Allah tsoro nake ji". Ta yi maganar tare da kankame shi sosai. Tabbas yaga tsananin tsoro kwance a cikin idanunta, hakan ya kara tabbatar mashi da cewa ba ƙaramar ɓarna suke aikatawa a cikin wannan Daular Mutuwar ba!,.
"Meesha bai kamata ki ji tsoron wani abin ba idan kina a tare da ni, ba zan bari ayi maki komai ba". Ya yi maganar yana mai cigaba da goge mata hawayen da suke ta gangaro mata.
"Is okey, a tsayar da kukan nan haka nan". Ya kai karshen maganar yana ɗago da idanuwansa izuwa kan Brr Naurat dake kallonsu.
"Brr just close this case like that, ni ban ga abin dawo da abin da ya wuce ba, a have alot of things da nake son zuwa na yi, so momma I will going to leave". Cewar Lion ɗin.
"No Saif, wannan ba shi ne maganar da na kiraka ka zo mu yi ba, tsaya ka ji maganar mana". Cewar gwaggon.
Shiru ya yi bai sake magana ba. Rimsha ce ta sake ce mashi "Noorish am feeling hungry too much". "Okey you can go and eat". Ya bata amsa.
Su Imran dai mamakin Lion ya hanasu yin magana, wai yau shi ne ya zauna yake hira da mace haka, macen ma ƴar yarinya kamar Rimsha, komai ta ce mashi zai bata amsa, mutumin da a baya sai ka yi magana goma sannan yake bada amsa ɗaya, ba ya taɓa baka amsa a kan kowace magana, wani lokaci ma amsar ma ba zaka samu ba, amma ita Rimsha kowani maganarta sai ya amsa, Allah mai iko!!.
Zaro idanu