Showing 189001 words to 192000 words out of 270744 words
bi ta kansu Cherish ba, cikin nutsuwa ya ce da Dr William da yake a tsaye yana bin parlourn da kallo. "Dad have a seat". Ya yi maganar kuma idanuwansa na'a kan screen ɗin wayar tasa, ya kunnata yana ƙoƙarin kiran number Areef, dan ya sanar da shi sun isa lafiya, saboda yasan halin ƴan uwan nasa, idan ɗaya daga cikinsu baya nan, to basu samun nutsuwa, bare kuma ace basu yi waya ba, duk suna shiga damuwa sosai, shiyasa duk in da zasu je a duniya, in dai sun sami dama to dole sai sun kira juna, hakance kawai yake samar masu da kwanciyar hankali.
Sam Dr William bai yi wa Lion musu ba, saboda duk da baya a cikin hayyacinsa, bai san ma wanenen shi ba, amma yana jin cewa Lion ɗansa ne, saboda kamanceceniya da suke yi da shi kansa, ga kuma kamanceceniya da sir Arvin da suke yi, hakan tasa ya ji cewa lallai Lion ɗansa ne, har cikin ransa yake jin kaunar Lion ɗin sosai, ji yake yi ma kamar yaje ya rungumesa, amma haka ya daure dai, ya sami waje a saman sofa set dake set ɗin kusa da su ya zauna, ya kasa kawar da blue eyes nasa daga kallon Lion ɗin, ya kalli Lion ya kalli Aseef, duk sai ya ji kamar ya je ya rungumi Aseef, yana jin kamar Aseef wani ɓangarene na zuciyar tasa, dama shi Aseef kun san shi da shiga rai kamar Rimshar Lion ɗin, so tun daddynsu bai dawo cikin hayyacinsa bama yake jin wani irin zazzafar kaunar Aseef ɗin.
Shi ma Aseef ɗin sai kallon daddyn nasu yake yi, yana son ya yi magana, amma ya yi shiru, saboda yasan ko ya yi magana ma Lion ba kula shi zai yi ba, sai time da yaga damar amsawa zai amsa masu, dan haka sai ya ja bakinsa ya yi shiru tare da zama kusa da Lion ɗin.
Sau biyu Lion ɗin yana gwada kiran number Areef, amma bata shiga, hakura ya yi sannan ya kira number gwaggo, a lokacin Rimsha ta tada kanta da cinyar gwaggon tana zuba shagwaɓarta son ranta, ita kuma gwaggon tana biye mata.
Sabuwar waya Areef yasa Tga ya sayawa gwaggon tun kafin yazo Nigeriar, tun time da Rimsha ta yi fushi ta fasa mata wayar tata.
Bugu ɗaya gwaggon ta ɗauka, dan dama sai neman numbersa take yi a kashe.
"Good afternoon momma". Ya faɗa a sanyaye
"Afternoon my son, how was your journey?".
"Alhamdulillah how are you and my wife?". Bawan Allah komai yake yi yana tunanin Rimsha sosai, tana ransa, bai san cewa ma fushi take yi da shi ba.
"Alhamdulillah, your wife gata nan tana zuba mani rigima".
Jin abin da gwaggon ta faɗa ne yasa Rimshar ta miƙe tare da saukowa kasa daga saman bed ɗin, tana ɗingisa kafa ta fice daga ɗakin, dan kada gwaggon ta ce zata haɗata da Lion ɗin, a cewarta fushi take yi da shi, baiwar Allah har yanzu bata iya tafiya da kyau, sai dai ta yi ta ɗingisa kafafu, kuma har yanzu tana ɗan jin zafi, barema idan tana tafiya wajen yana ɗan yi mata zafi, dan ma kullum gwaggo bata barinta sai ta shiga ruwan zafi ta gasu, hakan ce ma tasa abin ya yi mata sauki.
Da kallon mamaki gwaggon ta bita har ta fice daga ɗakin, dai'dai lokacin kuma Lion ɗin ya ce "Momma please give her the phone, i really missed her, i want to hear her voice". Ya yi maganar kasa kasa sosai, dan ko Aseef da yake a zaune kusa da shi saman sofa ɗaya ma bai ji me ya faɗa ba, dama can kullum maganarsa a kasa kasa take, amma fa idan zai yi magana da Rimsha ko zai yi magana a kanta, yana kara yin kasa sosai da muryarsa, ko kai da kake waya da shi idan ba kana da lafiyayyen kunne ba, bazaka taɓa jin abin da ya faɗa ba.
Thank God gwaggon dai ta ji abin da ya ce, sai dai ta rasa amsar da zata bashi, tun farko tarigada ta ce mashi ga Rimshar a kwance a kusa da ita, yanzu kuma ta ce mashi bata nan? Anya kuwa hakan zai yi wu? Ga shi yadda ta ji voice nasa duk a gajiye yake, uwa da ɗa, har tana iya fahimtar halin da yake a ciki ko da waya suke yi, Allahu Akbar, wani abin sai uwa! Allah dai ka kara masu lafiya da nisan kwana, waɗan da suka rigamu gidan gaskiya kuma Allah ya jikansu ya rahamcesu, ya kai haske cikin kabarinsu, daga karshe ya saka masu da gidan Aljannartul firdaus.
"Yanzu ta shiga toilet, sai ta fito". Ta bashi amsa da haka ba dan ta so ba!.
Shiru ya ɗan yi, duk da mommarsa ce, a wannan magana tata ya fahimci ba dai'dai ta gaya mashi ba, dan shi akwai shi da fahimta over, kuma gwaggon bata saba yin karya ba, dama haka ne, idan baka saba yin karya ba, in kayi sai an gane, duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, zuciyarsa tana gaya mashi cewa akwai wani abin a kasa, ko Rimsha bata da lafiya, ko kuma dai fushin da ta yi da shi ne har yau bata sauko ba, tabbas akwai wani abin da aka ɓoye mashi, duk sai ya ji ya damu, sai ya ji zuciyarsa babu daɗi, haka dai ya daure ya ce mata "Okey momma let me go and take a bath, daga nan zan yi barci kaɗan, sai dare zamu yi waya, and kada ki manta gobe zaku taso fa kuma, because i really missed you over, and then there's important thing that's waiting for you here".
"Okey my son, take good care of yourself, and ka kula mani da my autana sosai, komai yake so ku tabbatar kun bashi".
(Bala'i lallai gwaggo, wai komai Aseef yake so a bashi? Dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo?😂)
Nisawa ya yi a cikin zuciyarsa yana godiya ga Allah dayasa ba'a gaban gwaggo Aseef ya taso ba, da iskancin nasa sai ta wuce haka, yanzu ma ya suka kare da shi? Amma a haka Gwaggon take cewa ayi mashi komai da yake so? Lallai kuwa da ita ta rene shi lalacewarsa sai tafi haka.
Jin ya yi shiru ne yasa ta ce "Son are you okey? What are you thinking?". "Nothing momma, see you later". Ya kai karshen maganar cikin kasalalliyar murya tare da katse kiran. Sai bayan ya katse kiran ne ya ɗago da kallonsa izuwa kan su Handsome dake tsai tsaye cirko cirko, sun kasa zama, ganin parlourn suke yi tamkar ba'a duniya suke ba.
Miƙewa tsaye ya yi tare da nufar saman bene yana sanar da Aseef a kan ya kula dasu Handsome ɗin, ya basu wajen zama da ruwan sha tare da abinci, shi bari ya yi wanka ya kwanta ya yi barci.
Okey kawai Aseef ɗin ya bishi da shi, sannan ya ce su samu waje su zauna mana, sai a lokacin kuma ya sauke idanuwansa a kan Cherish, ɗan zuba mata idanu ya yi, yanzu kam ko ba'a gaya mashi meyake faruwa ba ya gane, dan gabaɗaya ƴaƴan Dr William shegen kaifin kwakwalwar bala'i ke garesu, yanzu ya fahimci in da komai ya dosa, saboda yasan Cherish a hoto, kuma yaji labarinta, ya san alaƙar dake a tsakaninta da gwaggon, kallon ɗai ɗai ya fara yi wa su Handsome ɗin, dan ya kara tabbatarwa da kansa abin da yake zargi. Alama ya yi wa Pinky da hannu a kan tazo.
Da farko kamar zataki zuwa, sai kuma ta tuna cewa ai gidansu suka zo, dan haka bata isa ta yi mashi musu ba, kuma taga su ba masu mugunta bane, tun da sun zubawa sir Arvin ruwa ya farfaɗo daga suma ya faɗa barci bawan Allah.
A hankali ta nufesa tana ɗan ɗari ɗari. Kusa da shi ya zaunar da ita yana mai cigaba da kallon face nata. Suma su Cherish zama a saman sofa guda ɗaya mai zaman mutun uku suka yi ita da Handsome ɗin.
Welcome Aseef ɗin ya yi masu kafin nan yasa bodyguards su kawo masu ruwa da kayan cima.
Bayan ya tabbatar ankawo masu, sannan ya miƙe tare da haurawa sama yana faɗa masu yana zuwa.
Okey handsome ha amsa mashi da shi, sannan suka fara cin abubuwan da aka zube masu a gabansu a saman carpet, yunwa suke ji yasa dole suka ci.
Sun ɗan yi nisa a ci abinci, miƙewa Cherish ta yi tare da nufar in da take zaton shi ne kitchen, tambayarta lafiya ina zata je? Handsome ya yi, "Am coming i want to check some type of their food". Ta bashi amsa.
Shiru ya yi bai sake yin magana ba.
Cikin kitchen ɗin ta shiga. Babu kowa a cikin kitchen ɗin, duk sun kammala aikinsu sun fita waje. Su kuwa su Pinky sai cin abinsu suke yi, dole tasa suke cin abincin ma ba dan yayi masu ba, sai dan yunwa da kuma basu da zaɓi, basu isa su ce bai yi masu ɗin ba.
After some minutes, bayan sun kammala cin abincin nasu, shiru shiru Dr Cherish bata dawo cikin parlourn ba, miƙewa Handsome ya yi domin ya je ya dubata lafiya bata dawo ba tun ɗazun, da kallo suka bishi har ya shige cikin kitchen ɗin.
Wani iri razababben ihu ya kurma tare da fitowa daga kitchen ɗin da gudu, a tare Dr William da Pinky suka miƙe tsaye suna tambayarsa lafiya?. Da gudu Aseef ya sauko kasa daga sama shi ma yana tambayar lafiya kuwa suke yin ihu?.
A tsananin ruɗe Handsome ɗin ya gaya masu abin da ya gani a cikin kitchen ɗin. A dubu ɗari kusan a tare Aseef da Dr William suka nufi cikin kitchen ɗin. Cherish ce kwance cikin jini malala a kasa, ta daɓawa kanta wuƙa a ciki, da alama ma ta ɗan ɗauki ƴan mintoci da mutuwa.
Zaro idanuwa waje sosai Aseef ya yi, cikin tashin hankali yake tambayar waye ya yi mata hakan? Waye ya kasheta?.
Tamkar daga sama ta bayansu wajen kofar shigowa cikin kitchen ɗin suka ji voice irin na Lion yana faɗin "Babu wanda ya yi mata hakan, ita ta yi wa kanta da kanta, nasan halinta sama da kowa a cikinmu, tana tunanin wancan mai kama da ni ɗin ba zai kyaleta ba, zai kasheta ne, shiyasa ta riga shi aiwatar da hakan, kowa dai yasan yadda dokar kasar China take a kan cin amana irin haka, so ita ta yi amfani da dokar in da ta baro ne ba in da take ba, dan haka babu wanda ya yi mata hakan, ita ce nan ta yi wa kanta".
A tare suka juyo da kallonsu dan su ga mai yin wannan magana, Sir Arvin ne a tsaye a bakin kofar shigowar, ihun da Handsome ya kurma ne ya farkar da shi daga barcin da ya ɗaukesa tun bayan farfaɗowarsa daga suma.
Da gudu Pinky ta tafi ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai sauti. Hannu yasa ya ɗauketa cak, da sauri ya juya da ita suka bar wajen, da yake shi ma ɗan zafin kai ne, sai ya nufi saman benen dan yana son ya yi magana da Lion, tun da kuma yaga Lion ɗin baya a nan to yasan bai wuce yana sama ba.
Su Aseef kuwa, sun tsaya cirko cirko a kan gawar sun rasa abin yi. Handsome hawaye bibbiyu ne yake zuba daga idanuwansa, shi bai san menene ya faru ba! Bai san kan magana ba, yana da buƙatar karin bayani bawan Allah, dan yasan meyasa mumynsu zata kashe kanta?!.
Yana haurawa parlourn sama ya ɗan fara ƴan waige waige yana neman ina ne ɗakin Lion ɗin? Akwai parts sosai a saman, akwai na Lion ɗin, Aseef, Areef da kuma wasu da babu kowa a ciki, so daddyn Rimsha yana a ɗaya daga ciki, sai kuma sama wato hawa ta uku, shi kuma akwai part na daddynsu na fake, sai part na uncle Herry, John da kuma Jay, shi kuma sama gabaɗaya wajen hutawa ne kawai da shan iska, sai kayan gym nasu a wajen, so a wannan hawa ta farkon dai parts na TRIPLETS ɗin ne a wajen sai daddyn Rimsha da yake a tare da su yanzu.
"What are you looking for?". Aseef da ya hauro saman yanzu ne yake tambayarsa. Ɗan zubawa Aseef ɗin idanuwa ya yi, lokaci guda ya ji wani irin kaunar Aseef ɗin tana ratsa zuciyarsa. "Am looking for that man that we looked alike".
Da hannu Aseef ɗin ya nuna mashi part na Lion ɗin ba tare da ya kyafta idanuwansa daga kan kallon da yake yi mashi ba, yana son sanin wanenen shi? Shi ma sir Arvin ɗin yana son sanin wanenen Aseef ɗin? Sai dai shi a jikinsa ya ji cewa lalllai Aseef yana ɗaya daga cikin QUADRUPLE nasa kenan kamar yadda Dr Cherish ta bada labari jiya a kasar China.
Gaba Aseef ɗin ya yi ya shige cikin part ɗin na Lion ɗin dan ya gaya mashi abin da yake faruwa a parlourn kasa. Bayansa sir Arvin ɗin ya bi, sai kalle kallen wajen Pinky take yi, ga hawaye a fuskarta jaga jaga, harda majina.
Ko da suka shiga parlourn Lion ɗin sai da sir Arvin ya ɗan tsorata, saboda ya ga abin fa ba na wasa bane, ya wuci tunaninsa, irin wannan dukiya da aka narka tamkar baza'a mutu ba?.
Lokacin da suka shiga cikin bedroom ɗin a lokacin Lion ya fito daga dressing room nasa, jikinsa na sanye da kayan barci masu bala'in kyau da tsada, kamar dai kullum launin up white mai haske sosai, sai dai ya ɗaura Jacket a saman kayan, saboda wani irin azababben sanyi da ake yi, duk da ya kunna na'urar ɗumama ɗaki, amma akwai sanyi, kun san kasarsu dama da bala'in sanyi.
Yana ƙoƙarin hayewa saman bed nasa suka shigo mashi, Aseef bakinsa a ɗauke da sallama, shi kuma sir Arvin excuse ya yi mashi.
Ɗago blue eyes nasa ya yi tare da fara binsu da kallo. Cike da tashin hankali Aseef ya kora mashi jawabin abin da yake faruwa. Tamkar bai ji me Aseef ɗin ya faɗa ba, idanuwansa suna a kan sir Arvin da yake ta faman kallonsa shi ma, ita ma Pinky ta kalli sir Arvin ɗin ta kuma sake juyowa ta kalli Lion ɗin, sun ɗaure mata kai baiwar Allah.
Fasa hayewa saman bed ɗin ya yi, wajen mirrornsa ya nufa, tissue mai bala'in kyau da tsada ya ɗauko, a gaban sir Arvin ɗin ya kariso cikin nutsuwa yake tafiya, yana zuwa ya fara gogewa Pinky hawaye da kuma majinar da yake a face nata ya yi jaga jaga, sannan ya kalli Aseef ɗin ya ce mashi zai zo ya duba gawar, amma sai ya tashi daga barci, dan haka kada su taɓata, su kyaleta.
Sir Arvin ne ya ce mashi "I want to talk to you".
Ɗauke hannunsa daga saman fuskar Pinky ya yi tare da wucewa ya koma saman bed nasa ya zauna bayan ya miƙawa Aseef dake a tsaye tissue ɗin.
"I don't have time for talk now, because am feeling sleeping too much, and ni ina da tsari! Bana haɗa two things one time, everything has his on time!". Ya kai karshen maganar tare da kwanciya abinsa.
Shiru kaɗan sir Arvin ɗin ya yi yana mamakin yadda aka yi halayyarsa da ta Lion ɗin iri guda, shi ma haka yake yi, sai ya ce baya haɗa abubuwa biyu lokaci guda, sannan komai da lokacinsa, to yau ga wanda ya fishi iya furta wannan kalmar!.
Yana tsaka da tunani zazzaƙar muryar Lion ɗin ta daki dodan kunnuwansu. "Come and have a seat". Ya faɗa tare da lumshe idanuwansa.
"No zan je kasa, idan ka tashi barci sai mu yi magana". Shiru bai amsa mashi ba, wucewa sir Arvin ɗin ya yi, ya nufi waje, shi kuma ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi. Da sauri Aseef ya bi bayan sir Arvin ɗin suka koma parlourn kasa
A ɓangaren su Jehan kuwa, tamkar yadda wannan matashi ya yi masu kwatance haka suka nufa, sun yi tafiya tun da daɗin rai har ya zamana babu daɗi, Jehan ta sha barci ta tashi, sai dai ta tashi a dai'dai, dan a lokacin suka isa wajen wannan dutsen, motarsu dai ta ji jiki ba kaɗan ba, duk da zama duk taɓo jikinta, ga hawa da sauka da suka rinƙa hawa, wata hanyar ma da kyar suka iya kutsawa suka wuce.
Yana isa wajen ya kashe motar tasa, juyo da kallonsa ya yi a kan Jehan ɗin, sai faman turo baki take yi, ta sha barci kamar ba gobe.
"Sorry my baby, na wahalar dake ko? Dama na barki a hospital ai". Ya faɗa yana kara tsareta da idanuwa. Matsowa ta yi ta kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa, a hankali ta motsa laɓɓanta da suke yi mata zafi saboda wahala, ga yunwa tana ji. "Yah Areef yunwa fa nake ji".
Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman flat tummy ɗin nata, kasa kasa ya ce "Sorry yanzu zamu koma gida In Sha Allah, amma kafin nan bari na rage maki yunwar kin ji ko?". Ya kai karshen maganar tare da juyowa gareta sosai, hakan ya bata damar shigewa Lion chest nasa da kyau ta lafe. Da alama sun mance a in da suke.
"My baby". Ya ambaci sunanta a hankali. A hankali ita ma ta ɗago da kanta, haɗe fuskokinsu ya yi tare da fara kissing nata.
Narke mashi ta yi a jiki tana ɗan matsa mashi ɓul ɓul ɗinsa. Ƙoƙarin wuce gona da iri ya yi, cikin sauri ta riko hannunsa da yake ƙoƙarin tura mata a cikin riga, a hankali ta zame bakinta daga nasa tana faɗin "Kai my baby ka bari mana, wai ka manta a in da muke ne?".
Lumshe idanuwansa da suka yi jajir kamar wuta ya yi, a hankali ya furta "Yunwa zamu ragewa juna fa, please ki barni na ɗan more mana". "Uhm ni ka bari sai mun koma gida".
Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "You're right, gobe muna da tafiya zuwa U.s a gabanmu, yakamata muyi komai a yau ne, dan haka let's go". Ya kai karshen maganar tare da buɗe kofar motar tasa.
Raba jikinta da