Showing 114001 words to 117000 words out of 270744 words
juna cool murmushi, suna tsananin kaunar juna sosai, amma sai dirama tamkar wasu ƴan wasa.
A hanzarce ya juya izuwa ga mirror, sauri sauri ya fara shafa lotions nasa, yana yi yana kallonta ta cikin mirror, ita ma ta tsare shi da idanu tana ta kallon shi, sai ɗaga mata gera ɗaya yake yi time to time idan sun haɗa idanu, abin gwanin birgewa.
Bayan ya kammala ya wuce dressing room nasa. Jim kaɗan ya fito shirye cikin wandon jeans baki kalar ta jikinta, da kuma T-shirt sky blue, ya yi matukar kyau ba ɗan kaɗan ba, sai dai bai samu dama ya busar da gashin kansa ba, da akwai ɗan danshin ruwa, amma haka ya wuce ya nufi waje yana ce mata bari ya zo yana magana yana ɗaure gashin kan nasa.
Okey kawai ta amsa mashi da shi tare da binshi da kallo har ya fuce, sannan ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da gyara kwanciyarta ta rungumo pillow da ya runguma ɗazun.
Shi kuwa yana fita bedroom na Lion ɗin ya nufa, bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga, sai dai babu kowa a ciki. Shiru ya ɗan yi yana mamakin yaushe Lion kuma ya tafi Washington? Ya dai san wancan number da Lion ɗin ya kirasa na Washington ne, to ko yaushe ya tafi?. Ya ɗan jima a cikin bedroom ɗin kafin ya fito ya nufi bedroom ɗin daddyn nasu, wato fake William.
Bakinsa ɗauke da excuse ya shiga cikin ɗakin. Turus ya tsaya ganin cewa babu kowa a cikin ɗakin, ya sha ruwan mamaki, dan kuwa shi dai yasan daddynsa baya fita waje, idan ma ya fito to a palon kasan suke zama shi da Uncle Herry su yi hira. Duddubasu ya fara yi yana neman a ina suke, sai dai shiru, babu su babu labarinsu.
Fitowa ya yi ya fara kewaye gidan yana nemansu, amma shiru babu su babu labarinsu, tambayar gateman ya yi a kan ko ya kalli su daddynsa? Ko sun fita ne. A'a basu fita ba gateman ya bashi amsa. Wucewa ya yi izuwa cikin gida, zuciyarsa cike da mamakin ina suka tafi, da kuma tunanin meyasa Lion zai ce a kashe daddyn nasu?. Haka dai ya nufi bedroom nasa.
Yana shigowa kiran Lion tana shigowa wayarsa, a hanzarce ya kariso ya ɗauki wayar tare da yin picking na call ɗin.
"Lion I didn't see dad and uncle Herry". Shiru Lion ɗin ya ɗan yi kafin ya ce mashi "Tun yaushe na sanyaka aikin? Anywhere now dai ka tura aje airport a ɗauki Shaikh Sultan, su William kuma sun koma in da suka fito".
"Lion like how sun koma in da suka fito? Wai ma what is happening ne?". "Areef go and send someone to airport i said, shi ma kuma ka ɓata mani lokaci irin na ɗazun!". Ya kai karshen maganar tare da katse kiran.
Sam Areef ɗin bai ji daɗi ba da bai yi wa Lion ɗin abin da ya sanya shi ba, ga shi yanzu da alama Lion ɗin ya ji babu daɗi, dan daga voice nasa zaka fahimci bai so hakan ba.
"My baby am coming". Ya faɗa tare da wucewa ya nufi waje again.
After some minutes ya dawo cikin ɗakin, kusa da ita ya zo ya tsaya tare da miƙa mata hannu a kan ta zo su tafi.
Ba musu ta miƙa mashi hannunta, rikota ya yi tare da jawota jikinsa, a haka suka nufi waje.
Kai tsaye ɗakin gwaggo suka nufa, yana rungume da ita, ita ma da yake ba kunya ke gareta ba, sai bata wani damu ba. Bakinsu a ɗauke da sallama suka shiga cikin ɗakin.
Gwaggo na zaune a bakin bed, Rimsha na kwance ta tada kai da cinyar Brr Naurat, baiwar Allah ta yi shiru kamar mai tunanin wani abin, ita kaɗai tasan me take ji, sai kallon Malika dake tsaye a kusa da mirror take yi, ita ma Malikar ita take ta kallo, sai dai dukka ɗakin babu mai iya ganin Malikar sai ita kaɗai, ita kuma Rimshar bata iya buɗe baki ma bare ta yi wata magana, Allah sarki sarai Malika tana sane da duk abin da ya faru da Rimshar, sai dai kuma bata yi wani yunkurin taimaka mata ba, saboda tana son Lion ya gane gaskiya, shi ne yasa bata taimaki Rimshar ba, ta san cewa idan ta bar Rimsha da wannan ciwon, to ba shakka Lion zai nemi sanin gaskiya, kun ga kuma kamar yanda ta yi hasashen hanance ta faru, Lion ɗin ya tafi neman sanin gaskiya, da ta taimaki Rimshar ta samu lafiya, to da Lion ba zai mayar da hankalinsa ya binciko gaskiya ba, sai dai ayi ta tafiya a haka har ƴaƴa da jikokinsu, shi ne yasa wani lokaci bata tanka abu a kan Rimshar idan ya faru, saboda tana son wani abin ne ya bayyana.
Kusa da gwaggo Areef ya zauna, ita kuma Jehan ta koma saman bedside drawer ta zauna, dan bata son hawa saman bed ɗin, tana hawa zasu fara yin faɗa da Rimshar, yanzu kamar wuta da audiga haka suka zama, basu haɗuwa waje guda, ba komai ne yasa hakan ba face ita ma Jehan tauraronta yana da nisa, ba'a banza ta cika faɗa da zafin ran nan irin na Lion ba, su ƴan baiwa ne, taurarinsu yana da nisa sosai, wanda taɓasu a wajen matsafa abu ne mai matuƙar wahala, ita ma Rimshar sai da suka ci bakar wahala tsawon watanni suna bibiyarta kafin su sami galaba a kanta, sun wahala fa fiye da tunaninku kafin su cinwa Rimshar. Kun tuna lokacin da Jehan ta gayawa fake William magana a palo? Kuma babu abin da ya iya yi mata, to hakan ce, ita sam sam bata taɓuwa, duk bala'i haka za'a ganta kuma a barta, kamar Lion take, shi ma dai nan gani nan bari, Rimsha ce dai mai ɗan rauni baiwar Allah, kuma duk wata gaskiya ta wajenta yake fara bankaɗowa, ita take zama sanadiyar bayyanar abubuwa da dama, baiwarta ya wuci tunanin mai tunani, ita ta je Daular Mutuwa, ita ta zama sanadiyar bayyanar Dr Salman, yanzu kuma kusan ita ce ta zama sanadiyar bayyanuwar wannan lukutar matsalar da suke a ciki!!.
"Good morning momma". Ya faɗa yana kallon Rimsha dake ta faman kallon wajen mirror.
"Good morning or good afternoon?". Brr Naurat ce ta tambayeshi. Ɗan murmushi ya yi yana faɗin "Kai ƴar tsohuwarnan, kin iya sa ido, to ai ni yanzu garina ya waye".
"E ba shakka yanzu garinka ya waye kam, ga alama nan na gani".
Ɗan zaro idanu ya yi yana faɗin "Ina alamar kuma?". Shiru ta yi bata yi mashi magana ba. Gwaggo ce ta ce "Areef ina Aseef? Ina autana? Ko dai bai tashi daga barcin bane?".
"I think bai tashi ba, our Rimsha what are you thinking? Naga hankalinki gabaɗaya baya a kanmu ne". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin kai hannu zai taɓa face nata.
Dakatar da shi gwaggo ta yi ta hanyar cewa "Kaga ne wlh ka rufa mana asiri, yadda take kwance shirun nan barta a haka, idan ka taɓota, kamar ka kwanto bana gidan rina ne! Idan ta fara bala'i sai mun rasa me yake yi mana daɗi".
"Momma like how? I didn't understand anything, yi mani bayani, Rimshar ce mai faɗa? Ita da take so silent". Cike da mamaki ya yi maganar.
Ba ɓoye ɓoye gwaggon ta bashi labarin duk abin da yake faruwa, da tafiyar Lion, har kiran da Lion ɗin ya yi mata ɗazun ya ce mata ga abin da yake faruwa, dan haka sai su kara taka tsantsan, dama wannan dalilin yasa ta ce Jehan ta kira mata shi, dan ta gaya mashi halin da ake ciki.
Shiru ya yi yana tunanin wasu abubuwa, maganganun Josephine ne kawai suka fara dawo mashi cikin kansa, a koda yaushe idan ya je wajenta kai mata ziyara, maganarta ɗaya shi ne tana taya su da addu'ar samun gane gaskiya cikin ƙanƙanin lokaci tun kafin komai ya kure masu, to shi a lokacin yana ɗauka ko gaskiya tsakaninta da Dr William ne take son su gane, bai san cewa ba haka abin yake ba, ga gaskiyar da take magana a kai yau sun fara ganewa, Allah sarki kullum baya taɓa sauraronta idan ya je, da ta fara kawo mashi labarin baya zai dakatar da ita, ya ce mata shi gaisheta ya zo yi ya kuma tambayeta me take da buƙata, dan ya saya mata, idan kuɗi take so ya bata, shi baya son wani dogon magana, bai san cewa ga abin da ta jima take son sanar da shi ba.
Duk sai ya ji jikinsa ya yi muguwar sanyi, ya shiga damuwa sosai, tunaninsa ɗaya yanzu ina ɗan uwan nasu, cikon QUADRUPLE nasu yake? Yana raye ko ya mutu? Ina ainahin daddynsu yake? Hakika ya tausayawa daddyn nasu da kuma momman nasu, sun sha wahala, an cutar da su, uncle Herry da Josephine suma an cutar da su matuƙa, ga Tga a gefe, wannan wani irin rayuwa ne?, Ga Rimsha baiwar Allah da bata san komai ba ita ma an jefata cikin bala'i.
Gwaggon ce ta katse shi da cewa "Saif ya ce kada kowa ya ɗaga hankalinsa, kada mu yi kamar akwai wata matsala, mu yi rayuwa kamar kullum, nan da lokaci ƙanƙani komai zai zo karshe, dan haka kada ka ɗaga hankalinka kai ma".
Nisawa ya yi tare da miƙewa, zuciyarsa na yi mashi kuna na rashin kashe William ɗin da bai yi ba, abin ya baƙanta mashi rai, ji yake yi kamar ya yi ta buga kansa da jikin bango ko zai sami sukuni, hanyar fita daga cikin ɗakin ya nufa yana faɗin "Momma am coming". Ya kai karshen maganar tare da ficewa.
Bin shi da kallo suka yi har ya fita, sannan gwaggo ta ce da Jehan "Jeki ki kai mashi abinci, nasan bai yi breakfast ba". Okey ta amsa tare da miƙewa ta bi bayansa.
A ɓangaren Lion kuwa, yana zaune a wajen da yake zaune tun ɗazun, bai motsa daga wajen ba, yana aikin latsa waya ga Tv tana magana, kamar daga sama ya fara jin wani ɗan jarida daga cikin Tvn yana bada rahoton wai GENERAL OF THE ARMY'S ROMEO ya kashe wani babban ƙusa a gwamnati babu gaira babu dalili, wanda kuma ya kasance kakansa ne, har gida ya shiga ya yi poisoning nashi, yanzu ƴan'sanda sun sami damar garzayawa gidan, suna kuma bincike a kan gawar, su kasance kusa da Tvnsu dan jin yanda komai zai na wakana.
A hankali ya ɗago idanuwansa izuwa kan makeken Tvn nasa, gawar kakan nasu ne aka hasko tare da hotonsa a zaune a saman bedside drawer kakan yana ta kallon kakan nasa. Sam bai yi mamakin ganin hakan ba, dan yasan da akwai CCTV camera a cikin ɗakin, tun time da ya shiga ya gani, kuma da gangan ya bar camerar a kunne ta naɗi komai, dan dama yasan ba zasu faɗi gaskiyar komai ba, zasu yanke video ne ba zasu nunawa duniya ainahin abin da ya faru a tsakaninsa da kakan nasa ba, sai dai su nuna iya in da kakan nasa ya fara fafutukan mutuwa, shi kuma ya fice daga gidan, su suna jin daɗi sun kafa mashi tarko, basu san cewa ya jefawa kifi namane a cikin bakin ruwa idan ta zo kamawa shi kuma sai ya capkota ba, sun shirya hakan suna son ruguje shi ta kowace hali, shi kuma ya shirya yi masu rubdugu, yasan cewa kakansa His excellence zai ma iya shiga ya fita ya sanya a cire mashi kayan aikinsa, ma'ana a karɓi mukaminsa na wajen aiki, saboda yanzu ya yi fito na fito da su, amma sam hakan ko a jikinsa bata damesa ba, saboda shi kaɗai yasan abin da ya ƙulla masu, shi kaɗai yasan abin da zai jijjigo, sai ya tashi kansu. BABBAR MAGANA, YAU AKE YINTA, YANZU WASAN ZAI FARA A TSAKANIN TSOFAFFIN NAN GUDA UKU, WATO HIS EXCELLENCE, ANDERSON, UWARGIJIYARSU, DA KUMA LION SHI KAƊAI, ZAMU GA WAYE YA IYA BUGA WASAN A CIKINSU, ZAMU GA WAYE ZAI ZAMA ZAKARAR GWAJIN DAFI A CIKINSU, SU UKU SHI KAƊAI! BA SHAKKA AKWAI YAKI BA KAƊAN BA, YANZU DAI GA SHI SUN YI MASHI SHARRIN YA KASHE BABBAN ƘUSAR GWAMNATI, SANNAN GA SHAIDA ƁARO ƁARO JAMA'A KOWA YA GANI, KUNGA KUWA DOLE LION YA FITO YA YI WA DUNIYA BAYANIN MEYASA YA KASHE BABBAN ƊAN SIYAYSA KAMAR WANNAN, DUK DA YAKE KAKANSA DOLE YA YI WA DUNIYA BAYANI, DUK DA YAKE GENERAL OF THE ARMY'S DOLE YA YI BAYANI, DAN BA ZAUNA GARI BANZA AKA KASHE BA, BARE ACE KILA ƁARAWO NE KO WANI MAI LAIFIN, BABBAN MUTUN MAI MURYAR FAƊA AJI AKA KASHE, AKWAI KALLO!! YANZU WASAN ZAI ƊAUKI ZAFI.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E20
Date: 30/4/2024
Mikewa ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya nufi cikin bedroom nasa. Ko'ina a cikin ɗakin a gyare fes fes, tamkar ba'a taɓa taɓa komai na cikin ɗakin ba, makekekiyar katafen gadonsa a shumfuɗe da white bed sheet na alfarma, mai matuƙar kyau da tsada, sai tashin daddaɗar kamshi air freshener mai kwantar da hankali tare da sanyayya zuciya bedroom ɗin nasa yake yi. Toilet ya nufa, wanka ya yi tare da fitowa ya shirya cikin wata kyakkywar farar jallabiya tas da ita, ya zo ya shumfuɗa dadduma ya tada sallar azzahar.
Bayan ya idar ya jima yana addu'a tare da kaiwa Allah kukansa, bayan ya shafa addu'ar ya mike ya nufi saman shumfuɗaɗɗiyar bed nasa.
Mikewa ya yi ya kwanta, yana tsananin kewar Meeshansa, a hankali ya lumshe idanuwansa, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
A gida Nigeria kuwa, Areef yana fita harabar gidan ya ci karo da motar Donal ya dawo daga airport, ya je ya ɗauko Sheikh Sultan, wato limamin masallacinsu na Washington. Iso ya yi wa Sultan ɗin izuwa cikin gida. Kai tsaye bedroom na Lion ya kai shi, sannan ya fita ya je ya sanar da su gwaggon zuwan Sultan ɗin, daga nan ya fito ya nufi waje, mota ya je ya shiga ya bar gidan mai gabaɗaya.
A ɓangaren Mark kuwa, an yi nasarar ɗaura mashi kafafun nasa, sai dai anci bakar wahala, sai da ma aka wuce da shi babban asibiti, a gida abin ya ci tura, Lion ya ce su shirya shi ya dawo Washington ya yi jinya a can, dan sun fi kwararrun likitoci da zasu kula da shi sosai, so yanzu ana shirye-shiryen ne, Brr Naurat ta ce yakamata kafin Mark ya koma Washington, to a ɗaura aurensa da Anaya, ya karɓi kalmar shahada, sai a ɗaura auren kawai su wuce tare da ita, wannan shawara da ta yanke kowa ya yi na'am da ita, dan ita ma Anayar ta damesu da kukan ciwon Mark ɗin, kukan yanzu daban na anjuma daban, ga shi daddynta ya hanata zuwa asibiti wajen Mark ɗin, sau ɗaya ta je ta rinƙa yi mashi kuka, yana fama da ciwo kuma ga kukanta, da wanne zai ji? Shi ne suka hanata zuwa kawai, sai dai ta yi ta takura masu da kukan a gida.
Abba, Abbi, daddyn Anayar, daddyn Jelly yau dukkansu za su koma gidajensu, sai dai za su bar Anaya a wajen Brr Naurat, Lion ya ce su bar Brr Naurat da Dr Salman a gidan nasa, shi ne yasa suka barsu, an bar Anaya, Aafia kuma zata tafi da Abbinta, baiwar Allah har yanzu dai sauki bai samu ba, yanzu haka asibiti zasu fitar da ita waje, tana jin duk abin da za su faɗa, bata manta kowa ba, magana ne dai bata yi masu, shiru shiru ta koma.
Sai misalin karfe 1:20 Aseef ya farka daga barcin da suke ta zubawa tun bayan sallar asuba. A hankali ya waro idanuwansa, idanun nasa sun yi jajir da su, har sun ɗan kumbura, saboda barcin da ya rinƙa zubawa kamar ba gobe.
A hankali ya kai kallonsa gefensa, har lokacin Akila tana zuba barci bata tashi ba. Nisawa ya yi tare da yunkurawa ya mike zaune, cikin wani irin kasala jikinsa duk zafi yake yi mashi, a hankali ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasan bed ɗin. Da kyar ya iya mikewa tsaye, a hankali ya fara jan kafafun nasa ya nufi toilet, sai aikin turo baki yake yi kamar wanda aka yi wa dole ya tashi. Ita kuwa Akila barci sai abin da ya ci gaba, dan ita ta fi shi gajiya.
Wanka ya yi tare da fitowa ya shirya cikin pajama launin maroon color, sannan ya shunfuɗa dadduma ya gabatar da sallar azzahar, bayan ya idar ya fito dan ya je wajen gwaggo.
A nan ya isko Sheikh Sultan yana yi wa Rimsha addu'a, ta kwanta shiru kamar bata a wajen, a zahirin gaskiya ba shiru ta kwanta ba, Malika ce ta danneta, dan bata son ta ɗaga masu hankali, amma banda haka wannan tofin da ake yi mata ɗin ba karamar haukata matsafan da suke tattare ita ya yi ba, da Malika ta kyaleta,