Showing 12001 words to 15000 words out of 270744 words

Chapter 5 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2922

shirinta na tafiya school.

Bayan ta kammala ne ta nufi kofar fita, a nan ne ta ga wayarta a kasa kaca kaca, sai lokacin ta tuna da time da wayar ta faɗi daga hannunta. Duƙawa ta yi ta fara haɗa wayar. A saman table ta ɗaura shi, sannan ta fito hannunta na rike da key ɗin motarta, da kuma wata yar jaka karama, kanta sam babu ɗankwali kamar ba ƴar musulma ba.

After some hours. Zaune take a cikin class tana duba wasu handouts dake a gabatan, Cherish bata kariso ba tukunnan. A zahirin gaskiya ba karatu take yi ba, tunanin Dr William kawai take yi, wani sabon son shi ne yake kara shigarta. Idan ka ganta zaka yi tunanin karatu take yi, ita kaɗai tasan me take yi.

Ta yi nisa cikin duniyar tunanin da ta afka, kamar daga sama ta ji an rufe mata idanu ta baya.

Cool murmushi ta saki kafin ta ce "My Dr me hakan?". A hankali ya zame hannun nasa daga idanun nata yana faɗin "Waye ya ce mani ni ne?". Ya yi maganar yana zagayowa ta gabanta. Sanye yake cikin wasu shegun kaya na manyan yara, crazy jeans ne mai bala'in tsada irin wanda Areef yake son yawan sakawa, sai high neck t-shirt irin wanda Lion yake son yawan sakawa, har wa yau wuyarsa na ɗaure da wanan diamond chain ɗin mai matukar kyau. Yau dai ya saki gashin kansa bai ɗaure ba, kamar kullum black glass ce a face nasa.

Abin da yasa suke son saka black glass shi da Lion shi ne, basu son yawan kallo, jama'a suna yawan tsaresu da idanu, dan kalar idanunsu abin so ne da kuma abin ban sha'awa ga mutane, ko a cikin turawa da wuya ka sami mai sky blue eyes masu girma dara dara suna kyalli da kyau tamkar nasu, so jama'a suna takura musu da kallo, hakan tasa suke yawan sanya black glass dan ma kada ayi ta kallonsu.

Kusa da ita ya zauna yana ɗan rungumota a jikinsa. Gabaɗaya jama'ar dake cikin class ɗin suna karatu, sai da suka saki ido da baki suna kallonsu, ko da sunan wasa, basu taɓa ganin Dr William yana magana da maza ƴan uwansa bama bare mace, idan ka ji yana magana a school ɗin, to faɗa yake yi da wani, dukan ɗan mutun yake yi, dan fa mafaɗaci ne over ga zafin rai da taurin kai, boss ɗin ne da gaske.

Shi kuwa ko kallo jama'ar cikin class ɗin basu ishe shi ba, sai ma hannu da ya sanya ya zame pil ɗin da ta makale gashinta da shi yana faɗin, shi baya son ta ɗaura gashin nan, yau saboda ita yasa bai ɗaure nashi ba, dan haka ita ma ta bar nata a haka. Jan dogon hancinsa ta yi tana murmushi ba tare da ta yi magana ba.

Haka suka kasance cikin so da kauna tare da nunawa juna kulawa har Cherish ta kariso ta samesu. Ta ji tsoro kuma ta sha jinin jikinta na ganin gwaggo da Dr William a tare, ita dai ta san kullum cikin faɗa suke, abokan faɗa ne, amma ya aka yi lokaci guda suka zama abokai?. Ta tambayi kanta.

Ganin bata da amsa ne yasa ta kariso wajen cike da tsoro da ɗar ɗar. Ko da ta zo kallo wannan bata samu daga wajen Dr ba, tamkar bai san da ita a wajen ba, sai kallon gwaggo kawai yake yi ba tare da ya yi magana ba, dan bashi da yawan magana!.

Can ya ciro sabuwar waya a kwalinta ya ajiye mata a gabanta yana faɗin ga wayarta da ya sanyata ta fasa daren jiya. Bin wayar da kallo ta yi, waya ce iya waya, ta haɗu sosai, ga tsada na wuce misali. Hannu ta kai ta ɗauka tana murmushi. Shi dai ban da wannan kallo babu wani abin da yake binta da shi.

A takaice haka suka kasance har tsawon shakara ɗaya, soyayya mai zafin gaske ne a tsakaninsu, kullum cikin kara kaunar juna suke yi, a cikin shakara ɗayan nan da suka yi, daga ƴan uwan gwaggo har nasa ba wanda ya san da suna tare, babban abin dubawa a soyayyar tasu shi ne yanda suka saki jiki wa juna, wani lokaci a gidanta yake kwana, suna romancing junansu son ransu, duk da basu taɓa kwatanta saduwa ko da sunan wasa ba, amma fa suna wuce gona da iri a wajen wasannin nasu. A wannan shekara ɗayar ta je gida hutu sau ɗaya, sai dai bata wani jima ba, sati ɗaya ta yi, shi ma a daddafe ta yi shi dan tana kewar Dr, sam hankalinta baya kan mutanen gidan, bata ma lura da Dr Salman ya kara aure ba, kanta na rawa sosai a lokacin, sam bata bi ta kan amarya ba, bata sami su Abba a gidan ba, kuma bata tambayi ina suke ba, dan a tunaninta, suna makaranta, harta daddyn Rimsha lokacin baya nan, shi ma bata neme shi ba, dan ta ɗauka yana school shi ma, bata san cewa yama bar gidan bakiɗaya ba, dan lokacin su Abba sun yi mishi wannan sharrin ya bar gida, daddyn Anaya kawai ta samu a gidan, sai daddyn jelly da yake karami, kullum tana manne da waya a kunne suna hira da Dr, ko kuma tana chatting da shi a Whatsapp, ba dare ba rana aiki ɗaya. Naurat baiwar Allah, tana fama da kanta da wahalar amarya, sam bata ta kansu gwaggon, ko da gwaggon ma ta ji Dr Salman ya yi aure, ko a jikinta, ita sam bata tare da kowa sai Dr.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*



E3



Haka ta yi hutun sati guda a daddafe ta dawo, ko da zata dawo, sai da Naurat ta yi mata faɗa sosai tare da nasiha mai ratsa jiki, sannan ta bata makudan kuɗaɗe, shi ma Dr Salman lokacin yana cikin hayyacinsa, dan idan baku manta ba, bayan tafiyar daddyn Rimsha sun sake samun jituwa da Na'urat har aka sami cikin Alex. To shi ma ya zubawa gwaggon makudan kuɗaɗe a account nata, tare da yi mata nasiha a kan ta kula da kanta kuma ta ji tsoron Allah a duk in da take.

To kawai ta amsa musu da shi, amma sam nasihar bai shiga kunnenta ba. Har ta koma bata haɗu da su Abba ba, kuma bata tambayi ina suke ba, a lokacin yes suna school basu dawo hutu ba, dan idan baku manta ba, dama hutu suka zo gida har wannan abin ya faru a tsakaninsu da daddyn Rimsha, to yanzu sun kowa makaranta.

Shi ma daddyn Anaya yana ta fama da school bai bi ta kan gwaggon ba, a takaice dai kowa yana fama da kansa, hakan ce tasa har ta koma ba su haɗu ba

GWAGGO

Tana dawowa daga hutu suka cigaba da gashi a ɓangaren soyayarsu ita da Dr William, sam bata hana shi ya juyata yanda yake so, ya yi wasa da ita, sai dai daga cibiyarta zuwa sama kawai ta bashi dama, ta hana shi kasan sam, dan tana mutuwar tsoron Dr Salman, saboda shi ma mutun ne mai tsananin zafin rai idan aka yi mishi ba daidai ba, to dan shi take rage wasu abubuwa, take kamewa.

Yanzu suna da almost shekara ɗaya da watanni a tare da Dr William, suna zuba soyayarsu, kullum tamkar ranar suka fara haɗuwa, a koda yaushe begen juna suke yi, wasa wasa har suka zama abin kwatance a cikin school ɗin nasu, kowa da su yake kwatance ta ɓangaren soyayya. Sai dai har lokacin fa Dr William dangerous boss ne, dan baya ɗaukar raini, ko kallon gwaggo mutun ya yi sai ya yi mashi hukunci, ba shi da sauki sam.

Yau babu school ta gama duk abin da zata yi a gida, ta yi wanka tana shirye cikin wando short zuwa gwiwa, da ƴar ƙaramar riga zuwa kugunta mai ƙaramin hannu. Tana kwance a saman bed nata tana aikin latsa waya, chatting suke yi da Dr William, dan idan ka ganta da waya a hannu, to da shi take magana, ko daddyn Rimsha da daddyn Anaya da suke ƴan lelenta ma, yanzu ta daina nemansu a waya, a baya sai ta kirasu fin awa uku suna hira, dan duk cikin ƴan uwan nata, ta fi kaunarsu sama da komai, dama idan baku manta ba, na gaya muku twins ɗin nan, Azharuddin da Nawazuddeen mugun shiga rai gare su, duk in da suka zauna, sai an kaunace su, aji ba'a son rabuwa da su, to ita ma Gwaggo haka ne, amma yanzu tana manne da Dr William, tama manta yaushe da rabon ta da ta kira gida, ko an kirata daga gidan kuma, sai ta ce musu tana karatun exams, ko dai tana yin wani abin, bata taɓa bawa kowa lokacinta idan ba karatu da kuma Dr William ba.

Sai dai abin jin daɗi a tarayyar tasu da Dr ɗaya ne, wato duk wannan soyayya da suke zubawa, sam basu wasa da karatu, suna dagewa sosai, idan Dr William ya zo first, gwaggo ce second, idan ta zo first shi ne second, ma'ana dai duk in da ɗaya ya saka kafa a karatu, to ɗayan ma yana biye da shi, kamar abin haɗin baki, amsoshinsu a Exams ma iri ɗaya ne, dan tare suke karatu, wani lokaci a gidanta yake kwana, su kwana karatu. Rashin wasa da karatunsu shi ne nasarar da suka cinma a soyayyar tasu, kuma shi ne kawai soyayyar tasu bai sa sun yi patali da shi ba.

A ɓangaren Dr William ma, iyayensa har sun gaji da tambayar a kan sauyawar da ya yi, yanzu sun zuba mashi idanu ne kawai suna kallon shi, sun yi, sun yi, su bibiyi abin da yake yi, amma yaki basu dama, hakan tasa dole suka hakura suna binshi da idanu kawai.

STORYN

Ta tada kai da pillow a saman bed nata daga ita sai wannan short ɗin wandon nata da kuma ƴar riga, ta rungumo pillow a kirjinta tana aikin chatting da shi. Sai zubawa Dr nata shagwaɓa take yi a kan ita tana kewarsa, sai biye mata yake yi yana bata hakuri.

Tamkar daga sama ta ga ya turo kofa ya shigo, dan yana da key a yanzu. Hakan na nufin duk chatting da suke yin nan ashe yana kan hanyar zuwa, kawai yaki gaya mata ne.

Da gudu ta diro kasa daga saman bed ɗin ta nufe shi, buɗe mata hannu ya yi ta faɗa jikinsa tana dariya. Rungumeta sosai ya yi yana ɗan shafa bayanta. Laluɓar hannunta ya yi a in da ya sanya mata wani shegen diamond ring mai bala'in tsada, nan take hannun nata ya fara kyalli. Bai bari ta fara zuba mishi tsalle da murna ba kawai ya ɗauketa cancak sai saman bed ɗin, tamkar dama a kusa yake.

Romancing na juna suka fara yi kamar yanda suka saba, sai dai a yau dai Dr William ya zo har wuya, ya kasa jurewa ya danne sha'awarsa, dan yana tsananin sha'awarta over.

Hana shi ta yi a in da ta saka mashi kuka, dole ba dan ya so ba ya rabu da ita tare da barin jikinta ya koma gefe guda a saman bed ɗin ya zauna, ya haɗa kai da gwiwa yana sauke numfashi a hankali hankali.

Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta dawo kusa da shi. Hannu ta kai tare da ɗago kan nasa tana ambatar sunansa.

Kasa amsa mata ya yi, saboda mawuyacin halin da yake ciki. Rungume shi ta yi a kirjinta tana bashi hakuri tare da saka mishi kuka, sam ba zata iya jurar ganin shi a cikin tashin hankali da damuwa ba, kun san zuciyar masoya! Ba abin da ba zasu iya yi wa junansu ba, in dai sun mace a wannan soyayyar tasu! To ita dai soyayyarsa ta yi mata mummunar kamu, makauniyar soyayya take yi mishi.

Haka shi ma a nashi ɓangaren, makauniyar soyayya yake yi mata! Ba zai iya ganinta cikin damuwa ba, duk yanda ya kai ga son abu, in dai bata so, to ko zai mutu! Haka yake hakura, sai dai ya yi ta fama da azabar raɗaɗi a cikin zuciyarsa, amma ba shakka zai hakura.

Ganin tabbas ya shiga tsakanin damuwa sosai na wuce misali ne yasa ta ce to ya zo ya biya bukatar tasa kawai, tana magana tana kuka.

Da kyar ya iya ɗago kallonsa izuwa gareta, hannu ya kai ya fara goge mata hawaye, muryarsa na rawa ya fara magana. "Ni da gaske nake sonki my beauty, ba nason abin da zai ɓata maki rai, ki bari kawai na hakura kin ji ko? Yanzu dai ki gaya mani, me zan yi na sameki? Ya zan yi ki zama matata mallakina, sai nayi yanda nake so dake babu wani sha'amaki?".

Cike da murna ta ce "Aure, aure ne kawai zai sanya na zama mallakinka ba wani shamaki, hakan kuma ba zai taɓa yiwu ba har sai ka zama musulmi, ba zai yiwu na aureka kana krista ba!". Cikin sauri ya ce mata "Na yarda, na yarda zan zama musulmi, ni dai kawai ki zama mallaki na!".

Sosai ta rungume shi tana murna tamkar ba gobe. Ganin tana murna ne yasa shi ma ya rungumeta sosai yana manna mata kiss a lips nata.

Haka suka kasance tsawon mintuna 20, sannan ya ce ta shirya bari suje gidansu sai ya gayawa mummynsa da daddynsa abin da ya yankewa kansa, a lokacin kuma TAG yana koyan tafiya.

Hakika ta yi tsananin murna, zata mallaki Dr ta. Cikin hanzari ta miƙe tare da faɗawa cikin toilet. Wanka ta yi cikin hanzari, yana zaune yana jiranta, amma shi kaɗai yasan halin da yake ciki na sha'awarta. A gabansa ta shafa Lotions nata kamar ko yaushe, sannan ta wuce zuwa dressing room.

Yau da yake ya ce gidan iyayensa za su je, sai ta mutunta su ta hanyar yin complete dressing mai kyau, wandon jeans ta sanya a ciki, tare da wani T-shirt da ya saya musu iri ɗaya da shi.

Bayan ta gama sai ta sanya after dress baka a saman kayan, dan ta ɗan suturta jikinta, still dai kanta babu ɗankwali ta fito.

Cike da tsantsar so da kauna tare da kulawa ya fara yabon irin kyan da ta yi, murmushi ta yi kafin ta taho ta faɗa jikinsa. Yana ƙoƙarin fara kissing nata, ta dakatar da shi ta hanyar sanya hannu ta rufe mishi baki.

"Haba my Dr, wai kai baka gajiya da shan lips na ne?".

Lumshe shanyayyun idanuwansa da suka sauya launi ya yi, cikin sanyin murya ya bata amsa da cewa "My beauty, ya za'ayi na gaji da shan lips naki? Ai ba zan taɓa gajiya ba, ni dai yanzu Please ki bani ko kaɗan ne, kin ji ko my wife?".

Harara ta wurga mishi kafin ta ce "Ai ba'a ɗaura auren ba ko?".

Nisawa ya yi yana mai faɗin "To ai an kusa, kin ma tuna mini, tashi muje wajensu mummy da wuri, daga nan sai mu wuce a ɗaura aure ko?".

Zata yi magana ya sanya mata yatsa a saman lips nata yana faɗin ta tashi su tafi da wuri. Ba musu ta tashi suka fice daga gidan.

A motar nasu ma, basu hakura ba, sai da suka ɗan yi romancing junansu kafin ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa, shi kuma ya kunna motar suka bar gidan.

(Yanzu kun fara ganin daga in da TRIPLETS suka yi gadon nasu jarabar ko? Da uwa da uba dukka ba sauki😂 mu je dai zuwa.)

Yau dai Gwaggo ta zuba kauyanci na ganin gidansu Dr, bata taɓa tunanin daga wannan aljannar duniya ya fito ba, tana tunani dai irin normal masu kuɗin, ɗan dai'dai ɗin nan, bata san mahaukatan kuɗi karesu ba.

Sake baki ta yi kawai tana ta kallon gidan abinta. Sai da ya ja hannunta suka nufi ciki, lefter suka hau zuwa hawa na uku, dan ya san confirm su mummynsa suna wajen, dan sun fi yawan zama a wajen. Ita dai sai mamakin gidan take yi, dan gida ne irin high rise building ɗin nan, ga wani haɗaɗɗen lefter mai matuƙar kyau, abin ba'a cewa komai, dan ya wuce tunanin mai tunani, idan na ce zan tsaya zayyana muku gidan Jacob Roshan ba ƙaramin aiki bane, dan kuwa sai mu kare book nan kaf a kansa kawai, dan fa ya haɗa komai, babu abin more rayuwa da ɗan adam zai buƙata babu a cikin gidan.

Sai yanzu gwaggo ta sake yarda cewa so gudan jini ne, yanzu idan ban da so me Dr William zai yi da ita? Irin wannan duniyar da suke ciki, ga kuɗi, kyau, isa da takama, abin ba'a magana.

Tamkar yanda Dr ya faɗa na cewa iyayensa suna hawa na uku, a can ya samesu, suna zaune a palonsu tare da Uncle Herry, Josephine da TGA, sai zuba hira suke yi. Jacob Roshan yana shan green tea, ita kuma mummynsu tana faman cin wasu korayen ganyayyaki masu karawa jiki lafiya da jini, ga wani makeken Tv dake gefe guda ta gabas maso tsakiya yana magana.

Tun da suka shigo palon gwaggo take bin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login