Showing 264001 words to 267000 words out of 270744 words

Chapter 89 - Triplets Book 4 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2936

ɗaura auren Uncle Herry da Ummin Dr Nawid ɗin, dan ta gama idda, kuma dama tun da ta je Washington time ɗin haihuwar su Jehan ya kamu da sonta da ya ji cewa mamar su John ta mutu, sai ya ji yana sha'awar ya auri ƴar Nigeria kamar yayansa Dr William kenan, duk da cewa shi Dr William kusan za'a ce ba ƴar Nigeria ya aura ba, dan gwaggo dai ƴar Russia ce, bata wani zauna a Nigeria ba koda suka dawo ɗin ma, kada ku manta da ta koma wajen daddyn Rimsha ma a Dubai suka zauna kafin daga baya su dawo gida Nigeria.

So a takaice dai sai da aka ɗaura auren Uncle Herry da Ummi kafin so dawo Abuja, kuma ya taho tare da matarsa, Ummi ta baro Katsina kenan, Allah mai kyauta mai kari, mai yin yadda yaso, tana son Aafia sosai, ga shi Allah ya sake haɗasu waje guda da Aafiar, sun sake curewa a family guda abin ya burge matuƙa.

A ɓangaren su Lion kuwa, kasancewar da jirgi suka tafi Ilorin ɗin, sai suka isa da wuri, kai tsaye gidan gwamna suka sauka, sai da suka ɗan huta kafin su bada sanarwar zasu je in da suka zo domin shi.

Dankara dankaran motoci goma sha biyar gwamna ya fitar dan a kai'su in da za su je ɗin.

Har kofar gidansu Kaunar aka kai'su, dan Rimsha bata mance da sunan unguwar ba, suna zuwa unguwar kuma ta gane gidan.

Tun da suka dimfaro unguwar jama'a suke ta kallon motocin, domin tsadaddun motoci a jere irin haka basu saba zuwa su wuce ba, ga kuma uban jiniya da motocin sojoji biyun da suka rakosu suka saki, jiniya ta karaɗe ko'ina tamkar filin yaki zasu tafi.

Ganin motocin sun yi parking a kofar gidansu Kausar ne yasa jama'a suka fara cincirindo suna fitowa daga gidajensu ne shagunansu ne, dan su kalli me yake faruwa.

Rimsha sarkin kauɗi, har ta kai hannu zata buɗe kofar motar ta fita Lion ya riƙota.

Da mamaki take binsa da kallo, ɗaure fuska sosai ya yi yana faɗin ina zata je?.

Ganin babu alama sauki a tattare da shi ne yasa ta nutsu, cikin sanyin murya ta bashi amsa da cikin gidansu Kausar.

Kallon driver da yake tuƙasu ya yi, cikin bada umarni ya ce. "Go and call Kausar for her".

A hanzarce bodyguard ɗin ya amsa da okey sir, sannan ya fito da sauri ya nufi cikin gidan.

Sojojin da suka rakosu kuwa, suna yin parking na motocinsu suka diro kasa daga saman bayan motocin, cikin ƙanƙanin lokaci suka kewaye arear wajen da bindigunsu dan tabbatar da tsaro, da gwamna ya so a tashi helicopters ne ma dan bawa Lion ɗin tsaro mai inganci, amma sai Lion ɗin ya ce mashi a'a baya bukatar hakan, iya motoci biyu na sojoji sun wadacesa, dan shi ba rago bane ba........😌

FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA CE.....✍️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥




TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*



E55



"Noorish a kirata kuma? Tom ai ba ita kaɗai bane, ina son in ga Iya ma".

Jawota jikinsa ya yi yana faɗin. "Koma waye kike son gani za'a kirasa ya zo nan, ba zaki shiga wannan local wajen ba, da na san a irin wannan kazamin wajen suke ma ai da ba zan kawo ki ba, sai dai nasa a ɗauko maki su ki gansu, amma saboda rigima irin taki sai da kika wahalar da ni kika kawoni dirty place ɗin nan".

Wai shi Lion bai san cewa ita Kausar ji da kanta take yi a matsayin big girl bane da zai zage masu unguwa?😂

Shiru ta kwanta a jikin nasa har bodyguard ɗin ya fito daga cikin gidan a tare da Kausar da kuma Iya, Kausar ɗin tana rike da wani baby boy mai kama da boda Jami'u, bakin kirin da shi.

Ganinsu yasa Lion ɗin yasa aka sauke mata glass ɗin motar ta side ɗinta, sannan ya ce ta tashi su gaisa dan shi ya gaji da kallon wannan kazamin unguwar, yana son su tafi.

Cikin zumuɗi ta tashi daga jikin nasa tana ambatar sunan Kausar ɗin.

Sam Kausar ɗin bata iya gane ta ba, saboda ba karya Rimsha fa ta canza gabaɗaya, ba zata taɓa cewa ita ɗin bace.

Sai da ta yi wa Kausar ɗin bayani, sannan ne ta iya gane ta, abinku da yarabawa, ihu Kausar ɗin ta fara zundumawa tana ambatar Rimsha! Rimsha!.

Sai murmushi Rimshar take yi, taso ta fita su gaisa da kyau, amma Lion ya hanata, wai ba zata sauka a cikin dattin nan ba, dole ta hakura suka gaisa tana daga cikin motar.

Kausar ɗin taso bata labarin bayan rabuwarsu da komawarta Daular Mutuwa da ruguje Daular Mutuwa da wasu bayin Allah suka yi suka sa ta fito, da cikin shegen da boda Jami'u ya yi mata ya gudu Lagos ya barta da yaro wai ya tafi neman kuɗin da zasu yi aure, da dai sauransu. Amma ina Lion ya ce su wuce, dan shi bashi da lokacin tsayawa shirmen matan nan, Rimsha ta so jin labari, amma ina ba dama, haka dai ta ji labarin sama sama.

Ta taya Kausar ɗin alhinin abin da suka faru, sannan ta ce Lion ya basu kuɗi mana, yana ta aikin latsa wayarsa tun lokacin da su Kausar ɗin suka zo, ba tare da ya ɗago kai ba ya ce ta ɗeba ta basu mana.

Sai ɗaga mashi gaisuwa Kausar da Iya suke yi, amma ina ko kallo basu isheshi ba, tamkar bai san da sun zo wajen ba, sai ya kama aikin latsa wayarsa kawai, sai kallonsa Kausar take yi, tana son ta yi wa Rimsha gulma ta tambayeta waye shi, amma tana tsoron shi, saboda bata ga fuska ba, kun san yadda face nasa take ai? Babu alamar wasa, ga kwarjini mai rikitar da mutane, hakan yasa Kausar ɗin ta sha jinin jikinta ta haɗa malaman jikinta ta nutsu.

Cikin zumuɗi Rimshar ta ɗebo maƙudan dollars daga aljihun Lion ɗin ta miƙawa Iya, sannan ta sake ɗebowa ta miƙawa Kausar ɗin. Abin ku da yarabawa, har kasa iya ta zube gwiwowinta tana zuba uban godiya.

Umarnin Lion ya yi wa drivers ɗin a kan su tafi. Ba ɓata lokaci suka tashi motocin a dubu suka bar unguwar.

Har suka ɓacewa ganinsu Iya da Kausar suna zube a saman gwiwowinsu suna aikin zuba godiya, iya har da kukanta da hawaye, dan ba kuɗin wasa Rimsha ta basu ba, idan zasu canza wannan kuɗi a kallah zai kai 5m, dan dollars ne, Lion bashi da wani kuɗin da ya wuce dollars, ga shi dama suna cikin halin babu, abinci ma idan sun sami na safe basu sa ran zasu sami na rana, sai ga shi yau Allah ya aiko masu Rimsha ƴar albarka ta zo ta basu kuɗin da basu taɓa tunanin zasu same shi ba a rayuwarsu, ai dole su yi kukan murna.

Suna barin unguwarsu Kausar kai tsaye airport suka nufa, dan su koma Abuja.

Su Akila kuma sun je Kaduna gidan Abbanta, a nan ne Ammienta take sanar da ita ɗan uwanta Duna ya dawo, ashe dama bai mutu ba, kuma ya musulunta shi ma, ya bar harkar tsafi, sannan ya gaya mata gaskiyar cewa Queen ba Mahaifiyarsu bace, yayarsu ce da suke uwa ɗaya uba ɗaya, dan haka ba Queen ce ta haifesu ba, sosai Ammien ta yi mamaki jin hakan, dama ita ta ra'ina girman Queen ɗin nan a ce uwarsu ce, ashe uwarsu ta mutu tun kanwar Ammien tana jaririya, kwananta uku da haifar kanwar Ammien ta rasu, Queen kuma ita ce babbar yayarsu, shi ne yasa ta rikesu tamkar ita ce uwarsu, dan ta girmesu sosai. Alhaji Mustapha mijin Hjy Zainab ma ya dawo, ashe bawan Allah yana a tare da Duna, tare suka gudu daga Daular Mutuwar lokacin da Queen ta yi ƙoƙarin kashesu, sun samu sun kuɓuta da kyar, sai dai ita Hjy Zainab kam ta mutu, Queen ta kasheta kamar yadda ta kashe Amarya matar Dr Salman, sai dai muce Allah ya sakawa Hjy Zainab kasheta da aka yi bada hakkinta ba, ita kuma Amarya dama mugun iri ce, sai dai muce masu hali irin nata su yi ƙoƙari su tuba su dai'na, ko kuma suma karshensu ta yi irin ta amarya ko fin haka.

Sosai Akila ta yi murna da jin cewa dan uwan mamanta Duna ya dawo, kuma ya musulunta, ko ba komai yanzu tana da uncle guda ɗaya musulmi.

Sun je gidan Abbin Irfan ma, a nan Abbi ya sanar da Aafia cewa kidnappers sun sako kawarta Rufee ta dawo gida, shi ma last week ya samu labari, amma sun yanke mata kafa guda ɗaya, dan kafar ta ruɓe, da kyar ma suka sakota, dan sun mayar da ita parkarsu ce, bada aure ba suke kwanciya da ita, kuma ba mutun ɗaya ba, wannan ya yi ya bawa wannan, tamkar wata karya haka suka mayar da ita, kawai Allah ya kaddara tana da rabon fitowa daga hannunsu ne ma yasa ta fito, badan haka ba da ai ita kam shikenan tata ta kare, yanzu ma cututtuka kala kala ta ɗauko, sai dai muce Allah ya bata lafiya ya kawo mijin aure, masu hali irin na Rufee ishara gareku, ku tuba ku da'ina.

Aafia ko a jikinta da ta ji wannan labari, sai ma cewa da ta yi Allah ya kara.

Sosai Aunty ta kara yi mata nasiha a kan ta zauna ta rike mijinta da kyau, ga shi ta samu miji jarumi ɗaya tamkar da dubu, ga kuɗi, mulki, ga shi soja, sannan ba karo mata kishiya zai yi ba, dan su mata ɗaya suke aura, dan haka ta kula da shi sosai su mori kuruciyarsu, ita ma Aunty ta haifi ɗanta namiji ɗaya. Godiya sosai Aafiar ta yi mata.

Misalin karfe 1 aka daura auren Irfan da Pinky a kofar gidan Abbin, sannan suka je gidan Azharuddin Bature, a nan aka ɗaura auren Handsome da Zaira, daga nan suka wuce Kano wajen daddyn Jelly, nan suka sami Ayla da babynta kyakkyawan gaske, ita ma Maman Ayla tana gidan, dan dama daddyn Jelly ya mayar da ita wajen iyayenta ta nemi yafiyarsu, ta kuma yi sa'a albarkacin daddyn sun yafe mata, to shi ne ta cigaba da zama a gidan nasu, da Ayla ta haihu ne sai ta zo zama da ita.

A hanyarsu ta dawowa Abuja daga Kano ne Jehan ta kalli A'isha ta gidan Hjyr daɗi a kan hanya kamar mahaukaciya tana tafiya, sai tsince tsince take yi, Allah sarki ashe har Kano su Hjy daɗi suka zo suka jefar da ita, ƙwaƙwalwarta ya taɓu.

Sosai Jehan ɗin ta ji babu daɗi, sannan ta roki Areef da yasa a kaita asibiti a nema mata lafiya.

Hakan kuwa aka yi, yasa sojoji suka ɗauketa dan su kaita asibiti.

Akil da Umaisha dai suna Madina hankalinsu a kwance da ɗan babynsu gwanin ban sha'awa.

Sun je kauyensu Maryam, a nan suka tarar da babanta ya mutu bayan fama da ya yi da jinya na tsawon lokaci, cutar daji ce ta kashe shi, ɗan banza ko alhakinsu Maryam ɗin ma ai ba zai barshi ba, haka zalika ita ma yayarta Allah ya yi mata rasuwa shekara ɗaya da suka wuce, Maryam ta sha kuka sosai da sosai, sai rarrashinta Sir Safwan yake yi. Masu hali irin na Baban Maryam aya gareku! Tun lokacin bai kure maku ba ku tuba!!.

Ita kuma Adiva sun yi sa'a da suka je Maiduguri sun sami mamanta a can, dan haka uncle Shitu ya ɗauko matarsa suka dawo Abuja.

Gaskiya ba karya family fa sun yi ziyara sosai, sun leƙe yan uwa da abokan arziki sosai. A takaice dai wata guda suka yi a Nigeria kafin su tattara su koma ƙasarsu.

Lion ya cigaba da renon cikin Rimsha yana tarairayar kayarsa har sai da cikin ya bayyana kowa ya gani.

Sun sha ruwan mamakin ganin cikin nata, a lokacin cikin nata ya kai almost 7 month, abin da yasa kuma basu gane da wuri ba, kowa dai yasan Rimsha bata fita, ko nan da part ɗin gwaggo Lion baya barinta ta je, kullum zaman ɗaki kamar wata mai takaba, matar kowa daga cikin QUADRUPLE suna yawonsu a cikin gidan, amma ban da ita, sai tafi sati bata fito daga cikin bedroom ba, abin ku da mai ciki, daga barci sai wanka, cin abinci da sallah, to da yake kowa yasan halin Lion da bakar kishi, sai babu wanda ya damu kansa ko ya yi tunanin wani abin a kan rashin fitowar tata, kawai sai suka zuba masu ido, basu ankara ba sai ganin Rimshar suka yi da katon ciki kamar me.

Murna iya murna sun yi, Brr Naurat ta rinƙa yi wa Lion tsiya, abinku da Turawa ba kunya ke garesu ba, haka ta rinƙa yi mashi tsiya tana faɗa mashi cewa ashe abin da ya aikatawa ƴar mutane kenan yasa yake ɓoyeta a daki, sai dai ya ce mata ya yi ɗin ba kayarsa bace?.

Dukkansu ba mai alamar kunya a idanunsa ko kaɗan, waɗan nan family guda biyu suna sha'aninsu son ransu.

Rayuwar farinciki ya wuce baki ya faɗa suke yi, Anderson da His Excellence Lion ya turasu bakin gida, wani gidan kurkuku ne da yake a cikin teku, ba halin gudu daga wannan gida, dan a tsakiyar ruwa yake, ga bakar azabar da ake ganawa prisoners ɗin, abinci sau ɗaya ake basu a rana, kuma abincin ma rabin plat ne, ga uban duka da suke sha na safe daban na yamma daban, wannan gida shi ma Areef yasa aka jefa Hjyr daɗi da kuma Zinariya and Ƴar gwal bayan ya ruguje gidan nasu kenan.

Rungunar sojoji ya sa suka dira a Nigeria bisa umarnin shugaban kasa, yasa suka yi pata pata da gidan Hjyr daɗin, aka saki duk yaran da suke a ciki dan su koma gidajen iyayensu, sannan suka kwaso Hjyr daɗin ita da masu goya mata baya, aka zubasu a bakin gida, wannan bakin gida sai mutun ya gwammaci mutuwa da shiga gidan, dan ɗakunan dake a cikin gidan ma a tsaye bawa yake kwana, ba halin kwanciya, kafafu duk su kumbura, idan kunga bawa ya miƙe kafafu ya ɗan kwanta, to sai da safe idan sun fito tsakar gidan, kuma ba kullum ake fito da su tsakar gidan ba, a sati sau biyu suke fitowa, sauran kwanaki duk suna cikin ɗaki a tsaye kamar gumaka, suna ganin izayar rayuwa. To masu hali irin nasu aya gareku, mugu dai karshensa bata kyau!!.

Su kuma family yanzu komai zam zam, rayuwa mai tsabta tare da farinciki mai kawa suke yi har izuwa ranar haihuwar Rimsha, a lokacin kuma Maryam ta haifi yaro ɗaya, Adiva ta haifi yarinyarta mace, Aafia ta haifi ƴan biyu dukka mata, Ummin Dr Nawid tuni ta karɓe yaran wai ita zata renesu, Allah sarki tana son yara sosai, ga shi har yanzu Jellynta kuma Jellyn Yah Imran bata haihu ba.

Gida ya kara cika sosai da yara da jikoki, yanzu kowa dakon jiran yaran Lion yake yi.

Tun safe Rimshar take naƙuda har karfe 2 na rana, amma shiru bata haihuwa, da alama ba zata iya haihuwa da kanta ba, hakan yasa Lion ya ce ayi mata aiki a cire babyn kawai, dan hankalinsa ya kai makura wajen tashi, ya shiga damuwa na wuce misali, ya ji ba zai iya jurewa ba, dole kawai ayi mata aiki a cire yaran nan kada matarsa ta mutu.

Dan dole su Dr William suka karɓi maganar Lion ɗin a in da aka shirya tsab aka yi mata aiki, cikin ikon Allah aka ciro mata baby's nata Maza guda uku da mace ɗaya, duk cikin QUADRUPLE ita kaɗai ta haifa masu ɗiya mace, yarinyar tamkar Pinky, ma'ana kamar Lion ɗin, harta kalar idanunta, duk yaran babu wanda ya biyo Rimshar, dukkansu Lion ɗin suka ɗauko, harta kwayar idanuwansu blue eyes ne, sak irin nasa.

Gwaggo baki har kunne, dama burinta kenan, ga shi Lion ya samu ɗiya mace, abin ba'a magana, gwaggo kamar baki ba zai rufu ba, kowa idan ya zo ganin baby's macen yake ɗauka, sun fi son macen sama da sauran mazan, dan sun gaji da rike maza, yanzu sun samu canji, harta su Areef da suka zo ganin yaran macen suka ɗauka, kowa santin macen kawai yake yi, daddyn Rimsha ma macen ya ɗauka da ya zo.

Abin har sai da yasa gwaggo ta ce, kai lafiya kuwa? Kowa idan ya zo sai ya ɗauki macen yana santinta, dole ta rinƙa yi wa yarinyar nan addu'a, idan ba haka ba ai sai a samu matsala. Yarinyar ne ta ɗauko shegen shiga rai irin na mamanta, kowa sonta yake yi, gata jajir irin babanta, kunsan blue eyes kuma da shiga rai da ɗaukar idanu, musamman a wajen kananan yara, sai hakan tasa yarinyar ta kara shiga ran kowa.

Shi kansa Lion ɗin ana ciro yaran bayan an gyarasu macen ya ɗauka, ita ya fara yi wa huɗuba, yau dai bai ce baya son ganin yara ba, wani irin azababben so ma yake yi wa ƴaƴan nasa, sai dai yafi son macen nan, dan wlh ita ce ta fito sak shi sosai tamkar an tsaga kara, ga ɗan bakin nan nata kamar nasa aka cire aka sanya mata, sosai yake jin azababben

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login